ZURI’A DAYA BOOK 1 CHAPTER 1 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 1 CHAPTER 1 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE 

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

Yammacin ranar asabar an tashi  da muku-mukun sanyi da hazo a Kwaryar birnin Kano, tun da garin Allah ya waye babu wani hasken ranarda_ya fito, haka garin yake a lumshe gwanin dadi * gamazauna birnin:’ Sanye take cikin Kananan kaya, dogon _*siket ne na (jeans) dogo har zuwa Kafarta hade ~ da Karamar riga a jikinta, sannan ta dauki wani jaket ta dora akai irin mai tarin gashin nan a . hannunta da wuyanta buzaza kamar gashin  mage, kanta sanye da hular sanyi da yayi Kokarin boye tarin yawan gashin kanta. Ta turo Kofar get din gidansu ta fito cikin (estate) din su ta ga gurin

wayam kaf babu kowa a waje, haka ta runtse idanunta ta huro Www.bankinhausanovels.com.ng numfashin da ta shaka nan take ya zamo hayaki, damuwa ta ziyarci’ kyakkyawar fuskarta, nan ta shiga addu’a cikin ranta na cewar Allah Ya kawo lokacin da burinta da mafarkinta zai zamo gaske, ranar da zata wayi gari ta ga (estate) din su ya rayu kamar yadda yake a da can da ZURI’Arsu take guri guda. Www.bankinhausanovels.com.ng
Haka ta taho tana bin tarin jerin gidajen da tun tasowarta ta iske su a haka wanda take KoKarin sanin dalilin barin shi haka. Tabbas tana iya tuno wani abu a (memory) dinta ada can, tasan da kowane gida cike yake da jama’a amma ta rasa sanin dalilin da ‘yasa lokaci guda ya zamo haka. Tun tana nacin tambaya har ta gaji ta daina, domin ba a taba bata wani labari da zai sa ta fahimci komai ba. Haka ta hakura da fitar da tunanin sanin komai game da gidajen.: ~
Abu daya ne yafi damunta ganin tun sanda suka taso su kadai ne suke rayauwa a cikin (etate) gida biyu su kadai suke zumuncin su kamar basu da wasu dangi a duniyar sai iya su kadai.
Ko da yake ba zata kira kanta da mai damuwa ba domin babu abinda ta rasa na jin dadi a rayuwa, ko da yaushe suna cikin farin ciki a rayuwar da suke a cikin gidansu. Babban abinda ya sanyata damuwa shi ne Kawaycmenta
da suke yawan mata tambaya akan wadannan gidajen meye dangantakar su?
Bata san lokacin da ta ce musu na wasu (family) dinsu ne da suka bar Kasar gaba daya suna can (abroad). Karyar da tayi musu ya tsaya mata a rai, domin haka yasa abin yake damunta da Kaunar da take ma ZURI’Arta ta sake jin tana (missing) dinsu, duk da kuwa bata tabbatar da hakan ne kuwa ko ba hakan bane? Ita dai tana jin a jikinta kamar ta rasa wasu jama’a da ta rayu da su a can da, to amma jin babu wani da ya taba fada nata hakan sai take ganin kamar wani tunani da wani buri nata yasa take saKa haka a cikin tunaninta www.bankinhausanovels.com.ng
Walwala da daddadar rayuwar jin dadin da suke yi cikin gidajen su guda biyu yasa take mantawa da tunanin da yake zo mata rai a duk lokacin da tayi KokKarin fadin wani abu akan abin da take yawan tunani akai, sai ta ga babu wanda zai mayar da hankali akan abin da take magana akai, wannan tun kafin ta kai haka take yi ma iyayenta, amma sai su mantar da abin su daukeshi shirme hakan yasa tabar abin a ranta ta daukeshe kamar shirmenta ne nan take itama ta shiga mantawa da hakan ta shiga harkokinta tunda kaff ZURIARTA babu wanda ya taba zama ya fuskanci abinda take nazari akansu tabbas jikinta ya bata kamar ba,ason tason komai na rayuwar baya da akai sam bare ana hira da ita don tuno mata rayuwar yarintarta ta jima a wajen tana ta zagaye a wajen nan taje taji wata (idea) tazo mata take ta juya ta koma cikin katafaren gidan nasu kai tsaye dakin kakarta ta nufa
Salam granny kwance ta ganta ta lullube jikinta da tattausan bargo tana kallon tauraron dan adam cikin tashar sunna tv
Da sauri tazo ta janye bargon da take lullube dashi  tana daria tace wai granny har wani sanyi ake a garinne da zaki shiga daki ki wani buya ki gito kawai kimu zazzaga waje ko kashinki zai Kara Kwari, amma idan kika zo kika zauna nan ba dole ki ji sanyi ba”.
“Toh ‘yar nema, kin fiso sanyi ya Karasani, ai sai ki tashi muje Dadinta ma ina da ke, sai ki tsaya ki yi jinyata”. Dariya ta saki, tace, “Wayyo Granny na, ai ni ba zan so na ganki cikin larura ba, domin zan shiga damuwa. Nafi so kullum na ganki cikin Koshin lafiya da nishadi ko na saki gaba ina tsokanar ki, haka yafi min dadi, amma ba na ganki cikin wahala ba”.
Murmushi tayi ta ce, “Ja’ira, to rufa min bargona naji dumina, don har na soma jin sanyi”.
“Hahaa! Granny idan ba ki fito kin yaki sanyin nan ba zai kwantar mana dake, gwara kawai ki fito mu dan fita waje, don kina daki Www.bankinhausanovels.com.ng
“ne shi yasa kike ta jin wannan sanyin, amma ni gashi da na fita babu wani sanyi da nake ji. Zo muje kawai kema ki dan motsa jikinki, kya dan ji dadin jikin naki”.
Murmushi ta sake yi ta ce, “Gaskiya fa kika fada, to miko min hijabi na saka ki gani muje ko da nan da bakin get nace sai mu dawo”.
Nan murna ta kama ta, domin ta nan ne zata dana mata wani tarko ko hasashenta zai cimma, domin ta san babu wanda zata bi ya fada mata abinda take son ji sama da kakarta, domin babu wata hanya da zata bi don zuwar musu da abin da take muradin son ji. Lokacin da suka fito basu iske kowa baa wajen har suka zo bakin (gate) din, nan ta ce mata.
‘ “Granny mu fita muje har zuwa Karshen gidajen nan sai mu dawo, kinga kema sai ki Karajin kuzari a jikin ki” Ba ta musa ba, haka suka taho suna hira, hankalin Granny gaba ya yi wani gun, . matashiyar budurwar tace
“Granny nayi miki wata yambaya kuwa da ta dade tana damuna”. Ta daga idanu ta dube ta, ta ce,
“Raihanatu ina jinki, game da me kike son yi min wannan tambayar?”
“Zan kuwa fada miki, na jima da burin samun wannan damar bana samu, ni kuma ba komai bane yasa na damu nima na saniba sai yawan tambayar da Kawayena suke min wanda ni kuma sai na rasa me zan ce da su? Dole sai dai na yi musu Karya, sai bayan nayi hakan sai nake jin damuwa cikin raina””.
“Raihanatu yi min tambayar ki, matuKar ina da masaniya zan baki haske akai ko menene kuwa”.
“Granny ba akan komai bane illa ina son sanin tarihin wadannan gidajen da tun tasowa ta na gansu a haka babu wani mahaluki da yake rayuwa a cikin sa in banda wanda muke rayuwa a cikin su guda biyun nan.
Shin MEYE DANGANTAKAR MU da wadannan gidajen masu kama da wadanda muke ° ciki a zaune? Shin su wane suka taba rayuwa cikin sa ko kuma babu wanda suka taba rayuwa sanda aka gina su? Idan kuma akwai su wane ne, kuma ina suke yanzu?
_ Na jima ina jin a cikin tunanina na yarinta kamar na taba rayuwa da wasu a cikin rayuwata
sai kuma ina jin kamar a mafarki hakan ya faru dani.
Na sha yiwa Abba da Ammi tambayar Www.bankinhausanovels.com.ng
Hakan sai suna zamar da abin shirme, haka kema ~ da su Mamah nace duk babu wanda yake zama
ya bani damar sanin wani abu a game da gidan,__. kai hatta Ya Abba Junior haka yake min, na rasa meye dalilin hakan?” Nan take wasu hawaye masu dumi suka gangaro daga idanunta, nan da nan ta sa hannu ta share, ta ce. . “Raihanatu kin yi gaskiya, kuma na Kara yabawa da hankalin ki da tunanin ki, tabbas_ – dukkanin mu muna sane da abinda kike nufi da gangan muke nuna miki bamu gane komai a tare. dake ba, dalilin mu kuwa bama son tuna abinda ya faru a baya ya sake dawowa cikin rayuwar mu, duk da kuwa an nuna anfi Karfina dole na . haKura na bar abin don bani da mataimaki. Na jima zuciyata tana saka min kamr ke ce zaki iya _ taimaka min, amma sai naga babu wata hanya da hakan zata faru”
Nan da nan hankalinta ya tashi ganin yadda hawaye ke fitowa ta fuskar Granny dinta.
“Granny me ya faru kike kuka? (Please) idan tambayar da nayi miki ne yasa ki kuka ki yafe min, ba zan sake ba, mu bar maganar mu koma gida”.
Murmushi tayi mata ta girgiza mata kai, ta ce.
“Raihanatu kar ki damu, babu komai, muje inda kike so sannan kiyi min duk tambayar da kike so zan baki amsa, amma da fatan za ki ja bakinki ki yi shiru, domin’ gudun rashin fada miki wani abu zai zo ya sake afkuwa, domin ni tuni na hango hakan, saninki da abin da ya faru a baya ina ganin hakan zai iya janyo mana haduwar ZURI’Armu, haduwa guriDAYA.
“Raihanatu duba tun daga can gidajen har zuwa nan duk na ZURI’A DAYA ne, tun taletale guri daya aka rayu, sai gashi lokaci daya ZURI’A ta tarwatse, duk yawan gidajen nan an zamo gida biyu ne kawai suke rayuwa a cikinsa. Rashin hakKuri da .duba meye kansa zumuncin duk shi ne ya kawo rabuwar ZURI’A din hade da son abin duniya da bakin hali da rashin yarda da Kaddara, wadannan su suka yi uwa suka yi makarbiyar tarwatsewar ZURI’A DAYA. Www.bankinhausanovels.com.ng
ZURI’Ar da ta ginu da son juna da zumunci tayi suna, amma sai gashi lokaci daya ta tarwatse kowa ya kama gabansa, babu wanda yasan halin da wani yake ciki. Bugu da Kari da taKama da tarin dukiyar dae cikin Zuri’ar duk sun taimaka gurin rashin dusayi da son duba muhimmancin meye Zumunci? Duk da kuwa akwai manya a cikinta amma shaidan da son zuciya bai sa an duba hakan ba, haka aka bari Zumuncin Allah ya watse”.
. “Rehana ki mu koma gida muje mu zauna na warware miki dukkan sarKaKiyar da guguwar da ta shigo ta: tarwatsa mu yau tsawon shekaru kusan ashirin babu daya cikinmu da ya waiwayi dan’uwansa don zumuncin Allah, tsabar shaidan ya gama nasara akan abin da ya yi niyya, amma na so ace yayanki Abba yana nan na baki wannan tarihin”
“Granny kina so ki ce min shima Ya Abba bai san komai ba har nake tunanin ya sani?”
“Ba zai rasa sanin wani ba tunda shima bai da wayo sosai abin ya faru, sai dai na san zai iya tuna wani abu da ya faru da sauran ‘yan uwansa. Ke dai muje za kiji yadda asalin ZURI’Arki
suke, cikin yardar Allah sai mun samu ta dawo yadda take da can duk kuwa da abin yana da matukar wuya saboda ba a rabu ta dadi ba”.
Haka suka dawo cikin wani irin alhini, a falo suka ci karo da Kannenta suna ta kallo, Kanwar ta Zulaiha ta ce.
“Aunty Haana ina kika je ga wayar ki a hannu na Zahra tana ta kiran ki na ce mata kin fita kin bar wayar a falo?” “(Okay)’ Zuly, ki riKa min wayar a gurinki, kowa ya kira ki ce bana kusa”.
Farouk ya ce, “Aunty Haana na karba na dana (game) don Allah?”
Haana shi ne sunan da kowa yake kiranta da shi, domin sunan kakarta ta ci Raihanatu, shi ne a gida suke kiranta da Haana har can ma (school) haka kowa ke kiranta. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Oya Ya Zuly ta baka ka dana din”.
Nan ya shiga mura, ita kuwa ta shiga tsokanar shi akan ba zata bashi ba daga Karshe dai ta bashi, sannan ita kuma ta juya ta bi bayan kakarta. .
Zaune ta iske ta tana jiran zuwanta, tayi sallama ta shiga. Guri ta nuna mata ta zauna, ta ce,
~ “Raihanatu ki nutsu ki bani hankalin ki, yanzu zan baki_ cikakken tarnhin = ryauwar ZURI’Ar ki da taki rayuwar gaba daya”Ji tayi dadi ya kama ta, ta ce.
“Yauwa Granny, shi yasa nake son ki, idan na gama ji ni kuma sannanzan fada miki burina da mafarki na akan ZURI’A ta”.
“Babu laifi, Allah Ya cika mana burinmu da mafarkinmu, yanzu za ki ji komai domin kema hakan ya zama izna gareki da mutanen duniya gaba daya, domin darasin dake cikin labarin”.

********

“Zuri’ar Alhaji Nasir Dan fillo Zuri’a ce da tayi fice da suna daga cikin tsatson su, asalin su mutanen Rano L.G.A ne, sannan Fulani ne na asali gabansu da bayan su, sun fito. cikin yankin fulanin garin ‘yan asali.
. Tun duniya na kwance Allah Ya yi masa tarin dukiya mai dumbin yawa tare da wayewa ta

Www.bankinhausanovels.com.ng

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *