ZUCIYA CHAPTER 2
D’akinta ta shiga tana tafe tana layi, shikam yana jin motsinta yai saurin kwanciya dan ya tabbata bazataso wani yaji wannan mumunan abun ba, Nafi na shiga ta karasa kusa dashi ta zauna hawaye ne kawai ke malala a idanunta, can tasa hannu ta goge sannan ta kalleshi cikin wani yanayi mai wuyar fassarawa tace “Dan binni yazanyi da ke? Gashi baki farfad’o ba bare ki bar wannan gidan mai cike da abin takaici dasan zuciya. ” Zuciyarshi ce ta karye da mamakin tana cikin wannan halin amma tausayinsa take? Wannan wace irin yarinya ce wacce zuciyarta take da tsananin kyau? Nafi ta kara sa hannunta ta goge hawayenta sannan ta cigaba ” Dan Binni ina cikin wani yanayi mai wuyar fassarawa, Mahaifina baisan komai ba sai dukiyarsa baya ganin mutunci ko darajar kowa banda ta dukiyarsa, mahaifiyata kuma san kanta ya mata yawa haka na taso a cikin irin iyayen nan, ba wanda ya damu da halin da nake ciki ko wanda zan shiga, a dazu nafijin haushin Baffa akan kin biyan bashin dayai sannan bai damu da in auri sa’ansa ba wanda a cikin ‘ya’yansa akwai wad’anda suka girmeni ba. ” Tai ajiyar zuciya sannan ta cigaba ” yanzu kuwa nafijin haushin Inna ta, tafi kowa sannin halin Baffa amma duk da haka taje ta ranci kud’i da sunansa, ni kuma da ko naira biyar bangani ba bashi na neman………… ” Kuka ne yaci karfinta ta kasa karasawa, mikewa tai tsaye tace “bari in samoma madara kasha nasan yunwa kake ji.” Tana fita ya bud’e idanunsa ga mamakinsa jiyai gaba daya jikinsa yayi wani mugun sanyi, meyasa mutane basuda imani? Yanzu me wannan yarinyar tayi da hakan ke faruwa da ita? Shiru yai yana tunanin meya kamata yai dan cetan rayuwarta? Bata dade ba ta shigo dauke da kwarya karami da chokali, nan ta dagoshi kadan ta shiga bashi, mamaki tayi dan kuwa yau madarar bata zubewa sai dai batai tunanin komai ba. Shikam sha kawai yake gardin madarar ce kesashi sha sai dai rashin sigari yasa madarar batamai armashi sosai ba. Ganin yadansha dayawa yasa ta gyaramai kwanciya sannan ta mike tai waje. A can bangaren Datti kuwa yatafi rigar Mahaifinsa nan ya shiga suka gaisa da iyayensa da ‘yan uwansa ya kuma sanar dasu auren Nafi wanda za’a daura anjima, tsananin mamaki ne ya kama Iyayensa da yayensa, mahaifinsa wanda ya tsufa sosai ya kalleshi yace ” yanzu Datti za’ai auren Nahi shine sai ranar auren zaka sanar damu? ” Datti cikin halin ko in kula yace ” to Kawo menene aciki nima sai yau naji zancen auren. ” Gaba daya suka kalleshi cikin tsananin mamakin kalamansa, Aji mahaifiyarsa tace ” Datti me kake san kace? ” Ya kalleta yace ” Aji to menene ban fada ba? Nima aradun Allah sai dazu nan na sani.” Tsannnanin akaici ne ya kama Aji ta mike cikin zafi tai gaba hartaje wajen dakinta ta dawo ta kallesu tace ” in har na isa da ku babu wanda zaije daurin auren Nahi ta gurin datti sannan ba wanda zai aika mata ko da kwayar samira ce, na sani ba laihinta bane sai dai Datti ya ja mata komai. ” Tana kai nan tai gaba a fusace Tanaji Datti nacewa ” Karki damu Aji nima ba kai mata samirun zan ba mijinta inya damu ya sai mata. ” Yayansa Sambo yace ” Datti me kake san fad’a? Bazaka mata kayan daki ba ko me?” Datti ya mike yace ” nifa nazo sanar daku ne bawai cewa nai kuzo ba, yar nan tawace ra’ayinane in mata kayan daki ko inki. ” Kallan mamaki suka bishi dashi inda sabo sun saba da halin Datti sai dai mamaki suke tunda yanzu abun ya shafi zancen ‘yarsa. *********** Sukam su Ali da ragowar abokansa murna suka shiga tayashi akan yasamu abu a bagas, lalai sun yadda Datti baya cikin hayyacinsa, waye zai saida ‘yarsa saboda dubu ashirin? STORY CONTINUES BELOW Sukam sunje sun sanar da liman nan suka shiga shirye shiryen, Ali yasa aka share mata daki daya acikin gidansa, matansa kansu basuyi kishi ba jin yarinya ce suna ganin baifisu kara samun mai musu girki ba. ************** Nafi ta gama aikin gida tsaf ta gyara dabobbi, shikam zaune yake yana addu’a fatansa d’ayane Allah ya bashi ikon taimakon wannan baiwar Allah, kamar yanda ta taimakeshi, yanaji a kasan ransa kamar Allah ya kawoshi garin nan ne dan ya ceci wannan baiwar Allah. Tunani guda d’aya ne ya tsayamai dole ne shi ha dauki nauyin biyan wannan bashin kila itace mafita. Mikewa yai ya fito daga dakin, ba kowa a wajen hakan yasa ya fita daga gidan. Toh fah!!!! Ganinsa yai a tsurar daji baya ganin komai sai daji mamaki ne ya kamashi, yanzu ace mutum ne yake rayuwa anan? Sai kace mara gaskiya? Jiyai ance kai waye nan? Da fillo akai maganar, Juyawa yai dan jin yasan kamar mai muryar nan. Ya kalleshi tare da da dan yin kasa dakai sannan ya mikamai hannu alamar gaisuwa, Datti ya bugamai harara sannan yace ” me kake anan? ” Yaa fada tare da kallan kayan jikinsa kamar yasan kayan nan, shikam dan binni ya daure ya sauke hannunsa sannan yace ” Dan Allah cikin gari nake tambaya. Jin yamai hausa yasa Datti yace ” Ka mike nan hanyar inkai tafiya mai tsaye zakaga gari. ” Bai jira komai ba yace ” Na gode yai gaba. ” Datti ya bishi da kallo kamar kayansa, sai dai ta ina kayansa zaije gun wannann kad’on? Yayi tafiya mai nisa dan har ya gaji sannan yaga gari, a ransa yace nan ne garin? Kauye ne sai dai yanada girma sosai ga mutane sunata hada hadarsu, wajen wani mai tabir din rake ya tsaya ya mikamai hannu suka gaisa sannan yace ” Dan Allah akwai ATM anan kusa? ” Kallan mamaki mai raken ya masa yace ” A me? ” Yadan dafa kansa sannan yace ” Banki fa? ” Me raki ya kalleshi sosai kana ganinshi duk da rigar dake jikinsa zaka gane ba daga nan yake ba, ya girgiza mai kai alamar bai sani ba sannan yace ” amma kaje can gurin masu mashina akwai Dan liti wanda yai karatun boko sai ka tambaye shi. ” Yamai godiya sannan ya karasa gun masu mashina, sallama ya musu sannan ya tambayesu waye D’an liti, wanda ke zaune ya sha riga da wando ya wani tsuke shi a dole dan boko ya kalleshi yace ” Yes ganinan. ” Kallansa yai ya wani daura kafa d’aya kan d’aya akan mashin, dariya tadan so kamashi ya daure yace ” Dan Allah tambaya nake san ma. ” Dan litti ya dan wani rangwad’a kai sannan yace ” what is your ansa? . ” wai so yake yace “what is your question?” lol Dariya ce ta kama Dan binni yai kasa da kansa tareda murmusawa jiyai abokansa sunce ” Kai Dan litti ka kure gayu fa. ” Dan litti ya wani sosa keya irin jin dadin nan, Dan binni ya dago sannan yace ” So nake in tambayeka ko akwai ATM anan kusa.” Fuska dan litti ya canza yadan gyara zama sannan yace ” AT me? ” Dan binni yai murmushi yace ” ka gane mana inda ake cirar kudi ba tare da anshiga banki ba. ” Tafi Dan litti yai yace ” Ohhhhhh ATN? Ha ha ha kai ne bakamin bayani ba, akwai amma gaskiya sai dai muje can gwaram. ” Dan binni yace ” inane kenan? ” Dan litti yai murmushi yace ” local gommant d’in mu.” Kai ya jinjina alamar gamsuwa sannan yace ” Zai kai minti nawa kan mu isa? ” ” A kalla minti 40 inaji. ” Shiru Dan binni yai sannan yace ” Muje to Allah yasa mu dawo kan azahar. ” Dan litti yace ” Maganar kudina fa?” ” in mun dawo mayi maganar ai tare zamu mu dawo tare. ” Dan litti ya kwama glass dinsa sannan yace ” Hau muje. “1 Dan binni ya hau yana tunanin yanda zaiyi tafiyar kusan hour daya da rabi akan mashin shida rabonsa da mashin har ya manta inbadai race suke da ‘yan uwansa ba shima race d’in sun dade basuyi ba kasancewar canjin yanayi da suke fuskanta a tsakaninsu. ************ Nafi zuciya d’aya tana gama aiki ta shigo gun D’an binni sai dai me? Ba shi ba alamarsa, tsoro da fargaba ne suka kamata nan ta fito ta shiga nemansa sai dai samm babu shi, idanunta ne suka ciciko da kwalla tace ” Wato ya warke shine ko sallama baxai min bako? Me yasa mutane suke min haka? Kowa baya sona? Kowa bai damuwa da halin da nake ciki ko wanda zan shiga? Wato shi kuma wannan zuciyarsa mara rama alkairi ce ko???????? Sun fara tafiya akan Mashin Dan litti yace ” Amma da alama kai ba dan garin nan bane ba ko?”+ Murmushi yai sannan yace ” ni ba dan garin nan bane kuma yau nakesa ran barin nan.” Dan litti yadan juyo sannan yace ” When are u fom?” Ya fada cikin irin isar nan wai shi a dole kwarare, Dariya Dan binni yasa hakan yasa Dan litti yace ” U don’t say English? ” Dan binni kam dariya yake yi har ransa hakan yadan sa ran Dan litti ya soso, yace ” Malam menene hakan ka sani a gaba sai dariya kake?” Dan binni ya daure yace ” A wacce makaranta kau karatu ne haka?” Mazewa dan litti yai yace ” Anan makarantar Gomnati ta Gwaram.” Yadan kare hade rai yace ” what matter?” Dan binni yace ” lalai naga kanata kokari ne wajen yin turanci.” Dan litti yai wani murmushin isa da takama yace ” Kaf garin mu ni kadai ne nai karatu hakan yasa mahaifina ke ji dani kamar kwai sannan yan mata suke sona.” Dan binni ya jinjina kai yace ” hmmm gaskiya kam a garin Jahilai dama ai……” Dan litti yace ” me kace?” Kai ya juya batareda yace komai ba. Inya tuna turancin Dan litti kawai sai ya saki murmushi lalai ana kwab’a a kasar nan. Tun yanajin dadin tafiya yana kalle kallen kauye har ya gaji kawai ya zauna yai dif. Yanaji Dan litti nata bashu labarin makaranta, shidai kam jinsa kawai yake fatansa Allah yasa suje su dawo kafin bakin alkalami ya bushe. Sunyi tafiya sosai kafin su isa Gwaram, nan Dan litti ya karasa bakin banki ya tsaya, ya kalli Dan binni yace ” Gashi mun iso.” Dan binni ya kalli bankin sannan ya kalli ATM din dake gun guda biyu ne a jere saidai mutanen dake tsaye a gun sunfi 20, wata iska ya furzar sannan yace ” Dan litti ba wani sai wannan?” Dan litti ya kalli mutanen gun yace ” Kasan karshen wata yayi ko munje wani gun ma hakan ne gwara mu tsaya anan.” Dan binni ya kalli mutanen gun sannan ya tuna Nafi wacce ake neman ruguza mata rayuwa, takawa yai yaje har ya tsaya a layi yaga abin kamar bazai yiwu ba, hakan yasa ya karasa ya fara neman alfarma, abinda tunda yake arayuwarsa bai tab’a yi ba kenan wai ace shi ne ya rusunar da kai yake neman alfarma gun wasu, ya taso rayuwarsa ba abinda ya rasa, haka ya daure yai ta neman alfarma har ya dawo na 8, suna nan tsaye har aka zi kansa, ya zaro wallet dinsa dake aljihun wandansa ya ciro ATM card dinsa ya sa. Dubu Ashirin ashirn sau biyu ya cira sannan ya ciri dubu goma ya kama hamsin kenan, ya musu godiya ya karasa gun Dan litti, tafi Dan litti yamai yace ” Gaskiya ka birgeni yanzu mu tafi?” Dan binni ya kalleshi yace ” yunwa dai nake dan ji.” Dan litti yace ” Ga mai Yam da Egg can muje sai ka siya.” Murmushi yai sannan yace ” Lalai Dan litti dan boko.” Dan litti ya shafa keya yace ” Can we went?” Dan binni ya juya kai sannan suka karasa gun mai doya, kashi biyu yace asa musu wato shida Dan litti, har zasu juya sai ya koma yace a kara samai wani daban, haka kawai yaji zuciyarshi ta tuno mai da Nafi. Dan litti ya shiga godiya nan suka ci sukasha leman kwalba sannan suka mike suka juya. ************ A can rigar Datti kuwa Nafi ce zaune a dakinta banda kuka ba abinda takeyi ga bakin cikin auren da za’ a mata gana guduwar dan binni, mamaki ne ya kamata dataji mutane suna sallama, nan ta fito dan tasan su ba baki suke ba tunda Baffa baso yake ba, turus ta tsaya tana kallan kanwan mamanta, sai dai ta kasa farin cikin ganinta sam. STORY CONTINUES BELOW Ganin haka yasa ta matso tare da rungume Nafi tace ” Nafi shine kina ganina zaki shareni? Bayan har da kawarki Hanne nazo miki da ita? ” Nafi ta maida hawayenta sannan tace ” Aunty nayi mamakin ganinki ne.” Tace” ai daga ke har Datti baku kyauta mana ba wau sai dazu aka turo mana almajiri wai yau ake auren ki? Haba Nafi ai ko Datti bai sanar damu ba ke kya fada mana ai.” Nafi kam kasa magana tai dan batasan taka maimai mema zata ceba cewa zatai an bada ita biyan bashi ko me? Hanne ce ta matso kusa da ita tace ” Nafi ya naga ba kowa a gidan? Kamar ba biki za’ai ba?” Nafi ta share hawayenta tace ” eh kinsan Baffa bayasan mutanene shiyasa.” Baki Hanne ta tab’e tace ” amma dai duk da haka, sannan ke ma kalleki kamar ba Amarya ba ko wanka ma da alama bakiyi ba.” Nafi tadan juya kanta gefe, Nan Maman Hanne tasa Hanne ta debo ruwa, da kanta ta tasata gaba sukaje ta wanketa fes, sannan suka fito, kayan Nafi ta kalla sam bana arziki bare aje ga sabo haushi da tausayi suka kamata ta kalli Hanne tace ” Hanne da alama ke zaki taimaka ki ciro kayan jikinki ta saka inyaso ke sai kisa nata.” Hanne ta kalli Nafi tace ” Allah Nafi shi yasa kike ban haushi ke wai bazaki taba cewa asai miki kaya ba? Ko sanda innarku nanan itama banga ta wani damu da miki dinki ba, yanzu dan Allah meye amfanin hakan?” Nafi tai kasa dakai, Hanne taja wani dogon tsaki tace ” sam ita wannan a kidahuman ma ita ta dabance, fa tsinanan kawaici da hakuri, wallahi babu inda zakiji ba’a cuce ki ba indai haka zaki cigaba.” Maman ta tace ” to ya isheni uwar ‘yan masifa.” Nan Hanne ta cire kayanta tana masifa. Nafi ta saka kayan sun amsheta kuwa nan Hanne ta shafa mata hoda tana shirin yi mata ja gira da kwalli Nafi tace ” Bashi Hanne kema kinsan banasan kwalliya.” Hanne ta mike cikin takaici tace ” ni dai kam ban taba ganin mutum irin ki ba, gaskiya Nafi kina neman addu’a ni wallahi haushi wannan halayen naki suke bani.” Tana kainan tai hanyar waje, jitai Nafi tace ” kiyi hakuri Hanne ba bata miki rai naso yi ba.” Hanne ta kara had’e rai tace ” kinganta ko Goggo? Yanzu me tayi na bada hakuri dan Allah?” Tai waje ba tareda ta jira amsa ba. Maman Hanne ta kalli Nafi tace ” Nafi kiyi hakuri kinsan kawartaki akwai masifa.” Hanne ce ta shigo cikin mamaki tace ” Nafi naga sun fara taruwa inaji yanzu za’a daura, ni ko mijin ban gani ba.” Gaban Nafi ne ya fadi tanasan yin kuka ba kuma taso su Hanne da mahaifiyarta susan halin da ake ciki, kasa kawai tai da kanta tana karanta Inalilahi a zuciyarta. Ango kam yasha babbar riga haka kuma ya taho da abokanansa dayawa dama yan uwa da makota, sannan sun taho da liman da maroka, Datti ne yashigo gida fuskarsa a sake wasai ko a jikinsa, ya zura riga babba shima, yanajin Mahaifiyar Hanne na gaisheshi ya shareta yai waje. Ta birma manya aka shimfida musu sannan Ali ya taho da goro nan aka ajiye, Aka dan gagaisa sannan aka zauna. A ciki kuwa mahaifiyar Hanne ce ta kalli Nafi tace ” Nafi amma an miki komai na kayan daki ko?” Nafi ta kalleta tare da kakaro murmushi kawai amma batace komai ba, hakan yasa itama tai shiru. An gama addu’oi nan aka ce ina Walliyin Alhaji Ali? Wani kanin mahifinsa yace ” Ganinan.” Akace walliyin Nafi fa? Datti yace gani. Kallan mamaki suka bishi dashi sukace ” Dakanka malam Datti? Ai kyanta wani dan uwanka na kusa zaka wakilta.” Datti ya hade rai yace ” wannan damuwarku ce amma nine zan zama walliyi a auren ‘yata ehe.” Sunyi shiru, liman ya kalli Ali, kai Ali ya daga mai akan ba komai a kyaleshi, nan liman yace to shikenan yanzu zamu gabatar da……… Ji sukai ance ” Ba abinda zaku gabatar domin kuwa ni na hana wannan auren.” Gaba daya suka juyo suka kalli inda maganar ke fito wa, ga mamakinsu wani saurayi ne ya sauka daga kan mashin sannan ya fara takowa gunsu cikin isa da takama, basusan fuskarba sai dai Datti yasanshi dan kuwa bai manta shi ba. Dan binni ya karaso inda suke zaune ya gaida liman sannan ya kalli Ali wanda yasha manyan kaya, ba shakka ya girmi mahaifin Nafi lalai mutanen nan basuda imani. Ali ya harareshi yace ” Kai menene kakeyi haka? Ba ka gani aure ake shirin daurawa?” Dan binni yai murmushi yace ” Aure? Dama haka ake aure?” Ali da ‘yan koronsa suka mike sukace ” kai meye hakan? ” Dan binni yasa hannu a aljihu ya ciro dubu ashirin daya waresu tun a banku yace ” ungo! Ba bashi kake binsu ba har kake tunanin kwace mutum akan wata banza dubu ashirin dan tsabar rashin imani?” Ali ya kalli kudin sannan yace ” ni na yafe Nafi nakeso a auren.” Dan binni yace ” Ai kuwa baka isa ba, yarinya ba sanka take ba kuma baka isa ka aureta ba, kai ko kunya ma bakaji ba kana yayan mahaifinta? Inbanda zuciyarka irin ta yarace ina kai ina neman wace batafi sa’an ‘ya’yanka ba?” Datti dake zaune ya mike tsaye yace ” Kai wai kai waye ne? Menene naka a ciki? ” Dan binni ya kalli Datti cikin takaici yace ” nine wanda ‘yarka ta taimaka a lokacin da nake kan karagar mutuwa ta.” Mamaki ya kama datti dama sauran ‘yan gun, Datti yace ” to naji, daga taimako sai akace ka isa da ita? Ka dubafa kaga yarinyar nan ta girma amma ba miji, in ka korar mata wannan d’in kai ne zaka aureta ko me?” Gaba daya kallo yakoma kan Dan binni suna jiran amsarsa. Gabansa ne ya fad’i baiyi tunanin abin zai juye haka ba, me kenan? Daga taimako?” Ali ya matso kusa dashi shima yace ” eh muna jinka kai ne zaka aureta ko me?” Innalilahi wa ina ilaihi raji’un!!!! Allahuma Ajirni fi Masibati wa aklifni kairan minha…… Addu’ar da Dan binni ya shiga yi kenan a ransa. Gaba d’aya hankalinsa yakai kololuwar tashi muryar Ali yaji yana cewa ” Kai yaro dakai muke magana, Kai zaka aureta amaimako na ko me? Yaran yanzu banda tsugudidi basuda aikin yi inbanda munafirci da shiga shara ba shanu dan ta taimakeka meye naka na shiga shirgin rayuwarta?”+ Dan binni ya kalleshi cikin bacin rai yace ” kai yanzu in ‘yar ka ce zata auri sa’anka ko wanda yafika zakaji dadi?” Ali ya kwashe da dariya yace ” to menene? Baifi karin zumunci ba.” Dan binni zaiyi magana yaji an dafashi, juyawa yai dan ganin waye, ga mamakinsa dan litti ya gani a tsaye a bayanshi, ya kalli Dan litti cikin wani yanayi. Dan litti yace ” Abokina ka fita harkarnan tun kafin kuzo kuna arment.” Dan binni ya kalleshi yace ” meye arment?” D’an Litti ya wani sosa kai su kuma mutane suka kalleshi da sha’awa jin yana turanci. D’an litti yace ” baka gane ba? Kar kuzo kuna musu nake nufi.” Wani kululun takaici ne ya kamashi dama mutanen gun nan sun gama kona mai rai shikuma D’an litti zai so mai da wani sabon takaici wai arguments ne arment? Kallanshi ya maida kan Liman wanda yake cewa ” ni yanzu a wani matsayi nake? Datti yace ” Aure za’a daura da Ali yanzun nan.” Ali ya gyara rigarsa, haushi ya kara turnuke dan binni yace ” in kuma nace zan aureta fa?” Gaba d’aya kowa juyawa yai ya kalleshi cikin tsananin mamaki, Datti yace ” Kana nufin zaka aurenta?” Gaban D’an Binni ya fad’i ya daure yace ” Eh.” Abinda kawaj zuciyarshi take rayamai Allah ya kawoshi garin nan ne dan ya taimake ta.” Matsowa D’an litti yai da kansa saitin kunnen D’an binni yace ” I am Crazy? Kasan me kake kuwa?” Dan binni ya juya ya kalli D’an litti sannan ya kalli Ali wanda yake hucci kamar zaki, shi a tunanin sa ai dan yace zai aureta baza’ace yanzu ba. Sai dai abinda kunnensa ya jiyo masa ya tada masa hankali, jiyai Datti yace ” to Liman yanzu sai a daura da wannan shikuma Ali sai ya amshi kudinsa yai gaba.” Kallan Datti yai cikin tsananin mamaki yace ” nikam ka tabbatar kaine mahaifinta?” Datti ya had’e rai yace ” wani banza zance kake yi hakan? In ba ‘yata bace ‘yar kace?” Dan binni ya dafa kai zaiyi magana yaji Ali yace ” da alama bai shirya ba gwara a daura dani……” Kallan da D’an binni yamai ne yasa yai shiru, yace ” na dauka nace a daura dani?” Datti yace ” to banga alamar kanaso ba gashi mu kana bata mana lokaci.” D’an binni ya ciro d’ayan dubu ashirin d’in wanda ya d’auko domin ba Nafi inzai tafi ya mikama D’an litti yace ” Sadaki ne mika musu.” D’an litti ya jinjina kai cikin mamaki yace ” Lalai I am crazy.” Yana kai nan ya karasa gun Liman yace ” wai ga sadakin Wancan.” Liman ya kalleshi yace ” to waye zai mai walliyanta? ” Datti ganin damin kudi yasa cikin saurin murya yace ” Ladan kawai yamai ai musulmi dan uwan musulmi ne.” D’an binni ya bishi da kallan mamaki lalai mutanen nan basuda cikaken hankali kaf cikinsu ba wanda ya tambayi inda yake? Mugu ne shi? Haka kawai suke neman bashi ‘ya ba wani bincike. Jiyai Ladan yace ” Ya sunan ka? ” ” ASHRAF” Abinda ya fito daga bakinsa kenan, yana tsaye har aka gama d’aurin auren Nafisa da Ashraf akan sadaki dubu ashirin. STORY CONTINUES BELOW Nan su Ali da mukarabansa suka watse cikin tsananin takaici, Datti wanda ya cafki kudin sadaki ne ya matso kusa da Ashraf yace ” Ashaf yanzu inane inda za’a kai ma Amaryarka?” Kallan Datti yai cikin mugun takaici yace ” Na dauka baka damu da inda za’a kai ‘yarka ba tunda banga alamun kanaso ka sani ba.” Ya kafe Datti da ido yace ” me Nafi take ma wanda kakeso tabar ma gidanka kota halin ka ka?” Datti yad’an had’e rai yace ” Kai Ashaf dan ka zama mijinta an fadama kanada damar fadamin magana san ranka?” Ashraf ya kalli D’an litti yace ” Please d’an jira ta fito mu tafi ka saukemu, dan banga alamar mashin ba ko zaka samomana d’aya saboda mu biyu ne?” D’an litti yace ” ba problem kaje ku shiryo I will came with one. ” Ashraf ya d’an yi murmushi kadan sannan ya kalli Datti yace ” a sanar da ita ta shirya dan ni ba anan garin nake ba.” Datti yace ” me?” Ashraf ya juya kai bai kara magana ba, har Datti sai sake magana sai ya fasa ya shiga ciki. Nafi kam ta kule a bayan gida banda kuka batada aiki shikenan Allah ne kadai yasan wace rayuwar zata fara daga yau, ina zata sa kanta?” Jitai Hanne na kiranta, hakan yasa ta goge hawayen ta tafito, Hanne ta kalleta tace ” kuka kike?” Nafi tace ” a’a.” Hanne tai tsaki tace ” wato memakon kiyi kuka a gabanmu mu samu damar lallashinki ki gwammace kinyi kuka ke kadai kin share hawayenki? Nafi nikam ina tsananin mamakin halayenki.” Tai gaba, Nafi ta bi ta a baya, har sunyi hanyar dakinta ta kalli igiya inda ta shanya kayan D’an binni ka ra sawa tai ta zare rigar ta rike a hannunta. D’aki ta shiga ga mamakinta Datti ta gani zaune akan tabirma wanda rabon da ko dakinta ya leka yaga a wani hali take ciki ita kanta ta manta. Shiga tai kanta a kasa, ta gaidashi sannan ta zauna kusa da Maman Hanne. Datti ya kallesu yace ” To aure dai an daura sai dai an samu canji daga Ali zuwa wani Ashaf.” Cikin tsananin mamaki Nafi ta d’ago ta kalli Baffa tace ” Ashaf?” Datti ya jinjina kai yace ” Kwarai nikaina nafisanshi akan Ali da alama yana da arziki sannan kuma shi saurayi ne.” Maman Hanne ta kalleshi tace ” nifa sam ban fahimci me ake nufi ba, banga ne daga Ali ba an koma Ashaf? Meye ma wani Ashaf? Ni bantaba jin sunan ba.” Datti ya buga mata wani kallo yace ” meye naki a ciki? ‘ yata ce ba ‘yar uban kowa ba sannan in baki tabajin suna Ashaf ba yau ai kinji.” Ya mike rai a bace sannan yace ” ke kuma ki shirya yanzun nan dan yace ba agarin nan yake ba zaku wuce yanzu.” Kallan mamaki kawai take ma babanta ta sani shi dabobinshi su kadai ne abinda ke gabansa kuma suka dameshi sai dai bata taba tunanin zai ma ‘yarsa ta cikinsa haka ba, sai kace wata kaza? Ganin kallan datake mai yasa yace ” in tunanin sadakinki kikeyi kima manta dan nima na dauki rabona na satar da uwarki tamin, yana kainan yai waje. Nafi kam kuka ma kasa zuwa mata yai jitai idanunta sun kafe kaf, sai dai rigar dake hannunta kawai ta shiga ninkewa jitake zuciyarya kamar zata tsage, Maman Hanne ta kalleta tace ” Nafi ki taimaka ki fadamin abinda ke faruwa dan Allah.” Nafi ta kalleta tace ” Auntu ko na fada miki menene amfani? Tunda aikin gama ya riga ya gama? ” Hanne ta mike cikin takaici tai waje. Nafi kam a zaune kawai take tana jiyo muryar Datti yana cewa suyi sauri. Ashraf kam yana tsaye a waje tunani sun taru sun mai yawa, ina zai sa kansa? Mai zai cewa masoyiyarsa kuma ‘yar uwarsa wacce saura wata biyu a daura musu aure? Yasan ta sarai yanda take tsananin so da kishinsa lalai zata iya yin komai inhar taji abinda ya faru, kansa ya dafa wanda yakeji yana sara mai. Karar mashin ne yasa ya kalli hanya, Su D’an litti ya hango nan suka karaso D’an litti ya kalleshi yace ” yama kace name d’inka?” “ASHRAF. ” D’an litti yai murmushi yace ” Gaskiya an cucen da aka samin D’an litti sunan ka yafimin dadi.” Ashraf yai musrmushi sannan yace ” D’an litti kenan.” Datti ne ya fito ya tsaya kusa da Ashraf yace ” Ashaf gatannan amma ya za’ayi in anaso aje gunta ina zance? ” Ashraf ya kalleshi sannan yace ” Kano anan garin nake, sannan ai kasan sunana.”yai maganar cikin bacin rai. D’an litti ya tafa mai yace ” Haba? Living Kano? I also came to kano.” Ashraf ya furzar da iskar takaici yace ” nikam D’an litti kadingamin hausa banasan turancin nan.” Dariya Datti yai yace ” gaskiya kam, yanzu kenan in wasu zasuje sai D’an litti ka rakasu ko?” D’an litti yai murmushi tare da sosa keya. Nafice ta fito sanye da lulub’i Hanne da mamanta na gefenta, Hanne ce ta kalli mazan gun su uku, tace waye mijin a ciki? Ta fada tana fatan Allah yasa ba wannan bane dan ya birgeta Allah yasa D’an litti ne.” Gani tai D’an litti ya nuna wanda yai masifar burgeta da yatsa, dukda rigar kauye ce a jikinsa kana ganinshi kasan daban yake, tadan yi yake tace ” to a rike mana ‘yar uwarmu dakyau, amma bamu zamu kaita ba?” . Datti yace ” bakiji me nace ba aciki ko kuma wani sabon kinibibi ne hakan? Ai nace su biyu zasu tafi ko?” Mamaki ne ya kama maman Hanne tace ” su biyu? Dama abinda kake nufi kenan? Taya zamu bari ‘yar mu ta tafi daga ita sai shi? ” Datti yace ” karki damu D’an litti yasan gidan.” Tai shiru, Nafi kam hawaye ne ya fara zubo mata itakam tana ganin rayuwa? Wasa wasa kaza ma ta fita matsayi itakam. Jitai ance ” Ina rigata? Ko kin barmin wannan?” D’agowa tai cikin tsananin mamaki, idanunsu ne suka hadu……..gabanta ne ya shiga fad’uwa sai dai ta kasa dauke ido daga kansa, ya sakar mata wani sansanyan murmushi……..