UMM ADIYYAH CHAPTER 39 BY AZIZA IDRIS GOMBE
Www.bankinhausanovels.com.ng
Gidan Maami ta koma, saboda rashin jin Karfin jikinta. Innayon ma can ta bi ta suka
tare, sai da suka shafe sati biyu. Duk iya zamansu a can. Zaid yake Karashe
wuninsa, daga ya taso aiki, baida wurin hira illa gidansu, dakin matarsa, ko falon Abba ko falon sama.
Maami kam ta kawo idanu kawai ta zuba akan wannan ikon Allah, idan ta tuno borin
da Adiyya ta rinka kantama masu akan ita an cuceta da aka aura mata Zaid. Wani abin dariya ma, duk dadewa da ya yi yana sintiri a kanta yana zuwa kullum dubata, fitarsa goma da ababensa na armashi yake tahowa, ko babban kyauta ko
Kanana ko na sawa ko na ciye-ciye.
Ranar Alhamis da ta shud, ta kula da yadda Ummun ta bi ta diririce, ita kadai sai fada take yi, tana cin magani, har ma ta sauke akan FaruK shi da bai ji ba, bai gani
ba. Ganin hakan ya sa Maamin ta tambayeta, “Ke wai me ke damunki tun safe?’ Kwafa ta yi, “Hmm! Babu komai Maami.”” “To akan babu za ki bi duk ki addabi kowa, ina kallon yadda duk ki ke ta wani tsaki,
tun kan na bar gidan nan, yanzu ma ga shi na dawo, amma ba abinda ya canza.”
“Maami banda wannan Yaya Zaid din ne ki na ga yau fa ko sau daya bai kira ya ji
yaya jikina ba, kuma na sani sarai yana da caji, don baya barin wayarsa ba caji. Ai Www.bankinhausanovels.com.ng
ko ba don mutum bane, ya ji ciwo ka tambayi yadda ya Kare bare ni Maami.”
“Allah na gode maka. Oh! Wani abin sai wurin wannan baiwa taka. Yanzu Ummu
don mijinki bai kiraki a waya bane, ni za ki kama ki takurawa nawa ‘ya’yan? To ba abinda zan ce miki, sai Allah ba ki sa’a. Www.bankinhausanovels.com.ng
Da ba ki ga wayar ta sa ba, in ce ke kin kira shi, da ki ka ji shiru, ki ji ko lafiya? Tunda shi ya saba kiranki.”
“Maami ai ni ce na ke ciwo.” Justice Khadija kam baki ta kama cikin al’ajabin ‘yarta. “Eh da kyau, shi kuma ai waliyyi ne baya ciwo, kar ki sake min maganarki, ta shiririta, idan za ki kira, ki kira, ki daina damun mutane.” Haka ta ki kira, ta kuma ci-gaba da kumburi. Da magariba kuwa sai ga shi niki-niki
da komai da ya san tana so, har da su Cornflakes a tarkacen da ya kawo mata, da
wata sabuwar waya mai rai da lafiya. Kwando guda ya hado mata na shirgi.
Kallonsa ta yi ta watsar, tana danne-dannen wayarta.
“Ina wuni?” Ya fada yana murmushi, ya san laifinsa, don haka bai ji haushi ba, da ta basar da shi.
Hannu ta sa tana wasa da silin kalabar ta da yake rito daga kafadarta. “Yau na ga ta
kaina Drama Queen ta motsa, ayi min afuwa (Meeting) muke yi tun safe.” Ai na ga bakwa sallah.” Ta fada hade da dauke kanta. Na amince, na yi laifi, ba ni da excuse na rashin kira, amma Allah-Allah na ke yi nazo na ganki, kin ga ai gani ya fi waya ko? Ki yi hakuri. Kuma na turo miki sako sai
yanzu a mota na ga ashe bai tafi ba.” “Duk daya ai, tunda ban gani ba.”
“Ya kamata mu koma asibitin nan dai mu ji ko akwai wani sinadarin (Hormones) da
ke Kara birkita mutum, bayan ya yi rashin lafiya.”
“Oho! Kai ka sani, ka tafi da kayanka, kaina yana ciwo. Ban jin yin hira yau.” Www.bankinhausanovels.com.ng
“Allah ya ba ki hakuri.” Ya fada ya ajiye mata ledojin, ya miKe ya bar bangaren falon.
Ita kuwa idanunta na dan kallonsa a fakaice, wato tafiya ma zai yi da gaske. A
hankali ta sa hannu ta dan bude ledar da ya shigo da ita, bayan kamar minti uku, ta
tabbatar ya fita daga falon. Tana budewa ta ga sabuwar wayar da ya saya mata, da
tarkacen kayan dadin ciki, murna ta shiga yi har da wurga hannu a iska. Sai kawai caraf! Suka yi ido hudu da shi. Jiki a sabule ta mayar da kwalin wayar cikin ledar, ta dan tsume hade da komawa ta
kwanta ta juya bayanta, kunya ta ji kamar ta natse cikin Kasa. Yau ta gama yawo a duniya.
“Haba Adiyyata, ke dai ki ce ashe kawaicin ne yau suka motsa, ni da ake fushi da ni,
me kuma zai sa ayi murna da abina. Daman na zo na dauka ne, amma tunda sun miki kyau shi kenan.” Tashi ta yi ta zauna, ta ja ledar ganbarta.
“Ai idan an yi kyauta ba a fasawa, ya zama kyautar ‘yan-wuta kenan.” Wata dariya
ce ta kucce masa, ya yi iya isarsa sosai. Sannan ya ce “Ke dai fadi gaskiya ki na so ki na wani kaiwa kumo,”
“Dauki kayanka na fasa.” Ta fada hade da harde hannayenta a Kirji. Suna cikin haka ne. Abba ya yi sallama, don haka Zaid ya kama kansa ya nufi cikin
falon Abban, inda suka dan tattauna wasu al’amuran, amma har ya tashi tafiya bai sake ganin Twinkle dinsa ba, shi kuma ba son hawa saman yake yi ba, tunda ta samu lafiya take zaman Kasa, ya daina nemanta a sama, idan tana can. Don haka
saKo ya tura mata ta waya akan ya wuce.
******
Bayan kwana biyu ne Abba ya ce mata. “Mamana, yanzu kam ai ya kamataki koma Www.bankinhausanovels.com.ng
gidanki ko? Na ga alama ko tsere aka hadaki da Faruk za ki wuce shi.” “Abba ba ma Fa’iz ba? Faruk ai yanzu ya fi Karfinmu.” Dariya ya yi. “Yaushe ku ka yi, za ki koma?” Kanta a kasa ta ce, “Ba mu yi maganar ba da shi.” To ai ya kamata ku yi, kin ga sintirin haka ba dadi ai, da gajiyarwa, kullum zai je aiki, idan ya taso ya yi nan, har sai can dare kuma ya Kara komawa gidansa, amma idan ki na can zirga-zirgar sai tayi masa sauKi, ga wuri ba kusa ba.” To Abba, za mu yi maganar.” Da zan dan miki kyauta amma na ga alama ke din Hajiya officer ce, kin ga sai ‘yan kwabban dan fansho su huta.” Dariya ta yi sannan ta ce “Abba akwai wanda ya ki kari ne? Bare ma ai kai ka fi mai
salary samu Abba, ka daina cewa ka yi Retire za ai maka dariya. Cewa za ka yi Alhamdulillahi.”
Shi din ma yanzu kam dariyar yake yi, “Kun faye son kanku, ku wayo, naku naku, amma nawa kowa ya bi ya yanyame.” “Saboda ai kai ne ginshiKinmu Abba. Allah Kara rufin asiri da tsawon rai mai albarka.”
“Ameen, to shi kenan zan turo miki ne, ko a hannu ki ke sonsu?” Abba a hannu kam kan Pizza duk za su Kare a sa dai a Account din.”
“To shi kenan, ku dai koyi tattali, ba komai aka samu ciki ba, akwai ranar ajiya.” To Abba, mun gode.”
Nan suka fada cikin wata hirar daban. Suna cikin magana ne, sai ga Maami ta shigo falon cike da fara’a. Yanzun nan muka gama waya da Zunnuraini. Asma’ ta sauka an samu baby girl.” “Maami! Mashaa-Allah, yayyyy.” Da sauri Umm Adiyya ta tashi har da tsallenta ta nufi inda ta jona wayarta a caji, ta hau danna lambar wayar Asma.
“Haba Adda Wallahi wannan cuwa-cuwa ne, kuma sai ba za ki fada mana kin fara jin muntsuni ba, mu zo mu yi kallon ihu?” “Ke meye haka? Ba ki da kirki Ummu A. Ga wanann tulelen kan ‘yar taku da ta kusa
aikani lahira.” “Duk ilimi ne a ciki, ki bar mata kanta yadda ki ka gani, ehem! Sa min ita na ji ta don
Allah.” “Don Allah ki bar ni, yanzu na fito (Labour Room), ko muryata ba ta daidaitu ba.” Ihu ki ka yi ta yi da gaske? Ba ki da dauriya Adda Asma.”
Maami ce ta Kwace wayar ta kashe, “Ke don Alajh Kyaleta ta huta.”
“Maami fa ba ta ba ni na ji muryar baby ba, ki ka kashe, ko Allah Ya raya ban ce ba.”
“Haka ake yi, ki bi ki cika mutune da surutu. Ban san yaushe ki ka yi baki ba ma.”
“Lokacin da ku ka koya mata masifa ke da danki.” Abba ya fada yana cire gilashinsa,
bayan ya lalubo lambar Asma’, don ya kira ya jita.
Umm Adiyya ta rufe idanunta da tafukan hannunta, “Abba fa ba na surutu da gaske.”
“Ungo Karasa gaisawa da ‘yar-uwar ta ki, na ji muryar sabuwar mata.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Maami sai fara’a take yi, daga gani tana tsantsar farin-ciki, ga Walid dai ga Safiyya,
amma yanzu wannan Karuwar da aka samu ya sake sa su Kara jin wani dadii, ita ma
dai Allah ya kawo ranar da za ta saka wannan farin-cikin a idanun mahaifanta, su
rike yaranta da na Yaya Zaid su kirasu jikokinsu.”
Suna gama gaisawa da Asma’, ta mikawa Abba wayarsa, ta koma sama. A daki ta yi
zamanta, tana karatun Al-Kur’ani, saboda
yawancin lokuta abinda ta fi yi kenan, don ya kan debe mata kewa, ya rage mata tunani.
Maimakon Maami ta ga Umm Adiyya ta fara shirin komawa gidanta kamar yadda Abba ya ce, sai ji ta yi tana hirar tafiya Kaduna. Wai ina ki ke so ki ce za ki je?” Ware idanu ta yi tana kallon mahaifiyarta, “Maami? Kaduna mana, ba gobe za ki je dubo Adda Asma’ ba?” “A’a ni motata ta cika, babu ke a cikin shirin tafiyarmu, ke da za ki koma gidanki gobe?”
A take Umm Adiyya ta turbune fuska. “Gaskiya ni ce ba a so a gidan nan, komai zan yi, sai a hanani. Maami ba fa kwana za ku yi ba, ku dan mammatsa, ai zan samu space, kuma daga ke, sai Aunty A’isha da Aunty Rakiya ina ce? Sai na zauna a gaba. Fa’iz ya tuKa ko Malam Bala.”
“Kin yi magana da mijinki ne? Ni ba na son yin shisshigi da katsalandan, ko zan ce
bai sani ba, ke kin hau shirin tafiya? Yaushe ki ka warware? Idan ba goben za a
dawo ba fa? Bayan an ce masa gobe za ki koma, ai kin ga sai abin ya yi yawa. Ki
hakura idan kin koma gidanki, in ya so sai ki tambaya, idan ya bar ki, sai ku taho
tare ko ya sa a kai ki. Amma yanzu idan kin bi mu tamkar mu muke masa iko da ke kenan.”
“Ayyi Maami, ai dama ba binku haka kawai zan yi ba, sai na fada masa tukun.” Www.bankinhausanovels.com.ng
“Duk ko ma dai menene, ki hakura sai kin koma gidanki, ki masa magana, tunda ai jiya aka yi haihuwar.”
Haka Umm Adiyya ta kumbura suntum! Kamar za ta fashe, ita a dai bar ta, ta je ta
ga yarinyar Asma. Ita kam dama kowa ya santa da son yara da kuma sha’aninsu, shi
ya sa Adda Zubaida take jin dadin zamanta, don duk wata hidima ta yaro, baya ba ta
wahala, kan ma ta yi aure, ta iya wankan sabbin jarirai. Akan Walid ta koya, duk
gidan da aka yi haihuwa kuwa, a makwabta,
nan take tarewa, sai Maami ta yi ta aiken a kirata ta dawo gida.
Wannan ya sa take Kara karaya a lamarinta, an taba ce mata masu son yara da
yawa, ba sa haihuwa. Ta san Karya ne, amma yanzu da abubuwa suka yi ta faruwa
da cikinta, sai take ji kamar hakan zai iya yiwuwa da gaske ne.
Suna hada kayan zuwa ganin masu jego. Umm Adiyya na shirin komawa gidanta. Matar gidansu Maami, Hajiya Larai ce take kan Asma, don tun ana saura sati guda, lokacin haihuwar ya gabato, ta tafi Kadunan daga Gombe. Sannan ga gidan Baffa
Mai-Kano ma ba su bar komai ba, tana samun cikakkiyar kulawa.
*********
Tunda magariba ta kula da yadda Yaya Zaid yake kallonta, ta san magana ce a bakin sa. Amma dai bai ce komai ba, don haka ita ma ta basar, ta kula tun
dawowarta ran Litinin yake dari-dari da ita. Haka kawai ta tsargu, amma za ta jira,
sai ya fada mata koma menene, don kansa.
Gyara filonta ta yi ta bubbuga yadda za ta ji dadin kwanciya a kai. Sannan ta karkade kan gadon . “Dr. Zainab tana gaishe ki.”
Juyowa ta yi tana dubansa. “A ina ku ka hadu?” Littafin hannunsa ya ajiye ya kurbi
Kahwansa, sannan ya ajiye a kan durowar gefen gado, ya zauna a kan gadon.
“Dazu da yamma ina wurinta.”
Kallonsa ta yi wani iri, cikin tsuke idanunta, “Okay… Tun yaushe Doctor Zainab ta dawo Likitan maza kuma?” Dariya ya yi ya ce, “Ba ta dawo ba. Na je ganinta ne akan batunki.”
Lokacin ne Umm Adiyya ta zauna ta ba shi dukkan natsuwarta. “A kaina kuma?”
“Uhum! Na ga dai yanzu kin gama warwarewa.” Ba ta fahimci inda zancensa ya dosa ba, don haka ta Kara natsuwa da kyau. “Shi ne ka je ka tabbatar da hakan a
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG