ZURI’A DAYA BOOK 1 CHAPTER 5 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 1 CHAPTER 5 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE 

            Www.bankinhausanovels.com.ng 

Na so na nuna cewa Aziza ta dawo gida, amma gudun kada na haifar da wata matsala cikin ZURI’A sai na ja baki na nayi shiru, domin dana ce wani abu za a iya canza min abin da nake nufi. Hakan yasa na yi wata hikima nayi shiru, sai dai abu daya nasa cikin raina zan saka idanu akan rayuwai aziza a cikin gidan, domn ban so ta tana mace ta taso da tarbiyyar taurin kai. Haka, na yi wata hikima da wayo da dabara, nakan shiga gidajen sauran yaranmu ba don komai ba sai don kada su gano cewa gidan – Jafar kadai nake zuwa ayi tunanin da bana zuwa sai da jikata ta koma gidan sannan na tsiri zuwa, sai na mayar da abin cikin hikima yadda babu wani da zai zarge ni da wani tunani, yau naje ‘ gidan wannan gobe naje gidan wancan, hakan _yasa na fara janyo Aziza jiki na. . A duk ranar da naje gidan nasu nakan ganin abinda raina baya min dadi, domin sai ina ganin Hameed na yawan jan Aziza jikinsa, wata

rana idan tana zaune zai zagayo ta baya ya rungume ta a gaban kowa a cikin gida yakeyi.
Ranar nan na zo gidan nayi mata wayo na ce ta Zo muje gidan kawunta, nan nake mata fada cikin wayo ina cewa. Ki daina bari yayanki Hlameef

yana_ , kwanciya a jikinki ko ya rungume ki haka Kawai, domin yin hakan babu kyau. Amma idan wani _ guri yaje ya dade ba ki ganshi ba za ki iya yi masa oyoyo. Karki manta fa girma kikeyi, wata rana Abban ki ma da kansa za ki daina yi masa haka”.Www.bankinhausanovels.com.ng
Nan dai da dabara na ganar da ita, wata rana kuwa da na zo gidan da kaina naga tana — cewa ya daina yi mata haka, bata so. A gaban iyayensa haka suka ji kunya, amma sai suka basar kamar ba su ji me take fada masa ba. Da kamar abin ya yi sauki, wata rana da ~ naje gidan sai na ise shi da ita da kannen sa a falo ya kwanta daga shi sai singileti da wando gajere, Wai ya gaji suna yi masa tausa, ita kuma kadai ce mace ciki. Nan na zo na tsawatar masa, nace kada ya sake ya Kara yin haka, wai bai san ya fara girma ba? Ina fadin haka karaf a kunnen Jafar ya
shigo cikin falon, nan naga yanayin sa ya sauya. Nima sai nawa ya sauya, nace Jafar, wai me yasa za kuna barin yaran nan haka ne ba za kuna nunawa Hameed girma yake ba?” Ayi hakuri Gwaggo, insha Allah za a kiyaye. Kai Hameed maza tashi ka bar gurin nan”.
Ransa bace ya bar gurin yana kumburo. baki abinsa, jikina babu dadi muka gaisa ban wani jima ba na fito na tafi gidan Aisha. Nan na labarta mata da abin da yake faruwa, nan ta  kwantar min da hankali, ta ce.
“Ummah kada ki ji komai, na tabbata Yaya Asiya za ta lura da su, cikin ikon Allah Zai kare komai”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Duk irin nusarwar da take min na jita ne kawai, amma bana jin jikina da zuciyata sun amince min.
Kullum hankalina ba ya kwanciya da tunanin haka nake kwana nakce tashi, ganin rai na ya kasa kwanciya yasa na tari Mustapha da maganar, nan ya kwantar min da zuciyata da kuma nuna min matuKar muka nemi Aziza ta ° dawo gida za su zargi wani abu, amma shi da kansa zai je ya kwaso su tunda dama nasa ne. . Jin haka sai raina ya yi sanyi domin na tabbatar idan yaran a gurin Aisha suke babu abin da zai daga min hankali, don nasan tana da kula duk da kuwa ba yara ne a gabanta ba amma iyayi na riKo na gani. A cikin kwanaki uku da muka yi maganar sai ga Aziza da Hameed sun dawo gida gurin Aisha, sai a lokacin hankalina ya kwanta domin nasan dole ne Aisha zata na kula da su duk da kuwa irin tsohon cikin da take da shi. Tun sanda suka dawo Hameed ya dinga jinsa duk a takure, ko me yake yi sai yana ji  kamar ana takura masa. Haka ya koma shan ruwan tsuntsaye, yau yana nan gobe yana can, haka ya sabar ma Aziza yau idan bata ganshi ba gobe zata ganshi. Hikimar sa nana ko zata koma ta bishi amma sai ya ga ta Ki komawa, dolensa
yake dawowa, domin sam baya sakewa_ idan yana gidan domin baya samun dama yana hada jikinsa da nata. Ana cikin wannan halin ne Allah Ya sauke ta lafiya, ta haifo ki, kyakkyawa da ke kamar ‘yar uwarki Aziza, domin tun zuwanki duniya kowa ya zo ya ganki sai yace kina kama da Aziza, kamar daga jikinta ki ka fito don kama. – Haba! Murna gurinmu babu misaltuwa, muka godewa Allah da zuwanki duniya”. Haana tayi murmushi ta ce, “Kai Granny dama dani? A raina na zata wani ne ko wata, amma gaskiya kin iya labari”. Murmushi tayi ta ci gaba da cewa, “Aziza ta shiga murna da tsalle wai itama tanyi Kanwa su zamo su biyu, ta daina zuwa gurin kowa tunda ga shi itama an yi mata baby girl abin da take so kenan dama.
Tsananin Kaunar da Aziza take nuna miki ya yi yawa, domin bata barin kowa ya dauke ki sai ita, don sabodake ma sam bata son zuwa Makaranta, kullum sai anyi da gaske sannan take tafiya. a .
Haka Hameed shi ma ya shiga nuna miki Kauna, don haka kowa sai da ya nuna farin cikin zuwan ki duniya. Ranar suna aka rada miki sunana Raihanatu, domin dama burin Mustapha kenan ya haihu ya yi min Www.bankinhausanovels.com.ng takwara. Tun bayan sunanki da sati Aziza ce da kanta tace Ita zata zaba miki sunan da za ana kiranki, ita ce ta zaba miki suna Haana, madadin, ana kiran ki Raihanatu. Kowa yaji dadin sunan, haka kuwa kowa yake kiran ki har yanzu. ° Tunda aka haife ki Aziza bata Kara yarda ta je gidan kowa ba, haka hameed yayi zuciya tun da ya koma gida bata yarda ta bishi ba, . dalilin haka yayi fishi ya daina zuwa gidan gaba _ daya. Sai a lokacin ne hankali na ya yi matuKar kwanciya tun da Hameed ya fita daga cikin rayuwar Aziza, ni dai ban san meye dalili ba. haka kawai nake jin ban son naga tasu taZo daya, saboda wasu dalilai da yadda nake jin wani abu a cikin rai na.
Haka kullum zai zo yana ta lallaba ta akan” ta dawo gidansu don yafi son yana ganinta kullum a kusa da shi, shi idan yana nan shi sam a takure yake saboda haka ta bar nan su koma gida. Ta Ki yarda ta ce shi ya dawo dai ita ba zata iya tafiya ta bar Haana dinta ba, dole ya haKura ya rabu da ita.
Cikin watanni biyu zuwa bakwai sai da muka samu Karuwar haihuwar yara mata har biyar, Haj. Bara’tu ta haifi Fadila, Asiya Haaya, Aisha ke, Maryam Rauda, Habiba matar Mukhtar ta haifi Sameeha.
Mun yi farin ciki Zuri’a sai Kara habaka take, sai ya kasance gida dai dai ne a wannan lokacin ake haifar da namiji.  Shekarun ki biyu da watanni a duniya, lokacin ita kuma Aziza ta shekara sha uku cif, kasancewar ta mai garin jiki ga kuma jin dadi da kwanciyar hankali babu abinda yake damunta, nan da nan ta fara zama budurwa, haka nan kyanta ya sake bayyana, kowa yana yaba kyawunta da surar da take da shi. Loakcin shi kuma Hameed yana da shekaru sha tara domin anyi-anyi da shi a fitar dashi waje karatu ya ki wai shi a nan zai yi wai don ya gama karatun sa ya auri Aziza, domin shi ya ce ita zai aura. Haka kowa ya yi murna domin dama kowa ya saka ran haka, ba don komai ba sai don sanin shakuwar su da irin nuna Kaunar da ya yi mata tun ranar da aka haife ta haka dama iyayen suka Kulle cewa za a hada su aure idan har sun girma. .
Tun lokacin da Aziza ta fara zama budurwa shi kenan Hameed yake kiranta da_ mata, baya jin kunya a gaban kowa da haka yake kiranta kasancewar ita din mai kunya ce a duk lokacin da ta ganshi cikin jama’a sai tana buya don bata so yana sa ta jin kunya. Haka zai taso wata rana haka zai ke rikota yana son hada ta da jikinsa, ita kuma sai tana ki tana fada masaya daina mata haka, ita bata so Www.bankinhausanovels.com.ng
Nan zai shiga bata hakuri idan yaga ta Bata rai, ranar nan kawai sai gashi abin ya faru a idanuna, hankalina ya yi mummunan_tashi, amma abin da yasa na Kara samu nutsuwa jin irin kalaman da Aziza tayi masa amfani da su. Hameed wai mene yake damun ka ne haka? Na fada maka ka daina yimin inn wannan
wasan, idan ba haka ba wallahi zan kai Karar ka gurin Abba. Sai kace kai ba Musulmi bane, idan ’ ka kuma yi min baka wallahi zan daina yi maka . magana har abada tunda kai baka san abin da ya dace ka yi ba da wanda bai dace ba”. Ina kallo ya durKusa yana bata haKuri da Kyar ta saurare shi, ganin yadda tayi masa yasa na saki raina na tabbatar ko ina Aziza take zata iya kare kanta da mutuncin ta, hakan yasa na rabu da ita ban bari sun ganni ba. Amma daga – baya na bita ta cikin hikima ina fada mata tana hankali da kanta gurin kowane irin da namiji, sai dai ban nuna mata dawa nake nufi ba, amma ganin ta fahimci abin da nake nifi kuma na san dole ne ta kawo Hameed cikin ranta, don haka sai na Kara samun damar ci gaba da yi mata nasiha don naga abin da nake fada mata yana ratsa ta. Tun daga lokacin na Kara ganin tana santseni da yayanta Hameed, hakan da na gani sai yake Kara sa ni sakin raina, domin shi kansa ya daina shisshige mata. Kullum rana ta Allah Aziza Kara girma take yi tare da bayyanar kyawunta, domin lokacin makerin budurcinta ya fara Kera ta, lokacin ne kyanta yake Kara bayyana, kowa yana yabawa da irin kyan da Allah Yayi mata. Duka a lokacin shekarunta na haihuwa sun dan dara sha hudu, idan kika ganta a lokacin za ki yi mamakin saurin girman nata. Www.bankinhausanovels.com.ng
Nutsuwa da kamun kai kullum daduwa suke a gurin ta, kaf cikin Zuri’ar babu wanda . baya Kaunar halinta da irin kyawun halinta, don haka kowa yake jin yana Kara son ta saboda ladabin da take da shi ga zumunci da nacin son ‘yan uwa. Da wuya a garin Allah ya waye bata je dukkan gidajen kawun nanta ta gai da su ba, idan bata je da safe ba da yamma, wata rana har dare take zuwa ta gaida su, wadanda take tunanin ba zata gansu ba sai a wannan lokacin.
Hakan yasa Aziza take Kara farin jini ga kowa, don bana jin da akwai wata diya da ake so , da Kauna a cikin Zuri’ar mu domin ta ko ina yabon halinta ake yi. A cikin ‘yan kwanakin nan haka nake kwana na tashi da wasu munanan mafarkai marasa dadi, domin yinsu nake yi barkatai, sai na kasa gane manufar su, sai idan na tashi na bisu da addu’a akan koma dai meye Allah Ya kare mu. Na kasa nutsuwa da na fara ganin duk lokacin da zan yi mafarkin sai na hango Aziza cikin wani irin yanayi mara dadi, don haka nan da nan na shiga addu’a akan ko ma dai meye Allah Ya tsare mu. ashe tashin hankali ne mai tsuma rai da bakin ciki, wanda ba zai taba goguwa ba cikin Zuciyar mu, sai dai babu yadda bawa zai yi da Kaddara, dole idan aka rubutata sai ya faru. Wata rana Hameed yana:gida ya kasa samun nutsuwar ransa, ga so da Kaunar Aziza yana ta addabar sa, ya kasa samun nutsuwa, bugu da Kari ga gudun da tayi masa na nisantar sa da tayi, domin sam yanzu bata barinsa yana naniKarta kamar da. Ranar anyi wata rasuwa cikin dangi kusan kowa yana can ta wani yaro ne dan wajen Lukman, to duk yawanci ana can. Haka Aziza ta fito rike da ke a hannunta, domin kunyi matuKar
shaKuwa da ita, sam ba kwa son rabuwa, lokacin shekarar ki uku da ‘yan watanni. Www.bankinhausanovels.com.ng
Nan ta hango hameed tsaye shi kadai yana ta kai komo a wajen gidansu, yana ganinta ya wani dimauce hade da jin wani mugun sonta da sha’awarta duk a lokaci daya sun tsirga masa, ganin irin kyan da tayi, yaji kamar yaje ya rungumeta wanda yake ganin yin hakan ne zai sa ya samu nutsuwar halin da yake ciki. To amma babu dama don tuni ta toshe masa hanyar samun wannan damar. Cikin wani irin yanayi yake mata magana, ya ce. Matar daga ina haka? Kamar kuwa kin san ke na fito ko zan hango ki sai gashi kuma na ganki”. Tayi murmushi ta ce, “Ba wani nan, don ka ganni ne yasa ka ce haka. To daga gidan rasuwar nan nake Haana ta hana mu sakat shi ne Ammi ta ce na zo gida da ita mu zauna ko tayi barci, don taga alamun fita kawai zata yi a gurin, gashi ta ishe mu da surutunta da baya Karewa, don ita ba zata gane wane hali ake ciki ba. Kuma nima dama na gaji, ji nayi kai na ya fara ciwo shi ne nake son mu koma gida mu dan runtsa kafin su dawo, gashi kuma rana ta soma takewa”.
““(Okay) nima ban jima da dawowa daga gidan ba, don bana son hayaniya. Oya to muje na raka ku gidan mana”, A’ah, da ka ma barshi mun Karasa, kaima kaje ka huta”.
Bai bata amsa ba ya sa hannu ya dauke ki ya saka ki a kafada suka jero suna hira, ke kuwa kin fara surutunki kafin ku Karasa har bacci ya dauke ki. A haka ya kai ku har Kofar gida, nan ya tsaya yana janta da hira har ta soma gajiya, nan ta ce masa ya miko ki taje ta kwnatar dake Www.bankinhausanovels.com.ng
Cikin sauri ya mika mata ke, sai da yayi wayon da ya hada hannunsa da Kirjinta, sai tayi kamar bata san yayi ba, don ko kallon sa bata yi ba. A tunaninta cikin rashin sani ne, amma tana ‘daga ido suna hadawa sai ya sakar mata ~ murmushi, nan take taji wata kunya ta kama ta, ta dai dake ta ce. .
“Na gode, kaje abinka zamu shiga don na fara jin kaina na sara min”.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *