TSINTACCIYAR MAGE CHAPTER 8 BY AUFANA
Dik wani lungu da sak’o na k’asar kebbi ba’inda ba’asaka matakan tsaro ba, hanyoyin shiga da fice filayen jirgi tashoshi dakuma hanyoyi ba’inda ba’asaka tsaroba ko’ina police ne da sojoji,, bincike ake sosai ko’ina da ko’ina ba kama hanun yaro domin kamo momy da mubina,,,,”….
+
Zaune suke suna firan irin k’ok’arinda Rayyan yai, acikin zuciyoyinsu kuwa farinciki ne fall yanzu abu d’aya suke jira shine kotu ta wanke MUFIDA daga zarginda ake mata koma ba’akamo su momy ba tinda dai antabbatar ba’itace ta aikataba to Alhmdllh,,,….
Cikin ikon Allah ana tsaka da bincike sai aka kira D.I.G daga office d’in masu tsaro na filin jirgin Ahmadu Bello International Airport wa’enda ake nema suna daya daga cikin basinjojin jirginda zai d’aga 2pm, nantake aka k’ara tsaro acikin filin jirgin lungu da sak’onsa,,,…
Cikin nasara kuwa Allah yasa akaga momy da mubina da mustapha zaune acikin office din d’aya daga cikin ma’aikatan wajen nan akamasu sannan aka daukesu aka wuce dasu izuwa court,,”….
3pm dot aka koma kotu akacigaba da gudanarda shari’a, bayan mai Shari’a ya’iso sai aka fito da momy da mubina aka kai musty gun momyn su faruk sukuma aka gurfanardasu agaban kotu sai rabon idanu suke dakagansu kaga marasa gaskiya,,,….
Bayan mai Shari’a yagama abunda yake saiya dago yadubesu sannan yacire glass d’in idonsa yafara magana “tabbas kwararan shaidu sun tabbatarda mubina kece kika kashe faruk saidai shaidu basu tabbatar da kece kika Nashe Alhj Ahmad ba amma dole kinada masaniya akan Wanda yakashesa saboda haka kotu na sauraronki daki fad’amata waya kashesa?” dube dube tafara nantake kwallah suka fara zubomata takalli momy wacca itama kwallan take sannan tafara magana “eh ni nice nakashe faruk amma banice nakashe dady ba momy ce” tana fad’a nantake motanen kotun kowa yace “SUBHANALLAH WA’IYAZUBILLAH” nanfa surutu yafara cika kotun saida mai shari’a yai magana “order order is ok” sannafa akai tsiitt,,,…..
Y’an rubuce rubuce mai Shari’a yai sannan yasake d’agowa yace “mubina meyasa kika kashe faruk meya maki akan wane daliline yasa kika kashesa?” Tsuru tai da idanu tana sai kwallah take zubarwa, ahankali tafara magana “Mahaifina shine silar canzawar halayyata wacca natashi bada itaba sakamakon nunamana fifiko dayake a tsakaninmu da wacca ba y’ar uwarmuba, tinda muka girma muka mallaki hankalin kanmu nafara sanin bambanci tsakanin farinciki da bak’inciki dad’i da d’aci fari da bak’i tin lokacin tsintsar tsanar MUFIDA tafara Shiga acikin zuciyata sakamakon fifiko da mahaifinmu ke nunawa a tsakaninmu da ita, tin muna yara dady yafison MUFIDA akanmu komai zai siyamana sai nata yafi namu kyau da tsada tin bama magana harmuka fara amma idan munyi sai mahaifiyarmu tace ai itace babba akanmu, a makaranta ma idan MUFIDA tai ta d’aya saiyamata kyauta amma ni idan nai bayamun, lokacinda mukaje university sainasamu wani saurayi Wanda nake matuk’ar so najima sosai atare dashi, kwatsam sainagansa da MUFIDA danamasa magana saiyamun tozarci ya wulak’antani a saboda ita, nahak’ura dashi nafara son yayanmu wato hamma faruk, nayi nisa sosai cikin soyayyarsa wacca takaiga harnakasa b’oyewa nafad’awa dady da momy sai dady yace najira harmugama karatu saboda so yake yahad’ani tareda MUFIDA da munira ya aurardamu atare, jin hakan yasa nakwantarda hankalina tinda shi dady yasanda zancen,, kwatsam wani lokaci munyi Hutu muna gida sainaji wai anyiwa MUFIDA baiko da hamma faruk, nayi kuka nayi kuka kamar raina zai fita lokacin ne nafara tinanin kashe faruk zuciyata take ingizani tinda narasasa to itama bazata auresaba” share kwallanda suka zubomata tai sannan tacigaba,,,….
Lokacinda natinkari momy da zancen lokacinne take fad’aman ai MUFIDA basu suka haifetaba, naji dadin hakan ba kad’anba sai momy tahanani d’aukan matakinda nai niyar d’auka tafad’aman tsarinda tai akan dady da MUFIDA, natsorata sosai saida tak’araman kyakkyawan bayani sannan hankalina ya kwanta na’amince da tsarin nata”,,,,….
STORY CONTINUES BELOW
Munjima sosai muna tsara yanda zamu kashe dady da faruk da MUFIDA, kwatsam munacikin wannan tsarin sai dady yake shaidamana yaraba dukiyarsa biyu yabama MUFIDA rabin to tindaga lokacin muka fara farautan rayukansu, Aranarda MUFIDA tazo gida sai mukai amfani da wannan damar bayan tafito daga d’akin dady momy tashiga yana a kwance kan kujera ta baya ta caka masa wuk’a a zuciya, saida ta tabbatar yamutu sannan tafito Wanda nikuma dai dai lokacin nariga nasami faruk a buge yanacikin halin maye nacaka masa wuk’a acik….I” kuka yacik’arfinta saita tsaya,,”….
Saida ta tsagaita sannan tacigaba “acikin tsarinmu hadda MUFIDA zamu kashe amma kasancewar tariga data gawar faruk shine tsarin ya sauya kada asirinmu ya tonu saikawai muka d’oramata kisan akanta, wannan shine abunda yafaru amma wallahi ahalin yanzu munyi nadama munyi ndamar abunda muka aikata muntuba dan Allah a yafemana wallahi sharrin shaid’an ne da binsan zuciya dakuma kwad’ayin abun duniya” acikin kuka take maganar”,,,….
Shuru yaratsa kotun sai sheshekar kukan MUFIDA da munira, mubina da Amira dakuma momy kakeji, su hajiya ma kukan suke amma baka jiyo nasu kukan,,,….
Tsawon mintina aka d’auka ahaka saida mai Shari’a yagama sannan yad’ago yafara magana “to Alhmdllh acigaba da sauraron k’ara da akayi dakuma kwarewa da gogewa had’eda jajircewar lauyoyi yasa muka samu kwararan hujjojinda suka taimakamana wajen kai k’arshen wannan shari’a, kotu tagama tattara hujjojinta kuma tayanke hukunci akan waenda suka aikata laifi wato Fatima da mubina, a saboda laifinda suka aikata kotu ta yankemasu hukunci daidai da laifinsu,,,, kotu tayankewa Fatima Alhassan da mubina Ahmad shitu hukuncin kisa ta hanyar rataya kamar yanda yazo a aya dakuma hadisi dik Wanda yakashe akashesa, sannan a k’ark’ashin kundin tsarin hukunci na Shari’a shima yace dik Wanda yakshe akashesa, wannan kotu kuma tana aikine da Qur’ani da hadisi dakuma kundin tsarin doka”,,,…..
Kotu tawanke MUFIDA Ahmad Shitu tass saboda ya tabbata ba’itace ta aikata laifinda ake zargintaba sannan kuma kotu namaibata hak’uri akan b’atamata suna da’akai kan cewa ta kashe mahaifinta da mijinta, da wannan ne kuma muka kawo k’arshen wannan shari’a sannan inaso nayi amfani da wannan damar wajen tinatarda al’umma”,,,,…..
Iyaye yakamata musan yanda zamu tarbiyyantarda y’ay’anmu idan d’a yawuce d’aya yakai biyu har yawuce to dole ne kasan yanda zaka nunamasu so dakuma k’auna karkace zaka nuna fifiko a tsakaninsu saboda zuciya batada k’ashi tabbas dole asamu zuciyarka tafi son daya daga cikin y’ay’anka to idan kasami hakan saikai amfani da tinaninka karka bari zuciya tafi k’arfinka,,,
Sannan mudingayin k’ok’ari wajen fin karfin zuciyoyinmu dakuma neman tsari akan shaid’an musani dukiya fa bakomai bace face turd’a abun shek’ewa iska ce ita kokamalleka watarana dole zaka barta wata dukiyarma bala’i ce ga mai ita saboda ko a gobe k’iyama sai talaka yariga mai kud’i shiga aljannah wani talakama saiyayi shekara d’ari uku kan mai kud’i yashigo saboda haka dan Allah
mudinga addua sannan mudinga kokari wajen fin karfin zuciyoyinmu Allah yak’ara tsaremana zuriyarmu yasa mufi karfin zuciyoyinmu yakuma karemu daga bin tafarkin shaid’an ameen,, Fatima Alhassan da Mubina Ahmad shitu sunada damar d’aukaka k’ara izuwa wata kotur daban nanda sati d’aya kan a zartanda hukunci akansu” yana gamawa yamik’e tsaye nankowa yamik’e tsaye,,,….
Tin kan mai shari’a bak’arasa fita ba Amira da munira sukazo da gudu suka rungume MUFIDA suna kukan farinciki nansuka durk’usa sukai sujudul shukru wato sujadar godiya ga ni’imar ubangiji, Rayyan ne yazo yanafad’in “Congratulation sister’s inatayaku murna sosai Allah kuma yak’ara tsare gaba” cikin farinciki Amira tace “Congratulation too Barrister Rayyan tabbas kacika cikakken lauya Wanda ya cancanci lambar yabo muna godiya sosai akan namijin kokarinda kai Allah I sakamaka da mafificin alkhairinsa” yai murmushi yace ameen,,,”…..
Kallonsa MUFIDA tai cikin tsintsar farinciki tana zubda kwallan farinciki tace “THANKS Barrister” yai murmushi yace “ur always wlcm MUFIDA” munira ma godiya tamasa sosai,,, momyn faruk da hajiya da Abbu da Abban ammar suma tasowa sukai sukazo gun MUFIDA kowannensu nazubda kwallah nan taje ta rungume hajiya tana kwallah kowa sai farinciki yake yau gaskiya ta bayyana su momy anji kunya sund’ora hanu a ka sai kuka suke rusawa police sunzo zasu wuce dasu gidan kaso kan lokacinda aka d’iba na zartarda hukunci yayi,,,”….
Atare suduka suka fito jami’an tsaro na bayansu suna fitowa kuwa yan jaridu sukayo Kansu da tambayoyi kowa da tasa kalar tambayar su Amira kuwa farinciki yacikasu harsunkasa amsa tambayoyin sai fara’a suke suna dariya, dakyar sojoji suka samu suka rakasu suka shiga motocinsu tareda escort d’insu suka wuce izuwa gidansu hajiyar dady saboda Abbu yace bazasu zauna sukad’ai acikin wannan k’aton gidanba,,”….
A canma koda suka isa cike yake taff da mutane nanma saida securitys sukai dagaske sannan akashigadasu cikin gidan, suna isa tashiga toilet tai wanka sannan tafito bayan tafito sannan tasaka kayanta tai sallar la’asar, bayan tagama sai baba mai aikin hajiya takawomata abinci, kad’an taci saboda cikinta batajin dad’insa kasancewar tajima batasakamasa abincin kirki acikinsaba,,,…..
Dakyar taiya cin rabinsa shima dan Amira tamatsane nan tasha ruwa sannan ta kwanta nantake bacci mai nauyi yai a won gaba daita, Amira tini nakira ummin ta tafad’amata nasararda suka samu sannan tafad’amata waenda suka aikata laifin, ummi tajinjina lamarin sosai daga bisani sukai sallama,,,”….
Tanacikin bacci saitai mafarkin dady ita da shi suna zaune suna fira wai sai kawai taga yatashi yana d’agamata hanu alamar bye bye yashige acikin wani haske mai haske sosai saikuma yai sama, dagudu taje tana kiransa yadawo yatafi da’ita tana fadin “dady dady dadyyyy” sai kawai tafarka dakarfi tana dube dube, Amira dakammala sallar magrib tana a gefenta takalleta tace “yanzu nakeda niyyar natasheki kiyi sallah nasan mafarkin dady ne kikai ko” hmmm….!!! tasauke numfashi mai nauyi tareda shafa fuskarta sannan tace “eh ko a prison ma sau biyu ina mafarkinsa kuma dik acikin fararan kaya daga karshe kuma sai munacikin fira saikawai yatashi yatafi yabarni ina kuka koda zan farka sainaga hawaye facha facha a fuskana”,,,,……
Hmm….!!! Amira ta sauke nannauyan numfashi sannan tace ” MUFIDA yanzu ba abunda dady yafi buk’ata agareki face addu’a itace abunda yake buk’ata agareku Allah yamasa rahama ya gafartamasa ya haskaka k’abarinsa” ta amsa da ameen sannan tamik’e tsaye tawuce toilet tad’auro alwala tafito,,,”…..
***** ****
Yau kimanin kwana biyu kenan da dawowar MUFIDA, xaune take akan gado tana rik’e da hoton dady a hanunta sai zubda kwallah take, munira ce tashigo ta taddata acikin yanayin, zama tai tareda dafa shoulder d’inta saita d’ago ta kalleta idanuwanta cike da kwallah, cikin muryar kuka tace “munira yanzu shikenan munrasa dady shikenan bazaya sake dawowaba har abada” saikuma tamaida kallonta kan hoton “Allah sarki dady na I really miss u, I hert u so so much my dad bansan izuwa wane lokacine hawayena zasu daina zubowaba tinda narasaka my dady, Allah yamaka rahama I hert u so much my dady” tak’arasa bakinta na rawa tana kuka,,,…..
Rungumeta munira tai itama tana kukan sannan tace “Aunty MUFIDA idan baki daina kukaba to mu yaza’ayi mudaina dady yatafi har abada saidai in mun cimmasa a can” ahankali munira ta d’ago tashare kwallanda suka zubomata tai murmushi tace “kinga nama manta Abbu ne yace nakiraki yana parlonsa” nansuka tashi sannan takai hoton ta’ajiye suka fita,,,”….
Cikin sallama suka isa kowa ya hallara acikin parlon harsu Abban ammar hajiya da Abbu suna daga gefe, k’arasawa sukai suka gaishedasu sannan suka zauna, Abbu ne yad’ago yafara magana “to Alhmdllh kowa ya’iso, bakomai yasa nataraku anaba saidan nasan gaskiyar zancenda nakeji akan MUFIDA” jin ya ambaci sunanta yasa tad’ago ta kallesa tace “Ni kuma Abbu menayi ne” kallonta yai sannan yajuya fuskarsa yacigaba “Fatima tace basune suka haifi MUFIDA ba bayan kuma bantab’asanin wasu iyaye waenda akace na MUFIDA bane saboda haka yau inabuk’atar sanin gaskiyar wannan lamarin”,,,….
Shuru yaratsa d’akin nawasu y’an dak’ik’u can Abban ammar yad’ago yafara magana…………..
, Shahida bata ankaraba kwatsam saiga ciki ya bayyana a jikinta, hankalinta yamatuk’ar tashi nantake taje tasami tajudeen tafad’amasa, shima hankalinsa yatashi sosai saboda dik y’ammatanda yake mu’amala dasu gwangwazajjin matane basa yarda su d’auki ciki amma ita wannan shine ya tirsasat dole badan halayyarta bane to yanzu yazaiyi da’ita, nantake dabara tafado masa saiyacemata kawai a zubda cikin daga baya saisuyi sure nanfa tace ita wallahi ita tinda tasab’awa Allah nafarko bazata sakeba bazata zubda cikinba saidai yasan yanda zaiyi saboda idan gidansu akasani wallahi tashiga tara mahaifinta ko kasheta zaiyi, hankalinsa yatashi sosai dan shid’inma tsoron nasa iyayen susani yake musamman dayakasance gidansu gidan mulki da sarauta ne sarki mahaifinsa sarki zai iya korarsa”,,,….
‘oyemata ba saboda yanzu Amira tawuce k’awa aminiya tazama y’aruwa agunta, Amira tayi mamaki sosai saidai ta jinjinawa dady matuk’a saboda abunda yai badik mutum ke iyayinsaba, nantake tafara shirin tafiyar itama,,,….
business d’ina dayake k’asar zannemesa namasa magana” daganan dai sukacigaba da tattaunawa harsuka yanke MUFIDA zata zauna anan BAGDAAZ izuwa wani dan lokaci saboda tasan y’an uwanta suma su santa,,,”….