TSANANI CHAPTER 20 THEND KARSHE

TSANANI






CHAPTER 20 THEND KARSHE




Komawa bacci nayi sbd tsananin gajiyar da nayi, shi kuma ya fita ya bar d’akin, ban farka ba sai da gari yayi haske sosai, a hankali na fara sakkowa daga kan gadon kowace gaba ta jikina ciwo take yi, banɗaki na wuce nayi wanka, fitowa nayi jikina daure da towel na xauna a gaban dressing mirror ina goge ruwan jikina tare da shafe jikina da humra da mayuka masu kamshi, ban yi aune ba naji mutum a bayana ta cikin mudubi na hango shi, ya rataya hannun shi a wuyana tare da sauke wani nannauyar ajiyar zuciya, yana ta shaƙar kamshin turaren jikina, a hankali na d’aga kai na kalle shi wani murmushi ya sakar min tare da juyo da ni muna fuskantar juna, saurin sunkuyar da kaina nayi sbd wani kallo da yake bi na da shi, sabule towel din da ke jikina yayi ya shiga jagwalgwala ni.
A hankali ya saita bakin shi da nawa cikin wata irin murya yace
“Barka da tashi babyna”
Kaina a sunkuye na amsa da
Barkanka babyna ina fatan ka tashi lafiya”
D’ago fuskata yayi ya tsotsi lips dina cike da tsokana yace
“Ya gajiyar jiya?”
Dan hararar shi nayi ban bashi amsa ba na juya tare da rufe idanuna da tafukan hannuna.
Juyo dani yayi yana murmushi
“Wai kunyata kike ji sa’ar mata? Lallai kina da aiki, ki bani amsa ko kuma yanxu na cire miki kunyar nan don ni bana son mace ta rika jin kunyar mijinta”
Ban iya bashi amsa ba sai ƙara shigar da kaina jikin shi da nayi ina jin wani tsananin kunyar shi.
Cikin rad’a yace
“Tunda ba amsa bari ki gani a aikace”
Kukan shagwaba na shiga yi masa, ina bashi hakuri amma sam bai saurare ni ba
sai da yayi mai isar sa sannan ya kyale ni ya kaini bathroom nayi wanka sannan ya shiga shirya ni, wasu English wears ya dakko min da kan shi ya saka min sannan ya daure min gashina kayan sun yi min kyau sosai, goya ni yayi a bayan shi sai da ya kaini har dining sannan ya dire ni.

Tararwa nayi ya soya mana chips da kwai ya haɗa mana tea mai kauri, a hankali ya janyo ni na faɗa kirjinshi na kwantar da kaina yana bani, ɗan kaɗan na iya ci na kawar da kaina alamar na koshi, tsare ni yayi da ido yana kallona.

“Ki ci abincin nan idan ba haka ba kuma kin san me xai biyo baya”
Ban yi masa musu ba na karba ina ci, da kyar nake tura abincin sbd bakina ba daɗi, duk fargaba ta tafar min da dandanon bakina, sai da muka koshi ya taimaka min muka gyara gidanmu muka yi turaren wuta.

Shiryawa yayi yace xai tafi gida ya gaida su mama, raina bai so ba na kyale shi ya tafi, sbd bana son xama ni kaɗai gashi har yamma tayi babu wanda ya leko inda nake, sai da nayi kuka da xamu rabu.

Kafin ya dawo na shiga kitchen nayi masa sakwara miyar agushi, na haɗa masa coconut juice, sbd na san yana son sakwara, Ina gamawa na shirya cikin wani material red color dinkin ya karbi jikina sosai, na sha kamshi ta ko’ina gidana ma kamshin yake yi, ina jin shigowar shi na fita da gudu na rungume shi tare da sumbatar goshinsa, kayan da ke hannun shi na karba muka shigo parlour, takalmansa na cire masa tare da rage masa kayan da ke jikinsa, sannan nayi masa sannu da xuwa, kama hannun shi nayi na kai shi dining sai da na tabbatar ya koshi sannan na kai shi bathroom na hada masa ruwan wanka, naxo fitowa ya janyo ni, shi sam baxan fita ba sai dai mu yi wankan tare, haka dai na daure muka yi wankan tare, Bayan mun shirya ya miko min wata leda yace yayar shi Aunty zainab ta bayar a bani.

Bude ledar na shiga yi kayan mata ne kala-kala a kunyace na dube shi.
“Yanzu duk wannan Aunty zainab tace a bani?”
Kallona yayi gami da shafa kwantaccen gashin fuskarsa
“Eh ta bayar ne ki kula da kaninta sosai, da har xan faɗa mata ma yadda kike tsoron kulawa da kaninta”

Da sauri na toshe masa baki a marairaice nace
“Amma dai baka fada mata ba ko”
Dan murmushi yayi wanda yake ƙara bayyanar masa da kyan sa.
“Idan kika cigaba xan fada ne ni kin san ba ruwana”

Yadda xan yi amfani da maganin ya shiga nuna min, a lokacin yasa na sha wani, naji dadin shi sosai don naji sassaucin xafin da nake ji.

Yau kusan satina ɗaya da kwana ɗaya babu wanda yaxo daga ɓangarena ko Rukayya bata dawo ba, don haka na ɗauki wayata nayi ta buge-bugen waya ina musu mitar baso zo sun ganni ba, Addah saratu na kira.

Cike da shagwaba nayi mata sallama
“Tunda ku ka kaini ku ka cillar dani babu wanda yaxo yaga halin da nake ciki ko Adda?”
Na ƙarasa maganar ina turo bakina kamar tana ganina.

Murmushi tayi
“Ya za a yi mu zo Sa’adatu mu hana ki jin dadi ke da mijinki, ke fa na tambaye ki ran nan ina kika je kika ce min wajen mijinki, shi yasa muka ‘ki xuwa kada mu zo ki kore mu”

Rufe fuskata nayi
“Haba dai Adda ni na isa na kore ki”

“Ai naga rashin kunyar ki ta girma ne Sa’adatu, shi yasa muka koma gefe, to ya gidan da me gidan da fatan dai komai lafiya”

“Lafiya lau Adda komai lafiya, sai dai ina shan wuya sosai a hannun shi”
Na ƙarasa maganar kamar xan yi kuka.

Dariya tayi har sai da naji sautin ta a cikin kunnena.

“Ba dai ke kike xumudi ba ai gashi nan kin gamu da dai-dai ke”

Shawarwarin yadda xan kula da kaina ta riƙa bani, godiya nayi mata tare da tambayar yaushe xasu xo, bata bani amsa ba ta kashe wayar.

Rayuwa mai cike da soyayya muke yi ni da izuddeen yana matukar kulawa da ni, ban taɓa neman wani abu a wajensa na rasa ba uwa uba ga soyayya, gashi yanxu har na fara sabawa da fitinarsa musamman da nake amfani da magungunan da Aunty zainab ta bani, kuma shawarar Adda saratu tana min tasiri sosai.

*********

A ɓangaren A’isha kuwa abin ba a cewa komai, gida ne babba aka kaita, sai dai gidan ba shi da wani kyan fasali, dankare yake da ya’ya, kowannen su babu uwarsa a gidan, gaba ɗaya gidan ya mutu da kazanta komai, girkin gidan gaba daya ita take yi, babu wanda yake taya ta a cikin yaran ga uwar rashin kunya da suke mata, tana yi wa yaro magana xai hau yi mata rashin kunya tare da xaginta, babu wata kulawa ko soyayya daga ɓangaren mai gidanta, don basu ci amarci da Alhaji yawale ba ya fara nuna halinsa, ko abincin kirki baya iya kawo mata, yanzu babu damar tayi masa gyara sai ya hau xaginta yana kiranta da yar matsiyata a sati biyun nan da suka yi har ta fara kwantsamewa, babban abinda ke tayar mata da hankali, babu damar yan uwanta su zo gidan sai ya hau yi musu korar kare gami da faɗa musu bakaken maganganu, wannan yasa babu mai ra’barta, da na sani da nadama duk sun cika zuciyarta, naci take masa a kan ya bari taje taga innarta amma ko kaɗan ya hanata dama shi sharadin gidansa ne ba a fita sai yaga dama, komai na rayuwar ta ya fara dagule mata, haushin Innah Salamatu take ji sbd ita ce taa hadata da wannan ƙaddarar.Satina huɗu a gidan izuddeen Rukayya ta kira ni a waya cewa xata kawo min xiyara, tun safiyar ranar nake murna shi kanshi ya lura da yadda nake xumudin xuwanta, don haka ya siyo min abubuwan da xan bata kyauta, tashi nayi na girka mata nau’ikan abinci kala-kala, kafin ta iso har na dameta da kira sbd ina bukatar ganin ta akwai maganganu da yawa da nake son yi da ita.

Ƙarfe biyu dai-dai ta iso gidana, da gudu na ƙarasa na rungumeta ina farin ciki, wani kallo take bi na da shi.
“Kinga yadda kika canja kika yi kyau kuwa Sa’adatu lallai izuddeen ya iya kiwo”
Gaba ɗaya muka kwashe da dariya.
“Mun iya kiwo dai, nima baki ga yadda na mayar da shi ba har ya fara tumbi”
Murmushi tayi gami da dukan bayana.
“Daga aure kuma sai tumbi tsabar sharri Sa’adatu”
Jan hannunta nayi muka shiga ɗaya daga cikin dakuna na, a kan gado muka xauna muna hirar mu ta aminai, labarin bikinta ta shiga bani, da irin hidimar da doctor yake yi mata, don yanzu zancen da ake yi ma har an kusa kawo kayan lefe, ba ƙaramin murna na taya ta ba, don na san xata samu cikakkiyar kulawa a wajen doctor sbd Mutum ne mai saukin hali, kamar yadda nake samu a wajen izuddeen, bata tafi ba har sai wajen sallar magariba kamar baxa mu rabu ba haka naji a raina, sai da muka haɗa mata sha tara ta arxiki ba ƙaramin dadi taji ba, har bakin gate nayi mata rakiya sannan na dawo.

Kitchen na wuce na shiga haɗa mana abincin da xamu ci da daddare, shi kuma ogan nawa yana daki ban san me yake yi a ciki ba, sai da na kammala na shiga, tarar da shi nayi ya fito daga bathroom d’aure yake da towel yana goge jikin shi, kyakkyawar fatarsa da muradadden jikinsa na lafiyyyen qaqqarfan ɗa namiji ya bayyana, jikinsa sai she’ki yake yi sbd hutun da ya bi fatarsa, gashi ne kwance a kirjinsa, ko kaɗan bai lura da shigowata ba.

Tsayawa yayi gaban mirror yana cigaba da goge jikinsa tare da taje gashin kansa, da kwantaccen sajen da yake ƙara fito masa da ainihin kyawunsa, a hankali na ƙarasa kusa da shi ina sakin siririn murmushi, shaukin son shi da kaunar shi na dokar min xuciyata, ta cikin mirror ya hango ni ina yi masa masa murmushi juyo wa yayi tare da lumshe kyawawan idanunsa, a hankali cikin sigar rikitarwa nasa hannu na fara shafo kwantaccen gashin da ke kirjinsa.
Sake lumshe idonsa yayi yana bi na da wani irin kasalallen kallo tare da bin hannuwana da kallo.

Bai yi tsammani ba yaji hannuna a bayan shi ina shafa shi tare da sabule towel din da ke jikinsa, a hankali ya saki wani shu’umin murmushi tare da kwanto da ni jikinshi, yana shafar duk wata gaba ta jikina.

Haɗa fuskata yayi da tashi, tare da danna kanshi cikin jikina yana shaƙar kamshin turarena, cikin wani salo ya ɗauke ni cak ya dora bisa bed din da ke ɗakin, ya shiga aikin da ya saba a ranar na gane kuskure na domin kuwa ni na fara tsokano shi cikin salo da kwarewa da baiwar da Allah yayi masa ta rikita ‘ya mace ya fitar da ni daga hayyacina, sarrafa ni yake ta ko’ina.

Sai da na sarrafu iya sarrafuwa sannan ya dawo cikin nutsuwar shi wanka muka yi, sannan yaja hannuna muka fita zuwa dining.

A baki na riƙa bashi abincin har sai da ya ci ya koshi, juyo da fuskata yayi ya sakar min wani hoto kiss, sannan ya jawo ni jikinshi cikin rad’a yake min magana.
“Kina da baiwa sosai Sa’adatu, baxan gajiya da yi miki hidima ba fatana Allah ya bani abinda xan cigaba da kulawa da ke har ƙarshen rayuwata, amma ni ban hangi wata mace bayan ki ba”

Wani malalacin murmushi na saki tare da sake manna kirjina da nashi.
“Ina jin dadi idan na bude idona naga kaine abokin rayuwata, bana fatan ranar da xan wayi gari na ganni ba tare da kai ba, burina kullum na kasance cikin kulawarka da soyayyarka”

Shafa fuskata yayi
“Har abada baxan taɓa barin ki ba ko mutuwa tare da ke nake so ta ɗauke mu, idan kika tafi kika barni ban san irin halin da xan tsinci kaina ba”
Murmushi nayi tare da kamo hannun shi ina wasa da ‘yan yatsun shi.

Juyo da ni yayi yana fuskanta ta, xuba min ido yayi na wasu mintuna sannan ya fara magana.
“Na manta ban faɗa miki ba farin cikina yau saura kwana uku na koma gurin aiki”
Xaro idanu nayi ina shirin sakin kuka, gaba ɗaya na manta izuddeen yana aiki kuma aikin ma ba a cikin garin mu ba, ban san lokacin da kuka ya kufce min ba. 

Kwanto da ni yayi yana rarrashina gami da bubbuga bayana.
“Kiyi hakuri babyna baxan dad’e ba xan dawo gare ki, niyyata sai nayi wata biyu xan tafi yanxu ma kiran gaggawa aka yi min shi yasa xan tafi, amma baxan dade ba xan dawo, kuma idan na dawo tare da ke xan tafi, kema kin san baxan iya rayuwa ba tare da ke a jikina ba” 

Idanuna cike da hawaye na d’ago na dube shi, cike da shagwaba nace
“Amma ni baxan kwana a gidan nan ba sai dai ka mayar da ni gidan Adda ko wajen innata” 

Kwantar da ni yayi a kafadarsa cikin kunnnena yake rad’a min
“Gaskiya babu inda xaki je ki kwana alhalin kina da dakin mijinki, sai dai ki xabi duk yarinyar da kike so tazo ta taya ki kwana ni kuma na yarda xan je na dakko miki ita, idan aka ganki a gida yanzu ai sai mutane su yi tsammanin ko matsala aka samu” 

Dagewa nayi sai na tafi gida da kyar ya shawo kaina na hakura na zabi ƴaƴan Adda da ƴaƴan yayarsa su ne xasu zo su taya ni xama.
Ana saura kwana ɗaya izuddeen ya koma wajen aiki duk na shiga damuwa har na fara ramewa sbd rashin abin kaunata da zan yi na wasu yan kwanaki, ban san yadda xan yi da kewar shi ba. 

Zaune nake a parlour bayan nayi sallar magarib, ina kallon wani series film na yan Turkish mai suna ÇÛƘÛR̃, gaba ɗaya na bada hankalina ga kallon film din sbd haɗuwar da yayi, ganin shi nayi ya fito daga daki sanye yake da wani yard fari kal yayi matuƙar kyau kayan sun karbi jikinsa, a  hankali yake takowa har ya ƙaraso inda nake, yana tafe yana saita agogon da yake shirin sanyawa a hannushi, wani kallo yake bi na da shi tare da ɗaga min gira, alamar na taso. 

A nutse na tako na taho tare da rungume shi, d’ago fuskata yayi
“yau film ya ɗauke miki hankali ko Angelina kin kyale mijinki yana ta aiki shi kaɗai” 

Sassauta riƙon da yayi min yayi, tare da cewa.
“ki shirya mu tafi gidan Innah da Adda mu gaishe su daga nan mu samo mai taya ki xama” 

Ji nayi kamar yayi min kyautar aljannah, ban san lokacin da na rungume shi ba ina tsallen murna, a hanzarce na shiga daki na d’akko mayafina, dama a gyare nake na sha kwalliyata, sanye nake da Gazner pink color wadda aka yi wa pant work da sky blue sai ratsin pink kaɗan, dinkin ba ƙaramin fito da kyawun shaddar yayi ba.
Mayafin da na yafa shi ma kalar panting shaddar ne, sky blue ba ƙaramin kyau nayi ba, rike da hannun juna muka fita, sai da muka biya ta wani kanti shop well ya siyawa su innah duk wani nau’in kayan abinci, tun daga kan shinkafa, hatta maggi sai da ya siya musu. 

Kama hanyar xuwa gidan muka yi, a kofar gida muka ci karo da Baba, yana ganin mu ya hau murna kamar xai goya mu haka yayi, yara muka samu suka fara shigar musu da kayan abincin da muka zo da shi, har ciki Baba yace izuddeen ya shiga ya gaida su Innah. 

Cikin Sa’a duk mutanen gidan mu suna tsakar gida, amma banda Innah Salamatu, ban san dalilin da yasa ban ganta ba, manne nake da jikin izuddeen har muka shiga cikin gidan, kana ganin mu ka san akwai soyayya mai yawa a tsakanin mu, tare  da xaman lafiya, sannan sutturar jikinmu kaɗai xata nuna maka muna cikin jin dadi da wadata, gaba ɗaya ido ya dawo kanmu sai kallon kurulla suke bin mu da shi, har ƙasa muka tsugunna muka gaishe su, sbd baƙin ciki da kyar suka iya amsawa. 

Innah na daki ta jiyo sallama ta bata iya fitowa ba sbd kunyar surukinta.
Murna a wajenta kuwa ba a magana, da murnarta ta tarbe mu tare da yi mana Barka da zuwa, dakinta muka shiga tayi mana shimfida a ladabce izuddeen ya gaisheta, sai da suka ɗan yi hira sannan ya tashi zai tafi, kuɗi mai yawa ya dan’ko ya bata ni kaina ban san adadinsu ba, nima bani nawa yayi yace duk matar da ta kwan ta tashi a gidan na bata, kayan abincin da muka zo da shi kuma na innah ne idan taga dama ta basu idan kuma ba tada ra’ayi ta riƙe nata ne. 

Tashi yayi ya tafi yace xai je gida ya gaida su Baba da Mama, sannan ya dawo ya ɗauke ni mu sake komawa na gaishe su. 

Da ya fita waje ma kuɗaɗe masu yawa ya bawa Baba, da rawar jiki ya shigo gida yana ta faman washe baki, a tsakar gida ya tsaya yana saka min albarka, ni kuma muna d’aki tare da innata muna hira, bude baki yayi sosai yana magana. 

“Wannan yarinya Sa’adatu Allah yayi miki albarka Allah yasa ki fi haka, yanxu na san na aurar da ‘ya, ‘yar kuma mai albarka da tausayi, amma da duk ba aure na yiwa ‘ya’yana ba, sai dai na siyar da akuya daga baya ta dawo tana cinye min danga, Allah dai yayi miki albarka ke da mijinki, ya ƙara haɗa kan ku ya kare ki daga sharrin masu sharri”
A hankali na amsa da ameen 

Story continues below


Kayan da muka zo da su ya shiga buɗewa, duk abinda ya d’akko sai yace Allah tayi min albarka, raba kayan ya shiga yi ya bawa Inna nata, sannan ya deberwa Innah Salamatu nata amma bai kai yawan na innah ba, ragowar guraren da ke gidanmu duk sai da ya aika musu da shi. 

Kiran zaliha yayi tana d’aki don tunda naxo ban ganta a tsakar gida ba daga ita bar innarta.
A sanyaye ta fito tana bin bango, wata harara ya dalla mata.
“Zo nan ki karbi abin arxikin da yar albarka ta kawo mana, ba irin ki ba sai dai yawon banxa da tara samari banxa ke ko koyi da ita ma bakya yi, gashi nan yanzu kin d’akko mana abin kunya, duniya sai xagin mu take ana ganin sakacin mu ne” 

Gabana ne ya fadi, sai na tsinci kaina cikin damuwa haɗe da tausayin halin da zaliha ta samu kanta, cike da damuwa na dubi Innah.
“Kin ji abinda Baba yake faɗa kuwa innah, anya kuwa haka ne abinda ya faɗa? nima fa haka ya riƙa yi min wannan kazafin a kwanakin baya” 

Rausayar da kai tayi
“Gaskiya ne abinda ya faɗa, ina ji tana faɗawa mutan gidan nan halin da xalihar ke ciki, amma ni bata faɗa min ba, shi yasa nima ban yi mata jaje ba, kada tace ko sa mata ido nake yi, ko kuma farin ciki nake yi da abinda ya same ta, kin san dai halinta sarai ba sai na tsaya ina yi miki bayani ba, yanzu ma zancen nan da nake miki, fafutukar yadda za a zubar da cikin suke tayi, amma likita ya tabbatar musu da cewa, cikin baxai zubu ba sbd yayi kwari xai kai wata bakwai, shi yasa kika ga bata fitowa kullum suna daki suna kullawa da kwancewa” 

A razane na kalli Innah
“Yanzu har ya kai wata bakwai kice tun muna gida ma take shashancinta” 

“Eh ta kwana biyu tana abinta ganewa ne basu yi ba, amma ni tuni na gane inda ta dosa, naso na ankarar da mahaifiyarta sai kuma naji tsoron kada tace ko sharri nake yi wa yarta” 

Girgiza kai nayi
“Kai amma ban ji dadin abinda ya sameta ba, na tausaya mata sosai cikin shege ba ƙaramar illa bace, da xan basu shawara su ɗauka da nace su je Hisba, don a tilastawa wanda yayi cikin ya aureta ko baya so” 

Kallona Innah tayi
“Ai baki san wani abu ba Sa’adatu,  baxa su iya rigima da yaron ba, sbd ɗan gata ne kuma iyayenshi masu kuɗi ne kuma shi ne dan su guda ɗaya da suka mallaka a duniya, yanxu maganar nan da nake miki har an bar ƙasar da shi” 

A fili nake furta Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, “amma basu yi wa dan su tarbiyya mai kyau ba” Babban abinda ke damuna shi ne ba mutuncin zaliha ne kaɗai ya xube ba har da na gidan mu, sbd ta bata mana suna, duk ahalin mu babu inda aka taɓa samun irin wannan matsalar sai a gidan mu shi yasa abin yake min yawo a raina. 

Hira muke yi da innah amma gaba ɗaya hankalina baya wajenta, yana kan abinda ya samu zaliha. 

Sai da muka sha hirar mu da Innah sannan ta umarce ni da na shiga kowane d’aki na gaishe su, na kuma basu sakon da izuddeen ya bayar a basu. 

Cikin nutsuwa na fita, da ɗakin Innah Salamatu na fara, sallama nayi shiru ba a amsa ba, sai da na sake yi a karo na biyu sannan ta fito daga uwar daki tana yi min sannu da xuwa, ko kaɗan bata fahimci ni ɗin bace, sbd bata yi tunanin ganina a irin wannan lokacin ba.
Tana ganina ta hau washe min baki, ban sani ba dariyar kauna take min, ko kuma ta ƙarfin hali take yi, don ganin canji na alkhairi da Allah yayi min, kallo ɗaya zaka yi mata ka fahimci tana cikin matsananciyar damuwa, duk ta rame tsufanta ya ƙara fitowa ko ta ina, sai kace ta girmi Baba furfura har a girarta. 

Shimfida ta saka min
“Amarya kin sha kamshi yau kuma keca a gidan namu”
Murmushi nayi 
“Nice Innah” 

Fuskarta a sake ta kwalwa zaliha kira
“Fito ga yar uwarki tazo ku gaisa, kuma ki taho mata da mafici don zafin garin nan yayi yawa” 

A hankali ta fito daga dakin tana wata irin tafiya, sanye take da xumbulelen hijabi, duk ta kumbura fuskarta da kafarta duk sun tashi kana ganinta ba sai an ce maka mai ciki bace, sama-sama muka gaisa ta koma d’aki. 

Hira Innah Salamatu take min kamar ba ita ba, kallona tayi kamar xata yi kuka.
“Oh!! Allah sarki rayuwa, mahakurci mawadaci Sa’adatu, dubi yadda kika canja kika yi kyau, da gani hankalin ki a kwance yake babu abinda ke damun ki, Allah kenan mai yadda yaso a sanda yaso ga wanda yaso, Allah sarkin da ba a yi masa dole Allah mun tuba”
Mamaki ne ya kama ni cikin xuciyata nace
“Me Innah Salamatu take tunawa da take wadannan maganganun”

Hawaye ne ya fara xuba daga idonta, muryar ta a sarke ta cigaba da cewa.
“Da ɗaya daga cikin ‘ya’yana xata samu irin yadda kika samu kwanciyar hankali da naji dadi, amma yadda kake so wa kanka ba haka Allah yaso ganinka ba”
Ta ƙarasa maganar tare da share hawayen da ya fara taruwa a idonta.

Kaina a sunkuye nace
“Ki daina kuka innah kowane bawa da irin arxikinsa, wani bai isa ya tokare maka ba arzikin ka ba, kowa kika gani a duniya rabonsa yake ci babu wanda xai ci rabon wani”

Girgiza kai tayi
“Haka ne Sa’adatu, amma kin bani sha’awa ne sosai shi yasa nake wannan maganar, rayuwar ki tayi kyau, sai dai fatan Allah ya baku xaman lafiya, yanzu ma abubuwa da yawa ke ci na a cikin xuciyata, na rasa inda zan saka kaina naji dadi, na san idan na faɗa miki dole ki tausaya wa yar uwarki halin da ta samu kanta yanzu, naka sai naka Sa’adatu baxan iya boye miki ba ke jinin zaliha ce baxa ki kwaye mata baya ba”
Cike da kulawa na dubeta

“Wani abin ne ya faru innah”? Sake goge hawayenta tayi
“Babu shakka abinda ya samu zaliha abin takaici ne, kuma duk wata ‘ya mace da take kishin ‘yar uwarta mace baxa ta so hakan ya samu wata ba”

Nuna mata nayi kamar ban ji abinda ya faru ba, cike da kulawa nace.
“Me ya faru da ita innah?”

Girgiza kai tayi
“Abin babu dadin ji Sa’adatu, wai zaliha ta rasa sakayyar da zata yi mana sai ta cikin shege, abinda muke tunanin shi a can wani wajen, yau kuma a gidan mu ya faru, abin takaici kuma a dakina”
Ta karasa maganar tare da fashewa da matsanancin kuka.

Dafe kirjina nayi ina salati
“ban ji dadin abinda ya faru ba innah Allah ya tsare gaba”

Idanunta da guntun hawaye tace “ameen”

Kuɗin da izuddeen ya bani na bata, nan fa ta rikice tana murna.
“Allah yayi miki albarka Allah sarki Sa’adatu sa’ar mata, ko baka da Sa’a a gidanka ka namo Sa’a, to ke Allah ya baki Sa’a a rayuwar ki, Allah ya bar ki da mijinki lafiya”
Amsawa nayi da ameen tare da tashi xan fita, har nasa kafata a waje ta janyo mayafina.

“Kin manta baki tambayi yar uwarki ba abokiyar aurenki”

Murmushi nayi
“Wlh gaba ɗaya na manta Innah da fatan tana lafiya”

Sunkuyar da kanta tayi
“Tana lafiya ba lafiya ba Sa’adatu, ita ma A’isha tana cikin mawuyacin hali, shi yasa abin yayi min yawa gashi raina ni kadai, nice nake ta fafutuka, xaki Yi mamakin yadda ta koma duk ta xama abin tausayi, ashe mijin da ta aura mugu ne Kamar ma ɗan shan jini ne, kada ki so kiga yadda ta ƙare, lefenta kuwa gaba ɗaya ya kwashe, ga uban duka da take sha sannan ba abinci, dan Allah Sa’adatu idan kin samu lokaci ki daure kije ki ganta, kuma idan kina da abinda xaki tallafa mata da shi ki rika aika mata, don tana cikin lukutin yanayi”

Gaba daya tausayin zuri’ar Innah Salamatu ne ya kama ni, bata taɓa tsammanin haka xata same ta ba, shi yasa a rayuwa kada ka yarda ka cu ci wani, baka san ta inda Allah zai kama ka ba, jakata na bude na kirgo dubu goma na bayar ta bata, kamar xata yi min sujjada haka tayi sbd murna.

haka na shiga duk sauran bangarorin da ke gidan mu, na gaishe su tare da basu kuɗin da aka bayar na basu, ba ƙaramin mamaki suka yi ba basu taɓa xaton ko na samu xan basu ba, sbd irin cin kashin da suka riƙa yi mana ni da mahaifiyata, ni kuwa basu san bana saka sharri da sharri ba, da alkhairi nake sakawa.

Tambayar inda ya saleem yake nayi, a nan nake samun labarin yana Lagos yana karatu a jami’ar lagos, ba ƙaramin farin ciki nayi ba, na ɗauki alkawarin indai naje Lagos sai naje har makarantar su nayi masa alkhairi mai yawa, sbd ya kula da ni a lokacin da nake abar kyamata ga kowa.

Izuddeen bai dawo ba sai wajen takwas da rabi, a kofar gida ya tsaya ya turo yaro ya kira ni, sai da na ƙara gyara fuskata tare da shafa powder sannan na fita, abin mamaki har soro Innah Salamatu ta rako ni tana yi min na gaida gida tare da yi min addu’a, ita kanta innah abin ya bata mamaki, a bakin motar shi na tarar da shi yana tsaye yana jiran karasowa ta, murfi ya buɗe min na shiga, gidan su muka je muka gaishe da su Mama, nan ma sai da yayi rabon kuɗi tare da siya musu kayan abinci kala-kala, bamu dad’e sosai ba muka wuce gidan Adda.

A Kofar gida ya ajiye motar shi, da gudu na shiga gidan ina murna sbd nayi kewarta sosai, tana ganina ita ma ta hau murna ita da yaranta har cikin tsakar gida mijinta yace izuddeen ya shigo, mun dad’e muna hira sannan na nemi a bani aron Ihsan mu tafi da ita, cewa tayi baxa ta bani ita mu tafi ba, sbd kada ta hana mu cin amarcin mu, sai dai mu bari gobe ta kawo mana ita.

Haka dai muka hakura muka tafi, ba don ranmu ya so ba, nan ma dubu goma ya bawa Adda da mijinta.

Duk inda muka je saka mana albarka ake yi, tare da taya ni murnar dacewa da miji na gari da nayi mai kaunata.


Ko da muka koma gida ban wani saki jikina ba sosai, sbd damuwar da ta cika xuciyata, tambayata izuddeen ya shiga yi a kan dole sai na faɗa masa abinda ke damuna ina ji ina gani haka na kwana da baƙin ciki, ba tare da na faɗa masa ba, sbd faɗa masa tamkar zubar da mutuncin kaina ne da tona asirin gidan mu. 

Washe gari da sassafe ya shirya sbd jirgin 8 xai bi ya wuce Lagos, ba ƙaramin kuka nayi ba da kyar muka iya rabuwa da junan mu, ko da na koma daki babu abinda na riƙa yi banda aikin kuka. 

A ranar Adda ta kawo ihsan xuwan ta ne ma ya ɗan saukaka min damuwata. 

Zaune nake a bedroom na fito daga wanka har yanzu zuciyata tunanin halin da ya’yan Innah Salamatu ke ciki take yi, wayata na ɗauka na kira A’isha sallama nayi mata a sanyaye ta amsa, da farko bata gane muryar mai magana ba, sbd ba tada numberta sai da nayi mata bayani, cikin farin ciki ta fara magana. 

Gaisawa muka yi sannan tayi min godiyar sakon da na aika mata da shi cike da kulawa nace
“Ba komai A’isha duk abinda nayi miki ban yi asara ba”
Cikin rawar murya tace
“Haka ne yaya Sa’adatu Allah ya biya ki na gode, wlh har naji kunyar ki sbd irin abubuwan da na riƙa yi miki a baya” 

Dafe baki nayi
“Wace irin kunya kuma A’isha” 

Ajiyar zuciya tayi
“Ban taba xaton idan kin samu abin alkhairi xaki tuna da ni ba, sbd abubuwan da innar mu take faɗa a kanki kullum sharrinki take faɗa bata fadar alkhairin ki, sannan kullum burinta taga ta raba tsakanin mu, wannan abin shi yayi tasiri a zuciyar mu har muka ji ba mu da makiyiyar da ta wuce ke, shi yasa a baya muka riƙa yi muku abubuwa na cin mutunci da musgunawa, da wulakanci ni da yan uwana dan Allah ki yafe mana” 

Murmushi nayi
“Ba komai A’isha ai komai ya wuce sai dai fatan Allah ya kara shiga tsakanin mu da shaidan” 

Jikinta a sanyaye ta amsa da ameen
Sallama nayi mata a karshe, na faɗa mata idan tana da buƙatar wani abu ta faɗa min Insha Allah xan taimaka mata.
Fashewa tayi da kuka 

“Idan akwai abinda nake buƙata a yanzu bai wuce ki rokar min Baba ya raba aurena da Alhaji yawale ba, ni kadai na san irin rayuwar da nake yi a gidansa, ƙoƙarin raba ni da kowa yake yi, yafi so na xama mallakinsa shi kadai ya cigaba da azabtar da ni, dan Allah yaya Sa’adatu kiyi min wannan alfarmar, yanzu haka a kulle nake a cikin wani daki ya hana a bani abincin axabobi kala-kala yake gana min, Yanzu haka ya aske min gashin kaina gaba daya nafi tunanin asiri zai min da shi” 

Nima ban San lokacin da na fashe da kuka ba, tausayin A’isha ne ya kama ni, cikin kuka nace.
“Kada ki damu Insha Allah xan faɗa masa”
Haka dai muka yi sallama zuciya ta cike da damuwa.

Kan gado na faɗa na cigaba da kuka mai cike da ban tausayi. 

Kwanakin izuddeen na cika ya dawo, tare da faɗa min cewa da ni xai koma sbd an gyara mana inda xamu xauna a can, kafin mu tafi lokacin bikin Rukayya yayi don haka ya jira nayi biki sai mu tafi tare. 

Kuɗi mai yawa ya bani nayi mata siyayyar kayan kitchen kala-kala ba ƙaramin dadi ta ji ba, kwanaki biyu kadai aka dauka ana biki aka kai amarya gidanta da ke tarauni, babu abinda ya wuce ni a wajen bikinta sbd izuddeen ya dade da sanin muhimmanci ta a wajena. 

********** 

A wata ranar juma’a ina zaune a dakina bayan na idar da Sallah ina addu’a number Aisha na gani ta kira ni, da sauri na kai hannu na ɗauka, cikin kuka take faɗa min wai zaliha ta haihu tana asibiti naje tana ta kiran sunana kamar ma so take tayi jijjiga na taimaka naje na ganta. 

Rasa abinda ke min daɗi a raina nayi, ban san me xan faɗawa izuddeen ba, haka dai nayi ta yawo a cikin daki ina tunanin karyar da xan shirya masa ba tare da ya gane abinda ya faru ba. 

Yana shigowa na faɗa masa zaliha ce ba lafiya da kansa ya kaini asibitin, kyale ni yayi a wajenta har yamma sannan yaxo ya dauke ni. 

Tun a mota yake tambayata abinda ya faru da ita amma sai na kasa fada masa haka dai ya kyale ni, na san ko ban fada masa ba zai ji a cikin unguwa.

*Wannan shafin gaba ɗaya naki ne kawata aminiyata A’ISHA SABO ABDULLAHI (maman teemah) ALLAH yaji kan teemah Allah ya baki hakurin jure rashinta, ina godiya da yadda kike bibiyar wannan littafi tun daga farkonsa har karshensa* 

*Godiya gare ku yan group din DUKKAN TSANANI FANS 1&2 da kuma JEEDDAH TIJJANI NOVEL Facebook and WhatsApp Ina godia da yadda ku ka jajirce wajen karfafa min gwiwa har na kammala rubuta wannan littafi* 

*Baxan manta da kai ba ABDURRAHMAN IBRAHIM admin HAFSAT HAUSA NOVEL FACEBOOK da jajircewar ka littafina ke shiga duk inda ban yi tunanin yana xuwa ba a duniya, ina godiya Allah ya bar zumunci*

             *70*

Sai yamma li’kis muka koma gida, duk jikina yayi tubus sbd gajiya, kitchen na faɗa na fara ƙoƙarin haɗa mana abincin dare, shi kuma ya fita zuwa wajen abokin shi, tuwon shinkafa miyar zogale nayi mana wacce taji wadataccen busashshen kifi, sai zobo drink da nayi mana, ina gamawa na shiga wanka,  shiryawa nayi cikin wata tsadaddiyar doguwar rigar atamfa ɗinkin dubai, na sha kamshi ko ta ina, sallar magariba na gabatar tare da yin addu’a Allah ya kawo wa yan uwana ƙarshen wannan matsalar da suke ciki, shafawa nayi ina mai mikewa tare da nad’e sallayar da nayi sallah a kanta, xan shiga d’aki kenan naji alamar bugun ‘kofar sa, da sauri na ƙarasa na rungume shi tare da karɓar ledojin da ke hannun shi, manna ni yayi a kirjinsa yana shaƙar kamshin turaren jikina, kama hannun shi nayi muka shiga d’aki, sai da nayi masa wanka na shirya shi, sannan muka isa dining don cin abinci. 

Ba ƙaramin daɗin tuwon yaji ba sbd dama shi ne abincin da ya fi so, sai faman santi yake yi, tare da saka min albarka, lumshe idanu yayi yana kallona.
“Ya zama wajibi na cigaba da kulawa da ke matata, kuma dole na baki tukwicin wannan kwalliyar da kika min da wannan girkin naki mai daɗi”
Murmushi nayi tare da kwantar da kaina a kafad’arsa
“Ko baka bani tukwici ba ka can-canci nayi maka fiye da wannan kulawar mijina, sbd dama aikina kenan kulawa da kai”
Shafa fuskata yayi 
“Na san na can-canci ki kula da ni, amma nima wajibina ne na faranta miki a duk lokacin da kika yi min abinda naji daɗi, don haka rufe idonki kiga wani abu” 

Ban yi gardama ba na rufe idanuna.
Ɗan murmushi ya saki wanda naji sautinsa a kunnena tare da cewa
“Buɗe yanzu” 

A hankali na fara buɗewa, mukullaye biyu naga ya miko min.
Kafin nayi magana har yace
“Wannan mukullin na motarki ne, dama na dayde da siya miki ita, ƙarasowa ne bata yi ba sai yau Allah ya nufa, yanzu fitar nan da nayi ita naje na d’akko”
Ban san lokacin da na rungume shi ba ina murna.
“Na godewa Allah da ya ƙaddara min kaine mijina mai kula da dukkan farin cikina, ba ni da abinda xan iya gode maka da shi sai dai nayi maka fatan gamawa da duniya lafiya, tare da samun sakamakon aljanna” 

Kwantar da ni yayi a kirjinsa yana shafa kwantaccen gashin kaina
“ki daina yi min godiya ni da ke mun xama abu ɗaya, dukiyata da ni kaina naki ne, kina da ikon sarrafata a duk lokacin da kika ga dama, kuma ki bawa duk wanda kika ga dama”
ɗaya mukullin da ne hannuna ya sake dakkowa tare da ajiye shi a kan cinyata. 

“Wannan kuma na Innah ne, na siya mata gida a nan kusa da gidan da take, sbd bai kamata a ce kamar Innah tana kwana a wannan dakin ba, nasa an gyara komai, sannan an xuba dukkan abubuwan da take buƙata, har da suttura bana so ta koma da komai” 

Rasa bakin godiya nayi sai wani hawaye da ke bin fuskata ɗaya bayan ɗaya.
Sake shigewa jikin shi nayi ina kuka, sosai yake rarrashina.
“Don nayi miki wannan kankanin abin kike kuka Sa’adatu? a soyayyar da kika nuna min ban miki komai ba, na san har abada baxan iya biyan ki bashin son da kike min ba, sai dai Allah ne xai biya ki, don haka ki daina kuka” 

Story continues below


Idanuna cike da hawaye na sake d’agowa ina kallon shi, hannu yasa yana goge min, muryata na rawa nace.
“Mun gode sosai mijina Allah ya ƙara maka arziki, Allah ya raba ka da Baba lafiya” 

Amsa min yayi da ameen yana ci-gaba da share min hawayena. 

Cikin xuciyata nace, Allah sarki Innah kinga Sakamakon hakuri tun ba a je ko ina ba Allah ya nuna ikonsa, sai yanxu maganar gwaggo Abu ta dawo min kunnena lokacin da ta dawo da innah ranar da tayi yaji a lokacin da za a aura min Malam Jibo, tana mai cewa nan ne gidan arzikinta tayi hakuri ta jure wata rana sai labari, kuma *DUKKAN TSANANI* yana tare da sauki, ashe kuwa maganar gwaggo Abu gaskiya ce, shi yasa duk musgunawar da ake yiwa mace a dakin mijinta yana da kyau tayi hakuri ta jure, musamman ma idan tana da ya’ya, idan bata huta da mijinta ba sai Allah ya yiwa ƴaƴanta arziki ta ji dadi ta sanadin su, duk inda hakuri yake baya fad’uwa ƙasa banxa. 

Katse min tunanin da nake yi yayi da cewa.
“Me kike tunani ne matata naga kin yi shiru” 

A hankali na d’ago, ina mai tambayarsa
“Ita kaɗai xata koma gidan ko har da su Innah Salamatu?” 

Gani nayi fuskar sa ta canja
“Ita kadai nake so ta koma ta huta taji dadi ita ma ta san ta haifi ‘ya’ya masu kishinta da tausayinta, idan suka koma ai bata canja xani ba kenan, abinda suke mata a baya zasu ci-gaba da yi” 

Duk ƙoƙarin da nayi don nuna masa cewa su Innah Salamatu sun canja gaba daya yaƙi yarda haka nan na kyale shi. 

Washe gari a motata muka fita ya fara koya min cikin ikon Allah har na fara iyawa, gidan da ya bawa Innah muka fara xuwa muka yi mata yan karkad’e-karkad’e, masha Allah komai yaji a gidan gwanin ban sha’awa,  gida ne na xamani mai kyawun gaske, ba ƙaramin ginuwa gidan yayi ba, parlour ne da dakuna guda uku a cikinsa sai kitchen, sai kuma babbar haraba wacce motoci uku ko huɗu xasu iya yin parking a bakin gidan, ba ƙaramin dadi xuciyata ke min ba idan na kalli gidan na tuna innata ce xata xauna a cikinsa, sai da nayi mata turaren wuta sannan muka kama hanyar xuwa wajenta don miƙa mata mukullin gidanta. 

Muna zuwa kofar gidanmu idon yan unguwa ya dawo kanmu, sai zubewa ƙasa suke suna gaida izuddeen, sbd shi mutum ne mai kyauta baxai taɓa kyale su su tafi haka ba, ba tare da ya basu kudi ba, tare da shi muka shiga cikin gida. 

A soro muka haɗu da Baba yau ma kamar xai goya mu haka yayi. 

A ladabce muka gaishe shi, motar da aka bani na nuna masa murna a wajensa bata misaltuwa sai sanya mana albarka yake yi, har ya tashi xai shiga ciki muka nuna masa mukullin gidan Innah, nan ma dai murnar yake yi kamar xai yi tsalle, da sauri ya shiga gida mu kuma muka bi shi a baya. 

Zaliha ce zaune a tsakar gida ta haɗa kai da gwiwa tana kuka ga jaririyar da ta haifa a gefe rana sai dukanta take yi, daga nesa na jiyo Innah Salamatu na cewa. 

“Ki tafi duk inda xaki je dama ai yar iska ce ke, sai ki bi duniyar da hujja, amma baxan iya zama da jika shege daki daya ba” 

Cikin tashin hankali na ƙarasa tare da d’ago kanta, ko kadan ban ji dadin kalaman Innah ba sbd bana son izuddeen ya gane halin da gidan mu ke ciki. Tsugunnawa nayi a gabanta tambayarta na shiga yi. 

“Zaliha me yasa kika xauna a tsakar gida ga rana ga jego kina yi, tashi ki shiga ciki kada ranar nan ta illata ki” 

A hankali ta d’ago ta dube ni kafin tayi magana har ta fashe da kuka.
“Baba da Innah ne suka kore ni wai na fita na bar musu gida, duk inda xan tafi naje”
Cike da tausayawa nace 
“Haba ai baxa a yi haka ba komai na rayuwa mukaddari ne bai kamata a yi miki haka ba” 

Ina cikin magana Baba da innah Salamatu suka fito, ita dama innata tana d’aki na san taji xuwana kunyar izuddeen ce baxa ta bari ta fito ba. 

A fusace Baba da innah Salamatu suka tsaya a gabana, ko ganin izuddeen bai sa sun ji kunya ba, dama su haka suke idan xasu yi tijarar su basa jin kunyar idon jama’a. 

Story continues below


“Kinga wannan tankadaddiyar yarinyar ya xama dole ta fita ta bar mana gida, ina xamu iya zama da ɗan shege a gida, dame xan ji Sa’adatu ga A’isha a gida ga wannan abin kunya ina zan sa kaina makiya ko ta ina dariya suke mana”
Wurgo mata kayanta suka shiga yi daga daki, sannan suka hau dukanta, ban san lokacin da na fara kuka ina basu hakuri ba sbd yarinyar gaba ɗaya abar tausayi ce. 

Da kyar muka lallaba su ni da izuddeen muka basu hakuri.
Baba ne ya fara magana. 

“Wlh ban da wannan yar albarkar tasa baki baxa ki ƙara kwana a gidan nan ba, babu abinda kike kawo mana na ci-gaba kullum sai masifa yanzu ga Sa’adatu nan ta canja min gida ga mijinta ya bata mota, kullum cigaba xuwar wa yarinyar nan yake sbd ta gari ce ita bata bata rayuwarta ba” 

Xaxxaro ido Innah Salamatu tayi 
“Da gaske malam”? 

Wani kallo yayi mata.
“To da karya nake miki? yarinya ce gata nan yar albarka ba irin yayanki ba yan iska, duk mugun halinki ya bi ya lalata su banda xagi babu abinda suke janyo min a unguwa, daga wadda taki zaman aure sai mai cikin shege”
Kasa magana nayi sbd kunya sai tijara Baba yake yi mata, ita kuma Innah Salamatu sai kuka take ta kasa rama wannan cin mutuncin da yake yi mata. 

Dakin Innah muka shiga shi kuma Baba ya biyo bayan mu. 

Da farin ciki Innah ta karɓe mu bayan mun gaisa muka miƙa mata mukullin gidanta, ba ƙaramin daɗi taji ba har da hawayenta albarka take saka wa izuddeen sosai, tare da yi masa fatan Allah ya raba shi da iyayensa lafiya. 

Tashi izuddeen yayi ya tafi gida gaida nasa iyayen da kuma ganin aikin da yasa ana yi musu. 

A lokacin Baba yace dole su tashi su tafi gidansu tunda dai an kammala haɗa musu komai su kawai ake jira, dama shi baya kaunar zaman nan na haɗa ka da ake yi, haka kuwa aka yi amma ba don Innah taso ba, taso a ce sai da ta faɗawa ma’kota sannan suka tashi, amma haka ta hakura ta fito, kulle d’akinta tayi sannan ta kama hanyar xuwa dakin Innah Salamatu, a ciki ta sameta ta haɗa kai da gwiwa tana kuka, nima bayanta nabi muka shiga, waje ta samu ta zauna, har yanzu Innah Salamatu tana zaune kanta a kasa ta kasa d’agowa su hada ido da Innah.
cikin kulawa Innah tace. 

“To innar su A’isha mu yau Allah yayi mana ɗagawa xan koma gidan da mijin Sa’adatu ya bani” 

A xabure ta d’ago tana kallonta.
“Wai dama abinda malam yake faɗa gaskiya ne, Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, yau naga ta kaina ni Salamatu, mugun abuna ya koma min kaina, shi yasa aka ce kada ka nufi kowa da sharri, yau gashi Allah ya azurta ki ya bar ni a cikin wahala, mijin da nake ta’kama da shi ya juya min baya, dan Allah ki yafe min mero, ko a iya nan naga karshena kaf cikin yayana babu na arziki, daga talakawa sai mai cikin shege sai wacce aka saka, abinda ta faru da Sa’adatu a baya duk Ni nake kulla mata sharri na……” 

Zata ci-gaba da magana Innah ta rufe mata baki, don ganin tana ƙoƙarin sakin layi, maganganu take yi tamkar wata zararriya, cike da kulawa innah tace 
“Kiyi hakuri kowane bawa da irin ƙaddarar sa, ni kuma na yafe miki duk abinda ya faru, amma ki daina waɗannan maganganun ki ci-gaba da addu’a Allah xai kawo miki mafita” 

A’isha ce ta jawo jiki ta fito daga uwar  daki, a hankali take takowa sbd rashin lafiyar da take fama da shi, tayi baƙi sosai ta rame, ga gashin kanta a aske, ga ƙaramin cikinta a jikinta har ya fara fitowa, xuwa tayi gaban mu ta xube tana kuka ita ma irin kalaman Innah salamatu take yi, tana faɗin cewa innar su ce ta cuce su duk rayuwar su ta lalace, ni dai da Innah hakuri kawai muke basu muna nuna musu komai ya wuce. 

Basu iya yi mana rakiya ba sbd tashin hankalin da muka bar su a ciki.
Ɓangarorin gidan mu muka rika shiga muna yi musu sallama, duk inda muka je sai sun yi mamakin wannan abin alkhairin da izuddeen ya yiwa Innah, banda neman gafararta babu abinda suke yi sbd sun san cutar da ita sosai.
Kafin mu fito ashe Baba shi har yayi gaba, sai da muka shiga ma’kota na kusa muka yi musu sallama sannan na saka innah a mota muka wuce gidan, duk inda muka yi sai an bi mu da kallon mamaki. 

Story continues below


Muna zuwa muka tarar da Kofar gidan a buɗe ɗakunan gidan Baba ya shiga, dubawa yake ta yi yana yi mana addu’a, sai yamma izuddeen yazo ya ɗauke ni, daga nan gidan Adda saratu muka wuce nan ma sha tara ta arziki izuddeen ya sauke mata sannan muka tafi gida. 

Washe gari da misalin ƙarfe tara na safe muka wuce Lagos , can ma gidan mu mai matuƙar kyau ne, watan mu biyar da aure na samu ciki lokacin da muka je awo aka tabbatar min da cewa yan biyu ne a tare da ni, murna a wajen izuddeen kuwa bata misaltuwa kullum cikin ririta ni yake da kulawa da ni, gaba ɗaya ko motsi baya son nayi komai masu aiki ke yi min. 

Watana daya a can ya saleem ya kawo min ziyara ba karamin daɗi naji ba  kwanan shi biyu ya koma makaranta, ba ƙaramin abin arziki muka haɗa masa ba, yayi farin cikin yadda naga na samu jin daɗi a rayuwata, kafin tafiyarsa sai da yayi min faɗa a kan na riƙe mijina tsakani da Allah na kuma kula da danginsa, yaji dadin gidan da izuddeen ya bawa Innah shi kansa sai da yayi masa godiya.

********* 

A ɓangaren Innah kuwa rayuwa ta canja yanxu har yar aiki gareta komai yi mata ake yi, sai dai tana daga kwancewa ta bada umarni, su Innah Salamatu da ƴaƴanta sai da su zo wajenta neman abu, yanzu haka A’isha ta tattara kayanta ta koma wajenta, a nan take ci-gaba da rainon cikinta sbd idan ta xauna a gidan su ba abinci, ga tsangwamar da Innah Salamatu take yi mata, yan kwanakin nan ma kamar neman xaucewa innar take son, yi sbd damuwar da ta saka a ranta, ita kuwa zaliha sam bata iya fita sbd tana fitowa jama’a xasu hau tsokanarta yara suna yi mata a ture a dan dole take samun guri ta xauna a gida, amma ita kanta da gidan Innah xata koma da rayuwa don ta san zata rike ta tsakani da Allah, mutane da dama suna xuga Innah a kan ta kore su ta hana su xauna mata a gida, amma ita sam bata jin shawarar su takan ce, ita ko yanzu taci ribar rayuwarta. 

Cikina na cika wata takwas na dawo gidan Innah, amma duk bayan sati biyu izuddeen na kan hanyar zuwa wajena, kulawa ta musamman yake bani, ita kanta Innah Salamatu kullum sai taxo wajena ta kula da ni ta canja, halinta gaba ɗaya kamar ba ita ba, duk wannan kiyayyar tayi jifa da ita gefe. 

A safiyar ranar lahadi ciwon ciki mai tsanani ya kama ni, ina jin wannan yanayi na kira izuddeen a waya na faɗa masa, a ranar ya biyo jirgi ya taho, da Innah Salamatu da Adda saratu da mama, su suka kaini asibiti, ban dad’e ina na’kuda ba na haifi  yan biyu dukan su maza, kyawawa da su kamar su ɗaya da baban su, gaba ɗayansu suna cikin koshin lafiya, ba ƙaramin kama suke yi da izuddeen abinda kowa yake faɗa kenan, murna a wajensa kuwa bata misaltuwa. kwanana daya aka sallame ni muka dawo gida. 

Yan uwa da abokan arziki haka suka riƙa xuwa daga gurare daban-daban suna min barka, kyauttukan da na samu kuwa ba su da adadi, tun daga kan kaya har zuwa kuɗi, gidan su izuddeen ma haka suka shirya min sha tara ta arxiki. 

Ranar suna aka sanyawa jarirai suna, Abdurrahman da Abdurraheem, ba ƙaramin shagali aka yi ba, an kashe kuɗaɗe sosai, walima ma biyu aka yi, da ta ranar suna da kuma washe garin suna wacce gidan su izuddeen suka haɗa min, sai da na d’inkawa su A’isha kaya kala uku sbd su fita fes kamar kowa, kasancewar ba su da wata sutturar kirki. 

Innata da Innah Salamatu da Adda saratu, duk dinki iri ɗaya nayi musu, abin ya bawa kowa mamaki, ganin bana ware Innah Salamatu a komai. 

A ranar da zamu cika kwana arba’in izuddeen yazo, har cikin parlourn Innah ya shigo ya miƙa mana wasu takardu, ina budewa naga visa ce xuwa umara, yayi mana ni da su Abdurrahman da Innah da Adda da kuma Baba. 

Kallon shi nayi ina murmushi.
“Yanzu duk hidimar nan da ka sha sai da ka ƙara ɗorawa kanka wani nauyin” 

Kallona yayi
“Na fada miki duk abinda nayi miki babu asara a ciki,  har da su mama da su Aunty zainab xaku tafi ku sha biyar na biyawa, fatana dai ku yi min addu’a mai yawa” 

Rausayar da kaina nayi, kamar xan yi kuka.
“Me yasa duk abinda xaka yi baka haɗawa da innah Salamatu ne?” 

Tsuke fuskarsa yayi.
“Ni ki daina kawo min maganar wannan matar, duk fa irin abubuwan da take miki ina da labari, ni kuma bana manta duk wanda ya cutar min da uwar yayana, kamar yadda bana manta wanda yayi mata alkhairi duk kankantarsa, na san da cewa ko lokacin da nazo neman aurenki ita ce taje har gidanmu ta faɗawa mama wai ni nake lalata ki, har yanzu idan na tuna da wannan maganar sai raina ya ɓaci, kuma ko yanzu idan na ganta sai na tuna da wannan abin da ta faɗa a kaina don haka kada ma ki sake cewa na bata kayana, idan kika yi xancenta ba bata min rai kike yi”
Ya fadi maganar tare da mi’kewa tsaye.
Shiru nayi ban iya bashi amsa ba, wajen Innah yaje ya bata visa din sannan ya tafi. 

Lokacin da labarin tafiyar mu makka ya je wa Innah Salamatu, ba ƙaramin takaici tayi ba zuciyar ta cike take da nadamar irin abubuwan da tayi mana a baya, ji take kamar tace min nasa a biya da ita amma baxa ta iya ba sbd kunya, ta san izuddeen yana da labarin duk irin tsiyar da ta shuka a baya. 

Cikin ‘kan’kanin lokaci rayuwar mu ta canja, muka xama wasu mutane na musamman, mutanen gidan mu kuwa, ba ƙaramin ji suke da ni da Innah ba, komai xasu yi sai an nemi shawarar ta, ita kuwa Innah Salamatu yanzu ba tada ta cewa tana yin magana za a goranta mata da irin abin kunyar da zaliha tayi, haka suke bi guri-guri suna tona mata asiri har irin abubuwan da take yiwa Baba a da na asiri, ita kuwa Innah sam bata yarda su kawo mata tsegumi sbd gaba ɗayan su ba abin yarda bane.

Kafin mu tafi umara sai da naje gidan Rukayya na ganta sbd ita ma ta kusa haihuwa yanxu ba sosai take samun damar fita ba, cikin rayuwa mai kyau na tarar da ita tana riƙe da ya’yan doctor kamar ƴaƴanta, kullum cigaba suke samu ita da mijinta suna rayuwa mai cike da farin ciki da yanci, ita ma tana taimakawa mahaifiyarta sosai ta ɓangarori da dama. 

Satin mu biyu a makka muka dawo, haka na riƙa rabon tsaraba guri-guri babu wanda ban bawa tsaraba ta ba a gidan mu, shi kuwa Baba hana su Innah Salamatu yayi suna ji suna gani haka ya riƙa fitar da kayan yana rabawa a waje. 

Kafin na koma lagos har izuddeen ya samar min admission a wata makarantar ilimin manya da ke Lagos, muna komawa na shiga yin karatuna cikin sa’a na fara ina ganewa sosai kamar dama can nayi makarantar boko, lokacin jarrabawa nayi na xana WAEC sannan nayi JAMB cikin sa’a na samu dukkan abinda ake nema, wannan dalilin ya karfafawa izuddeen gwiwar nema min admission a jami’ar Lagos ɓangaren law.

Hazakar da nake da ita ne ya sanya ni samun nasara a rayuwata, don tunda na shiga makarantar ban san wani abu mai suna C.O ba, kullum nasara nake samu a haka har na cika shakarar karatuna naje school of law, muna fitowa na zama babbar lawyer me kare hakkin mata da ƙananan yara. 

Kafin wani lokaci mai tsawo har sunana ya fara xaga garin mu, ganin yadda nake gwagwarmayar ‘kwatowa mata yancin su sai ya xamto ni ce kawai ‘ya ɗaya tilo da mahaifina ke alfahari da ni, haka na riƙa ƙoƙarin janyo su A’isha a jikina har na samu na mayar da su makaranta suka yi candy daga nan dai basu cigaba ba sbd ba su da sha’awar abin. 

Haka rayuwata da ta mahaifiyata ta cigaba da kasancewa cikin farin ciki muka xamto abin kwatance da alfahari a gari, a bangaren mijina kuwa da danginsa abin ba a cewa komai domin suna sona suna son dukkan farin cikina, sai da nayi shekara uku da haihuwar yan biyu sannan na sake haihuwar ‘ya mace inda yarinya taci sunan innah maryam amma ana kiranta da (Raihan) daga kanta sai da nayi shekara biyar sannan na sake haihuwar d’a namiji shi kuma sunan mahaifin izuddeen aka sanya masa amma muna kiran shi da (adeel) 

Daga haka haihuwata ta tsaya har zuwa lokacin da yarana suka girma suka yi wayo sosai. 

Tarbiyya mai kyau nake basu, a hannuna duka suke karatunsu na addini, wannan yasa suka fita daban a cikin yara.

Alhamdulillah a nan na kawo ƙarshen wannan littafin 

Ku kasance da ni a cikin littafina na gaba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *