UMM ADIYYAH CHAPTER 29 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 29 BY AZIZA IDRIS GOMBE

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

MUN TSAYA 

zai taba yarda ba. “Ka yi hakuri mana?” Dariya ya yi ya ce, “Ba wanda ya kai ki iya bada cin hanci, wannan idanun naki sun iya sawa ayi miki yadda ki ke so, kwana daya kacal amma! Ina ki ke so na shiga.
Idan ki ka kwana biyu nesa da ni? Za ki sa mutane su bude Kofar Extra daki kenan, Kaura zan yi.”
Dariya take yi ta ce, “Haba dai Kaura.” To shi kenan, kin dauka wasa ne ko?” Tuni ta shiga taitayinta, “A’a na isa? Na gode.” Sai kuma ta ce. “Yayyy.” Ta fada tana murna har da dan rawarta. Shi kuwa ya
shiririce cikin kallonta, yana jin wani sonta na Kara shigarsa, tana nan ‘yar dagwas da ita tamkar ya boye abarsa.

***********

Tun isarsu take Allah-Allah su isa gidan Adda Asma, amma Sai gidan wani abokinsa ya fara kai ta, suka gaisa tukuna, sannan suka wuce gidan Asman da ke (Gwamna Road).
Cikin murna sosai Asma’ ta tari Umm Adiyya. “Adda Asma’ za ki kada ni.”

ZAMU TASHI 

Shigowar Maami da Aunty A’isha Kanwar Maamin ne ya sa suka yi shiru da zancen.
“Oh ku nan ku ka yi zamanku, kun bar Yayyinku a ciki suna ta aiki.” “Maami, yanzu na shigo da Safiyya ta yi barci, a baya na kwantar da ita kenan, amma za mu fita ma.” “To maza ku yi ku zo, Asma zo ki ajiye su Goggo Amina a gida. Maimuna ta shanya su, daga bari ta je ta dawo, wai ta maKale a kasuwa. Kun san anjima lokacin kamun nan, kar ku je masu taro latti, ba dadi, in dai ku na so gobe su kawo maku amaryar
da wuri.” Oh, Maami ba sauKi, duk a cikin jiran Www.bankinhausanovels.com.ng surukar ne.” Asma’ ta fada tana dariya. “Yaran nan ba ku da kunya, maza ku bace min a nan.” “Ummu A. Ba ni Safiyyan ki je su Zubaidan na falon Abba, suna ware souvenirs ne.” Aunty A’isha ta fada tana mika hannu, don ta dauki babyn Adda Zubaida da take ta
shan barcin ta. “To.”

**************

Biki ya kankama, gida ya cika maKil! Ko ina ci ake, ana sha, ana sha’ani, da sauri Umm Adiyya ta jona wayarta a caji, ta danna kira. Kara kadan wayar ta yi, sannan aka daga. “Yi hakuri, wayar ba ta kusa ne da ni, muna cikin ribibi na ga Missed Calls.” “Ba wanin nan, kin ga dai hidima, kin share dan bataliki.” “Ni har na isa. Wallahi ba ka san yadda na damu ba, tun safe yau ban sa ka a idanu na ba, ban san halin da ka ke ciki ba, ni ma dai kawai ina nan ne, amma ba wani jin
dadin hidimar na ke yi ba.” Sautin murmushinsa ta jiyo, “Ko? To shi kenan, kin ga faduwa ta zo daidai da zama, sai ki fito mu wuce gida abin mu kawai. Dama su Anty sun taho nan.” “Ah kuma dai Yaya Zaid, ni fa wasa na kema. Za ma ki fadi gaskiya ai. Akwai wanda za ku gaisa, ki shirya ki samemu a falon Abba.” Www.bankinhausanovels.com.ng
To gani zuwa.” Ta fada hace da kashe wayar, tana juyowa ta yi ido hudu da Adda Zubaida, kunya ta ji kamar ta nitse cikin kasa.”Adda bafa…’ “A’a ni kin ji na ce wani abu ne? Tashi ki je, ko ba fita za ki yi ba?” “Baki ne fa za mu gaisa da su a falon Abba.”
“To a dawo lafiya.” Umm Adiyya ta gyara daurinta ta shafa hoda, ta dau mayafinta, hade da fesa turarenta marar Karfi sosai. Sannan ta nufi bangaren mahaifinta, cikin gidansu na Gombe, yanzu gidan ya yi shiru, ba kamar dazu da rana ba, da ake ta hayya-hayya! Abokansa biyu ta tarar tare da shi, nan ta hada masu abinci aka gaisa. Murmushi kawai Umm Adiyya ta yi, ita da idan an bar ta ma fa Yaya Zaid baida abokai, ta zaci komfutarsa ce kawai rayuwarsa, sai ga shi abin mamaki, idan ka gan shi cikin abokansa kamar ba shi ba, hira da dariya duka yi yake yi, wasu lokutan sai take tunani, wata Kila kasancewarsu tare da juna, ya Kara fiddo da asalin ko su waye ne. Duk da mutanen da suke hade a wurin, bai hana Zaid yi mata wani kallon da yake aika mata saKon ban hakuri ba, kau da kai ta yi kawai. Suna tafiya kuwa, can dare sai ga wayarsa, don haka ne tana dagawa ta ce, “Ni na sani ai, wani matsayi na ke
da shi da har zai sa a tuna da ni, idan ba na nan?’
“Tabbas kin yi gaskiya.” Zuciyarta ce ta buga, jin kalamansa. “Sau biyu kawai na ke tuna ki, lokacin da na ke ni kadai cikin kewarki da lokacin da na ke tare da sauran jama’u, wanda ba abinda na ke so illa kasancewa kusa da ke. Wannan ya gamsar da ke?”
Dama can a gamshe take da shi, ba ta buKatar bayani, domin soyayyar da Zaid ke mata ba sai ya bude baki ya fada ba, nunawa yake yi a kowani motsinsa. Don haka ba ta da komai da ya wuce na godewa Allah da wannan baiwar da ya yi mata na Www.bankinhausanovels.com.ng
samun nagartaccen miji, kamar Zaid AbdurRahman Nafada.

***********

“Ka daina kallona mana to.” Zaid ya Kara gimtse dariyarsa, “To na daina, ki fito ba zan yi dariya ba da gaske. Na ma rufe idanuna.” To ka juya ka fita tukuna.” “Oh ikon Allah, ki zo mu wuce asibiti, ki na ta bata mana lokaci, na san kuma me kika gani, don haka ki zo kawai ki karbi tukuici.” Kara leKo kanta ta yi ta Kofar bandakin. “Zan fito amma da gaske, kar kayi min dariya.” Jin motsin Kofa ta yi wannan ya sa ta tabbatar ya bar mata dakin da gaske, sannan
ta fito daga bandakin. Tun shekaranjiya ake abu daya, daga ya tasheta ta shirya su tafi aiki, ta yi juyi. “Yaya Zaid ka fara shiryawa, zan shirya ni ma, barcin bai isheni ba.” Daskarewa ya yi, ya bar duba wayarsa, “Me ki ka ce? Barci bai isheki ba? This is the
first. Ban taba sani ma barci ya dameki ba, ke da idan ki ka tashi tun asuba, ba kya komawa, maybe aiki ne ya miki yawa. Yau ki saurara haka, kar ki je ki fadi min.” Bude idanunta ta yi, dan silili tana dubansa, ba ta san ma ta sake komawa barci ba. “Ka yi wanka?”
“A’a jira na ke yi ki min. Yau da alama zan tafi na bar ki, za ki sa mu yi latti.” Breakfast!”
Rankwafowa ya yi saman gadon. Ya sumbaci goshinta, “Innayo za ta ban wani abu a kicin din, na saka miki alarm, nan da minti goma ki tashi kar ki yi latti, ina da morning briefing da Directors.” “Allah bada sa‘a.” Ta fada idanunta a rufe, ko rakiya ma ta kasa tashi tayi masa. Nannauyan barci ne ya yi awon gaba da ita. Alarm ya Karaci ihunsa ya gama. Ba ita ta tashi ba sai tara da rabi. A zabure ta yi bandaki ta yi wanka, ta shirya a gurguje cikin minti goma sha biyar, ta gama komai ta sauka. Ko karyawa ba ta yi ba, sai lokacin ta duba fuskar wayarta,
(Missed Calls) din Yaya Zaid hudu a wayarta, na Takiyya biyu, ga na Maami guda daya. Www.bankinhausanovels.com.ng
Maami ta fara kira, sannan ta kira shi. “Kin tashi kenan?” Uhm, ina hanya yanzu haka.” “Me ki ka sha ne haka? Kin tabbata ki na lafiya kuwa?”
“Uhum! Lafiyata lau, na gaji ne kawai, za ku Karasa mutum dai kawai da lodin aiki.” “Kar ki Kalawa kamfanina sharri, idan za ki Kala, ki Kalawa mijinki ne.” “Meye maraban dambe da fada?” Ta fada tana dariya. Zan bambance miki anjima.” “Ka gama (Meeting) din ne ka ke wayar nan?”Za ki zo ne?”
“Yaya Zaid, bye. Maami na kirana.” Tana jiyo dariyarsa. Ta kashe wayarta, ta kira Maami. Wacce take mata tuni akan kayanta da aka karbo na ankon bikin Maryam Kanwar Yaya Zaid.

***********?

Ya ji mamaki Kwarai da ya koma gida wuraren Karfe bakwai, ya samu har Umm Adiyya ta yi barci. Ya tsaya tare da wasu abokansa kan ya taho gidan.
A hankali ya ja Kofar dakin ya rufe mata, ya koma nasa dakin, fes! Ya samu komai, ko ina sai Kamshi yake yi. An lailaye gadon, an gyara tamkar ba a taba Batawa ba. Murmushi ya yi na jin dadi, tamkar ba ta je aiki ba, ya kan rasa yaya take abubuwanta.
Dole idan ta samu wuri ta share, ta yi ta zuba barcin gajiya. Wanka ya yi ya zauna ya taba karatun Al-Kur’ani kafin a kira sallah. Bai fi tsawon minti goma da fara karatun ba kuwa. Ya ji ana kiran salla, don haka da ya tashi tafiya masallaci, ya biya ya tasheta. Lokacin da ya dawo, ya sameta kan sallaya ne, ya ce “Twinkle, me ya yi zafi haka?”
Bude idanu ta yi cikin mamaki, “Me zai yi zafi kuwa?”
“Kuma wariyar ta kai ga har haka ne, ba za ki fada min abinda ki ke ciki ba?” Yaya Zaid, ban fahimci fa me ka ke fada ba.” “Come and give me my hug.” Gwalo idanu ta yi tana dubansa. “Na me?” “Sai da dalili?” Ya fada hade da sa ta a jikin sa, ya sumbaci saman goshinta, “Na gode.” “Ni dai Wallahi ka bar ni a duhu, idan ka gama, sai ka yi bayani. Barci na ke ji.” “Congratulations, you’re going to be a mother.”
Ka san hakan ta yaya Mr. Engr. Dr. Zaid Www.bankinhausanovels.com.ng AbdurRahman?” “Ke wace iri ce ma oho? Ba ki kula da canji ba a tare da ke?” “Yaya za ayi na kula kuwa? Ni lafiyata Kalau, ba na jin nauyin komai ni.” Silly, sai na ba ki horaswa na ga alama, ki na ina su mutane suke sanin irin wadannan abubuwan?” “Kai kuma a ina ka je ka san wannan abubuwan?” Ta fadi tana daga masa gira. “A garinku, da gaske na ke miki.” “Hmm…” Wannan ya kawo su ga gangarar zuwa asibiti. Ni fa ba zan je kawai asibiti na ce su wani gwada ni ba.”
“To zama ki ke so mu yi a gida, ki na ta ciwon barci da kasala? Da gaske ki shirya da safe na kai ki. Gobe ba ma aiki, kin ga ba ki da wani excuse.” Ka damu kanka, wata Kila duk gajiya ce ta biki, tunda muka je muke parade a kan Kafafunmu, ba mu zauna ba.” “Za ki je asibiti, kuma shi ne zance na Karshe.” Ni kam kunya na ke ji.” Dariya ya yi, tana jiyo dirin muryarsa a Kirjinsa, “Ahaf, ke da mijinki kuma ina ruwanki da wani?” “To ba ana dubawa a gida ba?” “Umm Adiyya!” “Yaya Zaid, ba za ka gane bane, ni yanzu duk ka sa ma barcina mai dadii ya watse.”
‘To shi kenan da safe zan samo miki abin gwajin Inshaa-Allahu. Me za ki ban idan nine da gaskiya?”
Ta san shirmensa yake yi, yaushe-yaushe ta gama al’adarta da ma zai yi tunanin ciki gareta? “Duk abinda ka ke so, ka fada, zan ba ka.” “Ba canza zance.” “Na amince.”
“Oya mu je mu rama wannan barcin da na katse, amma dai kafin nan, ina jin yunwa.” “Lah, an ce fa ba kyau barci, ana gama cin abinci.” Ba zan iya barci kuma da yunwa ba, ko kunu ne ki ba ni.” “Abincin ma zan ba ka, me ya yi zafi, tunda akwai, an dafa ba babu ba?” Tare suka koma Kasa, inda ta hada masa Tea, ta sako masa abinci marar yawa, suka zauna, ya gama ci. Ita kuma ta taya shi shan Tea din.
Tana gamawa ta mike da gudu sai bandakin cikin falonsa, bin bayanta ya yi don ya
tsorata, gefenta ya tsaya yana mata sannu. Sai da ta wanke fuska, ta fito ya ce, “Me na fada miki?’
“Ba wanin nan madarar ce kawai ina ga da na sa, ba na hada ganyen shayi da madara, dama yau kuma na saka.” “Eh irin ke za ki yi kwadayinku na masu ciki ko?” Wai kai ba ka jin nauyi ne? Ka yi shiru mana.” Ta fada cikin turbune fuska a shagwabe. “Allah ya kai mu gobe.” Ya fada yana mata
dariya.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *