UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 14 BY SHATU

 UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 14 BY SHATU

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Har me napep din ya fara kokarin ja, ta tsayar dashi tunawa da tayi Babu kudi hannunta, a hannun Amira da har lokacin take tsaye ta karba kudin sannan ya nufi race course da ita, tunda Suka nufi gidan ta hango motar Ismail Yana reverse da alamar zai bar gidanne, ta rufe fuskar ta yadda bazai ganta ba, shima dake Kai ya dauka caji Bai ma lura da ita ba. A kofar gidan ta fito hannunta rike da sabuwar halittar da ya kamata ace a killace take Amma se gata ana yawo da ita cikin napep. Ta sallameshi sannan ta nufi cikin gidan, tun daga kan security Suka fara gaida ta saboda sanin matsayin ta, kowanne mamakin me ya fito da ita itada aka ce ta haihu Daren jiya, straight parlor ta wuce sede dama tun a compound din gidan ta lura da motoci uku baki tana Kuma saka ran cewar barka suka fara zuwa se kace ba ita ta haihu ba.+

” Kaya sunyi kyau sosae Hajiya Furaira, ni se Naga kamar nata sunfi na matar tashi kyau”

Abinda ta fara ji kenan kafin ta saka kafarta cikin parlon, Bata ji me Ummaah tace ba Dan tsayawa tayi cak se sun Gama magana ta far musu,

” Ai ni nayi mamakin hada auren da Kika Yi, me Zaki da yarinyar da uwarta ta shanye ubanta, ai da Hunaynah ita ce daidai class din Ismail wallahi”

Ina Hanifa kasa cigaba tayi da jin abinda suke fada, wato da gaske dao aure zaayiwa Ismail dinta, ta girgiza Kai ta shiga ciki ta manta ma me ya kawo ta gidan, kawai ganinta Ummaah tayi da jaririya a hannu, ta dago ta kalleta sannan ta kalla kayan dake gaban ta na idon duniya tace

” Uwata lafiya? Na zata zaku wuce gidan jidda ne”

Aje yarinyar Hanifa tayi a gefe tana duban kayan tana jin zuciyar ta na wani irin tafasa kamar zata Kona kirjinta, se huci kawai take ta dubi Ummaah da sauran matan dake Mata kallon mamaki tace

” Banji daidai ba ko? Bawai Ismail Zaki aurawa wata ba ko? Kice min kunnena yaji ba daidai ba”

Ummaah ta Mike da kyar saboda yadda ciwon kafar ta ya tsananta kwana biyu, ta mayi booking appointment a wani asibiti dake America zataje a dubata, tana jiran ayi bikin Ismail a Gama ne.

” Hanifa kalleni ni saarki ce? Ni Zaki zo kina yiwa dibar albarka?”

Hannunta tasa a kunne ta rufe tana girgiza Kai tace

” Kinsan ke ba saata bace Zaki Shiga hurumin aurena? Meye matsalar ki da ni da Zaki ce se ya Kara aure, Bari kiji kuskure na farko da kikai shi ne hada auren mu da shi, wallahi Babu wata mace da ta Isa ta shigo gidana da sunan matar shi sede Yar aiki!”

Bata ankare ba taji Mari a fuskarta, Ummaah is still Ummaah, wannan izzar tata tana nan Babu inda taje, Hanifa ta rike kuncinta Dan Marin ya shige ta, ta Yi kan kayan da aka hada ta fara rarumar turarrruka tana fasawa cikin tsakiyar parlon, Hajiya zaituna ta fara kokarin rike ta Amma yadda kuka San karfin mutane ne aka hada Mata. Ummaah ta daka Mata tsawa tace

” Hanifa ki maida hankalin ki, ko uwar ki jidda tayi kadan ta Hana airennan balle ke”

A hankali taji hancinta ya shanshano Mata kamshin turaren shi, ta yadda Parket din oil rolls din dake hannunta ta juyo, shi dinne a tsaye Yana binta da kallo Yana kallon yadda parlon ya hargitse ga kamshin turarrruka da idan ka Shaka se sun saka ka mura, ta taho gareshi a hanzarce tareda rungume shi ta fara kuka tana fadin

” Kasan Ina sonka, kace Mata baka bukatar wata matar, ni kadai na ishe ka”

A hankali ya banbareta daga jikin shi sannan ya Isa inda Yar shi ke kwance ya dakkota ya fita daga parlon, Babu yadda Hanifa ta iya face tabi Bayan shi, a ranta taso ba yanzun yazo ba seda ta Kona kayan tukunna. Gidan Anty jidda ya kaita kamar yadda Suka tsara tun kafin ta haihu, ta riko hannun shi Jim tunda Suka taho ko uffan Bai ce Mata ba,

STORY CONTINUES BELOW

” I’m sorry for what I did, I’m sorry my love”

Ya kalleta sannan ya Mika Mata babyn dake cimyar shi yace

” Hanifa kinyi disappointing Dina, kina ganin zanyi aure Baki sani ba? Why will you go on kiyi abinda kikai that’s disrespectful of you, Ummaah mahaifiya tace I never wanted na aureki, saboda ita na aureki kullum nasan irin abubuwan da kike Mata, Amma Ina Baki dama tunda ni dake we’re living harmoniously, me yasa zakije kiyi haka? Why will you kina ganin Zan fasa idan ke kinyi hakan? You better call her and apologize if not wallahi sede ki cigaba da Zama gidan ku and please get out of my car!”

Kowa akwai weakness dinsa, duk yadda ka kasance you’re stern and strong akwai abinda shi ne nakasun ka, haka ya kasance ga Hanifa Ismail shi ne weakness dinta, ta girgiza jin abinda ya fada ta saki hannun shi a hankali ta fita a motar ta nufi ciki, lumshe idon shi yayi Yana jin daci a bakin shi saboda bacin Rai, inda ace komai zai daidaita zaifi kowa farin ciki, he loves his wife dukda yasan ta yadda akai akai auren Amma shi yasan Hanifa ta bashi nutsuwar da yayi tunanin a gurina kawai zai samu, bashida matsala da ita Banda na suna da Suka samu, matsalar ta itada Ummaah ne, ya zuba Ido saboda Yana ganin Ummaah ita taja komai. Gida ya koma ya samu koami daidai kamar baayi ba, tana zaune haka dukkan bakinta sun tafi, se ramlah dake zaune tana Mata order sababbin turarrruka Wanda zaayi replacing Wanda Hanifa ta Bata. Ya zauna tareda kallon sashen ramlah ta mike Bayan ta gaishe shi ta wuce sama.

” A yau Ina son ka saketa , ka saki Hanifa ka Gama Zama da ita”

Ya girgiza kan shi cikin gajiyawa yace

” Ummaah please stop this, Babu kyau! Ki daina beside..”

” Yarima ni Furaira kake fadawa haka? Ni na haifeka fa”

Kanshi ya daura saman kanshi ya birkita kan da Babu gashi se kadan saboda aski da yake samu lokaci akan lokaci, idanun shi sunyi ja yace

” Ummaah ba haka rayuwa take ba, Dan Allah ki tsaya a gyara abinnan, ta Yaya Zan sake ta Bayan Ina sonta, sannan kince nayi aure Bayan yarinyar da bakinta tace min tana da Wanda take so, Ummaah wannan ba maslaha bane, kina ganin auren zaisa Hanifa ta Miki biyayya, wallahi fandarewa zata Kara Yi.”

***

Ciki shi ne Abu na karshe da yazo Raina, na manta gaba daya idan anyi aure zaa iya samun ciki, na dauka zazzabin da nakeyi duk saboda tunda aka kawo ni banida lafiya ne, shima se ya biyeni ganin na Dan samu sauki, na daina zazzabin se kwadayi da ni kadai nasan inayin abina. Ranar jumaa wutar anguwar mu ta lalace ga uban zafi da akeyi, nayi wanka yafi a kirga Amma kwata kwata na kasa daina jin zafin, se kawai na dakko pillow da karamin rug na fito kofar balcony Dina na shimfida hannuna rike da novel Ina sanaar Dana saba, nayi nisa sosae naji ana shara, na dago Naga fadila ce keyi, dake ta samu admission a GSU Kuma bamuda nisa da gurin shiyasa take zaune kamar yadda Albi ya fada min. Tunda ta fara sharan seda tazo daidai inda nake ta tattara ta juya, shiru shiru Ina tunanin zaa kwashe naji shiru, na gyada Kai na cigaba da abinda nake se gata ta Kara fitowa, na dago nace Mata

” Ki Nemo Parker ki kwashe wannan sharar”

Ianga ko haushina dama takeji ne, se cewa tayi

” Idan Kuma naki fa? Ke bakida hannu ne”

Na saki baki Ina kallonta da Kuma mamakin abinda tace, ban Kara cewa koami ba na maida kaina kan karatuna, nidai a raina Ina ayyana bazan biye Mata ba, tunda ba zaman ta nake ba, ba miji daya muke aura ba. Se can yamma na Mike n koma ciki na bar sharar gurin dukda gate keeper dinmu yso ya kwashe na hanashi. Albi na shigowa yace min

” Sofy shara a waje mantawa kikai Baki kwashe ba? Kin gaji ko”

Ya fada sounding polite Yana Mika min briefcase din shi da nazo karba, Se na rasa me zance Masa se nace

” Nima haka na ganta”

Tunda yaji na bashi amsa a haka yasan bazan Kara magana ba, ban Kuma Kara ba na wuce ciki na Kai Masa Kaya daki na hada Masa ruwan wanka, nasan baya son kazanta ko kadan, wani lokacin da kanshi yake tayani shara, tsafta ce dashi sosae shiyasa na bar sharan nasan zaiyi magana. Ina fitowa naji Yana yiwa megadi fadan sharar, shi Kuma yana Masa bayanin abinda ya faru, kitchen na wuce Ina karasa aikin da nake, ya shigo ya tsaya bayana yace

” Fadila ta Miki rashin kunya Baki kirani kin fada min ba, why will you leave her?”

Na juyo Bayan na aje leak spoon din hannuna nace

” Meye naga kana fushi, ba wani Abu bane ba, yarinta ce and beside kaje kayi wanka yau I badly need you”

Na fada abin karshen a hankali tareda Masa wink, dariya yayi ya matso kusa Dani Yana kokarin cupping fuskata nayi saurin tura shi tareda toshe hancina Ina dariya nace

” Go and bath, warin office kake”

Ya Bata fuska tareda turo bakin shi kamar yadda nake idan ya zolaye ni yace

” Ni din mun bata Kuma bazan bada abin ba”

Ya fada ya juya zai tafi yaji na rungume shi, se ya tsaya cak Yana murmushi, a hakan muka shahshance har abinda ke wuta ya fara kauri sannan na dawo hayyacina, na saki ajiyar zuciya tareda banbare kaina daga jikin shi na kashe gas din, shima Bai ce komai ba ya wuce dakin.Nayi tunanin an gama case din shara, unknown to me Ashe ana ta piling min shara ta baya inda Nima ba gani zanyi ba Dan ban fiya bude kofar kitchen Dita ta baya, ranar Saturday ce Kuma tun safe ya fita, sun tafi bauchi shi da Baffa, yace min sunje nadin sarauta ne. Tunda ya barni a kwance se wajen Sha daya sannan na fito parlor na gyara abinda Zan gyara sannan na wuce kitchen, Zama nayi a bakin kofar Ina tunanin abinda Zan ci, to Kuma yunwar ma ba jinta nake ba, se kawai na Kara komawa daki na kwanta, ban fito ba seda nayi sallar azahar har lokacin banyi wanka ba Dan wata irin kiwar wankan nake gaba daya, kitchen na shiga Bayan na Kira Albi

+

” Se yanzun Kika tashi?”

Ya tambaya lokacin da ya dauki wayar, agogo na kalla naga biyu ta gota nace

” A’a tun dazun na tashi, karfe nawa zaku dawo?”

” Da an idar da laasar zamu dakko Hanya, have you eaten?”

Seda nace a’a sannan na tuna abinda na fada,

” Bakici abinci ba har past two? Me Kika dinga yi? My God!”

Tunda ya fara maganan nake murmushi, se daya gama yaji sautin murmushi na yace

” Dariya kike ko? Kin Raina ni ko?”

Na danyi dariya Ina rufe bakina nace

” Kai Hamma ya zanyi na rainaka, na tashi bana jin yunwa yanzun Kuma Abu nake son naci Kuma Babu a gidan”

” What’s that?”

Nace

” Kifi!”

Na tabbatar seda yayi raising brows dinsa, saboda yasan ba fan din kifi bace ni,

” Yau Kuma? To Zan saka a Aiko Miki da Kifin Amma kinsan bashi kadai Zaki ci ba ko?”

Wani karfi naji ya zo min nace

” Bashi kadai ba, Zan dafa wani abun”

Daga haka yayimin sallama akan idan zasu taho zai kirani, abinci na daura inata tunanin me zanyi da Kifin idan an kawo, grilling zanyi ko farfesu zanyi, baa Jima ba aka kawo, danyen catfish, na saka cikin bowl na bude kofar baya Dan na wanke kada na Bata kitchen Dina da karni, banma lura ba da gurin har na Gama wankewa na saka cikin colander Dan ya tsane, na juyo na hanga shara an tare ta a gurin, na tsaya hannuna rike da venigar, na Jima a tsaye Ina ayyana yaushe aka Tara sharar nan ne, ni dai nasan watana kusn biyu Amma taba fitowa gurin ba, na gyada Kiana na cigaba da aikina Amma ban kwashe ba, se wajen hudu na Gama aikin sannan nayi wanka na gyaran gidan, na shigo kitchen naji ana shara, nayi saurin aje plate din hannuna na leka ta window, fadila ke sharar tana ta bulo ta inda ta Saba, seda na Bari ta Gama ta juya zata tafi sannan na bude kofar na fito nace

” Fadila!”

Ta kuwa tsaya cak, sannan ta juyo ranta a bace, nima tawa fuskar Babu alamar Wasa nace Mata

” Nan ake Tara shara dama? Ki dakko Abu ki tattara Kika kwashe”

Ta min wani kallo daya Kara kullar dani, tace cikeda rashin kunya

” Me zakiyi idan naki kwashewa”

Nayi murmushi Ina kokarin danne fushina nace

” Ai fada kikai, ki gwada kiga abinda Zan Miki”

Ta juya zata tafi nace

” Kinsan Allah idan Kika tafi Baki kwashe sharar nan ba se na baki mamaki”

Ta Kara juyowa tace

” Lallai Kam mamaki! Ke wacece da Zaki saka ni nayi abinda banyi niyya ba…”

STORY CONTINUES BELOW

” Me yake faruwa?”

Naji muryar maman Afaf, ko kallonta inda take banyi ba har ta karaso inda nake tsaye tace

” Safiyya me ya faru?’

Jin Dani take na juyo na kalleta kamar yadda take kallona tana jiran Karin bayani,

” Dama anan ake Tara shara idan anyi? Ko Kuma ni aka Raina ake Tarawa shara anan?”

Ta kalli fadila da alamar tambaya tace

” Me yasa kike Tara Mata shara anan? Bana son neman rigima”

” To Parker ne ban gani ba”

Ta fada tana cuna Baki jin abinda ta fada,

” Ki wuce ki Kira min Dan sani yazo ya kwashe sharar”

Har ta juya zata tafi Naga idan na Bari Dan sani ya kwashe to lallai gobe ma zata Kara Tarawa,

” Babu wani me gadi da zai kwashe, ita ce zata kwashe sharar”

” Saboda me?”

Ta tambaya hannunta a kugunta, nayi folding nawa hannayen kan kirjina nace”

” Saboda  ita Tara Dan haka Dole ita zata kwashe”

” Baki Isa ba” ta fada Ina gama rufe bakina, nayi murmushi nace

” Zan gani idan da gaske ban Isa ba”

Juyawa tayi tana kwadawa Dan sani Kira, Babu Bata lokaci ya karaso, already na koma ciki dakko hijab, Ina fitowa tayi min wani mugun kallo tace Masa

” Kwashe sharar nan”

Har ya dakko Parker da bin zai fara kwashewa nace

” Malam kana son aikin ka na sani, wallahi idan ka kwashe sharar nan, Baban Amna na zuwa Zan fada Masa Kuma kasan kashedin daya maka!”

A hankali ya dago ya kalleni ya Kuma kalleta ita Kuma idanunta na kaina tana ayyana me Hamma yace Wanda Bata sani ba, yace

” Hajiya babba kiyi hakuri, Amma Alhaji yace kada na sake na shiga irin wannan abin”

” Zaka kuwa ka rasa aikin”

Shidai hakuri ya Bata ya juya ya tafi, nan ta dawo kaina tana fadin

” Ke wacece da Zaki zo gidan mijina kina min Isa da iko? Nan gidana ne”

Nayi Rolling idanuna Ina murmushi nace

” Allah sarki Ashe zaman haya nake, Ashe mijin naki me ke kadai. kawai ta kwashe shara shi ne abinda nace”

Tayi ta jaraba Ina tsaye ban ko kalleta ba, da na gaji na juya na koma ciki na datse kofata, saboda bacin Rai se na mayar da abincin cikin warmer na koma parlor na zauna. Ban Kara komawa ta kansu ba Amma ni dai na sani Babu wata Mata da zata juya ni a wañnan gidan, yadda take takama Albi nata ne Hala zalika nima, seda aka idar da maghrib sannan ya dawo, Ina zaune Ina Shan tea Dan tunda na wuni banci abinci ba idan na sake naci se nayi ciwon ciki, da murmushi ya shigo, se naji duk damuwar da nake ciki ta ragu, na Mike na karasa inda yake nace

” Sannu da zuwa Albi!”

Fuskata ya Dan shafa yace

” Sannu da gida, kinci abincin?”

Kaina na girgiza Muna shiga daki nace

” Jiranka nake shiyasa ban ci ba”

Bai ce komai ba na Taya shi ya rage kayan jikina shi sannan na barshi yayi wanka, Ina fitowa Naga Amna da Afaf a zaune, Amna da cup din Dana aje tana shan tea din da guntu ya rage. Na zauna Afaf ta dawo gefena tace

” Mama tace mu zo mu gaida Daddy”

Nace

” Daddy wanka yake yanzun zai fito kunji”

Ta gyada kanta, Amna ta taso ta Miko min cup din na karba ma bawa Afaf ta Kai kitchen sannan na kunna musu kallo na tafi hado abinci,a plate daya na saka musu na shimfida musu dining mat Suka fara ci se gashi ya fito ya shirya cikin kayan Dana fito Masa dashi,kansu ya shafa Yana amsa gaisuwa su sannan ya dubeni yace

” Me yasa Kika Basu abinci, idan Kika bibiya sunci fa”

Nace

” To se su Kara ai”

Ya gyada Kai tareda min sallama zaije masallaci, Allah ya kiyaye hanya na Masa, Yana fita nayi sallah Nima sannan na kwashe kayan da suka Bata, Yana dawowa ya tafi dasu can, ya Dan Jima sannan ya dawo nikam Ina zaune Ina jiran naji an Kai karata Amma har muka gama cin abinci muka kwanta baice komai ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *