TSINTACCIYAR MAGE CHAPTER 1 BY AUFANA

TSINTACCIYAR MAGE CHAPTER 1 BY AUFANA

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_+

*UGANDA….*

_JAWAHIR FEDERAL UNIVERSITY OF UGANDA 25/2/18~7:30PM_

Kyawawan y’ammata ne na hango guda uku acikin katafaren filin School d’in jawahir Federal University dake acikin k’asar UGANDA,,,,….

Tafiya suke acikin nutsuwa tamkar basasan taka k’asa tamkar tausayinta sukeji haka suke tafiya akanta, kyawawan yammatane kuma y’an gayu masu ji da gayu had’uwa dakuma wayewa,,..

   Kutsawa nai namatsa akusa dasu saina hango wata kyakkyawa wacca naga dikta fisu kyau had’uwa gayu dakuma iya sarrafa takon tafiya acikin salo da kwarewa,,…

Kyakkyawa ce sosai ajin farko,farace tass tamkar baturiya mai matsakaicin tsayi kantsa acike yake da suma tabazo ta sakko mata har gadon bayanta, fuskarta d’auke take da kyawawan sexy and blue eye’s, pink lips and doogon siririn hanci mai kamada ink, d’an k’aramin baki dai dai na kissing, yatsunta masu d’an tsayi farcenta kuma d’auke suke da jan lalle, farinta tass yake bayada sirkin ja atak’aice dai kyakkyawace ajin farko,,…

Tafiya suke suna fira da’alamu kuma sunajin dad’in firar tasu saboda yanda naga suna fara’a suna dariya suna tafawa hakan yatabbatarmin da sunajin dad’in firar tasu,,…

Suna cikin tafiya saiga wata dalleliyar mota black color tazo da gudu zata wucesu sai aka d’aga glass d’in murfi aka watso wa d’aya daga cikinsu wacca take ta farko kwalbar lemu wacca take da sauran lemu Orange juice mai color sosai  acikinta nantake sai kayanta sukad’an baci amma ba sosaiba,,…

Dasauri tajuya domin ganin wanda yamata wannan b’arnan cikin tsintsar b’acin rai dakuma masifa sai taga wannan motarce “kan uban can” tafad’a a bayyane cikin tsintsar masifa, jin abunda tafad’a yasa sauran sukajuyo domin ganin abundake faruwa saboda sam hankalinsu bayanan yana kan firardasuke,,…

Ganin abunda akamata yasa suma biyun sukace “kutmar uba kenan wane tsohon d’an rainin wayone yamaki wannan iskancin yanzu muje muyaga masa rigar mutunci” batace dasu komaiba saita masu nuni da motar, daalamu dai magana wuya take mata hhh lol,,…

Suna ganin motar sai d’ayar tace “waye keda wannan yagaggiyar motar acikin School d’innan dahar zai lallatamaki kaya amma bazai tsaya yabaki hak’uri ba bari kawai muje muwankesa mu nunamasa shidin bakowa bane”  tana fad’ar haka tajuya domin zuwa gun driver d’in motar,,…

Dasauri tarik’o hanunta ta dakatar da’ita dafad’in “no no my friend wannan aikin nawane saboda ba’ataba b’ataman rai acikin School d’innan ba kamar yau saboda haka nice zan hukunta dik wanda yamun wannan aikin dakaina”  tana gama fad’ar haka tajuya tawuce sukuma sukabi bayanta,,…

Motar na tsayawa tai parking sai mamallakin motar yafara sakko k’afarsa waje domin fitowa, ahankali yafito daga cikin motar yad’aga hannayensa sama yai mik’a tareda fad’in “laa’ilaha illallah muhammadar rasululluh s.a.w” bayan yagama saiya rufe murfin motar yasaka key yarufeta sannan yajuyo cikin wani irin salo yana juya Key’s d’insa acikin yatsansa na tsakiya,,…

Hmm…!!! Masha Allah nafurta azahiri saboda ganin wani handsome gyai mai k’irar samarin larabawa danai,, kyakkyawane sosai dan za’aiya sakashi acikin kyawawa sahun farko, fari ne mai sirkin ja, fuskarsa mai tsayice wacca take d’auke da dogon hanci da kyawawan eye’s, sumarsa tamkar ta JAWAAD habibin ZULAIHERT, bak’a ce wulik mai d’an tsayi,  idanuwansa nacikin bak’i ne wulik saikuma farin mai haske tamkar farinwata acikin sarararin samaniya, eye lashes nasa masu d’an tsayine dan idankagansu zakayi zaton sakamashi su akayi banasa bane, mai tsayine sosai saboda ba gajere bane kamar malam adamu ogan Mrs Adam’s hhhh Lol,,,…

Atak’aice dai kyawawane sosai,..

Waigowarda zaiyi sai kawai yaji saukan mari a hab’arsa mai shegen zafi, cikin masifa azuciye yad’ago domin ganin wanda yamaresa dakuma nufin cin uban dik wanda yamaresa,, mamakine yabayyana a fuskarsa ganin yarinya k’arama wacca bazatafi sa’an k’anwarsa ta hud’u ba a tsaye ta zazzaro dara daran idanuwanta tana huci tamkar kumurcin maciji,,….

Wani irin mugun kallo tamasa sannan tad’aga yatsanta ta nunasa da yatsan tana juyasa cikin tsintsar masifa tafara magana “idan kanacin k’asa to kakiyayi ta shuri saboda ruwa ba sa’an kwando bane,waye kai dahar zaka watsaman lemu ajiki kuma katafi abunka batareda katsaya kabani hak’uri ba, natabbata bakasan koni waceceba shiyasa ka aikata haka so zan iyamaka rangwame namaka hak’uri but bara kaji this is the forst and last dazaka sake aikataman haka kuma na kyaleta next idan kasake katabbatar saina hukuntaka sainamaka abunda har jikokinka bazasu mantaba so u have to be very careful saboda banad’aukan raini gadik wani kazamin talaka dake cikin wannan School d’in hope u understand me” tana kaiwa nan tatsaya shikuma saiya kyalkyale da wata iriyar dariyar mamaki, saida yatsagaita sannan yasha kunu yamurtuk’eta fuska tamkar baitab’a dariyaba yaduk’o dai dai fuskarta saboda yaga yamata tsayi kashedinda zai mata bazaishigeta dakyauba yace,,….

“heyy smolle baby look at me very well zahiri kinga namaki kama da sa’anki dazakizo kina fad’aman waennan banzayen zantukan naki, ni bana buk’atar sanin koke wacece ke kece kikeda buk’atar sanin koni waye saboda nangaba kisan yanda zakiman magana but let me tell u something, this is the last worning danabaki wanda zaki sake d’aga hanu ki tab’a fuskana harma kikaiga marina if not kuma i will teach u a good lesson inafatar kin fahimci kalamaina” dikda tarin masifa da bala’i datazo dasu domin ta saukemasa tanaganin fuskarsa dakuma yanda yake kalamansa nantake saitaji yamata kwarjini kwarjininsa dikya mamaye mata fuska amma dikda haka saita daure tak’ara shan kunu tace,,….

Hmm….!!! Kaine dai ke buk’atar sanin koni wacece saboda ni sanin kokai waye bayada amfani agareni bashida wani amfani agareni  kuma tinda kanuna kai taurin kaine dakai shikenan muzuba mugani wazai fara kwasa ni dakuma kai gafili ga mai doki amma kasani namaka alk’awarin saina nunamaka bakin rijiya ba wurin wasan makaho bane sannan ruwa sam basa’an kwando bane” wani irin tsakin kinma rainani yaja sannan yace “au hakama kikace” tace “eh hakanace kuma haka nake nufi” ohhk to shikenan wasan ai yanzu tafara muje zuwa ni da ke za’aga wanda zaiyi raki yafad’i. Yai murmushin gefen lebe itakuma tajuya zata wuce,,…

Har tayi tako d’aya biyu saita juyo cikin murtukewar fuska tace “inamaka fatan rashin nasara” shareta yai yabud’e murfin motarsa yashiga yama fasa yin abunda yakawoshi yau saboda jin rayuwarsa yake a b’ace nan yatada motar yai river’s sannan yafigeta da k’arfi yabar cikin School d’in,,,…

Yana wucewa tabuga wani uban tsaki itama tawuce izuwa gida domin sauya kaya cikin tsintsar b’acin rai batareda tajira sauran k’awayennan nata ba, suma kuma saboda sanin halinta yasa suka kyaleta harta sakko sannan subata hak’uri, motarta tafiddo wata galleliya ce pink color mai tsadar gaske, tana fiddota tabud’e tashiga tafigi motar tabar School d’in,,,…

Rai a bace ta’iso gida tanayin parking tafito tarufe murfin motar sannan tawuce cikin gida, tana shigowa parlor ba kowa kai tsaye tawuce izuwa d’akinta, bayan tasauya kaya tasake wata sabuwar make up wacca bazata wuce powder sai man baki ba donko kwalli bata shafawa barekuma jan baki, bayan tagama sannan tafito domin komawa School…Wunin ranar sam batayisa acikin jin dad’i ba saboda ji take ba’ataba rainataba kamar yau wai itace wani kazami zai watsawa juice ajiki kuma yatafi abunsa batareda yabata hak’uri ba kai ina hakan sam bazata tab’a yuwuwa ba dole ne tahukuntashi,,…+

Haka tad’auki lectures na ranar amma badan tafahimci abunda aka karantardaitaba saboda sam hankalinta da tinaninta basa gareta sunagun tinanin irin wulakancinda zatayiwa wannan gyai d’in domin tahuce abunda yamata saboda sam bazata bari kamarta had’addiyar lady awulak’antata agaban mutane batareda tad’auki fansa ba,,,…

Haka dai suka gama abunda suke a school d’in suka koma gida ita da k’annenta,,…

                *****  *****  ***** 

*SHIN WACECE ITA…..?*

MUFIDA AHMAD SHITU shine cikakken sunanta y’a ga vice governor of kebbi state, MUFIDA itace y’a tafarko agun iyayenta su hud’u suka haifa amma itace forst, MUFIDA MUBINA MUNIRA sai k’anensu MUSTAPHA,,, MUFIDA takasance mai shegen jijji da kai sangartatta shagwab’abb’a kuma miskila,,…

Mahaifinta shine ya sangartata yanuna mata cewa itafa y’ar babban mutum ce donhaka baidace tai mu’amala da k’ananun yaraba dole k’awayenta suzama y’ay’an manya ne, kasancewarta kyakkyawa sosai yasa take jan aji ga samari yanda takeso dik wanda yanuna yana k’aunarta saitacimasa mutunci ta wulk’antashi san ranta kuma idan mahaifinta yaji bazai tab’a yimata fad’a ba,,,…

Yanamatukar k’aunarta yana nunamata gata fiye da tinanin mai karatu yananuna fifiko sosai atsakaninta da y’an uwanta danko tafiya yai tsarabanta daban take data sauran y’an uwanta,,,….

Hakan kuwa bak’aramin batawa mahaifiyarsu hjy FATIMA rai yakeba saboda suma yaran tin basa damuwa har sunfara damuwa suna magana akan abunda dadyn su yakeyi, itama kuma hjyr batasan abunda yakeyi kullum cikin yimasa magana take akan yadaina ai dik y’ay’ansane, watarana datamasa magana yahassala saiyacemata “idan bai nunawa MUFIDA gataba wazai nunawa itafa jininsa ce y’ar sace wacca yafara gani a duniya to daga yanzu karta sake masa magana akan dik abunda taga yanayi MUFIDA wani yanki ce na jikinsa idan tacutu to kamar shima yacutu ne,,…

Ran hajiya yab’aci sosai amma haka tahak’ura takyalesa,, MUNIRA bata damuwa sosai saboda Allah yahad’a jininsu da MUFIDA suna k’aunar junansu sosai amma MUBINA kam wani lokacin har kuka takeyi akan bambancin da dadyn su ke nunawa a tsakaninsu hakan yasa sam basa shiri da MUFIDA shiyasa ma ko d’akinsu ba d’aya ba MUFIDA da MUNIRA d’akinsu d’aya MUBINA kuma nata daban,,,…

Bayan sunyi karatunsu na primary da secondry a Nigeria KEBBI sai MUFIDA tace tanaso dadyn su yakaisu UGANDA sucigaba da karatu, tsintsar soonda yakemata yasa ko musu baimataba yace angama amma mahaifiyarsu kam tace itakam bata amintaba bazata yarda adaukesu suna mata akaisu har wata k’asa daban karatu batareda su suna kuda dasuba,,…

MUFIDA tadage itafa sai UGANDA momy kuma tace bazasujeba matuk’ar baza’a had’asu da wani d’an uwansu namijiba, ganin abun kamar yanaso yazama rigima yasa dady yad’akko wani d’an k’anensa faruk wandasu MUFIDA suke kira da hamma faruk saiya had’asa dasu yanemamasu admission atare sannan yanemamasu gida namusamman saboda MUFIDA tace bataso su zauna hostel,,,….

Wannan shine tak’aitaccen labarin ta yanzu kuma MUFIDA da MUBINA 300level suke sai MUNIRA 200level hamma faruk kuma 400level.

To wannan kenan.

                   ********

Kwance take akan gadonta sai juyi take saboda yanda takejin zuciyarta ba dad’i, munira ce tafahimci tanacikin damuwa saitazo tazauna akusa da’ita cikin murmushi tadafa shoulder d’inta tace “Aunty feedom meke damunkine nafahimci wunin yau dika bakya cikin walwala pleace tell me what’s rong with u” nannauyan numfashi tasauke sannan tatashi daga kwancenda take takalleta tace,,….

“my blood tinda nake a school dinnan ba’ataba b’ata man rai ba kamar yau”  cikin damuwa munira tace “waya b’ata maki rai aunty MUFIDA” hmm wallahi wani d’an rainin wayou ne bayan nayi parking nafito muna tafiya ni da Amira da Nusaiba zamuje class kawai saiga wani d’an rainin wayou yazo zai wuce acikin mota yawatsoman orange juice akaya kayana dik suka baci saida nadawo gida nasauya wasu nakoma, to ni abunda yafi bani haushi shine wallahi gayennan tafiyansa yai yak’i bani hak’uri”,,,….

Shuru munira tai saboda tasan halin y’ar uwar tata can saitace “Eyyah kiyi hak’uri dan Allah kidaina saka irin waennan abubuwan a ranki karkizo kijawa kanki hypotention” hmm bawani hypotention wallahi saina nunawa gyai d’in shidin k’aramin mara kunya ne dan saina bashi mamaki. Kallonta munira tai kawai saboda tasan halinta komai zata iya aikatawa, kamar zataimata magana ganin takwanta tabata baya sai kawai itama takwanta abunta itadai mubina yau tana gidansu k’awarta may be acan zata kwana,,,…

Washe gari bayan sunyi sallah sukai breakfast saisukai wanka sukai shirin zuwa School, koda suka fito tini hamma yajima da wucewa shikam da’alamu yanada abunda zaiyi dawuri ne a school, motarta tafiddo suka shiga suka wuce sai school,…

Suna isa taje gunda yake mallakintane idan baitaba ba wanda ya’isa yai parking anan, tai parking d’in motarta sannan suka fito kowa kama gabansa,,,…

Ahankali take tafiya cikin takonta mai d’aukar hankali mai kallo,tinda tai parking motarta samari da y’ammata na school d’in suke kallonta wani ji yake kamar yaje yarungumeta amma ina ba hali, itakuwa ko ajikinta dan ko kallo basu ishetaba sai tafiyarta take cikin takon k’asaita idanuwanta rufe da glass mai suna no respect,,,…

Ahaka tacigaba da tafiyarta harta isa gun kawayemta dasuka k’araso tin tini suna jiran isowarta tana iso tacire glass d’inta sukaimata good morning ta karb’a cikin daurewar fuska sannan tace “inaso kurakani nanemo wannan gyai d’in acikin School dinnan kan mushiga lecture”  bamusu suka ce “to”  sannan kowaccensu tasaka glass d’inta suka kama hanyar gunda ake hutawa idan anfito lecture kokuma kan a shiga,,,…

Tafiyarsu suke acikin k’asaita har suka iso wajen hutawar, suna isowa kuwa hankalin kowa yadawo kansu nan akafara kallonsu cikin sha’awa mazan wajen wasu suna burgesu wasu kuma haushi da takaicinsu sukeji,,….

Glass d’in idanunsu suka cire suka fara dube duben inda zasu hangosa cikin sa’a kuwa nusaiba tahangosa can tsakiya zaune akan kujerun wajen hutawar shi da wani kyakkyawa, tabo MUFIDA tai tanunamata shi da hanu “ohhk” tafad’a afili sannan tasaka glass d’inta tawuce gun masu aikin wajen takarb’o coca cola juice kwalba d’aya sannan tatinkari gunsa,,,….

Firarsu suke cikin nishad’i sam basu damu da kowa nawurinba hakan yasa ma wanda suka zaune atare bai tinanin gunsu tayo ba, aikwa tana zuwa olready tabud’e kwalbar nan tad’agata tafara zubamasa ruwan ajiki tindaga samansa har izuwa k’asansa cikin tsintsar masifa……Dasauri suka d’ago atare domin ganin waye ganinta yasa yamik’e dasauri yakarb’i kwalbar yai jifa da’ita gefe d’aya shikuma d’ayan dasuke atare yad’aga hanunsa zaikai mata mari cikin b’acin rai sai yai saurin rik’e hanunsa tareda fad’in “no no Mubashir just go back wannan fad’an banaka bane” cikin tsintsar b’acin rai yace “haba ur Highness dan Allah kabarni bakoyawa wannan fitsararrar hankali yanzu” b’ata fuska yai yasha kunu hakan yasa dole yamatsa baya sannan shikuma yad’ago yana share lemon,,…+

K’awayenta ne suka k’araso suna kyalkyala dariya harda rik’e ciki Nusy tace “kai feedom wlh kina birgeni sosai saboda bakya barin takwana batareda kin tadataba” kallonsa tai tace “heyy mr man mena gayamaka aidama nafad’a maka wasan yanzu aka fara tinda bazaka iya bada hak’uri idan kai laifiba to nima bazan tab’a gajiyawa ba wajen cigaba da hukuntaka ba saboda ni ba irin k’ananun matan nan bane da’ake cuta ko yaudara a banza idan anman saina rama” murmushin gefen lebe yai sannan yakalleta yace,,,….

“gaskiya kinyi k’ok’ari sosai amma kisani dik ranarda nafara mayarmaki da martani bazaki tab’a yin dariya ba sannan kisani namaki alk’awari ni MUJAHID saina sakaki kinyi nadamar dik abunda kika aikataman saina sakaki yin dana sani yin fad’a da aljani haukane” hmm kaine zakayi nadama wlh baniba stupid man”  tana fad’ar haka tajuya tasaka glass d’inta tawuce k’awayenta suma sukabi bayanta suna kyalkyala dariya,,,….

Wani shu’umin kallo yabita dashi yana murmushin zaki gane kurenki yarinya sannan yad’auki Key’s d’insa yawuce,,,….

Yana zuwa yatada motarsa yashiga shima mubashir yashiga yana yacewa “haba ur Highness meyasa zaka bari wannan k’aramar yarinyar tadinga cin mutuncinka agaban mutane haba wannan fa ba girmanka bane to ma miye amfanina amatsayin mai tsaronka matuk’ar bazan dinga kareka daga sharrin irin waennan mutanen ba kadufi yanda tamareka jiya agaban kowa yauma gashi tasake watsamaka juice aka”  murmushi yai sannan yace “karka damu mubashir inaso ne nahukuntata acikin sauk’i so now inaso kanemoman labarinta wacece ita y’ar waye kuma daga ina tazo me take karantawa a school d’in nabaka nan da gobe hope u understand what i say” year ur Highness dik yanda kace haka za’ayi. “good yanzu zan saukeka a restaurant kamana order na take away kacimman a gida” ok ur Highness. Yafad’a cikin bin umarnin abunda yafad’a masa,,,….

Wunin yau acikin jin dad’i tayisa saboda tafara rama abunda yamata wannan kuma kad’an ne daga cikin abunda tafara shiryamasa na hukuntasa, bayan sungama lectures takwashi k’awayenta suka fita zaga gari wuraren shan iska da hutawa, har kusan 6pm sannan suka wuce restaurant tamasu order na take away ita dasu dakuma munira daganan suka wuce gida,,,…..

Saida tasaukesu sannan tawuce gida,koda taisa kuwa munira hartagama komai na tsabtace gidan tai wanka tasaka kayan bacci tana parlor tana kallon TV,,,….

Cikin sallama tashigo parlon agajiye tazube kayanda tashigo dasu munira tamata sannu da dawowa sannan takarb’i kayan takai kitchen itakuma tawuce bedroom d’insu, wanka tai sannan tai sallar isha bayan tagama tashafa mayukanta sannan tasaka kayanta na bacci,,,….

Parlor tafito takwanta kan kujera 2seater tad’akko wayarta takunna tashiga yanar gizo domin ganin abunda duniya take ciki, munira ce tashigo d’auke da plate a hanunta na abinci tazo kusa da’ita tamik’a mata d’aya sannan itama tazauna tafara cin nata,,,….

Bayan sungama cin abinci tacigaba da chat d’inta har kusan 9pm sannan ta tashi tashige bedroom tabar munira itakad’ai,,,….

Washe gari takasance weekend ba’ashiga school danhaka yau hutawa kawai suke, bayan sungama y’an gyare gyarensu suka saka kaya iri d’aya wando Jean’s da t-shirt fara sai y’ar k’aramar hula, kayan sunmasu kyau sosai musamman tauraruwar MUFIDA dik wata sura tata tabayyana matasan zamanta sunfito hakama dukiyar fulaninta abun sai masha Allah, bayan sungama shirinsu munira tace dan Allah suje side d’in hamma sugaidashi batamata musuba kuwa suka tashi suka wuce,,,….

Yana a zaune parlon sa yana kallon game shi da abokinsa suka shigo cikin sallama, ahankali ya amsa shikuma abokin nasa yakafe MUFIDA dana mujiya kamar yatabota, hamma farum naganin haka nantake kishinsa yataso saboda aduniya ba macenda yake mutuwar so kamar MUFIDA saidai ita tak’i tabashi had’in kai bama tasan yamata zancen dayafara zata tashi tabarmasa wurin,,,…

K’arasowa sukai suka gaidasa sannan suka gaida abokin nasa aikuwa kamar jira yake dasauri ya karbe yana murmushi, kallonsu hamma faruk yai cikin daurewar fuska yace “ina zakuje ne kuka fito haka bana hanaku saka irin waennan kayan ba maza kutashi kuje kuciresu ku sauya wasu”  bata fuska MUFIDA tai tashagwab’e kamar zatai kuka tace,,,….

Haba hamma haba shikenan mu bamuda damar musaka kayanda mukeso yanzu to miye aibun waennan” wani kallo yamata na bansan raini sannan yace “zaku tashi kosai namakeku anan” sanin halinsa yasa suka tashi dasauri suka fita MUFIDA na un’uni kamar zatai kuka,,,….

Kai tsaye gidansu nusy suka wuce suna isa kuwa cikin sa’a suka taddata nanfa suka had’e akaita shan fira, suna cikin fira sai MUFIDA tace “kai gyaiz kutashi muje gidansu Amira dan nifa yau yawo nakeji nagaji da zama gida wlh”  nusy na dariya ta tashi tasaka kayanta sannan suka fita,, suma Nusaiba da Amira dik y’an Nigeria ne karatune yakawosu nan kuma suma dik ba’a hostel suke zamaba wasu gidajen daban iyayensu suka kama masu,,,….

Agidan Amira ma basu jimaba itama tashirya suka fita yawo, sunjima sosai suna zaga gari daga bisani dasuka gaji suka wuce restaurant sukai take away sannan suka wuce gida, saida tasauke kowaccensu a gidanta sannan suka wuce ita da munira gida,,,….

A ranar MUBINA ta dawo kasancewar bawani shirine tsakanin mubina da MUFIDA ba yasa batawani ji dad’in dawowartaba,,,…

Yau takasance Monday tin 6am MUFIDA ta farka tai salla tahad’a masu break sannan tai wanka tai shirin zuwa school, bayan tashirya sannan tai break tad’auki key d’inta da jakarta tasauran littafanta tafita tasan tinda mubina tadawo dole idan zataje tawuce munira,,,….

Tin a bakin gate data danno hancin motarta gyaiz and ladies na school d’in suka zubama mayukan idanuwansu suna kallonta tasauke glass d’in motar tana tafiya ahankali,,…

Ahankali take tafiya harta k’araso gunda take parking motarta, cikin tsintsar mamaki tafito daga cikin motarta saboda ganin wata mota anyi parking nata a gunda take parking motarta abunda ba’ataba yiba tinda tazo School d’in saboda tsoron masifarta da’ake,,,…

Kallon motar tadingayi a shekeke kamar mai motarne take kallo, cikin masifa tajuyo takalli  y’ammatandake zaune akusa da wajen tasha kunu sosai saboda karma su nairata sannan tace “hey ladies plss waye yayi parking motarsa anan”  d’ayar ko d’agowa bataiba d’ayar ce tace “wasu samarine su biyu sunshiga cikin Library tin d’azu” batako jira taji k’arshen abunda zata fad’aba tawuce takama hanyar zuwa Library d’in cikin tsintsar masifa……

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *