TSINTACCIYAR MAGE CHAPTER 4 BY AUFANA
Dasauri harda gudu suka kama hanyar zuwa gunsu saidai kash suna kaiwa dai dai wajen masu tsaron hanyoyi saisuka taresu suka hanamasu wucewa saboda dokace bawanda yake wucewa daga nan zuwa gun flyt sai waenda zasu shiga jirgin,,,….+
Cikin magiya nusy tafara masu magana “pleace dan Allah kuyi hak’uri kubarmu mushiga gun yayanmu zamuje plss” kallonsu yai d’ayan yace “ina card’s d’inku” kallon juna sukai nusy tace “kaga a uzurce muke wlh bamuda card’s plss kubarmu muje” bindiga suka fiddo cikin masifa suka nunasu sukace “idan bakubar nan ba zamu harbeku wlh kokuma mukaiku station d’inmu” badan sunsoba haka sukabar wajen suna kallonsu MUJAHID har suka shige jirgi suka d’aga suka bar wajen,,,….
Wani naushi nusy takaiwa iska tareda fad’in “ohhh…!!!shettt” munira kuwa ji take kamar tai kuka tsabar takaici Amira kuwa shuru kawai tai tajuya sukabar wajen,,”…..
Saida sukai ban kwana da juna cikin fara’a sannan yashiga jirgin shi da mubashir, saida jirginsu yad’aga sannan rayyan yawuce izuwa gidansa yana kewar amininsa,,,…..
Har jirginsu yabar k’asar UGANDA MUJAHID nakallon k’asa ji yake kamar yai tsuntsu yaje yad’akko MUFIDA sutafi atare saidai ina bahalin yin hakan,,”….
Acikin mota suna tafiya kowa yai shuu zuciyoyinsu cike da takaici da b’acin rai, koda suka isa gida tana kwance akan kujera tai shuu mubina na gefenta tana danne dannen system, suna shigowa ta tashi dasauri tana kallonsu, a yanayinda taga fuskokinsu dakuma irin yanayinda suka shigo dashi shine ya tabbatarmata da amsarda take nufin tambayarsu ma’ana ba’adaceba,,,….
Wani murmushi tai wanda yafi kuka zafi tace “baku gansaba ko bakugansaba dama nasan bazaku gansaba shikenan narasa mr man narasashi narasashi har abad….a” tafashe da matsanancin kuka maicike daban tausayi munira da nusy ma kukan sukeyi munira tazo tarungumeta tana rarrashinta, wani mugun kallo mubina kebinsu dashi can kawai tad’auki earpiece tasaka a kunnenta sannan tamik’e tsaye tana waka tawuce abunta,,,”…
Kallo kawai suka bita dashi basuce mata uffan ba, sunjima acikin wannan halin daga k’arshe nusy da Amira suka fita suka wuce munira taja MUBINA suka shige ciki, wanka sukai suka sauya kaya sannan munira tabama MUBINA maganinta tasha takwanta,,,,”….
Washe gari around 8am suka gama shiri tsab, zaune take akan gado tad’ora hanunta a kanta tai shuuu idanuwanta suna kallon sama, mubina ce tashigo rik’e da akwatinta a hanu tana yatsine fuska tace “hamma yace kufito muwuce gashican acikin mota yana jiranmu” tana gama fad’ar hakan tai gaba abunta itako munira ko k’ala batace da’ita ba MUFIDA kuwa dama talula a duniyar tinani, bayan munira tagama komai tai rolling da veal d’in rigarta saitazo ta dafa shoulder d’inta dak’arfi tadawo hayyacinta cikin murmushi munira tace “am sorry big aunt hamma yafito yana jiranmu” murmushi tai tashafa fuskarta sannan tasakko tasaka takalmanta taje gun mirror tai rolling na veal d’in rigarta kasancewar kaya iri d’aya suka saka ita da munira Arabian gown red color,,,,…..
Bayan tagama sannan tad’auki jakarta da phone nata da jakar takalmansu suka fita, suna fita saigasu Amira nan suka rungume juna sannan sukai bankwana suka rakasu har gun mota,saida suka shiga suka wuce sannan su Amira suka wuce kasancewar su sai gobe zasu wuce,, suna isa airport basu wani dad’eba jirginsu yad’aga izuwa gida Nigeria,,,….
*KEBBI CITY…..*
1pm dot jirgunsu yasauka a katafaren filin jirginnan mai suna AHMADU BELLO INTERNATIONAL AIRPORT BIRNIN KEBBI, KEBBI STATE, suna fitowa saiga bodyguard’s d’insu sun iso suka karb’i kayansu sannan suka wuce, wasu galla gallan motocine nahango bak’ak’e wulik sai shining, tinda suka sakko MUFIDA tafiddo glass d’inta no respect tasaka, suna isa aka bud’e masu murfin mota suka shiga ga jamian tsaro gabansu da bayansu,,….
STORY CONTINUES BELOW
Kai tsaye katafaren gidansu dake G.R.A birnin kebbi aka wuce dasu MUFIDA sai raba ido take tana kallon waje tana shak’ar daddad’an iska mai sanyi, suna isa gateman yabud’e gate aka danna hancin motocin aciki, suna tsayawa akai saurin zowa aka bud’e masu murfin suka fito sannan jamian tsaro sai take masu baya suke har suka isa k’ofar shiga babban parlor sannan suka koma sukuma suke wuce ciki,,,…..
Suna shiga cikin parlon saisukaga mutanen gidan ashe surprising nasune akeso ayi, dariya suka kwashe da’ita gaba d’aya dadyn su yazo yana fad’in “wlcm back my lovely daughters” tana murmushi taje cikin shagwab’a tashige jikin dadyn ta shima yana murmushi yarungumeta yana fad’in “ohhh my sweetheart i really miss u so much” tace “mee too my dad” momy ce tamatso tareda ammin su da yakumbon su da matar k’anen dady dakuma mahaifiyar hamma faruk da k’annensa sukazo sunamasu barka da dawowa,,,….
Wani irin takaici mubina taji yatirniketa yanda dady ke nunamasu bam banci a fili tsakaninsu batama jira komaiba tawuce ciki batareda ta damu da mutanendake cikin parlon ba, hakama momy dan kawai akwai mutane acikin parlon ne shiyasa takyalesu,, munira kuwa murmushi take sosai itama taje tashige jikin dady yahadasu ya rungume tareda sumbatarsu a goshi,,”…
Bayan angama masu barka da dawowa sannan suka wuce ciki domin su huta,,,”…
Wanka sukayi suka sauya kaya izuwa material Blue color, 2am dot kowa yahad’u lambu domin yin launched, girke girke ne akayi kala kala masu matuk’ar birgewa da dad’i ma’aikatan gidan sai hidima suke, bayan angama had’a komai sannan aka zauna akafara launched d’in,,,”….
Kowa sai faraa yake ana wasa da dariya ana raha da barkwanci amma banda mubina, MUFIDA nakusa da dady munira ma na gefensa hamma faruk na kusa da MUFIDA sai kallonta yake yana janta da fira itakuma ko kallonsa batayi hankalinta sam baya garesa, batareda angama launched d’in ba mubina tabar wajen momy nakallonta amma batace da’ita uffan ba har saida aka gama sannan tabi bayanta,, MUFIDA kuma bayan angama launched d’in MUJAHID yad’aukesu suka fita yawo, wani katafaren gun hutawa da shak’atawa dakuma holewa yakaisu mai suna PLUS CENTER sukaci kayan maku lashe sukayi kallon halittun daji sannan suka shak’ata,,,….
Zaune take a gefen gado zuciyarta sai zafi take mata saboda tsintsar b’acin rai, momy ce tashigo tazauna gefenta sannan takalleta tace “mubina nafad’amaki kidaina saka kanki acikin damuwa kada kijawa kanki wata matsala” d’ago da jajayen idanuwanta tai takalli momy tace “haba momy meyasa bazan damuba bayan kema dakanki kina ganin yanda dady ke nunamana bam banci a fili tamkar mu ba y’ay’ansa bane itakad’ai ce y’ar sa plss momy kifad’aman wai kodai dady bashine mahaifinmuba” dasauri momy tace “kiyi gaggawar fitarda wannan banzan tinani acikin zuciyarki vice shine ubanku shine yahaifeku kawaidai banzan raayinsa ne yasa yake nunamaku haka kuma ki kwantarda hankalinki insha Allah zai daina kinji ko” numfashi tasauke sannan tace “hmm momy kenan wannan matsalar batin yanzu muke fama da’ita ba a gidannan bana tinanin dady zai daina abunda yake saidai kisani wallahi bazan cigaba da jurar ganin haka ba dole ne nad’auki mataki saboda yanzu na mallaki h
ankalin kaina nasan zafin ciwo nasan dad’in lafiya” itadai momy kallonta kawai take saboda tasan maganarta gaskiya ce abunda dady yake sam baya kyautawa amma ba yanda zatayi tinda tayi iyayinta tin suna yara amma yak’i yadaina yanzu gashi sungirma sunfahimci komai,,,…..
Saida tad’an kwantar mata da hankali sannan tafita tabarta,, sai 6pm sannan su MUFIDA suka dawo agajiye, bayan sunyi wanka sukai sallah sannan suka kwanta munira tad’akko wani hausa novel *BARKIN’DO* tafara karantawa, MUFIDA kuma wayarta tad’akko takira Amira sukai waya sannan takira nusaiba,,,…..
Sunjima suna waya da nusy daga baya sukai sallama takashe sannan ta tashi tai sallar isha, bayan sunyi sallah sannan suka fita dining sukai dinner, batawani ci komaiba sai juya cokali take daga k’arshe ma tawuce bedroom takwanta,,,”….
Koda munira tashigo tana kwance tai shuu sai zubda kwallah take tana sheshekar kuka, zama tai kusa da’ita sannan tace “aunty MUFIDA kefa musulma ce yakamata kiyarda da k’addara soyayyarki ga MUJAHID *MUK’ADDARI* ce daga Allah idan kuma Allah yayi zaku sake had’uwa saikiga kun had’u watakil ma harda rabon aure a tsakaninku, nidai nakeso agareki shine dan Allah kicire damuwa a zuciyarki kada kisake fad’awa halinda kika shiga kwanan baya a school” wani irin murmushi tai wanda yafi kuka ciwo sannan tace “wallahi munira da inada yanda zanyi nacire mr man a zuciyata da nayi da akwai maganinda zaasha acire mutum acikin zuciya wallahi da ko nawa yake saina siyesa saboda nacire mr man a zuciyata, ahalin yanzu nikad’ai nasan irin azabarda nakesha a zuciyata saboda son mr man” hmm….!!! munira tasauke nannauyan numfashi sannan tace “zancigaba da tayaki da addu’ah Allah yasake had’aki dashi koda a aljannah ne” tai murmushi tace ameen, dahaka sukai shirin bacci suka kwanta,,,….
Washe gari bayan sunyi sallah taje dak’in dady tamasa barka da safiya sannan tawuce d’akin momy, kamar ko yaushe yanda momy ke mata da fuska hakama yau tamata tadai karb’a kawai ta tashi tafito, akowane lokaci MUFIDA na mamakin yanda momy kemata wani lokacin sai zuciyarta taita cemata kodai ba’itace mahaifiyarta ba saboda yanda take mata dik wanda yagani zaice ba’itace ta haifetaba amma idan ta tambayi dady saiyace wai dan tana y’ar farine shine take mata hakan saidai har yanzu zuciyarta bata yarda da hakan ba,,,….
Tana fitowa daga d’akin momy saiga mubina bata kulaba kawai taji tamata wata wawiyar bangaza harsaida takusa fad’uwa kuma tana d’agowa sorry kawai tacemata tawuce abunta, ji tai kamar tanarka mata dukan tsiya saikuma wata zuciyar tace shareta karkibiyemata ajiku k’anwar kice danhaka sai kawai tawuce takyaleta saidai batajin dad’in yanda mubina ke mata amatsayinta na yayarta tana kyaleta ne kawai saboda nasiharda dadyn ta kemata amma badan hakaba dasaita raina kanta,,,”….
Wanka sukai suka sauya kaya, 10am driver yad’aukesu izuwa ghesse pes 1 gidan mahaifan dady wato kakanninsu MUFIDA, suna isa bayan anyi parking suka fito suka wuce cikin gidan, dasauri munira tawuce dak’in hajiya Inde kakarsu tana fad’in “hajjaju mutan makka kina inane” daga cikin bedroom d’inta ta amsa “a,a kai maraba da y’an makaranta y’ar gidan hajiya andawo kenan” dasauri taje tafad’a jikinta suka rungume juna, hajiya tace “ina sarkin miskilai ko bada ita kukazo ba” munira ta kyalkyale da dariya tace “kai hajiya aunty MUFIDA gatanan shigowa” ah to nasan halinta shiyasa daga gun dady ba inda take zuwa aidai jefata zamuyi gidan miji muhuta ak’aratacan da miskilancin. Munira tai dariya saigasu sunshigo,,,….
Cikin fara’a ba kamar yanda tasabayi ba tazo tadurk’usa tace “hajiya barka da safiya” tsaye hajiya tai tana kallon ikon Allah tace “ikon jallah jaka cikin jaka yaukuma y’ar zamani da wannan salon kikazo kodai shi uban nakine yafara koyamaki tarbiyya yanzu” murmushi MUFIDA tai batareda tace komaiba ta tashi tawuce side d’in su hamma faruk,,,”…
Tana shiga taci karo da musty autansu ashe dama yananan gun aboki Ammar sa’ansane aikwa da gudu yazo yarungumeta yana fad’in “oyoyo oyoyo Aunty feedom” itama tana dariya tad’aukesa hamma faruk da Bilkis dake zaune parlor sunajin musty yace Aunty feedom suka fito atare bilkis tazo suka gaisa takalli hamma tagaidashi fuska a d’aure sannan suka wuce ciki ita da bilkis,,,”…..
Wunin ranar gaba d’aya a nan sukayisa faruk sai shi shigewa MUFIDA yake itako sam batason hakan saboda itafa bata tab’a jin sonsa a zuciyarta ba,, saida Abbu yadawo kakansu sannan takoma side d’in hajiya ita da bilkis saboda dama tafi shiri da Abbu akan hajiya ita hajiya saitaita mata fad’a da masifa tana cemata miskila shiyasa basa shiri amma Abbu saisu zauna suyita fira abunsu,, sai 7pm sannan driver yazo yamaidasu gida,,,….
A y’an kwanakinda sukai daga dady har momy sunfahimci MUFIDA komai nata ya sauya mashi chasa’in acikin d’ari na d’abi’unta sunsauya musamman girman kanta da miskilancinta yanzu saima wasu halaye data aro kamar son zaman kad’aici rashin son damuwa zama so silent rashin son rigima sannan kusan kowanne lokacin idan ka kalli fuskarta zakaganta a kumbure kamar wacca tai kuka idan dady ya tambayeta saitace bakomai ba abunda ke damunta,,,”….
Yau kimanin watansu d’aya da dawowa tana zaune acikin d’aki itakad’ai wayarta na a hanunta tana juyata kanta na kan pillow saiga musty yashigo da gudu yafad’a kanta takwabe fuska tace “ohhh Lil bro zaka karyani” ya kyalkyala da dariya sannan yatashi a zaune yace “Aunty dady ne yace nakiraki yana parlon sa” dady kuma. Yace eh “to shine kuma zaka karyani kan kafad’a man sak’on” yatashi yasauka k’asa yana dariya nan itama ta tashi suka fita atare…………Atare suka shiga parlon hanunta na rik’e dana musty sai tsalle yake, cikin sallama suka shiga dady na zaune akan kujera momy na gefensa tana yanka masa fruit’s yanasha,,,….+
Cikin fara’a yakarb’a yana murmushi taje tazauna kusa dashi musty yahau kan k’afafunta yazauna, cikin ladabi tace “dady musty yace kana kirana” yai murmushi yace “eh magana nakeson nayi dake mai muhimmanci” murmushi kawai batareda tasake cewa komaiba shima yacigaba da shan fruits d’insa, saida yagama sannan yagyara zamansa yana fuskantarta cikin murya mai taushi yakalleta yace “MUFIDA inaso ki fuskanci maganarda zan maki yanzu sannan kimata kyakkywar fahimta a duniya banida burinda yawuce naganki kina farinciki kina dariya sannan ba abunda nafiso kamar farincikinki” murmushi tai tad’ago tace “nasani dady nasan hakan tin ina y’ar k’ank’anuwata kuma abune wanda nasani saboda haka basaika fad’a ba” murmushin jin dad’i yai sannan yacigaba da magana,,,”….
“MUFIDA dan Allah inaso ki kwantarda hankalinki karki tada hankalinki akan abunda zan fad’amaki yanzu wallahi babu hanuna aciki aikin Abbu da Abban Ammar ne (mahaifinsu hamma faruk ) dakuma hajiya banso hakan ba amma dole ba yanda naiya kema kuma dan Allah ki daure kiyi biyayya kinji ko” kallon ban fahimci abunda kake nufiba takemasa tace “dady har yanzu ban fahimci abunda kake nufiba fa kasani acikin duhu” takaicine yacika momy kamar tai magana dan haushi k’aramar yarinya kamar MUFIDA kuma y’ar cikinsa zai tsaya yana shakkar fad’amata magana kamar wata uwarsa, wani d’an siririn tsakai tai mara sauti saidai batasan dady yajiba,,,….
Cigaba yai da fad’in “MUFIDA Abbu yahad’a aurenki da FARUK a yau akayi baikonku bayan kin kammala karatunki za’ayi bikin” dasauri tad’ago takalli dady tareda mik’ewa tsaye nantake kwallah suka cicciko mata tace “what…..!!! Dady meyasa za’amun haka meyasa baza’a tambayi raayina kan a yanke hukunciba haba haba yanzu anmun adalci kenan kanasi wallahi bantab’a jin son hamma faruk a zuciyata ba bana sonsa taya zan amince da aurensa, yanzu dady kanaji kana gani za’amun auren dole kodai kadaina sonane dady” tasowa yai cikin damuwa yarik’o hanunta yace “No no my dear wallahi bahaka bane banida hanu acikin wannan lamarin nima saida aka gama komai sannan aka sanardani kidaina cewa nadaina sonki” janye hanunta tai cikin kuka tabud’e baki zatai magana sai kuka yakwace mata tajuya da gudu tafita,,,”…..
I
tadai momy kallonsu kawai take batace uffan ba dan itama da’akwai abunda take ji a zuciyarta akan wannan abun da Abbu yakulla,,,….
D’akinsu tawuce tafad’a kan gado tana rera kuka mai raunana zuciyar mai karatu, acikin kukan take fad’in “wai meyasa duniya ta sauyaman ta juyaman baya komai nawa yanzu a jagule yake tafiya narasa mr man namijinda farko da zuciyata takamu da k’aunarsa bayan kuma itace ta tsanesa komai nawa ya sauya asanadin haduwata da mr man nakamu da masifaffen sonsa saikuma kwatsam yatafi yabarni batareda na’isarmasa da sak’on zucitaba yanzu kuma ga wannan matsalar auren dole nikam nashiga uku wallahi mutuwa zanyi dan bazan taba iya auren faruk ba kuma natabbata suma dan basusan asalin halin faruk ba shiyasa zasu had’ani dashi da dady na yasani bazai bari ahad’ani dashi b…..a” tasake fashewa da wani kukan,,,,……
Munira ce tashigo tazo tazauna kusa da’ita takai hanunta ta dafata cikin sassanyar murya tace “Aunty MUFIDA dan Allah kiyi hak’uri kidaina kuka ki rungumi k’addara dik abunda kikaga yafaru da bawa to acikin k’addararsa yake taki k’addarar ce haka na tabbata da dady yasan asalin halayyar hamma da bazai bari a aura maki shiba hamma faruk zalwajahaini ne” dasauri tad’ago cikin mamaki tace “munira kinanufin kema kinsan halinsa” tad’aga mata kai alamar eh tace “nasani aunty MUFIDA amma su dady basusaniba saidai natabbata dole wata rana zasu sani kisani wallahi dady bashida laifi shima jiya ne suka kirasa Abbu yafad’a masa kinsan yanda dady ke gudun fushin iyayensa shiyasa dole baimasu musuba yace Allah yasanya alkhairi, tin jiya yake tinanin yanda zai kiraki yafad’a maki amma yakasa” zafafan kwallah ke zuba daga idanuwanta a yanzu dikkanin siffar MUJAHID itace take mata gezau a idanu, murmushi tai wanda yafi kuka ciwo tace “Allah sarki mr man Allah yasake had’a fuskokinmu koda a aljannah ne” munira tace ameen, cigaba da kwantar mata da hankali munira tadingayi saidai dik yanda taso ta kwantarda hankalinta abun yaci tira sai kuka take zuciyarta takasa samun nutsuwa MUJAHID taketa gani a idanuwanta k’aunarsa kuma sai dad’a ruruwa take acikin zuciyarta,,,”….
STORY CONTINUES BELOW
Momy ce zaune acikin d’akinta tana danne dannen laptop saiga mubina tashigo da gudu tana kuka tazo tafad’a kan momy,, dasauri momy ta’ajiye laptop d’in tarik’ota tana tambayarta abunda ke faruwa,,,….
Cikin kuka tafara magana “momy wallahi saina kashe MUFIDA saina kashet…” dasauri tarufe mata baki cikin masifa tace “ke kinada hankali kuwa meta maki dazakizo kina wannan banzan zancen naki” d’agowa tai da jajayen idanuwanta tashare kwallah da majina sannan tace “momy wai anyiwa MUFIDA baiko da faruk d’ina meyasa zasuman haka momy meyasa kinsan wallahi faruk shine zab’ina shine wanda nakeda muradin aure shi nakeso momy kuma kinsani meyasa zaki bari amun haka momy, to wallahi bazan tab’a bari hakan tafaruba bazan bari ta aure shiba” janyota momy tai tarungume tana rarrashi cikin tsintsar tausayinta,,,”…
D’agowa tai takalli momy cikin kuka tace “wai meyasa akeman haka momy ita komai saita kwacaman takwace man dady ta kwace man tsohon saurayina Abdul na school d’inmu wanda nasoshi kamar nafadawa ubangiji yanzu kuma zatasake rabani da faruk bayan kuma ita kanta tasan shi nakeso kuma dady ma yasani to wallahi bazan bari ta auresa ba saidai komai zai faru yafaru” numfashi momy tasauke sannan tace “mubina ki kwantarda hankalinki sannan inaso ki kawarda tinaninda kike a zuciyarki MUFIDA y’ar uwarkice sannan komai kikaga yafaru *MUK’ADDARI NE* daga Allah” hakadai momy tacigaba da tausan zuciyar mubina badan itama taso hakan tafaruba,,,”….
Yau kimanin kwana uku kenan dayin baikon MUFIDA da faruk kusan kullum saiya kirata a waya amma bata d’auka daga k’arshe ma saita saka number d’insa black list,, kwance take akan gado dak’in momy saiga musty yashigo yai tsalle yahau gadon yana dariya, murmushi tamasa tace “my Lil bro yatake ne” yai dariya yace “hakan take my Aunt hamma faruk ne yazo momy tace nakiraki yana parlon bak’i” b’ata fuska tai tajuya kamar takwallah ihu dan bak’inciki da takaici ganin haka shikam yasauka yawuce abunsa yana tsalle,,,”…..
Zamanta tai tak’i fita saiga momy tashigo a fusace tace “ke bakiga na aiko mustapha ba yafad’a maki faruk yanajiran a parlor ba” tashi tai jiki ba kwari tawuce d’akinsu, tana shiga tabud’e wardrobe tad’akko k’aton hijab zindimeme har k’asa tasaka,,, hmm abunda bata tab’a yiba kenan dan tama manta rabonta da hijab k’ato zundimeme haka saidai k’arami shima dan sallah ne data gama zata cire saikuma wata sallar,,,….
Bayan tasaka sannan tasaka wasu plate shue tabar wayarta anan tafita, ahankali tabud’e k’ofar parlon fuskarta a tirnike babu walwala ko alamun murmushi bare dariya a tattare da’ita, murya k’asa k’asa tai sallama sannan tak’arasa tazauna nesa dashi takuma juya fuskarta tamaida hankalinta kan TV d’inda ke kunne yana aiki,,,”….
Dakyar kamar bata iyayin magana tamkar wacca bakinta ke ciwo tace masa “Barka da wuni” murmushi yai yakalle kyakkyawar fuskarta yace “barka dai k’anwata ya gida” lafiya kawai tabashi amsa, munira ce tashigo tareda hadiman gidan d’auke da abinci da abunsha kala kala, dikda dai shi ba bako bane amma yau bako yake a gidan tinda tad’i yazo saboda haka dole a karramasa,,,”….
Cikin fara’a munira tace “barka da zuwa yayana” shima cikin murmushi yace “barka dai munira a,a harda hidima haka dayawa to nagode sosai” tai murmushi tace ai bakomai sannan suka fita, juyowa yai gun MUFIDA wacca kanta yake duke tana kallon k’asa yakira sunanta “MUFIDA” batareda ta d’ago ba ta amsa masa sannan yace “MUFIDA yakamata kibani aron hankalinki anan saboda koba komai ni yayan ki ne kuma d’an uwanki yanzu kuma K’iris yarage nazama mijinki uban y’ay’anki” yana fad’ar haka tad’ago dasauri ta kallesa idanuwanta suka cicciko da kwallah bai damuba yacigaba “MUFIDA inaso kisani wallahi nadad’e ina dakon son ki azuciyata kuma kema kinsan hakan dan Allah ki daure kikarb’eni a matsayin mijinki domin muji dad’in gudanarda rayuwar aurenmu cikin farinciki da jin dad’i” sai yataso daga kujerarda yake yadawo dab da’ita, matsawa tai dasauri tana hararansa yayinda idanuwanta ke zubda kwallah,,,….
“please MUFIDA kidaure ki k’aunaceni wallahi ina sonki har cikin b’argo na” yakai hanunsa yarik’o nata, dasauri cikin masifa tamik’e tsaye tazaro dara daran idanuwanta tace “a da ina ganin girmanka amma tin lokacinda ka furtaman kalmar so na tsaneka kuma wallahi babu ranarda zuciyata zata so ka saboda tariga data kamu da son wani kuma kasani zaka aureni ka mori gangar jikina amma zuciyata da ruhina gaba d’aya suna ga wanda zuciyata tafara k’auna faruk banasonka bana sonka bana k’aunarka Allah wadaran da masu irin halayenka, hmm wato dankaga su Abbu da dady basusan mummunar halayyarda kakeyi ba shine ka lallab’o ka kitsa masu magana kamasu dad’in baki har suka amince to kasani komai daren dad’ewa akwai ranar tonon asiri akwai kuma ranar k’in dillanci ranarda hajjin mai gari ta b’ata, ranarne kuma zaka gane kurenka, faruk kak’ara sani kuma ka k’ara ji bana sonka bana k’aunark….” bata k’arasa ba yataso cikin zafin nama yawanka mata mari ya zazzaro idanuwansa yanunata da yatsa jikinsa na rawa kamar d’an dambe yace “idan kinacin k’asa ki kiyayi ta shuru karki sake kice zakiman rashin kunya wallahi yanzu sainai b’alla b’alla dake”,,,,…..
Wata iriyar dariya ta kyalkyale da’ita sannan tace “kasani wallahi ni nafi k’arfinka kuma idan kasake kasaki marina wallahi saika bambamce tsakanin aya da tsakuwa kuma nasake fad’a bana sonka kuma bazan tab’a sonkaba saboda wani wanda yafika yariga daya mallake zuciyata da ruhin….” bata k’arasa ba yajanyota ya manne da k’irjinsa yahard’e bakinsu gu d’aya yafara tsotsa tareda saka harshensa yana tsotse yawunta, takarfin tsiya yakaita kan kujera ya kwantar sannan yasaka hanunsa yakai kan bobss d’inta yafara matsasu da k’arfi, dadika k’arfinta ta yunk’ura ta tallafeshi tai jifa dashi k’asa sannan ta Mike tsaye tana mayarda numfashi,,,….
Cikin tsintsar masifa tawa
nka masa kyawawan marika har biyu sanna tanunasa da yatsa tace “Allah yafika mugu azzalumi hak’arka bazata tab’a cimma ruwa a kainaba” tana gama fad’ar haka tajuya tafita tabarshi zaune akan carpet,,,”….
Tin daga wannan ranar faruk baisake zuwaba koma yazo bazaiga MUFIDA ba dan bata fitowa a waya kuma tasaka number nasa black list,,,…..
A b’angarenta kuma kusan kowanne lokaci cikin kuka take da takaicin auren faruk dazatayi gakuma k’aunar MUJAHID dake dad’a k’aruwa acikin zuciyarta tarasa yazatayi da rayuwarta gashi ba Amira da nusy dake bata shawara munira yarinyace bakomai tasaniba mubina da momy kuma dama basune abokan shawarartaba dady ne dady kuma yanzu basuda zama kullum sai 8pm yake dawowa idan kuma yadawo agajiye yake yana buk’atar hutu, haka dai tacigaba da rayuwa cikin k’unci dikta rame tai bak’i batacin abincin kirki sai zaman kad’aici da tinani,,,….
Wata ranar assabar ne koda munira tashigo d’aki taganta tana aman jini kwance a k’asa, cikin tashin hankali taje da gudu tafad’awa dady da momy, a rikice dady yazo yana zuwa yaga halinda take ciki kawai yad’auketa yafita, yana fita yabud’e mota yasakata baijira driver yazoba bashida ko takalma yashiga momy ma tashiga yatada motar sai hospital,, wata k’asaitacciyar hospital yawuce da’ita mai suna EQUITY SPECIAL HOSPITAL, dazuwansa yai parking yafito yad’auketa yai cikin asibitin,,,”….
Kasamcewar vice governor kowa yasanshi danhaka nantake cikin gaggawa aka karb’eta akawuce I.C.U da’ita, tinda suka fita mubina tafito parlor takunna TV tai kwanciyarta munira kuwa carkey tad’akko tabi bayansu,,,….
Saida aka kwashe kusan 1hour akanta sannan aka samu tadawo normal nan sukamata injection na bacci suka doramata drip da jini, bayan likitan yagama sannan yakira dady office yamasa cikakken bayani akan matsalar MUFIDA, hankalinsa yamatuk’ar tashi dajin MUFIDA na d’auke da ciwon hawan jini hypotention, nandai doctor yamasa k’arin bayani akan irin kularda za’adinga mata dakuma medicines d’inda zata dinga amfani dasu,,”….
Saida takwashe sati d’aya ana kula da’ita a hospital sannan aka sallameta,, satinta biyu da dawowa suka koma school,,,….
Bak’aramin jin dad’in komawarsu school taiba saboda zatafi sakewa yanzu kuma zata rage yawan tinani da damuwa dakuma rage tinanin mr man musamman idan tana kallon inda sukai rigima saitaga kamar komai yadawo baya wani lokacin idan tana kallon gunda take parking motarta saitaga kamar MUJAHID fitowa zaiyi tai murmushi sannan tawuce,,,….
Haka rayuwa tacigaba da tafiyarmata cikin k’unci, ahalin yanzu komai na MUFIDA ya sauya gaba d’aya rayuwarta ta sauya kamar ba MUFIDA ba mai jin kai da jiji da kai dakuma masifa tadawo so so silent yanzu, daga class sai gun hutuwa saikuma gida yanzu ko yawo tadainayi, su kansu y’an school d’in abun yabasu mamaki sosai saidai ba halin yin magana dan har yanzu shakkarta suke……..Lokacinda su Amira sukaji anyiwa MUFIDA baiko saida sukai kuka musamman nusy saboda sunsan yanzukam MUFIDA tarasa MUJAHID har abada, tausayin rayuwarda zatayi a gidan mijinta ta rashin sonsa yasa suka zubda kwallah,,,”….+
Ahalin yanzu kam karatu suke gadam gadam saboda yanzu final year suke suna gab da k’arewa, hakan yasa yanzu MUFIDA tarage damuwa da yawan tinani sosai saboda kusan kowanne lokaci sunacikin karatu ga tilin lectures dake gabanki basuda hutu hakan kuma yasa tama manta dawani zancen faruk saidai MUJAHID danshi dik lokacinda take zaune itakad’ai zakaganta tai shuu tai tagumi tana tinaninsa dakuma irin rigimarda sukai a baya,,,….
***** *****
Kwanci tashi asarar mai rai yau saura wata d’aya kacal su MUFIDA su kammala degree d’insu danhaka yanzu kusan kullum suna school suna karatu,,,….
Kwance take a parlor munira na gefenta tana danne dannen waya mubina kuma na lambu tana hutawa, su Amira ne suka shigo ta tashi tana dariya suka gaisa sannan suka zauna, nusy takalleta tace “feedom tashi ki shirya yau zamudan motsa kafa muhuta tinda yau weekend ne kuma yaune kad’ai mukeda enouf time” murmushi tai tace “a,a yau dai kice abun ya motsa kenan” tafad’a tana mik’ewa tsaye,,,”….
Amira ce ta kalli munira tace “a,a munira ana nan ana wannan ibadar ta chart ba’ako ajiyewa ahuta adan yi karatu” dariya munira tai tace “aunty Amira ai ba chart ne nakeyiba wani novel ne nake karatu *BARRISTER ALEEYAH* wlh yayi sweet sosai lbr yana torching hert sosai kamar nai kuka nakeji”,,,…..
Dariya nusy tai tace “aikuwa bakida aikinyi indai ina kibiye ta novel to hawayenki zasu k’are” MUFIDA ce tafito sanye da wandon Jeans da t-shirt fara anmata zanen flower’s bak’i da fari kanta sanye da veal bak’i sai takalma hills masu belt bak’ak’e,,,….
Tana fitowa nusy tace “woww feedom kinga yanda kikayi kyau kuwa inama ace mr man yana kusa na tabbata dasai ya yaba da wannan kyau dakikayi” murmushi kawai tai batace komaiba suka tashi suka wuce, guraren hutawa da shak’atawa suka zaga can sai suka wuce gidan zoo, suna cikin kallon halittun daji sai MUFIDA tahango wasu masoya suna tafiya suna shan love daka gansu kasan masoyan junane,,,….
Kuruuu tai da ido tana kallonsu cikin tsintsar sha’awa a ranta tace inama ace itace da mr man d’inta kai ta tabbata dasaisunfi waennan birgewa, saida Amira ta dafata sannan tadawo hayyacinta suka wuce,,, sai kusan 5pm sannan suka koma gida,,”….
***** ***** *****
Alhmdllh yau takasance Monday kuma itace ranarda su MUFIDA suka fara zana jarabawa ta kammala degree d’insu, zaune suka acikin restaurant sunacin abinci suna firar yanda exam d’in tabasu kashi kamar basumata shirin kanta ba, basuwani jimaba suka tattara suka wuce gida,,,”…..
Ahankali suke cigaba da zana jarabawan saidaifa sunashan wuya saboda malam basa tausaya masu gashi kullum biyu sukeyi hakan yasa yanzu basuda zama basuda tsayi any time sunacikin karatu kuma cikin ikon Allah suna samun nasara,,, yau saura biyu kacal suk’are wacca kuma sai ranar Monday mai zuwa zasu zanasu,,,….
Yau takasance Saturday tana zaune waje agun shak’atawa mujallah na hanunta tana karantawa saiga mubina, batareda tace mata komaiba tamik’a mata waya tace “karb’i hamma ne yakeson yin magana dake” tai maganar tana kallon sama alamar jin kai, saida takai aya sannan tad’ago tawatsa mata wata muguwar harara sannan tace “nagayamaki ina buk’atar yin magana dashine dahar zakizo kiman tsaye a ka saboda tsabar kin rainani ko” shekeke ta kalleta sannan tace “Ah kajiman MUFIDA to ai banice nakirasa nace yayi magana dakeba shine yakira dakansa saboda koya kiraki bata shiga” to bazan karb’a ba kuma kitafi kibani waje tinkan na sab’a maki kamanni wallahi ko don kinga ina kyaleki dik irin iskancinda kikeman to ba tsoronki nakeba wallahi yanzinnan sai nai k’asa k’asa dake anan. Sanin halin MUFIDA batada mutunci yasa dole taja kafa tana kumbure kumburen baki tana guna gani had’e da watso mata harara tabar wajen,,….
STORY CONTINUES BELOW
Around 6pm MUFIDA tahad’a kayanta tawuce gidan Amira saboda tafi jin dad’in karatu a can,,…..
Ranar Monday tin 6am suka tashi sukai sallah sannan suka shiga kitchen suka had’a breakfast sannan suka fito, bayan sungama break suka d’an gyara gidan sannan sukafara shiri, MUFIDA tafara shiga wanka sannan Amira koda Amira tafito tini MUFIDA harta shirya cikin wata tsadaddiyar Arabian gown black color mai d’auke da flower pink asamanta, yaukam tai make up abunda takusa yin shekara batayiba d’an k’aramin bakinta tashafamasa jan baki pink sannan tashafa kwalli da powder kana tafeshe jikinta da tiraruka sannan tai rolling da veal na rigar bak’i,,,,”….
Nantake tsintsar kyanta ya bayyana dikda bawata make up neba tai amma kyanta ya bayyana sosai, Amira tadubeta tace “umm pretty kenan kinga yanda kika had’u kuwa wannan a
i sai k’asar larabawa za’asami wacca tafiki kyau amma ba k’asar Nigeria ba inama inama hmm inama ace mr man ne zai mallaki wannan kyakkyawar surar natabbata dasaiya dawwama yana godiya ga ubangiji daya mallaka masa ke” murmushi kawai tai tareda share y’an kwallanda suka zubomata tad’auki phone nata tafita,,,”….
Cikin sauri Amira tashirya tafito suka wuce, da har MUFIDA tace yau ita zatai driving saboda yau kusan shekararta d’aya da barin driving tin lokacinda ta fasawa MUJAHID taya yau kuma taso tai saboda murnar zasu kammala degree amma Amira natinamata da MUJAHID saitaji dik kasala ta saukarmata danhaka dole Amira tajasu,,,”….
koda suka isa tini nusy tajima da zuwa ganin yanayinda fuskar MUFIDA ke d’auke dashi yasa ta tsaidasu tace “yau ranarace ta farinciki agaremu saboda haka sam b’acin rai da damuwa basu kamata a gansu a fuskokinmuba pleace MUFIDA ki daure kisake fuskarki ko muma maji dad’in yin walwala” murmushi tai tace “karki damu nusaiba muje kawai” itama murmushi tai suka rik’a hanun juna suka wuce ciki,,,”….
4pm dot suka gama zana jarabawan k’arshe suka fito, farinciki agunsu MUFIDA ba’amagana itadasu Amira haka sukakoma tamkar k’ananun yara sai wasa suke suna shafawa fuskokinsu fent kowa yafito sai murna da farinciki suke suna selpie,, ranar sai 6pm sannan suka koma gida,,,”….
Bayan sati d’aya da kammala zana jarabawansu school d’in ta shiryamasu biki, kwana d’aya saura ayi bikin dady da hamma faruk da muk’araban dady sukazo aikuwa murna agun MUFIDA ba’amagana saidai a b’angare d’aya sam bataji dad’i ba da akazo da hamma faruk sadai inda tad’an ji dad’i shine a hotel zasu zauna saboda haka bazai dameta ba,,,”…
Washe gari around 10am aka fara gudanarda bikin, anjima sosai anasauraron jawabai daga bakin shuwagabannin school d’in dakuma manyan bak’i da sukazo ciki kuwa hadda dady, daga nan akayaba kwazo da k’ok’arin d’alibbai sannan aka bada kyautuka ga gwarazan dalibai wanda MUFIDA takarb’i kyauta biyu hakama su Amira sun karb’a, daganan kuma akabar dalibai sukacigaba da shagalinsu, sai 2pm sannan aka kammala komai akai hotuna akai musayar number sannan kowa ya watse,,….
Daren ranar MUFIDA taredasu Amira ta kwana kasancewar gobe zasu wuce saboda dady yanada meeting gobe, daren ranar kuwa basuwani yi baccin kirkiba saboda kwana sukai suna shan fira, sai kusan 2am sannan suka kwanta bacci,,,”….
Washe gari tin 5am suka tashi sukafara shiri, 9am suka kammala komai suka wuce izuwa hotel d’inda su dady suke, 9:30am suka wuce izuwa airport taredasu Amira da nusy, saida jirginsu yasakko zasu wuce sannan su Amira sukai bankwana da juna nusy da MUFIDA harda kwallah suke dakyar Amira tacire nusy ajikin MUFIDA suka wuce har jirginsu yad’aga MUFIDA nakallonsu saida tadaina hangosu sannan tarufe window tajuya tana share kwallah,,,”….
2pm dot jirginsu yasauka k’asar Nigeria a Abuja city daga nan suka sake shiga jirgi wanda zai kawosu KEBBI State,,, sai 4pm sannan suka iso kebbi suna isowa motocinsu sukazo suka d’aukesu izuwa gida,,”….
Koda suka iso gida kuwa momy tashiryamasu had’addiyar liyafa domin tarbansu dakuma tayasu murnar kammala karatunsu, bayan sunyi wanka sunsauya kaya sannan suka fito domin gudanarda liyafar, cikin tsintsar farinciki sukai liyafar kowa sai farinciki yake amma banda MUFIDA da mubina, batawani ci abincin dayaba ta tashi tawuce kallo kawai momy tabita dashi mubina kuwa wani mugun kallo tarakata dashi wanda batamasan ma munira da dady sunganta tanayi ba,,,”…..
Satinsu d’aya da dawowa dady yashiryamasu k’asaitacciyar walima ta murna da farinciki dakuma tayasu murnar kammala karatunsu wacca za’ayi ranar Thursday mai zuwa………..