UKU BALA’I CHAPTER 3

UKU BALA’I CHAPTER 3

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

Sosai yake kaiwa da komowa cikin dakinsa, hannayensa sarke a kirjinsa, lokaci-lokaci ya kan ja tsaki kamar harshensa zai tsine. duk sanyin da A-C din dake dakin take bayarwa hakan bai hana gumi samon mazauni saman goshin sa ba.

Sosai ya cigaba da zarya a dakin cikin rashin mafita akan abin da ya addabi zuciyarsa sosai yake jin zafi da raɗaɗi a zuciyarsa da ruhinsa sosai ya ji komai da ya faru dashi kwanakin baya sun hanashi sukuni ya naji a ransa bai taba ganin ‘ya mace da ta raina masa hankali ta ci masa mutunci kamar wannan kankanuwar ƴarinyar wanda ko a zaben mata aka saka ta ba in da zata kai labari kwaila ma irin ta wacce sam bata san Darajar da mace ke da ita a wannan duniyar rayuwar ba ta yanzu ba amma har ta dubi tsabar idon sa ta gaya masa haka.

“Noo Impossible”.

Abinda ya fadi kenan cikin daga murya mai sauti yana faman kai wa kirjinsa naushi kamar a nan mai laifin take.

Kamar wanda aka tsikara haka ya zari Key din Motarsa ya fara tafiya cikin sassarfa kamar zai tashi sama a haka har yafice daga cikin dakin sosai yake taka benen da zai kai shi zuwa kasa sashin babban falon cikin gidan kallo daya zaka yi fuskarsa ka fahimci halin da yake ciki na kunar rai sosai yake zakar wani abu a ransa wanda yake da tabbacin shi kadaine mafita gareshi dole ya dauki mataki dole ya dan hukuncin da zai dauka dole ya nuna mata tayi kadan ba kowan kowa bace a cikin jerin mata ba ta kai Level din da zata raina shi ba ba ta kai matakin ‘ya mace da zai kalla har ya yaba ta raina masa hankali ba da wannan sakar zucci har ya fice daga sashin cikin gida ya doshi Mota Parkig ya fara kokarin fiddo da motarsa komai yake yin sa a hanzarce haka ya figi motar mai gadi na ganinsa ya doso shi da sauri ya mike ya nufi Get din ya bude sosai yake kallon fuskar Huzaif yanayin da ya ganta sai da gabanda ya fadi sosai.

“Allah Yakyauta”.

Abin da ya fadi kenan yana margaya kai ya mai da Get ya rufe bayan Huzaif ya fice.

Sosai yake gudu kan titi zuciyarsa na faman wassafo masa abubuwa ma bambanta sosai yake jin komai na zuwa masa a bazata wanda ya hakikance ba wanda ya assasa hakan sai wacce kwailar yarinƴar wacce ko kyautarta aka bashi ba abin da za tayi masa a rayuwarsa illah wahala.

Cikin mintin nan da ba su haura talatin ba ya isa Kofar Asbitin baban alis sosai yake kallon asibitin bayan yayi parking ya fito yana mai wasa da Key din motartashi gaban motar ya usa ya yi tsalle ya hau gabanta ya zauna gami da harɗe hannayensa duk biyu a kirji ya kure kofar asibitin da kallo yana tunanin abin yi domin shi dai zuciyarsa ce ta kawo sa amma bai san takamaiman abin da zai gudanar ba abubuwa biyu suke masa sukuwa da tunanin sa haushin Mariya da kuma son ganinta wanda duk ya ajje a hurumi daya wanda sam ba su da alaƙa da juna numfasawa yayi gami da zaro wayarsa daga aljihu yana shuga dandannawa kamar mai kokarin kira kamar wanda ya ga takaici sai kuma ya ja tsaki gami da maida wayar aljihunsa yana faman sakin numfashi.

*****

“na rasa me zan yi komai ya kwance mani”.

Abinda ta fadi kenan tana tura laɓɓanta cikin bakinta tana faman ya mutsa fuska kamar wacce aka sanya shan magani.

Sosai yake kallonta da yanayin da take ciki na yanayin rashin kwanciyar hankali komai ya bayyana a fuskarsa na tsananin damuwa har zurmawa tayi kamar wacce ta tashi daga gudawa.

“na rasa ta ina zan miki bayani ki fahimta, na rasa mai zance miki wanda zai ganar dake komai da komai kin kasa daukar abin da nake fada miki, ya zan yi dake Mariya?”.

gyaɗa kai kawai take yi tana faman dauke kwallar da taji suna kawo mata farmaki.

“Hakuri Dr.Aqeel. bani da komai da zai taimaka min domin samun natsuwa ta ka tuna yau kwanansa Biyar ban gan sa ba, yau kwanan sa biyar ban san a wani hali yake ba, dole dole ne na damu sosai da sosai zuciyata taki hakuri taki natsuwa”.

Ta karashe cikin karfin hali kamar mai som fashewa da kuka kai ta cigaba da gyaɗawa.

“ban san abin da yasa yaki jin magana ta ba, ban san abin da yasa bai yi amfani da abin da nace ba komai da komai Dr.Karami yace zai amma yaki yarda da hakan”.

Ya fadi yana kallon Mariya wacce gabadaya hankalin ta na wajan Habeeba wacce take sharar barcin ta hankali kwance kamar bata da wata matsala a duniyarta mai da kai tayi wajan Mu’azzam wanda shi barci yake yi. sosai take jin tausayin sa na damunta a rai sosai take tausayawa rayuwarsa.

Mikewa tayi ba tare da ta dubi Dr.Aqeel ba ta fara tafiya sannu hankali sai ka rantse rashin jini ne ke damunta.

“Uhmm nace ba”.

Ya fadi yana mai kallonta cak! tsaya ba tare da ta juyo ba.

“ina zaki kuma?”.

“waje zan fita”.

ta bashi amsa tare da kara saurin tafiyarta don ba ta so ta sake furta ko da kalma daya ne gareshi

So take ta je waje ko za ta samu sa’ida a zuciyara ba wai ta yarda dari bisa dari bane a,a kawai dai zaman dakin ne ya fara gunduranta dalilin Dr.Aqeel ba ta son a daidai wannan lokacin ace maganar wani na ratsa mata kunnuwa tana bukatar natsuwa ko yaya ne amma ta lura Dr.Aqeel ba zai bata wannan damar ba sam! Ba ta san me yake nufi da ita ba ta rasa ina zata sa kanka ko yaya ne ta samu hutun rai da ruhi.

“MACE ƘYANƘYAWA”.

Sautin muryaar da taji ne ya sanya ta katse tunanin da ta afka sosai gabanta taji ya bugu har sai da ta sanya hannu ta dafe tana ambaton ‘innalillahi wa’inna ilaihir raji’un’

Sosai ta fiddo da idanuwanta waje tana mai sauke so akan sa sosai taji komai yana kwance mata cikin kwakwalwarta.

Gabadaya idanuwansu suka sarƙe sosai suke ƙallon junansu an rasa mai dauke kallonsa daga dan’uwansa fuskar Huzaif ba abin da take saki sai murmushi sabanin ta Mariya da take a cungune waje daya kamar wacce aka aikowa da mutuwar wani cikin dangi

A hankali ya fara kokarin saukowa daga kan motar shi yana faman sakin murmushi wanda daka gan shi kasan akwai alamun tambaya akan sa.

Sosai yake tunkaro ta gabanta na sake tsananta faduwa komai take ji na kanta na wargaje mata ba abin da zuciyarta keyi sai ɗaci sosai.

Ba ta son ganinsa, bata muradin ganinsa cikin duniyar rayuwarta, ylta tsani shi a zuciyarta tun daga kalaman sa take jin wani irin ɗaci tun daga kasar ruhinta a dalilinsa sai dai wani bangare na zuciyarta sam yaki kin yarda da Huzaif domin kullum cikin tono mata sunan yake.

“Yaa Allah!”.

Ta fadi tana mai haɗe laɓɓanta waje tana cusa su cikin bakinta a hankali take daura hakoranta akai tana dannawa kanta a kasa tana jin saukar numfashin Huzaif kusa da ita hakan yakara tsinka mata zuciya ji take kamar ta kurma ihu don haushi.

“wai ke mai yasa kullum in za a ganki, sai an ganki tare da kunci ne?”.

Ya fadi yana kallonta sosai yana kallon yanayin Emotion dinta da ya sauya lokaci guda yana kallon yarda fuskarta ke wanzar da haushi da ƙi kuma ya tabbata akan sa ne Murmushi ya saki ganin tana kokarin barin wajan ya kai hannu ya riko mata nata hannu.

Ai ji tayi kamar an daura mata garwashin wuta a hannun nata nan da nan jikinta ya dau wani irin Shock har sai da komai ya motsa a jikinta da sauri ta dago kanta sosai take kallon Huzaif da rinannun idanuwanta ji take kamar ta tsinke shi da mari don takaci da bakin ciki bakin tane ya fara motsi alamun son magana laɓɓanta dake cikin bakinta har wannan lokaci ta shiga motsa su.

“Don Allah ka rabu dani!”.

Ta fadi cikin murya mai sauti da karamar tsawa a cikinta tana mai dauke kallonta daga gareshi bayan ta watsa masa wani mugun kallo.

Sosai yake mamakin yar mitsilar yarinyar nan, da yarda take yin komai nata cikin rashin tsoro ko fargabar abin da zai je ya dawo ya lura akwai tsoro a zuciyarta sai dai bata barinsa yayi tasiri a zahirinta ba.

A hankali ya saki hannunta da ya rike gami da jan guntun tsaki mara sauti amma hakan bai hana Mariya ji ba ko kallonsa ba tayi ba amma ta lura yaji haushin abin da tayi masa gyaɗa kai tayi ta fara hanzarin barin wajan amma maganarsa ce ta sanya ta saurin tsayawa.

“mai yasa baki son mai sonki da alheri, na lura wani naki ne bashi da lafiya amma kin ki bani damar da zan samu ikon duba shi, ko da yake ban san abin da kike tunani akai na ba ni dai ban dauke ki na ajje a zuciyata ba akan wani mugun nufi sai dai na ajje ki a zuciya a dalilin tausayinki da jin kai”.

Sosai maganganunsa suka shiga shigarta ta ko ina sosai take jin sautinsu na haifar mata da wasu lamura a kasar zuciyarta sosai take jin tasirinsu a kasar ruhinta sosai zuciyarta ta fara kokarin gasgatawa tunaninta ya karbi lamarin a saukake sosai take ajje numfashi a duk wani kalma daya da ya furta a hankali ta fara kokarin kallonsa idanuwanta a dan tsuke bata bari tasirin maganganunsa sun fito zahiri ba ta fara motsa laɓɓanta.

“bana tsammanin zan yarda waki bugun ya sake gintawa a tsakaninmu kasan ance dukan farko shine duka kuma ka lalata damar ka tun a karo na farko don haka ina mai rokan ka ka fice mani daga rayuwa bana so komai ya faru tsakanina da kai kaji ko kawai ka kama gabanka kowa yayi rayuwarsa ba abin da ya hada kifi da kaska balle kuma har su da zauna inuwa daya”.

yanayin yarda ta ajje furucinta cikin halin-ko-in-kula yayi matukar kara zafin zuciya gareshi sosai yake kallonta yana jin rashin wayon da ya nuna akanta har ya tsaya yar yarinyar nan na fada masa abin da ta so a ranta tsaki yaja sam bai lura ta wuce ba sai da ya fara motsa baki yana son yin magana sannan ya lura bata wajan naushi ya kai sa iska gami da cizon Laɓɓa sosai ya ke kallon kofar aasibitin domin ya hango shigarta sosai zuciyarsa take shiga kunci a hankali yana mamakin yarda akayi yake wahalar da kansa akan wannan halintar wanda ko a farkinsa ban yi zaton zai ganta har ta samu damar shiga rayuwarsa ba dole ya san abin yi dole ya dau mataki akanta domin tsana yake hangowa tasa a idanunta ya tabbata ta tsanshi haushi sa take ji a ranta har a bayyane a fuskarta.

“l’m Huzaif!”.

Ya fadi yana nuna kansa da dan yatsansa yana mai sakin murmushi gami da gyaɗa kai ya juya ya koma motarsa da gudu ya fuzge ta ya bar harabar asibitin.

*****

Sosai Dr.Karami yake aikinsa cikin kwanciyar hankali da kware a harkar cikin kwanaki talatin da biyar komai ya fara kamo hanyar samun waraka ga Habeeba ba wai Mariya kadai ba hanta su Dr.Aqeel sunyi matukar yin farinciki da hakan domin sosai suke ganin komai na zama Normal izuwa wannan lokaci Habeeba ta fara samu sauki sosai don yanzu duk na fizge fizge da rashin magana ya kau sai da lokaci-lokaci in kana hira da ita tana kau ce hanya cikin hirar zaka ji tana wani zance na daban wanda bashi kuke yi ba hakan ya so damunsu Mariya sai dai Dr.Karami yana kwantar musu da hankali gami da sanar da su dole hakan sai ta faru gareta a hankali komai zai daidaita kamar bata tabayin cutar ba.

Kamar ko yaushe yau mariya ce zaune ita da Dr.Karami suna hira domin shakuwa ce ta shiga tsakaninsu sosai da sosai Mariya tana matukar girmamashi gami da kunyarsa hakan yasanya Dr.Karami yake jinta a ransa sosai take burgeshi komai nata yanayi masa musamman da ya lura tana da hankali gami da natsuwa sosi a rayuwarta gata da gamun kai.

Dr.Karami ya numfasa bayan ya gama wayar da yake yi ya dubi Mariya da take ta faman wasa da Mu’azzam dake hannunta shikuma yana faman ƙyalkyala dariya.

Murmushi yayi yana gyaɗa kai kafin ya motsa laɓɓansa.

“Na lura sosai da sosai ki ke son Mu’azzam, anya za ki iya rabu dashi kuwa in wani abu ya taso na zuwa wani waje”.

Kasa tayi da kai alamun jin kunya sosai ya kureta da ido.

“kin fiye kunya Mariya anya kuwa”.

ya sake fadi yana dariya.

A hankali ta dago kanta ta kalle shi sannan ta ajje kallonta gefe.

“Uhmm Dan’uwana sosai nake son sa ban son rabu dashi ko na sakanne”.

“kenan yanzu ko lokacin aurenki yayi ba zaki iya rabu dashi ba a matsayin ki na ‘ya mace yar gidan wani”.

Ji tayi kamar ta tsune kasa don kunya dalilin aure da ya ambata gabadaya sai ta rikece sai motsu motsu take yi ta rasa abin yi gabadaya.

“wai shin ina zancen makarantarki ya kwana ya kamata ace kin koma makaranta Mariya zaman haka ba zai haifar miki da ɗa mai ido ba ke ‘ya mace ce sosai karatu ke da muhimmanci a rayuwarki ya kamata ace kin mai da hankali sosai zuwa ga karatun ki ita ce dama daya jal da kike da ita ko don taimakawa iyayenki wata rana kece babba ko da dai ke yar gidan wani ne amma duk da hakan kiyi karatu”.

Sosai kalamansa suke samun masauki a zuciyarta sosai take jin dadin yanayin furucinsa cikin sanyin murya mai cike da karfafawa zata so ace hakan ta kasance gareta zata so ace ta samu wannan damar za ta so ace tayi karatu na sosai da sosai domin ta lura karatu a rayuwar zamanin nan yana da muhimmanci sosai musamman ‘ya mace ko ba don komai wasu abubuwan na rayuwa da suke gudana a duniyar nan ya kamata ace mata suna samun wannan damar domin wasu fannonin ‘YA’YA MATA ya kamata ace a wajan ba maza ba musamman harkar likitanci ko ba komai taimako ne na al’umma ku hakan zai wuce takaicin da wasu ke yi wa mara hali a rayuwarsu.

Sosai take jin tausayin kanta da na iyayenta da kaninta Mu’azzam ta sani ƙaddara ta fado rayuwarsu gami da talauci da ya hana su gudanar da wasu abubuwa sosai da ya kamata ace sunayin sa ba wai rayuwar jindadin duniya take nufi ba a,a wasu abubuwan a rayuwar dangin rai dole yayi a karan kansa ba wai sai ya tsaya wani yayi masa ba musamman duniyar zamanin nan a yanzu in baka dashi ba mai yi da kai balle ya ya jikanka ta sani a duniyar nan in baka dashi kai da banza duk daya ne ta gani an aikaice akan ta anyi mata.

Hawayen da suka zubo mata ne ta sanya hannu ta dauke su sosai take gyaɗa kai ta na son yin magana amma ji tayi wani abu mai nauyi ya saukar mata a kirhi sosai take jin komai na rashin dadi na wanzuwa a gareta sosai take tuno rayuwar da tayi a makaranta da irin yarda ake korota dalilin rashin kuɗi sosai take tuno yarda ake mata gori a makaranta kowa ya gujeta ba ta da kawa ko daya domin ta fita zakka a cikin yaran makaranta kullum cikin rashin babu take ba ta ga watan da zai ya kare ba a ƙore ta ba ta ranar da zata zo har ta fadi ba a tuhume ta da rashin babu ba akan wani abun bukata a makaranta.

Kasa tayi da kai sosai take jin kuncin rayuwar da take yi sosai take hango ƙaddarar da take da wainiya da rayuwarta ita da ahalinta.

“Mariya!”.

Sautin muryar Dr.Karami ta sauka cikin kunnuwanta wanda gabadaya ta mance ma da wanzuwan sa a wajan a dan razane ta dago da koɗaɗɗun idanuwanta ta sauke akan sa.

“karki ce da ni ba ki son karatu, karki ce dani maganar da nayi miki ne ta sanya ki kuka”.

Kai ta shiga girgizawa sosai hawaye da sauka a kuncinta a hankali tashiga motsa laɓɓanta.

“ko daya ba ruwanka komai naka gaskiya ne mai kyau ne sai dai…”.

Shiru tayi gami da yin kasa da kai sosai ya kafe da ido don ya gama fahimtar inda ta dosa da batun nata amma nauyi ya hanata fadi tausayinta sosai yake ji komai nata na rayuwa yake tausayawa.

“Karki damu Mariya nayi miki Alkawari…”.

“Dr.Karami”.

Sautin Muryar Dr.Aqeel ne ta katse masa maganarsa tsaye yake ya harɗe hannu a kirjisa fuskarsa kadaran kadahan gabadaya ke kallonsu sosai yake son fahimtar abin da zuciyarsa take sanar dashi sosai yake kallon yarda Mariya take kuka wanda sam bai da sauti sai na hawaye sosai ya fara jin wani iri a kasar ruhinsa da zuciya zargin Dr.Karami yake da shiga rayuwar Mariya ya kunsa mata wani abun wanda yasanya shiga damuwa sosai.

“na lura cikin yan kwanakin nan wani lamari ne yake tsakaninka da Mariya, in dai har za ku zauna tare bana taba ganinta ta tashi da dadin rai”.

gabadayan su suka dubi Dr.Aqeel wanda shi kansa sai da ya tsargu sosai akan maganar da yayi duk sai yayi wani zuru zuru dashi yana faman yake.

Dr.Karami yayi murmushi domin ya rasa ina zai ajje zancen Dr.Aqeel bai fahimci in da ya saka gaba ba gabadaya tunaninsa ya tsaya akan zarginsa yake yi kenan da kuntata rayuwar Mariya? girgiza kai yayi kafin ya fara duban Mariya sannan ya dubi Dr.Aqeel.

“ce maka tayi ina takura mata hala?”.

Sosai Dr.Aqeel yake nuna nadamarsa akan abin da yace ya san tabbas maganar da yayi ba ta da hurumin da za a ajjeta sosai ya shiga girgiza kai yana faman ajje yake kamar wanda aka baiea kyautar bazawara.

“Noo ba haka nake nufi ba”.

Sosai su duka biyun suka kureshi da ita musamman Dr.Karami da ya fara hasaso wani abu da zuciyarsa ke sanar dashi amma yaki yarda da hakan mikewa yayi a hankali yana mai duban Mariya.

“ni zan tafi sai gobe kuma ki kula da kan ki sosai”.

Gyaɗa kai kawai tayi alamun amsawa sai dai har ga Allah bata so tafiyarsa ba har a ranta tana jin dadin zama dashi amma ta lura Dr.Aqeel yana yi mata kanzagi akan hakan kamar ba ya so zaman da suke yi a tare tashi tayi tana duban Dr.Karami da yake yiwa Dr.Aqeel Sallama.

“Nagode sosai gobe Allah ya kiyaye hanya ya tsare”.

ta na gama fadin haka ta gyarawa Mu’azzam kwanciya a kafadatar ta yi hanyar dakin da Ummanta take tana faman saka da warwara akan Dr.Aqeel gabadaya ta lura dashi ya fiye takura sosai duk da dai shi mai ALHERI ne amma wani lokacin abin da yake yi sam bai dace ba ya kamata ya san wani abu guda ba kowa ne zai iya daukar irin halin da yake nuna wa wanda zai san shi ba sai yaga kamar tsana ce kawai ko da ita a karan kanta ta fara dasa ayar tambaya akansa mafiya yawan lokaci in dai suna tare da Dr.Karami yana yi mata wasu abubuwa kamar natsana ita da Dr.Karami din ta rasa in ya dosa ta rasa menene nufin sa da hakan din.

Tsaki ta ja kamar harshenta zai tsinke ta karasa shiga dakin kwance ta sameta tana barci samun waje tayi ta zauna izuwa lokacin Mu’azzamn barci ya fara tafiya dashi sosai tashi tayi ta shimfiɗar dashi ta sannan ta samu gu ta zauna ta zabga tagumi ta fada duniyar tunanin mahaifinta wamda ba ta san a wani hali yake ba cikin duniyar rayuwarsa tun fitarsa kwanakin baya da yayi har yau ba alamun sa ta rasa ina ya tafi ta rasa mai yasa mahaifinta yayi mata haka ta ba so yayi misa da ita a kowani hali suka tsinci kansu tasani rashin abubuwa yana taka muhimmiyar rawa a duniyar rayuwarsu sai dai ba yarda za suyi ta sani rashin babu ne yasanya mahaifinta fita amma bai dace ace tsayin wannan kwanakin ba asan a inda yake ba har gida taje amma ta sami labarinsa ba sai ma rashin mutunci da Goggo Marka ta aikata mata da kuka ta baro gidan.

Sosai take jin faduwar gaba game da mahaifinta duk lokacin da take tunanin sa komai take ji bai mata dadi a rai ta rasa mai za tayi ta rasa mai ya dace tayi sosai kwakwalwarta ke caji wanda ita kanta ta san tunanin da take sanyawa kanta ya fi karfin kanta sai dai bata san mai za tayi ba komai a cakuɗe yake cikin duniyar rayuwarta.Sosai idanuwansa suka kaɗa sukayi jajir kamar wanda aka watsawa garwashin wuta. Sosai yake jin wani zafi da zugi a kasar zuciyarsa sosai da sosai kirjinsa yana wani irin bugawa kamar zai rabe gida biyu numfashi yake ajje wa lokaci-lokaci mai tsananin zafi da zugi.

Shisha din dake girke a tsakanin kafafuwansa ya zubawa ido sosai kamar wanda yake son fahimtar wani abu game da ita a hankali ya kamo yar igiyar da ake amfani da ita ya kai bakinsa ya zuga tsayin sakanni talatin kafin ya zare daga bakinsa gami da sakin wani hayaki wanda ya turke masa fuska gabadaya ya kasance ba ka hango kansa ma sosai hayakin yake tuntulowa daga bakinsa da hancinsa sai da hayakin ya debi lokaci kafin ya tsagaita da tuntulowa sosai idanuwansa suka kaɗa har da yar guntuwar kwalla kwance a ciki.

Gyaɗa kai yake faman yi ba abin da yake yi masa shawagi a duniyar tunaninsa da zuciyarsa sai wani lamari da ya kasa gasgata shi ya rasa a ina zai ajje shi domin samun saukin raɗaɗin zuciya dana ruhi sosai yake jin nauyi a kirjinsa sosai komai ke kwance masa na tunani sosai yake jin abubuwan da suke addabarsa suna amsa kuwwa  gami da sauti a kunnuwansa kirjinsa yake ji yana kara nauyi sosai numfashi ma dakyar yake samun ajjeshi.

A hankali ys ajje igiyar shisha din ya fara yinkurin mikewa wani irin nauyin kirji ya sake tokareshi daga hanzarin da ya so amfani dashi da sauri ya koma ya zauna ya na mai sakin numfashi da sauri-sauri kamar wanda aka sanyawa Oxgyen sosai yake jin bacin rai in ya tuna kalma guda da yanayin da take furtata akansa sosai yake jin ɗaci a ruhinsa akan duk kan wata kalma da ta fito daga bakinta sosai yake jin zafin tsakin da tayi masa a daidai wannan lokaci.

Mai yasa… Mai yasa mai dauki mataki tun a waccan lokacin ba, mai yasa ya bari damar ta subuce masa mai yasa yake kasa aiwatar da duk wani kudiri da ya daukarwa kansa in har yana kusa da ita ya rasa dalili.

Zancen da yake ta saƙawa kenan a kasar zuciyarsa sosai yake ganin tana yi masa kwarjini a idanuwa sosai yake kasa aiwatar da komai in yana gabanta.

Kai ya shiga girgizawa yana faman taunar laɓɓansa kamar su ne masu laifin sosai yake jin komai ya cushe masa sosai yake ganin kwanciyar hankalinsa na guje masa sosai komai ke shirin ƙwaɓe masa a rayuwa a dalilinta a matsayinta na kaskantaciya wacce bai dauka a bakin komai ba.

“Ni Huzaif ni ta wulakanta”.

da sauri yake girgiza kai ya nasake furta.

“ya zama dole nasan abin yi zuciyata ba zata yafe mani ba sam! na lura da hakan”.

Haka yake ta sakin zance kamar wani zararre tsayin lokaci kafin ya mike cikin karfi hali ya fada Toilet ruwa ya watsa wa kansa nan ya fito ya shirya domin ya lura in har yana zaune a waje daya komai zai iya hanashi sakat! musamman kan maganar yarinyar da yake ji a ransa ya tsana tsana mai tsanani.

*****

“Please Khairiyya!”.

Ya fadi cikin wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa a gareshi sosai yake jin zafi a zuciyarsa sosai yake jin ko ina na zuciyarsa na yayyagewa sosai kansa ke sara masa komai ya kwance masa sosai ya shiga tashin hankali mara yankewa wanda yake tsammanin zai iya tafiya da numfashin sa.

Sai da ya gama ja-in-ja da numfashin sa kafin ya daga laɓɓansa daƙyar.

“Ina cikin Matsala sosai da sosai na rasa ya zan yi komai yake kwance mani na tunani na komai zai iya faru ki taimaka ki zo”.

A wannan karon muryarsa ta rage sauti sannan kuma tana rawa hannayensa duk biyun ya daura akan sa bayan ya sauke wyar daga kunnansa sosai yake jin  tashin hankalin da ya tunkaro shi sosai yake jin bugun zuciyarsa na sauyawa daga kwanciya hankali zuwa akasinsa.

“ban san abin da ya sanya ni gamu da ita cikin duniyata ba, ban san abin da yasa ta shigo rayuwata ba ban san abin da yasa ranar ta zo mani a haka ba ban san mai yasa tsautsayin da nake gudu yake kokarin fado mani ba ban san gangancin da ya kai ni wannan ranar har hakan take dauko mani tashin hankali wanda ba zan iya dauka ba”.

Gabadaya ya zube kan cafet din dake tsakar dakin yana faman sakin numfashi a hankali ji yake yi kamar gabadaya tashin hankalin duniya a kansa ya kare.

Marikin kofar da yaji an murza ne ya sanya shi saurin buɗe idanuwansa da suke rintse sosai yake kallonta da yanayin da ta shigo dashi kau da kai yayi gami da jan gudun tsaki wani haushi ne yaji ya tokare masa wuya ji yake kamar ya tashi ya rufe ta da duka sai yanzu yake dana sanin kiranta bai san dalilin da yasanya shi kiranta ba wani haushi yake ji a game da ita gabadaya yake ganin muninta da wani haushi nata yana tun karoshi mai da idanunsa yayi ya rufe.

Ita kuwa ganin irin Halin-ko-in-kula da ya nuna mata sai ta dauke kai tana mai jan tsaki a hankali ta fara taku har ta isa kan daya daga kujerun falon ta zauna kafin ta dube shi sosai kallo take masa na TUHUMA sosai take ganin sauyi gareshi sosai take ganin komai nashi ya sauya ba yarda ta san shi ba kyaɓe baki tayi kafin ta motsa laɓɓanta da suka sha Pink din jambaki.

“Huzaif”.

Ta fadi a hankali tana kara kureshi da idanuwanta manya masu kalar madara sai faman kaɗa su take yi.

Bai motsa ba balle ta saka ran masawar sa sosai taji haushin haka amma bata nuna ma sai ma sake kiransa da tayi nan ma bai amsa mata ba hakan ya kara kular da ita a zafafe ta mike ta fara kokarin barin falon tana fadin.

“A rayuwa na kijin wulakanci zan iy daukar komai amma ban da wulakantawa kuma wannan zai zama karo na karshe wallahi!”.

tana gama fadin haka ta rike murfin kofa tana kokarin murɗawa ta fice.

Huzaif da yake fama da zafin zuciya ya kokarta buɗe idanuwansa ya sauke akanta.

“Khairiyya”.

ya fadi a raunane ita kanta sai da taji wani iri a jikinta a sanyaye ta saki kofar gami da juyowa ta dube shi tana harɗe hannayenta a kirji.

“Taimako nake bukata don Allah”.

Da mamaki take dubansa tana juya maganar tasa akanta kafin ta yi taku uku sannan ta tsaya.

“Huzaif taimako fa kace?”.

Kai ta shiga girgizawa tana faman sakin yaƙe.

“me ke damunka har kake neman taimako a duniyar nan?”.

Ta sake fadi tana mai kafeshi da idanu sosai.

“Nima ban sani ba komai ya kwance mani kawai ji nake kamar bani ba…”.

Da hanzari ta tare shi.

“Ban gane ba Huzaif?”.

Tashi yayi daga kwancen da yake a hankali ya mike tsaya sosai yake kallon Khairiyya sosai yake hango zata iya taimaka masa sosi yake ganin ita kadaice zata iya yi masa komai da yake bukata.

Gyaɗa kai yayi kafin ya ciji laɓɓansa hannunta ya kamata ya fara kokarin ja da sauri ta fizge tana masa kallo mai dauke da TUHUMA shima kallonta yayi wani iri kafin ya sake jan hannun nata suka fice daga cikin falon.

******

Sosai ya zuba musu ido yana jin wani iri a gameda su gabadaya zuciyarsa ta ki yarda da su sosai gabansa yake faduwa ji yake kamar akwai mugun nufi a tattare da su sosai ruhinsa da zuciyaesa suke nuna masa shakka akansu idanuwansa sosai yake dubansu da su tun da yayi Parking a harabar asibitin ya tokare a jikin motarsa kira BMW yanayin su kawai yake kallo yake hango rashin gaskiya da kuma tashin hankali a tattare da su a hankali ya fara takunsa cikin natsuwa idanuwansa na kan su har izuwa lokacin kofar da zata sada shi da cikin asibitin ya dosa sai da ya zo daidai da su gabadayansu idanuwansu suka sarƙewa juna wani irin kallo suke duban junansu dashi kamar wanda suka san juna da jimawa zuciyoyinsu sai fama kawo musu wani lamura suke ma bambanta wanda su akaran kan su ba su na me nene ba.

Kau da kai Dr.Karami yayi da sauri yana gyara zaman niktayal din wuyarsa ya cigaba da takunsa ba tare da ya sake bi ta kan su ba har ya isa cikin asibitin.

Sannu a hankali ya fara takunsa yana ajje wa dakin su Mariya yanu fa yana kokarin sa kai itama ta sanyo kai zata yo waje kamar daga taji a kirjinsa da sauri cikin yanayi na firgici ta ja da baya tana mai zare idanu.

“Subhanallah!”.

Ta fadi cikin tsanani kaɗuwa sosai take kallonsa shima idanuwansa na kanta sosai yaji wani irin Shock a ko ina na hanyar jininsa har sai da ya runtse idanuwansa domin ji yayi gabadaya kansa ya shiga juyawa kamar wanda wayar wuta ta zukar wa jini yayi low sosai

“Don Allah…”.

Ta fadi tana mai rawar baki idanuwanta ta sauke su kasa sosai da sosai take jin ko ina na jikinta na sauri jininta yana kara gudu zuciyarta na kara sauti wajan bugawa.

Hannu ya daga mata yana mai sakar mata murmushi gami da lumshe idanuwansa sosai yake fuskartar natsuwar da take dashi sosai yake jin tana burgeshi duk da kananun shekarunta amma hankalinta na yanayin natsuwarta kamar mai shekaru sama da ashirin ko da yake duk wanda ya ganta ba zai taba bata haura shekaru sha biyar domin Mariya tana da tsayi da kuma kaurin jiki irin matan nan ne masu diri da cikar matantaka sosai ta ko wani fanni sosai jikinta yake bayyana irin baiwar kirar jikin da Allah ya bata ko ina na jikinta sosai ya cika sai dai ace yarinya ne a jikinta rintse idanuwansa yayi jin zuciyarsa na hasaso masa abubuwa ma bambanta da sauri ya zare tunani ya ajje gefe yana mai sauke numfashi.

“Yaa Allah! Mariya zaki fasa min kirji ko”.

Ya fadi yana mai haɗe girarsa kamar gaske yanayin da ta dan razana ta dago kamt da sauri tana kallonsa lokaci guda idanuwanta sukayi rau-rau kamar za su zuvda hawaye.

“Don Allah…”.

Da sauri ya kai dan yatsarsa bakinsa gami da furta.

“Shiit”.

Yanayin yarda yayi salon sai ta saki baki tana kallonsa sosai taji ya burgeta da yanayin da murmushi ya sauka a fuskarsa ta tabbata wasa yake yi mata kasa tayi da kai ta dag laɓɓanta.

“Ban sani ba, ban san kana taho wa ba na rokeka…”.

“Nace kiyi shiru mana!”.

Ya fadi muryarsa da dan sauti a cikinta. Gyaɗa kai ta shiga yi tana kokarin giftashi ta wuce ya tae ta da cewa.

“Ina kike kokarin zuwa?”.

Shiru tayi tama rasa mai za tae dashi sai juya faka din dake hannunta take mai dauke shara.

Sosai ya gane in da ta dosa amma so yake yi tayi magana da kanta amma ya lura magana ma wuya take mata

“koma ciki to tunda ba in da zaki”.

Da sauri ta dago kanta tana kallonsa yanayin da taga ya ci mur ta san da gaske yake baki ta fara motsawa.

“Shara…”.

Abin da ta fadi kenan ta tsuke bakinta ta sake yin kasa da kai tana cigaba da wasa da fakar dake hannunta gabadaya taji gajiya na saukar mata sosai ta matsu ta bar wajan amma ta lura Dr.Karami sai ya ga kafarta ta zubda ita kasa sannan zai rabu da ita.

“Ya jikin Umma?”.

“Da sauki”.

Abin da ta fadi kenan domin ta lura in dai yayi magana bata amsa ba hakan ne zai sanya ya hanata tafiya.

“Madallah! zaki iya tafiya”.

Kamar wacce take jira da sauri ta fara jan jikinta har tana kokarin tuntuɓe sosai yake kallonta yana kallon yarda take ajje taukunta duk da dai cikin yanayin tsoro take amma hakan bai hana bayyanar da natsuwa a takunta ba sai da ya ga fitarta sannan ya numfasa ya karasa shiga dakin.

Tunda Mariya ta fice take gayyato natsuwa tana yafawa kanta sodai tsoro da kunyar Dr.Karami suke samun mazauni a zuciyarta sosai komai nashi yake burgeta sosai take jin wani iri in suna tare sosai zuciyarta ke natsuwa in suna tare amma a zahirince tsoro ne ke bayyyana a fuskarta ta rasa dalili ko da yake zata iya ajje hakan a matsayin Kwarjini da yake mata sosai musamman yanayinsa da cikar halintar mazanataka da yake dashi sosai take jin wani iri in tana gabansa sai ta raina kanta sai taga kamar dan tsako ne a gaban rakumi.

Har tasa inda za ta zubda sharar bata daina zancen zuci ba saura kadan ta afka cikin dan wajan da aka tanada don zubda shara ita kanta sai da taji kunya da sauri ta zubda sharar ta juyo domin komawa cikin asibitin taku kadan tayi da yake kanta a kasa yake sam ba ta lura da wanda yake gabanta ba gabadaya ta ji ta ci karo da mutum sosai ta tsoro zuciyarta lokaci guda ba wanda ta kawo mata sai Dr.Karami tunanin ya kawo mata wato yana biye da ita kenan lokaci guda ta sake tsora a ranta tana fatan Allah yasa bai ga halin da take ciki ba a dalilinsa.

Tunaninta ya tsaya lokacin da taji wani wari gami da kamshin tuarare sun haɗe waje daya sun ba da wani kamshi mara dadi don sai da taji zuciyarta ta fara tashi da sauri cikin tsananin haushi da takaici ta dago kanta ta sauke kan mutumin da ya kusan tafiya da numfshinta da sauri ta ja baya tana mai zare ido bakinta na ƙarkarwa sosai take kallonsa gabadaya take jin tsoro da dukan zuciyarta na karu yanayin da ta ga idanuwansa sun kaɗa sunyi jajir har wani launi duke sauyawa nan da nan ta shiga waige waige domin neman hanyar cetar kai sai dai sam hankalin mutane da suke kai kawo baya kan su da sauri ta ja da baya tana ambatar sunan Allah a zuciyarta lokaci guda ta ji wani irin takaici da haushinda ya sake turnuke ta kau da kai tayi domin ta fusakanci rainin hankali tsantsa yake son kawo mata sabo ya rainata ya raina girmanta ya ganta kankanuwa shiyasa ya sami lasisin da zai shigo rayuwarta ya yi abin da yake so saboda ya mai da ita marashin ‘yanci in ba wai tanuna masa zahirin ta bane ta nuna masa ita ma mutum ce kuma ta san darajar kanta ba za su zauka lafiya.

“Na rokeka da Allah da Annabi ka fice daga rayuwata amma ka ki ji ko to bari in hadaka da Iyayenka kila a dalilin su ka bar ni”.

Ta fadi tana kara tsuke fuska sosai idanuwana kansa amma sam bata ga yanuna wani alamun yin wani abuba sai ma kara wani yaƙe yake yi saman fuskarsa haka kular da ita sosai.

“ban san mai nayi maka ba, ban san mai yasa kake kokarin shigowa rayuwata ba, ban dan abin da ka gani a duniyata ba har kake kokarin shigowa na rokeka ka fita harkar ta bana bara ma da kai ko miskala zarratin”.

“Mariya!”.

Sautin muryarsa da ta doki kunnuwanta sosai hakan ya kara tsinka mata zuciya amma hakan bai sanya tsoro ya bayyana a fuskarta ba.

“karka sake kiran sunana kuma ina mai rokon ka da karka sake batar sunana mai so ka ajje sunan Mariya a matsayin wanda baka taba sani ba ko a Mafark…”.

Gabadaya taji hannunta cikin nasa ya sarƙe waje daya ba ta san lokacin da ta saki fakar dake hannunta ba cikin tashin hankali tana kokarin kware baki ta kurma ihu taji ya saka dayan hannunsa ya rufe mata baki nan ta kara hargitse tana faman zille-zille domin kwatar kai amma ina ta kasa domin ji take kamar wacce aka daure da sarƙa idanuwanta suka kara yo waje sai faman nishi take yi amma ko a jikinsa sai ma faman murmushi da yake yi idanuwansa na kara hargitsewa waje guda a hankali ya zare hannunsa daga bakinta hakan ya ta damar sakin ihu amma ba mai sauti ba ganin irin alamu da yayi mata alamun shiru.

“kin fiye tsiwa Mariya”.

Ya fadi yana kara sarke hannayensu waje daya yana murzawa kadan sosai take jik wani iri a jikinta ko wani sashi na hanyar jininta take jin yana tsayawa cak! da aiki sosai sumar wucin gadi ta ziyarceta a hankali ta fara rintse idanuwanta tana jin tashin hankali na samun ma sauki a kowa ni sashi na jikinta zuciyarta na kin abin da yake mata tsanarsa take ji sosai da sosai tana jin haushinsa na samun matsuguni a zuciyarta.

Sosai wani sashin zuciyarra ta shiga biya mata karatu.

‘Ke fa mace ce akan mi zaki tsaya wani namiji gardi yana rike miki hannun kin san illar haka kuwa shin ko kin manta kalamansa da yake fadi miki a haduwarku ta farko’.

Sosai zancen zucin ta yayi tasiri a ko ina na sashin jikinta abin zuciyarta take sanar da ita a yanzu shi kawai ke amsa kuwwa a kunnuwant sosai take jin tana da karfin gwuiwar aikatawa in dai ita kadai ce hanyar da zata kwai kanta da mutuncinta.

Tun da Mariya ta kulle idanuwanta ya zuba mata idanu sosai yake kallonta sosai yake kallon fuskarta da laɓɓanta da suka tsuke waje daya sun yi jajir da su hancinta dan madaidaici mai tsayi idamuwanta da suke rufe haƙa suka kara bayyanar da girmansu yake sosai yake jin zuciyarsa na sauya salon wasu lamurka sosai yake jin komai na kwance masa sosai yake kallonta tana burgeshi.

Mariya da ta buɗe idanuwanta a daidai lokacin shi kuma ya shigar da laɓɓansa cikin bakinsa yana lasa ba ta san lokacin da ta daga  hannu ta sauke masa zara-zaran yatsunta a kan kuncinsa ba ji kake Tasss!!.

“ji ba yar iskan ba ce ka sani ni ‘yar mutunci ce kuma iyayena masu mutunce ne sun san daraja da kimata ba wai sun haifeni bane don kowa ni dan duniya ya zo wajena ya yashe ka sani ni da kake gani nafi karfin ka wallahi bar ganina karama wanda yake baka lasisin zuwa gareni da mugun nufinka to ka sani nayi maka nisa wallahi na wuce da saninka ni ba irin ‘ya’yan da ake ribata bane har a bata masu rayuwa don haka ka kiyaye”.

Ta karashe cikin yanayi na rashin tsoro ko abin da zai je ya dawo a da sauri ta fizge hannunta tana tsartar masa da yawu ta wuce abin ta.

gabadaya komai nashi yaji ya tsaya na jikinsa sosai ya ji sa wata duniya wacce mai san ta mene ne ba sosai sosai yaji kansa na juyawa sosai yaji komai ya kwance masa gani yake yi kamar bashi ba gani yake yi wannan lamarin da ya faru kamar ba gaske ba gani yake yi ko a mafarkinsa ban yi tunani haka ta kasance ma dan yatsansa ya saka a baki sosai ya ciza shi kamar zai tsinkeshi zafin da yaji ya ziyarce shi ne ya sanyashi sauri buɗe idanunsa ganin lamarin gaske ne bai san lokacin da wasu kwala suka taru masa a idanu ba da sauri yayi kokarin mai da su yana mai dafe kirjinsa ba abin da yake hangowa sai hannun Mariya lokacin da ta daga ta sauke a fuskarsa ba abin da kunnuwansa ke jiyo masa sai yarda sautin marin ke sauka a kan fuskarsa.

Sosai kalaman da ta furta suke dawo masa sosai yake jin wani irin yanayi na zarya cikim gudu suna samun masauki a ransa sosai yake jin wani katon abu mai nauyi na samun masaukin a zuciyarsa da kasan ruhinsasosai yake jin wani irin abu maɗaci da bauri na sarƙe masa harshe sosai kalmar MUTUNCIN tana dashi yake amsa masa kuwwa a ko wacce dakika gyaɗa kai ya shigayi gabadaya ya kasa motsawa lokaci mai tsayi ya dauka a haka har zuwa lokacin mai gama tantacce abin da ya faru dashi gskiya bane.

“Uhm ai ita dama  WUYA MAKARANTAR KARE ce wallahi”.

Abin da muryar Khairiyya ta fadi kena tana dosa in da yake sosai take masa wani irin kallo na raini da takaicin abin da ya faru sosai take jin ɗaci a ranta musamman yarda taga komai ya faru akan idom ta ba abin da y kara tsikar mata da zuciya sai Yainyar da ta gani wai akanta Huzaifa yake zaucewa ta rasa ma mai ya dace tayi ji take kamar ta tsinke shi da mari amma ina! ba za ta iya ba a hankali ta fara riko hannunsa ta na murzawa sannu a hankali ta fara jansa tamkar rakumi da aƙala har suka isa wajan motar gidan baya ta buɗe ta turashi cikin wani irin yanayi kamar wanda akayi wa dukan shan gishiri.

Sai da ta kare masa kallo sosai da sosai tana kallon yarda ya rintse idanuwansa kirjinsa na harbawa da sauri-sauri kamar zuciya zata fasa ta fito kau da kai tayi jiki a sage ta koma gidan gaba wajan zaman direba ta shiga ta tada motar cikin wani irin yanayi ta fizgi motar har sai da kura ta tashi ta fice daga harabar Asibitin.

Kai komo kawai take yi a tsakar dakin ako wani takunta daya sai ta dubi Huzaif tana mai ajje numfashi sosai da sosai take jin haushinsa da takaici akan abin da ya aikata sosai take kallon abin a matsayin babban kuskure mai girma sosai a idanuwant sosai take ganin wautarsa da ganganci da kuma yada zuciya kare ya dauke.
Numfashi ta ajje bayan ta tsaigata da kai komon da take yi sosai ta ajje ganinta akansa.
“kasan kuwa abin da ka aikata kasan kuskuren da ka aikata ya girmama sosai a idanuwa…Well bana tunanin kai lamarin ka dauke shi a matsayin kuskure mai girma a idanuwanka”.
Ta fadi tana mai cizon laɓɓanta bayan ta turasu cikin bakinta sosai zuciyarta ke zafi da raɗaɗi akan komai da ya aikata sosai take jin abu mai nauyi ya tsaya mata a kirji ya samu gurbin zama sosai take jin tamkar ita ce akayi wa wannan cin kashin.
“Bana tsammanin Huzaif din dana sani ne wannan bana tunani Huzaif din asali ne wannan anya kuwa ba wasu abu akan ka ba na tunanin abin da kake sha zai sanya ka aikata wannan kuskuren mafi girma a idanuwana”.
Ta sake fadi tana mai girgiza kai sosai take jin komai da ya faru yana dawo mana ina ma tasan hakan zata kasance da tabbas sai Mariya ta raina kanta kamar ta yarinya karama har tasan ta daga hannu ta mari namiji namijin ma Huzaifa.
“Kaico!”.
Cikin wani irin sauti ta furta kalmar tana jin ɗacin lamarin ako ina na zuciyarta da ruhinta.
Harɗe hannayenta tayi a kirjinta tana kallon yarda komai na Huzaif ya canza sosai take ganin lalacia tsakanin idanuwansa da zuciyarsa sosai take hango gazawa a gareshi kau da kai tayi domin in har ta cigaba da dubanda da ganinta tabbas zuciyarta zata iya bugawa don tsananin takaici.
“Yaa Allah ta ya ya zan dubi wannan lamarin a wani MIZANIN HANKALI ya dace na ajje wannan lamarin bana tunani ko mai tabuwar kwakwalwa zai iya abin da ka aikata…”.
“KHAIRIYYA”.
Muryar Huzaif ce ta karaɗe dakin cikin wani irin sauti mai tsoratarwa cikin rashin tsammanin samun maganarsa ta ji ya ambace sosai ta saki zaren kalamanta ta saki baki tana kallonsa sosai take jin gabanta na bugawa gabadaya ganinta ta ajje a fuskarsa komai na shi take kallo da yarda tashin hankali da bacin rai suka nuna a filin komai nashi har zuwa lokain idanuwansa a rufe suke hannayensa saman fuskarsa sai faman juya su yake yi.
“Excuse me. Please”.
Abin da ya sake fadi kenan idanuwansa a rufe tana kallon yarda laɓɓansa suke rawa sosai wajan furta ko wani harafi guda na kalaman da ya furta.
“ki bar ni naji da abin da ke kokarin yayyaga mani zuciyata please ki barni naji da abin dake kokarin tafiya da ruhina sosai da sosai nake  jin bani bane Khairiyya bana zaton ni Huzaif”.
Yanayin yarda laɓɓansa ke rawa da yarda kalaman nasa suke turereniya ga junansu hakan zai tabbatar maka akwai tashin hankali mai girma a zuciyarsa da ruhinsa wanda bai yi zaton wanzuwansa ba a duniyarsa sosai komai na tashin hankali ke bayyana kansa a ko ina nasa.
Rintse idanuwa Khairiyya tayi sosai da sosai take jin wani abu mai nauyi na samun gurbi a zuciyarta sosai da sosai take jin zata iya daukar kowa ni tashin hankali da take hangowa cikin idanun Huzaif ba za ta iya daura ganinta ta cigaba da ganin halin da yake ciki ba ba za ta iya cigaba da jin numfashin sa mai cike da tashin hankali ba.
A hankali ya fara kokarin daga dan yatsar sa dake fama karkawa sosai yake jin wani iri cikin zuciyarsa da inda take zaune a kirjinsa gani yake kamar wauta ya tafƙa sosai a duniyarsa amma ban yi amanar haka a zuciyarsa ba hango Mariya yake yi a matsayim wacce take kokarin kashe kan ta da kanta domin kuwa sosai ta dauka wa kanta fitinar da ba zata iya saukewa kanta ba sosai yakke ganin hauka cikin komai da take aikatawa sosai yake ganin rashin kunya da fitsara tsantsa cikin idanuwanta dole ya dau mataki ko ba komai ya koya mata rayuwar duniyar nan da yarda ‘ya mace bata isa ta galaba akan ko wani ɗa namiji ba dole ta san waye HUZAIF ABDURRAZAQ.
A hankali ya mike yana duban Khairiyya da ta zuba masa idanu sosai murmushi yayi gami da dauke kan sa.
“You can go”.
Abin da ya fadi kenan ya fara daga kafafuwansa cikin wani irin yanayi mai cike da abubuwa marasa dadi ga zuciyarsa Toilet ya nufa har zuwa lokacin idanuwan Khairiyya na kansa sai faman suke numfashi take yi a sauri-sauri sosai take jin wani iri a zuciyarta sosai take hango abin da zai dauko mata tashin hankali ya ajje mata a rayuwa sosai take hango abin da zai hanata rawar gaban hantsi a duniyar Huzaif sosai take hango komai na wargaje.
Numfashi take ajjewa mai dauke da abubuwa masu yawa da take zaton za su sayo mata tashin hankalin rayuwa a hankali ta daga jakarta zuwa kafatar tana faman gyaɗa kai kawai take yi tana tana jin wani abu mai nauyi na sakar mata a zuciya da duk wani gurbi na cikinta a hankali ta fara takunta domin ficewa daga dakin zuciyarta na wassafo mata abubuwa ma bambanta.
********
Sosai da sosai take jin wani irin tashin hankali na kokarin samun masauki a ko ina na sassan jikinta sosai take jin yarda kwakwalwarta ke kwala ihu akan tunanin da ya zo mata a bazata sosai take jin wani sauti mai kara sosai yana amsa kuwwa a kunnuwanta sosai.
Bugun zuciyarta yake kara sauri sosai da sosai takun da take yi da kafafuwanta suke aika mata da wani lamari na daban wanda yake kara hargitsa tunaninta idanuwanta a rintse suke komai take hangiwa komai da komai da ya faru yake dawo mata baya kamar yanzu ne yake faruwa a gigice take ajje numfashi mai tauri a kokarin janyo mata ruhi zuwa waje.
Bata san lokacin da tayi cilli da fakar dake hannunta ba ta sanya hannayenta zuwa kunnuwanta ta rufe su ji take kamar za su tarwatse dalilin sauti da ke musu sukuwa a ko wacce dakiƙa.
“Yaa Allah!”.
Abin da ta furta kenan a kasan laɓɓanta cikin wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa a gareta jin gina tayi da kofar da zata sadata da cikin dakin gabadaya taji kafafuwanta na kokarin gaza daukar gangar jikinta ji take yi kamar jikin ba nata bane sosai take hango fuskarsa tun ranar farko komai yake dawo mata har izuwa wannan lokacin sautin saukar marin da tayi masa take ajin yana samun wajan ajje sautinsa a bangarori masu yawa daga sassa na jikinta sosai take hango wautar ta cikin aikata wannan kuskuren mai girma da zuciyarta ke ganin tayi sosai take ganin girmar lamarin na kara girmama a zuciyarta da tunaninta.
‘Mai ya kai ta, mai ya kai ta aikata wannan danyen aikin, ta ya ya ma haka ta faru gareta tun da take ba ta taba marin wani mai girma kamarsa ba ko da bai kai shi ba bata taba mai yasa tayi haka ina tunaninta ya kai ta lokacin ina zuciyarta ta cilla a lokacin mai yasa bata hana ta ba’.
Gyaɗa kai kawai take yi cikin daukar tashin hankalin da taji yana kawo mata hari, ta tabbata ba zai yafe mata ba, ta tabbata ba zai rabu da ita ba, ta tabbata zai shigo duniyar rayuwarta.
Ta ya ya ta wacce suffa zai zo mata?
Tunani da zuciyarta ke ta hasko mata ke tana kara gigita mata kwakwalwa da lamarin da take kara girmamashi.
Abu taji mai dumi na saukar saman kumatunta ko bata tabbata ba ta san Hawaye ne bayan  HAWAYEN ZUCIYA da taji ma tana yi abin har ya kai ga bayyana dole ta firgita da lamarin ita Mariya ta mari wani wanin ma mai girma girman da ya dace ace ta ganshi ta daraja shi amma ina! ZUCIYA BATA DA K’ASHI.
‘Akan mi akan wani dalilin zaki damu kan ki. Kina zaton in da ya cimma buri akan kudirinsa a kan ki tashin hankalin da za ki shiga mai ya girmema wannan ba kawai don mari har zaki bari tashin hankali ya yi girma mafi girma gareki karki yi sake har wannan kankanin abun ya hanaki abubuwa cikin rayuwarki’.
Wani sashi na zuciyarta ne taje tana amayo mata sautin zantukan nan.
Sosai tayi shiru tana nazarin kalaman sosai komai taji yana kokarin dawo mata daidai a hankali ta fara gyaɗa kai tana jin yarda zuciyarta ta cigaba da wanzar mata da wasu batutuwa masu girma a gareta.
‘Shin in da ya keta miki haddi mi kik zaton zai faru dake a duniyarki’
Numfashi mai girma ta ajje gami da buɗe idanuwanta gabadaya sosai take kallon kanta sosai take kallon yanayin kankatarta tana kara nasarin abin da ta aikata a hankali komai da zuciyarta take fadi mata ya fara tasiri sosai a kanta sosai da sosai zuciyar ta dake komai na tsoronsa ya kai sai dai abu daya da take jin sa a zuciyarta duk a dalilinsa sai dai bata dan me nene ba bata san a me zata fassara shi ba sai dai zata iya barin sa a matsayin ‘Mala’ har zuwa nan gaba.
A hankali ta fara daga kafafuwan ta da taji sunyi mata nauyi kamar an daura mata wani abu da yai karfin girman jikinta sosai take kokarin amfani karfin zuciya tana jansu tana sanya hannayenta tana dauke guntayen hawaye da suka zobo mata sosai take takaicin zubarsu akan wani can wanda bai san darajarta ba mai san kimarta ba mai san martabar ta ba…
“Mariya”.
kamar daga sama taji sautin muryar ya sauka a kunnuwanta da sauri ta ja kafafuwanta da take ja daƙyar ta ajje su waje guda ko ba a fada mata ba ta san waye hakan ya hanata juyawa domin adaidai wannan lokaci tana bukatar zaman kadaici ita kadai ba ta so ta sake daukar wani abu da zai so canja masa lissafin da take faman yi azuciyarta runtse idanu tayi jin takunsa na isowa gareta sosai take nuna rashin so wani abu a yanzu sosai fuskarta ta bayganar da haka.
A hankali ya isa gareta hannayensa sarƙe a juna jikinsa sanye da wani lallausar boyel mai kalar fari anyi masa dinki babu wuyar rigar an mata aiki da jare mai kyallin gold sosai kayan suka dace da jikinsa kansa sanye da hula ita ma dai kalar kyallin Gold ne doguwa ya dan rangwafar da ita kamar yarda yarbawa suke yi fuskar nan tashi fayau ba zaka ce ya hau shekaru talatin a duniya.
Sosai yake karantar yanayin ta da yarda ya hango damuwa dauke a fuskarsa sosai yaji rashin jin dadi a ransa ciza laɓɓansa yayi kafin ya gyaɗa kai.
“akwai abin da ke damunki Mariya”.
Ya fadi yana sake kafeta da idanuwansa manya sosai take jin rashin son magana a daidai wannan lokaci amma ba za iya ajje Dr.Aqeel a matsayi marashin girma gareta ba tana jin sa sosai a ranta da irin ALHERI da  yayi a rayuwarta.
“Uhmm bakomai kawai dai…”.
“Mariya mana”.
Ya fadi cikin muryar mai sauti da rarrashi a cikinta.
A hankali ta dago kanta ta dube shi na yan sakanni kafin ta kau da kai tana hango yanayin kulawa sosai cikin idanuwansa gareta tana hango yarda ya nuna alamun damuwa da damuwarta.
“Baabana”.
Ta fadi murya na rawa yanayin da tayi maganar zai tabbatar maka kamar iyakar gaskiyarta ta fadi ko da dai ba karya tayi ba lamarin bacewar Baabanta cikin rayuwarta yana cikin sahun abin da take zaton ƙaddara zata kawo mata na rashin natsuwa.
“Yaa Salam!”.
Dr.Aqeel ya furta cikin rauni sosai kafin ya daura hannunsa akai yana mai cigaba da cewa.
“Please Mariya ya kamat ace ki na sanyawa zuciyarki natsuwa gami da kwakwalwarki ke fa karamar yarinya ce sam bai dace ace har kin fara cin karo da irin wannan lamarin ba a rayuwarki kwakwalwarki ba komai zata iya dauka ba tsorona kar damu tayi miki yawa sosai wani abun zai iya kama ki na rashin dadin rai Please Mariya Rayuwarki tana bukatar komai mai dauke da sauki”.
Yanayin da yake ajje furucinsa da rauni a ciki da kuma rarrashi  sosai hakan ya taba zuciyar Mariya ji take yi kamar ta rushe da kuka ita a karan kanta ta san sosai take cikin SIRAƊIN RAYUWA sosai take ganin yarda rayuwarta ke zuwa a a hagu ita kanta ta dani komai na duniyarta ba mai natsuwa bane ta sani sosai da sosai ƙaddara ke dawainiya da ita a duniyarta.
“Mariya komai zai shige in har  baki dau komai da zafi ba, rayuwarki tana da muhimmanci  ga rasu rayuka masu yawa sosai wasu rayuka za su shiga tashin hankali mai girma in har ba ki rangwantawa kan ki ba”.
A dan tsora ce ta dago tana dubansa sosai taji kalamsa sosai take fahimtar in da ya saka gaba rintse idanu tayi kafin ta buɗe su ta fara kokarin daga laɓɓanta.
“Ta ya ya hakan zata kasance, ta ya ya zuciya zata iya daukar wannan lamari mai girma ta ya ya karamar kwakwalwata zata iya daukar wannan lamarin mai girma, bana tunanin zan iya amfanar da wasu rayuka a halin da nake ciki bana tunanin ƙaddara zata iya bani wannan damar bana zatom ƙaddara zata juya daga shafin da ta buɗe mana mai dauke da kaya mai girma na rashin kwanciyar hankali bana zaton hak…”.
A hankali ta rintse idanuwanta tana tura laɓɓanta cikin bakin ta sosai take jin abu mai nauyi yana samun gurbi a zuciyarta sodai take jin kirjinta na nauyi da girma a cikinsa.
“Bana tunanin Mahaifin ki zai guje ku a halin rayuwar da kuke ciki. Bana tunani zai samu kwanciyar hankali don ya bar ki bana tunanin saboda gazawa ce ko halin da mahaifiyarki take ciki ya sanya shi bacewa daga rayuwark…”.
“Dr.Aqeel mai yasa kake cewa haka, mai yasa kake kokarin sanar dani abin da zuciya ta ba zata iya samun wajan ajjewa ba”.
Nisawa tayi tana jin yarda zuciyarta ke wani karfi a duk fitar kalma daya daga bakinta.
“Mai yasa mai tsaya mun tafi tare ba, mai yasa da zai tabi bai tabbatar mani da in da zai je ba, mai yasa ya boye mani wani abu kuma ya san zuciyata ba iya dauka za tayi ba mai yasa ya tafi tsayin kwanaki fiye da arba’in ba tare da ya waiwayo mu ba ina jin zafi a zuciyata ina son Baabana sosai da sosai yarda baka zato ina bukatarsa kusa da ina ina bukatar kullum na dinga kallonsa yana wanzuwa a DUNIYARMU a kullu yau min. Ban so ya tafi wata duniya ba ta daban wacce ba musan a wani hali yake ba kullum tashin hankalin rashin sa kara girna yake yi a ko wani sashi na zuciyata”.
Yanayin yarda take ajje kalmominta sosai suke taɓa zuciyarsa zuciyarsa yake jin tana wani iri tana saukar da wani lamari mai nauyi gareshi sosai tausayinta ke kara samun gurbi a ko ina na zuciyarsa sosai yake jin ba zai iya cigaba da kallon yarda komai na muryarta da zuciyarta ke kara rauni ba.
“Yaa Salam! Mariya kiyi hakuri don Allah komai zai zo karshe, kuma Mahaifinki zai dawo gareki na sani duk in da yake kuna ransa domin ku ne rabin rayuwarsa ko ina ya ajje kafarsa dole ya kasance tunaninku yana zuciyarsa”.
“Amma…”.
“Haba mana Mariya”.
Ya tare da sauri domin sam ba ya bukatar ya sake jin wani furuci nata mai rauni ya daki kunnuwansa. A hankali ya fara juyawa domin komawa Office dama ita ya fito dubawa sosai yake jin yarda numfashinta ke sauka a hankali har ya bar wajan.
A hankali ta daga kai ta bashi da kallo sosai idanuwanta suka cika da kwalla suna kokarin zubowa bayan hannunta ta saka ta dauke su ta kwashe mintina a tsaye a wajan kafin ta kokarta jan jiki sosai take jin nauyi a ko ina na sassan jikinta musamman kirji don ji take kamar dutsen Dala aka daura mata kanta a kasa take tafiya sam bata lura da wanda ya ke gabanta ba sai da ya ga ta kokarin tureshi sannan yayi gyarar Murya a dan razane ta dago kai sau kadan ta bugi kirjinsa ta ja baya kadan tana mai jikin kunya sosai da sosai.
Ya lura da haka Murmushi yayi kafin ya fara kokarin magantuwa duk abin da suke yi da Dr.Aqeel akan idanunsa komai ya faru sosai ya ji nauyi mai girma a ransa da zuciyarsa musamman yarda ya ji muryar ta na amon kalamai mausu dauke da rauniya da gazawar zuciya.
“Mariya”.
Ya fadi a dan tausashe. Ba ta dago kai ba balle kuma ya saka ran amsawarsa ko da dai ba sosai yake bukatar amsawar ta ta don ya sani dole ya ji rauni a muryarta ko da kuwa ta amsa din shi kuma abin da baya so kenan a ransa.
“Me ya sa?”.
Kan ta ne taji ya daure sosai da abin da ya fadi ba ta san ina furucin masa ya dosa bata san mai zata iya cewa a matsayin amsa gareshi ba ta san tambaya yayi amma kuma bata san mai ya dace ta fadi a matsayin amsa ba sosai take jin tsauri a furucin nasa sosai take jin komai na kwance mata domin ita dai ta san ba zata ce ga abin da ya dace tace dashi ba.
Gyaɗa kai take faman yi sai motsa laɓɓanta take yi amma bata da abin cewa.
“Na rasa dalilin da baki daukar shawara, zuciyarki sam-sam bata daukar abin da ake sanar dake, Me ya sa?”.
Sosai take jin nauyinsa a zuciyarta sosai take jin kamar bata kyauta masa ba don a yanayin da take jin furucinsa ya tabbatar mata kamar bai ji dadi ba. Amma kuma ba ta san dalili ba, ta san abin da yasa yayi wannan furucin ba, sosai ta fuskanci akwai abin da yake nufi da furucin nasa.
A Hankali ta fara kokarin dago kai  domin kallonsa amma tana jin yarda gabanta ki bugwa da sauri sauri a hargitse ta kalle shi idanuwansa na kanta sosai yake kallonta fuskarsa ba ta san a wata matsaya zata ajje taba. Bata hango haushi a ciki ba kuma ba ta hango fara’a ciki ba. A hankali ta fara daga laɓɓanta da taji sun mat nauyi sosai bayan ta kau da idanuwanta daga gareshi.
“Hakuri…”.
“Bana bukata ni ba abin da kika yi mani, kuma ba abin da nake son ji daga gareki ba kenan”.
Yanayin da yayi maganar tasa sosai taji faduwar gaba don ta hango damuwa a cikinta sosai da sosai rintse idanu tayi ba ta so, ba ta so ko kadan ace ta dalilin ta mutum mai ALHERI ya shiga damuwa rashin kyautawa take hangowa a gareta.
“Ban san mai zance da kai ba, ban san ina ka dosa da maganar ka ba, bani da abin cewa domin maganar taka sosai na rasa inda zan ajje ta kayi hakuri don Allah”.
Maganar ta ta tayi rauni sosai hakan ya sanya shi sassautawa a muryarsa don ya fuskanci kamar taji damuwa a maganarsa.
“Ban so na shiga rayuwarki don ta kura miki ba, ban son abin da zai kara rikitar miki da tunani, bukatata kawai shine damuwarki a ranki ki rage ta sam! hakan bai da ce ba a matakin shekarun ki Mariya sosai take jin rashin dadi a rai na da lamarin daukar ki nake kamar kanwata ban son abin da zai dinga saki damuwa bana jin dai har kasar ruhina”.
Hannayensa ya yarfar cikin yanayi na rashin jindadi kafin ya sake cewa.
“ki shiga ciki don Allah ki wutar wa ranki  Umma ta tashi na bata magani haka Mu’azzam ya faka amma ya koma don haka ba abin da za kiyi yanzu illa ki zauna ki ragewa kan ki tunani in kuma kina da abin yi ki je kiyi don karki zauna kuma ki fada wata duniyar ta tunani na san halin ki Please Alkawari”.
Ya karashe cikin muryar rarrashi sosai da sosai taji wani iri a ranta hakan ya haifar mata da kasa mai yawa daga cikin abin da ke damunta a rai.
Kanta a kasa ta wuce shi sumui-sumui kamar maras gaskiya sai da ya ga shigewarta sannan ya saki ajiyar zuciya mai cike da tausaya kafin ya saki murmushi don ya lura ta amince da abin da yace kuma za tayi din rufe idanuwansa yayi na yan sakanni kafin ya buɗe su fuskarsa da fara’a kamar koyaushe ya fara taku domin ficewa.Hannu bibbuyu ta zabga tagumi idanuwanta kan Mu’azzam. sosai take kallonsa tana jin wani irin abu na sauka kan zuciyarta da ruhinta, sosai take jin wani abu mai kama da ruwa yana kwaranya a ko wani sashi da loko na ma’ajiyar zuciyarta, komai take ji yana yi mata wani iri sosai take jin kauna da so mai girma na saukar mata akan kaninta ba abin da take nisawa a ranta sai yarda duniya lokaci guda take shirin juye mata da wata irin ƙaddara mai girma a rayuwarta. sosai take jin duniyar na wargajewa da dukkan wani farinciki mai girma, da ta san tana samu cikin kankanuwar rayuwarta.+
Ya za tayi kenan in ta rasa wadannan madogaran rayuwarta ta mai duniyarta za ta kwaso mata in ta rasa wadannan mutane masu matukar muhimmanci a duniyarta.
Wasu hawaye masu zafi matuka taji suna sauka akan fuskarta da can cikin zuciyarta da ruhinta.
Ta sani kuma ta dade jimawa cikin duniyarta ba ta da sa’a a rayuwarta domin kuwa sosai ta fuskata ƙaddara mai kaifi ce ta fado mata da abubuwa masu matukar tashin hankali da yankewar farinciki Babanta ya tafi ya barta ga Ummanta bata da lafiya ga karamin kaninta wanda shi ƙaddara ta sunkuto shi cikin wannan duniyar mai dauke da kwamatsai rashin dadi ina ma tana da dama ina ma tana da iko ina ma ta san zai fado duniyar nan a haka da bata yarda ba da bata amince ba ina ma ace ana tuntuba kamin a sako dan’uwa duniya da ta roki ubangiji bai sako kaninta ba sai dai ba yarda ta iya komai na Allah tabbatacce ne a duniyar dangin rai kana naka yana nashi.
Hannu ta sanya tana mai dauke zafafan hawaye da take jin su a ko ina na sashin zuciyarta tana dauke su wasu na biyo bayan su tana jima cikin wannan yanayin kafin ta motsa ganin Mu’azzam yayi barci ta kai shi makwancinsa ta kwantar bayan tayi Hugging din sa a ko ina na fuskarsa sosai take jin kauna mai girma a tsakanin ko ina na sassan jikinta akan shi sosai take hango wa a duniyar nan bata da kowa dangin yan uwa sai shi dole ta kula dashi dole ta so shi domin shi kadai ne take zaton zai shafe duk wani daci da kunci da ukuba da take ji a zuciyarta na rashin yan uwantaka.
A hankali ta fara takawa har inda Umma take kwance ta na barci hankali kwance kallo daya zakayi mata ka tabbatar akwai alamun warakar natsuwa a tare da ita.
Idanuwanta sosai ta buɗe akanta tana kallonta kamar wacce aka ce in ta dauke idanuwanta za a gudu da ita zuciyarta taji tana wani amsawa da wasu abubuwa mabambanta wanda ita kanta ba za ta ce me nene ba.
Wani murmushi ya subuce mata kalaman Dr.Karami suke mata yawo a kunne a jiya bayan ya zo ya duba Umma.
****
Kallonta yake yi sosai yana yawatawa da idanuwansa masu wani irin yanayi mai matukar kashe jikin wanda ake kallo sosai take jin kallon nasa na shiga duk wani sassa na jikinta yana haifar mata da wasu abubuwa wanda ba ta san a mizanin da za ta ajje su ba sosai take jin bugun zuciyarta sosai take jin yarda zuciyar ta ta take tsalle a duk wata dakika daya na kallon da Dr.Karami yake yi mata ta rasa mai yasa take jin haka ta rasa dalili lokaci da dama ana kallonta mutane masu muhimmanci a idanuwanta amma bata jin haka sai a kansa shi kadai kwallin kwal!.
“Mariya”.
Yarda Dr.Karami ya ambaci sunan sai taji aduniyar rayuwarta bata taba jin wanda ya kira sunan da wani irin yanayi mai matukar amsa kuwwa a kwakwalwa da kashe jiki da sanya zuciya tsalle tsalle kamarsa ba sosai take jin duk wani sashi na jikinta na wani irin amsawa da narkewa kamar ana narka roba a wuta wani numfashi take ja mai matukar girma wanda take ji kamar in har batayi jarumtar jan sa ba numfashin katsewa zaiyi daga gareta kanta a kasa tana faman wasa da kasar rigar atamfar ta da take jikinta wanda kallo daya zaka yi mata kasan taji jiki sosai da sosai.
STORY CONTINUES BELOW
“kin fiye kunya da yawa. Ya kamata zuwa wannan lokaci ki saki jikin ki da ni domin an zama daya”.
Wani irin kuwwa taji maganar tasa ta nayi cikin kwakwalwarta ji take kamar kasa ta tsage ta zurma ciki sam bata son yarda Dr.Karami ke mata amma kuma ta na son ta zauna dashi sosai a waje daya domin mutum ne mai saukin kai da kokarin kwantarwa da mutum hankali.
A hankali take daga kai domin ita dai ba ta san mai zata ce dashi ba bama ta san yarda kalaman nasa su ke zuwa ba cikin kwakwalwarta ita dai kawai sautin muryarsa take jin na amsa amo nata.
“kin ga dai yau kuna cikin kwana na Arba’in da takwas kin ga kenan yau saura kwana goma sha biyu su cike KWANA SITTIN da nace in Allah ya yarje mana komai zai daidaita a wajan Umma. Shin ya kike ganin jikin nata me kike karanta game da ita?”.
Ya dasa aya yana mai dubanta sosai cikin idanuwansa yana faman murmushi yana gyada kai sosai yake jin Mariya na samun masauki a zuciyarsa da duk kan wani sashi na jikinta sosai yake jin ta tamkar uwa daya uba daya suke sosai yake jin wani abu mai girma yana samun waje a filin zuciyarsa yana zama wanda a kullum yana jin yarda yake daɗuwa ba wai raguwa ba murmushi ya sake yi.
“ban san mai zan ce miki ba, ban san ya kike rayuwarki bs, ban san mai yasa ba ki sakin jiki da mutum ba, ban san mai yasa kike gujewa mai…”.
Sosai yaji kalmar da zai fadi tayi nauyi a bakinsa ta danne harshensa da wani gingimeman abu mai girma sosai yake buɗe idanuwansa akanta wani irin bugu yake jin kirjinsa nayi bai san mai zuciyarsa take kokarin yi ba bai san abin da take kokarin dauko masa ba wanda sam bai yi tunanin haka ba.
A hankali take dago kanta tana kokarin ajje idanuwanta akansa cikin yanayi na TUHUMA tana jin yarda zancen da yake yi ya yanke wanda take jin alamun akwai dalili kamar wani abu ne daban ya hana shi furta abin da yake kokarin cewa ko da dai ita akaran kanta ba ta san ina ya dosa ba kallo daya tayi masa ta kau da kanta jin yarda jikinta da zuciyarta sukayi wani irin tsalle.
Girgiza kai ta shiga yi tana tura laɓɓanta cikin bakinta tana tsotsa kamar wacce ta samu alawa ta rasa mai zata ce masa bata san abin da ya dace ta ce dashi ba sosai take hango wasu abubuwa da suke rikirkita mata lissafin kwakwalwarta a idanuwansa sosai take jin abu mai girma game dashi sosai take hango kwarjini da haiba na dandatsa ko ina na cikin idanuwanta in ta dube shi can kasan makoshi ta fara kokarin furta wani abu a hankali laɓɓanta suka shiga motsawa.
“Ban san yarda zan fuskance ka na ce da kai komai ba, ban san da harufan da zan yi amfani wajan cewa da kai komai ba amm…”.
Da sauri taja numfashi gami da tafiya da sauran abin da tayi niyyar cewa.
Sosai ya ware idanu yana kallonta yana ganin yarda take datse laɓɓanta kamar wacce take tsoron furta wata kalma mai muni gareshi.
“Fadi mana  ko ya kike zo da maganar ki zan fahimta ba zan ajje ta a mizanin da bata dace ba”.
Ya fadi yana kara ware idanunsa sosai akanta wani matsayi yake jin ta na kara samu a gareshi sosai yake hango natsuwa da kula da kai tatttare da ita a hankali ya mike kan kafafuwansa yana duban in da Umma ke kwace tana barci Mu’azzam kusa da ita murmushi yayi kafin ya juyo ya dubi Mariya da take tsaye kikam! kamar wacce aka dasa gabadaya ta gama tafiya cikin wani irin yanayi, ba abin da take roko a ranta illa Dr.Karami ya tafi ko ta samu damar jan numfashi mai dauke da iskan Rahama.
“na tafi Mariya tun da yau na lura azumin magana kike yi”.
Yana gama fadin haka ya fara taka kafafuwansa kamar da gaske tafiyar yake yi so yake yi ta dago ta kalle shi haka kuwa akayi tana jin tafiyar tasa tayi nisa gabadaya ta dago da idanuwanta aiko sai suka sarke da nashi ba ta san lokacin da ta saki kara ba gami da ja da baya tana runtse idanuwanta sosai ta sanya tafukan hannunta ta kara rufewa wata irin kunya take ji tana yawatawa a dukkan sasssan jikinta ji take kamar kasa ta tsage ta shige.
Sosai ta bashi dariya ganin yarda tayi a hankali ya taka ya fice daga dakin yana faman sakin murmushi wanda shi kansa mamaki yake yi komai na Mariya na burge shi sosai da sosai.
****
“Yaa Allah!”.
Abin da ta furta kenan tana sakin murmushi gami da dafe kai bata san abin da ya shiga kanta ba gabadaya take jinta wani iri sosai take jin ta a wani irin yanayi in tana zaune ko suna tare da Dr.Karami rintse idanuwanta tayi gami da jan numfashi wani kamshi ne taji numfashin nata ya jawo mata ya kai mata cikin hanci a dan firgice ta ware idanuwanta tana Ambaton Allah tsoron ta daya Allah yasa ba Dr.Karami bane domin ko tantama bata yi wannan kamshin nasa ne amma bisa mamaki ba kowa da ta gani ajiyar zuciya tayi tana dungurin kanta domin ta tabbata sharrin tunani ne kawai da na zuciya suke mata haka.
*****
Dakiku masu dama ta dauka cikin motarta kafin ta fara kokarin buɗewa ta ziro kafafuwanta zuwa waje nan ma sai da ta ajje dakiku sannan ta fara kokarin ziro da gangar jikin zuwa waje ta mike kan kafafuwanta sosai take yawatawa da idanuwanta izuwa wajen da take tsaye tana faman yatsine fuska duk da bakin glass din da ya rufe mata idanu hakan bai hana bayyanar yarda take yi da fuskarta ba cikin wani irin yanayi ta tura murfin kofar gami da sanya mata secure kafun ta fara kokarin jan kafafuwanta.
Sanye take da wasu kaya riga da wando fitted sosai wandon ya matse ta wanda iyakarsa gwaurinta mai kalar pink rigar dake jikin yar shara-shara ce mai kalar white da hannayen rigar ves ne wanda hakan ya bayyanar da rabin kirjinta sosai da ilahirin damatsan hannayenta fuskarta dauke take da Make-up sosai hakan ya kara ƙawata fuskarta ta laɓɓanta sun sha pink din jan baki sai daukar idanu suke gashin kanta ya ci gyara sosai sai fama daukar idanu yake yi ta barbaza shi a gadon bayanta a hankali take takawa saman takalamanta masu matukar tsine sosai komai nata motsawa yake a duk lokacin da tayi taku daya.
Sannu a hankali har ta isa cikin wajan wanda kallo daya zakayi masa ka tabbatar da wani babban ma’aikace bene mai dauke da hawa goma sha biyu daga yanayinsa in ka kalla sai ka rantse ba a kasar najeriya yake ba.
Kofar da zata sada ta cikin wajan ta dosa mutane da yawa masu harkokin gaban su sai bin ta suke da kallo na mamaki har ta isa kofar glass da take watayawa da mutane domin zuwa duk wani bene da suke bukata.
Ba tayi kokarin barin baban Falon dake kasa na cikin ma’aikatar ba  domin ba ta bukatar haka koma ta bukata dole tayi hakuri a dalilin rashin sanin in da ta dosa ko ta shiga yau ne karo na farko da ta tako kafafuwanta zuwa cikin wannan waje yau ne farko da ta fara ajje idanuwanta akan wannan waje a zahirance yau ne kuma take bukatar duk wasu mafarkanta su tabbata yau ne take so ace sun yi gaba da gaba da shi yau ne take so komai ya zo kamar yarda ta jima tana burin abubuwa daban-daban kafin wannan rana tana so ace wannan rana ta kasance cikin ranakun da nasarrorin ta za su fara shawagi cikin duniyarta yau ne take da yakinin lissafinta zai fara aiki kamar yarda ta tsara komai nata…
“Madam!”.
abin da securty din wajan babbar kofar da suke zaune daya daga cikin su ya fadi kenan yana mai mikewa bisa kafafuwansa ya tsaya gabanta.
Da sauri ta dawo daga duniyar tunanin da take yi ta sauke idanuwanta gabadaya akansa tana wani yatsine fuska gami da da sauke glass din fuskanta kadan manyan idanuwanta farare fes suka sauka akansa sai da ta gama kare masa kallo kafin ta gyaɗa kai cikin nuna halin-ko-in-kula gareshi.
Shima bai damu da irin kallon da take masa ba haka ya sanya abin binciken dake hannunsa yana yawatawa dashi a sassan jikinta kafin ya dago kai ya dubeta yana mai bata hanya domin karasawa  wani murmushi ta saki wanda ita kadai ta san in da ya saka gaba a hankali ta kama Handle din kofar ta tura cikin wani irin taku na musamman wanda kallo daya zakayi mata kasan akwai abin da ta taka karan takun takalmanta bisa tayal din dake shimfiɗe a harabar wajan duk ya karkato  da mafiya yawancin mutanen da suke zazzaune suna gudanar da aiyukansu kowanne mutum daya akwai table a gabanda da kuma fiyal fiyal gefe guda kuma kwafuta ce girki tacin glass dinta take ƴawatawa da idanuwanta a dukkanin sassa da kowa ni mutum dake zaune sosai ta lura ita suka zuba wa idanu murmushi ta saki har gefen kumatun ta na loɓawa sosai taji wani abu na yawatawa a cikin kirjinta wanda take jin sa ba abin da ke cikin sa sai hango abubuwan da take tsammanin za su faru.
“Heyy”.
Abin da ta fadi kenan gaban wani table da wata mace ke zaune hankalinta gabadaya ya ta’allaka ga aikin da take yi  sanye take da jallabi mai kalar Ash ta nannaɗe fuskarta da kallabin jallabiyar fuskarta fayau ba wata kwaliyya ta azo a gani amma hakan bai hana bayyanar tsantsan kyan da Allah yayi mata baiwarsa ba.
A hankali ta fara dago kanta ta na saukewa a in da ta ji maganar sosai ta ware idanu ganin wacce take gabanta cikin yanayi na mamaki da wani irin haushi da ya kasa boyuwa har sai da ya fito cikin idanuwanta gyaɗa kai tayi kafin ta mai da kanta kan Aikin ta.
“Dr.Abdurrazaq Erena”.
Abin da ta fadi kenan tana mai wani kara bayyanar da wani murmushi dake fuskarta wanda kallo daya zakayi masa ka san ba a so ba.
Ba tare da ta dago da kallonta ba murya kasa kasa.
“Hawa na biyar hannunki na dama office mai lamba Uku”.
Ba ta tsaya ansa ta ba ta dauko kafafuwanta ta fara tafiya a haka har ta hau Abin da zai kaita wajan cikin yan sakanni ta isa bayan ta sauka ta kalli kwatance da kayi mata wata kofa glass ta hango sannan ta kalli samanta murmushi ta saki ta fara takawa a hankali ta isa sakatariya ta gani zaune tana ta faman aikinta hankali kwance kwankwasa kofa glass din tayi kadan tana mai kallonta cikin wajan a hankali ta dago kai ita ma ta sauke a kanta murmushi akan fuskarta lokacin da ta dago amma tana cin karo da wacce ke gabanta ta tsuke fuska hadi da jan guntun tsaki tana kau da kanta.
Sai da ta shafe sakanni kafin tayi mata alamun ta shigo a hankali ta taka ta shiga ta dan yi kasa da glass dinta ta shiga motsa laɓɓanta.
“Please wajan Dr. Abdurrazaq Erena nake bukatar zuwa”.
Kallon ban gane ba sakatariyar tayi mata tana mai kwaɓe baki kafun ta kau da kai hadi da fadin.
“Ya san da zuwan ki ne?”.
Shiru tayi ba tare da cewa komai ba na yan dakiku hakan ya kullar da sakatariyar da sauri ta shiga duba cikin kwafutar dake gabanta tana yawatawa da idanuwanta cikinta.
“Duk yau a cikin jerin mutanan da za su zo gare shi ban ga alamun da ke a ciki ba”.
Ta fadi tana mai dago kanta ta saukewa gareta.
a dan harzance ta sauke glass din ta sosai idanuwanta kan sakatariya kallonta take yi tana karantar yanayin da alamun so take ta samu wani tangarɗa da zata jona mata amma cikin nuna na fiki.
“ki je ki ce masa Areefa Saifullah ita ce take son ganin sa ya san da zuwana”.
Yanayin yarda take maganar a dake da yanayin bacin rai ya sanya sakatariyar ware idanu sosai gami da tallaɓe haɓa tana kallon yarda wannan mai kalar gangar ke mata magana akai.
A hankali ta mike saman kafafuwanta masu sanye da wasu takalma masu matukar tsine kamar za su karye a hankali ta fara taku da dan guntun suket dinta wanda iyakarsa guiwa kadan taɓe baki Areefa tayi tana bin dumemiyar matar da kallo wacce tayi biyunta.
Mintina kalilan sai gata ta dawo tana faman tsuke fuska.
“ki Shigo kofa ta uku ita ce in da yake ciki”.
Gyaɗa kai kawai tayi gami da wucewa tana taku ko ina na jikinta rawa yake yi lokaci guda ta canza tafiyar da take yi ita dai sakatariya sakin baki tayi tana kallon ikon Allah har sai da Areefa ta bace mata sannan ta saki ajjiyar zuciya ta koma ta cigaba da aikin da take yi.
“Areefa Saif…”.
Abin da ya fadi kenan yana hanzarin mikewa cikinsa har  ɓari yake yi ya zagayo izuwa in da take tsaye hannunta rike da Handle din kofar sai faman yawatawa da idanuwanta take yi cikin Office din har ya iso ya tadda ita nan tsaye sai faman sakin wani murmushi yake yi hakan ya bayyanar da wawulan hakorin sa daya na gaba da ya cire amma in ba ka gane ba sai kayi zaton wushirya ce ta buɗe sosai a jerin hakoransa masu dan duhu kadan.
“Ban yi zaton ai yau zaki zo ba, domin Alhaji Abdulwahab ce mani yayi sai nan da gobe”.
Ya fadi har lokacin idanuwansa na bin duk wani sashi na jikinta yana kallo kafun ya yi mata nuni da kujerun dake cikin office din alamun taje ta zauna sosai take kallonsa ta cikin glass dinta tana karantar yanayinsa sosai take hango komai kamar ma ya yuwu kallonsa take yi tun daga fuskarsa har kafafuwansa babban mutun ne don a kalla zai baiwa shekaru hamsin baya amma hakan bai nuna a fuskarsa ba saboda yanayin huta da jindadi da suka taimaka ma jikin nasa baki ne amma ba can ba yana da idanuwa masu dan girma sun dan yi ja kadan hancinsa ba dogo bane yana da fadi haka ma bakinsa mai dauke da manyan laɓɓa masu kalar baki baki haka zai tabbatar ma da yana shan wani abu.
Ba tare da ta ce da shi kala ba ta doshi cikin Office din sosai tana wata irin tafiya ta firgita duk wani namiji da yake gabanta har ta isa ta zauna ta ajje jakar dake hannunta gami da daura kafa daya kanta daya a hankali ta sauke glass din dake fuskarta gabadaya shima ta ajje shi kan Table din dake gaban kujerun ajje numfashi tayi alamun gajiya gami da dan dafe kai.
A hankali ya fara takowa in da take kallo daya zakayi masa kasan sosai Areefa ta tafi da guntun imaninsa jikinsa sai ɓari yake yi fuskarsa tana sakin murmushi idanuwansa kamar za su fado kasa.
“Areefa Saif…”.
Ya sake fadi cikin salo na yin kasa da murya kamar wanda yake rokon wani abu a gareta.
Kaɗa idanu tayi gami da dan daga girarta tana mai yawatawa da idanuwanta akan sa zuciyarta nayi mata wani tsalle na murna da jin wani dadi amma bata bari hakan yayi tasiri a fuskarta ba domin a gimtse take ba alamun dariya.
A hankali ta fara motsa laɓɓanta da wani irin yanayi tana mai kaɗa idanuwanta.
“Ya kamata ace ka koma ka zauna domin time dina a tsare yake akwai in da zan je ne”.
Ta fadi tana da murmushi a fuskarta da sauri ya ja gefe gami da ware idanuwansa sosai ba tare da yace komai ba ya koma can inda kujeransa take mai juyawa ya zauna gami da saka kan biro a bakinsa yana cizawa kujerar na watayawa dashi idanunsa akanta sai faman sakin murmushi yake yi a hankali ta kau da kai gami da tura masa fiyal din da ta zo dashi.
Hannusa guda ya kai yana janyo fiyal din yana mai sauke idanuwansa akansa buɗewa yayi a hankali yana yawatawa da idanuwansa a cikin tsayin minti daya kafun ya mai da ya rufe ya dan bugeshi kadan ya dago kansa ya dubi Areefa wacce ita ma hankalinta na kansa ta na kallon yarda yake duba fiyal din.
“Komai yayi daidai zaki iya fara aikin zuwa On Monday in kuma akwai Time din da kika zaba zaki iya amfani dashi…”.
Hannunta ta dan daga kadan tana dan murmushi.
“No ba ni da wani lokaci sai wanda ka yanke mani domin ina bukatar fara aikin ne akan lokaci ba tare da zabina ba sai zabin da kuka bani”.
Ta karashe tana mai mikewa kan kafafuwanta gami da daukar jakarta ta.
“Ina Godiya”.
Ta fadi tana mai kara sakar masa murmushi shi dai idanuwansa har zuwa lokacin suna kanta kamar wanda aka jona wa mayen karfe har ta fara taku amma bai motsa ba motsin Handle din da ya ji ne ya fargar dashi da sauri ya ware idanu yana kokarin tashi amma ina kafun ma ya kai ga tashi ta fice daga cikin Office din komawa ya yi ya zauna jikinsa ba kwari  hannu bibbiyu ya tallaɓe haba da su yana kallo kofar yana faman sauke numfashi a hankali.Sosai yake jin rashin natsuwa da kwanciyar hankali suna samun waje a filin zuciyarsa. Sosai yake jin wasu abubuwa masu kama da kibiyar ajali ga zuciyar na sassoke masa kirjinta. Sosai yake jin duk wata natsuwa tana fallewa da gudu daga filin rayuwarsa ta duniyarsa. Komai tafe yake da tashin hankali a yanzu cikin duniyarsa sosai yake tsammanin ba shi da wani farinciki a rayuwarsa cikin rashin zato da tsammani yake kallon komai na rugujewa a duniyarsa na farinciki kamar tubalin toka.
Sosai yake jin zuciyarsa na zafi da raɗaɗi in ya tuna abin da faru dashi kwanakin baya sosai yake ji kamar zuciyarsa zata yayyage daga kirjinsa yana jin yarda kunci ke wanzuwa a duk tuni da yayi akan abin da ya faru dashi sosai yake jin wani makaƙi mai daci daga makogoronsa har saman harshensa.
“Mu’iz ban san abin da yake damu na ba, ban san abin da ya ke kokarin dauke min farinciki da walwalar duniyata ba sosai komai ya ke kwance mani sosai nake jin bacin rai a cikin kokon zuciyata da ruhi…”.
Sosai yaji wani nauyi mai girma ya na samun mazauni a kirjinsa gami da saman harshensa gabadaya yaji maganar da yake kokarin karasawa ya kasa hakan laɓɓansa wanda suka dan bushe kadan ya tura cikin bakinsa yana cizawa hadi da rintse idanuwa ji yake yi kamar ba gaske ba gani yake yi kamar a mafarki ne komai ke faruwa dashi bai taba kawo wa kansa ƙaddara mara armashi zata fado masa ba ya yi zaton shi mai sa’a ne a duniyarsa dama rayuwarsa baki daya.
A hankali ya dago kansa dake sunkuye hannunsa rike da igiyar shisha da ya gama bankawa cikinsa a tunanin sa zata dawo masa da duniyarsa kamar da a tunaninsa komai zai wuce kamar ba ayi ba a tunanin sa za tayi masa maganin matsala ko ma yace matsalolinsa da suka tokare masa duniyar farincikinsa amma abun ya ci tura.
Nisawa yayi sosai har sai da kirjinsa ya harba.
“ba zan iya ce maka ga kwanakin da na dauka cikin wannan yanayin ba amma dai zan iya tuna ranar. Ranar da takasance mani SANADI ga duniyar natsuwa ta ranar da ta kasance mani tamkar BAKAR RANA mai cike da kwazazzaban  tashin hankali…”.
Nisawa yayi sosai yana kokawa da numfashinsa ji yake yi yana yawo dashi a wata duniya yana kokarin barin gangar jikinsa.
Mu’iz da ya tallabe haɓa idanuwansa kan Abokin nasa yana kallon yarda yake sauyawa lokaci guda mamaki abin yake bashi yarda yake ganin tashin hankali da wani abu wanda shi kansa bai san menene ba cikin idanunsa a hankali yake gyaɗa kai yana kara gyara zaman hannayensa a haɓarsa.
“Ban san in da bahagon zancen nan naka ya dosa ba ya kamata ace ka fito ka fada min dalili ba wai abin da kake ji nake so ba a’a yarda akayi komai naka nake ganin yana canzawa lokaci guda Me Ya Sa?”.
Ya ida yana mai yawata idanuwansa kan abokin nasa sosai  so yake yi yana hango wani abu wanda zai bashi karin haske akan lamarin amma sam bai gani ba sai tsagwaron tashin hankali da yake cikin idanuwansa da suka kaɗa sukayi jajir matuka.
“Mu’iz me ya sa ka kasa fahimta ta ya kamata ace duk wannan furucin da nake yi ka san in da na dosa ba wai ka nuna halin-ko-in-kula ba”.
Ya fadi yan gyada kai fuskansa na kara bayyanar da kuncin da yake ciki sosai zucyarsa ta fara kwaso masa wani lamari tana ajjewa a kokon kansa cikin mazaunin tunaninsa.
To da yake wannan hayagagar yace wa Mu’iz me mai zai ce masa me zai ce masa dalilin kuncinsa shi sai yanzu yake ganin wautarsa kamar yarda Khairiyya tace dashi taga rashin wayonsa da dabara akan wannan lamarin ba ta san abin da yasa yake zuzuta kankanin abu irin wannan ba wanda shan ruwa ma ya fishi sauki matuka.
Girgiza kai ya shiga yi yana jin wani sashi yana kambama lamarin sosai wanda hakan yake kara masa kunci a ransa da ruhinsa sosai yake jin wani hali na daban mai dauke da tsanani musamman in zuciyarsa ta bankado masa abin da ya faru gami da sunan da yake ji a ko wani sakan yake amsa masa kuwwa yake kara haifar masa da wasu abubuwa a zuciyarsa da ma gangar jiki baki daya.
“kai nake sauraro”.
Mu’iz ya katse masa tunanin da ya afka ciki yake yawata dashi wata duniyar ta daban.
Mikewa yayi daga cikin kujerar da ya cusa kansa ya saki igiyar shisha tayi kasa hannayensa duk biyu ya cusa cikin cikakkinyar suman kansa yana cakuɗawa gami da yatsine fuska kamar zai fashe da kuka a hankali ya fara taka kafafuwansa yana yawatawa cikin dakin  idanuwansa a rintse sosai kafin ya sake buɗe su ya sauke kan Mu’iz wanda shi ma idanuwansa na kansa.
Ba wanda ya sake kokarta cewa komai cikin su tsayin lokaci mai nisa iyakar nazarin Huzaif ya kasa samun abin da zai ce da Mu’iz wanda shi yake damunsa haka shima Mu’iz din yayi shiru ne domin jin abin da yake dawainiya da abokin nasa amma da alamun bashi da niyyar furta ko da kalma daya ce.
*****
“Sosai da sosai zan yi kewarki nan da yan kwanaki Mariya”.
Dr.Karami ya fadi hankalinsa da idanuwansa na kan Mu’azzam dake hannunsa yana yi masa wasa shi kuwa sai bangale baki yake yi.
Wani iri bugu Mariya taji kirjinta yayi wanda hakan ya haifar da tsayuwar abin da take yi sosai taji numfashinta yana sama da kasa kamar zai fice daga jikinta bakinta ta dan buɗe kadan daga sunkuyen da take domin samun daidaituwar numfashi ji take kamar numfashin da take shaƙa ta hanci yayi kadan gareta a hankali take juya fida din Mu’azzam da take wankewa cikin ruwan dake girke gabanta.  A hankali kalaman Dr.Karami taji suna haifar mata da wani irin yanayi gami da narkar mata da duk wani kuzari nata sosai ta fara jin wani gumi na keto mata daga cikin hanyoyin gashin dake jikin ta laɓɓanta ta tura cikin bakinta tana cizawa kadan-kadan jin furucin take kamar cikin duniyar mafarkinta jin su take kamar ba a zahiri ba ciza laɓɓanta da tayi hakan ya tabbatar mata da eh gaskiya ce tabbacciya.
“Ba ki so ko?”.
Ya fadi jin shirun nata ya yi yawa kallonta yake yi da duk kan idanunsa yana ganin yanayin da ta shiga ya tabbatar masa da haka din.
A dan razane ta dago kai ta dube shi kafin ta mai da kanta kasa tana yawata hannayenta cikin ruwan dake gabanta a hankali take girgiza kai tana motsa laɓɓanta alamun tana son cewa wani abu amma ta kasa shima ya lura da hakan.
“kawai shikenan ma tun da ba kya son tafiya  sai ki zauna ke ma ki  zama ma’aikaciyar asibiti “.
Yanayin yarda yake ajje furucinsa fuskarsa dauke da murmushi zai tabbatar da tsokanar da yake yi mata.
A karo na biyu ta sake dago kanta a dan razane kafun ta ware idanuwanta kadan akansa .
“Uhmm…”.
Sai kuma tayi shiru tana juya harshenta cikin bakinta idanuwanta akan Mu’azzam wanda shi izuwa wannan lokaci ita yake kallo.
“ko Bakya so?”.
Ya sake fadi da muryarsa dauke da dariya sosai yana kallon yanayin da take shiga wanda hakan ba karamin burgeshi yake yi ba sosai ya fahimci sanyin hali da rashin son magana irin nata sosai yake ganin magana tana yi mata matukar wuya in suna tare amma kuma yanayin ta da yanayin da take furta komai nata ba karamin tafiya yake da zuciyarsa ba ga ta dai ba wata babbar mace bane amma yanayin da da salon da take komai sai ka rantse wata mace ce babba wacce ta baiwa shekaru talatin baya.
“Na fa gaji Malama in kin gama ki zo ki amshi Mu’azzam tun da na lura zaman nan din bai ishe ki ba”.
Ya fadi cikin murya mai sauti yana mai kau da kai fuskarsa dauke da dariya amma yanayin muryar da yayi amfani da ita sai ka rantse bacin rai ne a cikinta.
Cikin hanzari ta mike jikinta har rawa yake yi zuciyarta na tsalle fuskarta lokaci guda tayi rauni sosai alamun ba ta so yanayin da ya nuna ba  cizon laɓɓanta tayi muryarta a raunane.
“Uhmm yi hakuri”.
Ta fadi dakyar tana mika hannu za ta amshi Mu’azzam gocewa yayi kafin ya juya ya kalle ta sosai yana murmushi.
“Kin fiye tsoro da yawa ban san dalili ba kina da shariya Mariya mai yasa ko ni ne…”.
ware idanun da tayi akan sa ya sanya shi sauri yin shiru yana dariya kafin ya juya ya fara tafiya ba tare da ya bata Mu’azzam din ba.
Sosai take ware idanuwanta akansa tana kallon yarda yake ajje takunsa a duk takunsa daya tana jin yarda zuciyarta da ruhi gami da gangar jiki ke amsawa kamar ita yake takawa da takalmar kafafuwansa sau ciki masu kalar ruwan kasa sai daukar idanu sukeyi da yanayin kyalli kirar kamfanin Gucci rintse idanu tayi sosai gabadaya taji tana juyawa kamar wacce aka saka a majanjawa take walagigituwa da ita ta dauki dakiku masu yawa a wajan kafun ta ware idanuwanta sosai wanda har zafi-zafi taji su na yi mata gyaɗa kai tayi gami da zubda ruwan da ta gama wankin fidar Mu’azzam ta dauki karikitan ta fara takun kan kafafuwanta a hankali kamar wacce kwai ya fashewa a ciki.
Sosai tayi nisa cikin tunani kawai ajje kafafuwan ta take a duk in da taji sun sauka duk taku daya sai taji numfashin ta na janta tana kwato shi.
“Mariya”.
Cak! ta tsaya kanta a kasa sosai taji muryar ta dakar mata kwanya gami da kara kawo mata wani abu na daban kuma zuciyarta lokaci guda ta buga.
Kwanaki kusan uku kenan rabon da   taji ko da muryarsa ta rasa dalili a zuciyarta tajima tana nazari anya ba laifi tayi masa ba ya dauke kafafuwansa yake guje mata ya daina son saka ta a idanuwansa sosai take lura da wasu halaye nashi na daban masu tsauri wanda a iya zaman ta dashi ta fuskanci haka mutum ne shi mai saurin fushi ga zuciya abu kadan ne yake sanya shi janye jiki ga mutum.
Takun da taji nasa yana tunkaro ta hakan ya kara sautin bugun zuciyarta  ta shiga kokawa da numfashin ta ta san shi mai alheri ne kuma ta gani sai dai ta rasa mai yasa cikin lokaci kalilan take jin wani irin abu game dashi sam bata so su kasance tare domin kuwa halayensa da yake amfani dasu sam ba su dace da ita ba sosai take jin ba dadi bata son mutum mai tsauri da sauri fushi akan abun da bai taka kara ya karya ba.
Ita dai a iyakar tsawon lokacin da suka dauka cikin asibitin nan daidai da rana daya ba ta tsammanin tayi abun da zai bata masa rai sai dai bata sani ba ko cikin rashin sani tayi masa ba daidai ba wanda sam bai kamata ace ya kama ta da laifi akan hakan ba.
“Mariya”.
Ta ji ya sake kira wannan kiran sai dai ya bambanta dana farko domin taji muryarsa da wani irin sauti wanda ta kasa tattance shi.
A hankali ta fara motsa laɓɓanta tana kokawa da numfashinta da taji yana sarkewa.
“Na’am”.
Sosai taji hucin numfashinsa a kusa da ita a dan tsorace ta ware idanuwanta da suke kasa kafafuwansa ta hanga sanye da takalma ash-colour sau ciki sai faman daukar idanu suke yi a hankali ta fara dauko idanunta tana bin sa da kallo tun daga kasa jikinsa sanye yake da suit Blue mai turuwa sai farar rigar dake ta ciki nektayal dinsa kalar ash-colour yarda takalminsa suke hannunsa duk biyu sanye suke cikin ajihun wandonsa saitin idanunsa ta sauke nata ganin sosai taji numfashin ta yayi sama da kasa ya koma daidai amma duk da hakan bai daina tsalle tsalle ba wani abu ne mai girman gaske take hangowa cikin idanunsa wanda tajima tana ganin hakan amma na yau ya bambanta sosai da sauran lokacin can baya kamar wacce ya rikewa idanu sam ta kasa daina kallonsa idanuwansa sarke da juna duk da nashi na cikin farin glass wanda ya kara ƙawata fuskar tashi duk da dai akwai rashin fara’a a cikinta.
“Uhmm…Dr.Aqeel…”.
Hannu ya daga mata ya wanzar da wani murmushi mai zafi a zuciyar mai yinsa girgiza kai yake yi kamar wanda aka fada masa wata magana da bai yarda da ita ba har zuciyarsa.
“Bana bukatar jin komai Mariya na lura kin yasar dani daga duniyar ki sam-sam kin daina tuna ni a rayuwarki sosai ki ka zare ni daga cikin duniyar rayuwarki ban san dalili ba..Uhmm…ni dai na san ban yi laifi ba amma kuma naga an dauki fushi dani Me Ya Sa?”.
Sosai take jin maganganunsa na haifar mata da wani irin yanayi mai wanzar da daci a zuciya sosai take jin haushin kalaman nashi ya fiye son kan sa da yawa ta lura da haka domin duk cikin kalamansa ba abin da ke yawarawa sai son kai ba ta san dalilin da yasa Dr.Aqeel yake yi mata haka ba bata san me yasa yake kokarin canza matsayin da ta samar masa a filin zuciyarta ba sosai take ganin girmansa domin kuwa bata ta ba manta alherin da ya saka mata a duniyar rayuwarta ba ita da makusantarta ba zata taba manta yarda ya dauke su ya kai su wani matsayi ba a lokacin da wasu suke kin su suke jifansu da wulakantaccen kallo sun mai da su marasa yanci da martaba a idanunsu shi ne yayi kokarin ganin an daina kallon su haka ta sanadinsa komai ya wanzu amma ba ta san me yasa yake kokarin canza komai nasa ba cikin kankanin lokaci wanda ko da wasa ba ta taba zaton hakan ba a filin zuciyarta.
Nisawa tayi gami da sanya hannunta guda tana dafe goshinta sosai take jin kanta na sarawa da duk wasu kalamai nashi sosai take jin rashin jindadin haka bata so zuciyarta ta canza mata matsayin Dr.Aqeel sosai da sosai take kallonsa a matsayin da take kallon Dr.Karami…
Rintse idanu tayi wani abu mai girma taji ya danne mata zuciya yana kokarin karyata zancen da take yi a yanzu.
Yaa Allah!
Ta fadi a can kasan makoshinta wanda take jin sa yana wani irin bauri-bauri.
“Ban san a wani matsayi kika ajje ni ba sosai da sosai nake ganin kin canza matsayin da nake dashi a idanunki da zuciyarki a can baya Me Ya Sa?”.
Ya sake fadi cikin wata irin murya wacce ta sanya Mariya saurin girgiza kai sosai take hango rashin adalci a furucinsa sosai take hango rashin dacewar hukuncin da yake yankewa a kanta sam! hakan bai dace ba ya kamata ace ya yi mata duba natsanake kuma ya ajje komai nasa na tunani a MIZANIN HANKALI kafun ya yanke mata hukunci sosai take ganin tsaurin hukuncin nasa wanda ta tabbata bai dace da ita ba.
Gyaɗa kai ta cigaba da yi tana tura laɓɓanta duk biyun cikin bakin ta.
“Dr.Aqeel bana zaton abin da kake fadi haka yake, bana zaton akwai adalci a wannan hukuncin da kake yankewa akaina. Ya kamata ace kayi nazarin komai sosai kake da matsayi na musamman a zuciyata ba zan manta alheri ba domin kuwa in har na mance alheri hakika na zama BUTULU wanda ba zan so haka ba”.
Yanayin da take furta duk kalma daya a furucinta tana faman rintse ido zai tabbatar maka da sosai take jin wani abu mai girma a zuciyarta wanda ba komai ya haifar da haka ba sai yarda lokaci guda take kallon mutumin da bata yi zato ba zai sauya daga yarda ta sansa a can baya.
“Yaa Rabb!”.
Abin da ya fadi kenan yana mai ware idanuwansa akanta sosai yake kallon yarda laɓɓanta ke motsawa kalamai masu taushi suna fesowa daga bakinta yana kallon yarda take cijewa da raunin da yake kawo mata hari amma sai tayi amfani da jarumar zuciyarta wajan fadi masa abin da take ganin shi ne ya dace sosai da sosai.
Gyaɗa kai yake yi yana faman yawatawa idanunwa a fuskarta dake fuskartarsa amma idanuwanta a dan kulle kadai wanda zara-zaran gashin idanunwan nata ya hana ya gane yanayin da kwayar idanuwan nata suke.
Shirun taji yayi yawa har kafafuwanta na kokarin kasa daukar gangar jikinta a hankali ta dago idanuwanta ta sauke su fes akansa batare da ko ɗar! ba yanayin kallon da ta gani yanayi mata ya kara rura wutar bugun zuciyarta amma taki bari hakan yayi tasiri a zahirance cikin karfin hali ta fara motsa laɓɓanta.
“Ban san abin da yasa kake kokarin daura min laifin da ban san dashi ba. Ban san abin da yasa kake kokarin canza komai ba. Kai kan ka kasani dole na damu da kai amma kuma kai na lura gabadaya ka sauya daga in da na san ka ban san dalili ba…Uhmm in laifi nayi maka kayi hakuri”.
Ta karashe fuskartar da wani murmushi wanda ita a karan kanta ba ta san yarda akayi ya samu gurbin zama a fuskar ta ta ba.
Ta fara gajiya da tsayuwar da take yi ta lura sam! shi gajiya bata fara rauni a kafafuwansa ba a hankali ta fara taku akan kafafuwanta da take jin su kamar na roba ne suke kokarin narkewa amma karfin zuciyar da tayi amfani dashi ya hana hakan tabbatuwa.
“Zuciyata…”.
Muryar Dr.Aqeel taji ta saki ihu da fadin haka wanda hakan ba karamin sakata cikin wani yanayi yayi ba matuka!
Cak! Ta tsaya da takun da take yi lokaci guda taji wani irin abu mai kama da ruwa yana bin sassan jikinta yana haifar mata da wata irin kasala mai kokarin zubda ita kasa a hankali taja jiki ta isa kofar dakin da suke ta dafa ta sosai take jin duniyarta na juyawa da sauri-sauri kamar zata watsar da ita wani waje mai nisan gaske.
Nisawa yayi yana kallon irin halin da ta shiga duk da jarumtar da ta sakawa kanta amma hakan bai hana wanzar da halin da ta faɗa ba nisawa yayi gami da cigaba da furucin nasa.
“Sosai take tausayin ki sosai take son ta ga kina cikin farinciki mai armashi…”.
Nisawa yayi wanda hakan ya sanya Mariya sakin Gwauron numfashi ta ciza laɓɓanta.
“Nasan da haka da dadewa shiyasa na baka matsayi mai girma a zuciyata kamar yarda kake fadi mani matsayina a gareka”.
Ta fadi tana mai yawatawa da hannunta saman kirjinta da take jin yana bugu kadan-kadan.
Da sauri ta ja kafafuwanta ta fada cikin dakin bayan ta sakar masa wani yaƙe wanda take zaton wai murmushi ne tayi masa wanda ta karyata hakan.
Sosai ya shiga gyada kai yana bin kofar da kallon kafun ya daga hannayensa duk biyun ya dafe kan sa da su yana mai faman juya kwayar idanunsa gami da ciza laɓɓansa.
Bai san abin da yake kokarin faruwa dashi ba. Bai san mai yake koƙarin saka shi cikin wani hali ba sosai yake ji a ransa akwai abin da ke shirin faruwa dashi a zuciyarsa zuciyarsa ta jima tana sanar dashi amma ya kasa gasgata haka ya dauki hakan a matsayin hauka irin ta zuciya mai kwashe kwashe bai san mai yasa yarinyar nan tunaninta yake wahalar masa da zuciya ba sosai yake kokarin yakice komai amma hakan ya gagara ganin haka yake a matsayin wauta na zuciya sosai yake ganin rashin hankalinta sosai yake son kin amsa komai da take yi  domin kuwa rashin dacewar haka ya ke gani a filin rayuwar duniyarsa.
Ya kaucewa ganinta ko zai samu sassaci akan komai ya gujewa haduwarsu domin ko zuciyarsa zata daina yi masa wannan labarin kanzon kurege da kullum take masa ya daina wanzuwa in da take ne a tunaninsa haduwarsu ne ke haifar da haka ashe ba hakan bane domin kuwa rashin haduwarsu hakan ya kara rura wutar abin da zuciyarsa take kokawar kawo masa filin rayuwarsa wanda sam ya ki amincewa da haka wanda ita kuma zuciyarsa ta hakikanace abin da take sanar dashi dole ya yarda dashi domin kuwa shi kadaine zai sassauta masa komai na filin zuciyar tasa dama filin rayuwarsa gabadaya…
Girgiza kai yake yina faman karyata zuciyarsa a hankali ya fara jan kafafuwansa da yake jin sun masa nauyi sosai, yana barin wajan domin ya lura zuciyarsa so take ta haukata shi da abin da yake zaton ba zai taba tabbatuwa ba har gaban abada…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *