UKU BALA’I CHAPTER 6

UKU BALA’I CHAPTER 6

                     Www.bankinhausanovels.com.ng 

Ta jima sosai cikin soron gidan nasu tana jan numfashi, yanayin da take jin kanta a ciki a wannan lokacin ba zata iya cewa ga yarda yake ba ta san dai tana cikin wani irin yanayi na rashin natsuwa gami da ciwon rai.+

Bata san ya zata yi da Dr.Aqeel ba bata san mai ya kamata tayi masa ba zuciyarta take jin tana shiga wani irin mataki mai raunin gaske yana haifar mata da yanayi na shiga ruɗani sosai take jin wani fili a zuciyarta ya na baiwa Dr.Aqeel matsayi da kalamansa wanda take jin su sun fi komai daga mata hankalin a wannan rana.

Hannunta daya ta saka cikin baki tana cizawa kafun ta fiddo shi tana yarfewa fuskarta na ya mutsewa da wani irin yanayi mai girman gaske a gareta. Ta jima kafun ta fara jan kafafuwanta da take jin su kamar ba nata ba kamar ba jikinta suke ba sosai take jin gajiya a cikin su ji take yi kamar za su watsar da ita kasa a hankali ta kai hannunta ta dafa bango tana tafiya a hankali har ta karasa shigewa cikin gidan.

“Na ce karuwanci kike koyawa  ‘yarki tana bin gardawa kamar wata karya kin ce ba haka ba yanzu me ne ne wannan Iyee nace yanzu menene wannan ai duk wanda ya ga

wadannan kayan ya san da walakin goro a miya ba yarda za ayi a dauki wannan uba uban kayan a baku su haka zikau ba tare da kuma an ci ribar ku ba”.

Maganganun da suka shiga dukan kunnuwan Mariya kenan a daidai lokacin da ta iso tsakar gidan ta tsinkayo muryar Goggo Marka cikin dakin su wani tashin hankali ne taji zuciyarta da kwanyarta sun dauka lokaci guda sun tsaya cak! da aikin da sukeyi lokaci guda duk wani

magudanan jinin ta suka tsaya komai nata take jin sa ya sauya ji take yi kamar ba a duniyar nan take ba ji take yi kamar ba RAI DA RUHI a gangar jikinta juwa taji ta fara daukarta lokaci guda ta durkushe a wajan cikin wani yanayi tana mai jan numfashi da k’yar yana fizgar kansa shi kuka take so tayi amma zuciyarta da idanuwanta sun ki bata damar haka sai zafi da raɗaɗi da take jin sunayi kamar zasu tayar da kan su daga gareta.

Hannayenta ta saka a saman kirjinta tana shafawa domin ji take kamar ya tarwatse gabadaya idanuwanta a runtse  a hankali ta fara kokarin tashi tana jin yarda kirjin nata yayi mata wani irin nauyi da abu mai girman gaske wanda take jin yana rinjayarta.

“Kin ce ‘yar ki makaranta take yi  ita ga wacce ta fi kowa son ilmi ko yanzu tsakanin ki da Allah Habeeba wannan shine makarantar da take zuwa don na tabbata a hanyar fitar da take yi ne ta hadu da wanda yayi mata wannan hidimar kuma na tabbata ba haka kawai bane sai da ta biyasa kafun ya bayar”.

‘Yaa zuljalalu wal’Ikram Ya Hayyu Yaa Kayyum’.

Abin da take jin wani sashi na zuciyarta na fadi kenan har ta iso bakin kofar ta tokare hannayenta a saman goshinta ji take yi kanta kamar zai tarwatse idanuwanta a runtse ta shiga ajje numfashi mai girma gaske wani abu taji ya zo mata makoshi ya tsaya tana jin yarda yake kartar mata ko ina na kirjinta har zuwa makoshi.

“Haba mana Goggo Marka ta ya kike tunanin zan jefa ‘yar da na haifa a cikina cikin wannan mugun yanayi ribar mai zan samu a ciki”.

Muryar Umma ta tsinkayo ta fadin haka muryarta cikin yanayi mai kama da kuka da sauri ta dago kanta ta ware idanunta kafun ta dage labulan dakin tsaye ta hango Goggo Marka sai faman tsaki take ja tana jifan Umma da mugun kallo jin motsi ne ya sanyata juyowa ganin Mariya ya sanya ta sakin wani murmushi na mugun kafun ta shiga tafa hannayenta.

“Uhmm a hakan kamar gaske musa a baki fir’auna a zuci”.

Ta fadi tana yatsine fuska kafun ta dan rangwafa inda kayan suke tana bincike kafun ta shiga ware wasu a gefe guda sai da ta ware masu isarta sannan ta sunguma tana duban su Umma.

STORY CONTINUES BELOW

“To mu ma dai bari mu ci albarkar kacin bariki ko kin san ko ina kayan alheri suke dadi gare su Allah ya karo mana irin su masu kyautatawa”.

Ta na gama fadin haka tayi hanyar yo wa waje Mariya da tayi sumar tsaye bangazar da taji anyi mata ya dawo da ita hayyacinta a rikice ta dubi Goggo Marka sannan ta dubi Umma wacce ta zabga tagumi hawaye sai shatata suke yi a fuskarta bakin ciki da takaicin duniya duk sun cike mata zuciya gabadaya ta hargitse sosai fuskarta ta ke nuni da tsananin tashin hankalin da take ciki ganin Mariya na dubanta ya sanyata saurin dauke hawayen da suke zubo mata tana sakin wani yake wanda yafi kuka ciwo.

Wani irin kuka ne Mariya taji yana zo mata a daidai wannan lokacin hannu ta saka ta toshe bakinta tana karasawa cikin dakin durkushewa tayi gaban Umma da wani irin yanayi na tashin hankali mai girman gaske laɓɓanta na rawa ta shiga motsa su.

“Na Shiga Uku wanna wacce irin rayuwa ce take kokarin tunkaromu a daidai wannan lokacin wannan wani irin yanayi ne mai sanya ciwon rai ya sanyo mu gaba”.

Hannu Umma ta daga mata alamun tayi shiru kafun ta fara magana cikin yanayi na rauni.

“Ni ban ga abin shiga uku ba don haka ki daina ambatar mana Uku a nan kin ji ko kina dai bata hawayenki ki share su domin in har kika ce zaki cigaba da zubda su to na tabbata zaki shekara dubu a haka in dai kina cikin wannan rayuwar duniyar nan”.

Fakare tayi da kunnuwa ta zubawa Umma idanu kamar wacce taga bakuwar fuska kafun ta shiga jan hanci kamar zata fizgeshi daga fuskanta.

“Haka nake nufi domin kuwa in har kace ba zaka dauki abin da ALKALAMIN ƘADDARA ya kawo maka rayuwa ba to kana tare da tashin hankali mai girman gaske”.

Hawaye suka sake balle mata domin ji tayi komai ya kwance mata zuciyarta na wani irin zugi da raɗaɗi.

“Amma Umma..”.

“Haba mana Mariya”.

Tayi sauri katseta kafun ta ja numfashi da take jin sa da wani irin yanayi mai zafi gaske.

“Ina kika baro shi”.

Runtse idanu tayi jin zuciya ta bugu kafun ta ciza laɓɓanta tana jin wani abu mai nauyin gaske na danne mata kirji da zuciya.

“Ba shi bane”.

Ta fadi a raunane kamar zata fashe da wani sabon kukan wanda ya fi wanda ta gama ciwo.

Ware idanu Umma tayi cike da mamaki jin abin da Mariya tace.

“Kamar ya bashi bane to waye?”.

Kamar ba zata ansa ta ba sai kuma tana ja numfashi ta fesar.

“Dr.Aqeel ne”.

Duban sosai Umma ta shiga yi mata kamar mai son karin bayani akan abin da ta fadi yanayin da ta nuna ya tabbatar mata akwai abin da yake faruwa ganin sai yatsi ne fuska take yi tana cizon laɓɓa.

“Me ke faruwa na ga sai dakune fuska ki ke yi?”.

“Bakomai yace yana gaishe ki”.

“Mariya!”.

Umma tafadi cikin wata irin murya mai zurfi har sai da gaban Mariya ya yanke ya fadi dago idanuwanta tayi da suke kasa ta dubi Umma da tayi mata kuri da Idanu da tuhuma cikinsu.

STORY CONTINUES BELOW

“Akwai abinda ke damun ki bayan Dr.Karami ki fada min ina bukatar sanin ko mene ne na gaji da wannan halin da kika aro ki ka saka a filin rayuwarki wanda sam! ban ga amfaninsa ba”.

Gyaɗa kai ta shiga yi kamar zata rushe da kuka zuciyarta da kwakwalwarta take jin su kamar za su kama da wuta saboda wani irin tashin hankali mai dauke da turiri take ji yana wanzuwa acikinsu.

“da ke  nake magana Mariya na gaji fa”.

“Umma!”.

Ta fadi cikin wani irin yanayi da rauri a muryarta kafun ta nisa ta na cizon laɓɓanta.

“ba abin da yake damu na…”.

“ban yarda ba…shikenan ma komai ya shige ki bar komai a zuciyar ki hakan daidai ne”.

Umma ta fadi tana mai kokarin mikewa kayan dake tsakar dakin ta shiga janyewa tana ajewa gefe guda ganin haka da Mariya tayi ta san Umma haushin taji shiyasa ta rabu da ita da sauri ta mike tana kokarin taya Umma kwashe kayan hannu ta daga mata ba tare da ta kalle ta ba.

“Bar shi kawai ki zauna ki yi tunanin abin da ya dace ki fidda kan ki daga damuwar da kike ciki tun da bakya bukatar abokin shawara a filin a rayuwarki”.

Jikin ta lokaci guda yayi sanyi jin abin da Umma tace hannu ta sa tana goge kwallar da taji sun kawo mata ziyara idanuwa.

“Kiyi hakuri Umma..”.

“ni ba kiyi mani komai ba Mariya ki je ki zauna ki huta ni na bukaci haka”.

Ba yarda ta iya domin yarda ta ga Umma na maganar ta san har kasar zuciyarta don haka a hankali ta ja jiki ta zauna in da Mu’azzam ke kwance yana faman barci abun sa.

Bata san mai ya dace tayi ba, ba ta san mai ya kamata ace tayi a filin duniyar rayuwarta a yanzu ba komai take ji yana sauya wa komai take ji yana canzawa a filin  rayuwarta ji take yi kamar ba ita ba jikinta take ji yana yi mata wani iri kamar wacce bata da lafiya zuciyarta take ji tana yi mata nauyi kamar wacce aka daura dutsen dala.

Ta jima cikin wannan yanayin kafun ta lura da har Umma ta gama kwashe kayan ta bar mata daki hannu bibbiyu ta daura a fuskarta ta zabga tagumi domin kuwa gabadaya take jin tunanin ta ya tsaya komai na ta ya tsaya cak! ba abin da take hangowa sai tashin hankalin dake gabanta yanzu bata san ina Dr.Karami yake ba a yanzu tsoron ta daya kar ya sake komawa ba tare da sun hadu da juna ba.

*******

“Umma Zan je gidan su Baseera”.

Mariya ta fadi cikin yanayi na fargaban abin da Umma zata ce domin tun jiya da ta shareta har yau bata sake tsayawa sun yi wata magana mai tsayi ba bayan gaisuwa da tayi mata da safe.

“Allah ya kiyaye hanya ki gaida Hajiyar ta Baseera”.

Abin da ta fadi kenan ba tare da ta dube ta ba hakan ya sanyayata jikin Mariya ta shiga gyaɗa kai da susar gefen fuskarta kafun ta shiga motsa baki.

“Umma don Allah kiyi hakuri…”.

“Mariya haba mana nace miki bakomai ki tafi kawai”.

Jin abin da tace ya sanya ta duban Mu’azzam dake hannun Umma hannunta kai ta shafi fuskarsa tana sakar masa murmushi kafun taja jiki ta fice daga cikin dakin.

STORY CONTINUES BELOW

A tsakar gida ta tsaya tana gyara hijabin dake jikinta domin ji take yi kamar bai zauna daidai ba a

hankalinta juya ta dubi bangaren su Goggo Marka Hafsi ta hango tsaye daga ita sai daurin kirji kamar wata uwar mata ta kafe ta da idanu tana faman yatsine fuska kau da kai tayi kamar bata ganta ba da sauri ta zira takalmanta ta fice daga cikin gidan domin a yarda take jin kanta ba ta bukatar wata magana ta sake shiga tsakanin ta da wani har ta isa gidan su Baseera.

Tafiya take yi a hankali domin isa bakin layi ko za ta samu napep din da zai kai ta Unguwarsu Baseera taji take yi zuciyarta da kwanyarta sai faman dauko mata tunani suke yi wanda sam bata so ace sune a kanta ba yanzu.

Kamar daga sama taji ana yi mata Horn bata yi tunanin da ita ake ba hakan ya sanyata kara sauri tana komawa gefe duk a tunanin ta wani ne a bayan ta yake mata horn domin ta bashi hanya amma ina ta ji an ci gaba da yi ba kankautawa hakan ya sanyata tsaya wa cak! waje daya tana daga kanta don dubin ganin abin da ke faruwa motar Huzaif ta hango yayi parking yana kokarin fitowa wata irin faduwar gaba taji tana zo mata lokaci guda wanda ita a karan kanta ba zata ce ga dalili.

Dubansa ta shiga yi cikin wani irin yanayi wanda ba za ta ce gashi ba amma dai tana jin yarda zuciyarta ke bugawa a dukkanin sakan

idanuwanta take yawatawa a kasa tana tunano yaushe rabon ta dashi sun kwana biyu ba su hadu ba sosai ta lura da yanayinsa kamar mara lafiya domin tafiyar ma kamar mai koyanta haka yake yin ta har ya iso in da take tsaye tana faman jan numfashi.

Lokaci guda idanuwansu suka sarƙe da juna aka rasa mai dauke nasa tsayin lokaci suna a haka kafun Mariya ta ja dogon numfashi ta fesar fuskar ta cikin yanayi na karan kadahan.

“Uhmm Huzaif dama kana duniyar nan”.

Hakan da ta fadi da yanayin da tayi maganar ba karamin sanya Huzaif cikin wani irin yanayi mai armashi a hankali ya shiga motsa laɓɓansa fuskarsa na wanzar da wani farinciki mai dauke da fara’a jan numfashi yake yi yana fesar wa idanunsa akan Mariya zuciyarsa yake ji tana daukar kanta tana kaiwa wani mataki mai girman gaske yanayin da yake kallon Mariya wani farin ciki da muradan jindadi yake jin sa a ciki.

Ya sani yayi kewar Mariya ba kadan ba zuciyarsa tayi jinyar rashin ta sosai ya shiga cikin wani hali na rashin jindadi sosai duniyar yake jin ta wani mataki a kwanakin baya da yake zaune yana jinyar kan sa dalilin rashin lafiyar da ta same shi.

” Baki damu dani ba Mariya shiyasa sam rashi na bai d’ad’a ki da kasa ba”.

Ya fadi yana mai dan haɗe rai kanta ta dago ta dube shi tana mai yatsine fuska kafun ta ja numfashi.

“akan mi zaka ce haka wa na sani na ka da zan tambaya ina kake so naje  ko so kake yi na bi layi ina cigiyar ka Huzaif bai dace ka yi mani wannan maganar ba sam”.

Kuri yayi mata da idanu yana kallon yarda take motsa laɓɓanta kalamai na fitowa wani irin farin ciki yake ji yana sake zundumawa a ciki.

“Allah ya baki hakuri amma dai zaman tare ai bai ce haka ba ko?”.

Ya fadi yana murmushi kau da kai tayi tana mai yatsine fuska sam bata bukatar magana ba ta so ace ta sake gamuwa da wani a daidai wannan lokacin ba tafi bukatar su hadu da Baseera domin ita kadai ne take so su zauna domin sanin abin da ya dace ita kadai take tunanin zata fada wa abin da yake kokarin faruwa da ita ko ma tace ya faru da ita…

STORY CONTINUES BELOW

“Ina su Umma da Mu’azzam?”.

Maganar Huzaif ta katse mata tunanin da ta jefa kanta a ciki.

“Uhmm suna gida suna lafiya”.

Ta fadi tana kokarin raɓashi ta wuce ganin haka ya sanya shi saurin dubanta.

“Meye haka kuma Mariya yake kike kokarin tafiya…wai ma ina zaki kike wannan saurin”.

Yanayin da yayi maganar kamar da bacin rai a ciki ita hakan ita ma ya so bata mata rai jin irin tambayar da yake yi mata kamar shi ne ya ajje ta ba ta ansa shi ba illa duban sa da tayi ta kau da kanta.

“Ina Zaki je ne?”.

Ya fadi ganin kamar ranta ya so baci yayi kasa da muryar.

“Unguwa zani shiyasa nake sauri bana so na bata lokaci a bakin titi”.

Gyaɗa kai yayi yana dubanta kafun ya numfasa cikin d’ard’dar.

“muje mana in kai ki ko”.

Wani duba tayi masa wanda sai da yaji yan cikin sa sun motsa dama ya san za ayi haka da sauri ya kau da kai don ba zai iya jure irin kallon da take masa ba zuciyarsa wani irin yanayi take fadawa mai girman gaske.

“Don Allah mana”.

Ya sake fadi yana mai hada hannayensa waje daya alamun roko.

Girgiza kai tashiga yi tana mai taku a hankali za ta bar wajan gabanta yasha yana mai harɗe hannayensa a kirjinsa idanuwansa ana ta tana watsa masa kallon ban son haka.

“Mariya wai shin ko laifi na sake yi ne ake kokarin hukunta ni ta wannan hanyar?”.

“ko daya kawai dai bana ra’ayin abin da ka zo mani dashi ne nagode kawai kayi tafiyarka”.

Ware idanu yayi jin abin da tace sosai yake dubanta yana kallon yadda ta kara haɗe fuska kamar hadari amma hakan bai hana kyanta ƙara bayyana ba wani irin kwarjini yake ganin tana yi masa  wanda ya shagalar dashi ga kallon ta har bai san lokacin da ta raɓashi ta wuce ba.

Firgigin yayi  ya dawo hayyacin sa ganin bata wajan ya yi saurin juyawa can ya hange ta tayi nisa dashi kadan.’Yaa Rabbi’.

Ya ambata yana takunsa cikin hanzari ya isa in da motasa take  ya shige tare da yi mata key bayan yayi ribas ya bi bayan ta da gudu cikin yan sakanni ya isa in da take tsaye tana kokarin tsaida wani mai Napep parking yayi ya fito ya iso in da take tsaye suna magana da mai Napep din ba tare da yace mata komai ba yace dubi mai Napep din.

“Yi hakuri don Allah yi tafiyarka”.

Ya fadi yana mai hade fuska da sauri Mariya ta juyo ta dubeshi da wani irin kallo ganin yarda ya hade fuska ita ma sai ta hade.

“Ya haka ya za ayi in tsaida abun hawa ka ce ya tafi ina ruwan ka dashi?”.

Bai tanka mata ba illa nuni da yayi mata da motarsa alamun ta je ta shiga.

“Ba zan shiga ba kaji ko Allah ba in da zani Huzaif bana bukatar takurawa bana son abin da zai bata mutuncin junanmu”.

“kawai Malama ki je ki shiga mu tafi ya za ayi ace ina waje kuma ga abin hawa a tare dani amma ki tare wani mai Napep wannan ai ba mutuncin ki bake”.

STORY CONTINUES BELOW

‘Ikon Allah’.

Ta fadi a ranta ta na sakin guntun murmushi kafun ta dubi Huzaif da ya haɗe rai kamar wani hadarin dake shirin zubda ruwa.

“wai don Allah Huzaif me yasa kake son takura mani ne na ce maka nagode ba zan shiga motarka ba to ka hakura mana”.

“Ban san wannan zancen ba kisan Allah in har baki shiga mun je ba sai dai mu kwana a nan in zaki tsaida Napep dari sai na kore su”.

Ware idanu tayi cikin yanayi na mamaki na karfi halin Huzaif ita abin ma dariya ya so ya bata.

Bata ga dalilin da zai sanya shi takura mata ba akan sai tayi abin da yake so shi ba mijinta ba shi ba ubanta ba amma ya kafe da bata Umarni.

Duban sa tayi ganin ya harɗe hannayenda ya jingina da gaban motarsa sai faman kaɗa kafa yake yi fuska a tamke ba alamun wasa kuma ta lura da gaske yake yi din sai dai su kwana a nan.

Wani tunani ne ya fado mata da sauri ta dube shi cikin mika wuya domin ta tabbata maganarsa da ya fadi tsaf zai aikata ita kuwa ta tsani tsayawa bakin titi ba ma wannan ba lokaci tafiya yake yi kuma in har ta jima bata koma gida ba dole ta fuskanci fushi a wajan Umma da ma ya ya ta barota balle kuma yanzu ta kara wani laifin ai sai abin yayi yawa shege da hauka.

Tsuke fuska tayi kamar hadari ita ma sannan ta isa wajansa tana mai kau da kai tana turo baki gaba hakan ba karamar dariya ya baiwa Huzaif ba amma sai ya kanne domin ya san in har yayi dariya zainl iya bata shirin nasa a hankali ya dube ta cikin danne dariyar da take kawo masa hari.

“To ya yan mata muje ne ko kuma mu cigaba da zama a nan har mahadi ya bayyana?”.

wata harara ta watsa masa bai san lokacin da ya saki dariya ba har da buga kafa ya isa ya bude mata gidan gama yayi mata alamun ta zo ta shiga.

Ware idanu tayi kafun ta kau da kai.

“nikam ba zan shiga gaba ba baya zan shiga”.

Dubanta yayi ganin da gaske take ba za tashiga ba cikin yanayi na zolaya ya dube ta.

“Kuturu mana…”

“A’uzubillahi minal shaidanir rajim zagi Huzaif”.

Ta fadi tana ware idanunwanta akansa shima zaro idanu yayi yana faman gyada kai.

“Uhm Uhm fa kar ki fassara ni Malama ni ba zagi zan yi ba”.

Harara ta wurga masa kafun ta isa wajan motar ta buɗe gidan baya ta shige.

Dariya yake yi mata ganin yanayin da ta nuna kamar zai hana ta shiga.

Shiga yayi shima ya na fadin.

“wato kin mai dani direban ki ko?”.

Ko kallon sa ba tayi ba kanta na bakin kofar tana kallon waje har yayi wa motar key kafun ya tambaya ne ta in da sukayi

“Pabeyi”.

Yanayin da ta fadi sunan Unguwar tana turo baki gaba sai ya bashi dariya ita ala dole fushi take yi dashi da gasken gaske.

Tafiya sukayi ta tsayin mintuna biyu ba wanda ya yi magana a tsakanin su ba abin da ke tashi cikin motar sai wakar ‘Because Of You’ ta Amanda Mena sosai wakar ta tafi da hankalin Mariya don sosai taji muryar

STORY CONTINUES BELOW

mawakiyar da yarda take sarrafa kalaman ta sun burgeta lokaci guda taji kaunar mawakiyar ya dalsu a

zuciyarta ji take yi kamar ta tambayi Huzaif wace ce ita amma ba za ta iya wannan ganganci ba yanzu ji take yi kamar tana zaune akan k’aya.

“Mariya”

Kamar daga sama taji muryar Huzaif ya furta hakan gabanta taji ya yanke ya fadi ta madubin gaban motar ta hango irin kallon da yake yi mata ba tare da sani ba ba ta ansa shi ba illa idanu da suka hada da sauri ta dauke kanta tana jin gabanta na cigaba da bugawa.

“me yasa wai har yanzu baki yarda dani bane na lura mafi akasari in muna tare bakya sakin jikin dani kamar zan cutar dake”.

Gyada kai tayi ba tare da tayi masa magana ba lokaci guda ta shashantar da maganar ma ta na nuna masa hanyar da za ta kai su layin su Baseera.

“Ya kamata ki bani hankalin ki nan magana nake so muyi ta fahimtar juna a tsakanina da ke”.

Da sauri ta dubeshi jin abin da yace gabanta lokaci guda ya yanke ya fadi ba wanda ta tuna a wannan lokacin sai Dr.Aqeel da yanayin da suka

kasance a tsakanin ta dashi a jiya maganganun sa ne suka shiga dawo mata kamar yanzu suka yi su gabanta ya cigaba da tsanar ta faduwa

zuciyarta na dauko mata wani lamari mai girman gaske wanda yake kara sanyaya mata jiki numfashi ta shiga ja a hankali kafun ta sake daga kai ta dubeshi har zuwa lokacin

idanuwansa na kanta wani abu mai girman gaske take hangowa a idanuwansa wanda suke ruɗa mata nata idanun da sauri ta dauke kai jin da tayi numfashin ta na fizga kamar zai fice daga gangar jikin ta lokaci guda ta ji nadama ta saukar mata ba ta san abin da yasa ta tsaya da Huzaif ba ta san abin da ya kai ta shiga motarsa ba har yake kokarin firgita ta.

“ba zan boye miki ba Mariya ina cikin wani irin hali mai wuyar fassaruwa ban san ta ya ya zan fada miki halin da nake ciki ba zuciyata tana cikin wani hali mai girman gaske Mariya komai na faruwa ne a dalilinki”.

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un”.

Abin da taji bakin ta na fadi kenan daga nan bata san wata duniyar kuma ta fada ba sai da ta shafe sakanni kafun ta dawo hayyacin ta dauke da tashin hankali sosai taji ana hajijiya da ita ji take yi kamar tana saman gajimare ana yawo da ita kwanyarta taji ta tsaya cak! da aiki zuciyarta na wani irin bugu kamar zata faso kirji ta fito a hankali ta dago kanta tana duban kofar  motar Huzaif ganin sun shiga layin su Baseera ta fara kokarin tsaida shi domin ya sauke ta a

yanayin da take jin kanta ko sakan bata fata ta sake yi a cikin wannan motar domin kuwa ji take yi kamar an daura ta a kan KASKON WUTA.

Idanuwanta ne sauka sauka kan wata dalleliyar mota sabuwa fil sai kyalli take yi haska rana na kara haskata hannu ta sa ta rufe idanuwanta domin sosai motar ta haske mata fuska da kyallin haka kawai taji gabanta ya fadi sannan kuma tana son kallon motar ware idanu tayi har motar ta karasa fitowa daga get din gidan su Baseera tana kokarin barin layin sosai take kallon motar har ta iso daidai in da suke shi kansa Huzaif hankalinsa ya tafi wajan motar sosai.

“Yaa Allah”.

Mariya ta furta da wani irin yanayi domin bugun da taji gabanta yayi sosai glass din motar a dage yake kuma gashi mai duhu ba ka gano wanda yake cikin motar hakan ya dan bata ran Mariya duk da tashin

hankalin da take ciki ta so ace ta ga waye a cikin motar domin zuciyarta sosai ta kwadaitu da son ganin ko waye.

“ajje ni a nan”.

Mariya ta fadi tana mai dafe kanta da sauri ya dawo da hankalinsa gareta ya dubanta ganin hankalinta bai gareshi hakan ya bashi damar sake kare mata kallo kafun yace.

“Ina son magana dake Mariya ki bani lokaci ko ya ya ne”.

“Please don Allah Huzaif ka barni da naji da abin da yake damu na bani da lokacin da zan iya zama naji abin da zaka fadi don Allah ka kyale ni”.

Ta karashe tana kokarin buɗe motar ta fice.

“Mariya!”.

Cak! ta tsaya ba tare da ta karasa ficewa ba a hankali ta juya ta dubeshi ganin yanayin da yake ba karamin faduwa gaba taji ba da sauri ta fice daga cikin motar har tana kokarin faduwa ko tsayawa dubansa bata yi  ba ta doshi gidan su Baseera cikin yanayi na rashin hayyaci sai faman hada hanya take yi kamar wacce ta sha kaya maye.

Mariya ta jima tsaye bakin get domin daidai kanta, sosai ta shiga tashin hankali komai taji yana kwance mata.+

tsayuwar ta a nan shine kawai take ganin mafita domin in har ta cigaba da tafiya zubewa zatayi warwas a

kasa, domin kuwa kafafuwanta take ji suna harɗewa kamar an narka roba.

Numfashi take ja ta na saukewa kafun ta sanya hannu tana kwankwasa Get din a yan sakanni mai gadi ya iso sai da ya leko ta ‘yar karamar kofar dake jiki ya ga wacece sannan ya zo ya

buɗe karamar kofar yana bin Mariya da kallo fuskarsa da fara’a da alamun ya santa dama.

Gaidashi tayi kafun ta juyo ta dubi in da Huzaif yake abin mamaki tsaye ta hango shi ya harɗe hannayensa idanuwansa na in da take tsaye

saurin dauke kai tayi tana mai cusa kanta cikin gidan bayan ta gaida baba maigadi.

Huzaif ganin ta shige cikin gidan hakan ya sanya shi dukan jikin motarsa da wani irin yanayi na tashin hankali mai girman gaske.

Zuciyarsa yake ji tana wani karta masa kamar an saka kaifaffiyar wuka ana yayyagawa idanuwansa sun kad’a sun yi jajir kamar wanda akayi wa surace da barkono hannayensa ya daura saman kansa yana dafewa ji

yake yi kamar zai tarwatse komai yaji yana kwance masa duniyar yake ji ta ishe shi ba san mai ya dace yayi ba bai san abin da ya kamata ace yayi a daidai wannan lokacin ba akan Mariya.

Ya sani zuciyarsa ba karamar wauta da ganganci tayi masa ba wanda bai san ya zai yi ba in har Mariya ba ta dubeshi ta anshi abin da ya zo mata dashi ba dole filin duniyar rayuwarsa ya kasance cikin tashin hankali mai girma.

A hankali ya fara taka kafafuwansa kamar wanda kwai ya fashewa a ciki yana jan numfashi da yake jinsa kamar zai gushe masa isa yayi ya bude motar ya shiga sai da ya shafe mintina kansa haɗe da sitiyari domin ji yake yi kamar ba zai iya tukin ba gabadaya a haka ya ja motar yana mai ficewa daga cikin unguwar domin dai ba zai iya tsayawa ba don ya tabbata

Mariya ko ta fito ba hawa motar tashi za tayi ba a yanayin da ya ga ta nuna akwai alamun tashin hankali da bacin rai mai girma tare da ita yana zaton laifin sa ne kuma ba na kowa ba da wannan tunanin zucin ya bar unguwar gabadaya.

Da Sallama ta shiga cikin babban falon yanayin ta kawai zaka kalla kasan akwai abin da ke damun ta a zuciyarta.

Sakanni ta shafe kafun a ansata a bata izinin shiga

Tunda ta saka kafarta cikin falon ta lura akwai mutane da yawa a ciki ba kamar daba da take zuwa ta samu Mami kawai ko Baseera amma yau abun ya sauya da alamun anyi bak’i.

Ba ta san ta karasa cikin falon ba sai da taji muryar Mami nayi mata sannu da zuwa da sauri ta gayyato natsuwa ta azawa kanta sosai ta shiga cikin wani yanayi ganin duk mutanan

dakin ita suke kallo a hankali ta fara takawa ta isa cikin falon sosai tana mai zubewa ta gaishe da Mami sanna ta gaida mace da namijin da taka gani wanda kallo daya tayi musu ta gane suna da alak’a da Mami domin ga kama nan da suke yi da Baseera musamman ma namijin.

“Mariya ke ce a gidan namu yau?”.

Gyada kai tayi tana faman yake don ta san da biyu Mami tayi mata magana na kin son zuwan ta gidan nasu sai dai Baseera taje nasu Mami ta sha turawa Mariya ta zo amma sai taki zuwa amma kuma ba laifin ta bane Umma ce ta nuna rashin yardarta don bata son shige-shigen nan musamman gida irin na su Mami masu farcen susa sai ayi wani tunanin daban ko wani abu ke kawo ta.

STORY CONTINUES BELOW

“Uhmm Mami dafatan na same ku lafiya?”.

“Lafiya lau Mariya ya su Umman da Mu’azzam”.

“Duk suna lafiya Umma tace na gaishe ki sosai da sosai”.

“Madalla ina ansawa”.

Daga nan ba wanda ya sake yin magana Mariya na son tambayar Baseera don bata ganta a falon ba amma duk sai taji ta kasa nauyin mutanan dake zaune take ji.

“Yusra yau dai Allah ya hadaku da ‘yar gidan mutuniyar taki ga Mariya nan da ake tayi miki kwakwazo akanta”.

Wacce aka kira da Yusra din da sauri ta dago kanta daga kan waya fuskar da fara’a kallo daya za kayi mata ka gane JINI DAYA suke da Baseera matashiya ce wacce ba zata haura shekaru talatin a duniya ba da alamun ma tana da aure akan ta domin akwai jariri wanda bai haura wata shidda ba a gefenta yana barci.

“Masha Allah ashe dai Aku mai magana ba tayi karya ba Mariya Sannu ko ya su Umma?”.

Mariya dake sunkuye da kai ta dago tana duban Yusra sosai tana mamakin yarda take yi mata magana cikin sakin jiki da fara’a da alamun dai wannan a jini su yake dukkan su ita ma Mami haka take haka ma Dady da wuya ka ga fushin sa gyada kai

Mariya tayi tana ansa ta kafun ta sake gaishe ta fuska ita ma a sake.

“Mutuniyar taki tana sama dakinta tun dazu ta shiga ban san abin da take kintsawa ba”.

Murmushi Mariya tayi kafun ta mike ta bi hanyar da za ta sada ta  da dakin Baseera.

“Ba ki ji ba Mariya”.

Mami ta fadi hakan ya sanya Mariya saurin tsayawa ta juyo ta na duban Mami.

“wadannan duk yayin Baseera ne wannan shine Babban su Babban d’ana kenan su nan sa Tareeq ita kuma wannan Yusra tana aure a Abuja  shi kuma Tareeq yana karatu ne a kasar waje”.

Gyada kai take yi tana faman sakin murmushi tunda Umma ta fara yi mata bayani mai da kanta tayi kan su tana kara dubansu.

Da sauri ta isa wajan Yusra kamar wacce aka tura ta isa wajan jaririyar dake kwance ta shafa mata kai kafun su hada ido da Yusra ta sakar mata murmushi.

“Dauke ta mana”.

Kamar abin da take jira kenan ta sanya hannu ta dauka tana faman sakin yake ita ana ta ganin murnushi take yi kamar wanda aka matsawar baki.

“Yah Yusra yariyarki mai kyau kamar Mu’azzam din mu ya sunanta?”.

Dariya Mami tayi kafun ta dubi Yusra da ta kafe Mariya da ido ganin yarda take barin jiki akan ‘yar ta duk sai taji Mariya ta kwanta mata a zuciya sosai da sosai.

“Mariya wai dama kina magana haka”.

Mami ta fadi cikin mamaki.

Da sauri tayi kasa da kai alamun jin kunya tana kokarin juyawa ta haye sama.

“Sunanta Nawwara”.

Yusra ta fadi da tausassan murmushi a fuskarta.

A hankali Mariya ta juyo ta dube su kafun ta sauke ganin ta kan Tareeq wanda ko kallon ta bai yi ba tun da tashigo har ga Allah taji zafin yanayin da ya nuna mata bata son mutum irin haka mai shariya duk hakan ta dauke shi a matsayin wulakanci ne a filin rayuwarta.

STORY CONTINUES BELOW

Dago kai tayi da zumar barin wajan caraf! suka hada ido da Mami rausayar da kai tayi da alamun ita ma Mami ta lura da halin-ko-in-kula da Tareeq ya nuna don haka tayi mata alamu da ido tayi hakuri kar ta damu

.

A hankali taja jiki ta bar falon tana jin Yusra na yabata a kan yanayin da ta nuna mata akan Nawwara da ita kanta.

A baje ta same ta tsakar gadonta duk ta warwatsa littattafai kamar wacce aka yi wa dole sai ta karance su a lokacin. Mariya bata san lokacin da ta saki dariya ba tana isa cikin dakin sosai.

Dariyar ce ta fargar da Baseera  da sauri ta daga kai ganin Mariya ya sanya ta sakin wata kara tana dirow daga kan gadon gabadaya tayo kanta ganin haka ya sanya Mariya matsawa gefe don ta san karamin aikin ta ne tace zata rungume ta kuma ga jaririya a hannunta.

“Uhm Uhm yau anyi kyan kai kenan, Mariya yau kece a gidanmu?”.

Ta fadi tana galla mata harara kamar idanunta za su fado kasa.

“Uhmm ni fa matsala ta dake wani lokacin hankali yawa yake yi miki yasin baki ganni da Yarinya bane zaki fado kai na”.

Yatsine fuska tayi kafun ta dubi Nawwara.

“Hala Adda Yusra ce ta  hadaki da wannan ‘yar ta ta mai shegen kuka kamar gyare?”.

Ware ido Mariya tayi.

“Nawwara din ce mai kuka”.

“Yo eh mana ba ta gajiya da kuka yanzu ma don tana barci ne amma yasin ta tashi ko Hmm sai kin mai da ita wajan uwarta nima abin da ya koro ni daga falon kenan kukanta tun dazu take abu guda kamar cin kwan makauniya”.

“ikon Allah gani da gajiyawa yo ke duk abin da kike yi ba a gaji dake ba sai kece zaki ce kin gaji irin wannan son kai haka har ina”.

Dariya Baseera tayi tana mai jawo ta ta zaunar da ita bakin gadon kafun ta juya ta isa wajan da dan madaidaicin firij dake can gefe lemo ta dauko mata da gorar ruwa gami da Cake ta kawo mata  da kanta tayi saving din ta amma sai bari Mariya tace ta bari zata dauko ta gode a hakan ma.

Sun jima cikin wannan yanayin Baseera sai fama ratata zance take yi kamar wata rediyo cikin maganganun nata ne wata magana ta so narkar da Mariya daga in da take zaune.

“wai shin da zaki shigo baki ga wata hadaddiyar mota ta fice daga layin nan ba?”.

Baseera ta fadi tana mai daukar Nawwara daga jikin Mariya, kaɗa idanu tayi kamar mai tunani kafun ta gyada kai alamun eh ta gani domin ta lura da mota da Baseera ke magana akanta.

“Dr.Karami ne ya zo muka gaisa…”.

Daga wannan batun Mariya ba ta sake sanin in da kanta yake ba gabadaya taji ana juyata kamar waina a tadda tashin hankalin da take ciki taji ya karu sosai sai yanzu ta gane faduwar gaban da tayi dazu da taga motar ashe Dr.Karami ne.

Sosai kan ta ya kulle komai taji na tunanin ta ya tsaya cak! Ba abin da ke dawainiya da ita sai mamaki da al’ajabi ta yarda Dr.Karami gabadaya ya sauya yake gujewa haduwarsu  ba ta san ya ya za tayi ba ita kam! Ba ta san mai yake nufi da ita ba.

“Yace ma jiya a gidanku ya wuni tun muna makaranta yaje ashe”.

Gyaɗa kai kawai Mariya take yi tana faman jan numfashi kirjinta take ji yayi mata wani irin nauyi mai girman gaske numfashin ma da k’yar take iya jan sa.

STORY CONTINUES BELOW

Jin shirun yayi yawa ya sanya Baseera dubanta sosai da sauri ta ware ido ganin yanayin Mariya dafa ta tayi cikin yanayi na sanyin jiki.

“Me ke faruwa ne wai lafiya kike kuwa Mariya naga gabadaya lokaci guda kin sauya ne me ke damun ki”.

Wani numfashi mai zafi ta ja ta fesar kafun ta dubi Baseera da idanunta masu kwalla cikin rauni ta fara magana tana cizon laɓɓanta.

“Kin san kuwa har yau ba mu hadu dashi ba”.

Ta karashe kamar zata rushe da kuka jin zuciyar ta take tana zafi da raɗaɗi kanta na wani irin sarawa kamar zai rabe gida biyu.

Ware idanu Baseera tayi gami da dafe kirji.

“Na Shiga Aljanna”.

Wani murmushi Mariya ta saki wanda ya fi kuka ciwo kafun ta ja numfashi wanda ya haifar mata da wani irin ciwo a zuciya dama duk gangar jikinta.

“Ni kuma na shiga Uku Bala’i Baseera”.

Zabura Baseera tayi ta mike gabadaya kan kafafuwan ta jikinta lokaci guda ya shiga rawa kamar wacce aka jonawa wayar wuta Nawwar dake

hannunta har kokarin faduwa take yi duban Mariya take yi cikin wani irin yanayi na ban san in da kika dosa ba dubanta take yi da wani irin yanayi mai dauke da rauni da tausayi

dubanta da take yi da wani irin tashin hankali mai girma da ya ziyarci zuciyarta dama dukkannin jikinta.

A hankali ta shiga jan numfashi tana mai kokarin kwantar da Nawwara don ta tabbata in ta cigaba da riketa zata iya watsar da ita ba tare da ta sani ba ba abin da ya kara daga mata hankali sai hawayen da ta gani a idanun Mariya suna zuba.

“Yaa Rabbi!”.

Ta fadi tana zubewa bakin gado kamar wata kayan wanki tagumi ta zabga tana ganin ikon Allah wai uwar miji da cin kazar amarci.

“Mariya wai shin me ke damun ki ne haka wallahi kin ta yar min da hankali ba kadan ba”.

Nisawa tayi zuciyarta na wani irin harbawa kafun ta ciji laɓɓanta.

“Ban san mai Alkalamin ƙaddarata yake kokarin rubuta mani ba, ban san wani irin tashin hankali ne yake kokarin shigowa rayuwata ba a daidai wannan lokaci Baseera ina cikin

matsala, matsala babban wacce ban san maganin taba zuciyata zafi take yi ruhina raɗaɗi yake yi kwanyata ta cushe da tashin hankali mai girma ji nake yi kamar bani ba a filin duniyar nan ji nake yi kamar komai ya sauya a jikina…”.

“Ya isa haka”.

Baseera ta fadi jin muryar Mariya ta fara rawa tana kokarin sakin kuka.

Ruwa ta tsiyaya cikin glass cup din dake ajje kan farantin da ta kawo mata lemo akai a hankali ta dauka ta mika mata ba musu ta ansa ta

kwankwade kamar dama can kishin ruwan take ji wani numfashi taja wanda ya sanya Baseera dubanta da sauri tana mai ware idanunwanta akanta domin gabadaya ta tsorata da yanayin da ta ga Mariyar a ciki.

Sun shafe mintina a haka ba wanda ya sake magana a tsakaninsu sai ajiyar zuciyar Mariya kawai sautin ki tashi ita kuwa  Baseera kafeta tayi da ido gami da zabga tagumi domin ta rasa ma mai ya dace domin sosai da sosai kanta ya dau caji ba kadan ba.

STORY CONTINUES BELOW

“wai shin har yanzu fushin da Dr.Karami yake yi dake ne duk ya sanya ki cikin wannan halin ko me ne ne?”.

Baseera ta fadi da wani irin yanayi mai girman gaske a zuciyarta muryarta tayi laushi sosai.

Girgiza kai Mariya ta shiga yi cikin rashin fahimta Baseera tace.

“To me ke damun ki wai shin?”.

Sai da taja numfashi mai ciwo kafun ta dubi Baseera.

“Sun sako ni gaba Baseera ban san ya zan yi ba ina cikin tashin hankali”.

“Yaa Allah! sun sako ki a gaba fa kika ce su waye haka me kuma suke nema dake?”.

“kina dai kallon yarda nake cikin tashin hankali akan Dr.Karami to ban gaba dawowa hayyacina ba shi kuma Dr.Aqeel ya sako ni gaba da wani lamari wanda ban san ya zan fassara miki shi ba bayan haka ga kuma

Huzaif shima ya dauko mani wani tashin hankalin yana kokarin jonawa min a filin rayuwata”.

“Uhmm ni fa ban gane ba ban san ina kika dosa ba?”.

Girgiza kai tayi tana jin yarda zuciyarta ke wani irin harbawa da wani tashin hankali mai girman gaske.

“Dr.Karami fushi yake yi dani wanda ban san dalilin fushin ba”.

“wai shin Mariya na tambaye ki mana ke tsakanin ki da Allah zaki ce baki san laifin da kikayi masa ba har yake gudun haduwarku  anya kuwa Mariya ya kamata ace kin yi tunani ya

kamata ace kin zauna kin yi nazari kin binciko abin da ya haifar da wannan lamarin a tsakaninku”.

Shiru Mariya tayi kamar mai tunano wani abu na daban kafun ta nisa ta dubi Baseera.

“kisan Allah tun ranar da muka fara haduwa dake har period dina ya zo to tun ranar rabona da samun fuska daga Dr.Karami tun ranar muka rabu wanda har yau ban sake sakashi a idona ba”.

Zaro idanu Baseera tayi tana  dafe kirji.

“ke Mariya da gaske kike don Allah?”.

Murmushi Mariya tayi mai ciwo kafun ta gyada kai alamun eh.

“Mun shiga Uku anya kuwa Mariya ba wani abu a kasa tsakaninki dashi kuwa?”.

“Ke ma dai Baseera ta ya ya zan yi wa Dr.Karami wani abu don na bata masa rai ai Alheri bai ce haka ba amma dai ban sani ba ko a cikin RASHIN SANI wanda ake cewa YAFI DARE DUHU nayi masa amma kuma ai ya kamata ace ya nuna min eh ga abin da nayi masa sai in bashi hakuri ba wai ya zauna yana fushi dani ba kuma bai son ganina kin ga kenan abin da nayi masa ba sauki gareshi ba…”.

“ki daina cewa baya son ganinki Dr.karami yafi kowa a filin duniyar nan son ganinki domin kuwa ni zan yi shaidar haka”.

Cikin rashin fahimta Mariya take dubanta kafun lokaci guda taji wani lamari ya tunkaro zuciyarta har ya kai cikin kwanyarta da sauri ta mike ta shiga zarya cikin dakin kafun ta tsaya cak! tana tura dan yatsar ta cikin baki tana yawata idanuwanta a sassa na cikin dakin kamar mai son tuno wani abu na daban.

“Ya akayi Mariya ko kin tuno wani abu ne na daban”.

Gyaɗa kai tayi kafun ta dubi Baseera.

STORY CONTINUES BELOW

“Ina zargin wani abu guda domin daga shine koma ya canza tsakanina da Dr.Karami”.

Da sauri Baseera ta mike jin abin da Mariya take fadi.

“zo ki bani labari zo ki sanar dani komai na san za a samu hanyar mafita”.

Hannunta ta janyo ta zaunar da ita bakin gado tana mai dubanta.

“Bani labari Mariya sanar dani komai”.

Sai da taja numfashi sosai tana jin yarda zuciyarta ke kara matsewa waje daya da wani irin yanayi na damuwa matsananciya.

“bana zargin komai sai su Dr.Aqeel da Huzaif domin ranar da muka baro gidanku mun tadda Huzaifa a kofar gidanmu yanayin da naga Dr.Karami ya nuna kamar bai so ba kuma daga lokacin ko kallona bai sake yi ba bayan haka na fito daga motarsa ina kokarin shiga gida sai ga Dr.Aqeel

shima ya zo to a wannan lokacin zan iya cewa komai ya faru domin daga lokacin ko kalma daya ba ta sake shiga tsakanina da Dr.Karami ba sosai na tsoro ta da irin kallon da yake mani a lokacin ko dai dai ban san tsananin bacin rai ba amma  lokacin na lura da yanayin da ya shiga na bacin rai sosai domin har sai da fuskarsa ta nuna”.

Hawaye ne suka zubo mata da sauri ta sanya hannu ta na shafe su Baseera ce ta dafa mata kafada tana girgiza kai alamun ya isa haka ta daina zubda hawayen.

“Meye tsakaninki da Dr.Karami”.

Kamar daga sam taji Baseera ta watso mata tambayar wanda hakan ya bata mamaki sosai nan tayi fakare da jajayen idanuwanta tana duban Baseera cikin yanayi na ban gane in da kika dosa ba.

“Bakomai”.

Ta kokarta ta fadi amma tana jin yarda zuciyarta ke karya ta ta akan abin da tace ita a karan kanta ta sani akwai wani abu mai girma tsakanin ta da Dr.Karami amma har zuwa wannan lokacin ba ta san menene ba, ba ta san yarda zata fassara yarda take ji game dashi ba…

“Shi kuma Dr.Aqeel fa?”.

Kamar daga sama ta tsinkayo muryar Baseera ta sake fadi.

Sosai ta shiga dubanta a wannan karon tana kallon idanun Baseera da yanayin da fuskarta take nuna alamun maganar da take yi da gaske, ba alamun wani wasa a ciki kan ta shia gyaɗawa kafun ta ja numfashi.

“Ban san me zan ce miki ba akan sa, amma dai shima…”.

“shima ba komai din ko?”.

Baseera ta katse ta da sauri tana mikewa kan kafafuwanta girgiza kai tashiga yi tana faman sakin yake mai kama da ciwo sosai a zuciya da ruhi take ji, taku biyu zuwa uku tayi kafun ta tsaya waje guda ta juyo ta fuskani Mariya sosai hannayenta sarke a kirjinta kallon sosai tayi mata kafun ta fesar da wata iska mai zafi.

“Huzaif fa shi kuma a wani mataki yake a gareki?”.

Runtse idanu tayi tana mai tallabe kanta da take jin yana dauko mata wani lamari a bangarori duk ukun ba tasan me yake kokarin tarwatsa mata kwanya ba sosai tajin komai na kwance mata tunani ne barkatai taji suna kawo mata farmaki.

“Yaa Allah! ban san abin da zana ce dake ba Baseera komai nawa ba ya kan mizanin natsuwa da zan iya warware miki”.

“Eh dole kice haka mana kuma dole komai ya rikice miki ki kasa gane in da komai na filin duniyar ki ya dosa”.

Duban ta take yi cikin rashin fahimta sosai ta kasa gane maganganun da Baseera ke yi a hankali taja numfashi kafun ta fesar da iska mai zafi.

“Da gaske nake sanar dake ban san komai ba”.

A hankali Baseera ta tako ta iso gareta kafadarta ta kama ta girgiza sosai idanuwansu suka sarke a juna.

“kisan me yake faruwa dake?”.

Girgiza kai tayi.

“Kin san abin da yasa kika shiga wannan matsalar ko ma nace matsaloli?”.

Nan ma girgiza kai tayi izuwa lokacin jikin ta ya fara sanyi gabanta na tsananta bugawa tana jin yarda zuciyarta ke harbawa da sauri-sauri.

Murmushi Baseera ta saki tana mai gyada kai kallo daya zakayi mata ka gane kallon tausayi da rauni take jifan Mariya dashi sai da ta ja numfashi sosai ta fesar kafun ta dauki gorar ruwa ta bulbulawa cikinta zuciyarta taji ta dan sarara da tashin hankalin da take hangowa Mariya a rayuwa ba ta san ta ya zata fara sanar da ita

halin da take ciki ba ba ta san ta ya ya zata fahimtar ita ba tare da ta shiga tashin hankali ba ba ma wannan ba sosai take ji a jikinta abin fa ba sauki mutuwar arne.

Tana numfasawa zuciyarta na kara mata kwarin gwuiwa akan kawai ta fahimtar da Mariya ita ce hanya daya da take gani komai zai gyaru har a samu mafita.

“Mariya ba zan boye miki ba a yarda na fahimci lamarin nan gabadayan wadannan mazajen da kike gani su uku  kishi ne a tsakanin su”.

Wani irin duba na razana Mariya tayi mata tana sauke hannun da Baseera ta daura mata a kafada ta shiga ja da baya a hankali tashiga motsa laɓɓanta.

“Ban gane kishi suke yi a tsakanin su ba a akan mi suke kishi”.

“Akan Sonki duk kan su son ki suke yi so kuwa mai tsanani ko wanne a tsakanin su akwai kalar so da yake yi miki tun kafun wanann lokacin…”.

Sulalewar da Mariya tayi ne kasa tare zaman yan bori ya sanya Baseera dubanta tana tsaigaitawa da maganarta ta.

Hawaye ne shaɓe-shaɓe ta hanga idanuwan Mariya suna zuba ta hade hannayenta duk waje daya ta daura a kai lokaci guda ta hade jikin ta waje guda kamar mai jin sanyi ko wacce za a rabata da wani abu nata.

“Na Shiga uku”.

Ta fadi tana mai bajewa kan Capet din dake malale tsakar dakin kamar wacce aka tsikara kuma ta mike zumbur tana duban. Baseera da wani irin yanayi.

“Ban yarda ba wallahi wannan ba gaskiya bane hauka suke yi wallahi hauka suke yi haba mana Baseera kamar ni za su ce suna so ki dube ni fa guda nawa nake a filin duniyar nan suke kokarin kashe ni da raina wannan wani irin Bala’i uku ne nake ciki ni Mariya”.

Haka ta saki baki tana sambatu kamar wata zautacciya kafun ta durkushe ta saki wani irin kuka mai zafin gaske da jefa zuciya cikin wani irin raɗaɗi na tashin hankali wanda ba tsammanin yankewarsa.

Baseera dake tsaye bata san lokacin da idanunta ita ma suka shiga zubda kwalla ba wani kuka ta ji ya zo mata da sauri ta sanya hannu ta toshe bakin ta tana karasawa wajan Mariya ita ma ta zube nan suka rugumi juna suka shiga rera kuka aka rasa mai rarrashi wani daga cikin su….

A hankali ta turo kofar dakin ta shigo tafiya take yi cikin natsuwa da kuma yanga da ta zame mata jiki da wuya kaga Areefa na tafiya da sauri-sauri a,a sai dai ka ga tafiyar ta kamar mai koyo duk hakan na cikin salo da  take amfani dashi cikin filin duniyar

rayuwarta sanye take da doguwar Riga Gown wanda tayi matukar amsar jikinta sosai da sosai ta fiddo mata da asalin kyanta da kuma fatarta mai

haske wanda tayi Fresh sosai da sosai hutu da jindadi sun taimaka kwarai wajan bayyana a jikin ta kanta ba kallabi sai dai ta tufke gashinta ta sanya rinbos mai kalar pink ta saki jelar gashin na reto a bayan ta fuskar nan fayau ba alamun ko digon tabo na kuraje.

Ba ta shafa komai ba natural fatarta kawai ce ke kyalli manyan idanuwanta masu haske sun kara taimakawa waja fiddo da kyan fuskarta hancinta dan madaidaici shi dai ba za a kira shi dogo ba sannan ba za ace dashi gajera ba yana tsaka tsakiya haka bakinta mai dauke da manyan laɓɓa masu kalar ja kadan ba sosai ba suma sun taimaka wajan kara bayyanar da kyan fuskar ta na halinta da Allah yayi mata.

A yanayin da ta shigo dakin in ka kalle ta zaka gane akwai abun dake damun ta a filin duniyar rayuwarta bisa yanayin da take yatsine fuska kamar wacce aka sanya dole shan magani sai faman kaɗa idanuwa take yi tana bin dakin da kallo.

Hajiya Layla dake zaune can gefe guda tana faman goge jikinta da shawul da alamun wanka ta fito take tsane jikinta.

Fuskarta take kallo cikin wani irin yanayi tana yatsine fuska tana duban MADUBI dake tsaye a bangon dakin.

Shigowar Areefa ya sanyata tsayawa da abin da take yi ta juyo ta dube ta kafun ta mai da kanta wajan fuskartar madubin.

A hankali ta karasa takowa ta iso gareta idanu suka hada ta madubi duk fuskokin su cike da damuwa sosai.

“Maama Lafiya kuwa na ga fuskar ki wani iri daban kamar akwai abin dake damun ki ko?”.

Areefa ta fadi tana mai yawatawa idanuwanta cikin na Hajiya Layla.

Numfashi ta ajje mai tauri kafun ta juyo ta dubi Areefa sosai da sosai kafun ta ajje shawul din tana mai riko hannun Areefa tana damkewa cikin nata kamar zata muntsuke sosai Areefa ta ji rikon har sai da ta rintse idanunta tana furta.

“Ouchhh!!”.

Dubanta tayi tana jin zuciyarta na wani irin shiga yanayi sosai take jin rashin dadi a jikinta gabadaya a hankali ta fara motsa laɓɓanta tana son yin magana amma kafun ta kai ga furta kalma daya tari mai karfi ya turnuketa ta shiga yin sa ba

k’ank’autawa da sauri Areefa ta ware idanu tana dubanta cikin yanayi na tsoro ta rikota sosai ita ma ta isa da ita daidai karamar kujerar dake gaban Madubin ta zaunar da ita har zuwa lokacin tarin bai lafa ba  kwace

hannunta tayi daga rikon da tayi mata ta fice daga cikin dakin cikin minti daya ta dawo hannunta rike da glass cup mai dauke da ruwa da sauri ta kai bakin Hajiya Layla wanda a lokacin tari ya tsaigaita sai dai wani lamari da Areefa ta gani ya so tayar mata da hankali domin kuwa wani bakin abu taga yana fita daga bakin Hajiya Layla.

“Yaa Rabb!”.

Ta furta tana mai janyo shawul din tana goge mata baki sannan ta sake mika mata ruwan zuwa bakinta kadan ta sha ta kau da kanta.

“Maama meke damunki haka baki da lafiya ne tashi mu tafi asibiti a duba ki mana don Allah kin ji”.

Yanayin da Areefa take maganar duk a rikice hakan ya sanya Hajiya Layla kakalo murmushi ta ajje a fuskarta duk da raɗaɗin da take jin zuciyarta nayi da wani abu mai girman gaske da ya tokare mata kirji sosai take jin tashin hankali  komai take ji na

STORY CONTINUES BELOW

duniyar ya sauya mata ba tun yau ba kusan shekara uku kenan take jin canji a jikinta tayi zayar zuwa asibiti wanda ita a karan kanta ba za ta ce a ga dadi ba sosai ta fara nadamar

rayuwar da tayi a shekarun baya sosai take jin daci a zuciyarta dama ruhinta gabadaya nisawa tayi tana mai sake kakalo murmushi tana

daurawa a fuskarta domin ta lura Areefa ta shiga tashin hankali matuka ganin yanayin da take ciki wanda ta hakikan ce ba laifin kowa bane sai nata ita ce silar komai da komai a rayuwarta.

“Uhmm Ya isa haka Areefa ba komai fa kawai dai tari ne ya tsarke ni magani na sha shine fa tun dazu nake wannan tarin amma yanzu naji komai ya yi sauki ki kwantar da hankalin ki”.

Rausayar da kai tayi cikin yanayi na sanyin jiki idanuwanta na duban Hajiya Layla da alamun bata gasgata abin da tace ba amma ba zata iya yi mata korafi ba a yarda take kallon ta a matsayin uwa mai kaunar ‘yar ta a filin duniyar nan ba za ta mance halaccin Hajiya Layla ba a duniyar ta ba zata taba manta taba domin tayi mata komai na rayuwa ita ce ta sauya mata komai na filin duniyarta a lokcin da ta rasa gata ta rasa wanda zai kula da rayuwarta ya taimaka mata ya ji k’anta a lokacin da ta rasa ‘yancita da komai nata a lokacin da take bukatar taimako ta rasa a lokacin Hajiya Layla ta fado rayuwarta tayi mata suttura da taimakon Allah ita ta taimaka mata ta dawo cikakkiyar mace mai ‘yanci wacce ba wulakanta ba duk da KETA HADDI da akayi mata aka ci zarafin ta a matsayinta na mace mai rauni a filin a rayuwarta.

Bata san hawaye na zuba a fuskarta ba sai da taji hannun Hajiya Layla na dauke mata su da sauri tayi firgigin ta dawo hayyacin ta suka kurawa juna ido kafun Hajiya Layla ta shiga girgiza kai.

“Haba mana Areefa har sai yaushe ne idanuwanki za su dai na wahalar da kan su ne har sai yaushe zaki daina zubda hawaye akan abin da ya riga ya wuce bana so ki daina kawai kin ji ko”.

Gyada kai ta shiga yi kamar wata kankanuwar yarinya kafun ta sanya hannu ta na kara goge fuskarta tana k’akalo yaken dole tana ajjewa a saman fuskarta.

Kuri Areefa tayi wa Fuskar Hajiya Layla tana yawatawa da idanuwanta kafun ta nisa.

“Maama me ya samu fuskarki haka duk tayi wani iri kamar wacce ta  kone da wuta sosai naga ta canza tana tattarewa?”.

Murmushi tayi wanda ya sanya zuciyarta da ruhinta ciwo sosai wasu HAWAYEN ZUCIYA taji suna ta

kwaranyo mata sosai ta san za a yi haka ta san komai daren dadewa sai yanayin nan ya faru da ita wanda ita a karan kan ta ta san ita ce silar faruwar komai a gareta numfashi ta fesar mai zafi kafun ta motsa laɓɓanta.

“Ban san ta ya ya zan sanar dake halin da nake ciki ba, ban san ta ya ya zan sanar dake lamarin da na daura wa kai na ba gashi yanzu yana kokarin illa tani ban san mai ya kai ni haka ba ban san mai yasa na kasa godewa Allah da baiwar da yayi mani ba na butulce masa da sani na”.

Shiru tayi tana jin yarda zuciyarta ke zafi da radadi rufe idanuwanta tayi ta buɗe su akan Areefa da tayi fakare tana kallon ta sosai taji tausayin ta sosai jikinta yayi sanyi da kalaman Hajiya Layla ko da bata ji abin da ya sanya ta shiga damuwa haka ba ta tabbata abin ba mai dadin bane a filin rayuwarta da alamu kuskure tayi ba tare da ta san kuskure bne a rayuwarta.

“Areefa kin ga yarda fuskata take  a haka cikin rashin kyan gani to haka duk wani sassan jiki na yake”.

Tana maganar tana janye shawul din dake daure daga kugunta zuwa kasa cinyoyinta ta bude sosai Areefa ta tsorata tana mai runtse idanuwanta kafun ta buɗe su a hankali zuciyarta na wani irin bugawa da sauri-sauri kafar Hajiya Layla take kallo har zuwa cinyarta gabadaya sun sauya kala kamar wanda tayi muguwar k’una ta bada tangarɗa wajan

STORY CONTINUES BELOW

warkewa duk tayi wani bakinkirin ga wasu dikon dikon kuraje marasa kyan gani dago idanunta tayi ta dubi Hajiy Layla dake faman sakin murmushi wanda yafi kuka ciwo.

“Maama me ya same ki haka a jiki nace baki da lafiya kin ce a,a ba haka ba ga kuma jikin ki ya nuna alamun baki da lafiya”.

Areefa ta fadi tana kai hannunta saman fuskar Hajiya Layla tana tabawa cikin yanayi na tsoro a fuskarta runtse idanu tayi jin yarda fatar tayi wani irin tauri da wani giris-giris kamar an shafa mata dakanken gawayi. 

“Wai meye haka a jikin ki Maama sosai fa jikin ki ya baci fa dubi kafarki ji fuskarki Maam muje asibiti a duba fatarki anya ba cutar fata ba ce ta kama ki?”.

Girgiza kai kawai take yi cikin matsananciyar nadama da dana sani kafin ta ciji laɓɓanta.

“Ba cutar fata bace Areefa ni na sanya wa kai na ba laifin kowa ni na ja wa kaina”.

Cikin rashin fahimta Areefa ke dubanta tana kara buɗe idanuwanta sosai cikin yanayi na firgici da abin da take ji Hajiya Layla na fadin.

“A can baya ni BAKAR MACE ce mutane da yawa suna yabawa na kalar fata ta duk da bakar ce amma ana cewa ina da kalar fata me kyau ba kowa bane ake samu da irin ta

Natural Skin ce mai wuyar samu domin da wuya ki ga fatar jiki na ta tattare ko ta yi kuraje ni kaina nasan ina da kyan fa sai dai abin takaici abin haushi a lokacin ni kuma ba abin da nake kauna  kamar farar fata da

yawan kawayena in suka ji ina cewa ina kaunar farar fata sai su ce bani da hankali ban san abu mai kyau ba har cewa suke yi da ana masayar fata dani za suyi ni kuwa a ganina hauka ce

kawai suke yi me ake yi da bakar fata ga ‘ya mace budurwa mai aji ai bakar fata sai namiji wanda ya gaji wuya da shiga rana ba ‘ya mace ba da aka sani ‘yar hutu da da zaman jindadi.

Duk kururuwar da zuzutawa da akeyi mani ina da kyan fata hakan bai hanani burin canza kalar fata ta ba a lokacin na shiga bincike har sai da na gano irin maya-mayen da ake shafawa ake canza fata zuwa fara a lokacin ba karamin dadi naji a rayuwa ta ba nayi farin ciki mara musaltuwa tun daga wannan lokacin na canza mayuka na da nake amfani da su haka sabulai na duk sai da na canza ban yi sati guda ina amfani da su ba na fara canzawa fuskata ta fara haske a lokacin

mutane da yawa sun so nusar dani amma ina na yi kunnan uwar shegu da su na cigaba da harkar ta in

takaice miki cikin kankanin lokaci na sauya gabadaya nayi fara tas na koma kamar in kika latsani jini ne zai fito daga jikina sosai na sauya komai

nawa ya canza mutane da yawa sun nuna rashin kyautawa akan abin da nayi domin cewa ma suke yi na koma sam bani da kyan gani fatata tada ta fi dacewa dani ni kuwa ko a jikina

Areefa na fi shekara goma sha biyar ina wannan abun tun ina kuruciya ta har zuwa tsufana ban daina ba domin ban gano illar haka ba sam  sai da shekaruna suka ja fatar jikina ta fara gajiya domin ta rigaya ta gama rauni sosai komai nata ya gama komawa nakashasshe”.

Shiru tayi tana shafar kafafuwan ta da suka koma kamar mai ciwon kuturta.

“Bani da yarda zan yi yanzu domin ni na jawa kaina duk abin da ya faru dani ni ce sila”.

Ta karasha cikin raunin muryar kafun ta miki ta isa gaban madubi ta janyo robar mai basilin tashiga muttsukawa jikin ta a hankali idanuwanta na kan fatarta tana kallon yarda ta sauya gabadaya kamar wata mai cutar

STORY CONTINUES BELOW

kuturta nisawa tayi ta dubi Areefa da tayi fakare tana bin ta da kallon ko motsi ta kasa yi.

“Yau ba zaki aiki bane hala lokaci fa na tafiya”.

Sai lokacin Areefa ta kaɗa idanuwanta tana mai jan numfashi ta bude idanunta sosai ga Hajiya Layla wani irin tausayinta take ji yana

samun masauki a zuciyarta da ko ina na gangar jikinta girgiza kai ta shiga yi alamun ba za ta je ba domin yanayin da take jin jikin ta duk yayi sanyi kalaman Hajiya Layla ba karamin sanya zuciyarta rauni sukayi ba.

Ware idanu Hajiya Layla tayi ganin abin da Areefa tayi kallonta tayi tana ma tsuke fuska.

“Maza wuce ki shirya ki tafi aiki kin ji ko akan me zaki ce ba zaki ba ke da ba wani abu ke damun ki ba”.

kau da kai tayi tana kokarin yin magana Hajiya Layla ta daga mata hannu.

“Bana bukatar naji komai kawai ki tafi nace ki shirya ki wuce Office”.

Ba ta sake yin magana ba gani ba wasa a fuskar Hajiya Layla din cikin sanyi jiki ta ja jiki ta fice daga daga dakin.

Kamar jira take yi Areefa ta fice  ta zube kan gado gami da zabga uban tagumi tana mai runtse idanuwanta sosai taji kanta na sara mata zuciyarta na zafi da wani irin yanayi mai

girman gaske nadama sosai take yi tana jin kunyar kanta fita ma waje kunya take ji ba ta so su hadu da muta ne gani take yi kamar kallon banza da kallon kyama suke yi mata.

*******

A hankali ta karasa shigowa cikin harabar Company din can gefe inda aka tanada Parking space ta isa ta ajje motarta sai da ta shafe mintina kafun ta fito daga cikin motar hannun ta rike da Key sai jaka kunnanta kuwa iyafis ta mak’ala fuskar ta kawai zaka kalla ka gane akwai damuwa tattare da ita.

A hankali ta fara taku lokaci-lokaci tana lumshe idanuwanta har ta isa babbar kofar da za ta shigar da ita cikin wajan aikin nata Securty suna yi mata sannu da zuwa amma ina hankalin ta yayi dogon zango.

Ko da ta isa ciki ba wanda ta tsaya kallo har ta isa wajan gefen ta ta buɗe yar karamar kofar da kayi domin kare wajan zaman nata ta buɗe ta shiga ta zauna tana sakin numfashi kadan-kadan table din dake dauke da

computer da file ta duba kafun ta janye files din da taga an anje mata gefe kanta ta daura akai tana

tallabewa da hannayen ta zuciyarta take ji tana tayi mata wani irin sosai take jin rashin dadi a jikin sosai

komai taki ji nata ya sauya yau daya wani irin kunci da zafin zuciya take ji sam bata so wani ya zo ya takura mata shiyasa bata so fitowa aiki ba amma ba yarda za tayi ne shiyasa…

Kwakwasa mata kofa da akayi ne ya sanya ta dago kai tana mai sakin guntun tsaki Sakatariyar Dr.Erena ce tsaye sai faman wani shan kamshi take yi tana harare harare kamar wacce ke kokarin kai duka.

“Sir ya ce sai ki zo”.

Ta fadi tana wani basarwa kamar ba da Areefa take yi ba.

Sosai Areefa ta ware ido tana kallon  ikon Allah wai suruka ta mari uwar miji ita abin ma dariya ya so ya bata wai batar basira rokon Allah da goge sai da ta gama kalle ta kafun ta ja wani dogon tsaki tana mai da kan ta kasa ta na kwanciya.

STORY CONTINUES BELOW

kwankwasawa taji an sake yi da sauri ta dago cikin bacin rai ta mike kan kafafuwan ta tana dubanta.

“Ke! ina wasa dake ne ko ni tsaran ki ce ba sako aka baki ba kin fadi ba sai ki tafi ba ko da sauran wani abu ne?”.

Areefa ta fadi cikin daga muryar har sai da sauran ma’aikatar hankalin su ya yo kan Areefa da sauri ta fizgi wayar ta ta fito ta tsaya gabanta tana watsa mata wani irin kallo kafun ta ja wani tsaki ta wuce abin ta. ta bar ta shanye da baki cikin yanayi na tsoro don bata taba tunanin Areefa haka take ba tun da ta fara aiki a Company din ba tayi zaton tana da fada haka ba ashe kallon kitse take yi wa rogo

kwaɓe baki tayi kafun ta ja jiki ta bar wajan tana duban Sauran ma’aikatan da suka kureta da ido kamar za su lashe duk sai taji kunya ta kamata.

Ko da Areefa ta isa Office din Dr.Erena banka kofar tayi ta shiga cike da bacin rai tsaye ta hangeshi sai faman safa da marwa yake yi jin banko kofar da

akayi ne yayi sauri tsaya cak! Yana duban kofar ganin Areefa ya sanya shi ware idanu musamman ganin yarda ta shigo kamar wacce zata rufe shi da duka.

“Dr.Erena ya kamata ka san wani abu ba wai don ina karkashin ka bane ina aiki zai baiwa sakatariyarka dama wani duk da yake cikin ma’aikatar nan raina ni ba fa maula na zo yi ba aiki na zo yi kamar kowa da yake tutiyar aiki ya zo yi don haka ba wanda ya isa ya taka ni na kyale shi”.

Ta karashe tana fesar da iska mai zafi shi kan sa sai da  ya razana da yanayin ta da sauri ya iso gareta jikin sa har rawa yakeyi.

“Lafiya me aka yi miki wani dan iskar ne ya bata miki rai a cikin Company nan nawa?”.

Yanayin da yake maganar cikin yanayi na harzuka ya sanya Areefa duban sa cike da mamaki kafun ta kau da fuska.

“kar ka sake tura mani sakatariyarka in kana nema na ai akwai waya ko ka kira ni mana”.

Tun kafun ta dire maganar ta taga ya figi jikin sa yayi kofar fita kofar ya banka cikin sauri ya fara kiran sunan sakatariyarsa wacce a daidai lokacin ta iso tana kokarin zama amma jin kiran da Ogan nata yake yi mata ya sanyata sauri mikewa tana rarraba ido kamar wacce ta san bata da gaskiya.

Yana isa gareta ya nuna ta da hannu kafun ya kwasheta da mari ji kake tas! wata kara ta saki gami da kiran

‘jesus’.

saura kadan ta hantsila bayan kujera nan ta shiga ja da baya idanuwanta a warwaje ganin yanayin da yake nunata da yatsa cikin matsanancin bacin rai.

“Sorry Sir…”.

Wata mahaukaciyar tsawa ya daka mata kafun ya fara magana cikin masifa.

“Baki da hankali uban me tayi miki zaki nemi raina mata wayo dana aike ki cewa nayi ki yi mata rashin

mutunci ba cewa nayi kawai ki duba in ta zo ki ce ina kiranta ba da yake ke dakikiya ce shine kika je kina yi mata hauka ko”.

ware idanu tayi tana duban hanyar Office din sa da wani irin yanayi na dacin rai a ranta tana sa ba wanda zai mata haka sai Areefa tun da suke da Dr.Erena bai taba ko zaginta ba amma yau ta dalilin ta ya mare ta dubansa tayi cike da takaici kafun ta kau da fuskarta zuciyarta na yi mata zafi ba abin da take yi a zuciyarta sai ‘Allah ya isa ba ta yafe ba’

Wani mugun kallo tabi shi dashi lokacin da ta ga ya ja tsaki ya koma office din itama dogon tsaki ta ja zuciyarta kamar ta fashe janyo kujera tayi cikin takaici ta zauna tana dukan saman table din dake gabanta.

Shikuwa Dr.Erena yana shiga Office dinsa zaune ya tadda Areefa sai faman girgiza kafa takeyi fuskar nan ta ta kamar hadari ba karamar razana yayi ba da sauri ya isa wajan yana mai bata hakuri yana kokarin zama kusa da ita tayi saurin jan jikin ta tana wurga masa wani wulakataccen kallon.

“Don Allah Areefa kiyi hakuri waccen tsinaniyar yarinyar ba hankali gareta ba shiyasa don Allah karki bata ran ki akan ta na hukunta ta”.

Kallo shekeke tayi masa gami da na raina maka wayo kafun ta ja guntun tsaki tana kokarin tsahi ta fice da sauri ya sha gabanta yana kallon idanuwanta da wani irin yanayi na tsananin so da yake yi mata.

“Haba mana magana fa zamuyi shiyasa nace a kira mani ke don Allah koma ki zauna maganar ba za ta yuwuwa ba a tsaye”.

“ka ga don Allah Dr.Erena ka rabu dani bana bukatar yawan magana a daidai wannan lokaci ina bukatar zaman kadaici ni kadai please”.

“Areefa don Allah ko mintin biyu ki bani wallahi maganar mai muhimmanci ce”.

Duban sa tayi ba tare da ta ce dashi komai ba ta koma ta zauna hakan da ya gani shima yayi saurin jan kujera ya zauna yana fuskartanta sai faman ajiya numfashi yake yi kafun ya kokarta duban idanunta sosai da sosai.

“Areefa ba zan boye miki ba a gaskiya nagaji da yanayin da kike yi mani na shariya da halin-ko-in- kula ya kamata in san matsayina domin ni dai da gaske son ki nake yi kuma ko auren ki zan iya yi…”.

wata irin zabura tayi ta mike kan kafafuwan ta kafun ta lailayo wasu tawagar ashariya ta sauke ta dora da fadin.

“Kan Uban can! So Aure fa ka ce Dr.Erena wa zaka aura”.

Ta fadi tana mai sakin wani murmushi mai kokarin tarwatsa mata zuciya da ruhi wani daci ne gami da raɗaɗi taji sun saukar mata a zuciya kirjinta yana wani irin bugawa kamar zai tarwatse lokaci guda taji

kwanyarta tayi wani irin hautsinewa kamar zata tarwatse itama duban sa take yi da wani irin yanayi na tsana mai girman gaske idanuwanta lokaci guda suka sauya fuskarta tashiga wani kunci runtse idanuwan ta tayi kafun ta sake dubansa ta girgiza kai da sauri ta ja kafarta tayi hanyar ficewa daga cikin office din cike da tashin hankali da a zuciya kiranta ya shiga yi amma ina ko ta kan sa ba tabi ba illa banka kofar da tayi har sai da office din gabadaya ya amsa da sauti mai girman gaske.

Da gudu ta isa kasa ba ta tsaya wata wata ba ta fizgo jakarta ta fice daga cikin wajan da yawan ma’aikata kallo suka bita dashi har fa fice wajan motarta ta isa ta buɗe ta shige tana mai da numfashi kai ta hada da

sitiyarin motar gabanta na wani irin dokawa tsanar Dr.Erena take ji tana kara samun filin zama a zuciyarta ko son ganin sa ba ta so ta sake yi ta lura da gaske yake yi kokari yake yi ya gama da ita tun kafun ta cika burin ta akan sa wanda ba zata so hakan ba sam!.

Ya zame mata dole ta canza taku dole na biyo masa ta hanya wacce zata yi saurin cimma kudirin ta domin a gaskiya ta gaji da zuwa wajan gani take yi kamar komai zai lalace yar da ta fuskanci al’amarin Dr.Erena so yake yi yayi mata yawo da hankali wanda ba za ta yarda haka ta kasance ba dole ta sake sabon lale tun wuri.

Cikin wani irin yanayi ta kai wayar kunnan ta sai faman jan numfashi take yi daƙyar idanuwanta sun kada sunyi jajir kamar an watsa mata barkono zuciyarta take ji tana mikata cikin wani irin waje mai dauke da tashin hankali mai girman gaske+

komai take ji ya tsaya mata cak! ji take yi kamar motar ta ta tuntsiran da ita ta mace ko ta huta da wannan tashin hankalin da kunar da zuciyarta ke yi tana babbaka duk wani sashi na kirjin ta ruhinta take ji yana wani irin fizga mai haifar mata da wani

matsanan cin ciwo a dukkan sassan jikinta.

Girgiza kai take yi tana jin yarda yake wani irin sarawa da duk tashin hankalin  da take ciki komai take ji a wannan lokacin yana barazana da duk ragowar farincikin da yayi sauya a gareta na filin duniyarta.

Ba ta san abin da ya sa ta fito yau ba bata san mai alkalamin ƙaddararta yake kokarin rubuto mata ba sosai take jin zuciyarta na haifar da wani kunci mai radadin gaske sosai take jin duk wani sashi na jikinta yake narkewa kamar ba na ta ba

kafafuwan da  suke kan giyoyin motar take jin su kamar ba a jikin ta suke ba ta tabbata da a tsaye take ba za su iya daukar gangar jikinta ba.

Nisawa tayi a daidai lokacin da taji iska mai nuna alamun an daga wayarta ta buso cikin kunnuwan ta runtse idanu tayi gami da tura laɓɓanta gabadaya cikin bakinta tana cizawa kamar zata fizgesu daga mazauninsu.

A hankali ta fara gangarawa gefen titin domin ba zata iya furta ko da kalma daya a yarda take jin zuciyarta ba, ba za iya motsa wani sashi na laɓɓanta a cikin halin tuki ba ji take yi kamar in ta motsa su komai zai tarwatse a gareta.

Sai da ta shafe mintina biyu kafun ta ja wani dogon numfashi ta fesar mai matukar ciwo.

“Alhaji Abdulwahaab”.

Ta fadi can kasar makoshin ta kamar wacce akayi wa dole sai ta ambaci sunan.

“Na’am Areefa”.

Ya ansa da yanayi na farinciki a muryarsa.

Runtse idanu tayi kafun ta sake jan numfashi.

“Kana ina Please I need your help right now?”.

Yanayin da take furta kalmar cikin sauti mai rauni ya sanya Alhaji Abdulwahaab yin sanyi sosai.

“What is wrong with you Areefa me ke faruwa dake ne naji muryar ki So Sad?”.

“Kana ina right now Alhaji Abdulwahaab don Allah ina son ganin ka ko a ina kake ka fada min gani nan zuwa”.

Sosai muryarta tayi rauni kamar zata fashe da kuka a hankali ta kai hannunta baki tana toshewa.

“Ok…Cool down Please yanzu haka ina Muhabbir Coffee daidai Alo-Vera Hotel ki zo nan ki same ni”.

Ba ta ji ra abin da zai ce ba da sauri ta sauke wayar tana cilli da ita kan kujerar dake gefen ta wani wawan ribas tayi tare da juya akalar motar ta koma kan titin sosai ta hau hanya.

Zabga gudu take yi kamar wacce zata tashi sama ita akaran kanta ba ta san ta nayin sa ba zuciya ce kawai ke

aikinta domin ba ta cikin hayyacita motoci da yawa sai dai su kauce mata domin  sun lura ba ta cikin hayyacin ta cikin mintina kalilan ta hau titin da zai kai ta alo-vera Hotel kwanar da zata sha saitin W. I .WUSHISHI

ESTATE.

STORY CONTINUES BELOW

Sukayi a rangama da wata motar saura kadan su haye juna Allah ya tsagaita amma duk da hakan ta bugar wa mai motar fitilu har sun dan tsage hannu kawai ta daga masa alamun bashi hakuri ta shiga layin girgiza kai yayi mai motar don ya lura bata cikin hayyacin ta.

Tun kafun ta isa Muhabbir Coffee din tayo parking din motarta gefe guda ta fito cikin hanzari murfin motar ma da kafarta ta tura ta shiga sauri kamar zata kifa har tana turgudewa Allah ya taimaka bata je kasa ba.

Ta shiga Get din wajan ta shiga rarraba idanu can gefe guda ta hango shi yana dago mata hannu kamar wacce aka ingiza haka ta tafi tana isa ta tsaya kinkam! A tsaye tana mai da numfashi ta shiga nuna kanta da

hannu kirjinta sai faman dagawa yake yi idanuwanta na juyawa kamar mai shirin zubewa a kasa da sauri Alhaji Abdulwahaab ya mike don ya lura bata cikin hayyacinta jakarta ya riko ya ajje kan Table din dake wajan kafun ya riko hannunta ya zauna da ita sosai gorar ruwan dake ajje a

wajan ya murɗewa kai ya tsiyaya cikin Glass Cup ya mika mata kau da kai tayi cikin wani irin yanayi.

“Haba mana anshi ki sha ko kya samu sa’ida a zuciyarki”.

“Bana tunanin ruwa zan yi mani wani amfani a halin da nake ciki a yanzu”.

Ta fadi cikin wani irin yanayi tana daura hannayenta saman goshinta da take ji kamar zai dare gida biyu.

“Ki ansa ki sha Areefa ruwa zai miki abin da baki taba zato ba”.

Ba ta bukatar surutu da yawa don haka ta anshi ruwan ta kai bakinta aiko sai gashi ta take ruwan gabadaya ta dire kofin da karfi har sai da ya

tsage don wahala runtse  idanuwanta tayi tana faman sauke ajiyar zuciya a hankali gumi ya karyo mata saman goshi idanuwanta a lumshe sosai taji wani sashi na zuciyarta da ruhinta sun yi sanyi kadan da ta sha ruwan.

Lokaci guda ta ware idanuwanta kan na Alhaji Abdulwahaab da yayi kuri yana dubanta nisawa tayi cikin fesar da wani zazzafan huci.

“Wai ni Dr.Erena yake so har yana ikirarin zai aure ni”.

Ta fadi tana runtse idanuwanta zuciyarta take ji tana kartawa da wani irin tashin hankali mai girma wata irin tsana mai tsanani da take ji akan Dr.Erena take samun fili a zuciyarta tana kara hauhawa  sosai take jin kalamansa na ansa kuwwa a

kwanyarta da zuciyarta.

Da na sani take yi na zuwan Company yau da na sani take yi da har ta je Office din sa ta saurare shi dana sani take yi da har ta bari kunnuwanta su ka jiyo mata kalaman da suke kokarin tarwatsa mata zuciya.

Wasu hawaye ne masu tsananin dumi taji suna biyo fuskarta da sauri ta ware ido tana kai hannayenta tana taba su murmushi take saki mai tsananin ciwo kafun ta dubi Alhaji Abdulwahaab mamaki fal a zuciyarta da fuskarta murmushi taga yanayi har hakoransa na bayyana kafun ya mike kan kafafuwansa yana taku a hankali hannayensa goye a bayan sa.

Juyowa yayi ya dubi Areefa har lokacin murmushin bai kau ba sai ma kara fadada da ya yi dawo wa yayi ya zauna sosai yana daura kafa daya kan daya ya jawo Mug din Coffee yana

kaiwa bakin sa da wani irin yanayi na nishadi sai da ya kurba sosai sannan ya dire ya daura hannunsa kan Table din yana dan

STORY CONTINUES BELOW

kwankwasawa har zuwa lokacin idanuwansa na kan Areefa da tayi fakare tana dubansa a wani irin yanayi mai cike da mamaki da AL’AJABI mai girma gaske wanda ya kusan sanya zuciyarta tsalle sama.

“wondefull Story”.

Ya fadi yana mai girgiza kai cike da farin ciki kafun ya dora da fadin.

“Sosai da sosai naji dadin wannan ranar a daidai wannan lokacin da na samu daddadar lamari irin wannan How Comes na ce miki yau ce ranar farko da nake hango cinmma nasarata akan Dr.Erena”.

Mikewa ya kuma yi kan kafafuwansa hannunsa rike da Mug din Coffee.

“Areefa ya kamata ace wannan lamarin ya samu nishadi a filin duniyar rayuwarki a yanzu…”.

“Alhaji Abdulwahaabbb!!”.

Areefa ta fadi cikin wani irin sauti mai haifar da ɗaci a saman zuciya tana mikewa kam kafafuwanta idanuwanta a warwaje tana dubansa ciki da kunci zuciyarta na wani irin zafi.

“Ban san mai yasa kake farin ciki da haka ba, Ban san mai yasa kake so nayi farin ciki da wannan lamarin ba, shin ka mance abin da ke tsakanani da Dr.Erena, shin ka mance abin da yasa na ke zaune a INUWA DAYA tare dashi, shin ka mance bani da makiyi a filin duniyar nan sam dashi, shin ka manta ba wanda na tsana duniyar nan na ke son na ga bayansa sama da Dr.Erena”.

Runtse idanu tayi tana jan numfshi kafun ta ciji laɓɓanta tana dakune fuska.

“Alhaji Abdulwahaab ta ya ya ke zaton zan yi farin ciki, ta ya ya kake zaton ko hakorana zan bayyana a fili a dalilin wannan maganar haba mana Alhaji Abdulwahaab kayi tunani mana”.

Ta karashe tana komawa saman kujera ta zauna hannayenta dukka biyu ta dafe kanta dasu wani irin yanayi take jin zuciyarta na haifa mata wanda take jinsa kamar kirjinta zai kama da wuta ya babbake duk wata halitta dake da gurbi a filin

kirjin nata ba ta san mai yasa ma ta zo wajan Alhaji Abdulwahaab ba tayi tunani zai ce da ita wani abu akan wannan lamarin ba amma sai taga sabanin haka wai farin ciki yake yi har ma da dariya.

“Yaa Salam!”.

Ta fadi tana saukar da hannunta daya tana dafe kirjinta dake ji yayi mata wani irin nauyi mai girman gaske.

“Areefa!”.

Alhaji Abdulwahaab ya fadi da murya mai zurfi. Dago kai tayi ba tare da ta ansa shi ba illa ido da ta zuba masa.

“Wannan lamarin da ya faru nasara ce a tsakanin ni da ke”.

Kau da fuskarta tayi jin zuciyarta na kara rura wutar zafin da take ji.

“Nasan zaki ji ba dadi amma wannan hanyar ita ce ta dace ki bi don cimma kudirin ki har ma da nawa”.

Girgiza kai ta shiga yi tana yatsine fuska kafun ta mike kan kafafuwanta tana dubansa.

“Ina! wannan ba hanyar mafita bace Alhaji Abdulwahaab bana hango nasara ta a wannan hanyar”.

“Don ya furta ya na son ki ko shine kike wa kallon rashin nasara?”.

Ta gaji da sauraron kalaman sa domin ranta ya fara baci ba za ta iya cigaba da zama ta na sauraronsa ba.

STORY CONTINUES BELOW

Hannu ta saka ta janyo jakarta kafun ta dube shi.

“Tafiya zan yi nayi tunanin in na zo maka da maganar nan zan samu mafita a gareka domin cimma burinmu da KUDIRI ashe ba haka bane”.

Ta karashe tana takawa kan kafafuwanta.

“Areefa”.

Ya fadi yana mikewa da sauri ya isa gabanta yanayin sa ya sauya sosai yake jin tausayin Areefa sai dai wani abu guda yake hango wanda wannan hanyar ce kawai da suka samu ita ce dama da ya kamata ace sunyi amfani da ita kar su sake ta kubace musu.

“ki tuna Areefa kudina ya ansa da sunan muyi haɗaka wajan bude Company kudin da bana wa ba kudin Marayu wanda sam bani da hakki a cikin su kudin da suke zama masifa ga duk wanda ya cisu ya kamata ki tuna ba yarda za ayi na so bayar da gudun mawa ya cutar dake nima ina bukatar naga Dr. Erena ya shiga tashin hankali ina so naga Dr.Erena ya fada cikin halin masifa domin ba mutum bane mai tausayi ba mutum bane mai imani jahadi zakiyi sosai yaci zarafin mutane da ba su ji ba su gani ba sosai ya zalunci mutane wanda na tabbata har dake a ciki. AL’UMMA zaki

taimakawa jama’a duniyar na zaki ceto daga fadawa komarsa damarki ce wannan lokacin ki ne wannan Areefa kiyi amfani da ita nasara na tare dake mutane da yawa za su shi miki

albarka za suyi miki fata nagari za suyi miki addu’a ki gama da duniya lafiya na rokeki ke kadai ce zaki iya wannan aikin”.

Komawa yayi ya zauna yana mai ajjiyar zuciya tausayin Areefa yake ji sosai a ransa ya sani dole taji ba dadi a ranta dole tashiga wani hali na tashin hankali

Amma kuma jahadi za tayi taimakon mutane za tayi ya sani Dr.Erena yana da hatsari Areefa kawai zata iya yin komai in tayi taka tsantsan ba tare da ya gano ta ba musamman yanzu da ya nuna yana sonta ya sani sosai

hankalinsa zai karka akanta da komai na shi ya sani Dr.Erena bai iya son abu ba yana nuna maitarsa a fili kuma yana bi ko ta halin k’ak’a ne don ganin ya cimma burinsa akan abin da yake so.

Areefa da ta kasa tafiya tun lokacin da Alhaji Abdulwahaab ya fara bayaninsa gabadaya jikinta yayi sanyi sosai taji zuciyarta narkewa da wani irin rauni mai girma a hankali ta juyo ta dube shi kafun ta gyada masa kai shima kai ya gyada mata don bai gane in da ta dosa ba.

A hankali ta juya ta fara tafiya a jiki a sanyaye zuciyarta na shiga wani iri yanayi tana cakuda maganganun Alhaji Abdulwahaab a zuciyarta da kwakwalwarta har ta fice daga wajan ta isa inda ta ajje motarta tashiga sai da ta shafe mintina kanta akan

sitiyari domin komai take ji ya tsaya mata cak! gabadaya taji duniyar tayi mata wani gin-girin-gim kafun ta yi wa Motar Key ta  falle kan titi.

*******

A hankali ta turo kofar falon idanuwanta a rufe kadan saboda raɗaɗin da taji sunayi mata kamar jijiyoyin su zasu tsintsinke haka ta zuro kafa cikin falon tana mai ware idanuwanta baki daya tana kokarin gayyato natsuwa ko ya ya ne bata so

Hajiya Layla ta san tashin hankalin da tashiga sosai da sosai bata so ta gane tayi kuka da idanuwanta bata so ta saka ita ma cikin tashin hankali don ta tabbata itama akwai abin da ke damun filin rayuwarta.

Nisawa take yi a hankali zuciyarta na kara matsewa wani irin yanayi mai girman gaske idanuwanta ta sauke a inda take tsammanin samunta kamar ko yaushe da ta maida wajan  zaunin ta har in ita ba ta nan.

STORY CONTINUES BELOW

Hango ta tayi zaune ta zabga tagumi da hannu daya hannu guda

Kuma rike yake da wani kwali wanda bata gama hakikance na mane ne ba amma zuciyarta ta buga lokacin da taga Hajiya Layla ta kura masa idanuwa ko kaftawa bata yi.

Kara ware idanuwa tayi tana fiddo su kamar wacce zata barsu su faɗo kasa nisawa take yi da wani irin yanayi ganin kwalin dake hannunta sosai ta tsorata tana sakin jakar dake

hannunta tana faduwa kasa ba tare da ta sani ba kafafuwanta taji sun shiga rawa kamar za su kasa daukar gangar jikinta da sauri ta fara taku tana haɗe hanya har ta isa gareta ba tare da ta sani ba.

Hannu ta kai ta ansa kwalin cikin wani irin yanayi mai nuna alamun mamaki matuka gaya idanuwanta take yawatawa kan kwalin ba tare da tace kazil ba ta shiga bin Hajiya Layla da kallo wacce ita ma ansar kwalin da Areefa da tayi a hannunta shi ya dawo da ita hayyacinta ta shiga duban

Areefa a daidai lokacin kwalla masu yawan gaske wanda suka jima tare a idanuwanta suka zubo ta shiga girgiza kai.

“Maama”.

Areefa ta fadi da muryarta mai zurfi idanuwanta da tuhuma acikin su take dubanta tana mai gyada kai tana jin yarda zuciyarta ke kara matsewa da mamakin da bata yi zaton taddashi a gidan ba.

“Dama Da…ma ba ki dai…na baaa!”.

Ta sake fadi muryarta na rawa kalmomin da take fadi suna rarrabuwa da junansu.

Wani kuka ne ya kufcewa Hajiya Layla hannu ta saka ta toshe bakin ta kafun ta shiga girgiza kai.

“A,a Areefa wallahi na daina ban sha yanzu kwata-kwata ko kaunar ta bana yi kisan nayi miki alkawari har gaban abada ba zan sake ba”.

Girgiza kai Areefa ta shiga yi tana mai zubewa a wajan numfashi take ja dakyar zuciyarta na wani irin zafi da radadi kafun ta fesar da wani zazzafan huci.

“Haba mana Maama sau nawa za muyi maganar nan dake na fada miki illar wannan abun likitoci ma sun fada miki wanda suke k’irk’irarta ma sunyi nuni da cewa tana da illa ga

rayuwar duk mai ta’amali da ita ya kamata ki san wannan ya kamata ki duba halin da kike ciki ya kamata ace kin ceto sauran rayuwarki da tayi

saura a filin duniyar nan kina ji likita ya fadi ta fara baki matsala sosai wanda yace in ba daina wa kikayi ba to tabbas nan da dan lokaci kadan zaki rasa rayuwarki gabadaya ni kuma ba zan so haka ba Maama

AKWAI ILLA a rayuwar shan taba tana da matukar hatsari ga duk mai rayuwa da ita kin sani kuma kinji a jikinki lokacin da kika kwanta rashin lafiya kin ga yanayin da kika shiga na tashin hankali da kyar da taimakon Allah ki ka samu kan ki sosai likitoci suka nuna miki dokoki da zaki bi

sannan kiyi kokarin fidda sha’awarta  a rayuwarki ko ganinta ki nisanta daga rayuwarki haba mana Maama me yasa haka me ya kawo kwallin taba cikin nan gidan?”.

Areefa ta karashe cikin muryar rawa da son fashewa da kuka tasowa tayi ta iso gareta ta kama hannayenta ta rike su gam!. Tana mai a jiyar zuciya laɓɓanta take tura cikin bakinta tana cizawa a hankali.

“Me ya kawo kwallin sigari nan gidan Maama?”.

Ta sake fadi idanuwanta na kawo kwalla kafun ta rintse idanu.

STORY CONTINUES BELOW

“Nayi dana sani a rayuwa ta nayi tir da rayuwar da nayi a duniyata duk a dalilin rashin ‘yanci yau na ga illar rashin iyaye yau na ga illar haihuwata da kayi a titi ban san me nayi wa

iyayena ba suka yasar dani suka tafi suka bar ni a titin Allah ban san mai yasa sukayi mani haka ba yanzu ga shi nan na rayuwa cikin rashin

amfani na tashi cikin rashin ‘yanci na rasa mai kwaɓata na rasa mai kula min da rayuwa har ya nuna min kuskure na rayuwata gabadaya ba

tayi amfani a duniyar nan ba ni ban yi aure ba balle na samu zuri’ar da za su ji k’ai na ni ban yi rayuwar yanci ba rayuwar titi nayi wacce ba zan ce miki ga yarda na kasance a rayuwata a shekarun yarinta ta ba”.

Nisawa tayi wasu hawaye suka zubo mata kafun ta cigaba da fadin.

“kawai na yi rayuwa ce a yarda ta zo mani a yarda Alkalamin kaddara ya zana min wani fannin kuma da nawa kason na lalacewar rayuwata ban san dadin iyaye ba ban san su waye iyaye ba ban san ya yaro yake ji a wajan

iyayen sa ba ban san wacce irin kauna ce da ake fadi ana ji a wajan UWA DA UBA ba  iyayena sun kasance  ne bakin titi da wajan masu abincin saidawa nan ne suka kasance jigon rayuwa ta su ne suka kasance

iyaye a gareni har lokacin da na dauki kazamar rayuwa da nake zaton ita ce mafita a gareni na daura a duniya ta”.

runtse idanu tayi tana jin yarda kirjinta ke harbawa da duk wani ɗaci gami da zafi a ranta.

“Areefa na daina shan sigari tun da nayi miki alkawari yau ma fita nayi aka zageni aka tsine mani har ake kokarin marina akan sigari wai don kawai nace na daina yaro karami

wanda in a haife ne na haife shi in jika ne ma zan iyayi dashi amma akan abin banza abin Allah wadai ya zage ni yana jifana da kwalin sigari dake hannunsa Yaa Allah wannan wacce irin rayuwa ce Areefa nayi dana sanin rayuwa a duniyar nan”.

Wata irin zabura tayi idanuwanta a warwaje hannayenta saman kirjinta.

“Maama zagi fa kika ce waye ya zage ki fada min waye shi na nuna masa ke ma kina da gata a rayuwarki rashin iyaye ba hauka bane zan nuna masa kina da gata kuma kina da ‘ya a filin duniyar nan da ta san darajar ki da kimarki ki fada min shi please Maama”.

Cikin sauti take maganar kamar wacce ta fice daga hayyacin ta da sauri Hajiya  Layla ta mike ganin Areefa na kokarin ficewa daga gidan sosai ta rikota ta zauna da ita tana mai kwantar da ita a jikinta tashiga shafa mata baya a hankali har zuwa lokacin idanuwanta na zubda hawaye masu tsananin zafi da take ji kamar za su keta mata duk wani sashi na kirjinta.

“ki bar komai na yafe masa rayuwa ce ta zo da haka inda ban yi harkar shan sigari ba ba yarda za ayi ya tare ni a hanya har ya ci mani mutunci in ba don ya ga alamun nayi shaye shaye ba a zamani na ba yarda za ayi ya dube ni yace na bashi sigari komai ya faru ni ce sanadi ni ce sila Areefa ki bar komai na yafe masa”.

Da sauri ta dago kanta tana duban Hajiya Layla da take shafe hawaye.

“Haba mana Maama hawaye fa ya sakaki zubdawa akan mi zaki ce a bar shi bayan ya ci miki mutunci”.

“ki bar shi nace kawai ki bar shi komai ya wuce a wajena har a zuciyata na yafe masa fata na Allah ya shirye shi ya sa daga kaina ya daina abin da yake yi domin na lura illar shaye-shaye yawa gareta ba abin da ba zata iya sanya wa ka aikata ba wanda zai cutar da rayuwarka sosai AKWAI ILLA sosai da sosai”.

Ta karashe tana mai kalato murmushi tana daurawa a fuskarta domin kwantarwa da Areefa hankali domin bata so ta sake sanya rayuwarta a damuwa nan ta shiga bubbuga bayanta domin kwantar mata da hankali.

Wani numfashi a Areefa taja mai tsayi kafin ta saki ajiyar zuciya.

“Maama ke dama baki da iyaye dama ke ma marainiya ce kamar ni”.

“Ya isa haka Areefa mu bar wannan zance haka ba shi da amfani”.

Ta katse ta da wani irin yanayi da ta ji zuciyarta na shiga da tashin hankali mai girma.

“Mai ya dawo dake wannan lokacin ba tare da lokacin tashi ya yi?”.

Ta fadi domin kau da zancen da Areefa ta dauko.

Da sauri ta tashi zaune tana duban idanun Hajiya Layla kafun taji wata irin tsanar Dr.Erena ta sake samun fili mai girma a zuciyarta a hankali ta shiga cizon laɓɓanta tana runtse idanu.

“Dr.Erena Maama”.

Ware idanu tayi kafun ta mike tsaye tana kai kawo a tsakar falon lokaci guda ta tsaya cak! fuskarta ta kara cakuɗewa da bacin rai mai girman gaske.

“Ba dai kin yi sake ya gano ke wa ce ce ba in kuwa haka ne komai zai wargaje mana”.

“A,a Maama wai cewa yayi yana sona har cewa yayi zai iya aure na in har na yarda dashi”.

Zare idanu tayi waje bakin ta na buɗe ta iso ta zauna tana janyo  Areefa jikinta gami da sarke hannayensu waje guda wani murmushi na takaici ta sako kafun ta dubi Areefa sosai da tayi fakare tana dubanta ganin abin da ke fuskarta.

“Lokaci ya zo Areefa lokacin da nake dako ne Allah ya kawo mana shi tabbas lokaci ne ya zo tsakanimu da Dr.Erena”.

“Ban gane ba Maama?”.

Areefa ta fadi a dan tsora ce tana kwace hannayenta daga cikin na Hajiya Layla.

“Karki damu kawai ke dai ki kwantar da hankalin ki ki cigaba da zuwa aiki karki sake ko da wasa ki nuna masa baki amince ba sannan gobe karki sake ki ce ba zaki office ba ki shirya ki je ki bar komai a hannu na”.

Cikin rashin fahimta da kara bayyanuwar  mamaki ta shiga motsa laɓɓanta tana kokarin yin magana amma Hajiya Layla ta hana ta tana mai cewa.

“Maza ta shi ki je ki watsa ruwa ki ci abinci ki huta kafin lokacin Sallah yayi”.

Ba musu ta mike zuciyarta da wani irin AL’AMARI wanda ta kasa gane kansa sosai kanta ya kulle sosai taji tunanin ta ya kasa buɗe mata wannan lamari wanda ya jefata a duhu sosai da sosai haka ta ja jiki tana duban Hajiya Layla har ta isa dakinta.

Mikewa Hajiya Layla tayi tana kai kawo cikin falon hannayenta take hadawa waje daya tana bugawa wani irin yanayi take ji a jikinta sosai taji dadin maganar nan da Areefa ta fadi mata komai take hangowa ya canza sosai take hango nasara a tsakanin ta da Dr.Erena za ta nuna masa ita

wacece kuma za ta nuna masa mace ma daraja gareta a duniyar nan ba kamar yarda ya dauka ba.

Tunda ta dago labulan dakin ta sanyo kai take dubanta da kallo kamar wacce taga bakuwar fuska, sosai ta lura da Mariya cikin yan kwanakin nan gabadaya ta sauya kamar ba ita ba sai sanyi jiki da rashin son magana ko aiki take yi haka take zama wata sukuku duk ta rame sai idanu da sukayi mata zuru-zuru ga tsayi da takuma yi sosai.+

Gyaɗa kai Umma tayi kafun ta kau da kanta daga kallon da takeyi mata sosai ta fahimta sosai ta gane akwai abin da ke dawainiya da ‘yarta wanda yake haifar mata da damuwa sosai a zuciya da ma jiki baki daya ba ta san mai Mariya take nufi da hakan ba ba ta san wacce irin rayuwa ta daukarwa kanta ba na zama cikin damuwa sosai ita kanta abin ke damunta a zuciyarta sai dai tana boyewa ne saboda ita

Mariyar domin ba ta bukatar ta ganta itama cikin damuwa abubuwa da yawa suke nukurkusar zuciyarta musamman batun mahaifin Mariya ba shi babu dalilin sa  anyi cigiyar amma ina ta sha fita ba tare da kowa ya sani ba ta nufi cikin gari amma ina haka take dawowa jiki a sage tasha zama tayi kukan dare domin rage radadin dake damunta in abun yayi mata yawa alwala take daurowa ta kaiwa Allah kukan ta akan ya bayyanar mata da mijinta in har yana raye a filin duniyar nan.

Wasu kwalle taji sun kawo mata ziyara cikin idanuwanta da sauri ta shafe su kafun Mariya ta gani. Dago kanta tayi tana duban Mariya dake tsaye tana zare hijabin makarantar da ta dawo kafun ta zube kan katifar tsakar dakin idanuwanta gabadaya ta daga sama tana kallon rufin dakin.

“Mariya!”.

Umma ta fadi cikin wata irin murya mai zurfin gaske tana sauke idanuwanta akan Mariya da ta dago tana dubanta daga kwance.

“Tashi mana magana nake so muyi”.

Wani irin yatsine fuska tayi kamar wacce zata fashe da kuka gabadaya bata so taji ana yi mata magana komai take ji ba dadi zuciyarta take ji wani iri tana yi mata ciwo mai girman gaske bata so a fiye tuhumanta akan abin da ke damun ta domin bata da abin da za ta iya cewa tasan Umma kuma tambayar ta za tayi gabadaya sai taji wani ba dadi a hankali ta shiga kokarin tashi tana cizon laɓɓanta kamar zata tsinke su zama tayi sosai kanta a kasa domin bata bukatar Umma ta gane yanayi da take ciki  domin ta tabbata duk wanda ya kalli idanuwanta sai yayi zargin wani abu daban ita kanta ta san tana cikin tashin hankali sosai take jin canji yanayi a jikinta sosai ta lura da komai nata ya sauya ji take yi kamar ba ita ce ba zuciyarta take ji tana wani irin ciwo mai matukar raɗaɗi da zafi ga kasar ruhinta da yake furzar da wani zazzafan huci.

“Mariya akwai abin da kike boye wa a ranki, wanda kika kasa bayyanar dashi a filin rayuwarki na lura dake kusan wata guda kenan gabadaya kin sauya kamar wacce bata da lafiya Me yasa haka?”.

Umma ta fadi cikin sanyin murya

Mariya kamar jira take yi Umma ta idar sai hawaye shar-shar sun fara zubo mata wani kuka take ji yana zuwa mata da sauri ta kai hannunta tana rufe bakin nata zuciyarta taji tana yi mata wani irin zafi da raɗaɗi kamar zata fasa kirjinta tayo waje kanta taji yana juya mata komai take kin na filin duniyar yana zama kunci a gareta ji take yi kamar ta mutu ta huta da wannan rayuwar ta duniyar nan ita kanta ta sani tana cikin tashin hankali zuciyarta ciwo take yi ciwo mai girman gaske wanda ko tantama ba tayi shine ajalinta.

Ware idanu Umma tayi sosai tana kallon ikon Allah wai na kwance ya fadi hawayen da take  gani a fuskar ‘yarta ya sanyata faduwar gaba.

“Yaa Salam! Mariya meye haka nake shirin gani hawaye a idanuwanki da girman ki me aka yi miki har haka ya sanya ki zubda hawaye”.

STORY CONTINUES BELOW

Runtse idanu tayi tana jin yarda zuciyarta ke zafi da wani irin huci kirjinta take ji yana kartawa da wani tashin hankali mai girman gaske.

Laɓɓanta ta shiga motsawa sosai muryarta tayi rauni jikinta har rawa yake yi.

“Inda mahaifina na filin duniyar nan ba yarda za ayi na kasance a haka, inda mahaifina na kusa dani ba yarda za ayi rayuwata ta kasance a haka, inda mahaifina na filin rayuwata ba wanda ya isa ya saka ni gaba ya dasa min ciwon rai. Ban san me ke kokarin shigowa rayuwa ta ba, Ban san me yake shirin faruwa dani ba, ban san wani irin BALA’I bane yake zawarcin rayuwa ta ba…”.

A firgice Umma take dubanta kamar wacce ta ga sabuwar  halitta wani irin bugu take jin zuciyarta nayi daga kirjinta sosai taji duniyar na juya mata tsoro take ji yana kara girma a gareta komai taji lokaci guda na duniyar na juya mata tsoronta daya ba damuwar batar Mijinta bane ya sanya ‘yarta cikin tashin hankali har haka gabanta taji ya sauya bugu da sauri-sauri a hankali ta shiga nuna Mariya da hannu idanuwanta na kawo kwalla ita kuwa Mariya sai kaar sautin kukan ta take yi kamar wacce ake bugu.

“Mariya karki ce dani damuwar rashin mahaifinki ce ta kai ki har haka, karki ce dani jarabawar da Allah ya dorawa rayuwarki kike kokarin butulce masa karki ce mani kin kasa YARDA DA ƘADDARA ba fa ke kadai wannan abun ke damu ba ni fa Mijina ne shi kadai ne yayi mani saura a rayuwata bani da kowa sai shi akan sa na rasa iyaye na ga shi yanzu shima na rasa shi amma nayi

TAWAKKALI na mikawa Allah kuka na domin shi kadai ne zai yi mani duk wata maganin matsalata Mariya ki sassautawa rayuwarki rayuwa bata son a dauke ta da zafi ke fa yarinya ce wacce take matakin kuruciyarta.

Bai kamata ace kin matsawa rayuwa ba karatu kike yi ya kamata ace kin ajje komai a gefe ki bar komai a zuciyarki sannan ki mikawa Allah lamarinki”.

Sosai Muryar Umma tayi sanyi zuciyarta take ji tana zafi da wani irin raɗaɗi mai girman gaske mikewa tayi kan kafafuwanta tana jin yarda idanuwanta suke kawo ruwa ficewa tayi daga cikin dakin domin ba za ta iya zama ba ta tabbata in ta zauna dukkannin su sai an rasa mai rarrashin dan’uwansa a cikinsu.

Kwanciya Mariya ta koma tayi tana faman ajjiyar zuciya mai sanya kirjinta zafi sosai  runtse idanuwa ta tayi ba abin da take hangowa sai tashin hankali mai girman gaske a bangarori UKU wanda suke shirin haifa mata da BALA’I UKU.

Ba ta san ya rayuwarta zata kasance ba cikin lokacin nan ba ta san ya za tayi ba sosai komai ya tsaya cak! a kwanyarta ina ma ta san a shafin rayuwarta akwai wannan masifar da ta roki Allah ya kasheta tun a cikin Ummanta ba ta san haka duniyar take ba da kwazazzaban tashin hankali da bata shigo ta ba amma ina ikon Allah sai kallo duk mai sauran rai a duniyar nan yana DA SAURAN KALLO.

Iskar da taji ta shigo cikin dakin ne ya sanyata sauri buɗe idanuwanta da suke rufe sun kaɗa sunyi jajir kofa ta kalla Hafsi ta gani tsaye tana watsa mata wani irin kallo tana faman yatsine fuska gami da tsaki sosai ta hango kiyayya tsantsa cikin idanuwan Hafsi tun da take da ita bata taba ganin tayi mata irin wannan kallon ba mai cike da tsana da sauri ta tashi zaune tana cizon laɓɓa.

“Yo me akai da maza, ai yanzu a ka fara zaman kishi da uwar miji, ki je waje ana kiran ki”.

Tana fadin haka ta buga wani uban tsaki kamar zata tsinke harshen ta ta fice daga cikin dakin.

Fakare Mariya tayi tana kallon ikon Allah  wai uwar miji da cin kazar amarci wasu hawaye taji sun zuba mata a zuciyarta ta na ayyanawa anya tana da sa’a a filin duniyar nan anya kuwa ba wani laifi tayi wa ubangiji ba yake hukuntata ta wannan hanyar.

STORY CONTINUES BELOW

“Astagafurullah wa’atubu ilai”.

Ta shiga fadi kafun ta shiga kokarin komawa ta kwanta tayi luf! kamar wacce bata numfashi tunanuka ne taji sun addabi zuciyarta da kwanyarta da sauri ta mike tana goge fuskarta ta zura hijabin ta akan kayan

makarantar da ba ta cire ba waje ta fito ta zira takalmin ta tana dube dube kafun ta jiyo karar saukar ruwa cikin bandakin su ajiyar zuciya ta sauke don ta tabbata Umma ce a hankali tayi hanyar waje Hafsi dake tokare bakin kofa tana kallonta wani mugun tsaki taja  fuskarta a hargitse kamar zata fashe da kuka ta juya ta koma cikin dakin kamar wata sabon kamu bakin gadon karfe ta zauna ta na faman turo baki gaba tana wani kumbure-kumbure kamar zata fashe.

Dubanta Goggo Marka ta shiga yi da mamaki ganin yarda take hauhawa kamar fulawa taji yis.

“Ke kuma meye haka na ga sai faman hawa kike kamar fulawa?”.

Sake turo baki tayi gaba tana buga kafa a kasa.

“Haba Goggo wai ni nafi kowa bakin jini ne a garin nan ace kullum.

nikenan ina zaune ko matayi babu”.

Zaro ido Goggo Marka tayi tana ajje kaɗin da take yi kafun tashiga sallallami tana tafawa hannaye baki sake.

“Muhammadu dan abdullahi me nake shirin gani Hafsi”.

Kau da kai tayi tana turo baki gaba.

“Ni gaskiya na ga ji kina kallon Mariya sai zarya samari masu zunduma-zudunman motoci suke mata jiniya a kofar gida nikuwa ko ‘ya’yan gidan Malam Shehu bana gani”.

“Iyee to ai shikenan bara na zo na sanya a rubuce miki suratul-Yusufa ki shanye tun da kin rasa mashinshi ne sai mu ga yarda Allah zai yi”.

Goggo Marka ta fadi tana mai bankamata harara kamar idanuwanta za su zubo kasa.

“nifa gaskiya Goggo kisan yarda za kiyi dani ba yarda za ayi ace Mariya ta fini farin jini samari kanta kawai suke zarya nikuwa kamar na hadiyi jaɓa don bakin jini dame ta fini ki duba fa ki gani”.

Ta fadi tana mai mikewa tana jujjuya jikinta.

Mamaki fal! zuciyar Goggo Marka gabadaya ta rasa ma abin da zata ce sai faman bin Hafsi take yi da ido ba tayi zaton Hafsi za tayi haka ba ba taba zaton irin wannan maganar zata fito daga bakinta ba ba kunya ba tsoron Allah.

Girgiza kai tayi tana mai sake duban Hafsi kwalla ta gani a idanunta tana yatsine fuska kamar zata rushe da kuka da sauri ta ware idanu ciki da tu’ajibi.

“Samarin Mariya Uku kuma duk masu Mota ni kuwa ko mai keke bani dashi ni gaskiya ba zan yarda ba ni dai kawai ki san yarda zakiyi dani na gaji nima saurayi nake so na ganni dashi in ba haka ba ai sai Mariya ta rainani sosai da sosai”.

“Ya isa haka Hafsi yi shiru zauna muyi magana”.

Turo baki tayi tana zauna sai faman kumburi take yi.

“Ke kina da wanda kike so?”.

“Na fa ce miki ba wanda yace yana sona sai fa kwanaki Danliti mai gini yace wai ni yake so ni kuma ba abin da zan yi dashi katon hanci gareshi ga kunnuwa fala-fala”.

Kuri Goggo Marka tayi mata dariya ta so kama ta amma sai ta kanne tana mai cewa.

“Naji to ke yanzu wa kike so?”.

STORY CONTINUES BELOW

farrr! tayi da idanunta tana mai saka dan yatsa cikin baki kamar mai son tunano wani abu kafun ta dubi Goggo

.

“ni so nake yi na samu mai mota irin na Mariya ko ma ta ban saurayin ta guda daya a ciki”.

“Shikenan waye a cikin su kike so nayi miki Alkawari zaki same shi Hafsi farin cikinki shine nawa  yo me akayi da waccan mai kalar zazzafin

shawarar ki sha kurumin ki ko duka samarin kike so zaki mallake su….”.

Wani ihu tayi tana mai kaiwa Goggo cafka tana rungume ta sai faman kyalkyalar dariya take yi.

“zo muje na zabi wanda ya zo yanzu gashi can a waje zo muje ki ganshi mai kyau ne motarsa luntsumemiya gashi dan gayu”.

“Nifa tsiyata dake gajen hakuri wallahi Hafsi me zamu je yi kuma ke dai kwantar da hankalin ki kamar kin yi bako ya mutu ki bar komai a waje na shi da kansa zai zo yana rokonki ki so shi”.

Wata irin dariya ta sake yi kafun ta mike tana tikar rawa.

Ita dai Goggo Marka baki ta saki tana kallon ikon Allah.

Tsagaitawa tayi da rawar da take yi ta shiga dube-dube kafun ta hango abin da take so kwanon soson wanka ta dauka tana duban Goggo Marka sannan ta fice.

Goggo Marka ta margaya kai tana mai fadin.

“ai sha kuruminki magana ai kuma ta kare mata tace da mijinta shege”.

******

Tun da Mariya ta doshi soron gidan su take ji gabanta na tsananta faduwa sosai take jin wani iri kamar ta koma amma wani sashi na zuciyarta na ingizata da taje ta gano waye sai da ta tsaya ta numfasa gami da saita kanta sanan tayi shahadar kuɗa ta fice gabadaya fuskarta a kasa.

Tsaye yake jikin motarsa kansa na duban takalman dake kafarsa kallo daya zakayi masa ka gano irin ramar da yayi sosai da sosai ya kara haske duk da duhun fatar da yake da ita takun da yaji ne ya sanya shi dago kansa a daidai lokacin ita ma Mariya ta dago kanta gabadaya suka sarke juna da kallo zuciyoyinsu suka shiga bugu da sauri-sauri kowa ya kasa dauke ido daga kallon dan uwansa sai da suka shafe tsayin lokaci kafun Mariya taja wani dogon numfashi kafafuwanta taji sun shiga rawa sosai ji take yi kamar zata zube kasa.

“Yaa Rabbi!”.

Ta furta cikin wani irin yanayi na rashin hayyaci a hankali tashiga juyawa domin komawa cikin gida gaban ta ji yana duka ba ta san abin da yasa ta fito ba, bata san ya akayi ba ta fito ba ba tare da ta san waye ba tajima da ajje Huzaif a gefe duk da kullum zuciyarta sai ta yi mata tunanin shi bata so ace sun sake haduwa ba domin bata bukatar sake ganinsa domin ganin sa ba karamin sanya ta yake yi cikin tashin hankali ba.

Ciwon zuciyarta daɗuwa yake yi tashin hankalin ta karuwa yake yi duniyarta sake rikicewa take yi a duk lokacin da tayi arba da Huzaif ba ma Huzaif ba duk wani wanda yake da takomashin sanya zuciyarta tashin hankali.

“karki yi mani haka Mariya zuciyata zata iya bugawa a ko wani lokaci in har kika ki tsayawa ki saurare ni ban san ya ba zuciya tana kuna ruhina na ciwo gangar jikina ya zama kamar ba nawa ba”.

Numfasa yasake yi yana jin yarda kirjinsa ke harbawa da duk wani tashin hankali da yake ciki zuciyarsa ciwo take masa ciwo mai tsanani.

STORY CONTINUES BELOW

“Rayuwata na cikin hatsari komai nawa ya shiga ruɗani ban san ya zan kwatanta miki tashin hankalin da duniya ta take ciki ba na rokeki ki saurare ni Mariya”.

A hankali ta fara tsaigatawa da tafiyar da take yi gabadaya taji duniyar na juya mata kafafuwan take ji kamar suna narkewa jikinta rawa yake yi zuciyarta lokaci guda ta sauya da bugu tana buɗe shafin da ta baiwa Huzaif ya zauna a ciki runtse idanu tayi tana jin yarda zuciyar ta ta ke kartawa kamar ana soka mata KIBIYAR AJALINTA.

A hankali ya shiga takowa yana jin yarda bugun zuciyarsa ke canza bugu da wani irin yanayi game da Mariya numfashi yake ajjewa da duk kamshi da yake ji yana tasowa daga jikin Mariya yana haifar masa da wani irin yanayi na kasala a jikin sa da

zuciyarsa gabanta ya karaso ya tsaya yana mai juya idanuwansa da suka kaɗa kadan fuskarsa cike da yanayi na rauni hannunsa ya kai saitin in da yake zaton zuciya na wajan ajje.

“Mariya kin ga nan dina ji nake yi kamar KIBIYAR AJALI ake sokamin ji nake yi kamar KASKON WUTA ake sauke mani a wajan Mariya sosai nake jin wani iri a game dake sosai nake jin zuciya tana kara buɗe fili mai girman gaske a game dake komai ma da komai na zuciyar ke ce a cikinsa…”.

“Ya isa haka Huzaif ya isa nace maka na gaji da jin wannan kalaman ka bar ni haka in har ba so kake yi

kwanyarta ta tarwatse ba in har ba so kake yi zuciyata ta buga ba na mutu hankalin ka ya kwanta”.

Numfashi ta shiga ja ta kai hannayenta duk biyu tana rufe bakinta jin kalaman nasa take yi kamar saukar narkakkiyar dalma a zuciyarta jin sa take yi kamar yana doka mata ganga mai matukar kara a cikin kunnuwanta sosai taji bugun zuciyarta ya sauya komai take ji na jikinta yana narkewa kamar ruwa.

‘Yaa Allah’.

Ta furta a can kasar zuciyarta da take ji tana kecewa da tashin hankali mai girman gaske.

“Mariya…”.

“Nace maka ya isa haka ka bar zuciyata ta huta mana Huzaif”.

Ta sake katse shi tana toshe kunnuwanta da take ji kamar za su tsinke.

Runtse idanu Huzaif yayi yana jin sautin muryarta na amsa sauti mai girma a kunnuwansa da kwanyarsa sosai ya ji zuciyarsa na bugawa da yanayin da Mariya take nuna wa a gareshi numfashinsa yake ji ya canza yanayi yana sama da kasa kamar zai dauke cikin yanayi na ciwo yake cizon laɓɓansa.

“Baki so na ko Mariya baki kauna ta bakya son gani na a filin duniyarki ko kiyi hakuri zuciyata ce ta matsa min zuciya ta kasa hakuri gabadaya ta hauka ce a dalilin ki ba ta jin sautin komai sai naki Mariya ki taimaka Huzaif din ki ne fa”.

Ya karashe muryarsa na karyewa da yanayi na son kuka a hankali yake hadiyar wani abu mai tauri da ya tsaya masa a kirji zafi yake ji zafi na sosai da sosai kansa yake ji yana kokarin darewa biyu nauyi yake ji yayi masa ji yake yi kamar bana sa ba

.

A hankali ya fara juya yana kai kawo kamar wani sabon hauka.

“Ban sani ba ashe zuciya ta tayi ganganci, ban san zuciya ta hauka take yi ba, ban san wai dama hauka nake yi ba, ban san dama ban dace da wajan da zuciya ta kawo ni ba, ban dan dama ni kadai nake jin irin wannan yanayin ba a zuciya  komai nawa ya sauya ya canza kamar bani ba, kamar ba Huzaif ba duniyar ta yi wani iri ba dadi komai ma ba dadi”.

Sosai Mariya ta tsorata da yanayin da taji yana sambatu idanuwanta sosai suka fito waje kanta ta ji ya shiga juyawa kamar zata zube kasa runtse idanu tayi zuciyarta na wani irin bugu da sauri-sauri.

“Yaa hayyu Yaa Kayyum”.

Kawai take fadi wasu zafafan HAWAYEN ZUCIYA ne taji suna saukar mata jin su take yi kamar tafasassu.

“Shikenan Mariya na tafi…na tafi tun da ba ki son ganina na takura miki ko yi hakuri shikenan na tafi”.

Ya fadi yana mai daga mata hannu murmushi a fuskarsa mai sanya zuciya ciwo mai girma a hankali ta shiga motsa laɓɓanta.

“Huzaif!”.

Ta fadi da wani irin yanayi mai girman gaske cak! Ya tsaya yana mai juyowa gabadaya idanuwansa sun kaɗa sun yi jajir.

“Kar ka tafi kayi hakuri karka ga laifi na nima ba yi na bane laifin zuciya tane ban san ya zan yi ba komai ya kulle a cikinta ta kasa daukar komai ma”.

Duban ta yake yi da wani irin yanayi cikin idanuwanta yake hango wasu abubuwa masu girman gaske su na sanya jikinsa narkewa da wani irin yanayi.

Baki ya shiga motsawa yana nuna ta da hannu magana yake son yi amma ya kasa sai faman girgiza kai kawai yake yana sakin wani yaƙe mai girma a fuskarsa.

Wani dogon tsaki suka ji an saki duk kan su suka juya suna duban in da suka ji sautin na tashi.

Hafsi ce tsaye ta rike kugu sai faman kumburi take yi kamar zata tarwatse wani kallon tsana da ƙi ta sake jifan Mariya dashi tana faman huci kamar kububuwa kafin ta juyar da kallonta wajan Huzaif  tana kare masa kallo zuciyarta take ji tana shiga yanayi game dashi girgiza kai tayi tana mai tsartar da yawu a hankali ta juya tana kallon Mariya ita ma ita take kallo cike da mamaki da tu’ajibi.

“Huzaif sai anjima”

Mariya ta fadi cike da wani yanyi mai ciwo yana kokarin yin magana amma ina har ta shige cikin soro  duban Hafsi yayi cikin haushi da takaici ji yake yi kamar ya shake ta don bakin ciki dunkule hannu yayi yana bugun iska yana mai cizon laɓɓa da sauri ya juya jikin sa sai kyarma yake yi ya isa wajan motarsa a hanzarce yayi mata key ya fizge ta rai bace har yana baɗe Hafsi da kura ya bar unguwar.

Wata irin shewa tayi tana tafa hannunta sannan ta juya cikin sauri ta fada cikin gida ranta fes!!.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *