UKU BALA’I CHAPTER 8
Www.bankinhausanovels.com.ng
Juyi kawai yake yi saman faffaɗar gadonsa da ya kusan cinye rabin dakin numfashi yake ja a hankali zuciyarsa na wani irin kartawa.
A hankali ya mike yana kai kawo a tsakiyar dakin gumi mai tsananin zafi sai tsantsafo masa yake yi a goshi lokaci-lokaci yake runtse idanuwansa ba abin da yake hangowa sai Huzaif da ya rike hannun Mariya sosai yaji zuciyarsa na zafi da zugi wani katon abu mai nauyi yaji ya zo masa zuciya ya tsaya cak!.
Bai san abin dake damun sa ba a daidai wannan lokacin zuciyarsa sosai take son firgita masa tunani game da Mariya sosai yake jin wani fili mai girma ya buɗe a zuciyarsa ba abin dake yada zango a cikin sa sai lamarin Mariya sosai yake hangowa a ranar da ya fara ganinta bayan shekaru hudu da suka shuɗe ba tare da ya sanyata a idanuwansa ba.
Runtse idanuwansa ya sake yi a karo na ba adadi kafin ya shiga taka kafafuwansa a hankali yana mai isa toilet din sa ruwa ya watsa domin ko zai samu sa’ida a zuciyarsa dama gangar jikinsa gabadaya.
Yana cikin goge sumar kansa da shawul wayarsa dake yashe gefen gadonsa ta dau Ringing ya tsine fuska yayi kafin ya dubi wayar cikin halin-ko-in-kula yana mai jan guntun tsaki sai da wayar ta tsinke sau biyu kafin a na uku ya kokarta zuwa ya dauka new number ga ni kuma bata najeriya bace shiru yayi yana tunanin inda number din ta fito amma ya kasa cankowa yayi kamar zai katse sai wata zuciyarsa ta bashi damar dagawa a hankali ya latsa madannin yana kaiwa kunnansa mai makon ya rike da hannunsa sai ya ƙi sai ya makale ta a kafaɗarsa.
“Dr.Karami”.
Yaji muryar ta doki dodon kunnuwansa da sauri ya yarda shawul din dake hannunsa ya dago wayar daga kunnansa yana duba number din sosai mamakin murya da yaji yake yi sosai gabansa ya buga kadan don yasan shi mai laifi ne sau ba adadi yana kiransa yana kin dauka wanda bai san dalilin ba a hankali ya ciji laɓɓansa yana mai da wayar kunnansa.
“Uhmm!”.
Ya fadi da dan sauti a muryarsa.
“Ka kyauta kaji Dr.Karami…”.
Runtse idanu yayi kafun ya motsa laɓɓansa.
“Please Sorry My Dr.Vijay kasan dai ba haka kawai zan shan yaka ba dole sai da dalili”.
“Ban yarda ba kawai kace mani wulakanci ne ya tashi ko abin da ba halayyakar baka…wai shin ma me ya zaunar da kai ki dawo wa aiki ne har yanzu 3weeks left fa haba mana ya kamata ace duk abin da kake yi izuwa wannan lokaci ka kammala shi ka dawo”.
Runtse idanu Dr.Karami yayi yana jin yarda zuciyarsa ke sake hautsinewa da wani irin yanayi mai girman gaske na tashin hankali ba ya zaton zai koma aiki ba tare da komai ya daidai ta ba, ba ya zaton zai koma Delhi a yanayin da yake a yanzu ko yace zai koma to tabbas karya yayi domin kuwa ko yaje din ganga jikinsa ne kawai zata je can din amma zuciyarsa da ruhinsa suna nan nisawa yayi kafin ya fesar da huci mai zafi.
“Ina cikin wani yanayi ne mai matukar girma Dr.Vijay a halin da ake ciki yanzu ban san ranar dawowa ta aiki ba in har ba wai komai ya zama Normal bane”.
“What?!. Me kake kokarin cewa dani Dr.Karami anya kana hayyacin ka kuwa aikin naka kake mai dawa haka kana masa halin ko in kula meye ya same ka har da kake wannan ikirarin haka ya kamata gaskiya ka sauya tunani tun wuri kuma ya kamata ace ka dawo aiki at this time domin ana bukata ka”.
“Ba zan iya ba”.
“Kan wani dalilin?”.
“Kawai dai ba zan iya dawowa a yanzu ba domin akwai abu mai girma da nake so ya zama normal in har ba wai ya zama normal din bane to gaskiya bana tunanin ko na dawo zan iya wani abun kirki”.
STORY CONTINUES BELOW
“Shikenan Allah ya kyauta”.
Abin da Dr.Vijay ya fadi kenan da damuwa a muryarsa shi kansa Dr.Karami ya lura da haka sai dai ba yarda zai yi a matakin da yake a yanzu ba ya tunanin zai iya komawa Delhi sauke wayar yayi bayan sun yi Sallama jiki a mace ya zube bakin gadon kamar wani kayan wanki hannunsa ya saka ya dafe kansa da yake jin yana yi masa wata irin sarawa kamar zai rabe gida biyu runtse idanuwansa yayi kafin ya buɗe su a hankali.
Sosai yake jin zuciyarsa na sonta sosai yake ji duk jikinsa na aiki ne da sosai yake jin zuciyarsa nayi mata ya jima yana karyata kansa akan cewa son ta yake yi ya jima yana jin zuciyarsa na sanar dashi amma ya ki ansar lamarin sosai yayi kunnan uwar shegu da komai ba tun yau ba lokaci mai tsayi da ya shuɗe zuciyarsa tana kawo masa abubuwa masu matukar girma a game da ita amma bai yi AMANNA ba.
Bai san ya zai yi ba bai san ya zai fuskance ta da wannan lamarin ba sosai yake jin wani iri a zuciyarsa sosai yake hango rashin nasara baya tunanin in ya tunkare ta da wannan lamarin zata ansheshi har ta bashi fili a zuciyarta.
Fushi take yi dashi fushi na sosai da sosai bai san mai yasa ba ya sani har da laifin sa laifin sa mai girma ne a gareta wanda bai san ya zai wanke kansa ba a idanuwanta ta ki yarda dashi taki bashi lokacin ta su zanta gudun sa take yi sosai ta ke kin haɗa ko da hanya dashi ne sosai yake bibiyarta amma bata bashi lokaci yayi iya yin sa saboda ita ya baro aikin sa saboda ita ya zauna har tsayin wannan lokacin tun da ya fara aiki bai taba zuwa ya zauna a kasar nan ba mai tsayi sai a dalilinta a dalilinta komai nashi yake canzawa wanda bai yi zato ko tsammani ba zuciyarsa ta dade da narkewa da duk wani lamarinta ruhinsa ya jima da daskarewa da duk wani abu nata kwanyarsa ta jima da buɗe fili mai girma na tunaninta.
A tunaninsa ba ta kai matsayin da zai so taba, a tunaninsa ba ta kai matsayin da zai tsaya ya nuna yana son taba, a shekarunsa gani yake yi kamar ba su dace ba, gani yake yi kamar sun bambanta a wajaje da dama sai dai wani abu da yake kokarin ruguza duk wani tunaninsa a lokaci kankani ganin yarda ta canza komai na ta ya sauya ta koma masa mace mai ansa sunanta mace ta ko wani fanni sosai yake ji a ransa yayi wauta a can baya tunaninsa bai yi masa adalci ba da ya tunano masa rashin dacewa tsakaninsa da ita sai yau ya kara tabbatar wa SO SHU’UMI NE so ba ruwansa da girma ko yarinta a ko wata zuciya zai iya sauka ya buɗe filinsa yayi yarda yake so da zuciyar.
Numfashi ya ja mai tauri kafin ya fesar da huci mai zafi a hankali ya mike ya shiga shiryawa cikin riga da wando rigar mai dogon hanni Milk-colour sai blue din wando mai haske kayan sun yi matukar ansarsa suka kara fito da tsarin halittarsa ta mazantaka kallo daya zakayi masa ka gane Allah yayi halittar ɗa namiji a wajan mai ji da kansa ta ko wani fanni.
Sosai ya feshe cikin sa da turare mai dadin kamshi dakin kansa sai da ya dauki kamshi na ban mamaki kamar anyi barinsa.
Bayan ya kammala ya dauki Key din motarsa da wayarsa ya fice can parking Space ya nufa ya fiddo motarsa sai da ya gama kare mata kallo kafin ya buɗe ya shiga yayi mata key a hankali ya ja ta ya fice daga harabar gidan ya cilla titi.
London Streat unguwar ya nufa in da gidan mahaifiyarsa yake tuki yake yi a hankali a jikinsa yake ji kamar bashi da lafiya sosai yake jin ko wani sashi na jikinsa kamar an doddoke masa cikin wannan yanayin ya isa gidan Horn yayi mai gadi ya buɗe masa Get Babban gida ne sosai kallo daya zaka yi masa kasan masu gidan akwai farcen susa ko wani sashi ka kalla tsaf yake Parking yayi ya fito bayan sun gaisa da Malam Audu mai gadi sannan ya nufa hanyar Falo din da sallama a bakin sa ya tura ya shiga ba kowa a falon sai Tv dake ta faman aiki yawatawa ya shiga yi da idanuwansa cikin falon da yake ta faman tashin kamshin turaren wuta a hankali ya ja numfashi yana mai sakin yak’e kamar wanda akayi wa dole da sauri yayi hanyar dakin mahaifiyar tasa don ya tabbata tana ciki.
STORY CONTINUES BELOW
Zaune ya tadda ita bayan yayi mata sallama ta ansa shi fuskarta da murmushi mai girma kallo daya zakayi mata ka tabbatar da ita ce mahaifiyar tasa suna kama sosai sai dai shi Dr.Karami ya fita hasken fata saboda hasken fatar mahaifinsa ya biyo kama ce dai ya dauko ta uwa sak!
A hankali ya isa gareta shi ma fuskarsa da murmushi kan salayar da take kai ya samu guri ya zauna ya na daura kansa a kafadarta shafar kansa tayi kafin ta rufe littafin Husnul-Muslim dake hannunta.
“My Son ya akayi ne?”.
Margaya kai yayi kamar wani karamin yaro kafin ya dago kansa ya dubeta.
“Ba komai Mami kawai dai yau bana jin dadin jikin nawa ne sosai”.
Zaro idanu waje tayi kafin ta furta.
“Yaa Allah da fatan dai ba wani abu bane yake damun ka”.
Girgiza kai kawai yayi kafun ya mai da kan nasa jikin kafadarta.
Wani numfashi taja mai kwari kafin ta dubi Dr.Karami sosai fuskarta da wani irin yanayi mai girma na damuwa.
“Hisham”.
Ta furta kamar bata so ba da hanzari ya mike yana dubanta jin ta ambaci sunansa sak! Wanda ya manta rabon da yaji ta kira shi da hakan sosai yake kallon ta jikinsa da wani irin yanayi gabansa ya ji yana bugawa a hankali.
Kau da kai tayi daga kallonsa.
“Na fara gajiya Hisham abin dai da baka so shi zan fadi ban san adadin lokutan da nake zaunar dakai muna irin wannan maganar ba ban san adadin lokacin da na dauka wannan lamarin na damuna ba abin ya fara shanlake tunani tun kafin rasuwar mahaifinka ake abu daya amma har yau babu wani lamari to maganar gaskiya in har ba so kake yi nima na mutu da wannan burin ba to ya kamata ace kayi wani abu akai ba wai takura maka nake yi ba abin da zai kuftar da kai daga fadawa halaka nake gujewa ba wai ina zargin ka bane da komai Hisham amma ya kamata ace a irin wannan shekarun naka yaci ace kana da mata har da ‘ya’ya duk da dai komai na rayuwar nan sai Allah ya sa zai tabbata san nan yake tabbata”.
Shiru yayi kansa na wani irin juya masa gabadaya yake jin komai na kara hargitse masa musamman yanayin da ya ga mahaifiyarsa a ciki a yau din nan ya san ta kai makura amma shi kam bai san ya zai yi akan maganar auren nan har yanzu bai jin akwai wacce zai iya zama da ita a filin duniyar nan a matsayin mata ba shi akaran kansa yana mamakin rashin aurensa bai san dalili ba bai san mai yasa sam a shekarun da ya kwashe na girman sa bai ji yana da muradin aure ba domin zuciyarsa har yau bai ji ta kamu da son wata ‘ya mace ba…
Shiru yayi jin zuciyarsa na karyatashi da abin da yake fadi wanda ya tabbata a yanayin da yake ciki yanzu komai ya sauya komai ya canza sosai yake jin so a cikin zuciyarsa son ma akan wanda bai taba tsammani ba.
“Hisham kai kadai ne ɗan mu a duniyar nan kai kadai Allah ya ba mu duk da muna son ‘ya’ya haka muka hakura da hukuncin Allah kai ya kamata ka share mana hawaye na ‘ya’ya bila adadin amma kuma ya kamata ace kai a bangaren ka kayi aure ka hayayyafa domin Ubangiji yayi alfahari da kai nima nayi alfahari da kai mu ba muyi ba ya kamata ace kai kayi Hisham a maganar gaskiya shekarun sun kai matakin da ya dace ace ka ajje iyali in har ba so kake yi ka koma ga mahaliccin ka a haka ba ba abinda ka rasa kana da arzuki daidai gwargwado kana da aikin yi ba rashin muhalli kana da lafiyarka ko mace fiye da daya Hisham kana da halin riketa to don Allah ka duba Hisham ba wai takura maka nake yi ba a,a so nake yi kai ma ace ko ka bar duniya to ka bar wanda za a gani ace naka ne wanda hakan ba zai sa a manta da kai ba a lokaci kankani”.
Dago kai yayi ya dube ta da damuwa kafin ya saki fara’a.
“Mami na! Shikenan naji in Allah ya yarda ba zan baki kunya ba a wannan lokacin kin san mi ma kawai ki nemo min matar aure kawai…”.
STORY CONTINUES BELOW
Wani kallo ta watsa masa.
“Ban yarda ba ai bani zan zauna maka da matar ba don haka da kanka zaka zaɓo matar auren ka don haka maza tashi ka bani waje na baka lokaci kayi abin da ya dace”.
Kokarin kwanciya yake yi da dariya a fuskarsa ta dube shi.
“Me zakayi kasan Allah ba yarda za ayi kana katoto da kai ka karasa ni maza tafi gidan ka kaje can ka kwanta ba wai ka zo nan ka isheni ba…wai shin sai yaushe zaka koma wajan aikin ka ne Hisham lokaci fa naja kuma nasan za su ne meka ban son abin da zai zo ana dana sani”.
“Na kusan komawa”.
Ya fadi yana mai mikewa domin a halin da yake yanzu sam bai so ayi masa maganar kin nan nasa sam ba ya gabansa wannan tashin hankalin da yake ciki ya ishe shi Sallama yayi wa Mahaifiyar tasa yayi tafiyarsa ita kanta ta lura da sauyin ɗan nata a lokaci guda sai dai fatan ta Allah yasa lafiya littafin Husnul Muslmin din ta dauƙa ta cigaba da dubawa.
*******
Ya tsine fuska ta shiga yi ganin wanda yake kiranta sai da ta gama kare masa kallo kafun ta isa gareshi shikuwa sai faman yashe baki yake yi kamar wanda aka ce an bashi ita kyauta.
Gaidashi tayi ba tare da nuna masa komai ba ta lura da Dr.Aqeel sosai yake son bata matsala a duk lamarinta sosai yake so yake haifar mata da tashin hankali lokaci da yawa yana zuwa amma sai yaji labarin Dr.Karami ya zo sannan zai fara mata zarya kamar wacce yake bi bashi a cikin satikan nan da Dr.Karami yayi Dr.Aqeel ya zo yafi a lissafa ta rasa mai yake nufi da haka sosai take hango kamar akwai wata manufa ta daban a zuciyarsa duk da ya nuna yana sonta din ta yarda amma ita halayensa ne ba su mata ba ya fiye zafin rai da mai da karamin abu babba ita kuma abin da ta ki jini a filin duniyarta zafin rai da sauri hassala…
“Mariya ban san ta ya ya zan billo miki ba iyakar bakin kokarina nayi amma abin har yanzu dai ba canji ya kamata izuwa wannan lokaci kin bani matsaya domin ni dai da gaske nake ba karya nake miki ba ni ba karamin yaro bane da za ai ta kai kawo akan abin da bai fi shan ruwa wuya ba”.
In akwai abin da ta tsana a filin duniyar Dr.Aqeel to rashin iya kalamai sam magana yake yi kamar saukar markaɗe ga shi murya ba kadan ba gabadaya sai ta cika mata kai ba wai bata son sa bane a,a sosai take jin sa a ranta amma ba ta tunanin za ta iya zama dashi a inuwa daya.
“Kice wani abu mana”.
Dago idanuwanta tayi ta dubeshi sosai Dr.Aqeel ba shi da makusa ko ta miskala zarratin amma bata san mai yasa zuciyarta har zuwa wannan lokaci ta kasa amanna dashi ba.
Horn din da ya doki kunnuwansu ya sanya su gabadaya suka juya kallo daya Mariya tayi wa motar ta gane wanene wani irin bugawa taji gabanta yayi da karfi idanuwanta suka yo waje wani matsanancin tsoro taji ya ziyarce ta nan ta shiga kallon kallo tsakanin Dr.Aqeel da Motar Dr.Karami yanayin da Dr.Aqeel ya ganta aciki ya tabbatar masa da akwai wani abu domin shidai bai gane waye ma a cikin motar ba.
Numfashi ta shiga ja a hankali ji take yi kamar ta kwasa da gudu sam bata so ace sun hadu da juna domin rabon dasu tsaya a tsakaninsu tun ranar da rigima ta kacame tsakanin Dr.Karami da Huzaif shikenan ta shiga wasan buya ko ya zo wajan ta sai ta san yarda tayi ta guje masa.
“Zan shiga gida Sai anjima”.
Mariya ta fadi muryarta na rawa da sauri Dr.Aqeel ya dubeta cikin mamaki da tuhuma kafin ya motsa laɓɓansa yana cizansu.
STORY CONTINUES BELOW
“Idan kika yi mani haka kina tunanin kinyi mani Adalci kenan Mariya me yasa wai baki son tsayawa ki fuskanci in da na dosa ne mai yasa kullu yau min in na zo wajanki baki taba bani lokacin ki…”.
Numfashi mai zafi ya fesar kafin ya sake kallon motar wacce har zuwa wannan lokacin ba alamun za a buɗe ta.
“Ina son ki Mariya so mai tsanani kuma na san ke ma kina sona ko baki so ni dan komai kin so ni taimako…”.
Ware idanu tayi sosai tana duban Dr.Aqeel da take jin kalamansa na saukar mata kamar aradu aka jin in da ya dosa ya sanyata daga masa hannu.
“Ban yi zaton haka daga gareka ba ban taba tsammanin zan ji haka daga gareka b Dr.Aqeel me kake son ce mani kana nufin ba saboda Allah ka taimaka mani ba ko me kana nufin dama akwai wata manufa a tsakanin taimakon da kayi mani”.
Lokaci guda idanuwansa sukayi ja bacin ranta ya bayyana sosai bakin ta na rawa ta sake dubansa kafin ta kau da kai.
“Kenan ba don Allah kake so na ba kenan dama can kana da wata manufa ta daban a haka kake so na so ka a haka kake so mu zauna inuwa daya da kai a haka kake son ko mun zama ma’aurata ba zaka mance taimakon da kayi mani ko da laifi nayi maka goranta min zaka din ga yi kaico!”.
Ta fadi tana mai dauke kwallar da suka zubo mata a fuska a hankali ta shiga takawa tana barin wajan zuciyarta na wani zafi da raɗaɗi kirjinta take ji yana kartawa kwanyarta na hautsine wa.
Gabanta ya sha cikin matsanancin tashin hankali idanuwansa sun kaɗa sunyi jajir.
“Mariya me kike nufi da haka mai yasa zaki yi saurin yanke min hukunci akan abin da ba haka bane mai yasa kike kokarin fuskantata a hagunce na rantse miki da…”.
Da sauri ta daga masa hannu izuwa wannan lokacin idanuwanta sun kawo ruwa.
“Ba abin da zaka ce mani Dr.Aqeel ba maganar da zaka sake fadamin na yarda na sani ni talaka ce wacce bata dashi wacce ubanta ya kawo su asibiti ya gudu ya bar su ba tare da komai ba…”.
Wani murmushi mai ciwo ta saki kafin ta dora da cewa.
“kana da damar fada min komai ko mai kace ban ga laifin ka ba ni ce mai laifi mu muka zo wajan ka mu muka nemi taimako zaka iya fada mana komai amma ka sani a duniyar nan hanyoyin da Allah ya buɗe su da yawa suke domin wani ya zo ya nemi wani abu a wajan dan’uwansa ka sani komai yake faruwa dani da sauran iyayena ba mu muka daurawa kan mu ba ka sani ALKALAMIN ƘADDARA ne ya zana mana kuma ka sani duk wani dangin rai a duniyar nan ba yarda ƙadddararsa bata zuwa masa domin kuwa ba komai bane bawa ke nema ya samu Dr.Aqeel…”.
Runtse idanu tayi jin yarda zuciyarta ke zafi da raɗaɗi a duniyar nan in akwai abin da ta tsana shine ayi mata gori tana jin zafin hakan sosai a ranta shiyasa ta kullacin hakan a ranta cewa duk yarda zatayi rufawa kanta asiri zata yi domin ta lura a duniyar nan ba abin da yafi bakinciki da takaici shine ka nema wajan wani ya dizga ka ko kuma yayi maka bayan idonka ya zo yana zaginka ko yana goranta maka a duniyar nan ba abin da yafi kwanciyar hankali da gujewa wulakanci kamar DOGARO DA KAI.
“Mariya don Allah kiyi hakuri wallahi tallahi ba haka nake nufi”.
“Don Allah Dr.Aqeel ka rabu dani in har ba so kake yi zuciya ta buga ba ka barni haka ka sani ban ga laifin ka ba don ka fadi haka maganar so kuma Dr.Aqeel ka sani ina son ka amma halayenka ne na tsana ba zan boye maka ba a yau na kara gasgata abin da zuciyata ta ɗade tana sanar dani bana tsammanin inuwa daya da kake kwadayin mi zauna a tare zai yuwu”.+
STORY CONTINUES BELOW
Ta karashe tana mai kaucewa tana wucewa da sauri ya shiga kokarin shan gabanta wani kallo tayi masa hakan ya sanyashi tsayawa cak! Yana dubanta har ta karasa cikin sauri-sauri gudu-gudu.
Zubewa ne kawai Dr.Aqeel bai yi ba a kasa domin zuciyarsa yake ji tana wani irin bugawa da sauri-sauri kamar zata faso kirji ta fito duniyar yaji tana juya masa bai san abin da ya kai shi yin wannan maganar ba bai san mai ya kai shi ba gashi yanzu bakin sa ya yanka masa wuya yankan da bai san ko zai warke ko ba zai warke ba yanayin da ya ga Mariya a ciki ba karamar kiɗima yayi ba a hankali ya fara taka kafafuwansa hannunsa rungume da kansa har isa wajan motarsa ya shiga kafun ya dago ya dubi Motar da tun dazu take tsaye ba tare da mai ita ya fito ba sosai yaji zuciyarsa tana azalzalarsa da ya tsaya ya ga kowa waye amma a halin da yake jin kansa a yanzu ba zai iya ba yana bukatar ya gansa a gida yana bukatar ya kebe kan sa waje daya domin yin tunani da samo mafita da za ta haifa masa da ɗa mai ido.
A hankali yayi wa motar key kafun yayi ribas ya fizge ta da gudu ya bar unguwar zuciyarsa a jagule.
Dr.Karami da zuciya ta kwasoshi tun dazu yana dannewa duk abin da ya wakana yana kallo ya dade yana zargin Dr.Aqeel akwai wani abu a tsakaninsa da Mariya bai gasgata ba sai yau da idanuwansa suka gane masa zuciyarsa yaji tana zafi da wani irin turiri sitiyarin motar ya buga tare da buɗe murfin motar ya fito sai faman huci yake yi kamar wani kumurci fuskarsa har ta canza launi saboda tsananin bacin rai ya shiga kai wa iska naushi kafin ya ja kakafuwansa zuwa cikin gidan da Sallama ya shiga ba kowa tsakar gida sai muryar Mu’azzam dake tashi cikin kuka sake sallamar yayi a lokacin Umma ta ansashi kafin ta bashi izini ya iso daga kofar dakin ya tsaya suka gaisa da Umma abin da bai saba yi ba yau yayi shi kansa sai da yaji wani bambara kwai wai namiji da suna Hajara ita kanta Umma sai da tayi mamaki amma ba ta nuna masa ba.
“Mariya na ciki Umma ce ina son ganinta”.
Ya fadi murya a sake amma a zuciyarsa shi kadai ya san abin da yake ji
Mariya dake dunkule waje guda tun dazu dama take jiran tsammani da sauri ta mike ta zauna tana rarraba idanu alamun rashin gaskiya sosai Umma ta shiga dubanta tana karantar yanayinta kafin ta wurga mata harara lokaci guda.
“Tashi ki fice mani daga daki sakayya”.
Rau-rau tayi da idanu kamar zatayi kuka don yarda Umma tayi maganar ya tabbatar zargin da take yi yiwa Dr.Karami laifi tayi shi shi haifar da komai.
“Tashi nace tun kafin na kwaɗe ki wallahi”.
Zabura tayi tana mike tana tura baki gaba har sai da ta ga Umma ta mike sannan tayi saurin ficewa daga cikin dakin bata same shi a tsakar gida ba hakan ya tabbatar mata yana waje a hankali ta fara takawa gabanta na faduwa a har ta isa cikin soron gida tana kokarin ficewa daga cikin sa sam bata lura da mutumin da ta wuce ba sai ji tayi ya kira sunanta a firgice ta waigo tana kokarin kwasa da gudu ya sha gabanta saura kadan ta fada jikinsa runtse idanu tayi jikinta ya shiga rawa sosai ta firgita da yanayin sa a hankali taji yayi gyarar murya.
“Buɗe idanunki”.
Ya fadi ba yabo ba fallasa jin abin da yace ya sanyata buɗe idonta daya tana kallonsa harararta yayi da sauri ta mai da ta rufe kafin ta bude su gabadaya a firgice.
“Ke kina tunanin wannan halin da kikeyi shine mafita a gareki ko a yarda kike a matsayinki na ‘ya mace kina tunanin abin da kike yi mutuncin kine na lura Mariya gabadaya kin canza halayenki ba yarda na san ki a da ba wai har kece kullum baki wajan wannan saurayi ba ki wajan waccan kuna rigima a matsayinki na ‘ya mace anya kuwa bana tunanin wacce ta san mutuncin kanta da darajar ta zata kasance a haka”.
Wata katangar tashin hankali taji ta rikito mata lokaci guda kanta ya shiga sarawa lokaci guda idanuwanta suka kawo kwalla ta shiga dubansa shikuwa nuna wa yayi ko a jikinsa amma can kasar zuciyarsa ji yake yi kamar ana hura masa wuta.
“Duk mace mai daraja ba za ta taba kasancewa a haka ba Mariya kin bani mamaki kin canza mani ban yi tsammanin haka kika koma ba…ba ma wannan ba tun yaushe nake garin nan amma daidai da rana daya kin ki bani lokacin ki amma kin iya baiwa wanda zaku tsaya layi kuna rigima da su saboda ni bani da wata daraja a idanunki ban cancani ki tsaya dani ba shikenan na gode amma ki sani in har kikace haka za ki cigaba da rayuwa da samari kina da katon aiki a gabanki”.
Yana gama fadin haka ya fice daga cikin soron zuciyarsa na suya sosai yaji ba dadi a ransa da maganar da ya gaya mata amma haka kawai yake ji a zuciyar tasa ita kadai hanyarsa ta samu sauki duk da dai bai san ya zata dauki lamarin ba.
Idanuwanta da suke zubda hawaye ta kure kofar da su tana jin wani tashin hankali mai girma yana wanzuwa gareta a hankali taji kafafuwanta na kokarin kasa daukarta zubewa tayi kan gwuiwowinta lokaci guda ta na sakin wani kuka mai ciwo da taba zuciya…A hankali take taka benan har ta isa bakin kofar tana jin yarda gabanta ke dokawa ba ta san ya zai kalleta ba bata san ya zai karbeta ba ita dai ta san tana son sa so mai tsanani wanda tun da take a filin duniyarta bata taba jin son wani ɗa namiji ba kamar Dr.Erena zuciyarta da ruhinta sun jima suna kai kawo akan son shi ta dalilin son sa ta zo aiki cikin Company sa saboda burinta ya cika take zaman aiki a company ba wai saboda kudi ba amma ta rasa ya zatayi ta rasa mai ya dace tayi a gareshi domin ya amince da ita har ya so ta sosai ta lura sam! baya kula duk yanayin da take nunawa don ya sota amma hakan sam ba ya wani tasiri akansa ba ta san ya za tayi ba abin da ya ke kara tayar mata da hankali yarda lokaci guda wata ta shigo cikin Company din take kokarin bata mata duk wani shirinta ta lura Dr.Erena son ta yake yi so kuwa mai tsanani abin da ta lura dashi ita Areefa ba son sa take yi ba shi yake kiɗin sa yana rawar sa ga inda ake son sa amma ya kwashi jiki ya tafi in da ba a son sa.
Ita dama tun da Areefa ta shigo cikin Company nan gabadaya taji bata kwanta mata ba sosai take ji a ranta akwai abin da zai faru don ta lura ita ma Areefa ba wai aiki ne kawai ya kawo mata ba har da wani KUDIRI nata na daban.
Tsaki taja kadan kafin ta gyara zaman rolling din da tayi wa dan kwallin jallabiyar dake jikinta sosai ta gyara zaman glass din dake fuskarta kallo daya kayi mata ka san ita ma ba baya b wajan kyau da kirar jiki fara ce amma ba can sosai ba.
A hankali ta turo kofar Office din ta shiga zuciyarta na bugaawa da halin tsoro don bata san abin da zai je ya dawo ba bata san yarda Dr.Erena zai karbeta ba ta san ya zai anshi abin da za taje masa dashi ba.
“…Bobby karka sake ka bata min rai kayi kawai abin da nace da kai ba wai ka kai shi can in da ba a dawowa ba a,a kawai so nake yi yaji a jikinsa ya san har yanzu Dr.Erena yana nan a yarda ya sanshi ba wai canzawa yayi ba”.
Tana kokarin buɗe baki tayi sallama ta tsinkayi muryar Dr.Erena ya na fadin haka ai mutuwar tsaye tayi idanuwanta a warwaje lokaci guda jikinta ya shiga ɓari kamar wacce akayi wa wankan ruwa mai tsanani sanyi gumi ya shiga tsantsafo mata a jiki lokaci guda duk taji jikinta ya shiga narkewa da duk wani kudiri da buri da ta zo don cimmawa a hankali ta shiga jan numfashi tana mamakin kalaman Dr.Erena bata taba zaton haka yake ba bata taba zaton akwai rashin imani har haka ba a ransa.
A hankali ta shiga kokarin juyawa don ficewa amma zuciyarta tana hanata akan kudirin da ta zo dashi sosai taji komai ya fara canzawa tsoro da fargabar da take yi ya ragu sosai zuciyarta na kara mata jarumta akan kawai taje ai mai nema ba ya rasawa ita fa abin da ta zo yi daban maganar da yake yi bai shafe ta ba kuma ba ta san abin da yasa yace haka ba.
Da wannan tunanin ta shiga saita kanta gabanta na faduwa kadan kadan.
Sallama tayi tana mai cusa kanta cikin Office din tsaye ta hangeshi yana kai kawo fuskarsa da murmushi wanda daka kallashi zaka gane na mugunta juyowa yayi jin sallamar da kayi dubanta yake yi cikin wani irin yanayi kafin ya kau da kan sa.
“Sannu Sir”.
Ta fadi da kokarin dauko jarumta ta azawa kanta ansawa yayi a ciki kafin ya dube ta ba yabo ba falla sa.
“Lafiya me ke faruwa ne Mufeeda?”.
Sosai taga yayi mata kwarjini a idanunta gabanta taji yana bugawa wata irin burgewa take jin lokaci guda tana karuwa akan Dr.Erena juya idanunta ta shiga yi tana faman yak’e kamar wacce bata da gaskiya.
Dubanta ya shiga yi da wani irin yanayi na tuhuma kafi ya tako inda take tsaye.
“Akwai wani abu ne?”.
STORY CONTINUES BELOW
Ya fadi yana kureta da kallo da ya kusan narkar mata zuciya da gangar jiki. A hankali ta shiga motsa baki zuciyarta na tsallen tsoro akan yarda zai anshi lamarin.
“Sir, dama akan maganar Areefa ce”.
Dan yatsine fuska yayi kafun yace.
“Me ya faru da Areefa din wani abu tayi miki ne?”.
Girgiza kai tayi kafun ta ja numfashi mai tauri tana jin yarda wani abu da ya tokare mata kirjiya ya sauka.
“Gaskiya Sir. Ban yarda da ita ba jikina sam! Bai kwanta da ita ba tun da ta zo Company din nan sosai nake ji ajiki kamar ba alheri bace a gareka da ma mu kafatanin ma’aikatanka…”.
Hautsine wa fuskarsa ta shiga yi da wani irin bacin rai idanuwansa suka shiga kaɗawa da tsananin haushi kafin ya dube ta sosai da sosai yana faman hirji kamar wani kumurci.
“Me kike cewa Mufeeda Areefa din ce ba alheri ba Areefa ce kike jifa da wadannan kalaman naki kina da hankali kuwa anya ba wani abu kika sha ba wanda ya rabaki da duniyar hankali gaskiya bana zaton kina cikin hayyacinki na lura ke ma kin fara yan kurɓe-kurɓen nan na yan matan wannan zamani in ba haka ba ina ruwan ki da ita mai ya shafe ki da ita rayuwarki daban ta ta daban don haka tun wuri tun muna kallo juna a mutunce ki fice mani daga Office tun kafin na keta miki rashin mutunci.”.
“Am…amma Sir. Daka tsaya ka fuskance ni gaskiya ce fa nake sanar da kai…”.
Wani kallo ya watsa mata kafun ya shiga nuna ta da hannu.
“I Say Get Out! tun kafin nayi miki abin da baki taba zato ba”.
ware idanu tayi sosai jin furucinsa ya taba mata zuciya amma sai taki barin haka yayi tasiri a zahirancen cikin jarumta ta sake dubansa murya alankwashe.
“Sosai na fuskat kamar akwai wata alaka a tsakanin kai da ita Sir hakan kuma bai dace ba sam ya kamata ace ka nemi mace mai daraja mutunci a matsayinka na mutum mai daraja da mutunci mutane da yawa yanzu kallon wani daban suke yi kamata ganin alakarka da Areefa…”.
“Mufeeda! Which can of nonsense kike kokarin gaya mini me kike nufi dani me kike so ki ce da nine akan Areefa ya kamata tun wuri ki gyara kalaman ki kuma ki sani indai akan Areefa ce kika zo kina yi mani wannan haukar wallahi tallahi gaf! kike da barin Company din nan”.
Gwalo idanu tayi waje sosai zuciyarta na wani irin raɗaɗi da zafi komai take ji na jikinta yana canzawa sosai take jin komai nata kamar ba nata ba kalaman Dr.Erena ba karamin taba mata zuciya sukayi ba ji take kamar ta daura hannu aka ta kurma ihu bata san ya zatayi ba bata san me zatayi Dr.Erena ya kalle ta a mutunce ba bata san hanyar da za ta bi ba domin ya kulata ya anshi tayin da take masa ya sota kamar yarda ta kamu da son sa a filin duniyar zuciyarta sosai take son sa so bana wasa ba tana kishinsa ba ta son duk wata mace ta ga tana kusantarsa sosai tashiga tashin hankali lokacin da ta ga Areefa ta fado rayuwarsa.
Wasu kwalla taji suna neman zuba mata da sauri ta dauke su ba tare da Dr.Erena ya gani ba amma sai dai tayi shuka a idon makwarwa domin kuwa duk motsinta akan idonsa take yi da mamaki yake dubanta sosai hawaye da ta shafe ya kara sanya shi a mamaki sosai sakanni ya dauka yana kallonta kafun ya ce da ita cikin muryar tuhuma.
“Hawaye Kuma me yayi zafi shi ba wuta ba Mufeeda me yake damun ki wani abu akayi miki ne Pleaae Leave my Office ba zan dauki wannan haukar taki ba kin ji ko I need to be alone ba na son abin da zai kawo mani ciwon kai don ba dauka zan yi ba”.
STORY CONTINUES BELOW
Murmushi tayi wanda ya fi kuka ciwo sosai take jin bakin ciki da takaici na rashin darajawa da Dr.Erena yake nunawa akanta sosai take ganin rawar kanta da gangacin da zuciya tayi mata na son wani wanda bai son tana yi ba ga ta yanzu a gaban shi amma yana nuna ita da banza duk daya bata san mai ya sa haka ba ta san dai SONE SILA wanda bai yi mata adalci ba bai dace ace yayi mata haka ba bai kamata ace AKAN SO tana kuka ba kukan ma akan wanda ba tayi tsammanin zuciyart za ta so shi ba ko a mafarkin ta ba ta taba zaton zuciyarta zata dauko mata son Dr.Erena ba ta kawo mata tun da ta fara aiki a Company tun ranar da ta daura idanuwanta akan sa taji ta kamu da son sa amma bata san ta yaya zata bayyanar son da take masa ba a gareshi domin sosai da sosai yake mata girma da kwarjini a idanunta.
Ba ta zaton za ta iya barin nan batare da ta amayar masa da abin da take ji game dashi ba bata zaton zata iya daukar gangar jikinta ta fice daga cikin Office din nan batare da ta bayyana son da take masa ba ko da kuwa hakan zai sanya ya kore ta daga Company din nan. Ba za ta iya cigaba da dakon son sa ba tana bukata zuciyarta ta sarara mata da tashin hankali da take samun kanta kullum a ciki runtse idanuwanta tayi kirjinta cike fargaba da tashin hankali mara musaltuwa tana jin yarda kirjinta ke bugawa da sauri-sauri motsa laɓɓanta ta shiga yi kanta take ji yana juyawa amma haka ta kinkimo jarumtar duniya ta daurawa kanta.
“Dr.Erena…”.
Ta fadi tana jan wani numfashi mai tauri gaske shi kuwa dubanta yake yi da mamaki cike da fuska jin a RANA DAYA Mufeeda ta kira sunansa abin da bata tabayi ba tsayin lokacin da ta fara aiki sosai ya natsu yana dubanta kafin ya ja kujera ya zauna.
“Na jima a duniyarka ina shawagin son ka amma sam baka lura da haka ba, na jima ina jiyar zuciyata da tayi gangancin daukar sonka ta azawa kanta, na jima ina kwaɓarta amma ta ki ji tayi nisa a sonka, na jima ina sanar da ita cewa ba mu dace ba amma bata ga hakan ba ta nuna min so ba ruwansa da haka, Dr.Erena naji ma ina son ka so mai tsanani sosai nayi zaton za ka gane in da na dosa amma ina sam hankalin ka bai kai nan ba maganar gaskiya ina son ka kai ne namiji na farko a filin duniyar nan da zuciya ta tayi amanna dashi a fannin so ban san ya zan kwatanta maka ba amma ka sani ina son ka so mai ansa suna so”.
Zabura yayi daga kan kujerar da yake zaune idanuwansa cike da tulin mamakin maganganun Mufeeda hannu ya shiga nuna ta dashi yana jan numfashi kafun ya saki wata dariya wacce ta kaɗa ‘yan hanjin Mufeeda sosai lokaci guda taji gabanta ya yanke ya fadi runtse idanu tayi wasu hawaye suka zubo ta kasar Glass din da ke fuskarta kafin ta shiga haɗe hannayenta waje daya tana Rolling din su.
“You Love Me? For God Sake! Mufeeda kina cikin hayyacin ki kuwa kin san waye Dr.Erena kuwa da kike daukar wa kan ki wahalar son sa to maganar gaskiya ba zan boye miki ba bana tunanin zan iya zama nayi soyayya dake bake ba ma hatta WATA MACE daban bayan Areefa bana zaton ko kallon arzuki zan iya yi mataa ya kamata ki san wani abu mace bata gabana mace daya na taba so kuma nake burin zama da ita ita ce Areefa ita ma ban san ya akayi zuciyata ta kamu da son ta ba a RANA DAYA ba zato ba tsammani naji KIBIYAR AJALI ta son ta ta cakar min zuciya wanda har zuwa wannan lokaci na kasa zareta sai kara lumewa take yi cikin zuciyata da duk wani gurbi na cikin ta”.
Dubansa take yi da duk idanuwanta da suka kaɗa sukayi jajir fuskarta har tana canza kala izuwa ja sosai take jin duniyar nayi juya mata da duk wasu kalaman Dr.Erena da take jin su kamar saukar garwashin wuta.
Numfashi take ja da take jin sa kamar ta na jan barkono izuwa kanta dama cikin ta sosai take jin duk wani sashi na jikinta na narkewa kamar zata watse a kasa dan yatsanta daya ta kai baki tana cizawa domin tabbatar da abin da yake faruwa da ita gaskiyane ba a mafarki bane yau ta kara tabbatar wa da maganar hausawa na cewa SON MASO WANI koshin wahala ne ta tabbatar da yau Dr.Erena baya tare da ita At All baya gayyatarta a filin duniyarsa bai ma san tana yi ba.
STORY CONTINUES BELOW
“Na lura da abin da kika zo dashi akan Areefa duk kishi ne kina tunanin son da nake yi mata zai bari na dauki abin da ki ka zo mani dashi a gaske to ko da kuwa gaske ne ba zan dauka ba Areefa mace ce da nake so so mai garman gaske wanda bana zaton a filin duniyar nan akwai macen da zan iya yiwa ko da kwatar son ne don haka fice mani daga cikin Office”.
Ya fadi yana mai yi mata nuni da hannu fuskarsa a murtuke kamar bakin hadarin da ya gangamo yake kokarin zubda ruwa.
“Dr.Erena MENE NE LAIFIN ZUCIYA don ta nuna so da kulawa akan abin da take so bana zaton son da nake yi maka zaka yi masa fatan KARKON KIFI ka sani so nake yi maka son da ban taba yi wa wani ɗa namiji ba a filin duniyar nan ya kamata ace ka girmama son da nake yi maka ka dauke shi da daraja ka killace shi a zuciyarka a wani fili ko ya ya ne…”.
“Are U At Of Your Sense Mufeeda kina da hankali kuwa wacce irin magana ce haka kike fadi wani irin hauka ne haka ina so dole ne nace bana yi na ce bana sonki leave alone mana”.
Murmushi ta saki mai ciwo kafun ta zare Glass din dake fuskarta idanuwanta da suke rine suka bayyana sosai take duban Dr.Erena da yake mata kallon wulakanci da raini laɓɓanta ta ciza.
“Karka yi tunanin don na furta kalmar so a gareka zai baka lasisin wulakanta ni, karka yi tunanin don buɗe baki na sauke aji na da daraja ta ta ‘ya mace za ka wulakanta ni ka sani ba aibu bane san nan ba zubda mutunci bane don mace ta buɗe bakinta ta fadiwa ɗa namiji tana son sa ba san nan haka ba yana baiwa ɗa namiji dama bane don ya wulaƙanta ‘ya mace don ta nuna tana ta son sa ba duk macen da zata iya buɗe baki tana cewa namiji tana son sa ba abin kunya bane kuma ba abin a wulakanta ta bane domin tayani don ceto kanta da halin da zata fada ka san wannan Dr.Erena karka yi tunanin son da na nuna ina yi akan ka zai baka damar tozartani ka wulakanta ni daraja da martaba ta tana nan ba abin da ya ragu sannan ko a duniyar masoya na san nayi abin kwarai wanda da yawan mata ba sa yi sannan kuma kamar yarda mata suke tsoro halin da ka nuna min da tozarci da wulakanci don kawai na nuna ina son ka ba laifi na bane laifin zuciya tane wacce ba ƙashi gareta ba”.
Dubanta ya sake yi a wulakance domin sosai zuciyarsa tayi zafi da kalamanta motsa baki ya shiga yi yana kokarin magana ta daga masa hannu.
“Ba sai ka daka min tsawa koka koreni kamar wata mara ‘yanci kai ba yanzu zan bar maka Office din ka”.
Tana fadin haka tayi hanyar fita daga Office har ta rike Handle din ta juyo ta dube shi sosai kafun ta kau da kai tare da ficewa daga cikin office din tana kokari hau benen da zai kai ta kasa ita kuma Areefa na sako kai saura kadan suyi gware nan suka shiga kallon kallo a tsakanin juna su fuskar Mufeeda cike da kunci da bakin ciki kallon Areefa take yi da wani irin yanayi kafun ta kau da kai gami da jan tsaki ta wuce ita dai Areefa bin ta take yi da kallo ganin yanayin da take ciki kamar akwai abin da take damun ta musamman idanuwanta da suka kaɗa sukayi jajir kafaɗarta ta daga cikin nuna halin ko in kula kafin ta isa ta tura kofar cikin Office din.
Tsaye ta same shi yana kai kawo hannayensa goye a bayan sa motsin shigowar tane ya sanya shi tsayawa yana jan numfashi fuskarsa a daure kamar hadari.
A hankali ta isa ta zauna tana mai daura kafa daya kan daya bakinta dauke da cingum tana faman taunawa idanuwanta akan Dr.Erena kallon sa take yi da wani irin yanayi mai haifar mata da ɗaci a zuciyarta sosai take dubansa da damuwar da take fuskarsa a ranta take fata dama ya dauwama a haka yaƙe ta saki kafun ta kaɗa idanuwanta.
“Me ke faruwa ne Dr.Erena?”.
Sai a lokacin yaja numfashi mai girma ya na huci gami da runtse idanuwansa dubanta yayi kafun ya ja kujera ya zauna.
STORY CONTINUES BELOW
“Wannan mai kalar haukar ne za tayi mani akunyanci bata san na fita da duk tashencin ta ba”.
Cikin rashin fahimta ta yatsine fuska cikin son karin bayani.
“Wai fa zuwa tayi tana sakin wasu banzayen kalamai kafun daga karshe ta dire da cewa wai ni take so ki ji fa wata wauta da kalar hauka”.
Fakare tayi tana kallonsa tana karantar yanayin sa mamaki ya cikata ta yarda Mufeeda ta iya jefa kanta son wannan mugun mutumin mara tausayi da imani ita kam bata ga abin so a jikinsa ba bata ga abin burgewa a gareshi ba har da Mufeeda zata zo tana fada masa tana son sa har ya samu damar ci mata mutunci ya wulakanta ta ko da yake kila kudin da yake dashi ya ruɗeta in kuwa haka ne Mufeeda bata yi wa kanta adalci ba da tayi sake ta fada motar kwadayi ta dire a tashar wulakanci da cin mutunci.
“Ni ban ga abin ta da jijiyoyin wuya ba don tace tana son ka ai ta dace ace kai ma ka anshi son da take yi maka duk macen da zata iya zuwa ta ce tana son ka ai bata cancanci wulakanci da tozaryawa ba duk da dai ku mafiyawancin maza haka kuke in har kuka ga mace ta mutu akan son ku shikenan kun samu hanyar wulakanta ta da cin zarafin ta iri-iri”.
Murmushi yayi lokaci guda kafun ya motsa laɓɓansa.
“Bana tunani haka zata kasance tsakani na da ke Areefa so daya nake yi kuma akan ki yake bana zaton akwai wata mace da zan so bayan ki akan ki na fara so kuma akan ki zan gama so ki san wannan”.
“Uhmm haka dai kace aiku dama haka kuke maza akan mace akwai iya dadin baki musamman in duniya na yi muku biyayya ba abin da ba za kuyi wa mace ba”.
“Areefa na lura kamar kina goyon bayan Mufeeda da ne ko baki jidadin abin da nayi mata ba”.
“Ko daya wallahi amma dai ka sani mace mace ce ko min lalacewarta don haka ka kula mace ba yar wulakanci bane ita mai daraja ce da kima duk da dai wasun mazan ba su dauki mace a bakin komai ba sun mai da ita kamar riga lokacin da suke ra’ayin ta za su saka ta da sun gama kuma su cire su ajje ita da banza duk daya”.
Mikewa tayi tana mai daukar jakarta ta dubi Dr.Erena da ya saki baki yana ta faman murmushi idanuwansa akanta kafun ya mike shima.
“Ya haka Areefa ina zaki daga zuwanki kuma Please ki zauna mana akwai maganar da nake so muyi dake mai muhimmanci ce”.
“At this Time bana tunanin zan iya zama kuma ina da abin yi gaskiya”.
“Please mana Areefa”.
Juya idanu tayi kafun ta dube shi cikin gyaɗa kai ganin haka ya sanya shi komawa ya zauna yana mata nuni da ta zauna ita ma ba musu ta zauna yana ma kallonta kallo na sosai da sosai kafun ya ja mumfashi.
“Areefa maganar gaskiya ya kamata ace kin ce wani abu akan alakar dake tsakaninmu ya kamata ace kin motsa motsawarki kawai nake buƙata a yanzu”.
Ci rashi bawa zancen nashi muhimmanci ta dubeshi kafun ta motsa laɓɓanta cikin ɗacin zuciya
.
“Ina jin ka me kake nufi?”.
Sai da ya sosai ƙeyarsa kafun ya saki murmushi na sosai da sosai.
“Maganar aure mana ya kamata ace mun tsayar da magana a wannan lokacin…”.
Da sauri ta daga masa hannu tana mikewa kan kafafuwanta zuciyarta take ji tayi wani bugawa da tashin hankali mai girman gaske jin zantukan nashi take yi kamar saukar aradu ƙwanyarta taji tana juya a hankali ta dube shi.
STORY CONTINUES BELOW
“Please ka bari za muyi waya in na koma gida kaji komai zai yi settling a cikin kan kanin lokaci”.
Tana gama fadin haka ta fice daga Office din cikin sauri kamar wacce zata kifa haka take ji komai taji lokaci guda ya canza mata da tashin hankali mai girma kunnuwanta take ji ba za su iya daukar kalamansa ba masu dauke da kunci da bakin ciki tafiya take yi har ta sauka kasa ta isa in da sashin ta yake komai ta kammala a hanzari ta zare key din motarta ta fice daga cikin reception din tun kafin ta isa in da motar ta take tayi mata key ta buɗe baya ta isa ta shige ta haɗe kanta da sitiyari tana mai da numfashi a hankali kanta take ji yana sarawa da karfin tsiya kamar zai rabe gida biyu sai da ta shafe lokaci mai tsayi kafin ta yiwa mota key ta fizge ta cilla ta saman titi ta shiga zabga gudu kamar wacce zata tashi sama burin ta kawai ta ganta a gida ko ta samu tayi saita kanta sosai take jin tashin hankali na tunkaro ta sosai take jin ranta na kara baci duk lokacin da suka hadu da Dr.Erena don dole kawai take zama dashi da umarnin Hajiya Layla.
*********
Tun da ya doso Muhabbir Coffee yake jin gabansa na yankewa yana faduwa lokaci lokaci hakan na karuwa sosai yaji a jikinsa akwai abin da ke kokarin faruwa dashi.
Parking yayi bayan yashiga wajan yayi oda din duk abin da yake bukata ka kawo masa a hankali yake kai Coffee bakin sa yana kurba har zuwa lokacin jikinsa bai daina sanar dashi wani abu dake kokarin faruwa dashi ba tun yana daukar lamarin da sauki har yaji zuciyarsa tana kara azalzalarsa da yabar wajan A hankali ya mike ya dauki wayarsa da key din sa bayan ya biya kudin abin da yayi oda ya doshi in da motarsa take ajje ya bude ya shiga ya zauna bayan kulle yana kokarin yi mata key yaji an dorasa masa bakin bindiga ta bayan kansa zare idanu yayi a firgice yana kallon mutane biyun da suke bayansa zaune ta glass din gaban motar.
“ja motar muje”.
Daya daga cikin su yace dashi murya a buɗe gabadaya kamar saukar markaɗe.
Jikin rawa ya shiga yi jin abin da suka ce dashi ware ido yayi yana kokarin juyawa ya dube su laɓɓansa na motsi daya daga cikinsu ya daka masa tsawa cak! ya tsaya da maganar da yake kokarin yi jikin sa na ƙyarma sai faman ambaton sunan Allah yakeyi.
A hankali yayi wa motarki bayan ya yi ribas ya fice daga cikin wajan. In ba wai kasan abin da yake faru a cikin motar ba ba zaka iya cewa komai ba dubin gabadaya glass din motar mai duhu kuma a zuge yake.
Suna fita daga cikin wajan suka shiga nuna masa hanyar da zai bi a hankali a hankali suke tafiyar har suka fara ficewa daga cikin gari nan Alhaji Abdulwahaab ya kara ruɗewa ganin suna tun karar daji da sauri yayi kokarin taka burki amma jin bindiga a keyarsa ya sanya shi kara wuta cikin hanzari jikinsa na rawa domin ya tabbatar wadannan mutanan barayi ne ko kuma yan satar mutane.
Daji sosai suka yanka sai da yashiga cikinsa sosai sannan suka ce yayi parking a hanzarce yayi sannan ya juya yana kokarin kallon su daya daga cikin su ya buga masa kan bingida a gefen fuska wanda hakan ya sanya shi sakin kara gami da yin lif! jikin kujera kamar wani mara lafiya wajan da suka dokar masa lokaci daya ya fara fiddo jini.
Gabadayan suka buɗe suka fito dayan su ya ja kofar gaban ya buɗe ya fizgo Alhaji Abdulwahaab zuwa waje ya baje akasa kansa na buguwa da gefen motar wata irin kara ya saki gami da ambaton sunan Allah numfashi kawai yake ja a hankali gabadaya ya gama shiga tashin hankali mai tsanani dagowa yayi cikin matsanancin yanayi yana duban su ganin su yake yi suna kasuwa bibbiyu idanuwansa suna lumshewa a hankali yana buɗe su bai ankaraba ya sake ji an kai masa wani wawan naushi a fuska an daki goshinsa da kan bindiga nan ya baje a sume bai sake sanin in da kan sa yake ba.
Duban juna sukayi suna masu sakin wata mahaukaciyar dariya kafin su tafa hannayensu a hankali suka fara tafiya suna ficewa daga wajan shikuwa Alhaji Abdulwahaab bai ma san in da kan sa yake ba.
Ya dauki lokaci mai tsayi can wajan magrib sanyin yamma ya kaɗashi ya farka a wahale yana kokarin buɗe idanuwansa amma jin su yake yi kamar ba a jikinsa suke ba dafe kan sa yayi sosai yana mai kara runtse idanuwansa lokaci daya ya buɗe su duhun daren da ya fara shigowa shi ya an karar dashi da sauri ya tashi zaune ya juya yaga motarsa hannu ya saka ciki Aljihu wayarsa yaji da sauri ya zaro yana dubawa 6:50pm shida da minti hamsin ya gani a hankali ya shiga kokarin tashi amma tsamin da jikinsa yayi ya hana shi kokarin da yake yi rarrafawa yayi har ya isa wajan motar ya dafata sannan ya mike yana faman cizon laɓɓansa buɗe motar yayi ya shiga a hankali yana faman numfarfashi yakeyi zama yayi sosai yana jin yarda bayansa ke amsawa da ciwo mai tsanani cikin dauriya yayi wa motar key Allah ya taimake shi ta ta shi ajiyar numfashi yayi mai karfi a hankali ya shiga yin ribas har ya juya hanyar da zata fiddo shi daga cikin daji.
Sosai ya fita daga cikin daji ya shiga gari daidai wani Super-Market ya tsaya ya daga kansa sama daidai wani shago da yake zaton clinic ne haka kuwa akayi KAMALA CLINIC ya ga an rubuta da dan hanzarin sa ya buɗe ya fito ya doshi wajan bayan yayi sallama ya shiga nan ya yi musu bayanin abin dake faruwa wani daga cikin ma’aikatar wajan ne ya zo yayi masa komai da ya dace har da allurai sai daya sha
Kafun ya fito ya dauki hanya zuwa gida zuciyarsa cunkushe da godiyar Allah da lamarin ya tsaya a haka ba tare da sunyi masa wata illa sosai ba.Wata alkarya.
10-July.
Ihu sukeyi gabadaya sun karaɗe wajan sai cukuikuye junansu sukeyi a waje daya cikin matsanancin tashin hankali kallo daya zakayi musu ka tabbatar suna cikin tsaka mai wuya gabadaya sun jeme sun yi baki kayan jikin su gabadaya sun gama fita hayyacin su wasun suma ko kallabi babu akan su.+
Janta yake yi yana faman dukanta da bakin bindiga itakuwa sai turjewa take yi tana janyon yan’uwanta suma sunan janta kallo daya zakayi mata ka gane tana cikin galabaitaccen yanayi idanuwanta gabadaya sun gama rufewa kawai fizgar ta yake yi har zuwa lokacin da ya fidda ita daga cikin wajan sai numfarfashi take yi can ciki tsakiyar rana yaja ta ya watsar da ita ga ranar ta kwala sosai kamar zata darkar da mutum.
A hankali ta shiga kokarin buɗe idanuwanta jin zafin ranar na dukanta ta ko ina gashi ba wata wadatacciyar suttura bace a jikinta wando ne dogo sai riga ita ma doguwa iyakar gwuiwa da guntun hannu amma yanayin da kayan su ka koma sai ka ka rantsee yagaggune daga bola aka tsinto su kanta kuwa ba kallabi wasu hawaye suka zuba daga cikin rufaffun idanuwanta kafin ta tashi zaune tana faman cizon laɓɓanta.
Wani irin murɗawa taji mararta tayi lokaci guda kamar yan hanjinta da mararta za su zazzage wata kara ta saki mai razanarwa kafin ta kai hannayentala duk biyun cikin galabaitaccen yanayi tana dafe wajan zubewa tayi gabadaya a kasa tashiga murkususu da shure-shure kamar kazar daka yanka take kokarin mutuwa cikin lokacin kankani ta fice daga hayyacinta ko motsi bata yi kafin can kuma jini ya balle ya shiga kwararowa ta kasanta mai dauke da gudaje-gudaje numfashi take ja jin komai na duniyar take kamar ba nata ba duniyar take ji tana canza mata da tashin hankali mai tsananin gaske zafin da take ji tun daga cikinta har zuwa mararta ya tabbatar mata da lokacin mutuwarta yayi sosai taji dumin da ke bin kafafuwanta hakan ya kara tsinkar mata da zuciya.
Tsaye yake kanta yana kallon duk abin da ke faruwa amma ko motsi bai yi ba sai faman murmushi yake yi kafin ya juya ya dubi gabadayan alkaryar tasu sannan ya juya ya dubi sauran yan’uwan nata da ke kargame ko wacce da sakar a hannayenta da wuyanta sai faman zubda kwalla suke yi suna gunjin kuka hannu suke miko mata amma ina bata san ma a ina take ba lokacin da suka lura da abin da ke faruwa da ita ba su san lokacin da suka kara sautin kukansu ba cikin matsanancin yanayi.
Bindigar da take hannunsa ya daga ya saita in da suke ji kake daram! ya sake nan take albushiri yayi fitar burgu ya sauka cikin wajan a saitin goshin daya daga cikin yan matan wani razanan nan ihu ta saki lokacin da kanta ya tarwatse kwanya ta watse duk ta bata yan uwanta kafin gangar jikinta ya zube kasa warwas.
Ganin abin da yake faruwa ya ka sanya su cikin matsanancin rikici lokaci guda duk su rikice suka shiga kai kawo cikin wajan ko wacce hannunta akanta suna faman kankame junansu.
Ihun da yake tashi ne a wajan yana ansa kuwwa ko ta isa ya sanya shi dago tambol din sa ya fito fuskarsa a murtuke kam! ya tsaya a tsaye yana faman bin filin wajan da kallo kafun ya sauke wajan yan matan da yake hangowa sun faman rusar ihu wata razananniya tsawa ya doka lokaci guda sautin tsawar ya karaɗe wajan ƙafin ya shiga takawa cikin matsanancin zafin rai idanuwansa da wani irin yanayi na tsananin rashin imani da tausayi idanuwansa na kan su sam bai lura da abin da yake gabansa ba sai da yaji yaci karo da mutum sannan ya tsaya yana duban wajan shame ya ganta ko alamun rai babu a jikinta da sauri ya daga kansa yana duban sa.
“Ita kuma wannan fa?”.
Ya tambaya cikin yanayi na halin ko in kula kafun ya sake dubanta iya zuwa lokacin tana fidda numfashi a hankali hankali.
“Shiga nayi na bukace ta shine ta saka min hakora a jiki”.
Ya fadi yana mai nannaɗe hannun rigarsa wani wawan cizo ne ya bayyana har fatar wajan ta dauke sosai.
STORY CONTINUES BELOW
Ji kake kau ya dauke shi da mari kafi ya tsartar masa da yawu cikin tsananin dacin rai.
“Mai ya hanaka rabata da filin duniyar nan tun da har zata yi maka taurin kai har haka”.
Yana gama fadin haka ya zaro wata karamar bindiga fisto ya saita ta lokaci guda ya sakar mata albushiri a kai shurawa daya tayi daga shi bata sake yin wani ba.
“Wa ya fada maka ana jayayya da su ai duk wacce ta tsaya tsaiko a tsakanin ku kawai dauki ranta don ba su da wani amfani a gare mu”.
Ya fadi yana mai tsartawa gawan dake yashe tana zubda jini daga kanta yawu kafun ya juya cikin takun isa yana mai juya bindigar dake hannunsa har ya isa garesu tun da suka ga ya tunkara garesu suka shiga haɗewa waje daya suna cakume junansu numfashin su na fita da sauri-sauri cikin matsanancin faduwar gaba da tsoro mai tsanani jikin kofar ragar da aka rufe su da ita ya tsaya yana mai yawatawa da idanuwansa akan su kafin ya saki wata mahaukaciyar dariya mai matukar razana su ya shiga sakin albushirin bindiga wajan na ansa sautin fitar albushirun hakan ya kara firgitar da su kafin lokaci daya ya daka musu tsawa da ta sanya su yin shiru wasun su har da sakin fitsari.
A hankali ya shiga kaucewa daga wajan yana faman cilla bindigar sama yana caɓewa har ya isa ga tambol din sa can nesa ya hangota tana ta faman kyalaye amai kamar zata amayar da kayan cikinta gabadaya ta gama galabaita numfashi kawai take saki cikin tsananin zafi da raɗaɗi gabadaya jikinta take ji ya canza komai nata jin sa take yi kamar ba nata ba a hankali ta shiga kokarin tashi amma jirin da taji yana dibarta ya sanyata komawa tayi zaman daɓaro idanuwanta sai faman shatatar da hawaye sukeyi gabadaya ta gama figewa ta rame kamar ba ita ba idanuwa duk sun zurma ga wani mahaukacin duhu da tayi kamar wacce ta shekara ba ta ga ruwa ba.
A hankali ya tako ya iso gareta yana bin ta da kallo kafin ya dan ranƙwafa sosai ya tallabo haɓarta a dan razane ta dago kai ganin waye ya sanya ta buge hannunsa tana mai jan jikinta can nesa dashi zuciyarta na kara cushewa waje daya ta wani tarin bakinciki da takaici mai yawan gaske kallonsa take yi kallo na tsana da kiyayya fuskarta a murtuke sai faman huci take yi ji take kamar ta cafko shi ta shake shi ya mutu ko ta huta da wannan bakar izaya da ukuba da take ciki a filin duniyar nan bata san yarda zata kira wannan lamarin ba bai ta san mai zata ce da wannan al’amarin ba bata san ya zata kwatanta rayuwar kaskanci da take cika ba ta rashin yancin da mutunta kallon kanta take yi a wata banza wacce bata da saura galihu tun da ta fado filin duniyar azzalumin mara imani wanda ba abin da ya saka gaba sai daukar rai da bai ji bai gani ba.
Murɗawar da cikinta yayi ne ya sanyata dafewa tana runtse idanu hadi da tura laɓɓanta duka cikin baki tana cizawa wata irin azaba ce taji tana kartar mata ciki da bayanta ji take yi kamar zata mutu don azaba da take ji hawaye suka shiga zuba wanda bata san ma suna zuba din ba kawai dumi take ji a sama kuncinta har zuwa kirjinta buɗe idanunta tayi ganin mutum tsaye akanta ya sanyata saurin matsawa tana watsa masa wani matsiyanci kallo mai cike da tsana da kiyayya mai girman gaske kafun ta shiga motsawa laɓɓanta suka shiga motsi hawaye sai faman ambali suke yi.
“Ka sani wannan dariyar da kake yi akwai ranar da za ta zame maka kukan jini, karka yi tunanin wannan rashin imanin da kake nunawa ba ranar da zai zo karshe, karka yi tunanin cin zarafi da keta haddi da kake yi ba zai zo karshe ba, ka sani duniyar ma gabadaya sai ka barta kamar yarda kake zama SILAR AJALI ga wasu to ka tabbata yarda ko wani dan aike yake zuwa ya dawo to ka tabbata kai ma dan aiken ka yana nan dawowa kuma duk abin da kake aiken sa yayo kai ma sai ya zo ya yi akan ka”.
Numfashi taja tana jin yarda zuciyarta ke zafi da raɗaɗi da tashin hankali mai girman gaske.
“Ka kashe mani iyaye na ka rabani da gari na ka keta min haddi ka zaja min UKU BALA’I bala’in da bai taba rabuwa dani ba ka ja zamanin bala’in da ba zai taba canzawa ya koma alheri da yake kamar da ba amma ka sani shi sharri dan aike ne wallahi”.
STORY CONTINUES BELOW
Mikewa ta shiga kokarin amma har lokacin jiri take ji wani fizga taji yayi mata ya watsar da ita kasa ya taka mata ruwan ciki da kafarsa mai dauke da wani kafcecen takalmi wani irin nishi ta saki hawaye suka zubo mata idanuwanta a runtse.
“Ina so ace na mutu amma abu daya zan roki Allah ya banni nayi rayuwa har zuwa lokacin da zan ga karshen ka zan fi kowa farin ciki da murna a filin duniyar nan mutane da yawa na san za suyi farinciki duk da dai baya in ta tafi bata taba dawowa amma ina so ace mutane da ka saka wa ciwon rai ka saka su a BALA’I zan so ace sun ga karshenka Malik”.
Buɗe idanu tayi tana jin yarda zuciyarta take kara kekeshewa da rashin tsoronsa yinkurawa tayi zata tashi tana mai ture kafarsa daga ruwan cikin ta.
Duban gawarwakin da ake kokarin dauka guda biyu na yan’uwanta tayi kafun ta dube shi fuskarta da murmushi mai ciwo.
” ‘Ya’ya Mata kayi wa haka ka sani komin daren dadewa wallahi sai hakkin su ya hanaka sukuni ba ganin ka na shiga rigar mutanan adalci kana nuna kai na Allah ne kana yaudarar mutane ta wannan hayar Uhmm…”.
Taja numfashi kafin ta girgiza kai.
“Lokaci ne ba wanda yake hanyar sabawa Allah ya samu nasara komin lokacin kuwa da ya dauka yana cin nasara to akwai RANA DAYA tak! da zata zo ta rushe duk wannan nasarorin da yake zaton ya samu”.
Sosai ya har zuƙa jikinsa har rawa yake yi wani wawan cafka ya kai wa wuyanta nan ta shiga kakari idanuwanta sukayo waje sun kaɗa sunyi jajir wani huci ya shiga fetar wa kamar zai ci babu kafin yayi cilli da ita can gefe guda ta hadu da wani katon dutse ta gaban goshinta lokaci guda gun ya tsage ya shiga zubda jini sosai ta ji zafin wajan amma ba ta nuna hakan ba tashi tayi ta sanya hannunta ta na dauke jinin a hankali a ko ina na sashin jikin ta azaba take ji amma jarumar zuciyarta ta kiyin rauni.
“Kisan kai da kakeyi ka dauka kuma aikin yi a filin duniyarka na rantse da Allah wata rana kai ma zaka mutu mutuwa kuwa ta wulakanci sai ka raina kan ka BAR GANIN ALLURA wallahi karfe ce bar ganin abin da kake yi kamar abun burgewa ne wallahi kai ma sai wannan hanyar ta zama silar barinka duniyar nan”.
Kallonta yake yi da wani irin yanayi na mamaki tun da yake bai taba gani mace mai taurin rai kamar ta ba tun da yake bai taba ganin an kwaso yan mata an kawo masa ya samu mai taurin rai haka ba har zata iya dubansa ta gaya masa magana son ranta ba tare da fargaba ko tsoro a fuskarta ba gyaɗa kai yayi kafin ya bar wajan yana faman dukan iska.
Ita kuwa kuka ta saki mai taba zuciya da soya ruhi sosai ta durkushe hannayenta saman kanta ji take yi kamar ta hadi zuciya ta mutu ta bar wannan duniyar komai na cikin ta ba dadi sai yau ta kara tabbatar da cewa DUNIYA BA ALJANNA BACE ta tabbata bakomai cikin duniyar na sai ta shin hankali da rashin imani kaicon wannan rayuwa kaicon wannan zamani.
*****
Numfashi take ajjewa kyar idanuwanta sun kaɗa sunyi jajir hannunta dafe da cikinta da take jin sa yana ta faman juyawa sosai ta shiga tashin hankali sosai tayi kuka kuka wanda har zuwa yau take yin sa kuma bata san ranar daina shi ba ta shiga kunci da ukuba da bala’i ta sani bata da wata dama da za ta sake zuwa mata ta dadin rayuwa ta sani ita kam rayuwarta ta gama karewa tunda ta fado hannun wadannan azzaluman mutanan maras imani da tausayi maras ganin darajar ‘YA MACE ba su dauke ta a bakin komai ba ‘Ya’ya Mata sun mai da su kamar Toilet din su na duk lokacin da suƙa bukata za su je su biya bukatar su ko hali ƙaƙa ne ba sa ganin darajar koma waye bata san wasu irin mutane ba ne su bata san wata alkibla suke bi ba har ga Allah zata iya cewa ba musulmai bane domin bata ganin su da suffar ni’imar musulci ba duk da dai suna ikirarin su din haka amma ita kam bata taba yarda ba.
STORY CONTINUES BELOW
Nisawa ta sake yi Hawaye na kwaranyo daga idanuwanta kamar daga sama taji ana dauke mata su firgigit tayi ta dawo hayyacinta dubansa tayi kafun ta kau da kanta zuciyarta nayi mata zafi da raɗaɗi ji take yi kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu da wannan bala’in da take ciki bata son ganinsa ko muryarsa bata son ji domin ganinsa kamar ganin bala’in rayuwa ne.
Murmushi yayi yana sake kai hannunsa bisa kuncinta.
“Ki yarda dani ki zauna dani mu rayu tare dake a filin duniyar nan ki yarda mu zama abu daya har gaban abada ni dake da abin da ke cikin ki”.
Wani irin zillo taji cikinta yayi kafun idanuwanta suyo waje sosai fargaba da tsoron da take ji a zuciyarta akan abun da take zargi shi ne ya tabbata tabbas haka ne maganar sa gaskiya ita kanta ta sani akwai abin da ke damunta sosai taji a jikinta komai ya canza sosai take jin motsi a cikin cikinta runtse idanuwa tayi duniyar taji tana juya mata kanta yana komawa kasa kafafuwanta na dawowa sama zuciyarta take ji tana yayyagewa muryarsa da bakaken kalamansa take ji suna ansa kuwwa akan ta da cikin kunnuwanta tartsatsi da rugugi take jin kwanyarta nayi.
“Ban san ta zan sanar dake ba amma ki sani ina cikin yanayi na bukatarki a gareni ina so ki kasance dani har karshen numfashina sosai nake ji a zuciyata sosai da sosai nake jin zuciyata ta baki wani fili mai girma kina rayuwa ki sani ban taba kaunar wata mace ba ban ta taba son wata mace ba iyakata da mace na biya bukatuna da ita domin ni ban dauki mace a abun darajawa ko girmamawa ba amma akan ki ina ji a zuciyata ke ta daban ce”.
Numfashi ya ja mai tauri kafun ya kureta da idanuwansa masu firgitar da ita a ko wani lokaci.
Bata san ya zata dauki wannan lamarin ba bata san a wani mizani zata ajje shi ba sosai take cikin wani mataki na rashin nasara a rayuwa sosai ta hango kaifaffan ALKALAMIN ƘADDARA ya daura tsininsa akan rayuwarta yana rubuta rubutun da take gani a matsayin ajalinta a duniyar nan rubutun da take ganin shine sanadin afkawar wannan rayuwar mai cike da tashin hankali da bakin ciki da ukuba sai yau ta kara tabbatar wa bata da sa’a ko daya a duniyar nan bata da sa’a matsayinta na ‘ya mace bata da duk wasu ababe da mace zata yi alfahari da shi a duniyarta komai ya ruguje komai ya lalace wai ita ce yau dauke da juna biyu, juna biyun da ba ta hanyar aure ta same shi ba junan biyun da ya kasance ta same shi ta hanyar bala’i da masifa da jafa’i juna biyun da zata iya kiransa da shine ajalin rayuwarta
.
‘Yaa Zuljalali wal-Ikram’.
Ta ambata a zuciyarta da take ji tana yayyagewa tana fadowa kirjinta da tashin hankali mai girma ga wani abu mai girman gaske da take jinsa tsakanin makoshinta da kirjinta ya tsaya cak!.
Bata san me zata ce ba ita dai ta san rayuwarta ta kare rokon Allah take ya dauki ranta a filin duniyar nan rayuwar take ji gabadaya ta ishe ta bata son ta bata son komai na cikinta komai baki ne take gani bata burin sake maimaita WATA RAYUWA a duniyar nan burinta kawai numfashinta ya dauke a daidai wannan lokacin lokacin da take ji yafi komai zama bala’i a gareta.
Hawaye suka cika gaba da zuba a idanuwanta shi kuwa sai hannu yake kai wa yana dauke mata su.
“Ki ce wani abu ina son abin da yake cikin ki ina kaunarsa har dake kan ki ki yarda mu rayuwa a inuwa daya a tare har zuwa numfashin mu na karshe”.
Daga idanu tayi ta dubi sashin da yan uwanta suke gabadaya sun gama mutuwa yawancin su da sunyi musu fyaɗe suke kashe su wasu kuma in suka ki yarda da bukatarsu suke kashe su su jefa gawarwakin a ruwa tana kallo bata da damar hanawa a gabanta sun kamo mutane masu yawa suna yin yarda suke so da su tana kallon yarda ake nunawa yan uwanta mata zallar rashin imani da tausayi amma bata san yarda zata yi ba agabanta an kashe har bata san a dadi ba an sha daukar bindiga ana bata ko wuka da sunan ta kashe wani amma bata tunanin zuciyarta zata iya zama mara imani da tausayi har haka yan uwanta musulmai ake kashewa har ake bata damar ta kashe batare da laifin komai ba.
STORY CONTINUES BELOW
Ruwan hawaye suka zuba mataa ta daga kai can nesa ta hango Baaba BG na kallonta tun da ta zo shi kadai ne mutumin da take kallo a mutum wanda ba irin su ba tana zaton shima kamar sato shi akayi kamar yarda suma aka sato su bata taba jin yayi magana ba bata taba jin ya buɗe baki ya furta kalma daya ba tausayinsa take ji mutum har mutum amma izayar da yake sha in da wahala na kisa da tuni ya mutu sosai ta fuskanci hakan bai son aikin da suke saka shi a lokuta da dama tana kallon yarda Malik yake basu umarnin aiwatar da wani aikin na mugunta amma shi sam ba yayi Malik lokuta da dama ya sha daura masa bindiga da sunan zai harbeshi amma sai ya fasa amma fa izaya ya na shanta ko yanzu da yake cikin razana tsaye sai faman gumi yake yi idanuwansa a sama yana kallon ranar da ta kyalla sosai idanuwansa sai faman zubda hawaye suke yi.
Malik ya sanya shi akan idonta yake bashi wannan azabar don kawai yaki yin mubaya’a akan abin da ya saka shi…
Karar albushirin da yaketo cikin dajin ne ya firgita su da sauri Malik ya mike yana kai kawo a tsakiyar wajan ita kuwa gabadaya ta firgice tashima ya gagare ta.
Yaran Malik ne taga suna ketowa kan baburansu a guje kamar za su tashi sama gabadaya wajan ya kaure da karar albushiri sosai da sosai Malik ya nufi cikin Tamfol din sa cikin hanzari lokaci guda kuma ya fito jikinsa da wata riga baka wulik mai kauri ga wasu igiyoyi da suke barbaje a jikinta da hanzari ya keta hanyar da ya ga yaransa na shigowa gudu yake yi kamar zai tashi sama can nesa ya hango bataliyar sojoji sun tun karo wajen bindigogin sa kirar Ak47 ya ya cilla sama tare da caɓe su a hannayesa ya shiga gudu yana sakin wuta ko ta ina cikin dajin sai da yayi tafiya sosai yana zubda sojojin da suka tunkaro alkaryar tasa albushiri ko ta ina amma shi ko a jikinsa domin albushiri da ta fado kansa yake watsewa kasa batare da ya bula jikinsa ba sai dai rigarsa ta dau hayaki a daidai inda albushirin ya sauka sosai ya cigaba da tafiya yana kallon yarda ake ta kashe masa yara hakan ya kara harzuka shi matuka lokaci guda zuciyarsa ta shiga tururi fuskarsa na kara hautsinewa idanuwansa suka kaɗa sukayi jajir a daidai lokacin da ya tun kari inda yake hango bataliyar sojojin adaidai kuma lokacin albushirin bindigun nasa suka kare watsar da su yayi tare da yin wata uwar sufa ya yi kasa ya tura hannayenssa cikin ciyayin da ke wajan lokaci guda ya dago wata bingida mai saffurin mai jigida ya cilla sama kafin ya sake mai da hannunsa cikin ciyayin ya fizgo albushiri mai matukar tsayin gaske ya mike kan kafafuwansa da wani irin karfi gaske domin inda yayi tsalle ya dire sai da ciyayin wajan suka yi sama bindigarsa da ta shilla sama a daidai lokacin tayo kasa da hannu daya ya caɓe ta tare da zura mata albushirin nan ya shiga sakin wuta ko ta ina yana faman juyi kamar wanda yake amfani da wani maganakisun majajjawa.
Abin da Malik bai sani ba shine sojojin sosai suka shirya domin kuwa ƙawayansu kayi wa dajin can bangaren alkaryar tashi tuni sojojin sun isa cikin ta suka shiga sakin wuta ga duk wani yaransa sosai yan matan suka firgita suka shiga ihu saboda sautin tashin albushiri da suke ta faman ji ko ta ina ba su tsinke da lamarin ba sai da suka mazaje na bajewa a kasa matattu Mubeena dake cikin Tamfol din Malik tana kai kawo hannuwanta saman kai sai faman du’a’i take yi da fatan Allah yasa masu Ceton Rai ne a garesu.
Wani albushiri ya ratso ta ciki wajan ya gogi kafatarta wani zafi ne mai cike da raɗaɗi ya ziyarce ta kwalla kara tayi da kafin gaske tare da zubewa a kasa ji take yi kamar hannu aka fizge daga jikinta zafin jinsa tayi a ko ina na sashin jikinta kararsa kuwa amsa kuwwa yayi cikin dodon kunnuwanta a hankali ta shiga jan numfashi da take jin sa kamar zai fice daga jikinta saboda tsabar azaba da raɗaɗi runtse idanuwa tayi a daidai lokacin aka banko tamfol din aka shigo sojoji ne guda biyu ko wane dauke da hula irin ta su ta sojoji hannayen su dauke da jibga jibgar bindigogi a resting din ta sukayi lokaci guda cikin cikin raɗaɗi ta buɗe idanuwanta ta kalle su lokaci guda ta mai da ta rufe tana jin suna surutunsu akan ta amma ko motsin arzuki bata iyayi ba daya daga cikin su ne ya lura da kafataɗarta da sauri yayi wa dan’uwansa alamu hakan ya tabbata masu alburushin ya same ta da sauri suka cinciɓe ta sukayo waje da ita gabadaya wajan ya zama fili sai gawarwaki dake baje can gefe kuma yan matan ne aka tare su waje guda sai faman rusar kuka suke yi gabadaya sun gama ficewa daga hayyacin su can suka nufa da Muneeba yan uwan naganinta da sauri su suka taso suka ansheta ganin halin da take ciki ya sanya su kara sautin kukan su kukan nasu ya farfado da ita daga sumar da tayi na wucin gadi a hankali ta shiga buɗe idanuwanta wanda hasken rana ya saito fuskarta komar da su tayi ta rufe kafin ta ciji laɓɓanta ta sake buɗe su sosai cikin karfin hali sosai ta shiga juya idanuwan nata tana kallon yarda sojoji sukayi wa wajan ƙawanya gabadaya numfashi taja mai tauri kafun ta dubi wanda suka riketa ganin yan uwanta ya sanya ta rushewa da wani irin kuka mai tsuma rai sosai da sosai jikinta har karkarwa yake nan suka sake buɗe babin kuka a tsakanin su sojojin sai bin su da kallo suke yi kafin su cigaba da shiga duk wani sashi na wajan.
A bangaren Baaba BG kuwa lokacin da sojojin suka fara sakin alburushin ba zato ba tsammani yaji saukarsa a hannunsa na hagu da hanzari cikin wahalallen yanayi ya saki wani nishi kamar ransa zai fita ya saukar da kansa daga kallon ranar da yake yi wanda suka gama wahaluwa jijiyoyin kansa sun fito sun burɗun-burɗun da su kwayar idanuwansa sai faman zubda ruwa suke yi.
Zubewa yayi a kasa yana kai hannun damarsa yana rike da hagun cikin wani irin yanayi mai matukar wahala sosai yaji kansa da duk jikinsa sun ansa da alburushin da ya fasa masa hannu runtse idanunsa yayi sosai kafun ya bude su dishi-dishi yake gani duban hannunsa yayi da yake ta faman zubda jini dafe wajan yayi sosai amma hakan bai hana jinin cigaba da zuba ba da hanzari ya shiga kokarin mikewa jiri na dibarsa sautin albushiri ne kawai yake ji ta ko ina zuciyarsa yaji ta kawo masa wani karfi mai girma gaske da hanzari ya tashi yana tangaɗi ko gani sosai bai yayi ya yanki daji yana jan jikin sa zafin raɗaɗi sai kara hauhawa yake yi tafiya ya yanka sosai sai yayi ta har kafafuwansa na kokarin kasa daukarsa amma zuciyarsa bata yi rauni ba karfi yake ji yana kara zuwa masa tun yana cijewa har ya fara gudu yana yankar daji numfashin sa na sama da kasa tafiya mai nisa yayi cikin wannan matsanancin halin har sai da sautin alburushirin dake tashi ya ragu yana jiyo sa daga can nesa bai ankara ba ya gashin gaban wani tafkeken kogi dake gudu cak! ya tsaya da tafiyar da yake yi yana mai da numfashi kafin ya zube kasa yana mai lumshe idanuwansa ko ina na jikinsa yake ji yana masa wani irin ansawa da ciwo mai tsanani buɗe
idanuwansa yayi ya kalli hannun nasa da yake digar da jini ganin jinin ya fara bushewa hakan ya tabbatar masa ba karamar tafiya yayi ba ga hannunsa ya kumbura sosai ko ya ya taba shi zafi da radaɗi yake jin suna ansawa a jikinsa.
A hankali ya tashi yana tangadi ya tunkari kogin sosai idanuwansa suna lumshewa bai san lokacin da ya isa bakin kogin ba har ya tsoma kafafuwansa kawai ji yayi ruwan ya fizgeshi da wani irin karfi ya antayashi ciki gudu kogin ya shiga yi dashi ba k’ank’autawa shi kansa bai sam ba a wani hali yake ba sosai ya mika dashi hanyar da kogin yake bi yana faman sama da kasa dashi.
A bangaren su Malik kuwa abu ya kacame fada sosai ake yi ba abin da ke tashi sai sautin albushiri gawarwaki kawai zaka ke gani ko ta ina ta sojoji da ta alkaryar Malik wanda suka rage kalilan ne wuta kawai Malik yake tafiya yana yi idanuwansa a rufe ba zato ba tsammani yaji saukar wani katoton abu ya daki goshinsa ya cilla dashi can gefe ya bugu ta wata katuwar bishiya mai matukar girma kafin ya sake cilla wa wani wajan can daban ya fada cikin ciyayi har sai da ya shiga cikinta sosai da sosai runtse idanuwansa yayi kafun ya bude su sun kaɗa sun yi jajir yinkurin mikewa yayi amma ina bayansa yaji yayi wani irin amsawa kamar an karya
bushesshen ice da sauri ya koma ya kwanta yana mai sakin numfashi ga wasu hawaye da suka shiga zubo masa a fuska ba kankautawa.
hannayensa duk biyun ya cusa cikin ciyayin wajan ya damka kana jin sautin yardda suke rumurmushewa da yake sun bushe wani bakin ciki yaji ya tokare masa kirji ga wani abu mai girma ya tsaya masa a makoshi da k’yar yake jan numfashi komai.
A karo na biyu ya sake buɗe idanuwansa jin motsi ta ko ina sojoji akansa sun yi masa ƙawanya sosai da sosai ko wannan su hannunsa dauke da bindiga sun saita shi wani takaici ne ya sake kume shi ya kurma wani irin razanan nan ihu da ya ansa sauti sosai cikin dajin…