YARIMA MUS’AB CHAPTER 2

 YARIMA MUS’AB CHAPTER 2

                   Www.bankinhausanovels.com.ng 

Murmushi tayi tare da Kawar da kai ganin kallon nashi ba mai karewa bane har suka iso bata sake kallon inda yake ba Babbane kuma ya hadu matuka wato Fadar Sarkin Bauchi a ranta tana mamakin wadan da suka fito daga wannan masarauta masu mabanban ta halayya wasu mai kyau wasu kuwa ko kare bazai ci ba misali Xieey

Ta tayar da Hafsat tana fadin “ke kasa tashi dallah an iso” ta tashi tana dan waro idanu “Amman gaskia anyi sauri” bata tanka ta ba illah fitowa da sukayi suna rige²n isa bangaren Ummi da gudu suka shige tana zaune kuyangu suna matsa mata k’afafu ganin shigowar su ta musu alamar su fita da hanzari suka mik’e suna gaida su sannan suka fita su kuma karisawa sukayi suka rungumeta suna farin cikin ganin ta shigowa yayi guard dinshi na dauke da akwatin kayansu bayan ya ajiye ya fita Mus’ab ya balla musu harara “da’allah Ku d’aga ta so kuke Ku karasa ta” Ummi tayi daria “oh to ina ruwan ka su da Ummin su?” ya wani shagwabe fuska “Allah ni zan tafi gidan Mamy na naga daga zuwan wad’an nan yaran har an fara min wariya” gwalo suka mai Ummi tace suje suyi wanka su fito cin abinci suka wuce dakin da Hafsat ke sauka idan tazo hutu gidan komai tsaf suka same shi wanka sukayi Hafsat ta sanya riga da skirt ita kuwa 3ple H doguwar riga ta saka Sea Green sai farar hula ta fito fes da ita domin shigar ta dace da kalar fatar ta mai duhu

Suka fito falo nan suka tarar da Mus’ab har yayi nashi wankan yana zaune a kasan kafet kusa da k’afafun Ummi ya daura kanshi bisa cinyar ta tana shafa kanshi suna tad’i sai zuba murmushi suke su Hafsat suka kariso wajen Lamido ta zauna gefen shi tana d’an turo baki ” Allah Ummi a daina min haka ba nice auta ba” MUS’AB ya mata daria Ummi ta d’an ture kanshi “dallah tashi na manta ynx kai ba auta na bane” gwalo yayi mata “Ummi kin ganshi ko?” ta fada “rabu dashi Baby nah” ta mike tana nufar d’akin cin abincin dake ‘bangaren nata tana fadin “kuzo kuci abinci kar Ku biye ma wannan matsokanin” sai lokacin ya juya yana kallon Hafsatou murmushi ya mata yana fad’in “Hafsy Blacky an mata ki tashi kije kici abinci munsan hali daman” murgud’a baki tayi “eh d’in dadin abin ma kowa yana ci” tayi gaba abinta suka bi bayanta suna mata daria har suka shiga dinning room d’in MUS’AB yana fad’in “Blacky acici tafi a hankali mana” bata kulasu ba taja ta zauna wata kuyanga dake tsaye tana jiran su zazzauna ta zuba wa kowa abinda yake so ta fara tambayar su murmushi Hafsatou tayi “jeki kawae zan zuba” cike da girmamawa ta rusuna tare da barin d’akin Ummi ma ta mike tana fad’in “ni fa kunsan yau Alhamis ina azumi bari in shiga gurin Umma(surukar ta) idan kun gama kuje Ku huta kunji ” to suka amsa suna fad’in a fito lafia a babban faranti ta zuba musu Dambun shinkafa sannan ta zuba wa kowa lemon kwakwa ta tura musu kallonta kawai yake yi komai nata a nutse take tamkar wata babbar mace suka fara cin abinci har lau dai idanun shi na kanta Hafsat dake kula d duk wani motsin shi tayi murmushi ya bude baki zaiyi magana kawai ya k’ware ya fara tari (kunsan sha’anin Dambu) da hanzari ko wacce ta mik’o mishi ruwa suna ta faman sannu duka biyu ya karba ya shanye sannan suka kalli juna suka tuntsire da daria shima cikin dariyar yace “to ba shikenan ba nasan halin Ku da rikici duk wacce nak’i karbar nata ynx zata tara min mutane” harara Hafsatou ta aika mishi tare da mikewa alamar ta k’oshi suma mik’ewar sukayi zuwa cikin falon suka zazzauna Hafsatou ta d’auki remote ta chanza channel zuwa MBC Bollywood su kuma suka fara hirar dangin su.+

Xieey zaune gefen Dad d’inta tana ta kuka gaba daya hankalin shi ya tashi yayin da Umman ta ta mik’e tare da ta’be baki domin tana jin haushin yadda ya sangarta yarinyar ta fice zuwa Sasan surukar tasu nan suka had’u da Ummi suka fara hirar su

Da k’yar ya samu tayi magana “Haba uwa ta ya zaki taso ni daga fada sa’an nan kuma ki zo ki tasa ni gaba kina kuka kink’i ki fada min damuwar ki” ta share hawaye “Daddy ni wlhy YARIMA nake so kuma in ban same shi ba kana dab da rasa ni” “subhanallahi haba uwa ta ya kike kiran min rasa ki please ki daina in dai YARIMA ne ki kwantar da hankalin ki da zaran kin gama makaran ta zan same shi da maganar nasan yaro ne mai biyayya so bazai bada matsala ba” ta sake fashewa da wani kukan “wlhy ban yarda ba Daddy ni yau nake so kuyi maganar in ya yarda shikenan” dafe kanshi yayi yana takaicin rashin jin magana irin ta ‘yar shi (LAIFIN WA?) oho “to shikenan naji je kici abinci anjima zan kira YARIMAn yazo muyi maganar dashi……..” Mik’ewa tayi tana kwalawa baiwar dake kula da bangaren abincin ta kira kan ta kawo mata abinci tayi hanyar d’akin ta…………

Da DARE……………Da dare bayan sallar Isha’i suna kan cin abinci Jakadiya tayi sallama ta shigo bayan tayi gaisuwa take sanar da sak’on Waziri da ya aiko cewar yana neman YARIMA nan ya amsa mata cewa yana nan tafe bayan sun gama ne ya mik’e yana fad’in “Ummi bari inje amsa kiran Daddy” ta amsa da to ai gaida su ya kalle su “Kuzo Ku rakani daga nan kwa gaeda Umma” Hafsat ta mik’e yace “ke Blacky ke fah?” ta d’an marairaice kasancewar tana kallon Best Korean film d’inta Boys Over Flowers na mutumin nata (Kim hyun Joong) yayi gaba a dole ta mik’e suka d’auko mayafi tare da bin bayan shi suna tafe bayi na risinawa suna gaidasu har xuwa ‘bangaren mahaifin Xieey wanda ya kasance Waxirin garin nasu a Babban falon gidan suka tarar da Umma da fara’ar ta ta kar’besu tana mai farincikin ganin su “sannun ku da shigowa maraba YARIMA” suka durk’usa har k’asa suna gaidata ta amsa cike da fara’a

Bayan sun gama gaisawa ne YARIMA ya nufi ‘bangaren Waxiri yana fad’in su jira shi kai tsaye yayi sallama falon domin baya buk’atar iso matsayin shi na YARIMA Daddy ya amsa yana fad’in “YARIMA kariso mana Ashe kana tafe” YARIMA ya zauna a k’asa bisa kafet d’in dake falon ya tank’washe kafafu tare da fad’in “Barka da dare Daddy fatan an wuni lafia” ya amsa da “lafia lau d’an albarka ya mahaifiyar taka?” “Lafia lau take, daman ance ne kana nema nah” ya washe baki “eh daman naji ka dawo ne ban ganka ba shiyasa” murmushi YARIMA yayi “to shikenan bari in shiga chan nasan ynx Abbah ma yana duba hanya ta banje mun gaisa ba” Daddy ya d’an ja numfashi yana me shakkar maganar da zaiyi sannan yace “YARIMA maganar k’anwar ka nake son muyi” ya kalle shi “wacce k’anwa ta fa Daddy? Ko Hafsat” baiji dad’i ba amman ya daure yace “YARIMA k’anwar ka Zainab nake nufi ta wajena”

“Ohh! Daddy wani abin ne kuma ya faru da ita?”ya fad’a in I don’t care voice Girgiza kai yayi “ko d’aya kawai gani nayi tunda ka k’are karatu ynx kuma sai maganar aure shine na yanke shawarar aura maka ita idan tayi Candy” wani Abu yaji ya soke shi a zuciya wai me ake shirin maida shine ya tambyi zuciar shi babu amsa sbd haka ya d’ago ya dubi k’anin mahaifin nashi yayi k’ok’arin dai²ta yanayin shi “ai Daddy anyi latti zuwa ynx Kam Dan har Ummi ta had’ani da d’iyar Yayan ta kuma ma mun daidaita” ran shi ya ‘baci gaskia Halima tana shiga mishi al’amura watou har auren ma ita zata za’barwa d’an nata yayi murmushi ai in tasan wata to bata san wata ba “to in banda abinka YARIMA ai namiji mijin mace hud’u ne musamman kai dake gidan sarauta kaga ai kafi k’arfin zama da mace d’aya sbd haka kaje ka shirya auren mata biyu” bai bashi damar cewa wani abin ba ya mik’e zuwa Bedroom d’in shi mik’ewa YARIMA yayi ya fara tafia kamar wanda baida laka har zuwa Babban falon gidan inda ya tarar da su Hafsat zaune suna hira da Umma yana shigowa ta mik’e ta nufi ‘bangaren maigidan nata daidai lokacin Xieey ta fito daga d’akinta zuwa falon ai ko tana hangoshi ta kariso da sauri da nufin rungume shi da sauri yaja baya tare da daka mata tsawa su Kansu sun razana da yanayin shi musamman Hafsatou wacce saida ta mik’e tsaye tana rarraba idanu ya iso kusa dasu baiyi magana ba illa hannuwan su da ya kamo ya fara jansu har suka fice daga ‘bangaren Xieey dake tsaye kamar gunki ta fashe da kuka tare da nufar falon mahaifin ta………+

A dai2 kofar falon Ummi ya sake su tare da nufar ‘bangaren Mai martaba suka tsaya suna kallon shi har ya shige ciki kafin kowacce ta sauke ajiyar zuciya suka shige falon kowacce da abinda take sak’awa cikin tata zuciyar

Sallama yayi a falon Mai martaba aka bashi izinin shiga suna zaune da Mama (kishiyar Ummin shi) gaidasu yayi cike da girmamawa Abbah ya tambayeshi ya wajen service d’in nashi ya amsa da “Alhamdulillah komai yana tafiya dai2” sannan yayi shiru wayar Abbah CE tayi k’ara nan ya d’auka ganin k’anin shi ke kira nan sukayi magana take fara’arshi ta fad’ad’a ya sauke wayar yana murmushi “YARIMA ynx Daddyn Ku yake sanar dani maganar da kukayi ashe kuma mata biyu zakayi ne” gabanshi ya fad’i kar dai Abbah ya amince shima ko dayike yasan daman za’ayi hakan ai ya girgiza kai “a gaskia Abbah nawa nake da har za’ace nayi mata biyu lkc d’aya ai Sam bai dace ba” had’e fuska yayi “to to MUS’AB ka nuna min cewa bamu isa dakai ba kawai shikenan ina sane dakai cewar in har ba Halima bace tayi mgn Sam baka d’aukar ta da muhimmanci,to bari kaji baka isa kaja da maganar Dan uwana ba sbd haka umarni ne kasa a ranka auren mai sunan Hajiyarmu dole ne” tayi dariya cikin ranta yau dai ta had’o Dan gold da Abbahn shi (sunan da Matan gidan ke kiran Mus’ab kenan) “to in banda abin YARIMA ai gata akai maka…..” Kallon da ya watsa mata ne yasa tayin shiru don yana da wani irin k’warjini “tashi ka bani wuri” cewar Abban nashi ya rusuna tare da fad’in “Allah ya huci zuciyar ka na barka lafia” ya fita duk yadda yaso danne damuwar shi ya kasa a dole ya nufi ‘bangaren Ummi suna zaune da Hafsatou yayin da Hafsat tuni tashige bacci ya shigo direct wajen Ummi ya nufa ya zauna kusa da k’afar ta ya fara magana “Ummi meyasa ne ake min haka a gidan nan? tun tasowa ta kowa yake iko dani tamkar nine kad’ai ‘Da ina ganin su Musa na gidan Daddy komi sukayi ba’a cewar komi sbd ni kad’ai ne ba’a so ko mi? Hatta karatu za’bar min Course d’in da akeso akayi kuma banyi musu ba haka nayi Amman har abin yakai cewar Matar aure ma sai an za’ba min? Shin an ta’ba tambaya ta ko akwae abinda nike so? Ko da wacce nake so?” Ya k’arishe maganar yana hawaye hak’ik’a ya bata tausayi amman ta daure tace “kenan YARIMA kana nufin don mun za’ba maka mata bamuyi dai² bane ko hakan yana nufin bamu sonka ne? Idan kuma kasan baka son Hafsat meysa ka amsa mana iye?” “Sam ni Ummi bazaki ta’ba bani wani Abu ink’i kar’ba ba koda banso balle ma ni ba Hafsat nake nufi ba Daddy ne ya kira ni wai sedai in auri Zainab kuma Abbah har ya amince” ya fad’a cikin d’acin zuciya

Ba Ummi ba hatta Hafsatou dake zaune nesa dasu tana kallon Playful Kiss sai da gaban ta ya fad’i tayi saurin kallon su akayi sa’a shima ya kallo inda take nan hankalin ta ya tashi ganin hawaye a idanun shi Ummi ta danne ‘bacin ranta “to ynx ya kake son nayi iye? Ko inje ince su fasa ne sbd basu isa dakai ba, ni kaga ka tashi kaban guri mahaifin Kane duk abinda ya yanke a kanka ya zama lallai kabi” ta fad’a cikin daga murya tare da mik’ewa tana fad’in “sai da safe kuma kada ka sake tunani ya hana ka bacci kayi addu’a komai zaixo da sauke” ta shige d’akin baccin ta tana mai jin zafin abinda ake ma d’an nata…..

Sunkuyar da kai yayi k’asa ya rasa ma mai zaiyi ita da yake ganin zata share mishi hawaye amman Sam ashe ba haka bane itama tabi bayansu kenan to shi yanxu Yaya zaiyi kenan

Ganin k’afafunta yayi masu kyau a gabanshi ya d’ago har izuwa fuskar ta tana tsaye ta zuba mishi idanu ya janyo hanunta tare da zaunar da ita a gabanshi yana jin inama ace matar shi CE da ya rungumeta ya fad’a mata damuwar shi ya raya hakan a ranshi har ynx hanunta na cikin nashi yake kallon ta kallo irin na ido cikin ido suke wa juna tana hango wani irin rauni cikin idon shi……. Tashi tayi tana k’ok’arin zare hanunta dake cikin nashi ya rik’e gam a hankali tace “Yi hkr Yaya ynx zan xo” don ta lura yau Malamin nasu rikici yakeyi ya sake ta ruwa mai sanyi ta d’auko ta zuba a kofi ta mik’a mishi bai karba ba sai ya bude baki tayi murmushi ta saka mishi kofin yasha ruwan…………………Kallon shi tayi a nutse bayan ya gama shan ruwan ta ajiye kofin a hankali ya fara magana “kina kallon abinda Ummi ta min ko Hafsatou, shin was take son in sanarwa damuwa ta bayan tun tasowa ta bata bani damar yin aboki ba da ita na saba sharing duk wata damuwa ta to ynx was take ganin zan nufa iye?” haka kawai yaji zuciyar shi ta aminta da ya fad’a mata matsalar shi ya lura tana da kaifin hankali duk da k’arancin shekarun ta da basu gaza 17 ba zuwa 18 ta runtse hanunshi dake cikin nata har saida ya d’anyi k’ara yana fad’in “Gaskia Blacky ke muguwa CE” gwalo ta mishi kafin ta had’e fuska ta fara magana “Yaya shin kana tunanin cewa Ummi bata damu da halin da kake ciki bane? Sam ba haka bane ita uwa da kk gani akwae wata k’aunar dake tsakanin ta da abinda ta haifa wanda ko yaya ya shiga damuwa takan shiga fiye da tashi,Ummi tayi hakane badon komi ba sai dan kasancewar duk yadda takai da son ka babu yadda za’ayi ta raba ka da Dangin mahaifin ka sbd idan aka wayi gari babu Abbah dole sune matsayin shi kuma kai kanka kasani cewa DA UBA AKE ADO wannan kalmar na dad’e ina jinta wajen Ammi nah tun tasowa ta kasan dai duk yadda Ummi ke son ka bazata je Masallaci da sunan kar’ba maka aure ba ko? So kuma ma ina laifin wanda ya d’auki d’iyar shi ya baka ai k’auna CE tasa hakan ko?”+

Tun da ta fara magana ya zuba mata idanu tamkar talabijin yake kallon yadda bakin ta Ke motsawa tabbas yarinyar ta shayar dashi mamaki jin kalaman dake fitowa daga bakin ta tamkar shirya mata su akayi “Hakane hakika yau naci gyaran Malama bahaushe dake cewa Abinda Babba ya hango yaro baya hangowa tabbas ba kowane Babban bane domin ni sam banyi tunanin hakan ba gani nake kawai kowa ya tsane ni? daria tayi jin abinda ya fad’a ” to amman Hafsatou kinsan fa halin harinyar nan sam batta da tarbiyya a ‘yan kwanakin da nayi da dawowa na fahimci hakan tartare da ita kuma ina yawan jin Malamai suna k’orafi kanta a Schl” ita tasan hakan amman domin ta k’arfafa mashi guiwa tace “haba Sir Xieey fa mace ce sannan kuma yarinya k’arama kuma tana Son ka na tabbata bazaka sami matsala ba wajen tank’wara ta zuwa kalar da kk so ba” ta karisa maganar tana kallon cikin idon shi gyad’a kai yayi “shikenan Hafsatou ina yaro k’arami an maidani mai mata da yawa” ya fad’a yana dariya tashi tayi tana kallon agogon falon ta zaro ido “Sir har karfe goma fa tayi muna zaune oya a tashi dare yayi”

Hararan ta yayi ya tashi “to ai kene kika tsayar damu yarinya sai surutu kamar aku” ta murguda bakin ta “oho dai jeka daman ba’a muku kai da waccan matar taka mai bacci kamar kaasa” ta fad’a tana kashe kayan kallon

Yana fara tafiya “eh anji dai Blacky Parrot” ta watsa mai sauran ruwan da ta dauko a Kofi ta nufi Fridge dake dinning room ta aje ya fita da d’an gudun shi yana mata dariya……

Komai na wuta saida ta tabbatar ta kashe sannan ta rufe k’ofar falon ta nufi d’akin baccin su tana murmushi ita kad’ai

Ajiyar zuciya Ummi ta sauke wanda tun fara maganar su take tsaye tana kallon su kasancewar ta fito bayan shigarta d’aki domin yiwa Hafsatou magana ta kulle falo sosai yarinyar ta burgeta tana da kaifin hankali sosai da sanin ya kamata kuma taji dad’in yadda ta kwantar wa da Autan nata hankali nan ta juya ta koma d’aki hankali kwance……

YARIMA bayan shigar shi d’aki ya gama komai na al’adarshi kamar wanka,alwala ya sanya Pyjamas tare da fesa turare sannan ya kwanta yana mai jin farin ciki a zuciyar shi yayin da wani bangaren na zuciyar tashi tana d’aci in ya tuna wai shi zai auri mata biyu kuma duka babu za’bin shi? Tunawa da gargad’in Ummi na cewar yayi bacci yasa yayi addu’a tare da Jan bargo yana rayawa a ranshi cewar a wannan karon babu mai hana zuciyar shi abinda take so ko ya za’ayi kuwa……..

Tana shiga d’akin tayi kwanciyar ta tana mai tunanin yanayin rayuwar YARIMA da ya kasance iri d’aya da tata duk kuwa da k’arancin shekarun ta amman ta experiencing abubuwa da dama a tun bayan rasuwar mahaifin ta lkcn tana k’arama amman ta kasance yarinya mai wayo sbd haka bata manta wasu abubuwan da suka faru da ita a haka bacci ‘barawo yayi awun gaba da ita………

Xieey tana shiga d’akin Mahaifin nata da hawaye ta fad’a jikin shi “Abbah ni wlh bazan iya ba sam YARIMA baya k’aunar ko gani na” ya shafa kanta “yi hkr Umman mu da yaddar Allah komai ya kusa zuwa k’arshe” nan ya sanar da ita yadda sukayi da YARIMAn duk da ta tsorita da jin cewar da Hafsat zai had’asu amman jin cewar ba sonta yake ba bashi ita akayi tad’an ji sanyi a gabanta kuma ya kira Mai martaba ya shaida mishi maganar kuma ya amince da haka ta mik’e ta nufi d’akin ta tad’au waya ta kira k’awar ta Saudah ta shaida mata yadda ake ciki nan ta kurma wani uban zagi tana fad’in “amman wannan uwar tashi akwae munafuka kar ki damu k’awata Indai Lamido ce zamu San yadda zamuyi da ita don bata da wani wayo daman 3ple H Ke kar’ba mata a Schl ammah in aka gama ai shikenan ko”. Nan dai suka gama k’ulle²n su kafin sukayi sallama kowacce ta nufi makwancin ta.

To asuba ta gari mutan Masarautar Bauchi………….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *