UKU BALA’I CHAPTER 7

UKU BALA’I CHAPTER 7

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

Tsaye tayi ki kam!. tana faman yatsine fuskarta da cizon laɓɓanta sai faman ajiyar numfashi take kamar wacce tayi Gudun ceto rai.+

“Ni wallahi gabadaya na gaji”.

Ta fadi tana mai jingina da bishiyar dogon yaron dake bakin hanyar da zata fiddo su daga cikin surkuk’in dajin da suke. kallo daya za kayi wa wajan ka tsoro ta sosai musamman in ka kasance mai karyayyiyar zuciya in aka ce ka shigo wajan ko da kudi ne ba zaka shigo ba daji ne sosai mai dauke da surkuk’in ciyayi da dogayen bishiyu kamar su sukayi kansu ga wasu gingima-gingiman duwatsu suma abin dai na tsoro gashi nan ba kajin kukan komai sai na gyare da tsintsaye.

Tsaya tayi da tafiyar da take yi jin abin da Hafsi ta fadi ta juyo kallo daya zakayi mata ka gane itama ba karamin gajiya tayi ba sai faman numfarfashi take yi jin jikinta take kamar wacce akayi wa dukan kawo wuka.

“Ke kam kin fiye tsirfa wallahi ni ban ce na gaji ba sai ke mai jikin kuruciya kai jama’a ke dai kam anyi ranguwa wallahi Hafsi”.

Sake turo baki tayi gaba tana kokarin zama gindin bishiyar.

“Haba mana Goggo Marka ki dubi uwar tafiyar da muka dauko fa aiko akan abun hawa muke wallahi sai mun gaji ga kuma fargaba da tsoro ki dubi dajin nan fa ki gani ba kowa bane zai iya shigarsa ko ni dai na shiga a tsakanin rayuwa ko mutuwa wallahi ban ma yi tunanin zan fito ba don tuni na fara dankaro salati a bakina…”.

Cak! ta tsaya da maganar da take hango maciji tayi saman jikin bishiyar da take jingine wata irin

razananniyar kara ta saki idanuwa warware Goggo Marka dake rike da kugu jin ihun Hafsi ya sanya Goggo Marka shekawa da gudu tana tsalle tsalle kamar wacce abu ke biwa kafa dama tuni a tsorace take tun da suka shigo cikin dajin gabanta ke faman dukan luguɗe.

Ihun Da Hafsi ta cigaba da yi ne ya sanyata tsayawa can gefe tana faman numfarfashi tana bin ko ina da kallo

.

“Ke Hafsi Lafiya kike kuwa”.

“Maci…ji neee”.

Ta fadi cikin rawar baki da na jiki da sauri Goggo Marka ta sake fallewa can gefe tana mai cewa.

“Rugo ki baro wajan mana tun kafin ya illata ki in ma zaki iya kashe shi kawai…”.

Ai ba ta karasa abin da take cewa ba itama kurma ihu jin abu ya taba mata kafa.

“Laha’ilaha ‘ilallahu muhammadan rasulullahi Sallallahu alaihin wassalam”.

Kam! ta kame a tsaye lokaci guda fitsari ya fara bin kafafuwanta.

Hafsi dake can gefe tana faman kurma ihu da tsalle-tsalle kamar wata biri lokaci guda ta fallo a guje tana mai wurgi da kallabin dake kanta zaninta kuwa gabadaya ta tattareshi ta cukuikuye zuwa kugunta a haka har ta iso wajan da Goggo Marka take a kame kanta tayi tana rungume gabadaya ta ma k’yalk’aleta ji kake rigija sun zube a kasa hakan ya dawo da Goggo Marka hayyacinta ta shiga ihu tana mai cewa.

“Ya sare mani kafa shi kenan na bani na lalace shikenan Alkiyamata ta zo wayyo ni kai na…”.

Hafsi ta gani zube gefe guda tana faman sakin numfashi gami da dariya ya sanyata yin fakare da idanuwa jikinta sai k’yarma yake yi a hankali ta shiga jan numfashi tana mikewa kafun ta gyara daurin zaninta.

“Ba dai ya sare ki ba ko Hafsi”.

Ta fadi tana bin sassan jikinta da kallo Hafsi ce ta sake kecewa da dariya tana mikewa har lokacin jikin nata bai daina bari ba.

STORY CONTINUES BELOW

“Goggo menene haka a jikin ki?”.

Jin abin da Hafsi ta fadi tana zare ido ya sanya Goggo Marka sakin sallallami tana tsalle kamar wata biri hakan ya kara baiwa Hafsi dariya har tana rike ciki ganin hakan ya sanya Goggo Marka dubanta tare da yi mata dakuwa don ta lura kawai so take yi ta firgita ta.

“Fitsari fa Goggo Marka”.

Ta sake fadi tana kwashewa da Dariya sai a lokacin ta lura.

“Ikon Allah”.

Ta fadi tana mai juya zanin nata da yayi jagaf!.

“kai Goggo Haka kike da tsoro ashe har na fiki dauriya ma”.

Harara ta galla mata.

“ke dalla jaye wahala ba dadi gareta ba, kuma ai tsoro halas ne wallahi ke yanzu in macijin nan ya gaftaramin sara ai sai dai buzu na… Kin ga tashi mu bar wannan azababben dajin tun kafin almatsutsan cikinsa su saukar mana akanmu mu bani mu lalace”.

Ta fadi tana mai tattare zaninta da yayi jagaf! Takalmanta a hannu a hankali take taka kasa tana mai dube dube.

Tafiya sosai sukayi kafun su fito hanyar da za ta kai su bakin titi nan ma sai da suka zauna suka huta sosai Hafsi sai faman kwakwazo take yi akan ita fa ta gaji bayan ta kamar zai karye haka take ji duban ragwanta Goggo Marka tayi mata.

“Ke dai akwai sakankiya wallahi na dauka duk ke ake yi wa wannan wahalar amma kin ishi mutane da ihu kin gaji”.

Turo baki tayi gaba tana kau da kai a hankali ta mike daga zaman yan borin da tayi ganin Goggo Marka ta dauki hanya ko magana batayi mata ba.

Sun yi tafiya mai dan tsayi kafin su isa bakin titi nan Goggo Marka ta shiga neman tsayar da Mai tasi domin shiga kowa ta tsayar ta sanar da shi inda zata sai ya ce a,a tun tana tsaye har taji ta fara gajiya amma ba su samu mai tasi ba ita kuwa Hafsi na can gefe yashe sai faman numfarfashi take yi.

“Don Allah taimaka”.

Ta fadi lokacin da wani mai Tasi  yayi slow daidai su jiki na bari ta isa gareshi.

“Gwada zaka kai mu don Allah”.

Dubanta yayi sosai kafun ya dubi Hafsi.

“Iyaka ta Kauyen Mutum Daya ba zan shiga Gwada ba”.

Ware idanu tayi tana mai yin kasa da murya.

“Haba d’ana taimaka don Allah wallahi mun jima a nan zaune ba mu samu abin hawa ba duk mun gaji ga rana ka ga jikanyata can ma zaune tana numfarfashi”.

Dubanta yake yi sosai yana sake duban Hafsi a hankali.

“Nawa za ku bayar?”.

“Naira dari za mu baka”.

Tsuke fuska yayi lokaci guda.

“nifa ba zan shiga Gwada ba sai dai in sauke ku a Mutum daya ku nemi wata motar ta karasa da ku”.

kara kashe murya tayi tana kokarin masa magiya yayi saurin tare.

“Allah ba zan je ba in zaku shiga na kai ku mutum daya to in ba kwaso nayi gaba”.

Shiru tayi tana tunani kafun ta juya ta dubi Hafsi da ta zuba musu ido tana jin komai gyada kai tayi alamun su je kawai da babu gwara ba dadi kuma a saka a baka yafi a rataya.

STORY CONTINUES BELOW

Haka suka dunguma cikin motar  Goggo Marka sai faman tsaki take yi tana gunguni wai dan tasi din ba shi da tausayi tana tsohuwa amma ba zai taimaka mata ba gashi ya tsula musu kudi.

Ba wanda ya kulata haka ta karaci maganar ta tayi shiru a haka har suka isa Mutum daya suka sauka ba su fi mintina biyu ba suka samu motar Gwada nan ma sai da aka kai ruwa rana da direba don ya lura Goggo Marka yan son banza ce shi kuwa ya nuna mata ya fi ta son kudi ko bakano haka ya ganshi ya barshi.

Haka tashiga motar tana ta mita shima sai masifa yake yi mata yana hadawa da yarensa na yarbanci abu yaki ci yaki cinyewa kamar cin kwan makauniya ganin da yayi ta zage sai surfa ruwan bala’i take ana bata hakuri amma ina aiko ya ja burki yace ta fice masa daga mota.

“kai kam anyi watsantsan d’a wallahi dan bakin mugun abu”.

Ta fadi a zuciya amma a fili sai tayi lakwas ganin haka ya sanya sauran fasinjan baiwa direban hakuri haka ya koma ya ja motar yana faman jan tsaki kamar harshensa zai katse.

********

9-May.

Wata Alkarya.

Tunda ga ne sa zaka hango tsilli tsille na tamfol da aka kankafa kamar dakuna wani saman tamfol kuma a kwai tuta dake kafe akai an rubutu  sunan Malik bin yazid da rubutun arabic sosai wajan yayi tsit kamar ba kowa sai mashina kiran bajat dake warwatse a tsakar wajan ko wani tamfol daya kuwa an kewayeshi da ginin dutse wanda ya kusan rufe shi can gefe guda kuma wani tamfol din ne amma duk yafi sauran girma da fadi nesa ba kusa ba.

Zaune yake jikinsa sanye da bakar jallabiya fuskarsa cike take da kasumba ga wani gemu ajje sosai ya naɗe kansa da farin kyalle mai laushi sosai  idanuwansa jajaye ne fuskarsa daure tamau kamar bai taba dariya ba gefensa bindigogi ne kirar Ak47 kusan biyar.

Duban mutumin dake durkusa gabansa yayi da wani irin kallo mai razanar da wanda akayi wa shi yana mai fadin.

“Baaba BG nayi maka gargaɗi na farko kuma na karshe a wannan alkaryar ban taba samun matsala da duk iyalan kungiyar nan ba sai kai a karo na uku kenan ina sanyaka aiki kana bani matsala ban san me kake nufi ba ya kamata ka sani wannan alkaryar da ka shigo ba a sassauci sannan ba a saka mutum aiki ya kiyi rayuwar saida rai ce a wannan sansanin rayuwa ce ko mutuwa ya kamata ka sani jahadi kake yi ko mutuwa kayi a wannan hanyar ka zama shahidi”.

Ya karashe yana mai dago daya daga cikin bindigun da suke yashe gefensa kafun ya daga zuwa sashi da kuka yake tashi lokaci guda ya saita jikake durum ya dauke mai kukan can gefe guda kansa yayi fata-fata kafafuwansa sai motsawa suke yi kafun su kame lokaci guda.

Wani dan kyalle ya dago yana mai goge jikin bindigar kafun ya saki wani murmushi mai zafin gaske yana duban Baaba BG da yake sunkuye jikinsa sanye da jallabiya kansa da rawani fuskarsa cike da kasumba ba ka iya gane asalin fuskarsa saboda tulin suma da ya tara.

“Ka sani ba zan yarda da wannan gangancin naka ba domin kuwa a ko wani lokaci zan iya dauke ka daga duniyar nan kamar yarda na dauke waccan yarinyar da take wa mutane ihu”.

Har zuwa lokacin Baaba BG bai dube shi ba kan sa na kasa sai faman jan numfashi yake yi.

Motoci ne kirar Sharon suka shigo wajan a jere guda uku ko wacce da tuta a jikin ta can gefe guda sukayi parking kafun su fara fitowa da ɗaiɗai ko wanne cikin su fuskarsa yane ba ka iya gane su hannayensu dauke da manya manyan bindigogi daya daga cikin su ne ya fara takowa har ya iso in da shugaban nasu yake ya zube a kasa kamar zai masu sujjada.

STORY CONTINUES BELOW

“Yah Shugaba mun kammala komai”.

Gyaɗa kai yayi kafun ya daga kai yana kallon yarda ake fiddo da mata matasa daga cikin motocin jikin su sanye da kaya iri daya kallo daya zakayi musu ka gane yan makaranta ne wacce fuskarta cike da tsoro wasu ma sai rusar kuka suke yi.

Murmushin gefen kunci yayi kafun ya mike kan kafafuwansa ya fara takawa kamar wani mai ji da sarauta da mulki har ya isa wajan izuwa lokacin an gama fiddo da su akalla za su kai dari da yan kai jera su akayi ya shiga bin su da kallo daya bayan daya yana kara fadada murmushin fuskarsa.

“Kun tabbata dukkansu ku ka kwaso”.

Duban juna sukayi su duka kafun su gyada kai alamun ‘eh’ daya daga cikin su ne ya dora da cewa.

“Yah Shugaba yanzu haka ma kauyen Sarwadi mun tayar dashi ba wani wanda yayi rai a cikin su.

Murmushinsa ne ya sake faɗaɗa kafun ya sanya hannu ya fizgo daya daga cikin matar wacce ta kasance ita kadai ce mace mara hijabi da cikakkiyar suttura sosai ya damki gashin kanta yana ja kafun ya yi wani gurgi da ita ta baje a kasa gami da sakin wata razananniyar kara mai sauti gaɓadayan sauran suka shiga ihu su ma suna kokarin tarwatsewa  da sauri  fizgo bindiga daga hannun yaran nasa ya shiga sakar musu wuta ciki zafin nama kawai zubewa suke yi a kasa kafin wani lokacin duk rabin su ya bajar da su akasa sauran kuwa takurewa sukayi waje daya wasu ba su daina gudu ba suka yanki cikin dajin sosai suna faman ihu da kururuwa.

Wata dariya ya saki kafun ya dubi Sauran Yaran sa.

“Kar ku sake daya daga cikin wadancan da suka yanki daji su sake numfashi a doron kasar nan ina son kafin mintina naga gawar su”.

Kafun ya dire kalamansa wasu su falle da gudu sun yanki daji sauran da ba su tafi ba ya dube su.

“ku kwashe dukkan su ku zuba masu sark’a”.

Yana fadin haka ya juya ya dubi wacca ya damkar wa gashi dazu sai faman rusa kuka take yi jikinta na kyarma idanuwanta sun kaɗa sun yi jajir gefen kanta na zubda jini in da ta bugu sosai.

Isa yayi gareta ya dan rankwafa yana mai sakin murmushi kafun wani lokaci fuskar canza ta koma wata kala daban ta tsananin rashin Imani da tausayi kanta ya sake kai hannu ya cafka yana mikar da ita kan kafafuwanta wani ihu ta saki gami da rushewa da kuka wani zafi ne da raɗaɗi da zugi take jin duk wani kafa ta sumar guda daya na fita komai take ji na jikinta yana canzawa kamar bana ta ba ji take yi kamar ba a duniya take ba kamar wata duniya ce ta azaba take ji ita kadai ne a ciki.

Haka ya ja ta akasa tana ihu tana komai har ya isa daidai mazauninsa har lokacin Baaba BG na durkushe in da ya barshi cilli  yayi da ita waje guda kafin ya dago bindiga ya saita goshin sa.

“In har kika sake naji wani abu mai kama da kuka sai na tarwatsa miki kan ki yanzun nan”.

Ya fadi yana tamke fuskarsa cikin wani irin yanayi na rashin tausayi da imani.

Dago idanuwanta tayi da take jin su kamar bana ta ba sun kaɗa sun yi jajir jijiyoyin kanta duk sun fito sunyi raɗa-raɗa abin ka da farin mutum gabadaƴa jikinta ya rine yayi jajir waje guda ta haɗe jikinta ta dunkule zuciyarta na kara dokawa da tashin hankali mai girman gaske ba abin da take tunawa sai yarda aka ci zarafin su aka keta musu mutunci a gaban idanuwansu aka yanka iyayen su a gaban idanuwansu aka bambaka musu kauyensu garinsu da suke zaune cikin kwanciyar hankali lokaci guda an canza musu rayuwa an kaskantar da su an mai da su ko dabbobi sun fi daraja da kima ba ta san yarda zata ce ba bata san ya zata kira wadannan mutanan ba sosai take hango salon da suka shigo masu gari da shi na tsayin sati biyu suna nuna musu suna Allah ne hanyar tsira da dacewa suke nuna musu ashe ba haka bane sai da suka saki jiki da su lokacin guda suka fiddo musu da kudirin su da manufarsu.

STORY CONTINUES BELOW

Wani kuka ne taji ya kufce mata lokaci guda da sauri ta kai hannunta ta toshe bakin ta amma duk da hakan sai da kukan nata ya fito waje runtse idanuwanta tayi cikin sadakarwa jira kawai take taji alburushi ya ratsa tsakanin kwanyarta sosai ta hango yarda a gabanta aka dannewa

mahaifinta kirji aka soka masa wuka a makoshi tana kallon yarda suka mai dashi kamar wani kare suka dinga ball da gawarsa har sai da suka ga numfashin sa ya daima motsi kafun su rabu dashi bayan sun cinna masa wuta.

Wasu zafafan hawaye take ji suna sauka a kuncin ta lokaci guda kuma taji ana dauke mata su a hankali ta fara buɗe idanuwanta da take jin kamar za su zazzzago kasa saboda raɗaɗi da zugi da taji suna yi mata.

Wani razananiyar kara ta saki ganin wanda yake gabanta lokaci guda ta dunkule waje daya jikin ta na faman kyarma idanuwanta na kansa

tsanarsa take ji tana tsarga ko wani sashi na jinin jikinta sosai take ji a fadin duniyar nan ba wanda ta tsana kamar sa rokon Allah take yi ya daukar mata ranta da wannan BALA’I da take ciki  rokon Allah take yi ya rabata da wannan mugun azzalamun da bai san imani da tausayi ba a zuciyarsa.

“Dama kin daina kukan nan domin kuwa yanzu rayuwa ce zaki sauya duniyarki zaki canza komai naki zai canza ki sani wannan wata duniya ce zaki fara rayuwa a cikinta tare dani zaki kasance har zuwa lokacin da nayi raayin rabuwa dake”.

Hannu ya kai yana kokarin shafe fuskarta a karo na biyu da sauri taja da baya gabanta na sake bugawa lokaci guda ta shiga kankame jikinta tana hadewa waje daya.

“ki kasance da Malik Bin Yazid a duniyarki sabuwa”.

Wani irin zaro idanu tayi waje kamar za su fada birkicewa da rkicewa da razana duk suka gauraya lokaci guda a gareta zuciyarta ta ji ta sauya bugu numfashin taji ya fara fizga cikin tashin hankali magunan jinin jikinta take ji suna yin kasa suna tsayawa cak! jikinta take ji yana narkewa kamar ruwa sunan da taji ya ambata ya shiga ansa amo mai sauti a

kwanyarta lokaci guda numfashinta ya tsaya cak! ta sankare a wajan.

Ta jima cikin wannan yanayin kafun ta ja wani numfashi mai tauri kirjinta taji yayi mata nauyi har zuwa lokacin idanuwanta na kansa shikuwa sai faman murmushi yake yi don ya luta da razanar da tayi.

‘Malik Bin Yazid’.

Ta fadi a zuciyarta sosai ta gane sunan sosai ta tuna sunan. sunan da ko fadin sa akayi dole ka shiga tashin hankali saboda irin tashin hankalin dake tattare dashi ba zata manta wannan sunan ba sosai tajima da haddace shi sosai ta gane shi rikakken dan ta’adda da ake nema RUWA A JALLO

mutumin da ya addabi al’umma mutumin da ya kasance masifa da bala’i a rayuwar al’umma ya hana su kwanciyar hankali da natsuwa yana rayuwarsu tafiya yarda ta kamata mutumin da ya haifar da bala’i da rashin kwanciyar hankali ga zuciyoyi masu yawa mutumin da ya haifar da ciwo mai girman gaske a zuciyoyi masu yawa  shine Allah ya hada ta dashi ita ce yau tare dashi rayuwar tace ta juye zuwa duniyarsa ita kuwa wata irin mummunar ƙaddara ce ta fado mata rayuwa ita kuwa wani irin BALA’I ya fado mata rayuwa a daidai wannan lokacin bata san mai za ta ce ba bata san ya za ce da wannan

ƙaddarar ba ta sani rayuwarta ta kare komai nata ya sauya zuwa tashin hankali da bala’i ta sani tayi

bankwana da farin ciki tayi bankwana da kwanciyar hankali ta rabu da iyayenta har abada ga shi yanzu ita kuma ƙaddararta ta jona ta da wannan bala’in wanda ba ta san ya zata kwatantashi ba.

STORY CONTINUES BELOW

Gyada kai ta shiga yi idanuwanta na fiddo da wasu hawaye masu tsananin zafi da kokarin yayyaga mata fatar fuska duban sa take yi da wani irin yanayi mai girman gaske tana

ayyanawa a ranta wannan mutumin mai rai daya a jikinsa shine ya addabi miliyoyin mutane ya hana su kwanciyar hankali bata san ya zata kwatatta wannan lamarin ba.

“Karki yi tunanin sake wata rayuwa kawai ki saka a ranki kina tare da Malik Bin Yazid”.

Wani zafi taji kirjinta nayi kafun wani abu mai girman gaske ya zo ya tokare mata kirji dago idanunta tayi tana duban Baaba BG wanda tun da aka kawo su duniyar BALA’In nan ta lura dashi a durkushe har izuwa wannan lokaci tsoho ne sosai wanda wahala da bala’i suka dakusar dashi wajan kara zama tsoho na karfi da yaji

fuskarsa kawai ta kalla ta gane bala’in da yake ciki idanuwansa a kasa ko motsin kirki ba yayi wani irin tausayin sa taji ya tsirgar mata da sauri ta kau da kai kafun ta dubi Malik wanda har lokacin yana rankwafe a gabanta.

Kallon sosai tayi masa lokaci guda ta ji zuciyarta ta kekeshe da duk wani tashin hankali da take ji komai taji tsaya mata na tsoro kallon sosai da sosai tayi masa kafun ta kau da kai tana jan tsaki can kasar makoshinta.

Wani wawan Mari da sanya ta sakin fitsari da ganin taurari taji ya gilma a kuncin ta lokaci guda ta baje a kasa gami da kurma uban ihu.

Mikewa yayi  zuciyarsa na wani irin tukuki da zafi bindigi ya ciru daga kugunsa karama lokaci guda ya saita ta sosai idanuwansa na bayyanar da wani tashin hankali mai girman gaske runtse idanu tayi tana jiran saukar alburushin domin ta gama sadakarwa ba za ta sake ko da minti daya a duniya nan ba.

Tun tana jin tafiyar numfashinta da sauri-sauri gabanta na wani bugu mai girman gaske a hankali ta fara kiran sunan Allah kafun taja numfashi mai girma ta buɗe idanuwanta tsaye ta hangeshi har yanzu bindigar na saitinta amma bai harba ba.

Mamaki ya cika mata zuciya sosai ganin yanayin da yake ciki gabadaya idanuwansa na kanta ga bindiga a hannunsa amma ya kasa harbawa kuri tayi masa da idanu tana mai sakin ajiyar zuciya sunayen Allah a laɓɓanta ba ta san ma mai za tayi ba komai take jin yana zama al’ajabi da mamaki a gareta ba ta ankara ba kawai taga ya cafko hannunta ya mikar da ita cikin wani irin yanayi na mazantaka ya shiga jan ta ciki hanzari kamar zai kifata da kasa ita kuwa baki ta saki tana kallon ikon Allah lokaci guda fargaba da razana da tsoro suka shiga tsalle -tsalle a zuciyarta har lokacin da suka iso wajan da Baaba BG yake yashe idanuwa ya dago a cikin

galabaitaccen yanayi ya dubeta ita ma shi take duba cikin wani yanayi na tsanani sadakarwa sosai suke kallon juna cikin yanayi na tashin hankali mai girman gaske tana kallon shi yana kallonta har zuwa lokacin da taji Malik ya fizge ta zuwa cikin tamfol din sa yayi cilli da ita a ciki ba komai a cikin tamfol sai hargitse wanda sam ba su dakyan gani bindigogi da alburusai can gefe kuma wata yakunaniyar shimfiɗa ce mai dauke komaitsai da sauri ta dago kai

gabanta na cigaba da bugawa tana dubansa shima ina ya ke duba kafun ya ajje kallonsa ga kan shimfiɗarsa.

“Zaki kasance dani kamar yarda na sanar dake ki shirya zama dani ki saka a ranki kina tare da Malik Bin Yazid”.

“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’una”.

Abin da zuciyarta ta shiga fadi kenan cikin kyarma da tsoro lokaci guda ta shiga matse jikinta waje daya duban sutturar jikinta take yi yarda aka kekketa ta sosai ana hango wasu sashi na jikinta ya bayyana a fili runtse idanu tayi wasu hawaye su ka balle mata.

Ta sani shikenan rayuwarta ta kare shikenan duniyarta ta gama k’awa da tashin hankali wnda ba ta san ran fita daga cikin sa

A Hankali taji ya fara takowaa kusa da ita gabanta yana tsananta faduwa jikinta sai kyarma yake yi lokaci guda numfashin ta ya fara sama da kasa lokaci guda ta saki razananniyar kara cikin firgici da tashin hankali komai taji ya tsaya mata cak! duniyar tana juya mata bata san abin da ke faruwa ba idanuwanta dai na kansa har lokacin da iso gareta ya rankwafa yana mai kamo hannayenta duk biyu yana mikar da ita a hankali idanuwanta suka shiga rufewa kafun taji jikinta na narkewa lokaci guda tana watsewa a kasa….Zuciyarta take ji tana yi mata nauyi, da abu mai girman gaske. komai take ji yana zama kamar tarihi gani take yi kamar ba ta kwashe wadannan+

shekarun da suka bawa rayuwarta baya ba  wai ita ce yau ta gama makaranta  wai ita ce yau ake bikin kammala makarantar su, a matakin sakandire. gani komai take yi kamar ba gaske ba, gani takeyi tamkar mafarki ne take yin sa wanda a ko wani lokaci zata iya farkawa.

A hankali ta kai yan yatsunan Hannunta na dama zuwa bakinta tana cizawa, kamar zata zare su daga jikinta komai take ji yana tabbatuwa, komai take ji yana gasgatuwa, komai take ji yana zama zahiri ba badini ba.

runtse idanuwanta tayi tana mai buɗewa ta shiga yawatawa da idanunta zuwa harabar makarantar dalibai birjin kowa sai murna yake yi da farinciki fuskokin su dauke da tsananin farin ciki mara gushewa.

‘Yaa Allah’.

Ta furta cikin wani irin yanayi mai girman gaske zuciyarta take ji tana buɗewa sosai tana haifar mata da wani lamari mai girman gaske

kwanyarta take ji ta shiga shawagi da ita cikin wata irin duniya na farinciki sosai take jin duk wata gaɓa ta jikinta tana ansa sakon da zuciya da ruhi suke miko musu na farin cikin da take ciki a yau din nan.

“Wayyo Allah na. Mariya gabadaya na gaji wallahi”.

Muryar Baseera ce ta doki dodon kunnuwanta da sauri ta dago kai tana dubanta tana mai sakin yak’e gami da gyaɗa ma kai.

Kuri Baseera tayi mata da idanu kamar mai son gano wani abu daban a hankali ta shiga janye hannayenta data dafa kafadun Mariya idanuwan na kara yo waje da yanayi na damuwa ba bacin rai.

“Meye haka Mariya, me fuskarki ke kokarin nuna min ba dai zaki ce mani ba kya farin ciki da wannan ranar ba Yaa Allah!”.

Ta karashe tana mai dafe kanta da take ji yana sara mata da wani irin yanayi mai girma da tashin hankali a cikinsa runtse idanu tayi kafun ta buɗe su kan Mariya da tayi shiru idanuwanta da wani yanayi na damuwa a ciki.

“Ban san me zan ce miki ba kuma Mariya, Shekaru fa tafiya suke yi kamar gudun ruwa a kogi ya kamata ace wannan shekarun da kika shafe kin canza komai a duniyarki, ki duba ki gani kin canza tsarin ki ya canza ke kan ki kin san komai game dake ya sauya sai dai abu daya…”.

Tayi shiru tana jan numfashi mai dauke da damuwa mai girman gaske kau da kai tayi daga barin kallon Mariya ta juya kan dalibai dake ta fara’a da farin ciki.

“…Zuciyarki Mariya taki sauyawa, komai ya ki canzawa a cikinta kin ki baiwa rayuwarki damar kawo maki farin ciki a filin duniyarki Ban san mai ya sa ba?”.

Sake kusantowa tayi gareta tana dafa kafadarta.

“ki na tunanin rayuwa zata yuwu a hakan kina tunanin wanan tsarin da ki daukar wa kan ki zai haifar miki da ɗa mai ido a rayuwarki ina! haka ba zai taba yuwuwa ba ya kamata ace kin sauya Mariya ki sauya rayuwarki!!!”.

Ta karashe cikin murya mai amo da sauti tana rike kafadun ta tana girgizawa har sai da mafiya yawan dalibai suka dube su sosai.

Runtse idanu Mariya tayi tana mai toshe kunnuwanta da hannu bibbiyu lokaci guda idanuwanta suka kaɗa sukayi jajir jikinta lokaci guda ya shiga rawa kamar wanda ruwa yayi mata duka sosai da sosai a hankali take duban Baseera da idanunta bakin ta na faman rawa kafin ta ciji laɓɓanta tana jin yarda zuciyarta ke matsewa a waje daya da girman damuwar da take ciki.

STORY CONTINUES BELOW

“Ban san ya zan yi ba Baseera, komai da komai duniyar ma gabadaya ta canza ban san haka duniyar take ba da ban so na shigo ta ba da na roki Allah ya barni a wata duniyar ba wannan ba zuciyarta ta gaji Baseera sosai zuciyata take zafi ban san meye maganinta ba kullum kullum komai kara rikice mani yake yi”.

Ta karashe wasu zafafan hawaye na zubowa a fuskarta kafin ta sanya hannayenta ta dauke su.

“Mu tafi gida Baseera”.

Mariya ta fadi tana mai shigar da hannun Baseera cikin nata tana jan ta ba tayi mata kardama ba haka tabi ta kamar rakumi da akala kawai binta take yi da idanu cikin wani irin

yanayi zuciyarta sai faman dokawa take yi da lamarin Mariya bata san inda rayuwar Mariya ta dosa ba sosai komai da komai ya fita daban a rayuwarta tana matukar tausaya mata musamman yarda Kuruciyarta ta kasance da tashin hankali wanda ta rasa gane in da ya dosa a filin duniyar nan.

“Ba muyi Sallama da kowa ba Mariya hakan bai kyautu ba”.

Baseera ta fadi cikin rashin abin yi tana faman jan numfashi.

Cak! ta tsaya Daga tafiyar da take yi kafun ta juyo ta dube Baseera suka fuskanci juna sosai idanuwansu na yawatawa a tsakani gyaɗa kai Mariya tayi kafun ta sake kallon filin makarantar da yarda dalibai suke kai komo.

“Ba abin da yayi saura da za mu tsaya muma kai kawo akan sa ban zan iya cigaba da zama bane na fi bukatar na je gida”.

Kallon ta take yi da duk yanayin da take magana dashi da sam ba wani abun na a zo a gani murmushi take sakar mata na karfafa gwuiwa don bata so ta karyarwa da Mariya zuciya

.

“Shikenan naji mu tafi gidan amma da kin bari Dadyna ya turo a dauke mu bari na kirasa”.

Ta fadi tana mai zuge tsakarta domin dauko wayarta da sauri Mariya ta tare ta.

“Barshi ba sai kin kira shi ba kawai mu tafi domin a hanya zamu rabu gida zan wuce daga nan”.

Ware idanu tayi kadan cike da mamaki.

“Ba zaki je gidan namu b…”.

“Kawai dai zan zo amma yanzu na fi bukatar naje gida bana tattare da natsuwa a filin rayuwata”.

Gyaɗa kai Baseera ta shiga yi kamar wata kadangaruwa a hankali ta fara taka kafafuwanta tana karasawa bakin titin dake kusa da Get din makarantar ta su.

Bata son ta matsawa rayuwar Mariya bata so ta fiye yi mata magama akan abin da ta san ba ranar karewarsa komai take gani a filin duniyar mariya sai kara rikicewa yake yi

sosai take jin tausayinta a zuciyarta da ruhinta sosai  ita a karan kanta tana jin rashin jindadi a rayuwar ta ba macen da ta dauko a matsayin yar uwa ba ƙawa ba kamar Mariya sosai take jin sashi na zuciya da gangar jikinta na sauyawa da duk wata damuwa ta Mariya.

Nisawa tayi kafun ta daga hannu tana mai tsaida mai Napep bayan ya tsaya ta kira Mariya dake can gefe guda ta zo su ka hau domin wucewa.

Ko a cikin Napep ba wanda ya yi magana kamar mutuwa ta gifta su cikin yan mintina kalilan suka isa layin su Baseera nan ta sauka ta biya mai Napep kudinsa har da na Mariya da zai kai ta gidan su.

“Mariya sai na zo ki gaida su Umma”.

Gyaɗa mata kai tayi tana mai sakin yak’e nan mai Napep ya dau hanya domin isa da Mariya gida.

STORY CONTINUES BELOW

****

A hankali take takawa ko ina sasan jikin ta motsawa yakeyi sanye take da doguwar riga mai kalar baki da fari sa mayafin da tayafa kalar ja fuskarta da saukakkiyar kwalliya laɓɓanta sun yi jajir dalilin jan bakin da ta saka ja mai turuwa tun daga kofar gida take

kallonsa da wani irin yanayi mai girman gaske tana faman sakin wani murmushi mai kayatarwa a haka har ta iso gareshi.

Jingine yake da motarsa ya harɗe hannayensa a kirjinsa idanuwansa kur! Akanta kamar ya ga sabuwar halitta a filin duniyar sa.

Sosai yaji gabansa yayi wani irin dokawa lokaci guda  rintse idanuwansa yayi cikin tsananin tashin hankali mai girman gaske a hankali ya shiga buɗe su yana saukewa akan ta a daidai lokacin da ta iso gareshi cikin takun ta na jan hankali kusa dashi ta tsaya tana mai sanya hannunta guda tana dafa jikin motar sosai ta fuskance shi tana mai kaɗa idanuwanta cikin salon jan hankali.

“Uhmm Huzaif ai ban yi tunanin zaka zo ba”.

Ta fadi tana mai kai hannayenta tana kara gyara zaman mayafin nata wanda a zahirin gaskiya ba wai tayi bane da sunan gyarawa a,a kawai tayi ne domin ta bayyanar da yarda rigar tayi matukar matse ta a kirji haka ya kara bayyanar da cikar kirjin nata na matashiyar budurwa mai ji da kanta.

Murmushin yake kawai yake saki kafun yaja numfashi.

“Eh wallahi amma… Nace ba…”.

Sai kuma yayi shiru yana mai dubanta idanuwanta da ta kafe sa da su sosai yake hango wani irin yanayi da yake narkar masa da duk wani sashi na jikinsa bai san abin da ya hadashi da Hafsat ba bai san ya akayi ta shigo filin duniyarsa ba bai san ya aka yi har yake tsaye suna magana ba sosai zuciyarsa ta buga a duk lokacin da ya ga Hafsat a gabansa komai da yake kwanyarsa da zuciyarsa

canzawa yake yi sosai yake jin filin duniyarsa na canzawa game da ita.

“Kayi magana mana Huzaif”.

Ta fadi cikin salon kashe murya sai faman juya idanuwanta take yi a nasa.

“Uhmm ba komai wai dama cewa nayi Mariya ta dawo?”.

Ya fadi cikin yanayi na ɗarɗar kamar wanda yayi laifi ake tuhumarsa.

Ware idanu tayi jin abinda ya fadi ta shiga tsuke fuska kamar biri da lemon tsami.

“Me kake nufi Huzaif me ya kawo Mariya a maganar mu meye kuma hadin ka da ita na dauko ba wata ‘ya mace a filin rayuwar ka a yanzu kamar ni wacece Mariya kuma?”.

Ta fadi cikin sauti kamar zata kai masa bugu kafun lokaci daya ta rikice da zubda hawaye tana shassheka.

Hakan ba karamin firgita Huzaif yayi ba da sauri ya shiga ba ta hakuri kamar zai yi mata sujjada jikinsa ba abin da yake sai ɓari da kakarwa a hankali ya zaro Hankicif a aljihunsa ya kai fuskarsa cikin rawar jiki yana dauke hawayen.

A daidai lokacin kuma Mai Napep yayi Parking Mariya da take ciki tana kokarin fitowa ta hango su wani irin bugu taji gabanta yayi kanta ya shiga juyawa kamar zata zube a kasa da sauri ta rike karfen kofar Napep din tana ambatar.

“Yaa Allah”.

Komawa tayi ta zauna idanuwanta a runtse tana jin yarda zuciyarta ke yayyakewa da tashin hankali mai girman gaske ba ta san lamarin su ya kai har haka ba bata san cin amanar har ya kai haka ba ta lura So suke yi su ga bayanta so suke yi su kashe ta da ranta ba ta san sai yaushe zata daina ganin wannan bakin lamarin ba ba ta san sai yaushe duniyarta zata canza yanayi.

STORY CONTINUES BELOW

Sosai take cikin tashin hankali mai girma gaske mai kokarin raba ta da duk wani farin cikin da yayi saura a filin duniyar…ko da yake ba ma zata ce akwai farinciki a cikin duniyarta ba a yanzu domin ya jima da gushewa shekaru uku ana abu daya zuciyarta kullum cikin ciwo take sosai take hango yarda ALKALAMIN ƘADDARA yake juya duk wata rayuwarta a duk sakan ba ta tsammanin a cikin

shekaru uku da suka bada baya daidai da rana daya ta samu farinciki bata tunanin a cikin shekaru uku da suka shuɗe daidai da minti daya tayi dariya wai ta farinciki ba ta san wacce irin rayuwa bace take yi a duniyar nan komai da komai nata na daban ne bata tsammanin a duniyar nan akwai mai rashin jindadi da kwanciyar hankali kamarta.

Numfashi ta ja mai karfi zuciyarta na dauko mata jarumta tana aza mata ta gaji ba zata iya cigaba da zubda hawaye akan mutanan da ba su san tana yi ba ba za ta kashe rayuwarta akan mutanan da ba su san darajar da kimarta ba ta daina damun kan ta ta daina sanya kaita a damuwa alkawari tayi daga yau ba wani daga cikin su da zai sake dasa mata ciwo a zuciya buɗe idanuwanta tayi a hankali ta saka hannayenta ta shafe kwallar da suka cicciko mata fitowa tayi daga cikin Napep ta dube mai Napep wanda yayi kuri yana kallonta ganin ta fito ya buɗe bakin sannan cikin yanayi na tausayawa don ya tabbata akwai abin da yake dawainiya da duniyar rayuwarta.

“Sai Hakuri yan mata lamarin duniya ne sai an din ga kai zuciya nesa”.

Gyaɗa kai kawai tayi tana mai sakin yaƙe wanda take jin sa har cikin zuciyarta da sauri ta janyo hijabin jikinta ya dan rufe mata fuska  cikin yanayi na hanzari ta doshi kofar gidan domin bata so ma su ganta balle wani cikinsu ya raina mata hankali…

“Mariya!”.

Kamar daga sama ta jiyo sautin muryarsa ya ambace ta cak! Ta ji ta tsaya da tafiyar da take yi  sosai ta ji sautin amon muryarsa ya ansa kuwwa a kunnuwanta da ma

kwanyarta bakidaya a hankali ta dago kanta jin sautin takunsa yana karaso wa in da take kallo daya tayi masa da kai jin yarda zuciyarta ta harba da wani irin yanayi mai ciwo sosai.

“Uhmm…”.

Da sauri ta dago kai gami da daga masa hannu lokaci guda idanuwanta suka kara rinewa fuskarta kamar hadari da yake kokarin zubda ruwa.

“Huzaif!”.

Ta ambata cikin muryar gargadi kafun tayi masa wani irin duba wanda shi akaran kansa sai da yaji a jikinsa.

“kana tunanin a filin duniyar na akwai KALMA DAYA  da zaka fadi na tsaya na saurareka akanta kana tunanin akwai lokacin da zan iya batawa akan ka”.

Wani murmushi ta saki kafun ta juya ta dubi Hafsat dake tsaye jikin motarsa sai fama cika take yi tana batsewa.

“Bana tunanin akwai wani abu yayi saura a tsakanina da kai na fadi maka ba sau daya ba ba sau biyu ba hanyarmu ta rabu ba zamu sake haduwa ba har abada ya kama ta ka san da haka amma na lura so kake yi ka ture lamari kaki dauƙarsa da muhimmanci ka sani ba yarda za ayi kana tare da yar uwata sannan kace kana tare dani ta ya ya wannan lamarin zai kasance ina so ka sani ni da kai ba wata ALAƘA da za ta sake shiga tsakaninmu don haka na rokake da ka fice mani a rayuwa Huzaif na rokeka daga yau…”.

Shiru tayi jin yarda zuciyarta tayi wani irin nauyi mai girman gaske kasa tayi da kanta tana jin yarda idanuwanta ke raɗaɗi da kokarin zubda kwalla da sauri ta bar wajan tana karasawa cikin gida.

Bin ta yayi da sauri yana kiranta amma ina sai ma ta kwasa da gudu ta fada cikin gidan cak! Ya tsaya bakin soron yana mai da numfashi da yake ji yana kai kawo kamar zai rabu da gangar jikinsa hannayensa duk biyu ya dafe kan sa da su ji yake yi duniyar gabadaya na juya masa da wani irin ta shin hankali mai girman gaske bai san abin da yasa Mariya take gudunsa ba bai san abin da yayi mata ba baya iya tuna komai komai yake ji yana sauya  a filin duniyarsa daga kansa yayi ya dubi Hafsat da tayi masa kuri da idanu sai faman kumbure kumbure take yi cikin hanzari ta baro jikin motar ta tun karoshi kamar wacce zata kifa.

STORY CONTINUES BELOW

“Huzaif ni zaka ci wa zarafi ni zaka wulakanta a gaban waccen karamar yar duniyar ni zaka ketawa mutunci a gabanta to billahillazi baka isa ba zaka san ni kayi wa haka ka saurare ni”.

Ta karashe tana mai jan tsaki kamar zata tsinke Harshenta.

“Hafsat mana! ki daina fadin haka ni ban ci miki mutunci ba sannan ban ci zarafin ki ba”.

Wani kallo ta yi masa tana mai sake narkar da muryar cikin yanayi kamar mai son sakin kuka.

“Haba mana Huzaif ya za ace a gaban makiyiya ta zaka tsaya kana kulata ai sai ta rainani gaskiya ni karka sake in kuma ba haka komai zai iya faruwa”.

“Naji shikenan ba za a kuma ba”.

ko dubansa ba ta sake yi ba domin kuwa taji haushi matuka da yanayin da ta ga ya tsaya da Mariya a hankali ta ja kafafuwanta ta shige cikin gida shi kuwa Huzaif nan ta barshi tallaɓe da kai yana jin duniyar na juya masa ji yake komai na kwance masa a

hankali ya ja jiki ya isa wajan motarsa ya shiga sai da ya shafe lokaci kafun yayi mata Key ya bar unguwar.

*******

Kallon da Umma ta watsa mata ne ya sanyata saurin yin kasa da kai tana kokarin shigewa daki ta dakatar da ita.

“Zo nan Mariya”.

Duban Umma tayi ganin ba wasa a fuskarta ya sanyata dawowa da baya ta samu waje ta zauna.

“Baki ji ko Mariya, baki dai ji ko ni ban isa dake ba, ban isa nace miki bana son abu ba ko, ke kenan kullum abu daya kamar cin kwan makauniya dube ki don Allah kullum jiya i yau kowa na auki da kuzari amma ban dake kamar wata kazar mayu ban san ya zan yi dake ba ban san mai zan miki ba kuma ni dai a gaskiya na gaji da wannan lamarin naki na lura dai so kike yi ki kashe kan ki sannan hankalin zai kwanta in ba haka ba ta ya ya mutum sam shi a rayuwarsa ba zai dauki ƙaddara da jarabawa ba”.

Yanayin da taji sautin Muryar Umma ya tabbatar mata yau dai  ta kaita karshe duk hakurin Umma yau tayi mata fada tabbas abin ya kai intaha runtse idanuwanta tayi ta sani Umma ta dade cikin damuwa da ta ta damuwar ta sani sosai lamarin ta yake damun Umma sosai take gani a yanayinta tsayin lokacin da ta dauka cikin wannan halin ita ma haka ne ya kasance wasu hawaye taji sun zo mata.

“In kika sake kikayi mani kuka a nan wallahi sai na kwada miki Mariya don naga lamarin naki ba sauki sai abu ya ki ci yaki cinyewa haba mana maza ki tashi ki bani waje nikam tun kafin ki kai ni Bango ance mutum ya girma amma sam rayuwarsa ba ta sauya ba”

.

Da sauri ta dago idanuwanta da suka cika da kwalla ta sanya hannu ta dauke su.

“Uhmm Umma fa ba wani abu bane ba abin da kike zargi bane fa kawai bana jin dadin jiki nane kisan yau muka kammala komai na makaranta daga yaushi kenan”.

Kuri tayi mata da idanu tana karantar yanayin ta ta san Mariya ba za tayi mata karya ba kuma in har bata manta ba kwanakin baya ta sanar da ita sun kusan kammala karatun nasu gyaɗa kai tayi tana mai sakin fuska sosai.

“Yo ai ke ce Mariya wani lokacin da kayan haushi kike wallahi sam ba a gane miki yarda kika san sahun keke ai shikenan Allah ya taimaka yasa anyi a sa’a kin ga yanzu dai burin naki ya fara ciki sai ki zage kuma ki cigaba da kokari kamar yarda kika saba”.

Gyada kai tayi tana mai kalato murmushi tana daura a fuska mikewa tayi.

“Yawwa na mance dazu ma Yayan naki ya kira ni a waya”.

STORY CONTINUES BELOW

Ras! Gaban ta ya fadk da sauri ta juyo ta dubi Umma cikin yanayi na tsoro.

“ya tambaya ina kike nace kina makarantar wai shi ne yace har yanzu baki kammala ba ne ya dauko tun wacce shekarar ai zaki gama”.

Yaƙe tayi.

“Ke ma dai Umma tun yaushe nace miki mun gama kawai mun dau shekara daya mun kara domin koyan sana’o’i hannu ke fa nan na fada miki an buɗe makarantar koyan sana’a na fada miki kuma kika aminci amma yanzu kina nuna ba ki sani ba”.

Dafe kai Umma tayi kafun ta dubi Mariya.

“Wai ni kam anya ban da cutar mantuwa kuwa Mariya haka fa mukayi da Yayan naki shekaran jiya wallahi yace an kawo sako nace a,a bayan kuma an kawo din”.

Murmushi Mariya tayi.

“Akwai abin da kika sakawa ranki Umma”.

“Ai komai ya faru kece sila mariya lamarin naki ne sosai ya firgita min rayuwa komai nawa sai a hankali…Allah dai ya kyauta kawai”.

“Ameen Yaa Rabbi”.

Mariya ta ansa tana mai shigewa daki zuciyarta da wani irin yanayi mai girman gaske ba abun da ke ansa kuwwa sai maganar Umma nacewa Dr.Karami ya kira wai har ya

tambayeta abin ya daure mata kai in har bata manta ba yau kusan shekaru hudu kenan rabonta dashi duk zuwan da yake ba sa haduwa kullum cikin wasan buya suke a tsakanin su ta rasa dalilin da yasa haka ta rasa mai ya ke damun Dr.Karami komai nashi ya sauya tunda ya dauki kafarsa ya bar kasar nan shikenan kuma ya shafe babin ta da farko ta dauka laifinta amma daga baya kuma zuciyarta ta jima tana sanar da ita cewa kawai dai baya bukatar ta ne cikin duniyarsa shiyasa itama ta ajjeshi gefe kamar yarda Baseera ta bata shawara akan ta ajje lamarinsa gefe in ba haka ba damuwa dashi da take yi sosai zai taba mata rayuwa ba kadan ba.

A yanzu a daidai wannan lokacin komai take ji yana dawowa sabo fil! Ji take yi kamar yanzu komai ke faruwa ji take yi kamar yanzu ne suka hadu da Dr.Karami ji take yi kamar yanzu shakuwarsu ta wanzu a duniyar nan sosai take jin zuciyarta nayi mata tuni akan komai wani irin yanayi take jin jikin ta ya shiga komai take ji na canzawa numfashin ta take ji yana  sauka a duk wata dakika da lamarin Dr.Karami sosai take jin bugun zuciyarta na sauyawa da duk wani lamarin Dr.Karami sosai take jin idanuwanta na bukatar ganinsa a daidai wannan lokacin sosai take jin zuciyarta da kwanyarta suna son tunaninsa.

Runtse idanuwanta tayi da karfin gaske tana mai kai hannunta saitin da take zaton nan zuciyarta take ajje a kirji sosai take jin bugunta na sauya komai ma da komai ji take yi ya sauya a lokaci guda.

Numfashi take ja a hankali har ta isa bakin katifarta ta baje tana mai duban saman dakin nasu zuciyarta sai zarya take yi da duk wani lamari da tunani na Dr.Karami lokaci guda taji wani murmshi ya subuce mata tuna rayuwarta tayi ita dashi a Asibiti…

“wato sabo ‘yar taki tayi kwantai ba mai so an gama yawan ta zubar shine yanzu take bibiyar samarin Hafsi ko to wallahi ba zata sabu ba bindiga a ruwa ko da bakar jaɓa take aiki ba ta isa ba tayi kadan mu zuba ni da ita shege ka fasa gata ga Hafsi nan ta cigaba da bibiyar samarin nata”.

Kamar daga sama Mariya taji saukar kalaman a firgice ta mike tayo waje Goggo Marka ta hango tsaye ita da Hafsat sai faman cika take yi tana bacewa duban Umma tayi dake zaune tayi banza da su kamar ba da ita take yi ba.

Wani kallo Goggo Marka tayi mata kafun ta nuna ta da tsaya.

“ke dan hular ubanki shine saurayin na Hafsi kike kokarin kwacewa saboda ke kin yi kwantar ko to wallahi baki isa ba tun wuri ki fita daga harkar Hafsi in kuma ba haka na rantse miki da Allah sai kin sha mamaki na”.

Fakare Mariya tayi mamaki ya cikata ga mari ga ansar jaka duk ba su isa ba ita batayi magana ba sai su ne za su zo suna gaya mata magana har sun manta waye Huzaif a wajanta har suke kokarin ci mata mutunci wani murmushi mai ciwo ya kufce mata ta dubi Hafsat da Goggo kafun da girgiza kai domin ita dai abin ta rasa ma gane kan sa wai kiri-kiri sai faman IHU BAYAN HARI suke yi gabadaya sun mance baya sun mance waye ita har da suke duban idanunta suna fadi mata haka ji tayi kamar ta buɗe baki ta mai da musu da martani amma ina ba zata iya ba domin sa tasan ran Umma in yayi dubu sai ya baci shirun shine mafi alheri a gareta da sauri ta juya ta koma cikin daki zuciyarta a cunkushe ji take yi kamar ta daura hannu akai ta kurma ihu don bakin ciki da takaici.

“FASHIN SAURAYI?”.

Ta ambata cikin wani irin yanayi mai haifar mata da wani lamari mai girman gaske mamaki abin yake bata wani lokacin kuma ya bata bakin ciki da takaici bata ganin laifin kowa sai Huzaif tayi mamaki da canzawarsa tayi mamaki da lokaci guda soyayyar da yake nuna mata ta gani kashe ni ta sauya gabadaya kamar bai taba furta mata KALMAR SO ba a duniyar nan komai take gani kamar a Mafarki.

Nisawa tayi tana tuno lokacin baya yarda ya haukace akanta yana nuna yana son ta amma yanzu kamar bashi ba ta ga laifin Hafsi ba domin sai bango ya tsage kadangare ke samun mafaka kuma tayi alkawari ita da Huzaif har abada zata nuna masa ta fi karfin  wulakanci da cin zarafi za ta nuna masa ita mace ce mai daraja da kima wacce ta san kanta ba irin matan da suke ɓarin jiki bane wajan kai kawo wajan saurayi ta daina damuwa dashi ta daina damuwa da bakin cikin da suke tura mata shi da Hafsat.Huce mai zafi yake fesarwa kamar wani kumurci. tashi yayi tsaye daga kan kujerar dayake zaune yana bugun Table din dake gabansa idanuwansa sunyi jajir kamar wanda aka yiwa sirace da barkano.+

“Alhaji Abdulwahaab na fada maka ka fice mani daga cikin Office in kuma ba haka zan yi maka abin da baka taba zato ba”.

Ya fadi yana mai kara turbuɗe fuskarsa kamar zai cinye shi danye.

Murmushi Alhaji Abdulwahaab yake saki mai cike da bakin ciki da takaici wai yau har shine Dr.Erena zai dubi tsabar idanuwansa yana fada masa magana son ransa kamar wani wanda ya zo maula wajansa numfashi ya ja kafun ya dubi Dr.Erena sosai yana mai gyaɗa kai wani irin tukuki yake ji zuciyarsa nayi ba abin da yafi bata masa rai kamar yarda Dr.Erena ya zage yana keta masa rashin mutum bai taba tsammanin haka ba bai taba kawo wa kansa haka ba bai yi tunanin duk rashin mutuncin Dr.Erena zai iya yi masa.

“Dr.Erena ni…”.

“I Say get out! i don wanna see you in my Office”.

Dr.Erena ya fadi a zafafe yana kara so wa wajansa har yana tunkuɗashi.

“Ka je kayi abin duk da zakayi kudi ne na cinye in akwai wanda ya isa ya kwatar maka ka turo shi tunda naga abin naka hauka ne har nawa ne kudin naka da zaka zo kana yi mani ihu kamar wani kare a cikin Compay”

.

Mamaki ne ya sake kume Alhaji Abdulwahaab jin zuciyarsa yake yi kamar zata faso kirji tayo waje gabadaya saboda tsabar tsananin bakin ciki dake nukurkusar sa hannunsa ya kai ya saukar da na Dr.Erena dake kafadarsa fuskarsa da wani murmushi kafin ya fara taka kafafuwansa a hankali har ya isa bakin kofar hannunsa saman Handle din ya juyo ya dubi Dr.Erena cikin wani irin kallon wanda shi kansa Dr.Erena sai da yaji wani iri a zuciyarsa amma bai bari hakan yayi tasiri a fuskarsa ba sai ma wata uwar harara da yake cilla masa.

A daidai lokacin da ya tura kofar domin fita ita kuma Areefa ta sanyo kai cikin Office din saura ka dan suyi gware dashi amma tayi saurin kauce wa don a tunanin ta Dr.Erena ne.

“Yaa Allah”.

Ta furta tana duban Alhaji Abdulwahaab da wani irin yanayi mai kama da tuhuma kafin ta dubi Dr.Erena da yake faman cika yana batsewa kamar zai tarwatse ganin Areefa ya sanya shi ware idanuwansa sosai mamaki na kokarin ka kashe shi ganin Areefa yau a cikin Office din sa How Comes yace ya manta rabon da ya ganta ko sashin sa ta zo amma yau ita ce a bangaren sa abin mamaki lokaci guda jikin sa ya shiga rawa ya fara takowa izuwa gareta a daidai lokacin ta juya ta dubi Alhaji Abdulwahaab yanayin da ta ganshi a aciki ya tabbatar mata akwai abin dake faruwa bata karasa tsinkewa da lamarin ba sai da ta ga Alhaji Abdulwahaab ya kashe mata idanu daya hakan ya kara jefata cikin wani irin yanayi mai girman gaske na mamaki.

“Nace ka fice mani daga Office, ko sai na saka an fitar da kai a rashin mutunci ne?”.

Dr.Erena ya sake fadi a zafafe ganin irin kallon da Areefa ke yi masa juyawa yayi ya dube ta yana faman sakin Murmushi kamar tsohon da aka bashi kyautar budurwa.

“Areefa ban yi zato ba…”.

Hannu ta daga masa alamun bata so fuskarta a tsuke.

“Haba mana Dr.Erena me haka kayi wanda sam bai dace ba abokin ka ne fa wanda bai kamata ace irin haka ya faru a tsakaninku ba”.

Ta fadi tana mai dubansa kafin ta dubi Alhaji Abdulwahaab wanda a daidai lokacin yake ficewa daga Cikin Office idanu ta kashe masa kafin ta juyo da kallon ta zuwa wajan Dr.Erena fuskarta da alamun damuwa.

STORY CONTINUES BELOW

“Ban san haka wasu in suka gani ai sai  su yi muku dariya”.

Wani gundumeman tsaki ya ja gami da kau da kansa.

“Bar ni kawai Areefa raina min hankali zai yi ni kuma a rayuwa ta abin da bana so kenan komin kusanci na da kai in har kace zakayi mani akuyanci to wallahi ba zan kyale ka”

.

Sosai ta gano in da lamarin ya dosa amma cikin basarwa da kin ba wa zancen muhimmanci ta dube shi.

“Good and Fine ina son mutum haka mai ra’ayi irin naka na rashin son daukar raini”.

Ai ji yayi kamar ta cilla shi a gidan aljanna haka ya shiga yashe baki kamar wani bugun shaho da sauri ya dube ta cikin rawar jiki yana yi mata nuna da ta zo ta zauna a hankali ta fara taka kafafuwanta idanuwanta na kansa kallon sa take yi da wani irin kiyayya mai girman gaske dubansa take yi da wani irin haushi da takaici zuciyarta take ji tana wani irin kartawa kamar zata faso kirjinta ta fito saboda tsabar tsanar sa da take ji a duk wani sashi na zuciyarta.

‘Ni yake so wai da aure’

Ta ji wani sashi na zuciyarta na fadin haka ji tayi kamar ta daura hannu aka ta kurma ihu don bakin ciki amma ina bata so ta bata shirinta ba ta so ta bata salon da Hajiya Layla ta karanta mata tayi amfani dashi bata so ta samu wata ɓaraka daga wannan KUDIRIN nata da take kokarin cin masa.

Isa tayi cikin takunta wanda yake kara fizgar Dr.Erena yana jefashi cikin wani irin hali na matsanancin son ta sosai ya firgice cikin lokaci kalilan sai kai kawo yake yi yama rasa abin da ya dace yayi sai kai kawo yake yi yana dube-dube sannan ya juya ya janyo kujera kamar zai zauna sai kuma ya fasa ya shiga sakar mata murmushi ita kan ta sai da taji wani iri na daban da yanayin da yake nuna wa amma zuciyarta wani irin kunci take jefa ta a duk lokacin da ta kalle shi ji take yi kamar ta tashi ta shake shi ya mutu kowa ya huta sai dai wani sashi yana gargadin ta da wannan kudirin nata na kisa wanda sam bai dace ace tana sanyo shi a lissafin ta ba.

“ka zauna mana gabadaya duk ka wani rikice sai kace wanda aka kama da satar butar masallaci”.

Sai a lokacin ya tsaya da kai kawon da yake yi ya janyo daya daga cikin kujerun dake girke a gaban Table din ya zauna yana fuskantar ta.

“Nayi mamaki matuka da ganin ki Areefa na dauka har yanzu ba a yafe mani gingimeman laifin da nayo ba”.

“wa yace kayi laifi?”.

Ta tare shi tana mai sakin wani yake da BAI KAI ZUCI BA.

“Uhmm dole nace haka mana Areefa yaushe rabon da  ki tsaya ki saurare ni yaushe rabon da ko alfarmar kallon arzuki na samu a gareki muna

Company daya amma har ki shigo ki gama abin da zaki yi ba ki dubana da  kallon arzuki in ma nayi miki magana sai ki nemi dizga ni don kawai na nuna ina son ki ban san laifin da nayi  har ya kai haka ba ban san me nayi miki da kika tsanani har haka”.

Runtse idanu tayi jin ya ambaci kalmar ‘ina son ki’ wani takaici da makakin bakin ciki taji sun taho sun tsaya mata a zuciya wani abu mai nauyin gaske taji ya zo saitin kirjinta ya zauna numfashin ta taji yana sama da kasa kamar zai katse.

Sosai taji ba za ta iya cigaba da zama cikin Office din nan ba sosai take ba za iya kara ko da minti guda bane tare da Dr.Erena komai zai iya faruwa sosai zuciyarta ke tururi sosai take ji kwanyarta na juya wa.

STORY CONTINUES BELOW

A hankali ta mike kan kafafuwan ta tana jin yarda kanta ke sarawa da wata irin tsana ta Dr.Erena bata zaton zata iya juri zuwa gareshi bata zaton zuciyarta za ta barta tayi abin da ya dace sosai take jin ina ma ace ta kashe shi shine kawai hanya guda da  take zaton samun nasararta a akansa amma ina hakan sam bai dace ba bai dace ace zuwa wannan lokacin ace ta kashe shi ba  ba ita kadai ke bukatar Dr.Erena ba ba ita kadai bane a filin duniyar nan take son daukar fansa akan sa mutane da yawa wanda ba ta san a dadin su ba suna BURI da KUDIRI mai girman gaske akansa sai dai rashin WATA DAMA da ba su samu ba amma gata ita ta samu amma tana kokarin ruguza komai.

“Areefa ya dai ba dai tafiya zakiyi ba?”.

Muryar Dr.Erena ta doki kunniwanta ba ta san ma ta fara tafiya ba sai da taji amonsa sanna ta dawo hayyacinta har ta kai bakin kofa da sauri ta juya ta dube shi fuskarta da wani irin murmushi wanda ita a karan kanta ba ta san ma tayi ba sam! ba tare da tace dashi komai ba ta buɗe kofar ta fita.

Fitar ta ke da wuya Dr.Erena ya mike cikin hanzari fuskarsa na kara haɗewa waje guda wayarsa ya janyo ya shiga danna kira yana mai kaita saitin kunnuwansa sai faman numfashi yake ja.

“Bobby”.

Ya fadi da wata irin murya kafun ya dora da fadin.

“Ina son ganin ku anjima a gida”.

Daga nan bai sake cewa komai ba ya sauke wayar yana mai sakin wani murmushi na mugunta yana murza gashin gemunsa.

“Alhaji Abdulwahaab”.

Ya furta yana mai hade hannayensa waje guda yana lankwasawa.

******

“Meye amfanin haka da kayi Alhaji Abdulwahaab baka tsoron Dr.Erena ya turo a kashe ka  don karka kawo masa tsaiko cikin lamarin sa kai fa da kanka ka fadi mani ko waye ya zo masa da rainin hankali ko yana kokarin tona masa asiri kashe shi yake yi amma kai kayi gangancin tunkaransa akan wani dalilin?”.

Areefa ta fadi tana mai duban Alhaji Abdulwahaab da takaicin duniya ya ishe shi sai faman huci yake yi kamar wanda zai hadiyi zuciya ya mutu.

Mikewa yayi tsaye ya shiga kai kawo sai faman kai wa iska naushi yake yi kamar da ita cikin wanda suka bata masa rai juyawa yayi ya dubi Areefa ita ma idanuwanta na kansa hannun ta rike da Glass Cup a hankali take kurbar lemon da yake ciki.

“Areefa ya kamata ki san wani abu wannan abin da ki ga nayi masa so nake yi na kara tunatar dashi cewar ina nan fa ban matan abin da ke tsakaninmu ba don na lura sam ya mance wani abu da ya shiga tsakanina dashi ba wai nayi bane don neman hakki akan sa a,a nasan ma ba samu zan yi ba nayi hakan ne don ya sani ina nan kuma komai daren dadewa sai ya bani hakki ba zai ci bulus ba”.

“Wannan ba magana bace Alhaji Abdulwahaab”.

Areefa ta katse shi da fadin haka kafun ta dora da cewa.

“Ko Shakka bana yi yanzu haka nasan yana nan ya na kokarin bin hanyar da zai kawar da kai a filin duniyar nan kar kayi tunanin ABOTA da ta ratsa tsakaninku zatayi wani tasiri a

gareshi na rantse maka da Allah yarda da lura da Dr.Erena duk da dai kafi ni saninsa amma ina da zaton ko kaninsa ne zai kawo masa wasa zai iyayi masa komai Dr.Erena MUGUN ABOKI ne a gareka domin kuwa ba ya bukatar ace ka samu cigaba yarda yake yi maka yana nuni da cewa da ma can abin ka yake so”.

Runtse idanu yayi yana kai komo zuciyarsa yake ji tana zafi bai taba zaton Dr.Erena zai masa haka ba bai taba zaton ko da a mafarki ne haka zata faru ba.

STORY CONTINUES BELOW

“Shikenan Areefa amma don Allah ya kamata ace zuwa yanzu kin san komai game dashi lokaci tafiya yake yi a ko wani lokaci zai iya gano ke wacece  tsoron abin da zai je ya dawo bana so ayi BIYU BABU ba wan ba kanin karatun dan kama”.

Wani murmushi ta saki kafun ta juya idanuwanta.

“Alhaji Abdulwahaab”.

Ta fadi cikin wani irin yanayi tana mikewa kan kafafuwanta da wani irin ƙarfi da take ji yana taso mata tun daga zuciya da rushi ajiya Cup din dake hannunta tayi kafin ta dauki jakarta dake kan Table din da suke zaune a hankali ta fara taku kamar ba zata ce dashi komai ba juyawa tayi a hankali har zuwa lokacin da murmushi a fuskarta da BAI KAI ZUCI BA amma yana tattare da abubuwa masu yawa.

“Yanzu za a fara Alhaji Abdulwahaab ka shirya zaman kallo”.

Ta fadi tana mai kashe masa idanu kafin ta juya ta cigaba da tafiyarta cikin sassarfa.

Hannu ya daga ya jinjina mata yana hango gaskiya a batunta yana hango kudiri da buri da ta dauka akan Dre.Erena abin da yake so kenan dama kuma tsaf ya shirya duk yanayi sai ya ga yarda wasan nan zai kare kamar yarda ta fada amma kuma dole ya ja baya da Dr.Erena kamar yarda Areefa ta fadi ya san dole ya farauce shi a ko wani yanayi zai iya yi masa bazata.

*******

Kai kawo kawai take yi cikin tsakiyar falon gabadaya kanta ya gama kullewa tunaninta take ji ya cak! ya daina tafiya yarda ya kamata numfashi take ja a hankali tana dukan hannunta da dayan idanuwanta sun kaɗa sun yi jajir kallo daya zakayi mata ka gane tana cikin damuwa matsananciya da tarin KALUBALE.

Sosai take ji a ranta lokaci yayi sosai take jin komai na dawo mata kamar yarda ya faru a shekarun bayan komai zuwa mata yake yi komai kallon sa take yi a yanzu yake faruwa ba TUNA BAYA bane runtse

idanuwanta tayi zuciyarta da wani raɗaɗi da zugi ga wani bugu da take yi kamar zata faso kirji ta yo waje.

Zubewa tayi kan kujera ta mai jan numfashi wasu kwalla suka cika mata idanuwa hannun bibbiyu ta dafe kanta da take ji yana barazanar tarwatsewa.

“Yaa Allah”.

Ta furta cikin wani irin yanayi matsananci duniyar take ji tayi mata zafi da kunci komai take ji babu dadi a hankali ta kuma mikewa

hannayenta goye a bayanta ta cigaba da safa da marwa so take yi ta tunano abin da ya dace tayi so take yi

zuciyarta ta kawo mata wata satar ansa da za tayi mata amfani so take yi kwanyarta ta binciko mata wani abu mai girman gaske da ya dace ace shi ya kamata tayi.

Motsin kofar da taji ne ya sanyata saurin juyawa Areefa ce ta gani tana kokarin shigowa cak! ta tsayar da idanuwanta akan ta sosai take jin komai na sake dawowa mata kamar yanzu ya faru wani tunani taji ya zo mata a bazata runtse idanu tayi tana mai sake buɗe su akan Areefa gabatan taji yayi wani irin dokawa da abu mai girma.

‘Anya kuwa?’

Ta fadi a can cikin ranta tana mai girgiza kai a daidai lokacin Areefa ta iso gareta tana mai dubanta.

“Ya dai Maama ko jikin ne?”.

Ta fadi tana mai yawatawa da idanuwanta akanta.

Girgiza ka tayi alamun babu komai hannunta ta riko tana mai sarkewa cikin nata da wani irin yanayi mai girman gaske da sauri Areefa ta bude idanuwanta tana kallon cikin yanayi na alamun son sanin wani abu

STORY CONTINUES BELOW

murmushi tayi mata kafun ta jata suka zauna waje daya suna fuskartar juna zuciyar Areefa sai kai kawo take yi so take yi ta san abin da ke faruwa domin ta hakiƙance yanayin da take ganin Hajiya Layla a ciki ya tabbatar mata akwai matsala bata saba ganinta cikin wannan yanayin ba duk da boyewar da take yi na abin dake damunta amma ita a jikinta taji kamar akwai wani abu mara dadi dake shirin faruwa.

A hankali ta shiga motsa laɓɓanta idanuwanta akan Hajiya Layla da sai faman yak’e take yi kamar wacce akayi wa dole zuciyarta na bugawa da wani irin yanayi na tashin hankali tsoro take ji tsoro mai girman gaske tana son tayi wa Areefa magana

amma zuciyarta na gargadinta akan haka bata san ya zata dauki lamarin ba bata san ya zata fuskata ba

tsoronta daya lamari ya maimaita kansa bata son haka bata son abin da zai sake dawowa a matsayin WAIWAYE sosai ta sani Areefa zata tashi hankalinta ita kuwa a filin duniyar nan abin da ta tsana kuma take gudunsa kamar shiga damuwar Areefa bata so ace ta sanadinta wani abu ya same ta so take yi ace har karshen rayuwarta ta dauwamar da Areefa cikin farinciki da muradan jin dadi amma Ta ya ya hakan zata kasance?.

‘Bata sani ba’.

Zuciyarta ta fadi duban Areefa tayi akaro na ba a dadi wacce gabadaya ta gama shiga yanayi lokaci guda jikinta yayi sanyi sosai.

“Maama wai meke faruwa ne don Allah sosai naji gabana na faduwa fa don Allah fada min”.

Ta fadi tana mai kara matse hannunta a na  Hajiya Layla.

“Ban san ya zance miki ba, ban san ta ya ya zan fuskance ki ba, sosai nake jin rashin jindadi sosai zuciyata ke bugawa ina tsoron abin da zai je ya dawo, ba na son ace ta sanadina kin sake fadawa halin damuwa bana so nayi miki Waiwaye…”.

“Maama!!!”.

Areefa ta fadi da sauti mai girma a muryarta kafun ta sake motsa laɓɓanta kamar zata yi kuka.

“Don Allah mene ne? Ki fada min zuciyata sosai take bugawa Allah taba ki ji”.

Ta karashe tana mai dago hannun Hajiya Layla tana kaiwa saitin inda take zaton zuciya na ajje.

“Areefa wani abu nake so na tambaye ki guda daya kwal! Amma kuma ban san yarda zaki dauki lamarin ba ban san da wacce fuska zaki anshe ni ba…”.

“Kawai ki fadi koma mene ne zan dauke shi a yarda ya zo mani nayi miki alkawari”.

Ta fadi da murmushi na kara karfin gwuiwa ga Hajiya Layla don ta lura da ita sosai yanayin ta ya sauya kamar da tsoro akan abin da take so tambayar ta akai.

“Zaki iya tuna ranar da muka dauko ki daga gidan marayu?”.

Yanayin da take furta kalmomin da yarda bugun zuciyarta ke sauyawa ya sanya Areefa kureta da idanuwa kanta taji lokaci guda ya ansa wata kara mai girman gaske kirjinta yayi wani irin dokawa kamar zuciyarta zata faso kirji ta fito a hankali ta ji duniyar na juya mata idanuwanta lokaci guda suka shiga lumshewa da wani irin tashin hankali mai girma wani CIWON RAI mai tsanani zafi da zugi taji ya ta so mata komai taji yana dawo mata kamar yanzu yake faruwa gabadaya numfashin ta ya dauke lokaci guda ta zube jikin Hajiya Layla ganin haka da ita kuma tayi ya

sanyata kwala kara mai sautin sai da falon ya ansa gabadaya cikin tsananin firgici da razana tashiga girgizata tana ambatar sunanta amma ina Areefa tayi nisa cikin wata duniya mai cike da kwazazzaben tashin hankali da sanya zuciya ciwo.

STORY CONTINUES BELOW

Da gudu ta mike ta isa wajan Firjin dake girke cikin falon ta buɗe gorar ruwan EVA ta sungoma tana mai balle murfin tana isowa gareta ta tuntule mata akai aiko wani numfashi mai karfi ta ja har tana sarkewa da sauri Hajiya Layla ta durkushe idanuwanta na zubda hawaye masu zafi jikin ta ba abin da yake yi sai rawa laɓɓanta na kaɗawa.

“kiyi Hakuri Areefa ban so haka ba, abin da nake gudu kenan shiyasa na ki tambayar ki ban son abin da zai jefa rayuwarki a wani yanayi ban son na sake fama miki ciwon da ya jima a zuciyarki…”.

Cikin wani irin yanayi Areefa ta daga mata hannu.

“Bakomai Maama wallahi ba komai karki damu tambaye ni abin da kike bukata na san ba wai zaki tambayeni bane don cutar dani”.

Ta fadi da hawaye a idanuwanta zuciyarta na wani irin motsawa da ciwo mai tsananin gaske laɓɓanta take tura cikin bakinta tana cizawa komai taji ya sauya mata jikinta take ji yana narkewa kamar ruwa.

Duban Hajiya Layla tayi wacce gabadaya ta gama rikicewa da tashin hankali ganin halin da Areefa ta shiga jikinta sai faman kaɗawa yake yi ta janyota jiki tana rungumewa.

“Kiyi Hakuri Areefa…”.

“Ya isa haka Maama don Allah”.

Shiru tayi jin abin da ta fadi dubanta take yi cikin wani irin yanayi na tausayawa zuciyarta na kara narkewa da kauna da tausayin Areefa.

“Shikenan na bari”.

Hajiya Layla ta fadi da murmushin yake a fuskarta Kafun ta riko hannun Areefa sosai tana kwanta da kanta a kafadarta.

“Abu daya nake so ki fama min in har zaki iya tunawa Areefa kuma in har ba za ki kuma shiga yanayin nan da kika shiga yanzu ba kiyi man alkawari”.

Gyaɗa kai tayi da murmushi a fuskarta tana mai kara kwantar da kanta a kafadar Hajiya Layla.

“NAYI ALKAWARI”.

Shiru ne ya ratsa falon na yan mintina ba wanda ya sake magana a cikin su sai ajiyar zuciya kawai a hankali Hajiya Layla take shafar kan Areefa tana son yin magana amma zuciyarta na tsoratar da ita akan yin maganar domin bata san abin da zai faruwa ba sai dai kuma bata da zaɓi dole sai tayi tambayar domin ita kadai ce hanyar da take hango mafita a gareta da ita kan ta Areefa din.

“Bayan fita ta daga cikin Motar Dr.Erena shin gidan sa kuka tafi ko kun biya wani waje daban ne?”.

Tsoro sosai ya bayyana a fuskarta lokacin da take maganar tana jin yarda jikin Areefa ya dauki rawa lokaci guda tana kankameta ajikinta sosai taji wani irin yanayi wanda bata san ya zata misaltashi ba game da Areefa  lokaci guda taji gabanta ya yanke ya fadi da tashin hankali.

“Areefa”.

Ta kirata muryarta na rawa.

“Na’am Maama”.

Ta ansa ta da son nuna ba komai amma yarda take ji a zuciyarta da ruhin ta kamar an dauko KASKO WUTA an juye mata haka take jin kirjin ta na wani azabar zafi runtse idanu tayi kafun ta motsa baki.

“Ba gidansa muka je ba wani daji muka nausa sosai ya kaini wani gida wanda shi kadai ne a wannan lokacin…”.

Da hanzari Hajiya Layla ta dagata tana dubanta bakinta har rawa yake yi.

“Kenan ba gidan sa ya kai ki ba ko to gidan da kike ce kun je din waye a cikinsa?”.

Runtse idanu ta sake yi idanuwanta na kawo kwalla.

“Haba mana Areefa karki yi kuka kin yi mani alkawari”.

Hannu ta saka ta dauke hawayenta kafun ta shiga bata labrin abin da ya faru shekaru masu dama da suka shuɗe.

Kuka sosai Hajiya Layla take yi zuciyarta da ruhinta na zafi sosai ta rungumi Areefa ita ma da take kuka a hankali ta mike fuskata da murmushi mai tsananin ciwo.

“Shikenan Areefa ina so duk runtsi duk wuya karki sake daidai da rana daya Dr.Erena ya san nan gidan sannan ko yace yana so ya gana da iyayenki kice masa zakiyi shawara ki zo ki same ni don nasan nan da dan lokaci ya bukaci son ganin iyayenki domin neman auren ki auren da nake so ayi sa…”.

“Maama”.

“Shiru Areefa kiyi abin da nace kawai”.

Daga nan ba wanda ya sake magana a cikin su Hajiya Layla sai safa da marwa take yi a tsakar dakin ita kuwa Areefa kwance tayi luf! tana jin yarda tsana da kiyayyar Dr.Erena ke kara samun masauki a filin zuciyarta KUDIRI tayi tare da Alkawari duk runtse sai taga bayan sa a filin duniyar nan..A firgice ya farka daga barcin da yake yi mai dauke da wani RIKITACCEN AL’AMARI wanda ya kusan sanya zuciyarsa da kwanyarsa daina aiki na wucin gadi sosai ya firgita da mafarkin barcin da yake jin sa kamar a zahiran ce ne ya faru ba wai a badinance ba.6

Da sauri ya zuro santala santalar kafafuwansa da hutu ya gama yi musu ƙawa a hankali ya sanya takalmarsa da suke bakin gadon ajje masu matukar kyau da burgewa kallo daya zakayi musu ka gane na zallar fata ce.

Mikewa yayi kan kafafuwansa jikinsa sanye da Boxer wanda ya kawo masa har gwuiwa sai singilet mai kalar ash-colour wanda tayi matukar kama jikinsa ta bayyanar da cikar halittarsa ta mazantaka yana da damatsa da budadden kirji sosai mai dauke da kwantaciyar suma mai santsi  kugunsa kuwa ba shi da fadi sosai ya dan tsuke kadan.

A hankali ya dauko jallabiyarsa mai ruwan jinin kare dake rataye ya sanyawa jikinsa wanda hakan ya kara haskakashi matuka Toilet ya nufa ya wanke baki sannan ya watsa ruwa sosai kafin ya fito ya shirya cikin Suit baka sosai ya gyara  sajensa gami da tararren gashin kansa gyararre in ka gani sai ka rantse Shampoo ya saka masa amma ko kadan haka sufarsa take baka sidik sai sheki da take yi sosai ya ke kula da ita wajan gyara kwantattacen sajensa  shima haka fuskarsa ta fito fes da ita manyan idanuwansa da dogon hanci gami da bakinsan dan madaidaici sun yi matukar tasira wajan kara ƙawata fuskar tashi.

Cikin hanzari ya gama shirye shiryensa kafin ya dauke Berifcase dinsa da sauran karikitan sa ya fice daga cikin dakin ya kulle can harabar gidan ya nufa in da motarsa take park-space tun kafin ya isa gareta ya danna mata Remove ta saki wani dan sauti tare da dallo wasu kalolin haske masu kayatarwa isa yayi ya bude ya shige yayi mata key kafin ya danna Remove dan madaidai cin Get din gidan ya buɗe kansa da kansa ya cilla motar zuwa waje cikin yanayi na kwarewa a tuki yana ficewa Get din ya koma ya rufe kansa.

Gida ne dan madaidai na zaman mutum daya kirar gidan da ka ganshi zaka gane gine akayi sa na burgewa kuma na zaman yan gayu.

A hankali yake tuki yana jin yarda zuciyarsa da kwanyarsa suke kokari rakito masa lamarin da ya faru dashi a barcin sa da ya tashi a wayewar garin yau sosai ya ji zuciyarsa na kai kawo idanuwansa na buɗewa suna wanzar masa da komai kamar yanzu komai ke faruwa runtse idanuwansa yayi yana mai daura hannunsa daya saman goshinsa a hankali yake furta.

“Yaa Allah what is wrong with me?”.

Numfashi ya ja ya fesar kafin ya ware idanuwansa jin da yayi ana ta danna masa Horn sosai ya zaro idanuwansa waje ganin in da yake yayi mamaki sosai bai yi zaton ma wai tuki yake yi ba ya dauka yayi Parking domin ji da yayi akan sa a wata duniyar cikin sauri ya taka burki yana mai ambaton sunayen Allah kafun ya hada kansa da sitiyarin yana mai da numfashi.

“Yaa Allah wai shin me ke faruwa dani ne haka?”.

Ya tambayi kansa tambayar da ya san ba wai yana da ansar ta ba ne komai yake ji a yau ya canza masa komai na duniya yana juya masa wani iri daban ba yarda ya sa ba ji ba zuciyarsa yake ji tana kai komo da wani lamari mai girman gaske wanda yake kokarin hana shi kwanciyar hankali da natsuwa.

1

STORY CONTINUES BELOW

Tafiya mai ‘yar tsayi yayi kafun ya isa Asibitin( Fortis Escorts Heart Institute) dake birnin Delhi a nan India da yake aiki a harabar yayi parking kamar yarda sauran yan uwansa likitoci sukayi ya jima kafin ya fito daga cikin motar don kuwa jin zuciyarsa yake tana kara narkewa da wannan lamarin da bai yi zaton lamarin har ya kai har haka ba ya jima yana binnewa a zuciyarsa ya jima yana dakon lamarin yana boye duk wata hanya da zata taso masa dashi ta hanashi kwanciyar hankali sosai yake danne zuciyarsa sosai yake hakurkurta da zuciyarsa akan lamarin da yake zaton ba zai taba kasancewa ba ko da kuwa ba azahiri bane ya raina lamarin rainuwa mai girman gaske amma a yanzu a wannan ranar a daidai wannan lokacin komai na shirin canza masa komai na shirin juye masa komai na shirin birkice masa ba tare da zato da tsammani ba.

A hankali yake takawa idanuwansa na bin sashi da sashi na cikin asibitin har ya isa babbar kofar da zata sa dashi da Reception din.

Kallo daya zakayi wa asibtin ka gane babba ne sosai domin akalla benensa zai kai hawa biyar zuwa shida cikin asibitin kuwa ko ina malale yake da tayal mai matukar daukar idanu da burgewa yanayin tsarin ma’aikatan dake zirga-zirga da kai komo kawai in ka kalla zaka gane ba karami asibiti bane lura da yanayin sa na kudi ne (Privet Hospital).

Haka Dr.Karami ya shiga taka kafafuwansa cikin asibitin ko wani bangare yabi sai ya daga masu hannu suma suna daga masa suna mai furta ‘Morning’ komai da yake cikin sauri yake yin sa saboda lura da yayi ya kusan makara sosai a haka har ya isa bangaren da Offices din sa yake da hanzari ya buɗe ya shiga yana mai yasar da Brifcase dinsa saman Table din tare da sauran hargitsen dake hannunsa danginsu waya da key.

Rufe idanuwansa yayi yana mai jan numfashi kafun ya isa kan kujerarsa yana mai cire Coat din saman suit dinsa yana mai rataye ta jikin kujerar zama yayi sosai yana mai jujjuyawa hannayensa saman kan sa jinsa yake yi a wani mataki na musamman wanda tunda lamarin yake faru dashi bai taba yi masa tsamari kamar na yau ba sosai yake jin zuciyarsa na ansawa  kwanyarsa na rikicewa da lamarin da ya dauka ba mai sauki bane gareshi sosai yaji a daidai wannan lokacin ya na bukata komawa gida sosai yake jin zuciyarsa ta shiga azalzalarsa da ya tashi ya tafi sosai kwanyarsa ke tunano masa kasar sa.

Numfashi ya ja mai zafi yana fesar wa kafin ya mike tsaye cikin wani irin yanayi mai matukar razana zuciya da ruhi Table din dake gabansa ya kai wa bugu wanda sai da kayan da suke kai sukayi rawa sosai a hankali ya shiga safa da marwa cikin Office lokaci

guda wani gumi yaji yana ke to masa wanda bai san ta ya ya hakan ya faru  ba hannunsa ya dungule waje guda yana mai sakin wani numfashi mai zafi.

Kofar da yaji an taɓa ne ta sanya shi saurin juyawa ya fuskance ta idanuwansa a lokacin sun fara canzawa suna lumshewa kamar me jin barci.

“Dr.Vijay”.

Ya fadi can kasar makoshinsa cikin halin damuwa.

Murmushi ya sakar masa yana mai karasowa inda yake tsaye hannu ya mika masa.

“Kayi latti yau zuwa na kusan uku ban samun ka abin ya bani mamaki ban san ka da haka ba ban san ka da latti a wajan aiki ba domin kai sam baka African Time kamar mu Why?”.

Ya fadi yana mai sauke idanuwansa sosai akan na Dr.Karami da yayi masa kuri kamar mai son fahimtar wani abu game dashi kafin ya kau da idanuwansa yana mai jan numfashi mai zafin gaske wanda yake ji har zuciyarsa tururinsa na kai masa yana haifar masa da wani irin yanayi a ƙasar ruhinsa.

Sosai Dr.Vijay ya lura da yanayin da yake ciki kamar akwai abin da ke damunsa bisa lakari da yayi da yarda idanuwansa da fuskarsa suka canza lokaci guda kamar ba nasa ba hannu ya kai ya dafa kafadarsa murya a tausashe.

STORY CONTINUES BELOW

“Dr.Karami something is wrong with you I think?”.

Ya fadi yana mai kuresa da kallo.

“I don No but Dr.Vijay…”.

Hannu ya daga masa kafun ya ja hannunsa su karasa wajan kujerun dake fuskartar juna guda biyu na tsakiyar Office din zaunar dashi yayi kafun shima ya zauna ya na mai dubansa sosai yanayin sa kawai yake karanta da yanayin Emotion din sa gami da Tension din sa da suka sauya sosai da sosai hannunsa ya kamo ya sarke a tsakanin nasa.

“Me ke damun ka Dr.Karami?”.

Ya tambayeshi gami da kuresa da idanu.

Girgiza kai ya shiga yi kafin lokaci daya ya mike yana kwace hannunsa.

“I Need To Go Home Right Now”.

Ya fadi yana mai dafe kansa da wani irin numfashi da yake fesar wa mai zafin gaske gabadaya ya rikice lokaci guda zuciyarsa yake ji ta azalzalsa ji yake yi kamar zata tarwatse jin komai yake yi na jikinsa kamar zai narke kawai gida yake so ya koma kasar sa yake bukatar ya gansa a ciki baya so ya kara ko da kwana daya ne ba ma kwana daya ba ko awa daya baya bukatar ace ya kara jin sa yake yi kamar in ya cigaba da zama zuciyarsa zata buga a ko wani lokaci zuciyarsa ta gaji matukar gajiyawa.

“What? Dr.Karami you need to go home? Akan wani dalili?!”.

Mikewa yayi kan kafafuwansa yana dubansa cikin wani irin yanayi na mamaki da tu’ajibi kafin ya shiga nuna sa da hannu.

“Anya kalau kake kuwa da alamun akwai abin dake dawainiya da kai in ba haka ba ana cikin tsakiyar aiki rana daya kace zaka tafi Najeriya wannan ba zai taba yuwuwa ba Dr.Karami ka canza tunan…”.

“Dr Vijay!”.

Dr.Karami ya fadi muryarsa da sauti sosai idanuwansa izuwa lokacin sun kaɗa matuka duban sa yake yi cikin wani irin yanayi kafun ya narkar da muryar.

“I Need Help Please ka taimaka min ina son naje gida a yau din nan ba zan iya cigaba da zama ba domin kuwa sosai da sosai nake ji a jikina kamar akwai abin da ke kokarin faruwa dani zuciya taba kaji…”.

Ya fadi yana mai kamo hannunsa yana kaiwa saitin kirjin nasa yana mai lumshe idanunsa.

Ware idanu Dr.Vijay yayi sosai jin yarda bugun zuciyarsa yake sauri a ko wani lokaci yana kara sauri kamar wanda yayi matsananci gudu.

“…ina so a yau din nan na bar Delhi Dr.Vijay ina so ka saman min jirgi da zai dauke ni ya fita dani daga wannan kasar cikin mintina”.

Yanayin da yake maganar a hargitse kamar wanda ya kamu da hauka ya sanya Dr.Vijay saurin rikesa yana mai bubbuga bayansa a hankali kafin ya fara magana cikin sanyin murya.

“Cool Down mana aboki na fada min meya same ka mai yasa kake so ka bar wajan aikin ka a irin wannan lokacin da ake matukar bukatar ka ya kamata ka zauna kayi tunanin kafin ka zartar da hukunc…”.

“Dr.Vijay Please mana”.

Ya fadi yana mai katse shi cikin yanayi na bukata sosai da gajiya da maganar da yake yi masa.

“Dr.Karami”.

Dr.Vijay ya fadi yana mai sakin sa yana mai duban idanuwansa.

STORY CONTINUES BELOW

“…Kasan dai yau ba zaka samu jirgin ba ko duk jiragen dake tashi ba wanda zai yi wajan kasarka ko don haka ya zama dole kayi hakuri zuwa gobe…”.

“Ba zan iya ba Dr.Vijay ba zan iya sake ko da awa ba ne akasar nan kawai ka taimaka min ko babu jirgin da zai  tashi yau to ni kaje kayi mani Boking na jirgin gabadaya zan iya daukarsa ko nawa ne kuwa zan biya”.

Ware idanu yayi sosai jin abin da Dr.Karami yake fadi kamar wanda bai da hankali.

“What? Dr.Karami jirgin ne zaka dauka zuwa kasarku…Ina hakan ba zai taba yuwuwa ba kasan kuwa ko zaka samu nawa zaka kashe…”.

“Wannan ba damuwa ta bace kawai kayi mani abin da nace maka in zakayi”.

“Gaskiya da matsala ba zan iya ba domin ko nace zan iya nayi maka karya”.

“Shikenan Nagode”.

Dr.Karami ya fadi rai bace yana mai zubewa kan kujera cikin tsananin bacin rai hannayensa duka saman kansa da yake ji yana barazanar tarwatsewa zuciyarsa yake ji tana yi masa zafi da raɗaɗi ji yake yi kamar ya farka kirjinsa ya zaro ta ya ajje ta waje.

Dr.Vijay da yayi fakare yana dubansa gabadaya yaji lokaci guda ya bashi tausayi duk da dai bai san abin da ya saka abokin nashi cikin wannan halin ba amma ya tabbata abin ba mai sauki bane sosai ya lura dashi ya fice daga hayyacin sa sosai.

A hankali ya fara takawa har iyasa gareshi kafadarsa ya dafa yana mai bubbuga masa baya a hankali.

“Kayi Hakuri don Allah duk da dai ban san abin da ke damunka ba amma na tabbata ba mai sauki bane amma kayi hakuri zuwa gobe please nayi maka alkawari jirgin farko da kai zai daga…”.

Hannu ya daga masa cikin wani irin yanayi.

“Please ka rabu dani kawai tun da ba zaka yi mani abin da na bukata ba ni ma ai ba nakasasshe bane zan iya da kai na”.

Da hanzari ya mike yana faman huci har lokaci hannunsa na kansa key din motarsa ya dauka yana kokarin fita Dr.Vijay yayi saurin rikesa sosai runtse idanu Dr.Karami yayi kafun ya buɗe su da wani irin yanayi na bacin rai a cikin su.

“Please sake mani hannu Dr.Vijay tun da nace kayi mani kace ba zaka yi ba ban ga dalilin da zai sanya ni kuma ka hanani yi ba wanda kuma bai zai taba yuwuwa bane”.

“Ban san ka da gardama ba, ban saba ganin ka cikin wannan halin ba, ban san ka da zafin zuciya har haka ba, Dr.Karami karka canza yanayin da nake kallon ka dashi na mutumin kirki mai hakuri da kai zuciya nesa karka canza kallon da nake maka a matsayin mai TAWAKKALI akan duk abin da ya same ka kaifa musulmi ne ya kamata ace  kana rungumar ko wani irin yanayi ka samu kan ka aciki ya kamata ace kana danne zuciyarka akan duk abin da zata bijiro maka dashi wannan tashin hankalin da ka saka kan ka a ciki bana tunanin shine maganin abin da yake damun ka ya kamata ka sassauta ka mai da komai ba komai ba sannan kayi tunanin abin da ya dace duk abin da hakuri bai bayar ba bana tunanin rashin sa zai bayar”.

Juya yayi ya dube shi yana mai sakin ajiyar zuciya kafin ya ja jiki ya isa kan kujera ya zauna yana mai runtse idanuwansa gabadaya hakan da Dr.Vijaya ya gani ya tabbatar masa Dr.Karami ya fara saukowa don haka ya isa gareshi yana bashi baki da tausasa zuciya a hankali zuciayarsa ta fara rage zukin da take yi masa da rikicin da kwanyarsa take masa don ya tabbatar maganar Dr.Vijay gaskiya ne shi a karan kansa ya sani duk haukar da yake yi nacewa zai bar Delhi a yau ya san hakan ba yuwuwa zai yi ba domin kuwa ya san ba jirgin a yau sai dai zuwa gobe din.

STORY CONTINUES BELOW

Sun jima Dr.Vijay na bashi baki kafin ya hakura zuwa goben amma yarda yake jin zuciyar tashi kamar ba zata iya barinsa ya kai goben ba duk da hakurin da ya jona mata.

A ranar dai haka ya wuni ba tare da tabuka komai ba illa kai kawo da yake tayi a cikin Office din har zuwa lokacin tashin sa yayi a lokacin ma sai da Dr.Vijay ya sake dawowa ya din ga bashi baki har gida ya rakashe ya tabbatar da ya hakuri din sannan ya barshi sukayi sallama.

Ko da dare yayi kasa barci yayi domin gani yake yi kamar in ya kwanta din zai makara ko da dai Dr.Vijay yace zai yi masa komai kafin gobe din har da su Viza duk zai samar masa amma duk da hakan hankalin sa bai kwanta ba haka ya dinga safa da marwa da ya kwanta sai ya tashi yashiga zarya a daki daga daki zuwa falo lokaci-lokaci yana duban Agogo sam! ya kasa

tsayawa waje daya kamar wanda yake fama da basir zaman ma ya gagareshi a tsaye ya dinga gangaɗi da yaji yana kokarin fin karfin sa sai yayi Toilet ya wanko fuskarsa ya dawo haka ya dinga yi har zuwa lokacin da barci barawo gwanin iya sata yayi awan gaba dashi bayan ya zauna a kan hannun kujera bai san lokacin da ya tuntsure a cikinta ba.

Misalin karfe hudu ya farka a firgice kamar wanda aka shekawa ruwa da sauri ya dubi Agogon falon ganin karfe hudu da yan mintina ya sanya shi ware idanu ya na mikewa cikin hanzari yayi hanyar Toilet da gudu kamar wanda gudawa take kokarin kufce masa bai dau tsawon wani lokaci ba ya fito ya shirya cikin kananun kaya da sukayi matukar amsarsa ya gyara sumar kansa da sajen fuskarsa, fuskarsa tasa tayi fayau sai idanuwansa da suka dan kumbura na rashin isasshen barci da bai yi ba karamar jaka ya dauka ya zuba abin da yake bukata na tarkacen sa kaya ko kala daya bai dauka ba bayan na jikin sa.

Wayarsa ya dauka ya danna wa Dr.Vijay kira a daidai lokaci agogo ya buga karfe biyar minti kamar uku aka dauka kafin ya dau wayar don har ya fara rawar jiki jin an ansa shi ya sanshi saurin yin magana baki na rawa.

“Morning Dr.Vijay ni fa na gama shirina ga ni nan zuwa…”.

Zabura Dr.Vijay yayi daga kwancen da yake idanuwa a warwaje.

“Ka shirya kace? kai kam kalau kake karfe nawa yanzu ka sani? don Allah Malam ka koma ka kwanta don nasan da alamun ko barci bakayi ba jirgin fa ma sai biyun rana zai tashi”.

Wata ashariya Dr.Karami ya dauko ya sauke.

Sai da Dr.Vijay ya tsorata duk da dai bai san abin da yace ba amma ya tabbatar abun ba mai kyau bane.

Cikin bacin rai Dr.Karami ya dora da cewa.

“Ban son wulakanci kaji ko ta ya ya zaka ka ma min jirgin rana nida nake so na tashi da safiyar nan ban so rana ta fito ta tadda ni a kasar nan”.

Dariya sosai Dr.Vijay yayi kafin yace.

“Wai anya ba Amarya aka ce an baka ba kake wannan rawar jikin ni abin naka ne naga ba sauki…”.

“Ka ga don Allah Malam karka bata min rai kuma ka taso kawai ka zo ka dauke ni ko kuma na fito yanzu ka ganni a gidan ka”.

“Allah ya baka hakuri bani 30Mins yanzu zaka ganni”.

Sauke wayar yayi yana faman tsuki jakarsa ya dauka ya fito falo duk ya kashe kayan wuta da suke jone kafin ya fito ya kulle kofar fallon sannan ya yi wa motarsa securty-Key ya samu waje ya zauna a harabar gidan yarda kasan wanda aka koro sosai ya ƙagu duk bayan mintina biyu sai ya dannawa Dr.Vijay kira tun yana dauka har ya daina hakan ya kara tunzura Dr.Karami daga karshe ma da yakira Dr.Vijay sai yaji wayar akashe hakan yayi matukar kular dashi da hanzari ya mike yana kokarin buɗe motarsa yaji Horn wata irin ajiyar zuciya ya saki kafin ya figi jakarsa yayi waje cikin hanzari Dr.Vijay ya hango yayi parking yana kokarin fitowa daga cikin motar sai da galla masa harara kafin ya jingina da motar ya harɗe hannayensa a kirji yana faman dubansa fuskarsa a tsuke a haka Dr.Karami ya kulle gidan ya  karaso wajansa.

STORY CONTINUES BELOW

“Wai ma na tambayeka duk wannan ɓarin jikin da kake yi ka nemi izini daga wajan aiki ne jiya”.

Wani irin duba yayi masa kafin ya isa ya buɗe motar ya cillar jakarsa ciki ya juyo ya dube shi.

“Ban yi ba kai  yau sai kayi mani ko?”.

Ya fadi yana faman murmushin yake.

“Ai wallahi baka isa ba in ka ga na rakaka Airport to wallahi muje ka nemi izini ne”.

“Yaa Allah wai shin me yasa kake son takura mani ne har haka mai yasa kake son bata min rai ne?”.

“Ni ban bata maka rai nayi ba gaskiya ce na fada maka”.

“Ni gaskiya at this Time ba zan iya zuwa ba sai dai ka taimaka in kaje  ka nema min”.

Gyaɗa kai yayi kafun ya juya ya shige cikin motarta kafun shima Dr.Karami ya shige yana faman lallashin Dr.Vijay akan ya taimaka in yaje Asibiti ya

neman masa izini gami da tafiyar da zai yi shi dai Dr.Vijay bai ce masa komai ba haka ya figi motar suka dauki hanya domin zuwa Airport.

Cikin mintina da ba su haura ashirin ba suka isa Airport jirgin karfe bakwai Dr.Karami zai hau domin keta hazo zuwa kasar sa Najeriya.

Dr.Vija sai iya shege yake masa wai bai yarda dashi ba anya rawar jikin da yake yi ba amarya aka bashi ba ya matsu yaje ya kanta.

Shi dai yaƙe kawai yake yi masa domin dai a daidai wannan lokaci. ya matsu ya ga jirkin su ya tashi ya sauka a kasarsa.

Bakwai da minti biyar jirginsu Dr.Karami ya daga zuwa najeriya.

********

Ya mutsa fuska tayi tana mikewa kan kafafuwanta duk ta hada gumi a goshi hannunta face-face da kwabin fulawar Cake duban Umma tayi kamar za tayi kuka domin kuwa gabadaya take jin jikinta yayi sanyi da nauyi kamar wacce aka doddokewa kafadu lokaci-lokaci tana jin gabanta na faduwa wanda ta rasa dalilin haka tun da garin Allah ya waye a yau take jin ta a haka kwabin Cake din sai dakyar take yin sa jin Umma tace bazata yi mata ba ta gaji da son jikin da take yi sai kace mai laulayi.

“Don Allah Umma ki karasa min wallahi ba dadi nake ji ba a jikina”.

Wani kallo ta watsa mata kafun ta dubi kwabin Cake din.

“Ai ke zan ga ranar da zaki daina son jikin nan naki wallahi kina mace amma ke gabadaya kamar wata mage ai ko mage ba zata nuna miki son jiki ba yarda ki kasan ruwa haka kike kuma ki karasa kwabin ki don ba yi maki zan yi ba ga dai yamma dai nan ta sako kai in kika bari har aka kira magrib wallahi ba zan tayaki aikin daren nan naki ba barci na zanyi”.

Marere ce fuska tayi kamar zata fashe da kuka.

“Haba don Allah Umma daure ki karasa min…”.

“Yaa Allah wai Mariya na tambayeki haka in kika yi aure zaki je kina wa mijin ki wannan SANGARTAR aiko tun wuri ki sauya don ba a san mace da nawa ba duk mace mai nawa sai kin same da kazanta da rashin sanin yarda zata kula da gidan auren ta”.

“Naji Umma don Allah tausaya min Allah bana jin dadin jikina ne gabadaya yau din nan…”.

“Sannu. ba rashin jin dadi ba kece General Hospital karewarta”.

Umma ta fadi tana kokarin mikewa a daidai lokacin Mu’azzam yashigo da gudu ba in da ya dosa sai wajan kwabin Cake din ganin haka da Mariya ta yi ya sanyata saurin hanzarin cafko shi tana matse masa kunne.

“Sannu Biri sarkin barna wai kai don Allah Mu’azzam baka gani dai ka kyale sai ka bata ko to wallahi zan dinga dukan ka bar ganin Umma na goyan maka baya”.

Turo baki yayi gaba kamar zai fashe da kuka Umma da ke tsaye ta shiga yi musu dariya.

“Yo cewa fa kikayi kin gaji ba sai ki barshi ya karasa miki ba ai sha yanzu magani yanzu ne Auta ba shi da jinkiri in dai wajan aiki ne yanzun nan zai yi sa yaro ba kiwa kenan”.

Ware idanu Mariya tayi gami da tura baki gaba kamar zata rushe da kuka ta dubi Mu’azzam da yake kici-kicin kwace kansa ta tallake masa keya.

“Kai Umma wannan yaron naki ke kike goya masa baya kullum in zan yi kwabi  sai ya nemi bata min bayan kuma in nayi duk shi yake cinye ‘yar ribar”.

“Kan ki ake ji miko min kwabin na karasa miki don na lura in na biye miki wannan kwabin sai ya dauko lalacewa”.

Ai sai ta saki dariya da hanzari ta saki Mu’azzam ta dauki kwabin ta mikawa Umma da sauri ta shiga wake hannayenta cikin kwanon dake girke da ruwa a ciki.

Doguwar rikace a jikinta sai kallabi da ta daura kan ta dashi fuskarta fayau ba alamun kwalliya amma hakan bai hana sirrin kyanta fitowa sosai da sosai doguwar rigar ta anshe ta ta dan kamata kadan daga kugunta wanda yake cike sosai daga cikinta kuwa a matse yake kamar wacce bata cin abinci kirjinta ya cika sosai har yana kokarin rinjayarta saboda rashin ƙiɓarta doguwa ce amma ba can sosai ba jikinta kiran coca-cola ne.

A hankali ta warware dan kwalin kanta bayan ta matse daga kusa da Umma tufkanken gashin kanta ya baje sosai wanda yake ta faman sheki da daukar idanu a hankali ta shiga

tattare shi a daidai lokacin wani kamshi mai dadin shaka ta ji ya doki hancinta da sauri ta ware idanu gami da kara buɗe hancin nata don sosai kamshin ya tafi da imaninta a daidai lokacin kuma wata murya wacce ta kusan narkar da Mariya kasa tayi Sallama wanda ya sanya gaban

Mariya dokawa cikin wani irin yanayi mai razanarwa sumar tsaye tayi a daidai lokacin da ta daga fararen idanuwanta manya ta sauke su akan saitin mutumin dake tsaye cak! A kofar fuskarsa da wani irin yanayi idanuwansa dauke da wani kallon da ya sanya numfashinta kusan daukewa….Numfashin ta take ji yana fizga kamar zai bar jikinta wani irin juwa da jiri taji tana kwasarta kamar zata watsar da ita kasa idanuwanta sun ya cak! waje ko juyawa ba sayi sosai take dubansa da kallo na mamaki da wani irin yanayi zuciyarta take ji tana

bugawa da duk wani jan numfashin ta kamshin take ji yana dokar mata hancinta wani irin yanayi wanda ya haifarwa jikinta da wani irin

kasalallan yanayi jikinta take ji yana narkewa kamar ruwa kafafuwanta sai ƙarƙarwa suke yi suna kokarin zubda ita kasa.

Juyar da take ji tana wani irin juyawa da ita kamar wacce take samar gajimare runtse idanuwanta tayi a daidai lokacin da ta hango wasu abubuwa sun fito daga idanuwansa sun dire ana kamar saukar KIBIYAR AJALI lokaci guda zuciyata ta buga da wani irin yanayi mai girman gaske.

Sosai taji zuciyarta na buɗe a wani killataccen waje wanda ya jima1

kargame da katon kwado makullin sa ita kanta ba ta san inda ta jefashi ba sosai ta ji zuciyarta ta sauya bugu da wani al’amari mai girman gaske.

Ganin komai take yi tamkar a mafarki ba a zahiri ba ganin komai ta ke yi kamar ba a duniyar zahiri yake

faruwa ba magudanan jinin jikinta take ji sun sauya a wani mataki wanda ita kanta ba zata ce gashi ba kwanyarta ta shiga kai kawo da wasu lamari masu yawan gaske wanda ta jima da binne su a zuciyarta.

A hankali take buɗe idanuwanta hancinta na sake dauko mata daddar kamshin sa wanda yayi matukar tasiri wajan juyar mata da duk wani kamshi da ta taba ji a filin duniyar nan.

Da sauri ta shiga warware dan-kwalin da ke kanta jikinta sai kyarma yake yi idanuwanta akansa har yanzu zuciyarta ba ta gama yarda da cewa shi ne ba sosai take ganin komai tamkar a mafarki dan yatsanta guda ta daga tana mai nuna shi bakinta na wani irin ɓari kamar wacce ruwan sama yayi wa dan banzan duka take rawar sanyi.

Shikam! mutuwar tsaye yayi zuciyarsa na bugawa da wani irin yanayi sosai yake yajin sa a sama duniyar na kai kawo dashi komai yake ji na kwanyarsa na wargajewa zuciyarsa na buɗe wani makeken fili tana dasa wata bishiya mai girman gaske wacce tayi rassa a lokaci guda duk ta mamaye kafatanin filin zuciyarsa.

Murmushi yake saki wanda shi akaran kasa bai san yanayi ba idanuwansa na juyawa da wani lamari mai girman gaske sosai idanuwansa suke bin Mariya da kallo kafun ya kau da kai cikin yanayin na bugun zuciyarsa da yake ji kamar zata tarwatse.

A hankali yashiga kokarin saita kansa yana jan numfashi mai taurin gaske kirjinsa yake ji yana nauyi sosai da wani abu mai girma gaske a hankali ya runtse idanuwansa.

“Yah Dr.Karami”.

Mariya ta furta da wani irin sauti a muryarta wacce bata sam ma tana dashi ba bata san ta yi amfani dashi ba sosai take kallonsa sosai take jin jikinta na ansa wasu sakonni masu narkar mata da zuciya su hargitsa mata tunani.

Murmushi yayi kafun wani abu da ya tsaya masa azuciya ya wuce bayan ya haɗeshi dakyar.

Sautin muryarta da yaji yana ansa kuwwa a kunnuwansa hakan ba karamin narkar masa da jiki yayi ba gabadaya ji yayi sautin yana bin jikinsa yana ansa kuwwa a kwanyarsa da wani irin yanayi mai girman gaske.

“Mariya”.

Ya fadi zuciyarsa na wani irin zillo kamar zata faso kirji ta yo waje.

“Yaa Allah Mariya wai da gaske kece?”.

Ya sake fadi da wani murmushi mai kama da son fashewa da kuka idanuwansa naa kara narkewa da wani irin ruwa kamar na Rose tsakiyar kwayar idanunsa wani haske mai kama da na kibiya yake fitowa da sauri-sauri yana isa ga Mariya da ta gama narkewa cikin wani hali

STORY CONTINUES BELOW

zuciyarta na wanzar da wani farinciki mara musaltuwa ji take yi kamar ta daka tsalle ta isa wajansa ta rungumeshu duniyar take ji tana sauyawa da duk wani hali da take ciki duniyar take ji tana kamfato mata wani farinciki tana ajje mata runtse idanu tayi jin abin da yace da sauri ta juya wajan da su Umma suke wayam! ta ga wajan ba kowa wata ajiyar

zuciya tayi kafin taja kafa cikin sauri ko wani sashi na jikinta sai kaɗawa yake yi musamman kugunta da kirjinta. kafafuwanta kawai zaka kalla ka gane a harɗe suke tafiyar take yi amma ji take yi kamar zata kifa.

Fakare yayi da baki fuskarsa da wani kayataccen murmushi mai girman gaske idanuwansa kawai yake yawatawa akanta mamaki ne da tu’ajibi suka cika shi har yanzu zuciyarsa bata gasgata masa wai

Mariya bace gani yake yi kamar wata halittace daban a tsaye a gabansa take yi masa magana gani yake yi kamar wata daban ce take tafiya a yanzu ba Mariya da yasani shekaru hudu baya ba komai ya sauya komai nata ya canza muryarta kirar jiki ta yanayin tafiyarta…

“Yaa Allah”.

Ya furta yana kai hannayensa yana muttsuka idanuwansa da yake zaton karya suke yi masa gizo suke yi masa da wata mace ba Mariya ba zuciyarta na kara gasgatawa amma shi yaki AMANNA dan yatsarsa daya ya saka cikin baki yana cizawa da karfi jin zafin ya sanya shi sakin kara mai dan sauti.

“Ouchhh!!”.

Ya furta yana yarfar dan yatsar nashi.

Ko da Mariya ta shiga dakin Umma na zaune tana karasa kwabin Cake din bango ta jingina dashi tana mai da numfashi da sauri-sauri idanuwanta a lumshe  fuskarsa nayi mata yawo a idanuwanta murmushisa

idanuwansa  kai gabadaya ma fuskarsa take ganin tana kai kawo a cikin runtsantsun idanuwanta zuciyarta na wata irin harbawa da wani irin yanayi mai girman gaske numfashi ta ja kafun ta buɗe idanuwanta a saitin Umma da tayi mata fakare tana kallon Ikon Allah wai akace in kana da sauran numfashi kana DA SAURAN KALLO a filin duniyar nan mamaki ne ya cikata lokaci guda da taga canzawar Mariya yanayi da take kallon fuskarta da yanayin da jikin nata ya nuna wanda a tsayon lokaci mai yawa bata ga haka ba ta mance rabon da ta ga Mariya a haka bazama ta iya tunawa ba.

“Ke wai lafiyarki kuwa?”.

Umma ta fadi tana mai tsuke fuska cike da mamakin Mariya tun lokacin da ta lura da shigowar Dr.Karami da yanayin da ta ga Mariya a ciki shiyasa ta zare jiki ta yo cikin dakin don ta lura tsaf! Mariya zata yi abin da zai tasa ta ji kunya a gabansa bata iya ƙewar mutum ba sam!

A duk lokacin da ta ga wani wanda suka jima ba su hadu ba ta dinga ɓarin jiki kenan amma na yau ya bambanta da sauran lokuta.

Wani murmushi mai kwari ne ya kufcewa Mariya kafun ta kai hannayenta tana toshe bakinta har zuwa lokacin jikinta bai daina ɓari ba.

“Yah Dr.Karami ne fa”.

Uwar harara ta watsa mata kafin ta ja tsaki.

“Eh na san shine ai shiyasa na ga sai ɓarin jiki kike kamar wata sakarya ke a tunanin ki hakan da kikayi burgewa ce kina ‘ya mace ki barin jiki ai sai ya dauke ki ba ki da natsuwa duk na ga abin da ya faru wanda sam bai dace ace ke a karan kan ki kike  haka ba”.

Zaro idanu waje tayi jin abin da Umma ta fadi da sauri ta sauya fuska alamun damuwa zame jiki tayi ta zauna kasa don jin kafafuwanta take yi kamar ba za su dauke ba.

“Au! zama kikayi ki bar shi a tsaye a tsakar gidan so kike yi ya lura da wautarki”.

Runtse idanu tayi zuciyarta na wata irin harɓawa da sauri ta mike tana kokarin ficewa amma ta kasa sai kai kawo take yi tana susar kai Umma na lura da yanayin ta da sauri ta mike ta shiga kintsa dakin duk da ba wata gyara yake bukata ba komai tsaf yake hijab dinta ta dauko ta saka kafin ta dubi Mu’azzam da yake ta kasumar Cake sannan ta dubi Mariya.

STORY CONTINUES BELOW

“Ki dai kintsa ko”.

Ta fadi fuskarta a daure kasa Mariya tayi da kai kafun ta gyara daurin dan kwallinta ta dauko hijab ta saka ita ma gabanta har lokacin bai daina bugawa ba fargaba kawai take yi ji takeyi kamar in ta fita ba zata ganshi ba gani take yi kamar a mafarki ne.

Numfashi ta ja kafun ta runtse idanu ta buɗe addu’a tayi domin samun sauki a zuciyarta.

A hankali taka ta fice daga cikin dakin kanta a kasa har yanzu yana nan tsaye harɗe da hannayesa a kirji dago kanta tayi ta dubesa idanuwansu suka sarƙewa waje daya lokaci guda zuciyoyinsu suka buga a tare da sauri tayi kasa da kai ganin wani murmushi da ya saki da ya kusan tafiya da imaninta.

“Sannu da zuwa Umma tace ka shigo daga ciki”.

Ta fadi a wahale kafun ta juya tana kokarin komawa dakin.

“Bana son gaisuwar ai ni ba wajanki na zo ba”.

Dr.Karami ya fadi da rashin wasa a muryarsa cak! ta tsaya da tafiyar da takeyi zuciyarta tayi mata wani wawan bugu ta runtse idanu kafun ta juyo cikin tsuke fuska da gayyato juriya ta ajjewa kanta zuciyarta na tuno mata da abin da ya faru na halin ko in kula da ya nuna a kanta tsayin shekaru sosai zuciyarta ta fara dauko laifinsa duk da dai bai taka kara ya karaya ba.

“Nima ai ba don halin ka na yi ba”.

Ta fadi tana mai hanzarin barin wajan ta fada cikin dakin.

Murmushi yake saki yana mai nuna ta da hannu mamaki kamar ya kashe shi wai Mariya ce take magana haka ita ce tayi baki haka Mariyar da ya sani acan baya mai shiru-shiru magana ma wuya take yi mata wai ita ce da mai da masa da magana da yanayin fushi take yi dashi sai da ya gama shan sharafin mamakinsa sannan ya taka zuwa dakin a daidai lokacin ita kuma Mariya ta fito hannunta dauke da Jug na roba saura kadan suyi gware da sauri ta kauce ko kallonsa ba tayi ba fuskarta ba yabo ba fallasa yana kokarin mataa magana tayi masa wani kallo da ya sanyashi sauri sakin murmushi yana mai shigea dakin bakin sa dauke da sallama.

Bayansa tabi da kallo kafin ta ajje Jug din tayi hanyar waje kankara ta sayo ta zo ta hada masa lemo mai kayan kamshi da yake Umma na ajje kayan kamshi da kayan jinja saboda irin wannan yanayi na bako idon kunya sosai ta hada lemon sai kamshi yake yi sannan ta farfasa kankara ta saka a ciki sai da ta bashi kamar minti daya sannan ta dauka domin kai masa fuskarta a gimtse sai ka rantse bata taba yin dariya ba murya can kasar makoshi tayi sallama ta shiga

idanuwansa kuwa na saitin kofar tana shiga da idanuwansa ta fara cin karo da sauri ta dauke kanta ta isa garesa ta ajje a gabansa ta mike wani plat ta dauko ta zubo masa Cake ta zo ta ajje masa duk kanta na kasa ta ki kallonsa amma shi duk motsinta na idonsa hanyar waje tayi tana kokarin fita.

“Mariya!”.

Umma ta kira da wani sauti na tuhuma da sauri ta juyo ta dubeta  alamu tayi mata da ido aiko sai ta kara tsuke fuska tana turo baki gaba ta gefen ido ta kalli Dr.Karami ya dauki Jug din lemon yana sha amma idanuwansa na kanta da sauri ta fice daga cikin dakin.

******

Duban Baseera tayi a dan hargitse idanuwanta ta bude su sosai kafun ta watsa mata wani kallo.

“Ke fa tsiyata dake wauta yasin daga fada miki magana kina kokarin canza mani manufa ta daban…”.

Wayar dake hannun Baseera ta daura Ringing da sauri ta duba lokaci guda ta balle da dariya tana duban Mariya da tayi fakare da idanuwanta kallo daya zakayi mata ka gane ba cikin hayyacin take ba.

STORY CONTINUES BELOW

“Ke My Besty Mutumin ne fa yasin…”.

Duka ta kai mata kafun ta mike tana kokarin ficewa a daidai lokacin ita kuma Baseera ta daga tana ansawa ganin Baseera na kokarin fita tayi sauri dauke wayar daga kunnanta.

“Billahillazi yana kofar gida ya biyo ki”.

a firgice Mariya ta juya tana dubanta Baseera dake faman kwasar dariya idanuwanta a warwaje lokaci guda suka kaɗa kamar za tayi kuka.

“Yo ni mai ya dame shi dashi ai ba waje na ya zo ba…”.

Da sauri Baseera ta mike tana katse wayar da dariya a bakinta.

“Yasin Karya kike daga gidan Umma yake yana nemanki Umma ta fada masa kika na nan yarinya kin gudu baki tsira bane bari ki ga”.

Baseera ta mike tana zarar mayafinta tana kokarin fita waje ganin haka ya sanya Mariya saurin riketa.

“Ke fa ba hankali kika cika b ina kuma zaki kin san Allah ko kin je kin ce ina gidan ba zan fita ba domin kuwa ba abin da zan masa”.

Tagumi Baseera tayi da hannu daya kafun ta saki wata dariya.

“Uhmm wai ma ni wallahi dariya kike bani mutumin nan yau satin sa kusan biyu yana zarya akan ki yana baki hakuri akan abin da yayi miki amma ke kamar wata dutse gabadaya kin kasa bashi lokacinki Mariya karki mance fa waye Dr.Karami karki mance lokacin da kika saka ni gaba akan baya kula ki ya manta dake amma yanzu dama ta samu kina kokarin sakinta”.

Haushi ne ya turnuke Mariya tayi sauri ta fizge jikinta daga Baseera ta koma bakin gado ta zauna ta na mai zabga tagumi fuskar nan a haɗe

kamar hadari da sauri Baseera ta iso gareta tana mai dafa mata kafada.

“Yi hakuri mutuniyar tashi don Allah muje bai da ace mutum kamar Dr.Karami kina yi masa haka ba…”.

“Don Allah ki rabu dani Baseera karki saka raina ya bace kisan Allah ba zan fita ba ai in na fita kamar bani da zuciya ne”.

Zaro idanu tayi waje kafun ta shiga dubanta sosai ganimn take yi kamar ba Mariya ba komai take ganin ya canza game da ita fushin da ba nata ba take ganin Mariya ta aro ta

daurawa kanta akan mutumin da sam bai dace ace tayi wa haka abin yayi matukar daure mata kai don haka sai ta koma gefe tana mai latsa wayarta ta ba banza ajiyar Mariya.

******

Da sauri ta sauka a Napep din ta nufi hanyar shiga gida ko gabanta bata kallo idanuwanta gabadaya a rufe suke ba zato ba tsammani taji tayi karo da mutum da sauri ta dago kanta ta na fiddo su waje cikin yanayi na tsoro da firgita tsuke fuska tayi ganin wanda yake gabanta da sauri ta kau ce tana kokarin wucewa cikin gida caraf! taji ya rike mata hannu ai ji tayi kamar ta kurma ihu wani kallo ta watsa masa kafun ta fizge hannun nata rai bace ta shiga nuna sa da yatsa.

“Huzaif kana da hankali kuwa kasan abin da kake aikatawa hannu na fa kari ke…”.

Wani kallo da yayi mata yana kokarin sake riketa da sauri ta ja baya kafun ta daga hannu ta zabga masa mari cikin tsananin takaici da bakin ciki.

“An gaya maka ni irin watsantsun matan da kasani ne an gayamaka RA’AYINMU DAYA da su ne ko an gaya maka halayarmu daya da su ne tun wuri ka dawo hayyacin ka in kuma ba haka ba na rantse da Allah zan yi maka abin da baka taba zato ba”.

STORY CONTINUES BELOW

Murmushi ya saki yana yawatawa da idanuwansa a jikinta kafun ya shiga kokarin kaiwa gareta a hankali ta shiga ja daya baya idanuwanta a warwaje cikin tsananin tsoro da firgita yanayin da ta ga Huzaif a ciki ya tabbata mata ba ya cikin

hankalinsa da sauri ta juya tana kokarin kwasa da guda sautin karar marin da taji ya karaɗe kunnuwanta ne ya sanyata tsayawa cak! kafin ta juya a firgice.

“Dr.Karami!”.

Ta fadi a firgice jikinta har rawa yake yi wani irin huci yake yi kamar kumurci yana faman cika fuskarsa  ta rine tayi jajir idanuwansa sun kaɗa sosai  hannusa akan Huzaif da ya dafe kuncin sa domin kuwa sosai yaji shigar marin da Dr.Karami yayi masa kallon kallo suka shiga yi wa juna a tsakanin su sosai suka so tuna in da suka san junansu.

Dr.Karami ya ja numfashi mai zafi kafun ya dubi Mariya da tayi matukar shiga firgice kamar wacce zata saki fitsari ba abin da jikinta yake yi sai rawa sosai ta tsorata da yanayin da taga Dr.Karami a ciki musamman irin kallon da taga yana watsa mata kau da kai tayi tana kokarin barin wajan wata irin razananniyar tsawa ya doka mata lokaci guda ta tsaya da tserewar da take kokarin yi a hankali ya shiga takowa inda yake gabanta na dokawa da tashin hankali mai girman gaske nuna ta yayi da yatsa bakin sa sai motsi yake yi yana son yin magana amma ya kasa ya dunkule hannu ya naushi iska yana mai cizon laɓɓansa kafin ya juya ya kalli Huzaif da har lokacin yake tsaye dafe da kuncin sa karasawa yayi gareshi yana kallonsa ido cikin idon kafin ya ja huci mai zafi.

“In har kasa sake gangancin ka ya sake dibarka har kayi kokarin taba ko da gyalan jikinta ne na rantse maka da Allah sai na daureka har igiya tayi rara don na lura kuruciya na damun kwanyarka zan saita maka ita”.

A hansale Huzaif ya dube shi.

“kan wannan kucakar yarinya ka mare ni kan wannan mai kama da birin ka mare…”.

Ji kake kau! Dr.Karami ya sake dauke shi da mari wanda yafi na dazu ya cakumi wuyar rigarsa.

“wai kan dan gidan uban wanene fada min uban waye uban ka a garin nan na rantse da Allah in bakayi wasa ba kafatanin zuri’arku sai sun ji a jikinsu”.

Yana gama fadin haka ya watsar dashi gefe kafun ya dubi in da Mariya take cikin tsananin firgice da razana bata yi zaton zafin Dr.Karami ya kai har haka ba sosai taji tsoronsa ya sami ma sauki a zuciyarta kasa tayi da kai ganin wani kallo da ya watsa mata mai cike da tuhuma zuciyarta taji tayi wani irin dokawa da hanzari ya isa can gefen hanya in da yayi parking lokacin da ya ga abin da ke faruwa tsakanin Mariya da Huzaif a hanzarce ya isa yayi mata ki ya fizge ta cikin tsananin bacin rai huci kawai yake yi zuciyarsa na wani irin zafi da raɗaɗi ji yake kamar ya hada Huzaif din da Mariya yayi musa dan banzan duka.

Sai da taga bacewarsa sannan ta juya ta dubi Huzaifa tana mai galla masa harara tayi hanyar shiga cikin gida a soro ta ci karo da Hafsat tana kokarin fitowa taci uban kwalliya da dinkin atamfa wanda yayi matukar kama mata jiki ainun in ka ganta sai ka rantse wata rikakkiyar wayayyice nan kuwa kanta empty ne a hankali take taku Mariya na binta da kallon

mamaki da tu’aji bi da yarda Hafsat ta bari duniya ta buɗe mata ido haka ko da yake bata ga laifin ta ba Goggo Marka ce ta daure mata kugun yin abin da take so tun da suka hadu da Huzaif shikenan ta daina zaman gida kullum yana hanyar daukar ta suna ficewa ita dai nata ido domin bazata taba mance cin amanar da Huzaif da ita kanta Hafsat din sukayi mata ba kallon su kawai take yi girgiza kai tayi tana mai shigewa cikin gida zuciyarta a jagule komai take jin ya kwance mata duniyar gabadaya tayi mata zafi ji take yi kamar ba ita ba.

“Kan Uban can!”.

Hafsat ta fadi lokacin da taga Huzaif na faman huci hannunsa dafe da kuncin sa idanuwansa sun kaɗa sun yi jajir kamar wanda kayi wa sura ce da barkono.

“Me ya same ka haka?”.

Ta fadi tana mai duban sa, tsaki ya ja kafun ya shiga safa da marwa a wajan sai fama huci yake yi.

“wani dan iska ne wai don kawai waccan yarinyar ta gidan ku za ta gaya min ba dadi shine ya zo ya daura min tafi a fuska”.

Zaro ido tayi waje kafun ta dubi kofar gidan su.

“Mariya ko?”.

“to akwai wata yarinya ce a gidan ku bayan ita”.

Ya fadi a hassale kamar zai kifeta da mari ita ma tsaki ta ja tana mai galla masa harara.

“Huzaif na lura so kake yi ka raina min hankali in ba don haka ba ina ruwanka da ita ai ko me akayi maka kai ka ja yasin”.

Wani wawan cafka ya kai wa hannunta ya murɗe ta saki kara mai sautin.

“Ni zaki raina wa hankali Hafsat kin san Allah in bakiyi wasa ba sai na sauke akan ki”.

“Sauke mana in ka isa ai bani na saka ka kula ta ba Malam balle ka sauke fushin ka akai na”.

Dunkule hannu yayi kamar zai kai mata naushi amma sai ya bugi iska gami da jan tsaki ya isa in da yayi parking ya buɗe mota ya shiga ransa a bace zuciyarsa sai faman tururi take da takaici

Hafsat dake tsaye ganin yarda ya shiga motar rai bace ba tare da yayi mata magana ba haushi ya cika ta ja tsaki kafin ta isa gareshi kallonsa kawai tayi ta watsar kafun ta buɗe motar ta shiga  ko kula ta bai yi ba ya yiwa motar Key ya fizge ta ya bar layin yana mai fadin.

“Billahillazi sai na baiwa Mariya mamaki ba dai ni ta saka akayi wa cin mutuncin ba zan nuna mata na fita iya shege”.

Hafsat da ta kula tsaki taja a ranta tana fadin ‘Allah ya kara ai ni nafin son haka dama kiyayya mai karfi ta ratsa tsakaninku’.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *