ZUCIYA CHAPTER 9

ZUCIYA CHAPTER 9

Yau saura bikin Ashraf da Aneesa wata d’aya da kwana 10, a wannan ranar ce kuma Nafi ta shirya tsaf cikin uniform d’inta, Little tayi kokari wajen koya mata komai, Nafi ta fito fes da ita abin sha’awa ga kayan sunsha guga. A wannan lokacin inba fad’ama akai ba ko hausarta kaji ba tabbas bazaka gane daga riga ta fito ba, Little ta jawo a kwatinta tana cewa ” Zaki tafi ki barni ni kad’ai. “+ Nafi tai murmushi a ranta tace da ina riga bana fita, yanzu nazo nan kuma shima gashi zan koma wani gun. Little ta dafata tace ” Muje Ya Habib na jiranmu. ” Nafi ta kalleta sannan ta d’anyi kasa da kanta tana wasa da hannunta tace ” Maryam bazanje inma yaya sallama ba? ” Little ta d’anyi dariya sannan tace ” kije mana, amma bada ni zaki ba, ni zanje gun Mumy inkin gama sai kizo can mu had’u. ” Nafi ta d’aga mata kai alamar eh sannan ta fito da saurinta, tana tafe tana tunanin me zata cemai, sam bata kula da Asim a zaune akan kujera ba, har ta wuceshi taji ance ” ke dan kut**** baki iya gaisuwa ba? Ko dan zaki tafi wata kucakar makaranta kike tunanin kinfi kowa? ” Nafi wacce tsoro ya rufeta ta kalleshi a tsorace tace ” yahkuri Ya Asim wlh ban kula bane. ” Ya girgiza kai sannan yace ” da alama ma kayan sa miki akai. ” Nafi tai kasa da kanta kawai batace komai ba, ya tab’e baki sannan ya juya kai tare da cewa ” sai aje ayi sallama da dadiron ki. ” Nafi kam bata fahimci me yake nufi sam da dadiro ba shiyasa ma bata damuba, ta juya ta cigaba da tafiyarta a ranta tana mamakin irin zuciya ta wannan mutumin. B’angaren Ashraf tanufa, a hankali ta kwankwasa kofar, daga ciki Ashraf ya amsa da ashigo. A hankali Nafi ta murd’a kofar sannan ta shiga ciki, yana zaune akan kujera rike da laptop da alama aiki yakeyi, bai d’ago ya kalleta ba bare tasa ran zai tanka mata. A hankali take d’agowa tana kallansa sai dai ganin har yanzu hankalinsa nakan laptop d’in ga lokaci na tafiya yasa ta d’aure tace ” Yaya zamu tafi. ” “To Nafisa Allah ya kiyaye. ” abinda ya fada mata kenan har yanzu hankalinsa nakan abinda yakeyi, Nafi ta kalleshi jiki a sanyaye, makullin d’akinsa ta ciro sannan a hankali ta fara takawa har zuwa inda yake, mikamai makullan tai tace ” gashi yaya.” D’agowa yai ya kalleta, idanunsu ne suka had’u gabanta yai wani irin fad’uwa da sauri tai kasa da ido, shikam har yanzu idanunsa na kanta bai kuma amshi makullin ba sai cewa yai “Sanda na baki cewa nai ki dawon da shi in zaki wani gun? ” Nafi ta d’ago a hankali ta kalleshi, idanunsa na kanta hakan yasa ta karayin kasa dakai tare da cewa ” kafin in dawo kayi aure nasan kuma a lokacin baka bukatar aikina. ” Bai san sanda ya saki murmushi ba sannan ya maida kansa kan aikinsa tare da sa hannu ba tare da ya kalleta ba dan ya amsa, hannunsu ne suka had’u da juna, sai dai abin mamaki ya kasa d’auke hannunsa haka itama. Ganin yanda take mutsu mutsu da baki yasa ya rike hannunta tare da makullin. Yanaji sanda ta d’an zabura kad’an shi dariya ma taso bashi, ta d’ago tare da kafeshi da ido, mamaki ne ya kamata ganin hankalinsa ma baya kanta. Idanunta na kansa sam ta kasa d’aukewa, jitai yace ” kallan bai isa ba? ” Da sauri tai kasa da kanta, yace ” ba jiranki ake ba? ” Kallansa tai da mamaki taya za’ai ta tafi bayan ya rike hannunta? Ashraf ya kalleta cikin mamaki yace ” So kike kuyi dare ko da wani abin da zaki fad’amin? ” STORY CONTINUES BELOW Nafi ta d’an yi rau rau da ido tace ” Yaya Hanuna fa? ” Yanda tai maganar ita kanta batasan ta iya ba, ya kalleta sannan ya kalli hannun, sakin hannun ta yai tare da zare makullin, ya kalleta yace “zan ajiye in ko in dawo sai kizo ki amsa. ” Ta kalleshi da mamakin kalamansa, ta daure kawaj sai cewa tai ” Yaya nagode insha Allah bazan baka kunya ba. ” Ya mata wani kallo sannan yace ” kada dai kije ki biyewa kawayen banza, sannan kar ki kuskura kiyi kuka da sunan wai kinyi rashin mahaifinki ko nan. ” Nafi ta d’aga kai jiki a sanyaye, nan tamai sallama ta juya a hankali take tafiya har ta fita daga kofar. Tayiwa Mumy sallama nan Mumy ta bata dubu biyar wai kudin kashewa, itakam Nafi kin amsa tai sai da taga ran mumy ya b’aci tukunna, nan tai godiya suka fito, b’angaren Umma sukaje. Tana zaune a falo, Aneesa na gefe itada kawarta suna kallan wasu kaya, da kyar aka amsa sallamar ta, jiki a sanyaye ta shiga sannan ta tsuguna tagaida Umma sannan tagaida Aneesa da kyar suka amsa suna mata kallan uku saura kwata, Umma tace ” ai anyi dabara da aka saki boarding dan na gaji da ganin yar rigar fulani tana yawo a gidan nan. ” Nafi batace komai ba, Aneesa ta harareta tace ” Allah ya raka taki gona. ” Jiki a sanyaye Nafi ta fito daga b’angaren nan ta karasa kitchen tama su Goggo sallama. A mota ta taradda Little zaune a gaban Mota kusa da Habib suna hira, tasa hannu ta goge fuskarta sannan ta karasa cikin mota. Habib ya juyo ya kalleta yace ” Gimbiya Nafeesa irin wannan jira da aka sani haka? ” Murmushi ta d’anyi sannan tace ” Tuba nake, amma gimbiya ai Maryam ce bani ba. ” Habib ya kalli Little wacce taji dadin kalaman Nafi, yace ” to me kike so indinga ce miki? ” “sunana mana. ” Habib yai dariya yace ” ai ni bana fadan sunan mutum, kowa da sunan da nake cemai. ” Nafi ta kalli little tace ” Little ki zabarmin to. ” Su dukansu dariya sukai, nan Habib ya tada mota, Nafi dama tana baya, ita kuna Little na gaba. Sun fara tafiya Little ta juyo tace ” Kinje kunyi sallama da yayan? ” Nafi tai murmushi tare da dg mata kai, Habib ya kalli Nafi yace ” me yakeyi? ” Tace ” na daiga yana danna abu irin na Little a falo. ” Suka sa mata dariya sannan Habib yace ” Ashraf kenan, yanada kwakwalwa ga iya aiki amma har yanzu na rasa me yake hanashi yin aikinsa. ” Nafi ta kalli Habib da mamaki sai dai batasan me zata tambaya ba, jitai Little tace ” anya ba abin da bane yake damunsa? ” Habib yai ajiyar zuciya yace ” nima ina tunanin wannan, ai ko waye dole ne abin ya zamarmai Karma. ” Kai Little ta jinjina tace ” Shiyasa bana ganin laifinsa in yana fada, itama Mumyn ai…. ” Sai kuma tai shiru. Nafi kam ta kasa shiru ta kalli Little tace ” Me ya sameshi dan Allah. ” Little tai ajiyan zuciya tace ” Nafi ki bari sai kin dawo zan sanar dake.” Habib ya kalli Little baice komai ba. Har suka isa makaranta zuciyar Nafi fal take da tunani kala kala menene ya faru da Ashraf? Ita kanta tana mamakin Mumy da ta auri kanin babansa kuma harda ‘ya a tsakaninsu. Sun shiga makaranta nan Principal ta hadata da wata Copper wacce zata dinga nata extra lessons, sunyi sallama Little ta shiga mota duk tausayin Nafi ya kamata. Nafi kam sai data b’oye hawayenta, Habib ya mata alkawarin zuwa d’aukota shida Little in biki yazo, itakam batace komai ba dan bata wani damu taje bikin ba. Tana nan a tsaye har suka shiga mota suka tafi, ta goge hawayenta sannan ta karasa gun House Captain dinsu da aka kira, nan ta kira yara yan Js 1 suka kwashi kayan Nafi. ¤¤¤¤¤ A gida kam har yanzu Ashraf bai sakema Aneesa kamar da ba, sai dai yanzu tana iya kokarinta wurin ganin ta farantamai rai, sosai take kula dashi, sai dai wannan ba damuwarsa bace in fact gani yakema ta takura mai bayan shi mutum ne dayakesan ya zauna shi kad’ai. Mumy da ita da mahaifiyar Habib suka shiga kasuwan ni kala kala mall da sauransu, suka had’a lefe na gani na fad’a, sunso suje Dubai sai dai Ashraf ya hanasu, yace ” shi baiga wani abu da za’a siya da har za’a rasashi anan kasar ba. ” Kaya kam anyishi, naira ta gurzu, sai dai wannan ba komai bane a kan irin dumbin kud’in da Ashraf yake dasu. ¤¤¤¤¤¤ An ba Nafi d’aki cikin ‘yan ajinsu, gaishesu ta shiga yi dan ita a gunta hakan shine daidai. Dariya sosai suka mata, jin hausarta yasa suka san bafulatana ce, d’aya daga cikinsu wacce kana ganinta kaga wayayyiya tana kwance saman up na gado, sanye da vest da wando ta zuro kai tace ” lalai da alama mun sami yar kwana. ” Dariya suka kara kwashewa dashi wata tace ” Ferry ashe kin gano? Da alama kan ba komai sai iyaye suka sami kud’in gomnati. ” tafad’a tana kallan tulin kayan provision din Nafi. Dariya suka kara sawa, Nafi tana nan tsaye idanunta suka fara neman kawo ruwa, watace ta dafata tace ” ki shiga da kayanki, sai ki zauna a up gadan dake kallan na Ferry. ” Nafi ta d’aga kai alamar to, sannan ta shiga da kayan, daga ganin yanda suke mata kallan wulakanci yasa tasan bazataji dadin wannan zaman ba. Sai dai ya zatai????? Tana gama jera kayanta aka turo wata yarinya akan ta fito karatu karfe 2 tayi, Nafi tayi mamaki ganin ai yau tazo, sai dai ba yanda zatai sallah kawai tai tafita waje tanaji suna gulmar ta. Sun fara daga kan farkon karatu wato English Alphabet,Nafi ta zake sosai wajen ganin ta koyi abinda ake koya mata, sai karfe 5 sannan wannan matar ta mike akan sai gobe a daidai wannan lokacin zasu sake haduwa. A galabaice ta dawo hostel yunwa duk ta isheta, ba kowa a d’akin hakan yasa taji dadi, cornflakes ta had’a ta zauna tasha, jin cikinta ya d’auka yasa ta fito tai alwala tai sallar la’asar. Tana zaune a kan sallaya tana kara tisa karatunta a ranta sai gashi ‘yan d’akin sun dawo. Nan suka mata wani kallo Ferry tace ” ke kina nan wato mu muna can an samu wankin toilet ko? ” Nafi ta kalleta tace ” wlh bam sani ba. ” Wacce ta dafata d’azu yanzun ma ita tace ” haba Ferry taya za’ayi yarinya tazo yau d’in nan amma kice tai aiki? ” Ferryn ta kalleta cikin kuluwa tace ” Ke Jibiya banasan salon iskanci, meye naki a ciki? Ko dake nake magana? ” Wacce aka kira da Jibiya itama cikin fad’a tace ” badani kike ba amma hakki nane in fada miki gaskiya sannan ko yanzu kika kara abinda bai dace ba dole ne in fada miki gaskiya koda kuwa zakiji haushina.” Ta ja tsaki a karshen maganarta sannan tai waje a zuciye, Ferry ta bita da harara tace ” Yarinyar nan ta gama rainani wlh. ” Itakam Nafi tana zaune duk jikinta yai sanyi,ba abinda ta tsana irin taga anyi fad’a a kanta. Mik’ewa tai ta kalli Ferry tace ” D’an Allah kiyi hakuri.” sannan tai waje inda taga waccan ta fita. Ga mamakinta a zaune taganta cikin mutane suna ta hira da dariya. Nafi ta karasa inda take tare da musu sallama, Jibiya ta d’ago ta kalleta sannan tace ” new comer ya akai? ” Nafi ta d’an motsa baki alamar tana san magana, ganin haka yasa ta mike taso kusa da ita, Nafi ta kalleta tace ” Banji dadi ba daga zuwana kuna fada akaina, d’an Allah kiyi hakuri. ” Jibiya tasa dariya sannan ta kama hannun Nafi suka zauna tace ” Karki damu da wannan, Ferry yayatace, ubanmu d’aya, indai fad’a ne irin wannan mun saba. ” Nafi ta kalleta cikin mamaki tace ” Ayya bansani ba. ” Hannu ta mika mata alamar suyi musabaha tare da cewa ” Sunana Aisha Isma’il. ” Nafi tai murmushi sannan ta mika mata hannu itama tace ” Sunana Nafisa Abubakar. ” Murmushi sukama juna, Jibiya ta kalleta tace ” a kano kike? ” Nafi ta d’aga kai alamar eh, fara’arta ce ta kara bayyana tace nima haka. ” Nafi tai murmushi, jibiya tace ” Karki damu da Farida ko ince Ferry kamar yanda ake cemata, a ido ne take haka amma a zuciyarta sam mace ce mai saukin kai. ” Nafi kam murmushi kawai tai, suna nan a zaune Jibiya na janta da hira sama sama har magrib tayi. Nam suka mike sukai alwala suka nufi massallaci. Washegari bayan sun shirya da safe suka fito aji dukansu ‘yan d’akin, Nafi an shiga cikin Uniform ba laifi tayi kyau dagwas da ita. Sunshiga aji malamin Math ne ya fara shigowa, itakam Nafi kawai iya kacinta kallon duk malamin daya shigo dan ko kad’an bata fahimtar kalma d’aya da take fahimta ba. Sai dai ta kalli Malami ta kuma kalli alo, haka malamai sukai ta fita wasu na shiga har aka tashi, itadai tasan kawai dumama benci kawai takeyi. ¤¤¤¤¤¤¤¤ Wani mugun kallo Ashraf ya ma wata kawar Aneesa da sauri ta kalli Aneesa a tsorace, Aneesa ta kalleshi tace ” Hubby me kake nufi? Events d’in ne bakaso kome?” STORY CONTINUES BELOW Ashraf ya kalleta yace ” Anie kanki d’aya kuwa? Biki kwaya d’aya shine kike neman yin event kusan guda 10? Sannan kina san ni in hallarci guda 8? Akan me? ” Aneesa ta kalleshi tace ” bangane akan me ba?” Ya dan rufe ido kad’an sannan yace ” tambayar ki ai nake akan me zanje? ” Kawar Aneesa ta daure tace ” Ashraf amma….. “kallan daya mata yasa tajs bakinta tai dif, Aneesa ta mike rai b’ace tace ” Yaya meyasa kake min haka?” Murmushi ya sakar mata sannan yace ” me kuma nai yanzun? ” Aneesa ta kafeshi da ido ranta duk ya gama b’aci ta daure tace ” Ka tab’a ganin mijin daya ce ma matar da zai aura akan me zaije gun bikinsu? ” Ashraf ya d’an daga kafad’a tare da d’aukan wayarsa ya fara dannawa sannan can yace ” kowa da irin zuciyarsa, sannan dama namiji aka sani dayin kyale kyalen biki ko mace? ” Aneesa idanunta ns kansa ranta yakau kololuwa gun tashi, ta bud’e baki zatai magana tags ya d’au waya ya kira wata number sanan taga yaa mike yai cikin d’aki. Idanu ta bishi da shi sannan tai waje fuuu, kawarta ta mike ta biyo bayanta. D’akin Umma ta shiga da gudu ba ko sallama, Umma na zaune tanacin abinci, Aneesa ta fad’o kanta sannan ta saki kuka. Nan Umma duk ta rud’e ta shiga tambayarta abinda ke faruwa, kawarta ce ta sanar ma Umma komai, ran Umma ya b’aci sosaii ta kalli Aneesa rai a b’ace tace ” Akan haka ne kike kuka? Ai nasha fad’a miki ki cire san Ashraf aranki kiso kud’insa kawai ba wai shi ba amma nsga alama sam kin kasa fahimtata. ” Aneesa cikin kuka tace ” Umma ya zanyi? Nafa fad’ama friends d’ina zancen events d’innnan. ” Umma ya shafa kanta tare da kama hannunta sukai d’aki. A bakin gado suka zauna, Umma ta kalleta tace” ki rage events d’in daga goma zuwa bakwai, a wannan lokacin kibar Ashraf ya sami duk abinda yakeso, karki kuskura ki b’ata masa rai har zuwa lokacin da zai aureki ki amshi wasiyyar mahaifinsa. ” Aneesa ta kalli Umma sai dai batace komai ba, Umma ta cigaba “a sanda kika samu kansa kikasan ya gama mutuwa akanki lokacin ne zamu samu ya barma yayanki company d’insa.” Aneesa da mamaki tace “Umma taya zanso mijina yabarma Yayana Company d’in mahaifinsa? ” Umma tai wani tsaki na kulawar tace ” Aneesa ke yarinyace bazaki tab’a fahimta ba, alokacin da Ashraf ya amshi aikinsa, dukiya da aiki suka fara mai yawa kina tunanin zai samu lokacin ki? ” Aneesa ta girgiza kai, Umma ta dafata tace ” Aneesa kiyi tunani dakyau a haka ma mutumin da ba aiki yake ba baya ganin wani darajarki bare kunyi aure? Yana ganin shi ke da iko dake? ” Aneesa tai shiru sai dai Umma ta tabbatar kalamanta sun ratsa Aneesa sosai…… Nan ta mike ta barta a d’akin, shiru Aneesa tai tana tunani kalakala da wulakancin da Ashraf ke mata duk suna dawowa cikin zuciyarta, kwanciya tai akan gadon zuciyarta na mata sake sake kala kala…… ¤¤¤¤¤¤ Yau satin Nafi d’aya a makaranta, har a wannan lokacin itadai bata fahimtar me ake a aji, sai dai tana kokari sosai a gun karatun da ake koya mata. Yau aka kawo musu wani sabon malami na Computer bayan yayi introducing d’in kansa ne ya fara tashin mutane one by one dan tabbatar da abinda suka sani a gun waccan malamin nasu. “Ke tashi.” abinda Nafi taji malamin ya fad’a kenan idanunsa ns kanta, a tsorace Nafi ta kalleshi sai da ya kara ce mata ta tashi kafin ta mike jikinta duk ya fara rawa, Malamin ya kalleta yace “List 3 input of computer.” Nafi ta zare ido cikin tsoro, ‘yan aji kam gani sukau ba wanda ya samu saukin tambaya irin tata. Nafi tai shiru sai wasa da hannunta data shiga yi, zufa sai keto mata take a cikin jikinta. Ran malamin yakai kololuwa gun tashi gani yake kamar yamata tambayar yara taya za’ai wannan tambayar ta gagari ‘yar Js 3? Ranshi ya b’aci yace ” get out. ” ya fad’a tare da nuna mata hanyar waje. Batasan me yace ba sai dai ganin ya nuna da hannu yasa ta had’a hannayenta biyu tashiga bashi hakuri. Dariya ‘yan aji suka saka mata, ran Malam ya kara b’aci ganin taki fita, a zuciye ya d’au bulsla ya fara zuba mata, Nafi kam ta daku sannan yace ” ya bata nan da sati d’aya zai kirata a gaban class ya mata tambayoyi, inta kuskura ta kasa to wlh ba shakka sai tayi dana sani mai tsanani.” Nafi kam zama kawai tai tana hawaye……. Ni kaina ganin halin da Nafi take ciki sai dayasa hannuna ya fara rawa wanda na kasa cigaba da rubutun nan…… Nafi kwance a saman gado, ba shakka taji zafin dukan da aka mata sosai, ita kad’ai ce a d’akin tana kwance Ferry ta shigo, kasancewar ba magana take mata ba yasa Nafi tace ” Sannu da dawowa. “+ Kallan da Ferry ta mata yau ba kamar yanda ta saba mata ba, wato kallan banzan data saba ba, yau kallanta tai cikin mutunci, Nafi tai murmushi sannan ta gyara kwanciyarta, jitai Ferry tace ” Nafisa ya akai kika kasa bada amsa d’azu? Baici ace duk dakikantarki kinkasa ba. ” Nafi ta mike zaune sannan ta kalleta fuskarta cikin farin ciki, tace ” Bansan amsar na Ferry. ” Ferry ta shiga cire kayanta tana cewa ” to in dai haka ne lalai zakici doka a gun malamai, ya kamata ki samu Jibiya ta koya miki tun kafin a gama raina ki. ” Nafi ta jinjina kai cikin farinciki tace ” Nagode Ferry. ” Ferry ta harareta tace ” karkiyi tunanin sanki nake yanzu, ni bana kawa da wacce bata kile ba, bana kawa mara kwalliya, ba kuma na kawa mara aji. ” Nafi ta sauko daga sama tace ” Ferry nikam kina burgeni wlh, duk da ba kulani kike ba inasan tsarinki yana birgeni. ” Ferry ta d’aura towel sannan tace ” abinda yake b’atamin rai kenan da mata irin ku, sam bakwa abin mace, bakwa kwalliya, yanzu kamar ke sam duk abinda mutum zai miki ban taba ji kin d’aga ma wani murya ba, komai sai dai ki bada hakuri, ke ba dutse ba.” Taja tsaki ta zari kwandon wankanta tai waje. Nafi ta bita da kallo ba shakka abinda ta fad’a gaskiya ne, to amma ya zatai? Bayan haka halinta yake? A satin nan Nafi har sai da ta rame tsabar karatu kala biyu, ga na lesson d’in da ake mata gana computer, a wannan zaman karatun da jibiya take koya mata anan ta fahimci Nafi batai wani karatu ba ganin duk yanda taso tai pronounce d’in kalmomi abun yake gagara, sai dai hakan yasa ta kara tausayama Nafi sannan ta jajjirce wajen kara koya mata. Yanzu kam suna ‘yar magana sama sama da Ferry. Sati d’aya ya cika, malam ya kira Nafi gaban black board ya shiga zuba mata tambaya, tambaya 5 ya mata da kyar Nafi ta amsa biyu, wannan dalili yasa Malam ya yanke mata hakunci akan ta dawo gaba kusa da Ferry da zama sannan duk karshen week sati biyu zai dinga mata tambaya. Nafi kam duk ta rame saboda karatu, sam bata samun damar tunanin gida ko wani abu, sai dai ta rasa dalili duk sanda ta tashi daga bacci sai zuciyarta ta rage mata kwana d’aya akan kwanakin bikin Ashraf. *A KANO* An kai lefe sannan anata hidimomin biki, sai dai sam Ashraf abin nan baya gabansa, tabbas yasan a ransa yanasan Aneesa sai dai bayajin wani farin ciki game da wannan auren. Ita kad’ai take kid’anta take rawarta, duk dinkunansa sai Habib ta samu sukaje suka siyo, sam Ashraf baya walwala bare farincikin wannan auran. Duk yanda Aneesa taso daurewa karta nunamai jin haushinta sai data kasa tamai magana, sai dai duk sanda tamau magana kanta abin yake komawa, karshe tazo tana bada hakuri. Gida ya fara taruwa da mutane, little kam sai rawar kai dinkuna tayi yakai kala 10 ta musu kuma anko da Nafi kala 5, murna kam ba’acewa komai agunsu Umma. Yau saura kwana biyu a fara hidimomin biki Mumy ta kira Ashraf zuwa falonta, bayan ya zaunane Mumy ta kalleshi cikin kuluwa tare da tattara hankalinta kansa, ta fara magana cikin kulawa ” Ashraf yau saura kwana biyu a d’aura maka aure da ‘yar uwarka.” Ashraf kansa na kasa sai dai baice komai ba, tace ” Muhammad! ” D’agowa yai cikin mamaki dan bai tab’aji ta fad’i wannan sunan ba d’an sunan baban mahaifinsa ne. Mumy ta kalleshi tace ” kayi hakuri abinda na maka. ” Kallan mamaki yake binta dashi, yace “name? ” Ta kalleshi idanunta a raunane tace ” Ashraf na sani sarai abinda na maka shekarun baya masu yawa shine yasa ka zama haka, sam bakasan ‘yan uwanka, kanka kawai ka sani, ba ka tunanin maganar da zaka fad’a ko zai b’atama wani rai. ” Ashraf dai kallanta kawai yakeyi, Mumy tai ajiyar zuciya tace ” bazaka tab’a fahimtar me yasani na auri kanin mahaifinka ba daga rasuwar Abbanka ba har sai lokacin da kasan komai na gidan nan da kuma abinda ke cikin zuciyar kowa na gidan nan. ” Ashraf da mamaki yace ” Mumy. ” Ta sakar masa murmushi tace ” na sani nayi laifi a gareka, na rashin sanar dakai komai danai har sai sanda aka haifi Little, sai dai inaso ka sani komai nai a rayuwa to tabbas d’an kai nayi shi, ban tab’ayin wani abu dan in farantawa kaina rai ba, a ko da yaushe kai nake fara sawa a gaba akan komai na rayuwata kafin inyi tunanin kaina. ” Shiru tai sai dai ta kawar dakanta gefe kad’an alamar so take ta b’oye kwallar ta, Ashraf kam kalaman Mumy sun tab’ashi sai dai haryanzu gani yake koma meye dalili shi bai fahimci dalilin auranta da kanin Abbansa ba.” Mumy ta d’anja hanci sannan tace ” Mahaifinka na tsananin san kaninsa, sannan babban burinsa bai wuce yaga ya had’a zuri’a dashi ba, nasani da yana da rai sai yafi kowa farin cikin wannan abun duk da yasan shi kanin nasa ba sanshi yake ba. ” Ashraf ya kalleta cikin mamaki yace ” Mumy me kike nufi da basanshi yake ba? ” Mumy tai murmushi tace “la ba haka zan fad’a ba subutar harshe nai. ” Ashraf yai shiru sai dai tabbas yasan da wani abu. Mumy tai saurin wayancewa da cewa ” Ashraf kasan me ake nufi da aure ba sai na sanar dakai ba dan Allah ka rike matarka yanda ya dace, Aneesa na sanka kowa ya sani. ” Ashraf bai amsa hakan yasa Mumy tace ” Ashraf maganar aiki. ” Kallanta yai sannan ya daure yace ” Mumy me yasa kike so im fara aiki a company d’in Abba? ” Mumy tace ” saboda hakkinka ne.” Ashraf yai murmushi yace ” idan na fara aiki a wani matsayi kawu zai zauna? Sannan ni a wani matsayi employees na company d’in zasu d’auken?” Mumy da mamaki tace ” Ashraf me kake nufi? ” Yai murmushi sannan yace ” zan fara aiki a company d’in Abba sai dai bawai a matsayina na magaji ba inasan ne in amshi hakkina da kokarina bawai dan ni d’an Abba bane. ” Mumy ta jinjina kai tace ” kana nufin zaka fara aiki a company d’in daga farko? Tun daga kan interview?” Kai ya d’aga Mumy tai murmushi lalai ta yaba da tunanin d’an nata ta sani sarai dama yanada hangen nesa sai dai bata tab’a tunanin zaiyi tunani haka ba. ¤¤¤¤¤¤ Nafi ce zaune tana shafa mai Ferry ta kalleta tace ” Nafi yau tunda kika tashi naga kamar bakida lafiya. ” Nafi ta kalli Ferry tace ” Ferry dan Allah tambaya. ” Kai Ferry ta d’aga mata alamar eh tanaji. “Yayanane zaiyi aure a satin nan, na rasa meke damuna sam duk sanda na tuna sai inji raina yana b’aci. ” Ferry ta kwashe da wani dariya tace ” Innocent Feenah dama haka kike? Oh a ido kamar…. ” Nafi tace ” ban gane ba, wani abun ne? ” Ferry ta fara tafi tace ” Innocent girl, yayan naki uwa d’aya kuke ko uba? ” Nafi ta girgiza kai, Ferry ta kara sa dariya sannan tace ” gaskiya Feena kin tashi daga Innocent kin koma green snake. ” Nafi ta mata kallan mamaki tace ” ni na tambayeki abu ma baki amsa min ba kin bige da dariya. ” Ferry tace ” Good haka nakesanki in abu bai miki ba ki fito ki fad’i gaskiya, sannan zancen yayanki ai ba komai bane sanshi kawai kike. ” Da sauri Nafi ta mike ta zura hijab d’inta tai waje tana cewa ” Ni? Wacce ni? Ni kaza?????

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *