ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 6 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE
Mun tsaya
Haana da Rauda sun zama abin tararaiya a‘cikin Zuri’arsu, kowa da irin so da Kaunar da yake ba su. Haka sukejin farin ciki na Kara kamasu, sam ba ma za ka gansu tare ba saboda daga wannan ya ja wancan, sai wannan ya janye wancan sai kuwa suka dinga jin dadi.
Abin da idanun Haana ya ke mata shi ne gizo, duk wani da namiji da yake cikin zuri’arsu sai ta ga ya na yi mata kama da Malam M.J, musamman Alh
Ja’afar, don ranar ma da ta ganshi sai taga kamar ‘ M.J dinta ta gani.
Da kanta ta yiwa kanta fada cikin zuciyarta na cewa. Mene ne za ta damu da shi bayan ma ya tafi ya barta cikin kewarsa, amma ya barta sai ganin kowa ta ke yi kamar shi. Da sauri ta cire wannan magination din da ya ke yawo cikin ranta ta fara fadin.
“Allah sarki Malam M.J na, yau ga shi na cika burina na ganin hadin kan Zuria’ata, na kuma hadu da su. Zamannan kuma da na yi da su sai nake jin kamar na Karasa sauran rayuwata da su. Nagode da addu’arka, kuma ladanka ya na nan wajen Allah na
niyyarka da son bani gudummawa, ina fatan Allah ya dawo min da kai cikin rayuwata na samu dukkan farin cikin rayuwata da nake nema”. Www.bankinhausanovels.com.ng
A zaune ya shigo ya sameta a falon gidan Alh Hamza, ya na ganinta ya saki wani murmushi mai Kayatarwa, sannan ya yi mata sallama, itama ta amsa cikin sakin fuska.
“Miss Haana kina lafiya?, sam haduwa ta yi mana wuya, ga shi kuma ina ta yi miki waya bakya dagawa. Kin ga kuwa yawan gidajen da naje nemanki ban sameki ba, wato kin ga ‘yan uwanki kin manta da ni shaf”’.
Murmushi ta yi itama sannan tace. “Ayya Mr.Sameer ya za’ayi na manta da kai, irin wannan tarin farin cikin da ka bani, ai ya shiga cikin kundin tarihin rayuwata. Ba zan taba mantawa da kai ba. Ka ba ni abubuwan farin ciki ma su yawa, dole ne
nima na saka maka da dukkan wani abu da zai sa ka farin ciki a rayuwarka, bayan kuma tarin ladan da ka samu a wajen Allah”.
Dadi ne ya kamashi mara misaltuwa, ta ke ya dinga jin wani nishadi ya na shigarsa. “Nagode da wannan matsayi da na samu a wajenki. Da fatan ba zan samu canjaba daga wannan matsayi?”.
Dariya ta yi sannan ita ma ta tambaye shi, “Canji kuma kamar ya ya?”. Ya bude baki zai mayar mata da amsa ne wayarta ta yi Kara alamar kira ya shigo. Da sauri ta rarumi wayar sannan ta dube shi tace masa.
“Minti guda Mr.Sameer, bari na daga na ji mai kirana don Allah, don ban gane lambar ba”. Shi kuwa soka hannuwansa ya yi a saman Kirjinsa ya zuba mata idanuwa ya na kallonta cike da murmushi a saman fuskarsa. Haka kawai ya ji komai idan ta yi birgeshi ta ke yi. Www.bankinhausanovels.com.ng
Tun kafin ma ya ce mata wani abu ta kara wayar a kunnenta. Ji ya yi ta kurma wani ihu mai hade da murna da doki. “Da gaske Ya Abba muryarka nake ji ka dawo gida jiya?”’.
Can daga can shima ya ce mata. “Eh tun jiya na dawo da daddare, na kuma kira wayarki ban samu ba, Ammi ta ce min kuna Kaduna”,
“Muna can Ya Abbana, amma na ji babu dadi da ka dawo ba ma nan. Amma ka jira yau din nan za ka gan mu insha Allah, ba zan iya jira ba, akwai labarai ma su dadin gaske, sai dai na zo kawai’. Cikin doki da zumudi suke wayar har ta ajiye.
“Mr.Sameer I can’t wait, Ya Abbana ya dawo, Yau dinnan za ka mayar da mu Kano, ko da kuwa Granny ba za ta tafi ba, ni kam zan tafi abina. Ba ri na kira Rauda na fada mata”.
Kafin ma yace wani abu har ta kira ta fada mata cewar su fara shiri ita dai yau za ta koma. Yadda ya ga doki da murnar sun yi yawa, sai kawai ya fara jin irin kishi ya na yawo a ranshi ji ya ke babu dadi cikin ransa. “Ya batun maganar mu to?, na ga kamar
– murnar da ki ke ba za ta barmu mu yi maganar mu ba yanzu’”. Murmushi ta yi tare da rausayar da kai ta ce. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Lokacin da zan ji dadin saurarenta ma kenan, amma ka bari idan mun hau mota sai mu yi abarmu”
‘ Dadi ne ya kama shi ya ce “To idan kuma Granny tana tare da mu ya ya zan iya fada miki?”.
Ta zaro idanuwa tare da cewa. “Au maganar babba ce kenan?, ba na jin ma za ta bimu, saboda_ naga ba ta shirya ma tafiya ba. Fatana dai Allah ya sa ta barmu mu tafin. Idan kuma da ita sai ka bari idan munje gida sai mu yi’Kar ki damu, ki je ki fada mata. Yadda ku ka yi sai ki fada min mu san yadda za’a yi, idan kuma ta hana sai mu yi maganar”.
Zaro idanuwa ta yi tare da harararsa tace “Hmm bari na barka Sameer kar ka yi mana baki za ka janyo a rusa min farin cikina”. Da sauri ta mike ta ba shi wajen.
Dariya shi ma ya bita da ita ya na tsokanarta, amma ba ta saurare shi ba. A tare suka fito daga gidan, Rauda tana ganinsu tare sai da ta ji babu dadi, amma haka ta hadiye damuwarta.
A tare suka shiga falon suka iske Kakannin na su zaune. A yadda suka gansu sai suka ji wani farin ciki ya kama su ganin kansu a hade suna tafe suna hira tamkar babu wani abu da ya taba faruwa a tsakanin Zuri’ar. Kallo daya za ka yiwa tsoffin nan kasan suna cikin jin dadi.
Sallama suka yi musu, cikin jin dadi Haana ta kalle su “Granny kun yi waya da Ya Abba?, yanzu muka gama waya da shi”.
Cikin sakin fuska ta kalleta ta ce “Ya kira ni bayan kun gama wayar da shi’’
“Granny amma ai yau za mu tafi ko?, don ba zan iya jinkirin ganinsa ba”. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Ga hanya nan, ban hanaku ba, amma ni kam na zo gida, kuma ba ni da niyyar komawa. Ku dai gaisar min da shi’. Nan kuwa Haana da sauri ta amsa da “‘Aha”’. Jikinta na rawa..
Nan Hajiya Babba ta ce “Wato Raihanatu kun ga ji da mu kenan?, har ku ke shirin guduwa’”’. Ta’ fada ta na mai dariya. Rauda kuwa ta kalleta ta ce.
*“‘Hajiya ba haka bane, da munje mun ganshi za mu dawo har sai randa muka koma makaranta sannan za mu dawo”’
“Shikenan Raihanatu kun yi mana AlkKawari dai ko?”’. Kafin ta ce wani abu kuwa sai suka ji sallama. Da sauri suka juya suna ma su amsawa.
Wata matsahiyar budurwa ce ajin farko mai kyau sosai. Kai da ka ganta kasan za’a yi girman kai a tare da ita. Da sauri taje ta rungume Haj Babba ta na wani yauki da narkewa a jikinta. Cikin kulawa Haj Babba ta ce.
“A’ah, su Haj Fadeelah ne mutanen Abuja, har kun Karaso kenan?”.
“Eh Haj, su Mommy za su zo next week. Ni na taho abuna ne don na yi kewarki da yawa ke da kishiyata”. Ta na nufin Haj Safiyya. Haj Babba ta ce “To ai ga daya kishiyar ta ki nan sai ku gaisa da Kannenki’’. _
“Granny ta ce, Fadeelah kece haka kin girma sosai?. Allah mai iko, ai kuwa ga shi nan kamar taki ba ta bace min ba”.
“Hajiya Umma na ji dadin ganinku wallahi, Allah ya Kara mana dankon zumunci, ya kuma kawar da sharrin shaidan. Mommy ta fada min komai, ta kuma ce na gaishe ki Www.bankinhausanovels.com.ng
“Ina amsawa ‘yar albarka”. Haj Babba ta amsa. Haj Rukayya ta ce
“Fadeelah ga Kannenki nan da ba ku san juna ba tun kuna yara, yaran kawunki ne
da gwaggwonki. Ku kuma ga yayarku nan ‘yar
gidan gwaggwonku ce Bara’atu. Ita ce babbar yayar iyayenku, don ita muka fara samu a cikin Zuri’a din mu”.Rauda da Haana suka dubeta cikin jin dadi suka ce “Masha Allahu”, su na ma su yi mata murmushi. Fadeelah ta baro jikin kakarta cikin
shagaba sai ka ce wata Mage don son jiki, sannan ta dube su cikin sakin fuska sannan ta miKa musu hannu suka gaisa tace
“Tam Fadeelah Zahraddeen”. Cikin murmushi Rauda ta karbi hannun sannan ta ce “Rauda Aliyu, nice to meet you Fadeelah ko kuma naa ce Yaya Fadeelah ”. Murmushi ita ma ta yi mata ta ce “Nagode Rauda”’.
Sannan ta mika hannunta ga Haana ta ce “Fadeelah”. Nan Haana ma ta yi murmushi tare da mika mata hannu ta ce.
“Raihanatu Mustapha Naseer, amma an fi kirana da Haana. Nima ina murmar haduwar mu, ina fatan Allah ya hada kanmu zumuncin mu ya fi na da”.
“Haana” Fadeelah ta maimaita sunan sannan ta tsare ta da idanuwa, har lokacin kuma suna rike da hannun juna, har sai da Haana ta tsargu da kallon da take mata”
Can ta yi KoKari sannan ta tabe baki sannan ta make kafada ta sake cewa “Ok to ya ya ki ke?”. ta sake fada amma yanzun ta sauya fuska. “Lafiya”. Ita ma ta fada a takaice. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Look Fadeelah! Ba na son fitinarki, ki barni na yi rayuwata kema ki yi taki. Na fada miki na riga da na yiwa kaina tanadin RUHINA Haana. Ba na son ki kawo min wata damuwa bayan wacce kuma nake ciki”. .
Kalaman da Fadeelah ta ji sun fado mata kenan a zuciyarta lokacin da take shirin barin London yadda suka yi da Ya Muhammad dinta. Haana kema a london ki ka yi karatu ne?”, tambayar da ta ji Fadeelah ta watso mata kenan, Girgiza mata kai ta yi sannan ta ce ‘A’a ba a can na yi ba, a Nijeriya na ke yi. Ina nan BUK ina karantar Law yanzu haka zan shiga level 4”. Wa ta irin ajiyar zuciya Fadeelah ta yi sannan ta ce Ba ke ba ce ashe. Wata nake zargi da na taba sani. Ashe kuma ba ke ba ce, don da na ji sunan naki sai na ji kamar na sanki”’Ayya ba ni ba ce gaskiya”.
“Na ga alama ai, to ya ya family dinku?”Kowa lafiya, ya ya naku?”Kalau”. Tana gama fadin haka sai kawai ta kwanta jikin kakarta ba ta sake bi ta kansu ba. Rauda kuwa da Haana suka kalli junansu sannan suka tabe baki tare da jan Kwafa. Granny ba ki ce komai ba kan batun tafiyar ta mu, mu fa shirin tafiya za mu yi yanzu”’.
Fadeelah ce ta kama hannun kakarta suka mike suka bar wajen, dai-dai lokacin kuma da wayar Haj RuKayya ta fara Kara kenan sai itama ta daga wayar ta ba su waje.
Nan suka naniKewa Granny su ma suna jiran su Ji me za ta ce da su. Ta kalle su sannan ta ce “Ku mu je dakina sai mu yi maganar’”’.
A zaunce su ke a dakin suna sauraren su ji me za ta ce da su kan tafiyar. Nan ta bude baki tace ““Ku shirya ku tafi, amma ni kam babu ni ba komawa. Ban samu na yi muku maganar yadda mu ka yi da Abbanku ba, shima tun jiya muka yi da shi yau zai dawo. Na fada masa ba ma gari muna Kaduna, ya jima ya na mamakin jin cewa ina Kaduna.
ina jinsa ya gama fadansa kamar shi neya’ haifeni, ban katse shi ba sai da ya sauke don kansa sannan na ce. Ya yi duk abin da zai yi. Yaransa kuma da na taho da su kuma gobe zan sa a dawo masa da su. Ni kuwa na dawo nan har sai ranar da ya gane ya daina fushin da ‘yan uwansa na dawo. Ban dora komai akan hakan ba na kashe wayar, har zuwa yanzu kuma ban Kara jin ya kira ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Dazu da na ga wayar Yayanku na zata ma shi ne, sai daga baya na fahimci ba shi bane don haka dama ko ku baku zo min da maganar ba zan saka Sameer ya mayar da ku ya dawo dai ya same ku a gida, don ya nuna min don me zan taho’ masa da ku”
Nan take Haana ta ji abin bai yi mata dadi ba, nan ta kalli Granny ta ce. “Haba Granny, bai kamata kema ki yi fushi ba, don Abba ya ce miki haka, ransa ne kawai ya ke a bace, kuma na tabbatar yanzu ya na cikin damuwa na kashe masa waya da ki ka yi haba ke kuwa Grannyna”’
Cikin alhini ita ma ta ce. “‘Rathanatu na fiki sanin Abbanku, mutuKar ban nuna masa nawa fushin ba, to kuwa ba zai taba sakkowa ba, saboda
tunda ya yi fishinnan bai taba sakkowa ba. Ni kaina ban so na yi masa haka ba, amma tunda kun gani kowa a gabanku ya saduda, to idan ban yi masa haka ba, babu wata rana da zai sakkowa a samu dai-daituwa.
Amma yanzu tinda ya san ban taba yin fishi da shi kamar haka ba, ina ganin zai sakko da kanshi”
Nan su biyun suka hadu suna kwantar mata da hankali da kuma ba ta hakuri kan don Allah kada ta sake kashewa Abbansu waya, idan ba haka ba sai ya shiga damuwar kuma da ta fi ta da. Daga Karshe dai suka tsayar da maganar tafiyarsu.
Duk iyayen na su ba su so tafiyar ta su ba, amma babu yadda suka iya, dole.suka yarda tunda sun ce musu za su dawo har sai hutun su na makarantar ya Kare saboda Karya suka yi don dai kar wani daga cikin iyayen ya hana tafiyar, sai suka bada wani uziri wanda za’a yarda da shi.
Jin kuma Umma ce ta fadi hakan, sai kowa ya yi amanna da tafiyar ta su. Gaba daya family din na su, yara da manya babu wanda ya ji dadin tafiyar ta su. Da za su tafi kuwa su Haana sai ‘suka dinga jin kamar za su rabu da wani farin cikin su ne mai girma cikin zuciyarsu. Haka suka taho da abin alkhairi mai tarin yawa.
Sun dauki hanyar komawa Kano, Haana ce a gaban mota Sameer ne ya ke Ja sai kuma Rauda da ta ke baya. Rauda ta kalli Sameer ta ce.
“Ya Samecr wai don Allah na tambayeka mana, wai dama cikin family dinmu akwai mai son
jiki irin na Fadeelah, ko kuma dai mu ta ke yiwa hakan?. Na ganta kamar ba ta da Human Relation da kuma manner”.
Haana ta karba, “Gaskiya ne Rauda, dama ni ma ina son yi masa wannan tambayar, har ga Allah na ji haushin yadda ta ke yi, don kaf cikin wanda na hadu da su cikin Zuri’armu, ita kadai ce ba na son Atitude na ta, ta na da wani hali da bana so, amma mun yi mata UZURI (Sunan littafina mai zuwa insha Allah) don ba mu gama gane halinta ba tukunna, but ni dai ba ta yi min ba”.
Dariya ya yi har da buga sitiyari ya ce. “Ku dai kam a gaida ku, ai yadda ku ka ga Fadeelah haka ta ke tuntuni da wannan danyan kan na ta da ta ke yiwa wanda ta ke ganin za ta yiwa. Da dama daga cikin ‘yan matan family kowa kuka ya ke da ita, wai don kada kowa ya yi mata shisshigi akan wanda ta ke so wato Muhammad dan wajen Daddy Ja’afar ne.
Kin san a can London ta yi karatu, to a gidansu ta taso. Kullum ita burinta a shirya ko don a dawo da auren zumunci. Banda haka ba na jin ta na yiwa wani namiji cikinmu wani abu banda matan. Ashe kuma ta nuna muku halin nata?”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Haana ta tabe baki ta ce. “Lallai ta na da aiki, wato ita burinta aure ne, ba wai a shirya don zumunci ba. Da ace babu wannan tunanin na son tayi auren zumuncin da ba za ta so a shirya ba”
Murmushi ya yi. “Ina ganin ba ita kadai ba ma, ni kaina ina son a shirya, don a dawo da batun
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG