TSINTACCIYAR MAGE CHAPTER 9 BY AUFANA

TSINTACCIYAR MAGE CHAPTER 9 BY AUFANA

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

Washe gari bayan sunyi sallah sukai break saitai wanka tasaka wata abaya mai kyau tai rolling da veal sannan tasaka takalma tazauna tanajiran Amira tashirya, bayan Amira tashirya itama cikin abaya, kallon MUFIDA amira tai tasha kunu sai MUFIDA tai murmushi tace “yadai Amira” batace da’ita uffanba saitaje gun mirror tad’akko kwalli da jan baki tazo tamik’amata tace “karb’a ki shafa” murmushi tai ba musu ta karb’a tashafa, woww Amira tafad’a sannan tace “kingakuwa yanda kikai kyau gaskiya yanzukam tinda kinhad’u da TOM d’inki dole kidinga tsantsara masa kwalliya yanagani” dariya tai tace “kai Amira nifa kinsan kwalliyarnan ba damuna taiba” tab aikuwa yanzu dole ta dameki dan dole arik’ayiwa yayanmu. Tak’arasa maganar cikin tsokana MUFIDA batasake cewa komaiba tai murmushi sannan suka saka takalmansu suka fita,,,…..+

Koda suka fito parlor momy da abban ammar suna zaune nansukamasu barka da safiya sannan suka wuce,,,…..

Kai tsaye fadar sarki sukawuce koda suka shiga kuwa yana kishingid’e yanakaratun wani littafe hisnul muslim nan suka durk’usa suka kwashi gaisuwa, yadubesu cikin fara’a ya amsa sannan suka fita, daganan suka wuce sashen tsohon sarki mai martaba suna isa suka taddasa da Abbu da gimbiya matarsa suna fira, cikin girmamawa suka durk’usa suka gaidasu sannan suka zauna suma akacigaba da firar dasu,,,”…..

Sunjima anan sannan mai martaba yasaka aka kira Nasmat sukazo saiyamasu magana cikin harshen larabci sannan yajuyo gunsu MUFIDA yace “zakubisu kuzaga gari sannan sukaiku gidajen sauran y’an uwa kisansu daganan kuwuce gidan mahaifinki saboda matansa susanki kinji ko yata” bayanda MUFIDA taiya dole badan tasoba ta amsa da to sannan suka tashi suka fita,,”….

Wunin ranar gaba d’aya su MUFIDA basu zauna ba koina da ko’ina saida sukaje daga k’arshe dai suka sauka a gidan mahaifinta, acan suka k’arasa wuni kuma Alhmdllh matan sun karb’eta sosai sai nan nan suke da’ita saboda MUFIDA tanada shiga rai sosai dik wanda yaganta nantake zaiji tashiga ransa gatakuma tanada kama da mahaifinta sosai, sai dare sannan suka baro can suka dawo gida,,”…..

Around 8pm tai wanka tasaka kayan baccinta saita saka katon hijab tafita, gun Abbu taje yana zaune acikin parlon mai martaba cikin sallama tashiga tagaidasa ya amsa sannan ta zauna, y’ar fira suka fara kasancewar dama MUFIDA da abbu suna shiri sosai, suna cikin fira saitace “yawwa Abbu dama inaso na tambayeka nifa gidannan nakasa gane kansa wallahi please kamun bayani yanda zan gane sosai” murmushi abbu yai sannan yatashi daga kishingid’enda yake yace,,,…

Wannan tsohon sarkin mai martaba kenan shine mahaifin sarki na yanzu wato Abdul samad sai tajudeen mahaifinki sai kanwarsu Sarah, Abdul-samad shine yahaifi Biryama wato MUJAHID sai k’anensa Ma’aruf wanda yake Cyprus yana karanta BIOCHEMISTRY sai k’annensa twin’s Nasma da Nasmat sukuma anan suke karatu a wata University dake Madina, sai tajudeen mahaifinki shi bayan ke baisake haihuwaba sai kanwarsu Sarah wacca takeda yaya shida to kinji yanzukam” murmushi tai sannan tasake cewa “to Abbu ya zumuntarku take da mai martaba naga kai Nigeria ne family naka suke kuma su sunajin hausa gasu kuma basa garinda ake hausa” murmushi Abbu yai sannan yace,,,….

Eh sunajin hausa amma basosaiba yanda zumuntarmu take da mai martaba shine mahaifiyata da mahaifiyar mai martaba uwarsu d’aya yagaji sarautane ta gefen mahaifinsa wanda dama su asalin y’an BAGDAAZ ne yanajin hausane saboda a Nigeria yagirma saida akabashi mulki sannan yadawo nan gabad’aya amma har aka haifi su tajudeen dik yanazuwa yanzune dai da tsufa yakamasa yadaina zuwa suma kuma yaran yanamasu hausa shiyasa suke d’an yi amma basosaiba” eh naga ai basuma iyataba sosai musamman su Nasmat inma sunayi kamar kai dariya wallahi. Nandai sukacigaba da shan firarsu har mai martaba yashigo sukacigaba da yi, sai kusan 10pm sannan MUFIDA taje ta kwanta,,,,…..

STORY CONTINUES BELOW

Washe gari tin basuyi wankaba su Nasmat sukazo dole sukai wanka da sauri sukai break sannan suka fita,,….

Wata wasace suke gudanarwa a dik irin waennan ranakun idan sunzo kusan al’adar masarautarce, koda suka fito gaba d’aya ko’ina na gidan ciki da wajensa ansakamasa flower’s da kyalli sai shining yake abun gwanin birgewa ga hadimai sai gyaran gidan suke, hannayensu sakad’e dana juna sukai can bayan gidan koda sukaje acanma gyara ake anzuba flower’s da color’s masu kyan gaske itatuwa suma ansakamasu kyalli, MUFIDA najuyawa bayanta tahango MUJAHID zaune a karkashin wata bishiya yana shan tufa sai kallonta yake yana murmushi, itama murmushin tai tabuya bayan Amira batareda Amira tasan abunda takenufiba,,,….

Jansu su Nasma sukayi sukaje can baya wurin wani lambu akamasu lalle ja a hanu sannan akayiwa su Nasma gyaran suma, saida aka gama masu sannan akafarawa MUFIDA kasancewar itace tace afaramasu kawai,, anacikin yimata saiga MUJAHID da Rayyan sunshigo,  dasauri tad’auki mayafi tarufe jikinta sannan suka gaisa da Rayyan nan yataimakawa MUJAHID yazauna sannan yajasu Amira da Nasma suka fita,,,”….

Shuru yaratsa wajen sai kukan tsintsaye kakejiyowa, dakyar tabud’e baki tace “am dan Allah mr man kai hak’uri da abunda yafaru abaya wallahi sharrin shaid’an ne da bin san zuciy…..a” bata k’arasaba yamatso dab da’ita tareda kai yatsansa kan lips d’inta yafurta “Shiiiiitttt…..!!! is OK komai yawuce” k’urawa juna ido sukayi suna kallon cikin idon junansu cikin tsintsar so da k’aunar junansu had’eda kewar junansu, itace tai saurin d’auke nata idon saboda wata iriyar kunyarsa dataji tana shigarta taredayin murmushi, shima murmushin yai yana kallon kyakkyawar surarta, hanunsa yakai ya yaye mayafinda tarufe jikinta dashi nantake saiga sumarta tazubo mata gwanin birgewa har gadan bayanta, dasauri tad’ago takai hanunta zata kamo mayafin tana d’ora hanun sai kan nasa nan sukaji wani shork yajasu dasauri yarufe idanuwansa saboda wani irin yanayi dayaji,,….

Ahankali yabud’e idanuwansa yazubawa sumarta yana kallo sannan yakai hanunsa ya yayemata wanda yazubo yarufemata fuskarta nan suka k’urawa juna ido, matsowa yai yakai bakinsa dai dai kunnenta yamata rad’a a kunne banji abunda yaceba sai kawai tafashe da dariya harsaida fararan hak’oranta suka bayyana wishiryanta ta bayyana d’an dimples d’inta yalotsa shima yai murmushi sannan yakai hanunsa ya tallafo hannayenta yana kallon lallenda akamata, binsa tai da kallo ganin yanda yake kallon lallen kamar baitaba ganin lalle ba,,,”…..

Ganindai abunsa yai yawa yasa tamike tsaye dasauri tana murmushi zata wuce da gudu yai saurin rik’o hanunta, mikewa yai tsaye yajanyota da k’arfi tafad’o kan k’irjinsa tareda jan numfashi,  duk’oda fuskarsa yai kamar yana shinshinarta yakai hanunsa yaye sumarda ta rufemata fuska, yanayin yanda hanunsa ke tab’a jikinta yasa saitakejin wani iri taja numfashi tareda rufe idanuwanta, duk’owa yai dai dai fuskarta kuma dai dai kunnenta ahankali tamkar wanda bayason yin magana cikin wani irin yanayi muryarsa cikin taushi yace “my Jerry will u marry me” wani murmushi tai wanda yalutsarda dimples d’inta batareda ta bayyanarda hak’oranta ba tad’ago fuskarta takafesa da sexy eye’s nata, shima kallon nata yake ganin irin kallonda takem
asa, bai ankaraba yaji tashafa masa lalle a hanci sannan tagudu tana kyalkyala dariya, shima dariyar yai yana bin bayanta da kallo harta b’acemasa,,….

Around 10am kowa yashirya yafito gunda za’agudanarda al’adar hadimai sai yawo suke suna bama mutane coffee da shayin y’an Arab’s, kowa da kowa yaiso har matan Abban MUFIDA tajudeen gimbiya Zainab ma tafito da tawagarta hakama gimbiya uwar gidan mai martaba, martaba da abbu da abban ammar dik sun fito sarki yaiso da fadawansa kowa dai yafito har anfara gudanarda al’adar,,….

  Cikin shiga mai kyau ta alfarma irinta y’ay’an masu mulki MUJAHID da Rayyan suka fito yanzukam ma shike tafiya dakansa bamai rikonsa saidai da sanda yake, yai matuk’ar yin kyau yafito asalinsa na balaraben asali, MUJAHID dogone fari tass mamallakin fuska mai tsayi mai d’an fad’i wacca take d’auke da manyan idanuwana masu black eye lashes da baki mai d’an girma kuma red ne, hancinsa mai d’an tsayine amma bakamar na MUFIDA ba dan ita nata haryakusa cimma bakinta, faffad’an k’irji ne dashi atak’aice dai kyakkyawane na asali,,,….

STORY CONTINUES BELOW

Cikin kasaita irinta yarima mai jiran gado yake tafiya harsuka k’arasa, sarki na ganinsa yai murmushi, kujerarda aka tanadar dominsa ya zauna Rayyan yazauna gefensa suka fara kallon wasan saidai shi sam hankalinsa baya gun wasan yanacan gun naman inda idanuwansa zasuyi tozali da abar k’aunarsa, yanacikin dube dube kuwa saiya hangosu suna tahowa su hud’u cikin shiga iri d’aya sunyi matuk’ar yin kyau musamman tauraruwar tasa saima yake ganin itakad’aice ke haske acikinsu, wani irin murmushi yai wanda yakasa fassarasa yak’uramata sexy eye’s nashi yana kallonta, har suka k’arasa suka zauna baidaina kallontaba harsataji ajikinta wani yana kallonta nantafara waige waige caraf tasauke iadnuwanta kansa yak’uramata ido yana kallonta, murmushi tai saita d’agamasa gira alamar yadai shikuma saiya kashe mata ido d’aya saita zaro idanuwanta tafirfito dasu waje tareda kai hanunta d’aya tarufe bakinta tana dariya, ganin yaki daina kallonta yasa ta tashi tasauya waje saita d’an lek’o taga yab’ata fuska alamar baiji dadi ba, dariya tai tacigaba da zamanta anan har akagama wasan,,,…..

Bayan amgama suka gudu rafinda ke cikin masarautar wanda yabi ta cikinta yawuce, wajen yanada dad’i sosai ga sanyi gakuma ruwa tsintsaye sai wasansu suke kanari mai dad’in sauti sai kuka yake wajen dai gwanin birgewa, takalmansu suka cire suka yaye rigarsu suka zauna suka saka kafafuwansu acikin ruwan suna fira, magana sukaji anyi a bayanzu saisuka waigo atare, MUJAHID ne da Rayyan sai wani kyakkyawan saurayi daganidai shima jinin sarautane, suna waigowa sai MUJAHID yanuna MUFIDA da yatsa yace “wannan itace” alamar dai yana nunawa abokin nasa MUFIDA ne,,,…..

Badan tasoba dole tace “barka da safiya” ya amsa mata “barka dai sarauniya ya hidima da jama’a” ta duk’arda kanta tace Alhmdllh nan suma su Amira suka gaidasa ya karb’a sannan suka wuce, jim kadan saigashi yadawo shik’adai yacewa su Nasma “Sisters kuje Ummi nanemanku” nan suka tashi tareda Amira suka wuce, har zasu wuce sai Nasmat tace “batawata ummi dake nemanmu kaidai soyayya kazo sha” tana fada suka kyalkyale da dariya sannan suka wuce,,,….

Itama mikewa tai tsaye takama hanyar wucewa saiyai saurin rik’o hanunta tareda fadin “haba my Jerry inakuma zakije ne bayan nazone muyi fira” k’in nuyowa tai tacigaba da tsayuwarta, sunanta yakira “MUFIDA” saita waigo nantake ta zaro daran daran idanuwanta ta firfito dasu waje tareda kai hanunta d’aya tarufe bakinta tana murmushi ganinsa durk’ushe a gabanta hanunsa rik’e da flower red tana d’auke da zobe mai shegen kyau, jin tai yace “my MUFIDA will u marry me please…!!! my only one answer me” rufe fuskanta tai tana dariya sannan tace “yes I will my heartbeat” wani irin murmushi yai yamike tsaye yakamo hanunta yasakamata zoben a yatsa sannan yai kissing d’insa yace “yanzu munyi engagement kenan zanje nasami Abi na ( means dady ) namasa magana azo asakamana rana ayi bikinmu” kallonsa tai tace “kacika zumud’i dawuri haka tin bamugama fahimtar junaba” hararanta yai sannan yace “eh naji ai dole nai zumud’i akan abunda nasha wahala akansa kan nasamesa kinsanfa hausawa sunce abari yahuce shike kawo rabon wani saboda haka gwanda nai sauri nafad’a karkuma wani yazo yakwaceman” murmushi tai tace “bama wanda zai kwacemaka rabonkane insha Allah” wani kallo yamata yace “Allah ko” tareda kashe mata ido d’aya tai dariya tareda juyawa tawuce,,,”…..

Ahankali shak’uwa ke kara shiga a tsakaninsu yayinda wutar k’aunar junansu ke kara ruruwa acikin zuciyoyinsu,, kimanin satinsu d’aya da zuwa su abban ammar suka gano asalin garin mahaifiyar MUFIDA Turkish nan suka shirya hadda su MUJAHID sukaje, lokacinda suka isa antaryesu da kyau jin daga masarautar BAGDAAZ suke bayan sunhuta sun gama gaisawa nan Abban ammar yafad’amsu abunda yakawosu, nantake aka kaisu gidan hajiya shahida, tinda suka isa MUFIDA taita kallonta MUJAHID kuwa yana ganinta yatabbata itace mahaifiyar MUFIDA dan dikda MUFIDA nada kama da Abba taju amma kamarta tafi yawa da mahaifiyarta,,,”….

Tarba ta musamman tamasu bayan sunsha ruwa suka gaisa sai abban ammar yafad’amata abunda yakawosu, dajin abunda abban ammar yafada nantake komai daya faru a baya yadawomata sabo a brain nata, kuka tafara tana zubda kwallah sannan tace “inatake yarinyata” abban ammar yanunamata MUFIDA saitaje gun MUFIDA tashafa fuskarta tana zubda kwallah itama MUFIDA tana kuka sannan tace “kiyafeman yata wallahi badan banasonkibane yasa na yadaki tsoron halinda zan shiga idan iyayena da dangina sukaji abunda na aikata shine yasa na barki amma badan banasonkiba har izuwa yanzu dikna tina dake saina zubda kwallah zuciyata taita mun kuna dan Allah kiyafeman” banda kuka ba abunda MUFIDA keyi takasa cewa uffan sai sheshekar kuka take,,,…..

Shuru yaratsa parlon nawasu y’an mintina can abban ammar yace “to Alhmdllh dama fatanmu shine tasanki kema kuma kisan tana raye kuma kisan inda take yanzu tinda kinganta shikenan” basuwani jimaba sosai ba suka tashi zasu wuce saita rok’esu dan Allah sujira mijinta yadawo yaganta kuma tanaso suje gidansu gun iyayenta suma suganta, basumata musuba kuwa suka zauna har mijinta yadawo k’annenta su uku suka dawo daga School dik suka ganta sannan suka wuce can gun kakaninta, jin abunda yafaru a baya yasa ran iyayen shahida ya baci sosai har saida suka zubda kwallah saida abban ammar dasu MUJAHID sukaita rarrashinsu suna basu hak’uri sannanfa sukace sun yafemata nansuka janyo MUFIDA ajikinsu,,,……

Sunjima sosai anan daga bisani suka barosu suka kamo hanyar BAGDAAZ,,,….

Bayan sundawo MUJAHID da Rayyan suka sami Abbu sukamasa zancen soyayyarsa da MUFIDA, abbu yaji dad’in maganar sosai saboda koba komai za’ak’ara jaddada zumunci gashi shikuma abbu ba abunda yafi so kamar zumunci danhaka nantake yai na’am da maganar kuma yace su kwantarda hankalinsu aure kamar anyi angama insha Allah, dad’i kamar yasan yanda yai da MUJAHID sai faman murmushi yake yana godiya ga abbu yana sinne kai k’asa,,,…..

A daren ranar bayan sunyi dinner shi da mai martaba saiyamasa zancen, shima mai martaba yaji dad’in abun sosai musamman dayaji cewar suna k’aunar junansu nantake yace ya amince Allah kuma i sanya alkhairi abbu yace amin cikin fara’a dajin dad’in zancensa,,,,…..

Cikin kankanen lokaci zancen yakarad’e gidan gabad’aya kuma Alhmdllh kowa yayi farinciki da abun sai mahaifiyar MUJAHID kad’aice batace komaiba kuma bata nuna farincikinta ba,,,….

Satinsu biyu da zuwa su abbu suka shirya suka koma gida Nigeria sukabar MUFIDA anan………….

Zaune take acikin bedroom d’insu tana shirin bacci, harta saka kayan baccinta saita tina tafa baro phone nata a parlor d’azu dasuka zauna acan suna kallo ita dasu Nasma, cikin sauri tasaka takalmanta batadako mayafi tafita,,,……+
Cikin sauri take tafiya saboda tsoron kar a d’aukemata waya tinda gidan mutane ne acikinsa ba adadi, bata ankaraba taji tai karo da mutum, sentsi yajata tai suluu zata fad’i tarintse idanuwanta cikin tsintsar firgice da tsoro, dasauri yakai hanunsa d’aya yarik’ota yajanyota tafad’o k’irjinsa han
unsa ‘daya kuma yakai yarik’o wayardake hanunsa dazata fad’i,,,…..
K’ura wa kyakkyawar surarta yai ido yana kallonta, sanye take acikin kayan bacci wando iya gwuiwa da riga mai k’aramin hanu itama iya gwuiwa kanta ba mayafi sumarta a tufke amma bada ribom ba tidin bobbs d’inta kusan rabi dik a waje suke kasancewar ba brez a jikinta rigarce kawai,, wani irin shauk’i yaji yaziyarcesa harsaida sandan girmansa ta motsa tamik’e a tsaye jin tidin bobbs d’inta manne a k’irjinsa gakuma gangar jikinsu tahad’u, dasauri yadawo hayyacinsa yatureta a kasalance jin an tureta yasa tabud’e idanuwanta dasukai ja saboda rintsesu datai dakuma fargaba da tsoronda taji,,,”…..
Ganin MUJAHID tsaye a gabanta yasa ta tabbata shine tai karo dashi, wani irin kallonda yai tsaye yana mata yasa tai saurin kallon jikinta taga kayanda take sanye dasu nantake wata iriyar kunya takamata tai murmushi tareda rufe fuskarta da tafukan hannayenta sannan tajuya da sauri zata wuce,, hanunsa yakai dasauri a kasalance yarik’o hanunta murya a disashe yacemata “ina zakije kuma” cikin jin kunya tace “zanje na kwanta ne” matsowa yai dab da’ita yanamata wani irin kallo yai murmushi sannan yace “to da inazakije ne kina tafiya bakiko kallon gabanki kuma zaki fita bako mayafi a jikinta kuma kinsan gidannan a kowanne lokaci akwai mutane a cikinsa” yanayin kallonda yake mata yasa kunya take kara mamayeta, d’an matsawa tai daga kusa dashi sannan tace “dama wayanace na manta a parlon Ummi shine zanje na d’akko” kallon cikin ido yamata danhaka dasauri tad’auke idanuwanta cikin jin kunya, kunu yasha sannan yace “to this is the last worning dazan baki karna sake ganin kin fito a haka koda kuwa parlon Ummin zakije kinji ko” d’agamasa kai tai alamar eh ganin yanda yasha murr kamar wanda baitaba dariya ba, hartajuya taza wuce yace “dakata” saita tsaya cakk yace “ga wayar a hanuna nina dauka dana ganta a can” yafada yana bata wayar takarba tareda fadin “thanks” tajuya tawuce abunta,,,….
Tsaye yai yak’uramata ido yana kallon bayanta yanda take tafiya cikin kunya dikda bamai jiki bace ita amma tanada hips sosai ga matasan zamanta dai dai jikinta gatakuma da gantsarwa irinta matan fulani k’irjinta kuma cike yake da dukiyar fulani, wani irin farinciki yaji yai murmushi tareda shafa kansa da hanunsa ‘daya hanunsa d’aya kuma yarike sandar girmansa dake kokarin bayyana kanta a waje saboda shauk’i, a zuciyarsa yace “kai my Jerry badai suraba kam harma tafi kyanta bayyana tabbas yanzune lokacinda zan rama abunda tamun a baya musamman marinda nafi komai jin zafinsa a matsayina na yarima” a fili kuma yace “tabbas ina k’aunarki MUFIDA k’aunarki acikin jinina take danke aka halicceni kuna insha Allah ni nakine har abada ke ‘daya” yanagama zancen yajuya yawuce,,,…..
Washe gari yana zaune a parlonsa Umminsa ta’aiko tana nemansa nan take cikin sauri ya ajiye abunda yake yabi bayan y’ar aiken kasancewar MUJAHID yanamatukar son mahaifiyarsa yana kuma gudun dik wani abu dazai batamata rai, cikin sallama yashiga parlonta tana a tsaye sai zarya take acikin parlon hadimanta kuma sai faman gyara parlon suke, cikin sallama yak’arasa yadurk’usa yakwashi gaisuwa sannan ya zaune a gabanta, zama tai fuskarta a tamke ta dubesa cikin harshen larabci tafara nasa magana “Biryama sam ban amince da had’in aurenku da wannan yarinyarba banasonta baita nakeso ka auraba kuma kasani y’ar y’ar’uwata asma’u nakeso ka aura saboda haka kai gaggawar cireta a ranka saboda ban amince ka auretaba inkuma har bakajin maganata to kaje kayi abunda kakeso amma kasani bazan tab’a sakawa aurenku albarkaba kuma nai fushi dakai har abada” a tsorace yad’ago da fuskarsa cikin tsintsar tashin hankali yakalleta sannan yace “haba Ummi meyasa zakice haka kinfasan banason asma’u ni MUFIDA nakeso itace wacca nadade ina mafarkin na aura itace wacca nakwashe shekara d’aya da wata bakwai ina jiran zuwanta itace wacca sanadin rashinta kusa dani nakwanta ciwon shekara d’aya da wata bakwai batareda naiya tafiya da k’afafuwana ba dan Allah Ummi na karki hanani auren MUFIDA wallahi banason asma….” bai k’arasaba tai saurin taresa da fadin “to idandai har bakason asma’u kuma bazaka auretaba to ka tabbatar dacewa ba ni ba kai har abada kuma babu hanuna acikin dikkannin lamarinka” tana gama fadar haka ta tashi rai a bace tafita,,….
STORY CONTINUES BELOW
Hankalinsa yamatuk’ar tashi saboda furucin mahaifiyarsa akansa sam bazai iya tab’a auren wata y’a mace inba MUFIDA ba saboda itace zuciyarsa ke k’auna yariga ya mallaka mata zuciyarsa da gangar jikinsa gaba ‘daya, haka yatashi jiki ba kwari yafita,,,….
              *****  *****
Kimanin satinsu Abbu ‘daya da tafiya mai martaba yashirya tafiya shima Nigeria tareda MUFIDA da sarki da MUJAHID da sauran tsofaffin fada, cikin sauri aka shirya tafiyar akai komai jibi around 10am jirginsu zai d’aya izuwa gida Nigeria,,….
Zaune take acikin lambu itakad’ai kasancewar su Nasma sunje school, wani littafene take karatu hausa novel RASHIN SANI na marubuciyar zamani Hauwa A usman, jin motsi a bayanta yasa tai saurin waigawa saitagansa shi da Rayyan suna tahowa izuwa gunta, cikin fara’a da tsintsar kunya tagyara zamanta, k’arasowa sukai tareda yimata sallama saita dago ta amsa taredayin murmushi, Rayyan ne yace “a,a amarya MUFIDA kenan sannu da hutawa” cikin murmushi tace “Barrister Rayyan barka da fitowa” yace “barka dai sarauniya ko nace gimbiya nanda shekara d’aya” dariya tai cikin jin kunya saboda ta fahimci inda zancensa ya dosa, gyaran murya yai sannan ya zauna tai murmushi sannan tace “barka da fitowa mr man” wani irin kallo yamata mai kama da harara sannan yace “ke malama bafanason wannan sunan kiyi gaggawar sauyasa ehi” murmushi tai tace “to wanne kakeso my Tom naga kaima Jerry kake kirana kumama bayan mr man wanne suna yadace dakai” hararanta yai sannan yace “zanyi maganinki tayanda zaki tina da sunanda yadace kidinga kirana dashi” daga ita har Rayyan kwashewa sukai da dariya Rayyan yace “wato dai har yanzu bazakudaina wannan rigimar takuba to yanzudai baruwanmu ehi ni da Amira tafiyanmu ma zamuyi amma fa sai bayan anyi bikinku” dariya sukai sannan sukacigaba da firarsu,,,”….
Rayyan baijimaba yatashi yawuce yabarsu anan, matsowa yai dab da’ita yaduko fuskarsa dai dai tata yacusa sexy eye’s nasa acikin nata yanamata wani salon kallon masoya, cikin murya mai taushi kamar wanda bayason yin magana yace “MUFIDA i really love u so so so so much plss MUFIDA karki sake gujemin kinji kiman alk’awarin bazaki sake rabuwa daniba har abada wallahi ina sonki ina matuk’ar k’aunarki ina maki sonda fatar baki bazata tab’a iya misaltashiba tabbas MUFIDA ke wani bangarece na jikina wanda inbabu shi to bazan tab’a cigaba da rayuwaba plss narok’ek’i ki furtaman kalmar so koda sau ‘daya ne please….!!!”  duk’arda kanta tai cikin yanayin kunya tana murmushi mara misaltuwa zuciyarta nacike da tsintsar farinciki,,,…
Shuru tai takasa cewa uffan sai wasa take da yatsunta amma daka ganta kasan cike take da farinciki, hannayensa yakai yarik’o nata yace “please…!!! My only one kifada naji” murmushi tai sannan tace “wallahi MUJAHID bansan waenni kalmomi ne zanyi amfani dasu ba wajen fadamaka kalmar so saboda gani nake dik waenda ake amfani dasu basuda tsada ammadai nasan sonka acikin jinina yake kuma inamaka sonda yafi karfin zuciyata da bakina wajen misaltashi, sonda nake maka shine wanda ba’aiya siya komai dukiyar mutum, sonda nake maka shine wanda yake saka mai k’arfi yasunkiya kamar kai yakuma sanya mara k’arfi zubda kwallah kamar ni shine wanda yakeda babbar fada wacca take acikin babban gida na mulki, tabbas masana ilimi sunyi gaskiya dasuka fassara so da wani marurune dake azabtarda zuciyoyin masoya kuma wata halittace da Allah ke halitta acikin zukatan mutane tabbas kuma sunyi gaskiya,  MUJAHID nakamu da sonka alokacinda bawani wanda nafi tsana a duniya kamar kai nakuma yimaka sonda ni kaina nayi mamakinsa, MUJAHID bantaba sanin zafin ciwo, k’uncun rayuwa da wahalar rayuwaba sai a sanadin sonka,  ina sonka MUJAHID ina matuk’ar k’aunarka inamaka so
mai cike da tsabta I LOVE U FOREVER AND EVER……AND EVER”,,,…
Wani irin farinciki ne yaji ya mamaye ko’ina na jikinsa yai murmushi cikin tsintsar farinciki so dakuma k’aunarta yajanyota yarungume tsam a jikinsa tareda zubda kwallan jin dad’i,,,….
A hankali ta zame jikinta daga nasa cikin murmushi tana fadin “a,a my mr man irin wannan rikon haka kamar zaakwace maka ni ai saika karyani” dariya yai yana share kwallanda suka zubomasa yakalleta sannan yakai hanunsa ‘daya yarik’o gementa yak’urawa fuskarta ido cikin fara’a yace “I LOVE U MORE THAN MY LIFE MUFIDA INA MATUK’AR K’AUNARKI” murmushi tai tace “Nima haka amma nawa sonda nake maka yafi wanda kakeman” hararanta yai yace “a,a sam banyardaba nawa yafi” tai dariya tareda mikewa tsaye tace “zanshiga ciki nagaji inaso na kwanta” binta kawai da yai dawani irin shu’umin kallo tai murmushi kawai tawuce,,,…..
              *****  *****
Yau itace ranarda zasu tafi gida Nigeria danhaka tin 5am bawanda yasake kwanciya sai shirye shirye suke, 8am dalla dallan motocin masarautar sukazo suka daukesu izuwa airport, sai 10am dot sannan jirginsu yadaga izuwa k’asar Nigeria k’asa mai tarin albarka,,”….
   *NIGERIA*
3pm dot jirginsu yasauka k’asar Nigeria suna sauka kuwa driver’s dasu Abbu da abban ammar sunanan suna jiransu nan suka taryesu cikin fara’a sukamasu barka da isowa lafiya sannan suka wuce suka shiga motocinsu,,….
Koda suka isa kuwa ko’ina da ko’ina angyara an tsabtace domin taryansu nan akawuce dasu masauki MUFIDA kuma tawuce can gidansu gidan dadynta, bayan sun huta sannan su momy suka shigo suka gaidasu suka masu barka da isowa lafiya nanfa akashiga hidima da bak’i ma’aikatan gidan sai faman aiki suke,,….
Aranarda suka zone MUFIDA tasami labarin su momy sun d’aukaka kara izuwa wata kotu y’an k’ungiyar human right tashigo tai kane kane tai ruwa tai tsaki harsaida aka d’aukaka k’arar izuwa wata Court, a can ne aka yankemasu hukuncin zaman gidan kaso na tsawon shekara bakwai da tarar kudi naira million shida, kuka iya kuka MUFIDA tayisa tana fadin “oohh duniya ina zaki damu son kudi son zuciya da son mulki yana nema yahallaka mutane anmaida kisa ba komaiba rayuwar mutum tamkar rayuwar kiyashi Allah sarki dady na hamma faruk ka yafeman nahanaka hak’k’inka kayafeman insha Allah zancigaba da sakaka acikin addua Allah i maka rahama dady na banida kamarka a duniya kamayeman gurbin uwa dakuma uba” haka taita magana tana kuka mai ban tausayi,,,…..
Kwanansu biyu da zuwa akai baikon MUFIDA DA MUJAHID dakuma sadaki naira dubu d’ari da tamanin had’e da jajayen rak’uma guda shida da dawakai guda hud’u sannan aka saka ranar bikin nanda karshen wannan watan dai dai y’an makaranta sunyi hutu kowa yana gida,, farinciki agun kowa baya misaltuwa musamman MUJAHID da abbu zumunta zata kara k’arfi, a ranar saboda farinciki saida MUJAHID yai sujudul shukru sannan yahad’a y’ar walima had’e da saukan Qur’an dik saboda murna da farinciki yayiwa Allah godiya…………Saikusan 9pm sannan tadawo gida tana dawowa kawai tawuce d’akinta tatufe, wanka tai sannan tai sallah tai shirin bacci tai kwanciyarta,,….+
Washe gari ma bata fitoba sai kusan 9am sannan tai wanka tashirya tafito, d’akin hajiya taje tamata barka da safiya sannan taje d’akin Abbu a can ta tadda mai martaba da sarki nanta durk’usa takwashi gaisuwa cikin tsintsar ladabi suka amsa mata tareda sakamata albarka sannan tafito,,….
Tana fitowa saitai kicib’is da MUJAHID zaishigo, dasauri taja da baya tai tsuru tana kallonsa, murmushi yasakarmata sannan yai tsaye ya rungume hannayensa yana kallonta, murmushi itama tasakarmasa sannan ta duk’arda kanta tace masa “barka da safiya mr man” cikin murmushi yace “barka dai amaryata fatan kintashi cikin lafiya” tace “Alhmdllh” gyara tsayuwarsa yai yakalleta yace “lafiya baki fito break ba d’azu kowa yafito kekad’aice” d’an sosa kanta tai kamar mara gaskiya sannan tace “umm….um bacci ne yad’aukeni wallahi bayan nagama sallah” yai murmushi,,,…..
Ammar ne da musty suka shigo da gudu cikin uniforms d’insu, dasauri musty yarik’e hanun MUJAHID yanafadin “yeee narigaka wallahi nine number one” tsaye ammar yai yakwabe fuskarsa kamar zaiyi kuka, dasauri MUJAHID yarik’o hanunsa yana fadin “a,a my Lil bro karkayi kuka mana kai namijine kazama jarumi kaima watarana kamatsa sosai kacinyesa kazama number one kajiko” murmushi ammar yai yace “dagaskiya brother me nima zan iya cinye musty nazama number one kullum fa musty shike na ‘daya a school a komaima shike na ‘daya”  yai maganar cikin yanayin kuka,  MUJAHID yai murmushi yace “sosai ma kuwa zaka iya amma saika daina kuka kadinga jajircewa sannan zaka iya zama nmbr one kaima kadaina kuka akan yacinyeka kaima kayi karatu kayi kokari kai na d’aya, yanzudai meya maidaku gida ba school kukajeba” musty ne yai saurin cewa “ammar ne yamanta littafensa na homework kuma auntyn mu duka take sosai shine muka dawo ya dauka” itadai MUFIDA kallonsu kawai take tana dariya, MUJAHID yace “ok oya to kuje ku d’akko kuwuce school kuma kuyi karatu sosai” suka ce “toh” sannan suka wuce da gudu,,,….
Mayarda dubansa yai gun MUFIDA datai tsaye tana kallonsu tana murmushi, shima murmushin yai saitacemasa “wannan rigimar tasu ta tinaman abunda yafaru abaya daga cikin labarina” murmushi kawai baice komaiba saita juya tawuce abunta tana share y’an kwallanda suka zubomata,,,…..
    Kimanin kwanansu MUJAHID biyar a k’asar Nigeria sannan suka tattara suka koma k’asar BAGDAAZ yana kewar abar k’aunarsa haka itama tana kewarsa sosai,,,…..
MUFIDA tacigaba da fita aikinta saidai batajin dad’in aikin yinsa kawai take gashi yanzu ayyuka sunmata yawa kusan kullum suna kan hanyar k’asashe daban daban domin kulla alak’a da wasu companonin daban hakan yasa yanzu batada lokacin kanta bare kuma nawani wani lokacin ma dole saita kashe wayarta saboda kar adameta da kira,,,….
              *****  *****
Rayuwa tacigaba da gudana cikin farinciki da walwala tini aka raba gadon Alhj Doctor Ahmad Shitu dukiyar MUFIDA kuma aka damk’amata abarta, a ranar wuni tai kuka saboda abun yatinamata da rayuwarta ta baya yanda dady ke nuna tsintsar kulawarsa a gareta yake bata gata da jindadi tamkar yarsa tacikinsa daya haifa, tai kuka sosai kamar ranta zai fita saida tagaji tabama kanta hak’uri,,,…..
Munira tadawo itama ta kammala degree d’inta MUFIDA tashiryamata walima had’addiya sannan tabata kyauta mai tsoka ta musamman, a ranar kuwa saida sukai kuka sosai saboda tinawa da mahaifinsu, tinda munira tadawo suka koma gidansu kasancewar akwai security’s kuma dik hadiman gidan sunanan donhaka suka koma acan,,,….
STORY CONTINUES BELOW
Anfara shirye shiryen biki a dika gidajen biyu nan gida Nigeria dakuma can BAGDAAZ, tini Amira ta’iso nan suka hadu sukafara shirye shiryen,, bak’i sunfara isowa na nesa dana kusa tini gida yafara cika da bak’i Aunty maryam taiso yayar hamma faruk itace ta d’auki nauyin dikwani gyara da zaayiwa amarya, akwatayya uku tacikowa MUFIDA da English were’s had’addu masu d’aukan hankali had’eda kayan bacci kala kala ita MUFIDA abunma kunya yakebata dan ko kallon kayan bataiba saida Amira tad’akko tabud’e sannan suka gani tanata dariya wai ita wallahi bazata iya saka waennan kayan ba Amira tace “hmm ganinku muke b’arayin barkono dakanki zaki kira kice asake kawomakisu idan akwai” dariya tai takaiwa Amira dukan wasa,,,…..
Yau kwana hud’u kacal yarage afara gudanarda bikin, mahaifiyar MUFIDA tazo tareda k’annen MUFIDA da mijinta da y’an uwanta guda bakwai maza da mata da yara y’ammata uku, hakan bak’aramin dad’i yayiwasu abbu ba nantake aka taryesu cikin fara’a aka kaisu masauki, ranarda sukazo takira MUFIDA a sirrance sukai magana sannan tadamk’ata kud’i naira dubu d’ari shida da wasu kayan mata na sha, godiya tamata sosai sannan takarbi kudin tawuce,,,”…..
Tini Aunty maryam tafara gyaran MUFIDA gya
ra nakwarai wankan dilka da kurkur,  wankan lalle, tiraren tsuguno, girki da ruwan bagaruwa,  tsalki da ruwan lalle da bagaruwa, romuwar kazar hausa da gundarin namanta, haka tasakata agaba tana gyaranta aikuwa cikin y’an kwanaki MUFIDA tamurje tak’ara kyau tsintsar kyanta yabayyana a fili kyakkyawar surarta tak’ara fitowa tai fari tass fatarta sai sentsi take tana shining tai laushi kamar ta jinjiri sabon haihuwa, ita kanta tasan tasauya jin kanta take kamar baita ba,,,….
Yau kwana ‘daya kacal yarage afara gudanarda shagalin danhaka aka d’aukesu akawuce dasu gun gyaran suma da lalle da gyaran jiki, saida akamasu lalle sannan akamasu saloon abun gwanin birgewa abunka da fararan fata saisuka zama tamkar larabawan asali,,,….
Yau itace ranarda zaafara event 1 wato kamu, around 3pm suna zaune a gidan aunty maryam na G.R.A wanda ke kusa da gidansu MUFIDA gidan dadynta saiga nusaiba kawarsu MUFIDA ta ukunsu driver yakawota nan, farinciki agunsu baamagana nanfa suka rungume juna cikin tsintsar kewar junansu, saida suka gaisa sannan suka shiga ciki akafara firar yaushe rabo,,….
4pm dot akafara gudanarda kamun anan gidan aunty maryam d’in, amarya tai kyau bakad’anba kamar ka d’auketa ka tsere tai kyau tamkar y’ar tsana tasha make-up kayanta white color material zane da riga dinkin yoruba anmata nad’i da d’an kwalinta, sai kusan 7pm sannan aka gama gudanarda kamun kowa ya watse,,,….
Washe gari su MUJAHID suka iso shi da abokanansa da Rayyan kasancewar anan ne za’ad’ura auren kuma washe gari ne, hakan yasa dole suzo a yau d’in,suna isowa suka had’e dasu Amira nanfa sukaita barkwanci abokanan ango da kawayen amarya abun gwanin birgewa, 10pm motocin su ango sukazo d’aukan amarya da kawayenta izuwa diner, a katafaren holl d’innan ROYAL za’agudanarda diner d’in, wata tsadaddiyar wedding gown ce amarya tasaka blue and white color shikuma angonta tsadaddiyar shadda ce yasaka gizna white color riga da wando da babbar riga wacca tasha aikin hanu blue color hakama hularsa blue and white color ce, sunyi kyau matuka amarya tasha make-up sukuma su Amira wani material ne suka saka suma blue and white color sunsha make-up, hakama su Rayyan shadda ce sukasaka white color tasha aiki blue color amma su ba manyan rigina Rayyan ne kadai yasakata, suna isowa aka budewa amarya da ango suka fito hanunsu a sakale dana juna MUJAHID saifaman wasan hakora yake yana dariya, Rayyan da amira ne suka shiga a gaba sannan sukuma sukabi bayansu sannan saran kawayen nasu da abokanan ango, atare suka shiga cikin holl d’in suna fara shiga nanfa akafara basu flasher ana d’aukan su hotuna abun gwanin birgewa, saida suka isa gunda aka tanadar domin ango da amarya suka zauna sannan sukuma sukaje suka zauna,,,….
Bayan anyi hotuna sannan aka yanka cake daganan akafara shagali, saida akabama amarya da ango fili sukad’an taka sannan k’awayen amarya da abokanan ango suka shigo sukafara liki suna taka rawa suma, daganan kuma kowa yadinga shigowa yana taka rawa yana liki, sai kusan 2am sannan aka gama diner d’in kowa yawatse,,”…
Saida suka sauke amarya da kawayenta gidan aunty maryam sannan sukuma suka wuce,,….
Washe garine za’adaura aure kuma za’ayi Arabian day saidai acan BAGDAAZ ne za’ayi arabian day d’in,,,, washe gari tin 8am suka shirya ita da kawayenta sukabi jirgin 10am sukawuce BAGDAAZ, 12pm dot dubban mutane suka shaida d’aurin auren MUJAHID ABDUL-SAMAD da MUFIDA AHMAD SHITU, d’aurin aurenda yasami halartar manyan mutane ciki kuwa hadda sarkin k’asar BAGDAAZ da manyan y’an boko da shahararru kasaitattun y’an kasuwa da shuwagabannin gomnati, bayan angama d’aurin auren MUJAHID yashirya walima hakama su abbu ana gama walimar su MUJAHID suka hau jirgi suka wuce BAGDAAZ,,,….
           *BAGDAAZ*
Wasu shahararrun matane MUJAHID yanema suka saka MUFIDA agaba da gyara tamkar ba’ataba mata wani gyaraba haka suka dinga gyaranta ita abun yabata mamaki sosai wai MUJAHID ne kuma yaturosu yace sugyaramasa amaryarsa tsab kai maza dai basuda kunya, bayan sungama ne sannan suka shiga yimata make-up na zuwa arabian day d’in, wata rigace suka sakamata gown ce pink color har k’asa da mayafinta sukamata rolling dashi sannan suka sakamata takalma hils silver color, bayan sungama saisuka kirasa suka shaidamasa sunkammala, saikusan 4pm sannan sukazo suka d’aukesu izuwa gunda za’ayi,,…
Wani katafaren holl ne na MUJAHID wanda yake ‘daya daga cikin abunda ya mallaka, angyarasa sosai yasha kwalliya da flower’s kala kala da bolom bolom kowa ya hallara amarya da angonta kawai ake jira danhaka suna isowa akafara gudanarda event d’in, dik wanda zaka gani acikin wajen to zaka gansa sanye da jallabiya mata kuma abaya jallabiya na mata kuma dikansu arab’s ne saisu Amira ne kad’ai ba arab’s ba,,,….
Yan nasihohi ne akai akan zaman aure daga bisani akai walima akaci akasha akai al’adun larabawa sannan aka rarraba y’an kayan walima 6pm kowa ya watse, daga nan kai tsaye gidan mahaifin MUFIDA wato tajudeen aka wuce da’ita da kawayenta, sunjima sosai acan saida tai wankan lalle tashirya tsab sannan aka kaita gun mahaifinta, nasihohi yamata masu ratsa zuciya da gangar jiki akan zaman aure da biyayya ga miji, banda kuka ba abunda MUFIDA keyi saboda tinawa da dadyn ta datai ranarda za’akaita gidan hamma faruk shima irin waennan nasihohin yamata,,,…..
Yajima sosai yana jan hankalinta daga bisani aka wuce da’ita masarauta, acan ma sakata sukai a gaba da nasihohi masu ratsa zuciya sai kuka take tana kara tinawa da dadynta a zuciyarta tanata masa adduoi,, 8pm dot motoci sukazo suka d’auki amarya da kawayenta da sauran mutane izuwa gidan mijinta Biryama MUJAHID……………

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *