UMM ADIYYAH CHAPTER 37 BY AZIZA IDRIS GOMBE
Www.bankinhausanovels.com.ng
MUN TSAYA
yana shafa mata bayanta a hankali. “Ya isa my Twinkle.” Dago kanta ya yi yana duban idanunta da suka yi ja, suka yi
luhu-luhu da hawaye, ya san ko ba komai, yau ta samu sa’idar cewa an warware
komai, zargi ya bar kanta, wanda duk da ta san ba ita ta aikata ba, amma sharri ba
abinda ya fi shi muni, da bacin suna, wanda har abada ba kowa bane zai fahimta, bare ace kowa ya zo ya yarda da gaskiyarka daga baya. “Uhm-uhm…” Gyarar murya suka ji daga bakin Kofa. Umm Adiyya ta yi saurin sake Zaid, ta shiga share hawayenta, sannan ta matsa bangaren kujerun zaman baki, (Couch) Ta zauna, yayin da Fayemi ya Karaso cikin ofishin.
Ya kula da kallon kissan da Zaid ya watso masa, amma ya matse ya Karaso. “Ehm… Ku yi haKuri da shigowata kai tsaye. Yallabai, ina buKatar sa hannunka a nan.” Karba ya yi, ya duba takardar sannan ya saka masa hannu. Ga shi.” “Saura nan.”
Zaid ya Kara karba ya saka, “Akwai wani wuri kuma?” Ya tambaya cikin nuna
ZAMU TASHI
Kosawarsa. “Babu na gode.””Ka cewa Stella, ba na nan har nan da minti talatin, duk wanda ya zo ya jira.” Fayemi ya gyada masa kai sannan ya wuce. Yana fita ya dan ware idanu, yana
murmushi ya ce da Stella, “Idan ba na sa ma mana satar amsa ba sweetheart,” Stella ta dan yi murmushi tana juya idanunta ga abin sonta, “Ka fara jan ran naka ko?” “Ki yi shiru, ina fada miki yau Oga ba dama ne. Ya ce ace wa koma waye ne baya nan tsawon nan da minti talatin.” Ta soma dariyar Kasa-Kasa ne, suka ji murya a bayansu, “Ka ce masa mahaifinsa ya zo, shin zai iya ganinsa ko shi ma ya koma?” Ba shiri, duk suka shiga taitayinsu, “Ina wuni Yallabai?” “Lafiya Kalau, ke shiga ki ce ga Abdur-Rahman Muhammadu Nafadia yana sallama
da shi Ogan naki.” Daf, bayansa sai ga Abba ya shigo yana maida numfashi, alamaa sauri suka yi ta
tika. Stella don tsabar kidima, ba ta samu damar Kwankwasa Kofa ba, kawai ta fada Www.bankinhausanovels.com.ng
ciki. “Fayemi…” “Sir, ina ga Baba ne ya zo.”
A fusace Zaid ya juyo yana kallon Kofar daga inda yake zaune da Umm Adiyya a
Barin kujerun dakin, yana Kara rarrashinta, “Me ki ke nufi da cewa ki na ga Baba ne ya zo?” Sannu da himma, Zaid. Ko na ce Mr. Zaid Abdur-Rahman.”
Wani abu ya hadiya ba shiri. Zit! Umm Adiyya ta mike, ta buya a bayan Zaid. Kamar ta ga Kura. Ke zo ki shige gida.” Ta ji muryar Abbanta, ta gefe ta dan leKo ta ga tare suke da Baffa Abdu. Me ya kawo su?
“Wato kai har ka girma, ka kuma rika ka isa,
abu mai girma irin haka yana faruwa a rayuwarka, ba mu da damar da za mu sani, sai rana tsaka, ayi mana waya ana mana mura yadda mai shahararran kamfanin (AZ IT Consultants) ya yi nasarar Www.bankinhausanovels.com.ng
bankado asirin masu sata a kamfaninsu, wanda ya dau watanni ana fafatawa. Zaid watanni? Sai a waya mu iyayenka za mu ji?” Kai a waya ka ji ba yanzu muna tare ba na ke nuna maka abinda na gani a Twitter
Yaya?” Abba ya fada yana nunawa Baffa wayar hannunsa. Ke zo, yaya aka yi ba ki fadawa iyayenki mata ba?” Baffa Abdu ya fada yana leKo Adiyya.
“Baffa ka yi haKuri, daman… daman” Zaid ne ya sa hannu ya fito da ita daga bayansa. Umm Adiyya dau jakar ki ki jirani zan masu bayani.” Baffa, Abba ku yi hakuri, ga wurin zama. Zan fada maku yadda komai ya faru, ba da gangan bane, shi ya sa ya zamana ba ku ji abin da yake faruwa ba.” Wane irin ba da gangan ba? Ashe ko addu’ar yawun bakinmu ba za ku nema ba, bayan ku na cikin tsaka mai wuya haka? To kodayake, me addu’o’in bakinmu za su yi wa ‘yan zamani irinku?” “Ya-Salam, Abba don Allah ka tayani bawa Baffa hakuri, abin ya dagula mana hankali, ya tafi da tunaninmu, domin duk randa muka ga mun yi kusa cimma nasara, sai abin ya kufce, hakan ne ya dauki hankalinmu har ma ya zamana ba mu kai ga
fada maku ba, mun san addu’o’inku na tasiri a kanmu ko mun fada ko ba mu fada ba, amma dai cikin nufin Allah da albarkarku, muka iso haka, kuma cikin albarkarku muke fata mu fi haka. Ku yi hakuri, mun yi kuskure da ba mu fadi abin da yake faruwa ba.
Yanzu aka tafi da mutumin, zai kuma ambaci wadanda suka sanya shi aikata wannan ta’asar.” To Abinda dai ya wuce ya wuce. Allah ya Kara kiyaye gaba, ya tsareku da dukkan tsarewarsa, ya sa ku gama lafiya.” Abba ya fada cikin saukin murya. Baffa kam
gyara babbar rigarsa ya yi, zai fice. Stella ta mannu da Kofar ofishin da tire rangameme shake da kayan ciman ofis, dangin su Crackers biskit da sauransu.
“Baffa ba ka sha ruwa ba, ko shayi za a sa maka?” Zaid ya sa baki ya tambaya. “Ni ba ruwa na zo sha ba, ka riKe ruwanka.” Www.bankinhausanovels.com.ng
“Assha, Yaya ka yi haKuri.”. Abba ya bi bayansa yana masa magana. Zaid, kam ya san laifinsa ne, domin ko Maami duk kusancin su bai fada mata abinda ake ciki ba na rikicin kamfaninsu. Haka Mama ma ba wanda suka fadawa daga shi sai Umm Adiyya.
Haka suka tattara suka koma gidan Abba. Don lallashin nan ba na tsaye bane, an fafata sai da Maami ta sa baki, sannan Baffa Abdu ya sauko.
“Ai na zaci ko bokon ne ya shiga kanku har haka ku ka manta da neman albarkar iyaye, amma tunda ka ce bincike ne mai tsauri da ke buKatar sirri ai na gane. Amma me ya kai ka jawo mata kuma a cikin wannan al’amarin? Za ka kama ka sa ‘yata a gaba da matsalolin aikinka. Ji yadda duk ka jemar da ita, ba tantama ba ta samun barci.” Baffa lafiyarta Kalau.” Zaid ya fada cikin dan gunaguni. “Yi shiru ba kai na tambaya ba, ai tana da baki ka bar ta dai ta fada da kanta sai na gamsu.”” Nan kallo ya koma kan Adiiyya wacce ba ta san ma ana yi ba, ta dan dago kanta ne
ta ga kowa ita yake kallo. “Na’am.” To ba ga irinta ba? Yarinya shiru-shiru, ka na neman ka dora mata damuwar duk duniya a kanta, daga yau, ka ji na gaya ma ka je can kai da ma’‘aikatanka ku warware matsalolinku, kar na sake jin ka jawota cikin damuwarka.” “Baffa, Umm Adiyya ma ma’aikaciyata ce ai.””To ta bar aikin daga yau, kuma dole a biyata albashin, ai ba haramun bane, don ka ba ta kudinka ko?” Umm Adiyya kam sai tsuru-tsuru take yi da idanu, ba daman ta ce wani abu. Yau dai an tabo Baffa Abdu, duk cikin Baffaninta, ya fi su lumana da sanyi, ga shi yau ya dirawa Zaid kamar ya yi masa duka. Baffa Abdu, ba damuwa zan iya aikin ma. Kawai ace masu su daina sa ni aiki a Karshen mako.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Salati Baffa Abdu ya sa ya kalli Zaid, “Ka ji baKar mugunta, to ko bature yana aiki a Karshen mako ne?” Gaba daya falon aka sa dariya. “Je ki abinki, ko albashinsa gaba daya ki ke so ki dauka sai ki dauka. Allah ya yi maku albarka, ya kareku daga duk wata masifa. Na ji dadi Kwarai, wannan ya nuna irin hadin kanku da jajircewanku kan zamantakewa.
Allah Kara hada kanku ya albarka ce ku da zuri’a dayyaba da za su jiKanku, yadda ku ke jinKanmu.”
Ba Karamin dadi wannan addu’o’i suka yiwa Zaid da Umm Adiyya ba. Haka aka ci aka sha, aka kuma fitar da sadaKa, don godewa Allah da ya kawo Karshen wannan matsalar.
Sai waya suke samu daga ‘yan-uwa na kusa ana jajanta abinda ya faru. A daren suka koma gidansu. Zaid ya nunawa Umm Adiyya godiyarsa ta musamman, domin kasancewa da ta yi a gangarsa cikin wannan lokacin taskun nasu.
*************
BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI
“Noorie, Please, ka yi haKuri. Da gaske kamar yau ne za ka ga sati uku ya yi, ka ga idan na tafi, abubuwa da yawa za su tsaya min.” Shi kenan ki kammala Www.bankinhausanovels.com.ng abubuwanki, masu muhimmanci.” Tabbas ta ji dacin da ke cikin maganarsa, amma yaya Za ta yi? Ba zai yiwu haka nan ta rinKa biye masa tana yadda take so a wurin aiki ba, da a ce wani wurin daban ne, ba zai mata hakan ba Kuma tunda suka yi hakan har ga shi yanzu ana gobe tafiyar ta sa, bai sake dago
mata zancen tafiyar ba. Ko kayansa ma sai gani ta yi ya shirya abinsa. Koda ta yi masa Korafi, sai cewa ya yi.Kin ga, kar fa ki dagawa kanki hankali, abinda tafiyar ma ni kadai zan yi ta kin ga ba
amfanin na saba da wata kulawar da ba samun irin hakan zan yi ba gaba kadan,gwamma na saba.”
“Noorie, ka yi hakuri. Allah zan so na yi maka rakiya, amma ina duba… I mean wa zai ki zuwa Istanbul a rayuwa? Ga Yaya Zaid a hada da Istanbul, ai aljannar duniya ce, amma sati uku da yawa, ba na son su rinka ganin bambanci. Kuma ka ga bada
notis ya yi kadan, bare ace na dauki hutuna na shekara.” Ki bar dogon bayananki, na fahimta. Kawai ki kula da kanki a bayana, idan har akwai wata damuwa, ki samu Maamina za ta duba min ke, kin ji? Kuma banda zaman shan Cornflakes, don Allah, ina sane sarai, kullum na yi tafiya, haka ki ke
rayuwa kan Cornflakes, saboda katan nan da nan yake Karewa. Ki taimaka ki daina Www.bankinhausanovels.com.ng
wahalar da dattijuwar nan Hajja Innayo.” “Wallahi ina ba ta shinkafa har ma da tuwo.” Dariya yayi mata ganin ta hakiKance kan batun an ce ba ta ciyar da Innayo.Na sani, ko kin manta na fada ranar aurenmu, matata ba ta da rowa? Ki ci-gaba da
riko da nagartattun halayenki, wadanda suke Kara min sonki a kowane dakika. Ina
sonki a yadda ki ke, yanzu taho nan” Ya fada dai-dai lokacin da ya cusata a jikin sa
cikin gamsasshiyar runguma, mai dumama ruhi. Wata ajiyar zuciya ya sauke mai cike da gamsuwa.
Duk boyewarsa ta sani, can Kasan ransa ya ji zafin rashin binsa da ta yi, yaya za ayi ta bi shi? A wuni daya zai fuskanci halin da take ciki.
*************
TURKEY, ISTANBUL.
“A‘a fa kar mu yi haka da ke, ki min rakiya, ina ce ki ka Ki? Yanzu za ki wani ce ‘you miss me’. Ban fahimci wannan al’amarin ba, kuma tsaya yaya na ke jin muryarki wani iri?”
“Agalawa ce ta kama ni tun shekaranjiya, na ke fama da zazzabi.” Ya kamata ki je asibiti ai to, ba ki zauna a gida ba, yana da illa sosai.” “Na ji Likita.” Murmushi ya yi ya kawar da zancen, “Amiran ta iso ko?”
“Eh muna nan da ita tun safe ai, bayan ta ce kai ka ke ta hana ta zuwa har ga shi hutunsu ya kusa ya Kare.” Haka ta ce?”
“Kusan dai hakan ne tunda ba ta furta ba, amma ta ce Uncle Zaid ya ce shi zai je ya
dauko ta, bayan ka san al’amura sun maka yawa, ba iya zuwan za ka yi ba nan kusa.” Www.bankinhausanovels.com.ng
“So, a taKaice kin amince mijinki bai da kirki kenan? Ki fada min da mace mai gudun mijinta da miji mai tarairayar matarsa, waye marar kirki?”
“Ho! Ya-Salaam da na san haka za ka matsa min da gori Allah da ban Ki tafiyar nan ba, idan ya so kowa ya ce Shugaban (AZ IT) ya faye son kai.”
“Ba na fada miki ba, ni kam ai da zan dauki nauyin abina, amma haka kawai ina ji, ina gani aka min rinto, gani nan an bar ni da kame-kame kawai.”
Zabura ta yi daga kan gadonta ta zauna, “Kame-kamen me?” Oho, ina ruwanki.”
“Zaid Abdur-Rahman, idan ka kuskura ka yi abinda ba daidai ba…”
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG