WANENE SHI
CHAPTER 10
“Kin min shiru Sa’adha don Allah kiyi magana, ko har yanzu fushin ne?”
Nanne ta sake tankwashe k’afarta akan gadon tana nannad’e bakin rigar filon dake kan cinyarta, a hankali tace.
“Kana lafiya?”
“Ina lafiya kuma yanzu da kika tambaya sai na k’ara jin lafiyar ta kama ni.”
Tayi murmushi mai fad’i.
“Ina jinki ki fad’a min sau nawa kika tuna ni bayan lokacin da kika ce min sai da safe?”
Bata ce komai ba kamar yadda ya zata.
“Ko sau d’aya ne kawai sanda kika yi min flashing?”
Da sauri tace.
“Ni ba flashing nayi ba ban sani bane kawai kiran ya shiga na zauna a kusa da wayar.”
“Irin wannan bayani haka kamar laifi kika yi?…yanzu toh ba wannan ba, baki tambayeni sauran bayanin jiya ba.”
Ta d’an hade girarta kad’an.
“Wane bayanin?”
“Bayanin koni WAYE mana, ko ba kya sonp kiji abinda nace wa baffa ya bani aurenki? ko kuma ki san wane irin miji zaki aura?”
“Na san zaka fad’a min ai.”
“Ta yaya kika sani? saboda kin san ina sonki?”
Kamar baza ta amsa ba sai kuma tace.
“Mhmmm..”
“Toh mhmm kema kina sona?”
Ta sake yin shiru.
“Ya Allah! Sa’adha kin mayar dani d’an jarida sai tambaya nake tayi akai-akai.”
“Toh ina jinka, ka fad’a min.”
“Shikenan mu ajiye wannan a gefe zamu dawo kansa daga baya, bari in fara baki tarihin mijinki tukunna.
Sunana Imran kamar yadda kika sani, amma full name d’in Imran Siddiq, ni d’an garin bauchi ne iyayena sun mutu tun ina yaro saboda haka a hannun k’annin mahaifina na tashi, A bauchi nayi duk karatuna da komai, sai daga baya na samu aiki anan garinku.
Aiki a company ORZ dake kula da harkokin talla na media platforms, shi yasa nake zaune ni kad’ai ba tare da kowa ba, don dukkan ‘yan uwana suna can.”
This is it! just simple kamar yadda suka tsara a farko zuwansa, haka normal rayuwar matashi irinsa ya kamata ta kasance.
Jin tayi shiru yasa ya cigaba da cewa.
“Tun daga bauchi ‘yan uwana suka zo nema min aurenki kwanansu biyu a garin nan, kuma a duk kwanakin suna ta yabawa da irin tarbiyyar gidanku, sunce baffa mutumin kirki ne zanyi sa’ar auren ‘yarsa.”
Ta cigaba da nannad’e rigar filon a hannunta.
“Tun da suka koma kuma ake ta min waya daga gida, masu son ganinki na da yawa Sa’adha, basu san cewa ni kaina an hana ni zuwa ba.”
Story continues below

Ya k’arashe zancen a hankali yana jin nauyin kalamansa na baya, tun farkon sanda ya fara wannan rayuwar, yana tafiya ne akan wannan tsarin, wannan k’aryar…amma tunda yake bai tab’a jin komai ba sai a yanzu da yake gayawa Sa’adha.
Amma duk da haka yaji yana son sanin me take tunani a yanzu, meke faruwa a cikin kanta, ya rufe idonsa da k’arfi amma ya kasa jin komai, zuciyarta tayi masa nisan da ba zai iya reaching ba.
Saboda haka yayi shiru shima yana sauraren fitar numfashinta a hankali da kuma bugun zuciyarta. kusan minti biyu kafin ya kira sunanta, ga mamakinsa sai yaji ta amsa nan take.
“Zan iya ganinki gobe?”
“Me za’a yi?”
Kamar a lokutan baya, tana iya jiyo sautin murmushinsa daga d’aya b’angaren kafin yace.
“So nake inzo inyi hira da iyalina.”
Kalmar tayi mata nauyi da kuma dad’i a lokaci daya, taji son da take yi masa ya k’aru a cikin zuciyarta, kamar a d’ebo yayi ne a k’ara akan wutar dake ci.
A hankali ta fad’i abinda take fad’a a kodayaushe.
“May be da yamma?”
“Baki tabbatar ba?”
Ta rufe idonta sannan tace.
“Na tabbatar Allah ya kaimu.”
“Ameen Noory!”
Jin wani sabon sunan yasa ta bud’e idanunta kad’an sannan ta lumshe su.
Noory yau kuma?
******
Har k’arfe hud’u na yamma Imran na jin kuzari a jikinsa da wani irin annashuwa daya manta lokaci na k’arshe da yaji haka.
Wayar da yayi da sa’adha d’azu k’arya ce, haka ma duk maganganun daya gaya mata, amma the fact that ta yarda dashi kuma a cikin duniyarta babu tunanin cewa k’aryar ne shi yake masa dad’i, yana son ya ture gaskiyar shima ya tafi da tunaninsa a hakan, ba don komai sai saboda yana jin dad’in abinda yake yi, yana jin dad’in duk wani moment d’in da yake tare da ita.
Duk cewa da yana tsoron kar biyewa son zuciyarsa ya jawo musu wata matsalar kamar yadda a baya ya jawo wadda suke cikinta a yanzu. Amma wannan tunanin baya tab’a zuwa duk sanda yake tare da ita.
“Uhmm….Siddiq are you with us?”
Muryar Ibrahim ta shigo cikin tunaninsa, ya d’ago da sauri ya kalle su, sai yanzu ya tuna suna zaune a cikin office d’insa su biyar suna tattaunawa akan advert d’in sabon company da suka yi meeting dasu d’azu, wanda har sunyi signing contract da komai yanzu zasu fara shirya yadda za’a baiyana wa al’umma kayaiyakinsu ne, wato irin tallan da za’a yiwa jama’a.
“I’m sorry dan Allah, wani abu ne ya d’an shiga kaina.”
Ya karb’i file d’in da yake mik’o masa ya shiga karantawa, sai da ya gama tsaf! sannan ya d’ago ya kalle su yace.
“I don’t think i like this idea, can’t you come up with anything that will leave an immediate and strong impression?”
Wani usman ya d’an duba paper gabansa sannan yace.
“We just thought since the products are fibres, a simple advert will do.”
Imran ya girgiza kansa.
“You should’nt have thought that, advert komai k’ank’artarsa komai rashin amfanin kayan ga al’umma, hakk’in mune mu tallata shi in a way da zamu iya karkata tunanin mutane daga kan neccesssities d’insu zuwa shi.
Saboda haka zuwa gobe, just keep thinking about something any idea that wiil catch the mind of viewers, prepare something more spectacular please.
Usman after that, I think you can work with Director Phillps to come up with a way to convey it. Ibrahim you will be in charge of the copy writing, and Maryam…
Ya juya ya kalleta, tana zaune a gefensa cikin shigarta ta matsatstsun kaya kamar kullum d’an karamin mayafinta na reto a kafad’a. Ba abinda ya sashi tsayawa da maganar kenan ba, hannayenta, hannayenta da suka sha wani had’add’en kunshi daya zauna d’as akan farar fatarta. Bai san ya akayi tun farko ya bari ta fahimci cewa yana son k’unshi ba, shi yasa duk sanda ta san zasu had’u take zuwa tayi don ta san ko ba komai zata samu alfarmar ya saurareta. Ya had’iye wani abu a mak’ogwaronsa kafin ya cigaba.
“…make a list of all the client that we will work with for the next quarter by tomorrow.
Ya juya ya kalli wata dattijuwar mata da kowa a companyn ke kira da Aunty Fati, mace ce mai tsananin kirki da sanin hakk’in al’umma, shi kansa yana ganin girmanta sosai saboda yadda ta maidashi kamar d’anta, don babban d’anta ma Abdullahi ya girme shi kuma ya sanshi duk sanda suka had’u suna gaisawa sosai.
“Aunty can you make me an appointment with Dr Turaki? I need to see him tomorrow.”
Tayi murmushi kafin tace.
“Insha Allah Imran.”
“Okay, we can call it a day.”
Da haka kowa ya d’auki takardunsa suka mik’e, sai dai kafin Aunty fati ta kai ga fita, Imran ya tuna da abinda jaamil ya gaya masa jiya.
_”Abu biyu ne da suka rage mana yanzu, wai akwai kaya da ake kaiwa gidansu yarinyar sunansa lefe, ni ban san ta yaya zamu had’a su ba._
_Da kuma zancen gida, dole ne sai ka tashi daga gidan nan, saboda yayi kusa daga gidansu kuma ance min suna kawo kayan gida daga wajensu suma. Saboda haka inda zaka nema bana tunanin sai ka sayi komai._
Tuno hakan yasa yayi saurin tsaida ita, ta dawo ta zauna a kujerar dake gefensa.
“Aunty Faty wani abu ne ya taso min wallahi, kin san families d’ina ba’a nan kusa suke ba kamar yadda na fada muku…”
Ya d’an yi shiru yana juya abinda zai fad’a, amma murmushin fuskarta ya sashi cigaba da magana
“…Toh aure na ne ya tashi, kuma bana son har sai na tafi can kafin a had’a lefe, shine nake so in tambaye ki ko zaki taimaka…”
“Kar ka kuskura ka k’arasa Imran, in har kace taimako kenan baka yin uwar dani kamar yadda ni na d’auke ka, Alhmdlilahi, wallahi naji dad’in wannan zancen sosai, dama na dad’e ina maka sha’awar aure a wannan lokacin, don shine cikar mutuncin kowanne mutumin arziki.
Zancen lefe kuma kar ka sami damuwa, insha Allahu za’a had’a ba da wata matsala ba, dana koma gida zan samu ‘yan uwana, mu zauna muyi lissafin yadda muka had’a na Abdullahi, zaka ji duk wani bayani daga baya. Nayi murna sosai wallahi, Allah ya tabbatar mana ya sanya alkhairinsa a cikin lamarin.
Allah yasa kuma ta zama alkhairi a gare ka da kuma ‘ya’yan da zaku samu a gaba.”
*******
A cikin sati uku, kusan komai ya koma daidai a rayuwar Nanne, sunyi jarabawar first term sun k’are har an bada hutu na wata d’aya.
Hutun data san ita ta gama zuwa makaranta kenan, don baza ta koma second term ba sai lokacin Waec da Neco kawai kamar yadda baffa yace. Shirye-shirye ya kankama sosai daga kowanne b’angare, don hatta iyayen Imran maza sun kawo lefe akwati goma sha uku, Sannan ya had’a ta da’yan uwansa a waya sun gaisa.
Daga b’angaren inna kusan ba abinda bata tanada ba na harkar kayan d’akinta, ko baffa abinda ya bayar kad’an ne inna tace ta yafe masa tunda bai dad’e da bikin mata hud’u ba.
A cikin wannan lokacin ma Nuratu tazo da nata gudunmawar ita da ‘yan uwanta, a sannan ne kuma Nanne take jin cewa shima Nuran da tayi mata zancensa an kusa bikinsa a lokacin itace bata sani ba a lokacin.
Ranta yayi fari kal! da tunanin shawararta Nanne ta karb’a ta yarda da aure a yanzu, musamman kafin su tafi da Imran yazo suka gaisa, sai farin cikinta ya k’aru, tana ganin ba k’aramar sa’a Nanne tayi na samun miji irinsa ba.
A kullum kuma alak’ar dake tsakanin Nanne da Imran k’aruwa take, a yanzu ta saba dashi sosai don har tana sakewa tayi masa hira a waya ko kuma in yazo. Duk da cewar wayar tasu tafi yawa, don a k’aida ne kullum zai kirata sau uku, da safe in ta tashi, da rana in yana office, da kuma da daddare in zasu kwanta.
Da gaske ne ya dad’a koya mata yadda zata so shi, don ko kad’an yanzu ba alamun wannan damuwar data shiga kwanaki sanda baffa yace aure zai mata, ta daina tunanin duk wasu abubuwa da zasu faru nan gaba, burinta kawai a kullum Imran ya kirata ya kara tuna mata cewa ta kusa zama tasa, duniyar gaba da take hangowa mai tsananin kyau ce tunda tana tare dashi
Don hatta karatun da take tunanin zata cigaba a yanzu ji take yi meye ma amfaninsa in dai Imran yana cikin duniyarta.
Kusan komai ya gama kammala a satin da aka tsayar na auren. Imran ya bada muk’ullin gida a can wata unguwa dake nesa dasu.
Gini ne na zamani mai kyau sosai, d’an moderate house mai d’auke da falo biyu da three bedroms, dining da kitchen da kuma toilets uku. Ba wai tamfatsetsen gida bane amma yadda ya zama well furnished ya k’ayatar da kowa akayi ta santinsa.
A yadda inna ta tsara, babu wata hayaniyar biki da za’ayi. Kamu da walima ne za’a fara ranar juma’a anan cikin gidan nasu, sai washegari asabar ayi d’aurin aure da yini. Da yamma kuma akai amarya.
Nanne ta gaiyaci kusan duk ‘yan ajinsu na islamiyya da kuma boko, don har islamiyar data bari sai da taje ta kai musu cards d’in, kowa yayi ta mamakin yadda basu tab’a jin zancen ba sai kati kawai suka gani, don lokacin da ta gayawa Aminah komai, sai da ta gargad’e ta kar ta fad’awa mutane saboda gudun surutu.
‘Yan islamiyya kuma ba wajen wanda zasu ji tunda Rahma ba fad’a zata yi ba, kuma ko wasu daga ‘yan layinsu ma basu ji ba sai da komai ya matso kusa.
Amma duk da haka sai da zance ya fara yawo a makarantar bokonsu cewa auren kud’i zata yi, wai irinsu dama basa gama makaranta suke samun Alhazan birni su aure su. Sai dai da yake shine bikin ‘yar Ajin na farko da zasu fara, sai d’oki ya hana wannan gulmar tasiri, kowa ya shiga fafutukar siyan an anko wanda Amina ta fitar da kuma shirye-shirye.
Sanda Nanne taje ita da Rahma suka kaiwa su Malam Murtala katin d’aurin aure, ba karamin farin ciki da murna suka nuna ba, ta san tunaninsu iri d’aya ne da malaman da suka cewa Baffa aljanu na shirin shigarta kuma aure ne kawai abinda zai iya kore su.
A yanzu da sune silar farin cikinta bata sani ba gode musu zata yi sab’anin a farko da take ji sun juya duniyarta upside down?
Ranar laraba da daddare bayan ta wanke lallen da aka tsantsara mata, tayi wanka sannan ta saka kayan bacci, da kyar ma ta iya samun wanda zata saka don inna ta riga ta gama had’a dukkanin kayanta da zata tafi dasu sauran kuma duk ta rabar, harda wad’anda take tsananin so ba damar tace a bar mata.
Ta kwanta a kan gado cike da gajiya, daga nan tana iya jiyo hayaniyar ‘yan falo wanda ke cike taf! ana musu nasu lallen.
Idan wani ya shigo cikin ba zaice dama bayan bikinsu ya Aisha ‘yan niger sun koma ba, don wannan karon harda k’arin wasu aka samu tunda bikin na inna ne
Banbancin kawai shine na ‘yan uwansu mama halime, mama rabi da kuma hajiya Babba da basa nan wannan karon. Duk inda ta juya taga mutane sai ta kasa yarda cewa wai bikinta za’ayi, wai duk sunzo ne duk saboda ita kawai…
Wayar inna a kusa da ita tayi k’ara, Amina ce, ta d’aga ta kara a kunnenta.
“Toh Wallahi dole jibi sai mun fita da wuri, don su Aysha mahmoud naji duk sunce wajen suma Zarah zasu je kwalliya, kuma kin san ita first come first serve take yi, zata iya miki ni tawa tace sai ta musu tukunna ta b’ata mana tsari.”
“Toh Allah ya kaimu sai mu tafi tun sha d’aya, me ake ciki da masu ashoken?”
“Gobe zanje in karb’o insha Allah, don sun kirani sunce sun gama, sai dai mai beads ne zai b’ata min rai da alama, don jiya sai masifa yake wai an bashi a k’urarren lokaci.”
“Kiji sai kace ba biyansa za’ayi ba, shi kad’ai ne ya iya, in kinje bai gama ba ki bar masa kayansa aje wani wajen, na san ko ya aka k’ara musu kud’i akai da gudu zasu yi wallahi.”
“Nima tunanin da nake yi kenan, yawwa ki cewa Rahma mu had’u goben wajen sha biyu, tace zata kai kayanta itama a mata beads d’in.”
“Toh shikenan, in mun fito saloon sai ku had’u kawai, don wajen goma dama nake tunanin mu fita.”
“Amma dai Sa’adha ba mai zaki sawa kanki ba koh?”
“Wallahi da nayi niyya amma Aunty nafisa ta hanani, steaming kawai zanyi.”
“Ai gwara, in ba haka ba b’ata gashinki zaki yi, duk laushinsa me zaki k’ara akai.”
“Toh kar dai ki manta gobe duk ki d’ebo kayanki, dazu na k’ara kiran umma (maman Aminar) tace da kwana biyu da uku ai duk d’aya ne.”
“Eh nima dazu ta fad’a min, zan d’uro akwatuna na a motar Sani, da daddare ya kawo min in na gama zagayena a gari.”
“Toh shikenan sai goben.”
Tana kashe wayar Aunty maryama ta shigo da kofi a hannu, Nanne taji ranta ya b’aci a lokaci guda, d’azu har tana murna cewa sun manta ashe yana tafe, kusan sati biyu kenan ana d’ura mata jik’e-jik’en da ita ba amfaninsu take gani ba.
Ance na gyaran jiki ne, bayan na gidan matar da kusan satinta biyu tana zuwa sai jiya ta sallameta, wai don ma za’ayi k’unshi yau ne, da ta tabbata sai yau d’in ma taje.
“Wata yamutsa fuskar ki fa baza ta sa in fasa ba wallahi…”
Aunty maryaman ta fad’a bayan ta tsaya a jikin gadon, ta mik’a mata.
“…ban kofin yanzun nan.”
Nanne ta had’e rai sannan ta k’arb’a ta rufe idonta, ta had’iye shi a lokaci guda.
“Kya gama had’e ranki ne, Allah ya kaimu ranar da zaki zo da kanki ki tambayeni, anan zaki ga nawa had’e ran nima.”
Bayan fitar ta, ta jawo ragowar katinan bikin dake kan bedside drawer.
Sau ba adadi kenan take karantawa, amma har yanzu gani take kamar ba nata bane, kamar ba sunanta ne a jiki ba. Idonta ya kai kan sunasa, wanda aka rubuta da italian font mai lankwasar nan.
Imran Siddiq!
Me yasa ne shi komai nasa ya had’u?
Wayar inna ta sake k’ara a kusa da ita, ba sai ta duba ba, tariga ta san ko waye, don a lokacin k’arfe goma ne daidai kuma ringtone d’in ma daban yake.
“Assalamu Alaikum.”
Tayi murmishi sosai, a k’aidar waya wanda ya d’auka shi zaiyi sallama amma shi kullum ita ke amsa masa sallama, tana d’auka ya sani.
“Wa’alaikum Salam.”
Muryarsa can k’asa-k’asa kamar mai jin bacci yace.
“Sweetheart anyi k’unshin?”
Murmushinta ya k’aru sanda ta d’go da hannayenta tana kallo, daga nan ta san abinda zai zama topic d’in wayar!
Iye di dide
Ayye yaraye nanaye ‘yanmata…
‘Yan matan yanzu sun saka kallabi ga coge
Hannayensu d’auke da zobe, ‘yan gayu!
Iye di dide
Ayye yaraye nanaye ‘yanmata…
Amarsu ta ango, ki kika ce kina so ungo
Jeki ki bashi tutar k’auna, ‘yar gata!
“…Dan Allah jama’a a marmatsa daga hanya don Allah, amarya da k’awayenta sun shirya…hanyar da zasu shigo suke nema…masu d’aukar hoto da video dan Allah ku matsa gefe, amarya zata shigo.”
Muryar Mc ta karad’e wajen yana yi yana kallon hanyar gate d’in gidan wadda ta cunkushe da tarin mutane jin ance Amarya ta k’araso. Daga gabansu train d’in k’awayen amarya ne wanda suka yi ankon wani dark yellow material sun jeru sai faman selfie suke yi wasu kuma na bin kid’an suna rawar, wajen ya cakud’e da hayaniya sai ka d’aga murya zaka ji na kusa da kai tukunna.
Nanne na zaune a cikin wata hadadd’iyar Hyundai da Imran ya aiko aka d’aukota daga wajen kwalliya, tana ciki sai kallon mutane take tana murmushi.
Wani material ne mai kyau pitch da red na fitted gown a jikinta, daurin head d’in kanta mai kyau dark red yasha duwatsu, sannan kwalliyarta light ce sosai, ba blush, ba fake lashes sannan ba heavy janbaki, lips d’inta light pink ne sosai sai kyallin gloss kawai da suke, sannan eyakeup dinta ma light ne, kohl d’in kawai aka sa suka fito.
Muryar Mc ta cigaba da karad’e wajen.
“Dan Allah jama’a a bawa amarya da k’awayenta hanya, ance mutanen Niger ne a wajen, dan Allah a matsa ba cukwi ake rabawa ba…amarya ce zata shigo ciki ku ganta..”
Abin ya bawa Nanne dariya, Bata ga Rahma ba amma ta hango Aminah nata k’ok’arin sake jera layin ‘yan ankon wanda yawanci ‘yan makarantar bokonsu ne, itama cikin shigar material d’in amma harda head, wani dark colour mai kama da golden, tayi kyau sosai musamman beads d’in data sha wahala kafin a had’a musu shi ya k’ara haskata, Ta kalli na wuyanta, yayi kyau shima dark red don tun a wajen kwalliyar ake tambayarsu inda aka had’a musu.
Tana d’ago da kanta taga Anty maryama tazo gaban windon tana kwankwasa screen.
“Bana son rashin mutuncinki Nanne, ya ana ta jiranki zaki yi zamanki kina kallon mutane?”
Ta bud’e kofar da sauri tana dariya.
“Toh Aunty gani nayi duk an cakude hanyar….”
Kafin ta karasa muryarta ta b’ata a cikin d’imbin hayaniyar mutanen da suka matso da niyyar fara d’aukan hoto.
A lokacin Zainab (‘yar autar mama halime) ta k’araso ta cikin mutane ta miko wata sabuwar atamfa mai kyau Ash da red. itama tayi kyau sosai kayanta light pink harda head, sai kallon Nanne take tana murmushi, itama tayi ta washe mata baki tunda ta san ba magana zata yi ba, ita haka Allah yayi ta kafin kaji muryarta da wuya.
“Yawwa Zainab, rik’e min d’aya kiga…”
Ta ware zani d’aya ta shiga d’aura mata a k’ugunta.
“Kayan meye kuma wannan?”
“Kayan kamu ne…sai anyi tukunna zaki cire su…”
Ta karb’i d’aya zanin ta yafa mata tun daga kan gwaggwaron har ya rufe fuskarta lokacin da Aunty Nafisa ke rabawa Aminah da wasu ‘yan mata uku k’ananan kaskon turaren wuta dake hayak’i.
Nanne ta jawo hannun Aminah bayan ta k’arb’a tace.
“Gaskiya a canja wak’ar nan, ni ba zan shiga da ita ba.”
Story continues below

“…Aikuwa ba ta yadda zan ga Mc anan? kin san dai ba zan kutsa in shiga…”
Kafin ta rufe baki, kid’an ya canja, nan take ‘yanmatan suka fara bin takun wak’ar…
Ga turare
k’amshi..k’amshinsa yana gun amare.
Ga turare…
Cikin takun steps mai kyau aka shiga da Nanne filin harabar gidansu a matsayin amarya, mutane sai cincirindon d’aukan hoto suke duk da fuskarta da kayanta na rufe. aka kaita can gefe inda aka tanada wata ‘yar karamar rumfa mai kujera d’aya.
Wata tsohuwa da Nanne ta gane a lokacin bikin su ya Aisha tayi ta rangad’a guda mai zak’i, sauran tsofaffin kuma na tsokanarta wai yau ranarsu ce, sai sun ga dama ma zasu bawa angon ita.
Inna ta bud’e sabon turaren a kwalinsa ta shiga fesawa Nanne tana ta zubo Addu’o’inta, wasu irin adduo’i masu kashe jiki wanda suka sata kuka wiwi sai dai kyar su Aunty Nafisa suka sa tayi shiru, suna fad’in zata b’ata kwalliyarta, ga ‘yan biki na jiranta a waje.
Bayan an gama kamun ne, aka cire mata atamfar sannan ‘yan matan suka sake jeruwa don raka ta main rumfar da zata zauna, tana fitowa wajen ya d’auka da wak’ar ‘Duru’ ta kowanne b’angare.
See the love i dey see for ur eyes..
I love you baby i no talk am twice
Your beauty making me do realize..
Say nepa don bring light..
So you must marry mee…
Eh eh…
You go love me
you go killing me baby..
you go follow me…eh
you are my remedy
you’re my melody..
Eh baby na harmony
you go give me
Baby palanga…
i’ll show you love dat you never seen….!
Tun Mc na magana akan d’aukar hoto har ya hak’ura yayi shiru. don kowa son d’aukan hoton yake saboda yadda ‘yar k’aramar amaryar ta burge kowa cikin shigarta da kwalliyarta mai kyau.
Aka raba abinci mai dad’i cikin nutsuwa wanda hakan ya burge kowa, sannan kuma aka shiga rabon souveneirs a jaka ga duk wanda yazo zai tafi.
Duk cikin wannan hargitsin idon Nanne na kan mutanen da akace ‘yan uwan mijinta ne, tun bayan da akayi kamu, basu kara tasowa ba sai da aka kira su d’aukan hoto, sannan basu sake ba balle har su d’an shiga cikin ‘yan uwanta, iyaka wanda yayi musu magana kawai su bishi da murmushi. Gasu farare tas! dasu kamar wani jinsi na shuwa Arab, sannan ta lura yawanci attention d’in mutane yana kansu.
“‘Yan uwan mijinki miskilaine, amma fa akwai kyau kamar shi, zaki haifo beauties in gaya miki.”
Aminah ta rad’a mata a kunne, ta kai mata duka sanda tawagarsu Inna ke shigowa rumfar don d’aukan hoto suma.
K’arfe bakwai daidai Mc ya fara shelar cewa Ango da tawagar abokansa sun k’araso. Nanne taji wani irin farin ciki ya kamata ashe rok’on da tayi ta masa yana cewa ba lallai yazo ba dama duk jinta kawai yake kenan, ko d’azu a wajen kwalliya daya kirata yawo yai ta mata da hankali da zancen zai zo ko ba zai zo ba.
A lokacin mutane sun fara raguwa, amma daga jin ance Ango yazo, sai taga kamar dawo dasu akayi, saboda yadda kowa yake mik’a wuya yana jiran yaga wane ne Angon, hatta k’awayenta na makaranta da ‘yan islamiyya ta lura duk hankalinsu ya tafi wajen ganin adadin girman Alhajin da suke zaton ta aura.
Mc yace k’awaye biyu su raka amarya ta taho da Angonta, sai a lokacin taga Rahma da kuma wata Sadiya Awwal, don Aminah ta tafi can fafutukar karb’owa ‘yan ajinsu jakar souveneirs.
A lokacin da suka k’arasa bakin gate d’in ta hango Imran a tsakiyar abokansa, ji tayi kamar zata narke a inda take tsaye saboda tsabar kyan da yayi, yasa kaya shade d’in brown da babbar riga wadda akayi mata aikin da darkbrown zare, sannan hular kansa ma darkbrown ce, yayi wani irin fresh yayi kyau kamar a cikin zane yake, murmushin fuskarsa ya k’ara dulmiyar da ita, taji kamar ta juya baya ne ta hango wata amaryar na tahowa wajensa, don ji take yi kamar ba itace dashi ba. he’s too good for her!
“Ya salam!… kinyi kyau sosai Sa’adha i can’t breath.”
Ya rad’a a daidai kunnenta sanda ya k’araso gabanta, tayi saurin juyar da fuskarta kan hasken flashers d’in dake ta dallare su. Ta gefen idonta tana iya hango bakin Sadiya Awwal a bud’e, idanunta na nuna tsananin mamaki, kamar taga wani abu ne da a zahiri ba zai tab’a zama gaskiya, to ba ita kad’ai ba kusan dukkanin mutanen ciki da kuma sauran k’awayenta haka suka cika da tsantsar mamakin ganin had’uwar Imran.
A lokacin kowa ya san hotonan da aka d’auka a baya ba komai bane, don har Mc ya fara shirin yace Amarya da Ango su shigo tsakiyar fili, yaga abin ba zai yiwu ba ya samu kujera kawai ya zauna, wajen ya zama ba abinda akeyi sai d’aukan hoto da kuma wasu ‘yan mata dake rawa.
A sannan ne ma yayyenta maza gabad’aya suka zo, bata san wa ya tsara hakan ba amma abin ya burgeta, suma su san ana biki a gidansu ba ace iya d’aurin Aure kawai zasu ba, Sadiq yayi ta tsokanarta dashi da tarin nasa gaiyar na ‘yan ajinsu maza wato ‘yan B class, daga baya kuma suka koma kan ‘yan matan ajin nasu wajen ya koma musu kamar School party.
Akayi ta hotuna sannan aka kawo musu abinci tare da sauran abokan Imran, filin ya koma na ‘yan samari da k’awayenta ‘yanmata kawai.
Kusan duk mutanen da suka d’auki hoton Amarya da Ango sun d’auka ne Imran baya kallon camera, idonsa da hankalinsa gaba daya na kan ‘yar Amaryasa dake ta murmushi kamar ba ita ce tasha kuka d’azu ba.
Har abokansa data fahimci ‘yan wajen aikinsu na tayi masa tsiya wai ‘Gobe ne fa’
Sai wajen goma sannan tawagar Ango suka bar wajen kasancewar a lokacin kusan kowa ya tafi. Aka bar Nanne da sauran ‘yan gidan nata cigaba da d’aukan hoto, musamman ‘yan niger wanda ak’alla kowaccensu tayi fiye da kala goma, sai da mai hoton yaga abin nasu ba zai k’are ba ma sannan ya tattara ya tafi shima.
“Na shiga uku, sallah Rahma ko maghriba fa banyi ba.”
Nanne ta fad’a lokacin da rumfar ta zama daga ita sai su Rahman kawai.
“Wallahi muma bamu yi ba yanzu zamu je mu had’a da isha, sai dai Allah ya yafe mana.”
Aminah ta kalleta tace.
“Ki zauna in samo ruwa da hijabi kawai muyi anan, don wallahi kina shiga ciki ba samu zaki yi su barki ba, mutane ne kamar ba wanda ya tafi ciki aka koma.”
Bayan an k’are duk wata hayaniya ta daren, Nanne ta samu tayi wanka sannan ta lalubi gadonta, wanda inna ta hana kowa kwanciya a d’akin sai ita da Amina da Rahma kawai. A lokacin k’arfe biyu saura na dare, amma ko’ina a gidan da hayaniya don da yawa basu da alamar yin bacci.
Tana kwanciya akan gadon taji kamar an dake ta da guduma a tsakiyar kanta, shikenan fa yanzu wannan ne daren ta na k’arshe a gidan nan, darenta na k’arshe a d’akinsu sannan darenta na k’arshe akan gadonta.
Daga gobe rayuwarta zata canja, komai zai canja game da ita, za’a d’aura mata aure da wani ta tafi ta bar kowa data sani, ta bar Innarta ta tafi wani gidan daban ta fara rayuwa tare dashi, shi kad’ai kawai a gida d’aya…ta yaya zata fara hakan? anya zata iya kuwa?
Ita fa duk bata hango wannan ba sai yanzu, yanzun da taga cewa da gaske ne fa, da gaske gobe za’a sallamata. wani irin tsoro ya kamata, ta tashi zaune ta rungume filon da k’arfi sanda hawaye ya cika idonta.
“Me ya faru?”
Rahma da ta fito daga band’aki da brush a hannu ta tambaya tana kallonta, hawayen daya taru ya gangaro kan kumatunta masu d’umi dasu. Aminah ta juyo daga lalubo kayan baccinta a cikin akwati tace.
“Me kuwa ya faru? taraddadin barin gida ne ya fara kamata…sai hak’uri Sa’adha, wani kukan ma ai sai gobe..!”
Ta fad’a da murmushinta, wanda hakan yasa hawayenta k’aruwa. Rahma ta zauna a gefenta.
“Toh meye abin kuka Nanne, aure ai abin farinciki ne da godiyar Allah, don Allah kar kiyi kuka, keda ba nisa zaki yi ba a garin nan fa zaki zauna, duk sanda kike so zamu zo kuma shima na san zai dinga kawo ki kiga inna….
Maimakon kalaman su kwantar da hankalinta sai taji kukan ma ya sake k’aruwa, ta kifa kanta akan gadon ta shiga rera shi kuwa, tana jin wani k’ullutun abu a k’irjinta.
Tun Aminah na tsokanarta har taga dai abin da gaske ne ta sauko ta fara bata hak’uri itama.
******
A cikin wannan daren mai d’aukar hoton nan ya shiga aikin editing pictures d’in daya d’auka shi da yaransa, saboda kar aiki ya musu yawa don gobe ma zai je yayi na d’aurin aure da yini kuma a satin suna da biki uku da zasu je.
Suna ta editing d’in suna kuma printing wasu har wajen k’arfe uku na dare, a sannan ne suka ci karo da wani abu mai tsananin mamaki daya d’aure musu kai.
Wani abu da kowannensu ya kasa yarda cewa daidai idonsa ke gane masa, wani abu da yasa kusan dukkaninsu suka cika da tsantsar tsoro.
Gabad’aya hotonan da suka d’auka na mutanen da akace dangin ango ne, babu abinda ya fito a cikinsu sai Amaryar kawai, amma dukkaninsu…dukkaninsu yadda suka tsaya a kowanne gefen babu siffarsu, sai siffar Amaryar kawai da kuma mutanen can baya.
Kuma ga alamun cewa da mutane a kusa da ita daga yanayin tsaiwarta amma kuma babu kowa.
Suka binciko gabad’aya hotonan da suka d’auka, kowanne daidai yake sai iya na dangin angon da akace ne kawai.
Wanda a yanzu, babu su ba alamarsu!
Sautin kid’an algaita, kid’an marok’a, hayaniya da turereniyar mutane a layin gidan Alhaji Mustapha Bashir shi zai tabbatar maka cewa ba’a dad’e da d’aura auren ba. Auren…
IMRAN SIDDIQ
DA
SA’DAH MUSTAPHA
Ko ina ka duba mutane ne cikin kaya masu kyau anata d’aukan hotona da kuma k’ok’arin kaiwa wajen ango don taya shi murna.
Imran yayi kyau cikin fararen kaya, hula kalar Ash wadda ta dace da aikin kayansa, sai faman murmushi yake yana gaisawa da kuma d’aukan hoto da mutanen da yawanci ba saninsu yayi ba.
Daga cikin gidan kuma mutane ne koina fal! anata hidima da hayaniya, masu rabon abinci nayi, masu rawar kid’an kwarya nayi, masu hira had’e da gud’a nayi, kowa nata farin ciki da annashushuwa sai dai duk wannan abin da ake, Nanne na can d’akin Aunty amrya inda su Aunty maryama suka tsaya akanta da abinci, don tun jiya ba wani abin kirki da taci sai kame-kame kawai.
Tana cin abincin tana share hawaye kamar k’aramar yarinya, jikinta wani lallausan lace ne colour maroon and pitch da akayi masa d’inki mai kyau, adon rigar yasha stones sannan skirt din 8 pieces ne mai bud’ewa sosai.
Aunty Nafisa ta shigo cikin d’akin da kwalliyarta itama.
“Akace kuna d’akin mama halime, can naje ban ganku ba.”
“Ai can ta tafi ita da Aminah ta b’oye d’azu, yanzun nan muka kawo ta nan, gata nan tana ci kamar guba ake bata.”
Nanne ta k’are hade rai jin haka, ita fa yunwar ce kwata-kwata bata jinta, saboda gabad’aya jikinta dama tunaninta wani iri take jinsu kamar ba’a jikinta suke, ga kuma fad’an Aunty maryama da tun safe take binta dashi, ita bata tab’a ma ganin amaryar da akewa fad’a ranar bikinta ba sai ita.
“Idan ta gama, tazo falon inna babarta da ‘yan uwanta sun zo.”
Nanne ta had’iye lomar bakinta jin haka, a d’an tsukin nan taga Nuratu kusan sau hud:u kenan, wanda a da sai ta shafe kusan shekara biyu bata ganta ba, hakan na nufin cewa da gaske rayuwarta ta canja kenan, ko kuma tana shirin canjawar don bata sani ba ko a yanzu an d’aura au….
Aaaayiryiryiryiri….!
Wata tsohowa ta bankad’o labulen d’akin ta shigo ita da wasu matan.
“Aure ya d’auru…an d’aura shi yanzu yanzun nan….Sadakinki dubu d’ari ‘yan nan…kin zama matar aure, Rana bata k’arya, girma ya hau kanki sai fatan…
Nanne taji kamar a daidai lokacin nan matar ta d’auko wani k’aton dutse tad’ora mata a kai, shikenan yanzu ta zama matar AURE? kuma matar Imran? duk mutanen nan sun shaida kuma ba wanda ya isa ya kwance?
“….Allah ya tabbatar da alkhairinsa, Allah yasa bad’i war haka muzo suna….”
Hayaniyar matan ya cika kanta, sai kawai ta ajiye plate d’in hannunta ta koma ta duk’unk’une akan gadon Aunty Amarya, ta cusa kanta tsakanin cinyoyinta sannan a hankali hawaye masu d’umi suka shiga bin kumatunta.
“Kuka ba naki bane ‘yar nan, ke da Allah ya kashe ya baki zankadeden saurayi kamar a manna a goshi…Tashi zaki yi kiyi sallah ki godewa Allah….”
Mutane suka cigaba k’aruwa a d’akin, kowa sai faman shigowa yake yana ‘Nanne Allah ya sanya alkhairi’ Tun tana jinsu har tunaninta ya zame daga d’akin ya tafi yadda zata iya zuk’e kowa na gidan ta mayar dashi inda ya fito, bata son ganin kowa a yanzu, so take kawai a barta daga ita sai Inna a d’akinsu ko ta samu ta rok’e ta cewa a bar zancen tafiya da ita yau, a bari sai zuwa nan da sati d’aya watak’ila kafin nan ta shirya tukunna.
Story continues below

Kusan minti talatin sannan Nuratu da tawagar ‘yan uwanta su shigo d’akin, shima da kyar don sunga Nannen bata da niyyar fitowa ne. Da kyar ta iya sakewa dasu don Nuratun ta dage sai bayaninsu take mata wanda ita ba ganewa take ba.
“Nanne mun kawo kaya suna d’akin Inna, akwai standing fan da kayan kitchen set wajen goma sannan…”
Da sauri ta katse ta.
“Toh Addano madallah.”
Bata san me yasa in suka kawo abu sai tayi mata bayanin komai dalla-dalla ba, ko gani take su innan zasu rik’e ne ko me?
Karfe sha d’aya da rabi, Aunty Maryama ta janyeta daga d’akin, zuwa can d’akin su Mama Azumi dake k’asa inda ba muyane sosai. Ta d’auko mata wata doguwar farar riga ta material daga cikin kayanta, rigar tayi kyau sosai saboda tana da bud’ewar umbrella.
“Ga mai kwalliya nan zata gyara miki fuska kisa wannan kayan, Sulaiman yace zasu taho da angon da abokanansa daga wajen reception su zo nan ayi hotuna.”
Nanne ta juya ta kalli budurwar dake zaune akan kujera, ta baje kit d’in kwalliyarta, ita sai yanzu ta lura ma da ita tun da suka shigo d’akin.
“Bari inje kar su lami su tafi.”
“Aunty dan Allah ki turo min Aminah.”
Tana fita ta juyo ta kalli mai kwalliyar tace.
“Hoda kawai zaki sa min sai kwalli.”
*******
Karfe Sha biyu da ‘yan mintuna tawagar ‘yan d’aurin Aure suka karaso gidan.
A lokacin Nanne ta gama shiryawa cikin kayan da suka mutukar karbeta, anyi mata rolling da wani farin mayafi mai taushi a saman rigar, tayi kyau kamar zanata akayi, sai dai duk da adadin kwallin dake idonta, sunyi fulufulu almun kowa ya ganta ya san tasha kuka.
A falon baffa kusan kowa ya taru aka yi ta d’aukar hoton, akayi da ita da Imran da inna, sannan akayi su hud’u harda baffa, sannan akayi da inna da su hajiya babba, sannan akayi da ‘yan mazan gidan, da ‘yanmatan gidan sannan akayi tayi da mutane da yawa.
Anan ne ma taga jamila, don taji ance duk amaren sun zo amma ita ko a bikin jiya bata ganta ba, su nafisa da maryam ‘ya’yan mama halime kawai ta gani sai Aisha da har kyautar sababbin English wears ta mata kusan akwati guda.
Gabad’ayansu su hud’un sun canja daga yadda ta sansu, sunyi wani fresh dasu sun murmure, wani gefen zuciyarta ya hasko mata cewa itama haka zata zama nan da wani lokaci.
A sannan ne ta kalli Imran sosai sanda ya tsugunna shi da abokansa suna yiwa Baffa sallama, tun daya kirata a wajen kwalliyar nan, basu sake waya ba, koda yake ko ya kiratan a jiya ba d’auka zata yi ba, amma yau ma bai nemeta ba, tun safe har kuma aka d’aura auren.
Ta kalli kayan jikinsa yayi mutuk’ar kyau fiye ka da jiya, farar colour da Ash, ta dade a rayuwarta bata ga mutumin da komai ke yi masa kyau irinsa ba.
Idonta na kansa har sanda shida abokansa suka bar d’akin, abinda kuma ya dad’a bata mamaki shine, ko kad’an bai kalle ta ba, balle taga wannan murmushin nasa. hankalinsa ma gabad’aya baya kanta har suka tafi, kamar ita d’in bata da banbanci a yanzu da sauran mutanen d’akin.
Ta ture wani abu mai kama da damuwa dake shirin samun waje a zuciyarta, A lokacin Sadiq ya shigo ya biyo ta cikin mutanen ya kirata, tabi bayansa suka fita.
A daidai barandar wajen d’akinsu Sulaiman, Imran na tsaye yana kallonta, shi kad’ai ba tare da abokansa ba, akwai mutane dake ta hadaniyarsu a compound d’in, kwarjininsa ya cika idonta saboda haka ba musu k’afarta ta k’arasa wajensa.
“Kinyi kyau sosai Sa’adha, I just want a picture.”
Kafin ta gama fahimtar maganarsa, ya rik’o tafin hannunta na hagu sannan ya juyar da ita gefe, masu hoton nan na tsaye suka shiga dallara musu.
A wannan lokacin Nanne taji d’umin hannunsa kamar yana zuk’e damuwar dake tare da ita ne, jikinta yayi wani irin sanyi sannan a hankali ya shiga rawa, amma abu d’aya ke yawo a ranta, Me ya sami Imran? tayi zaton zata ga murnarsa fiye da haka, a yanzu da ta riga ta zama tasa? amma ko murmurshi irin na jiya bata samu ba.
*******
Wajen karfe d’aya Addano da ‘yan uwanta suka yi sallama suka tafi ganin gidan amarya daga nan kuma zasu wuce adamawa.
Yini bikin ya cigaba da wakana, a kowanne lokaci mutane k’ara zuwa suke yi, musamman wad’anda basu samu zuwa jiya ba, k’awayenta ma da d’an yawa sun zo, anata d’aukan hoto da rawar kid’an kwarya, Har saida aka d’ora wata tukunyar abincin a gidan sab’anin da farko da duk kawowa akayi daga wajen da akayi order.
Kafin La’asar muryar inna ta dashe saboda yawan magana da amsa gaisuwa. A sannan ne kuma aka fara shirye-shiryen kai amarya.
Motocin da Imran ya aiko dasu tun daga farkon layin aka jera su har bakin titi, saboda yawa mutane har canja mota suka dinga yi, sai a shiga wannan a fito.
Aka sa Nanne ta sake wani wankan sannan ta shirya cikin wata lallausar lafaya kalar lemon green, jikinta sai tashin sassanyan k’amshi na turarurruka daban-daban yake yi, a lokacin zuciyarta ta riga ta gama tsinkewa, gani take ko ku’da ne ya hau kanta zata iya fashewa da kuka.
********
“….Aljannarki tana wajensa Nanne, shi yasa nake ta maimaita miki biyayya da hak’uri, hak’urinki shi zai sa miki tausayinki a ransa sannan biyayyarki ita zata maye gurbin duk wani abu da zaki nema a wajensa…”
Kukanta ya k’aru sosai to the point that duk wata doguwar maganar data biyo bayan nan bata iya jinta, tunaninta ya cakud’e gabad’aya ya tafi can wani waje, ta damk’e hannayen Aunty Nafisa dake gefenta tana sheshshek’a jikinta har d’agawa yake saboda ajiyar zuciya. Inna da muk’arrabanta suka yi tanasiharsu suna zaiyano abubuwan da ita a lokacin ba fahimtar su take yi ba.
Daga k’arshe aka kaita wajen Baffa, a nan ma taci wani kukan ta k’oshi don bud’ar bakin sa da farko hak’uri ya fara bata, zuciyarta ta tsinke…ta yaya baffa zai bata hak’uri? akwai abinda zai tab’a yi mata a duniya da zai sa ya bata hak’uri?
Tayi niyyar ta gaya masa ita ba abinda yayi mata, ita ba a cikin damuwa take ba, auren Imran ba zai zame mata matsala ba, amma kukan dake cinta ya hana ta, tana ji tana gani aka fitar da ita daga gidansu aka sata a mota, gidan da ta taso tun yarintarta, gidan da mahaifiyarta ta tafi ta barta a cikin sa, gidan da Inna ta raine ta da dukkan kulawarta, gidan ta fara gina rayuwarta a cikinsa, da gaske ne da ake cewa aure yak’in mata, yau ta fahimci wannan yak’in da ake nufi, don a yanzu ji take kamar runduna guda zata tafi tunkara.
Mutane sun ragu sosai a lokacin duk an tafi d’akin ya rage daga su Aminah sai Aunty maryamah da Aunty Zainab kad’ai, har a lokacin Nanne na k’udundune a cikin lafayarta tana sheshshek’ar kuka.
Aunty zainab dake kan stool ta kalli agogo tace.
“Gaskiya tafiya zamu zo muyi, babu alamun zuwan dangin ango a wannan daren.”
Daidai sannan wayar aunty maryama tayi k’ara, bata nan tana kitchen ita da Rahma saboda haka Aunty zainab d’in ta d’aga.
Abu daya ta fad’a Nanne ta gane inna ce mai kiran.
“Gamu nan, yanzu zamu taho wallahi bari in gaya musu.”
Ta kashe wayar sannan tace da Aminah.
“D’auki jakarki, bari in kira su tafiya zamu yi.”
Tana fita Aminah ta cigaba maganar da take mata.
“….Sa’adha dan Allah ki rage kukan nan, kar ya shigo ya ganki kina tayi ba k’akkautawa.”
Da kyar ta had’iye shi a mokogwaronta tace.
“Yau zaki tafi?”
“A’ah sai gobe dai, ai yanzu dare yayi su Rahman zan bi.”
“Dan Allah toh kizo goben.”
“In naga wasu zasu zo, zan biyo su amma gaskiya ba zan miki alkawari ba.”
Tayi raurau da ido kamar k’aramar yarinya.
“Gaskiya ne ai sa’adah, aure fa kika yi, dole ne ki hakura da komai ki saba da canjin rayuwarki.”
Canji rayuwa, canjin rayuwarta…tun jiya take maimaitawa kanta wannan kalmar amma har yanzu ta kasa nutsewa cikin kanta, tana kallo ba yadda ta iya haka suka tafi suka barta, bayan su Aunty maryama sun k’ara binta da nasihohin da ita ba fahimtarsu take ba. Tashin motarsu da kuma rufewar gate d’in data fahimci akwai maigadi a gidan ya dawo da hawayenta, ta sake dukunkune jikinta akan gadon tana jin gidan ya mata girma, kamar wata tsakuwa guda d’aya akan faranti.
Bata san iya adadin mintunan da suka wuce ko lokacin da ya tafi ba kafin ta jiyo wani k’arar bud’e gate d’in, ta san dai kawai a lokacin hawayenta sun k’afe, sai ajiyar zuciya da take yi a hankali.
Ta rufe idonta sanda ta jiyo k’arar taku daga inda take tunanin corridor ne, ba sai an gaya mata ba ta san waye ya shigo, Imran ne, mutumin da a yanzu kowa ke kira da mijinta.
“Assalamu Alaikum..”
Wannan muryar, wannan muryar mai taushi ta shiga cikin kunnenta, sai dai yau ba a waya ba, ko kan kan hanya ko gadon asibiti, a cikin gida ne, gidan dake mallakinsu su biyu a matsayin mata da miji.
Ba tare da ta d’ago kanta daga tsakanin cinyoyinta ba ta amsa a hankali, ba lallai ne ma in yaji ba.
“Hey….” muryar ta sake shiga kanta da wani irin amo sanda ya zauna a gefen gadon sannan bata zato taji ya lalubo hannuta daga cikin lafayar.
Numfashinta ya d’an d’auke a lokacin da d’umin hannunsa ya ziyarci fatarta, kamar dazu taji wani abu na shiga jikinta yana soothing damuwarta.
“Kuka kike yi?”
Kamar mai bashi amsa sai tayi ajiyar zuciya tare da jan hanci, shima ya d’auki hakan a matsayi amsa.
“Kukan rabuwa da Inna ne?”
Bata amsa ba yace.
“In dai haka ne dan Allah kiyi shiru, ko gobe in kina so zan kaiki wajenta…”
“Kinjiiii…?”
Taji kamar ta d’ago a lokacin ta tambaye shi da gaske yake? da gaske gobe zai iya kaita gida? amma hannunsa dake nannad’e da nata ya hanata magana, wani abu ne daga cikinsu yake shiga jikinta yana goge duk wata damuwarta.
Story continues below

“Sa’adha…” ya kira sunanta a hankali.
“Ko mu koma yanzu sai mu dawo anjima?”
Ta d’ago da kanta da sauri ta kalle shi.
Ya salam! yayi kyau cikin wani bak’in yadi d’inkin fitted mai kyau, sannan yasa bak’ar hula wadda ta fito da d’an hasken fatarsa.
Yana kalonta da idanunsa masu kama da maik’o a cikinsu, da kuma d’an k’aramin murmushi a lebb’ensa, murmushin da a d’azu taso ganinsa kamar me. Ta sauke kanta k’asa sannan muryarta ta fito.
“Yanzu dare yayi ai.” ita har ga Allah a lokacin ta yarda cewa zai iya mayar da ita gidan ne a yau, saboda haka ta k’arashe da cewa.
“A bari kawai sai goben.”
Taji k’arar murmushinsa kafin ya lalubo d’aya hannun nata.
“Zo muje kiga…”
Ya mik’e tsaye rik’e da hannayen nata, ba musu kuwa k’afafunta suka mik’e suma, ya jata har jikin wata k’ofa dake gefen wardrobe, wanda ta san toilet ne, aikuwa yana bud’ewa mamaki ya kamata ganin girmansa da bata yi zato ba, gashi komai na cikinsa light Ash ne, daga toiletries har tiles d’in, sannan ga wata fitila mai k’arfi da ko allura ce ta fad’i tana zaton za’a ganta.
Ya tsayar da ita a jikin sink sannan ya koma ta bayanta ya rik’o kafad’unta, daga cikin mudubin da suke facing tana iya ganin tazarar kafad’arsa da kanta, ta san yana da tsawo amma bata san cewa banbancin ta dashi ya kai haka ba.
“Sa’adha… I want to tell you something.”
Ya fad’i kowacce kalma a hankali kuma da nutsuwa, idanunsa kuma basu bar kallonta ta cikin mudubin ba, rudani da wata irin kasala suka saukar mata sanda taji ya zamo hannayensa daga kafad’arta, ya rik’o tafin hannayenta, zuciyarta ta dinga bugawa har tana jin kamar zai iya jinta.
Sannan tunaninta ya tsaya cak! ta tsura masa ido ta cikin mudubin, kwarjininsa na k’ara dulmiyar da ita, musamman idanunsa da suke da kyalli kamar ya d’iga mai a cikinsu, They were clear and deep! taji zata iya nutsewa a cikinsu ta manta da duk damuwarta.
“I want to share a part of my life with you, kiyi hak’uri na san kin gaji…amma in ya wuce yanzu, ya wuce yau bana tunanin zan iya sake fad’a miki.”
Ya sake shiru yana sauraren fitar numfashinta, kamar iya abinda zai fad’a kenan kafin ya fara.
“Sa’adha tun da na tashi a rayuwata ban tab’a sanin iyayena ba, sun rasu tun kafin in san kaina, haka kuma bani da wani dan’uwa na jini, sannan rayuwata tana had’e da k’alubale da yawa, na fuskanci wahalhalu da yawa a lokacin yarintata, sai daga baya na sami tallafin wata halitta da ta rik’e ni da dukkan kulawarta, ta jawo ni jikinta, ta bud’e min sabuwar duniyar dana sami komai dana rasa a baya, ‘yan uwa, d’aukaka, matsayi da kuma tarin abubuwan da a da nake musu hangen nesa.
Shi yasa nima a lokacin na d’auki dukkan soyayyata na dank’a mata, na yarda cewa bani da wani farin ciki a duniyar nan daya wuce nata.
A cikin haka sai k’addara ta jefo ni wajenki, tun daga ranar dana fara ganinki kuma rayuwata ta canja. ban san taya zan fad’a miki ki fahimta ba amma zuciyata ta fara sonki tun ranar da kuka dawo daga islamiyyar nan ke da Rahma, tun ban san ko ke wacece ba, da farko nayi kok’arin takura kaina da cewar ni da ke bamu dace ba, amma duk lokacin da nake tare dake ko na ganki sai zuciyata ta kasa daurewa.
For the first time tun lokacin da na sake sabuwar rayuwa nayi failing a wani abu, nayi failing wajen controlling zuciyata akanki, shi yasa na fara bibiyarki tun baki sani ba, har kika fara lura dani. Daga nan kuma abubuwa da yawa suka dinga had’a mu, har zuwa yanzu da Allah ya k’addara aure zai shiga tsakanin mu.
So, kome zai faru Sa’adha, kome zai faru nan gaba, I want you to keep in mind that son da nake miki da gaske ne, and it will forever be real.”
Yana rufe bakinsa, ta juyo da fuskarta ta kalleshi, yana tsaye dab! da bayanta ne, saboda haka numfashinsa ya shiga busawa akan goshinta.
“Me zai faru nan gaba?” mamaki ya fito sosai a ‘yar karamar muryarta.
Ya lumshe idanunsa akanta.
“I don’t know, abubuwa da yawa suna faruwa a rayuwar nan, i just felt like telling you saboda gudun mistunderstanding nan gaba.”
Sai tayi shiru kawai kwakwalwarta na nazari, amma nazarin ma ya kasa yiwuwa saboda yadda yake tsaye dab? da ita, tunda take bata tab’a tsayawa kusa da wani namiji haka ba, sai a yau ranar farko da ta zama matar aure.
Tunaninta ya katse, sanda ya d’ago da hannunsa a hankali ya sake juyar da ita tayi facing sink d’in, sannan ya kunna fanfon ruwa ya fara zuba.
“Kiyi alwala muyi sallah Sa’adha, mu rok’i Allah ya kore duk wani abu da zai shiga tsakaninmu.”
Har tayi alwalar ta bishi jam’in sallah raka’a biyu, kwakwalwarta nazari take yi sosai na maganganunsa, amma har a lokacin abubuwa da yawa ta kasa fahimtarsu.
Bayan sun idar da sallar, ya juyo ya sake rik’e tafin hannayenta sannan yayi addu’o’i wanda da yawansu na nema musu zaman lafiya ne sannan yace da ita taje tayi wanka ta rage kayan jikinta.
Yana fita daga d’akin ta murd’a muk’ulli sannan ta cire lafayar jikinta, akwai heater a band’akin ta had’a ruwa mai d’umi sannan tayi wankan, tana yi tana kallon band’akin tana tuno nasu itada inna, tana ganin kyansa kamar me amma wannan ya ninka shi a komai.
Ta zura wata doguwar rigar bacci har k’asa bayan ta fito sannan ta feshe jikinta da turare. Har ta kashe fitilar ta kwanta sai kuma wani tunani yazo mata, ta taso ta bud’e muk’ullin sannan ta koma tana sak’e-sak’en yadda daren yau zai kasance mata.
Maganganun Imran suka yi ta yawo akanta, ta san addu’ar neman zaman lafiya abu ne mai kyau da ya dace su fara dashi, amma yadda yayi ta maimatawa da kuma addu’o’insa da suka fi yawa akai, ya sata wani tunanin.
Ta dunk’ule hannayenta tana tuno yadda a dare d’aya kawai ta fara sabawa da yadda yake rik’e su.
Kusan minti biyar sannan ya turo k’ofar d’akin ya shigo, da alamun shima wanka yayi, don ya canja kayansa zuwa wata light jallabiya, gashinsa alamun a jik’e sannan k’amshinsa ya cika d’akin.
Ya shigo cikin bargon lokacin da ta sake duk’unkune jikinta daga can k’arshen gadon, bata ko d’ago da kanta ba don idanunta na kan yatsunta, amma taji alamun kamar ya kalleta kafin yaja bargon jikinsa sannan yace.
“Allah ya tashe mu lafiya wifey.”
Wani dad’i ya ratsa ta, abinda take fatan taji kenan, sai kuma yazo har da k’arin wani sunan mai dad’i. Wifey!
tayi murmushi a hankali sannan ta amsa.
“Ameen.”
********
“Zaka jira nan da kamar minti goma ayi warming d’insu sir.”
Matar dake zaune a kujerar cashier ta fad’a fuskarta d’auke da mirmushi.
Good. Imran ya amsa a cikin ransa a fili kuma sai ya d’aga mata kai sannan ya juya ya fita daga restaurant d’in ya nufi cikin motarsa ya zauna.
Yana bukatar lokaci dama, alone time d’in da zaiyi tunanin dake cikin kansa kala-kala. A driving seat yake zaune amma senses d’in hancinsa na iya jiyo masa wannan cool k’amshin da yaji a jikinta jiya, alamun har a yanzu motar bata rabu da k’amshin inda ta zauna sanda za’a kawo ta gidansa.
Komai ya riga ya kammala a yanzu, Sa’adha ta zama matarsa bisa k’okari da fasahar jaamil, saboda kusan komai daya faru shi ya tsara, shi ya tsara duk tarin abubuwan da suka faru a d’an tsukin nan, tun daga kan iyayen daya gabatar a wajen Baffanta har zuwa matan da suka je a matsayin danginsa wanda duk babu su a gaske, ya rufewa mutane ido ne kawai sunga alamun siffarsu amma babu su d’in a zahiri.
Hallucination ne kawai yayi planting a cikin idanunsu. don da ace an samu wanda zai haska su a wajen da mudubi ba zai gansu a ciki ba. Shi yasa ma mai hoton nan ya kusa kawo musu matsala, ba don Allah yasa jamil ya….
Tunaninsa ya katse, sanda wani saurayi ya kwankwasa masa glass.
“Yawwa yallab’ai gasu nan gabad’aya ne, harda receipt d’in.”
Ya fad’a yana zuro masa ledojin hannunsa, Imran yayi godiya sannan ya rufe glass d’in, ya tada motar ya cilla ta saman titi haka ma zuciyarsa ma ta cilla can inda ya nufa a yanzu wato gidansa.
Tsawon shekara d’aya kenan da uzirinsu ya shigo dashi wannan rayuwar, ya bar al’adarsa da komai ya canja yanayin halittarsa, amma duk tsawon wannan lokacin bai tab’a jinsa more human ba irin jiya da yau, watakila har gobe ma da jibi…har zuwa ranar da komai zai k’are.
Sau ba adadi ya sani aurensa da Sa’adha ba abu ne mai d’orewa ba, don ko a yanzu baya tunanin suna da abinda ya wuce karfin watanni, shi yasa a jiya bayan an gama d’aura auren zuciyarsa ta karye da ganin irin d’imbin farin cikin dake faruwa a gidansu, ya hango ranar da shi d’in da kowannesu ke yabo a yanzu, zai zama abin la’ana a wajensu, a lokacin da shi d’in baya nan kuma, baya cikin wannan jikin da mutane suka sanshi dashi.
Ranar da shi kansa zai ji haushin kansa, zai k’ara yin nadama da regreting abinda yayi sau ba adadi, mistake d’in da yayi tun farko na shiga jikinta, don da ba hakan ba, da komai dake faruwa a yanzu bai kasance ba.
Da Sa’adha na can na karatunta bata zama matarsa ba, da watakila shima ya gama abinda ya kawo shi ya koma nahiyarsu, can wajen gimbiyarsa Sareefa. Amma k’addara ba haka ta tanadar masa ba, ta shigo da sa’adha cikin rayuwarsa a wani irin yanayi da yafi k’arfin tunaninsa, don da gaske ne abinda ya fad’a mata jiya.
A yanzu, ya yardarwa kansa cewa da gaske yana son ta, zuciyarsa ta nutsu da ita kamar yadda ta amince da Sareefa a baya, shi yasa ya bud’e mata wani b’arin zuciyarsa da yake babu shi a tsarinsu shida jaamil, a lokacin tausayinta ne ya kamashi ganin tana kuka, ya san ya yaudareta ne ya rabo ta da iyayenta ya kawo ta cikin fake rayuwarsa, atleast she deserve to know something that is true about him, duk da cewa ma baya tunanin ta fahimci dukkan zancensa. ba lallai ne ma ta gane ba.
Sannan yayi ta nanata zancen nema musu zaman lafiya ne saboda zamanta dashi had’ari ne, ita d’in ba abokiyar halittarsa bace, dole ne yayi taka tsan-tsan da kansa a wajenta, dole ne in yana tare da ita hankalinsa ya zama fully a jikinsa don she’s so fragile to him, kamar mutum ne ya rik’a wasa da circle d’in kwanduwar kwai a hannunsa, kuma ya na yi da zummar cewa ba zai fasa cikinta ba.
Saboda haka ba zai tab’a bari zamansa da ita ya samu matsala ba, zai iya k’ok’arinsa wajen nuna mata dukkan kulawarsa yadda ba zata fahimci rashin wasu abubuwa ba, don kamar yadda ya sani kuma jaamil ya dad’a fad’a masa a jiya, akwai abubuwan da ba zai tab’a bari su faru tsakaninsu ba.
Ya tuno d’azu da yazo tashinta sallar asuba, tana baccinta peacefully a lokacin, hular kanta ta zame gefe kad’an sannan strands d’in gashinta mai kyau ya kwanta smoothly akan filon, ta rik’e fuskarta da tafin hannayenta biyu a kowanne gefe kamar k’aramar yarinya, sannan bakinta slightly a bud’e.
Yana iya jin fitar numfashinta a hankali daga tsakanin leb’b’en nata, a lokacin yaji kamar ya matsa kusa da ita ya d’ora yatsansa akan leb’b’en, yaji irin taushi da d’umin da suke dasu amma ya hana kansa.
Yadda ya barta tayi baccinta hankali a kwance jiya ba zai so ya tashe ta da wani abu da bata saba ba.
Ya lashe gefen lebb’ensa sanda ya k’araso bakin gate d’in. Tun kafin ya danna horn maigadin ya fara k’ok’arin bud’e gate din. Sunansa Malam Aminu, wani tsohon dattijo a kamfaninsu da ya d’auko shi tun sanda ya siya gidan a matsayin mai gadi.
“Sannu da zuwa Alhaji, Sannu da zuwa.”
Ya fad’a lokacin daya shigo da kan motar cikin gidan. Maimakon ya amsa sai yace.
“Ina kwana Baba, mun tashi lafiya?”
“Alhmdlilahi Alhaji, Alhmdlilah. Jiya ina taso in tuna maka zancen tankin nan na baya daya fashe kuma sai naga dare yayi.”
“Ya salam, na manta ne amma da kayi magana ai, yanzu to babu ruwa a ciki ne?”
“A’ah ai da yake jiya na sami b’arin wasu robobi a can baya na aikin gidan, sai na k’ona su na manne shi, to ya ragu dai amma har yanzu ruwan na zuba.”
“Toh shikenan Baba, zan fita anjima sai in taho da wanda zai canja shi….ga wannan.”
Ya d’auko d’aya daga cikin ledojin gefensa ya mik’o masa, ya karb’a da godiya sannan ya k’arasa ciki, ya ajiye motar a daidai balcony k’ofar falo sannan ya fita, ya kwaso ledojin ya rufe motar.
Sai da ya tsaya a gaban k’ofar sannan ya fara k’ok’arin lalubo key d’in a cikin na motarsa. sai dai kafin ya kai ga budewa ya jiyo wasu ‘yan k’ananan taku daga ciki, sannan hannu yana fumbling da k’ofar, a sakan d’aya k’ofar ta wangale Sa’adha ta tsaya a gabansa cikin shigar wata doguwar riga ta orange material, rigar ta haska kalar fatarta da tayi fresh sannan ga hannayen nan nata da suka sha kunshi d’as, ya illahi! ya had’iye yawu da kyar sanda ya lura da idanunta.
Me ya same ta?
Kuka take yi!
●﹏●