TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 6
Tun tana tsumayen Zulaikha har ta tabbatar da ba za ta dawo a ranar ba, hakan ya sanya ta zama sukuku kamar raguwar ciwo, duk yanda ta so kar ta zurfafa tunani ta gaza hakan ya sa ta ɗauki littafin da ta fi so watau Don’t be Sad ta fara bibiyar hikimomi na samun nagartaccen kwanciyar hankali,da haka bacci ɓarawo ya sace ta.2 Washegari Monday basu da aji sai ƙarfe tara na safe, hakan ya sanya ta ɗaukan lokacin ta wajen shiryawa. Takwas da rabi daidai ta fita daga hostel. Sauri take don ba ta fatan ganin Dee. Ta kai daidai biological science da za ta bi ta je chemistry department in da za su yi ajin ta jiyo sallama. Ƙara sauri ta yi don ba ta da niyyar tsayawa duk da sautin muryar kamar wanda ta sani. “Anty Amatullah an tashi lafiya” ya faɗi hakan ya sanya mata juyawa, tana ganin fuskarsa ta juya cikin sauri ta cigaba da tafiya. Ba za ta ce ga yadda aka yi yazo gabanta ba.2 “Don Allah kiyi hakuri, wallahi na yi tunanin ya faɗa miki ne shi ya sa na kaiki don Allah ki gafarce ni” yace cikin sanyin murya. “Babu laifin da ka yi min Yaya Hamza, ban tsaya bane saboda guje ma keta haddin aure. Babu sauran Alaƙa tsakanina da Dee. Ina masa fatan Alkhairi” tace tana mai jan jikinta ganin Taran na gabatowa. “ban gane haddin Aure ba, ai ba a sanin maci tuwa” yace yana dariya. “wannan miyar ta daɗe da ƙarewa. Yau kwana goma kenan da ɗaura min aure, David bai faɗa maka ba?” tace tana ƙirƙiro farin ciki. “Kinga yau kwana goma kenan da mutuwar mahaifin Dee Yusuf. Kice double rashi yayi” ya faɗa cike da Alhini tare da tausayin amininsa.2 “Allahu Akbar, Allah ya jikan musulmai, su kuma Allah ya basu hakurin rashi. Bari in je kar in latti” tace tana barin sa tsaye. Mamaki ya cika shi ainun, duk ya cika da tsarguwa akan tashin hankalin da ya gani a idon Dee. Amatullah kuwa tana gama magana da shi ta juya ta isa aji cikin sauri, ta shiga ko hutawa ba ta yi ba malamin ya shigo, karatun rabi da rabi ta fahimta saboda tsilla-tsilla da zuciyarta ke mata akan halin da Dee Yusuf ke ciki da istigfari da take yi.2 Sai da azahar ta samu ganin su zulaikha wainda su ka zo latti. “Amarya!” su ka haɗe bakin faɗi. Dariya ta bi su da shi wanda ko laɓɓanta bai wuce ba. Nan su ka zauna suna mata tambayoyi kamar wacce ke gaban kuliya. Wasu ta amsa musu wasu ta sa musu dariya kawai. “Kinga Amatullah ki kwantar da hankalinki, zan kawo miki littafan hausa ki karanta saboda ki san yanda za ki tafiyar da Megida Saifullah. Duk taƙamarsa da ya ɗanɗana zumarki dole ya so ki, dole yai marmari ki” maman Jaafar tace tana mai dulmiyar da Amatullah cikin duhu don ita ba ta san wani abu zuma ba, ita Sam ba ta damuwa da sanin abubuwan da su ka shafi wannan, ita dai a barta da karanta littafan addini sun fi komi sa ta nishaɗi. Haka dai Maman Jafar ta shiga yi mata bayani akan yanda za ta sace zuciyar angon na ta, ita kuwa Amatullah jin ta take kawai, gani ta ke soyayya tsakanin ta da Saifullahi abu ne mara yiyuwa. Sai dai biyayyar aure.2 *** Ranar talata ya kama ranar bikin birne mamacin ƴan uwa da abokan arziki sun yi dandazo a Coci, duka sanye cikin bakaken kaya mazan su da matan su. Gawar mamaci aje gaban jama’a cikin akwatin da aka kayata da furanni. An bude taron ne da yiwa mamaci addu’a bisa ga al’adar kiristanci na raye-raye, bayan an gama minister ya ba da taikaiceccen jawabi akan rayuwa da mutuwa, haka kuma aka bawa ɗan uwan sa mafi kusa da shi damar jawabi akan halayyar mamaci da abinda ya bari na iyali. Tun da aka fara Dee bai bar gefen mahaifiyar shi ba, wacce in ban da hawaye babu abin da ke fita daga idanun ta. Minister ne ya bada taikaiceccen lokaci ga jama’a domin mika ta’aziyan su ga iyalan mamacin, kafin aka dauki gawar zuwa makabarta su na mai cashewa yayinda kiɗa da waƙa ke tashi, da ya ke babu laifi mamacin mai jama’a ne, na kasa da na mota haka aka dunguma zuwa makabarta.2 STORY CONTINUES BELOW Hankalin mahaifiyar Dee bai tashi ba sai da ta ga an ɗauki akwati an sa cikin rami, nan ta ƙwalla ihu ta na mai kiran sunan mamaci yayinda da ta ke kokarin shiga ramin, da kyar Dee tare da taimakon kannen mahaifiyar ta shi su ka fitar da ita daga makabartar.4 Babu laifi an cashe, an kuma ci an koshi domin kuwa gangarumin biki aka yi a ranar, idan aka ɗauke Dee da mahaifiyar sa, da kannan sa biyu babu wanda bai cashe ba. Ranar haka aka kwana ana raye raye da ciye ciye family house ɗin gidan mamacin. 3 *** Bayan kwana uku Dee zaune a falo, hannun sa biyu bisa kuncin sa ya rasa abin da ke masa daɗi a duniya, idan akwai tunanin da baya so ya bi bayan na komawar shi makaranta ba, ba dan komai ba sai dan Amatullah, Sam ba ya fatan sake saka ta a Ido alhalin ta na matar wani, tsananin kishi da bakin cikin auren ta ya fi komai damun shi a halin yanzu.2 Babban falo ne mai dauke da manya manyan kujeru, da ya ke family din mamacin babu laifi suna da arziki. Bai ji shigowar ta ba, kamshin turarenta ne ya bakunci hancin shi. Dab da shi ta zauna kugunta na gogan na shi yayin da ta ɗaura hannu bisa kafaɗar shi ta na mai fadin “Dee is owk na, ka fa tuna sanda Dady ya mutu kai ne kan gaba wajan kula da ni, you told me Dady will not be happy if I keep crying…….Dee” “I’m not crying Mimi” Cewar Dee yayinda ya dago ya na duban cousin ɗin ta shi da ya kira Mimi. Mimi diyar Yayan mamacin ce, ma’ana uncle din Dee da ya mutu watanni uku da su ka wuce. Yar matashiyar buduwar ce mai kimanin shekara goma sha bakwai a duniya, irin wannan siraran da ake danganta su da model, mashaAllah idan kyau ne ko cikin larabawa ta shiga ba a mata kushe ba, Mimi kamar dawisu ga kyau ga ado. Kusan yanayin farin ta daya da Dee, haka kuma dangantakar ta da Dee dangantaka ce na shakuwa kwarai, hatta mamatan biyu sun sheda wannan shakuwar.2 Kanta ta daura bisa kafadar Dee, cikin alhini ta ce “It’s so sad you know, just three months fa da mutuwan Dady, yanzu kuma uncle sai ka ce abin sa hannu…..” “Shhhhhh” Dee ya katseta ta hanyar dora hannu bisa lebenta, hannun sa ya sa cikin na ta sannan ya ce “Such is life, we lost people we love, ko da kuwa babu mutuwa, so let’s just be strong and pray whoever we lost ta mutuwa ko ba mutuwa, are in a better place, owk?” Kai ta gyada alamar eh. Shiru ne ya biyo baya kafin daga bisani ta furta “Dee?” “Yes dear” Dee ya amsa mata a takaice. “Please ka yi ma Mum magana ta barni na zo school din ku, na ci Jamb fa, I want to study pharmacy”2 Gaban Dee ne ya fadi jin ta furta pharmacy yayin da Amatullah ta sake faɗowa ran shi. Cikin kokarin boye damuwar sa ya amsa mata da “Ke din ce Mimi kin fiya rawan kai shi ya ba ta so ki yi nisa da ita, well Pharmacy is good course, plus you have the brain, but why ABU?” “Because you are in ABU….” Ta amsa cike da shagwaba har sai da ta sanya ya murmusa, shi kan shi ya manta rabon da yayi fara’a. “Mimi rigima, me wey dey graduate in the next 6 weeks? Abi you want make I spill over? Infact makarantar ta fita rai na” “No I want you to stay for me, go for your masters mana….”4 Ta fada cikin magiya. Kai ya girgiza “Ah ah Mimi, zan dai yiwa Mum magana ta bar ki, saboda ABU is a great University, Amma I can’t stay darling, I really I can’t… ” Yana maganar ne yayinda ya ke hango Amatullah cikin zuciyar sa. *** Ango a na shi ɓangaren tun komawar sa Russia ya ke neman hanyar da zai shaidawa Ayush maganar auren da aka ɗaura masa a gida, amma ya kasa tsabagen shakkar ta da ya ke. Haushin Baban Sasa ya sanya shi canza layin waya ya kuma ki kiran gida da sabuwar number din ta shi. Zaune su ke cikin ajin su, kusan miti talatin da fitar lecturer, kowa ya watse ya bar su. Idanu ta kafe shi da su cikin kallan zargi ta ce2 “Saif ni fa na kasa gane ka, are you owk?” Kyeya ya sosa, da ka gan shi ka ga mara gaskiya. Ya na dan murmushi ya ce “No babu komai fa, tunanin wani lamari da ya sami abokina ne ke damuna” Ya tsinci kan sa ya na mai mata karya.2 “Abokin ka? Wani abokin na ka? Menene ya same shi?” Cewar Ayush yayinda ta tattaro duka nutsuwar ta gare shi. Kai ya girgiza mata tare da cewa “never mind, yanzu in tambaye ki misali, just misali fa, ace kawai muna zaune kasar nan kawai sai a min waya a ce an daura min aure a gida…….” “Burauba!!!!”3 Ayush ce ta katse shi, kana ta kara da “Za ma a kwance ne!! Kut rainin wayo ma kenan! Shi abokin na ka ne yayiwa budurwar ta shi wannan rainin wayo? Cousin aka ɗaura masa halan? Dan rainin wayo wallahi ya na sane! Karya ya ke wallahi, akwai wanda ya isa ya tinkare ni da wannan rainin wayon ma!!!!!!!” Jikin Saifullahi tuni ya kara sanyi, yayinda yayi sororo ya na duban ta. Cikin ran sa kuwa cewa yayi “Baban Sasa ya kwanto min kura……” “Ya na ga ka wani saki baki ka na kallo na? I don’t get you! Yanzu kamar kai wa ya isa ya maka auren dole? Sai dai ka na so kai ma”2 Cewar Aysuh cike da tsiwa, ta na magana ne idanun ta cikin na sa. Ganin dai in yayi sake allura ce za ta tono garma, dan haka Saifullahi na mai sosa kyeya ya furta “Ayush kenan, Allah ya sa mu dace….” “Ba Allah ya sa mu dace ba, answer me! Yanzu akwai wanda zai iya ma maka auren dole?” Ayush ta sake katse shi ta na masa irin kallon nan mai cike da alamar tambaya. “Aysuh?” Ya kira sunan ta da kakkausar murya. “Yea? Ina jinka” “Kin yarda da ni?” Kai ta gyada masa ala’mar eh. Hannun ta biyu ya riƙe kana ya ce “Alhamdulillah, toh ina so ki yarda ki kuma amince babu wani mahaluki a duniyar nan da ya isa ya sanya tazara a tsakanin mu”2 Cikin jin dadin maganar ta sakar masa murmushi mai kayatarwa tare da faɗin “I trust you Boo, and I love you so so much” “I love you more Ayush” Cewar Saifullahi, cikin ransa ya na mai yakinin kare hakkin soyayyar su daga dukkanin fitinar Baban Sasa. **** Sai da ya ƙara kwana uku bayan bikin jana’iza kafin yayi haramar komawa Zaria. Ranar juma’a da safe ya tashi da shiri cikin ran sa ya na mai baƙin cikin komawar sa makaranta. A ɗaki ya tadda mahaifiyar shi, zaune bisa gado, kallo daya za a mata a tabbatar da damuwar da ke tattare da ita. Gaban ta ya je ya durkusa, cike da lababi ya ce “Mummy, wannan damuwar da na ke ganin ki ciki ya na breaking heart ɗina, it makes me want to stay with you and forget about going back to school Mummy….” “Shhhhh!” Ta katse shi ta na mai dafa kan sa, kan ta ce “David my son, damuwa ya zama dole, rashin masoyi abu ne mai wuya, you will not understand, I hope you don’t have to experience it in your life my son…..” ‘I have Mummy, I’ve lost Amatullah forever’ Cewar Dee cikin zuciyar shi. “Amma rayuwa ba za ta tsaya ba, life goes on, so ina ba ka umarnin komawa makaranta, ka gama karatun ka, make sure you graduate with flying colors, kar ka manta ka na da ƙanne that are looking up to you, make us proud as always” Ta karasa maganar ne yayinda ƙwalla ya cika idanun ta. Cikin sassanyar murya ya furta “I will Mummy, I shall make you proud” “Ni kuwa David ya batun yarinyar nan da ka ke so? Kasan mutuwar nan bai bari mun yi magana ba, Kun sasanta? Yaushe za ka je Hadeja?” Gaban sa ne yayi mummunar faɗuwa, ya so Allah ya mantar da ita ba dan komai ba sai dan gujin bacin ran da za ta shiga idan ta ji yanda aka wulakanta shi kasancewar ya so ya musulunta sanadin soyayya. “Ina jin ka David, ko dai da matsala ne?” Ta sake tambayar shi cike da damuwa ganin yayi shiru. A hankali ya furta “Mummy forget about that girl, she is as good as dead to me”2 Shiru ta yi ta na duban sa, cikin ran ta tana so ta tambayi dalilin canjin ra’ayin Dee, amma kuma yanayin sa da kuma yanda ta ji muryar sa yayinda da ya ke maganar ya sanya ta sake shawara. Ta ce “I understand” STORY CONTINUES BELOW Tashi yayi tsaye gudun kar ta sake jan maganar ya furta “Mummy bari na wuce, ranar Monday za ki wuce Abujan ko?” “Yes my dear” Ita ma ɗin tashi ta yi, tare da shi su ka fice tana masa nasiha, sai da ta tabbatar ya yi wa kowa na gidan sallama kafin ta raka shi har bakin gate, tana sa masa albarka idanu cike da ƙwalla haka su ka yi sallama, Dee ya ɗauki hanyar Zaria zuciyar shi ya kuna kwarai da gaske. **** Kamar yadda Zuwaira ta yi alkawari sai gata da littafai cikin jakar viva. Dariya sosai Amatullah tayi tana ɗaga su ɗaya bayan ɗaya. “Yanzu da wanne zan ji? Su chemistry dinnan masu shegen chain ko hadisan Kanon nan” tace cike da shaƙiyanci don ita dai ba za ta ce za ta yarda da kalaman maman Jaafar ba duk da cewa ta san bature na faɗin experience is the best teacher.4 “Samar masa lokaci za ki yi, don mahimmancin su, in kuma so kike ki zama bora a gida shike nan” maman Jaafar ta ce a dake.2 Dariya Zulaikha da Amatullah su ka sanya mata ganin yadda ta ke haɗe gira don Amatullah ta ɗauki zancenta da mahimmanci. “Ni fa tsoro na shine anya ma zai karɓe ni a matsayin mata mai daraja, duba da yanda yake hantarata ya ke min kallon wata ƙaskantaciyar halitta” tace cikin tausayin kanta. “By the time ya ci gasasshiyar hanta, sabuwar gashi ai dole ya sauko. Ke dai ga wainnan littafan ki karanta” tace mata cikin jadaddawa. Zuwan wasu yan ajinsu wajen ya sanya su chanza akalar zancen su nan aka koma zancen karatu tare da yi ma juna bayanin abubuwan da suka shige duhu. **** Yanda Amatullah ke fargaban haɗuwa da Dee, haka shi kuwa sam ba ya kaunar ganin ta ba dan komai ba sai dan tsananin kishi da takaicin ganin ta a matsayin matar wani. Tun isar sa Hamza ya faɗa ma sa haduwar shi da Amatulah, tare da masa jajen rashin ta, ga mamakin Hamza sai ji yayi ya ce idan ya na so su shirya kar ya sake ma sa maganar matar wani. Tun daga ranar ya ja bakin shi yayi shiru dan ya san halin Dee ba dai fushi iya fushi ba.2 **** Kwanci tashi asarar mai rai, haka karatun su Amatullah ya dinga tafiya, sosai ta dage da karatu saboda samun sakamako mai kyau ganin result dinsu na zangon farko ya fita tana da 4bisa biyar (4.00)ya sanya ta dagewa don samun fiye da haka ko kuma tsayawa a daidai hakan. Karatu ta ke yi babu dare babu rana duk da sau da yawa takan ɓace cikin tunanin Dee Yusuf da gaba ɗaya ba ta sake ɗaura idanunta a kanshi ba. Sau da yawa ta kan roki Allah da ya jiɓinci Al’amarinsa a duk inda Yake. Tun da ta dawo hutun mid semester sau ɗaya ta je gida, shima a kan tunanin Baban Sasa. Halin da ta rike shi ya bata mamaki, domin Baban Sasa kamar ba shi ne ƙoda ya kwantar ba. Yayi kyau har da ƙibansa hakan ya bata mamaki.8 “Megida wannan kyau haka, Allah abin godiya” tace masa cike da farin ciki. Shima dariya yayi mata ya ɗaura da fadin “Ciwon nan har da fargaba ya ƙara kwantar da ni fa” kallon sa ta shiga yi cike da alamun tambaya shin wani fargaba kuma, hakan ya sanya shi ɗaurawa da “wallahi Amatu, tun da na fara ciwo sai nake ganin ba zan ga aurenku ba, Allah Laɗifu sai gashi ya aminta na gani, yanzu hankali na kwance” dariya ta shiga yi da mamakin ƙarfin hali irin nashi. “Allah mun gode maka, yanzu ina ke maka ciwo?” ta ce cikin kulawa. “Toh yanzu dai ba inda ke ciwo, ina shan habbatus saudah kuma yana taimakawa. Ai yanda nake jin jikin nan se naga auren yayanku” yace yana dariya.2 “Allahu ya amince” ta fadi itama cikin dariya. A nan ta ke jin labarin tun bayan tafiyar Saifullah ba sake samun shi ko da a waya bane. Ba ta yi mamaki ko bakin ciki ba don ta san har abin da ya fi ɓata zai iya yi. Tun wannan zuwan ba ta sake zuwa ba, duk da sun rabu da mahaifiyar ta cikin kewan juna amma burin ta na samun sakamako mai kyau ya danne duk wani kewan gida da take yi. **** Duk wani lungu da saƙo da ya san zai iya ganin Amatullah daina zuwa yayi, hatta ajin da su ka saba zama ya koya mata karatu ji yayi duk duniya babu inda yake shakkar shiga tamkar ajin. Wani shiga jama’a da hayaniyar aluta duka aje su yayi, haka duka activities da wani cultural weeks da ake yi cikin makarantar bai yi participating ba. Tun su Hamza na kokarin jan shi ciki, har su ka hakura su ka sa masa idanu kawai. Zuwan Mimi Post -ume ne ma ya dan sa ya saki ran sa, kwanan ta biyu kacal ta koma Kano abin ta. Ana gobe za su fara jarrabawa sakon dawowar Saifullah ya isko Amatullah daga ƙanin ta Hafiz. Tsoronta ya zo bai karɓe ta a wata aba mai daraja ba, amma littafan da ta karanta ya sa ta aminta da cewa ana auren kiyayya miji ya so matarsa bayan ya ci sadakinsa, sannan ta yarda da duk abin da miji ke ma mata na tozartarwa matukar yana kiranta makwanci toh yana sonta.6 Ta wannan fannin sai ta ga kawai ta gama samun Saifullah ta gama don ba za ta taɓa hana masa ba. Da wannan cikin ranta ta aje tunanin Saifullahi ta dukufa wajan karatu da neman sa’ar jarabawa. **** Rana ɗaya Dee da Amatulah su ka gama jarabawa, banbanci shi ne ita Amatullah jarabawar na ta na safiya ne, shi kuma Dee da rana. Ko da ya fito da ga jarabawar bai iya tsayawa murnar da celebration da dalibai su ka ba na gama makaranta ba, motar shi ya shige kai tsaye gate ya nufa da niyar komawa gida ya haɗa na shi ya na shi ya bar Zaria, ya na mai fatan bayan clearance da karban result, kar Allah ya kara kawo dalilin da zai sa ya sake dawowa makaranta. Dan karamin go slow da ya tadda a bakin gate kasancewa ababan hawa sun yawaita saboda dalibai dayawa ranar su ke komawa gida. Kamar ance Ya kalli gaban sa, nan ya hango ta bakin gate ta na faman jan katon akwatin da ya karfin ta, daga dukkan alama ita ma ɗin gida ta yi. Kallon ta ya ke yayinda ya ji wani abu ya taso ya tokare sa a kirji. Sanye ta ke cikin farin hijab har kasa, kafafunta sanye da safa, abinka da sha’anin sheɗan gani ya ke tun da ya ke ganin ta ba ta taɓa masa kyau ba kamar yanda ta yi yanzu da ya ke kallan ta. “Amatullah…….” Ya furta a bayyane. “Ina fatan wannan shi ne gani na karshe da zan mi ki a rayuwa ta, ba dan komai ba sai dan tazarar da ke tsakanin mu, Amma soyayyarki ta riga min shigar gaggawa, ta min illa….” Motsawar da motan da ke gaban sa yayi ya sanya shi yin gaba da tashi motar, ya zo daidai gaban ta, daga idanun ta ke da wuya su ka yi ido biyu, gaban ta yayi mummunar faɗuwa amma ta kasa ɗauke idanun ta daga kallon sa “Dee…..” Ta tsinci leɓan ta na mai fitar da sautin sunan sa. Securityn da ke karbar gate pass ne ya tura hannun sa cikin motan Dee domin karbar pass daga hannun Dee, amma ina Dee be ma san yanayi ba. Karar horn da kuma yanda security ya kwankwasa motar ya sanya Dee ya farga daga barin kallon ta, cikin bada hakuri ya mika masa pass din, yana mai taka motar ya fice daga makarantar ba tare da ya sake waiwayan in da Amatulah ke tsaye ba.2 Amatullah kuwa da kyar ta ƙarasa jan akwatin zuwa gate in da ta tadda Hafiz tare da sauran kayan ta, bakin gilashin motar da su ka zo daukan ta da shi ya sa aka hana su shigowa. Gaban ta bai daina faɗuwa ba har ta isa gida.Ganin Dee da ta yi ba ƙaramin fama mata gyambo ta yi ba, haka ta maƙale a ɗakinsu ba tare da ta fito ba don gaba ɗaya ta rasa gane kanta. Ko ɗakin Baban Sasa ba ta shiga ba, haka ɗakin Hajiya iyaka wainda ta ci karo da su kafin ta shige su ne su ka san da dawowarta. A nan tsakar gida Hajiya ta tsinci labarin dawowarta, duk da ba lale tayi da dawowarta ba sai ta tsinci zuciyarta da yi mata ƙuna akan rashin shigowar ta gaisheta.4 *** Angon Amatullah wato Saifullah kuwa bai so dawowa Nijeriya ba duk da kuwa ya kammala karatun shi sakamako kawai ya ke tsimayi. Ayush ce ta takura lallai su dawo a yi maganar auren su a wuce wajen. Gashi har yanzu ya kasa buɗa baki ya faɗa mata halin da ake ciki na game da auren shi da Amatulah, ya so ya hure mata kunne su yi zaman su can su nemi aikin yi ko da kuwa na shekara guda ne amma Ayush ta yi kememe ta ki, ita aure ta ke so, in kuma auren na ta ne ba zai yi ba sai ya faɗa mata. Akan wannan batu su ka dawo gida, in da Saifullahi ke cikin halin haula’i.2 Bayan Sallar isha’i Saifullah ya shigo ɗakin mahaifiyar tasa, so yake ya nemi shawararta akan yanda zai faɗi ma Ayush ba tare da ya rasata ba sanin da yayi in dai wannan fannin ne Hajiyarsa ba ta da part two. “Ka haɗu da yarinyar nan ne?” Ta tambaye shi, yanayin da ya kallo ta cikin rashin fahimta ya sa ta ƙara da “Amatullah fa” tace tana kallon sa.3 Tsoro take kar ya zo ya faɗa tarkon son yarinyar don ta san kwana bakwai Baban Sasa da Baba Anas su ka ɗauka suna addu’ar gina soyayya tsakanin wa’inda ke samun saɓani. Sannan ta yarda da ƙarfin addu’ar don tana yi a duk lokacin da su ka samu saɓani da megidanta.4 “Ni wallahi gaba ɗaya na manta da wata halitta haka, ni yanzu mafita na zo ki sama min, Ayush! Ban son na rasa ta Hajiya” ya ƙarasa yana marairaicewa. Shiru ta yi tana tunani kafin ta samu mafitar da cikin farin ciki ya bar ɗakin tare da niyyar ɗaukan hanyar Kano Washegari.2 “Ka nemi yarinyar can dai komi dare yau, na san yan sa ido sun fi ɗaurawa a kanka” ya tsinkayi muryar hajiya sa’ilin da ya ke barin ɗakin. Ficewa yayi yana tunanin yanda zai yi da ita, ji yake ina ma kashe rai ya halatta a duniya da tuni ya aika ta lahira don ya ji dadin rayuwarsa da Ayush.7 Har ya zo wucewa ya ga Siddiƙa kanwar Amatullah za ta shiga ɗakinsu. “Uhmmmn wacece nan” yace cikin ɗan ɗaga murya. “Siddiƙa ce” ta faɗi tana ɗan tsayawa. Sai ta ya matso kusa da ita sannan yace “ki ce ma Amat ta kawo min abinci ɗaki” yana gama faɗi ya sa kai ya fice.4 Da murna ta shiga ɗakin lokacin Amatullah na zaune suna hira da mahaifiyarsu wanda rabi da rabi ne hankalinta a wajen. “Yaya Amatullah wai ki kai ma Yaya Saifullah abincinsa ɗaki, kin ji yanda ya kira sunanki, Aamat ya ce, wallahi Yaya Saifullah ɗan gayu ne…” “Dilla rufe ma mutane baki, ba ɗan gayu kaɗai ba” Amatullah ta katse ta cikin tsawa, ba ta ga dalilin da zai sa ya nemi ta kai masa abinci ba.2 ‘Zai so ki fa, kuma ki saki jiki ki sabar masa da jikinki, da farko a kwai wuya amma shine soyayya’ ta tuna kalaman maman Jaafar. Nan sai ta ji sanyin jiki. Kenan har ya fara sonta tun da har ya nemi ta kai masa abinci.2 ‘da farko a kwai wuya’ ya sake faɗo mata a rai, nan ta tsorata ainun don in akwai abin da ta tsana abin da zai sa ta ji zafi a jikinta. Ta tuna a littafan da ta karanta yanda aka sa amare na sumewa in aka kai su. Ba ta san lokacin da hawaye su ka soma gangaro mata ba, kawai ɗuminsu ta ji.2 “Amatullah haramun ne tsaurara kiyayya, balle wannan mijinki ne wanda Aljannarki ke tafin ƙafarsa. Ga abincin sa can maza ɗauka ki kai masa” Goggo mairo ta faɗi bayan ta sa hannu ta goge mata hawayen. Cikin sanyin jiki ta ɗauki abincin ta kai masa ɗaki. Film yake kallo ƴar America, ganin ta bai sa ya kashe ba duk da kuwa abin da ake haskowa ya saɓa ma shari’a. Duƙar da kai tayi don tun da take abin da bata taɓa gani ba kenan. “Daga kai ki gani, ki ga yanda su ka dace da juna, shin ni ɗin ya dace na gauraye gumi da bagidajiya irinki? Kalle su fa, wai ke har kina tunanin kin kai mace da za a gani a so? Na so tsine ma ranar da aka ɗau cikinki don ranar bai zama mai adalci a rayuwata ba”12 yace yana mai jan farantin da ta shigo da shi ya soma cin abincin da hankali kwance. “Hijabin nan naki ƙarni ya ke yi, ki yi hakuri ki bani waje ko iskan zai yi daɗi” ya ce yana nuna mata hanyar fita.3 Tsoro ya hana mata fita tun a farko, don ta san yana iya ƙulla mata wani sharrin, ga shi ta zauna, amma zaman bai mata amfani ba. Kuka ya taso mata bayan fitowarta daga ɗakin, tsayawa ta yi ta tattaro duk wani natsuwa nata kafin ta isa ɗakin Baban Sasa, nan hira sosai su ka yi, sannan ya bata tukuicin hira da sanya tariyarsu sati biyu masu zuwa. Yana faɗa mata lokacin za ta tafi ne, take ta ji duk wani natsuwar tafiya ya ɓace. “Baban Sasa zan yi missing ɗinka don Allah kara lokaci” ta samu kanta da faɗi. Kallonta yayi cikin dariyar su ta manya ya ce “Ai muna tare, ki yi hakuri kuma ki bi mijinki, Allah ya sanya alkhairi ya muku Albarka, Nan da sati daya Saifullahi zai haɗo mana lefan ki bisa al’ada, kasancewar tsatso ɗaya kuka taso ba zai sa a toye mi ki hakkin ki na lefe” ba ta amsa ba anan ta sanya kuka mai tsuma rai, gaba ɗaya ta haɗa masa tun daga wanda ta ƙunso daga ɗakin Saifullah har zuwa na Tariya ga fuskar Dee Yusuf da ta gani a gate sai mata gizo ya ke a idanu. *** Baban Sasa ne ya ruguzawa Saifullahi shirin shi na zuwa Kano a washagari, maganar tarewa nan da sati biyu, da na lefe da gidan da za su zauna ne gaba ɗaya ya ɓata masa lissafi. Yayi kokarin ɗaga tariyar ta hanyar ba da uzirin rashin kammala ginin sa da ya fara, Amma Baban Sasa ya ce wannan ba wani abu ba ne, zai iya zama ɗaya daga gidadan shi, ya zaɓi duk wanda ya masa a fara gyara. Haka ya kasance cikin bakin ciki da dana sanin biyewa Aysuh da yayi su ka dawo.3 Magungunan mata da su tsumin da ‘yan uwan Gwaggo ke angaza mata ba karamin tayarwa da Amatulah hankali su ke ba, tun tana musu alkunya ta na karɓa in ta shiga bandaki ta zubar har ta gaji ta fili ta ce musu su daina ɓata lokacin su, ita ba sha ta ke ba kuma ba ta ga dalilin sha ba. Haka kuma baccin ran da su ka nuna bai sa ta canza ra’ayin ta, har su ka gaji su ka bar ta da halin ta. Satin biyun nan sun zo masu ne kamar kyaftawar ido, ba ta wani wahalar yin gayya ba sai su zulaikha da ya zama mata dole. Ana saura kwana uku aka nuna lehenta, wanda ya fi na duk wata ya mace da aka aurar a gidan. Ranar bikin ta ci leshin ta masu kyau da atamfa ta dinga canzawa kowanne da hijab da ya shiga da shi. Wannan shigan ya fi komi ɗaga hankalin Saifullah don a rayuwarshi bai taɓa fuskantar tozarta wa irin sa ba, wai shi kamar sa ana bikin sa duk da auren suna kawai ya tara amma a ce matarsa zulum zulum cikin Hijabi.