UMM ADIYYAH CHAPTER 41 BY AZIZA IDRIS GOMBE
Www.bankinhausanovels.com.ng
Ranar da suka cika sati uku ne, ya shigo falon sama ya samu tana tsefe kanta. Gashinta ya bazu a bayanta da saman kafadunta a cike da shi baki wuluk! Sai sheki yake yi. Wariya kenan, shi ne ko a jirani na zo nayi tsifar ko?’ Sa hannu ta yi ta tufke gefe daya da babban abin daure gashi, sannan ta ce
“Taimakon da yake Kara kulle min kai, maimakon warwarewa ba.” Twinkle, Hajja Ku ma za ta sara miki yanzu kam a neman fad, daga tayin taimako?”
“Tunda ba ni na nema ba, ai da sauki, sai a barni.
Zama ya yi a kujerar da take, ya sa hannu ya karbi matajin gashin nata. Ya ajiye a gefe ya rikKe hannayenta. Me ya sa ki ke son ki tsiri abi’ar da ba ta ki ba? Ba kya tunanin hakKina ya kamaki
Adiyya? Rabona da ke watanni uku fa, tun kan na tafi Turkey. Yaya ki ke so na yi?”
Kawar da kanta ta yi gefe. KoKarin zame hannayenta take yi daga nasa. Shirun da na ke yi, da sararin da na ke ba ki, ba wai don ina jin tsoronki bane ko
kuma ba yadda zan yi da ke bane, idan na so ko yaya na ga dama zan yi da ke, don haka ki san me ki ke ciki, tun kafin haKurina ya Kare a kanki.”
Habar ta ne ya fara rawa, cikin KoKarinta na danne kukan da take son yi. Saboda ta gama tsorata da kalaman Yaya Zaid a gareta.
Rankwafowa ya yi daf ita, hucin numfashin na sauka a hankali a kan gefen fuskarta,
duk ya cikata da Kamshinsa, “HakKina ne a kanki da ya zama wajibi ki sauke ko ki Www.bankinhausanovels.com.ng
na so ko ba kya so, kar ki ba ni dalilin da zai sa na Kwata.” Ya rada mata cikin
kunnenta, sannan sama-sama ya sumbaci Kasan habar ta cikin wuyanta, inda ya
san tabbas ya yi mata tasiri. Wanda take ji tamkar yana tsaga mata Kashi.
Da sauri ta mike daga kujerar tana baya-baya, sai da ta tabbatar tayi masa nisa ta
sa gudu zuwa daki, ta rufo Kofa da makulli tana kuka.
Ai ko duniya za ta nade, sai dai ta nade, yaya za ta ba shi kanta, alhali Kiri-Kiri ya nuna bai damu da ita ba. Ta kai rashin damuwarsa har ya fito Karara ya nuna baya son hada zuri’a da ita. Ai ko idan haka ne, babu wani hakKinsa da ya rataya a wuyanta, don ta yi hakan. Shiru ba ta ji motsinsa ba. A dunKule a kan gadonta ta kanannade har barci ya yi
awon gaba da ita. Ba ta gan shi ba washegari da ta fito, bayan ta shirya. Ba Karamin tabata hakan ya yi ba, tunda bai saba haka ba. Domin mafi yawaicin lokuta koda
kowa zai tafi da motarsa wurin aiki, tare suke fita. Fitarsa a yau ya tabbatar mata cewa yaki yake nema. Yaya ma za ayi ka ce za ka auri mata, ka ce kana sonta, sannan ka ce wai kar ta yi tsamamnin samun yara da kai? Ai ba a kanta aka fara bari ba, kuma tunda bai kasheta ba, ai sai a bar ta.
Ita Yara take so, idan zai ba ta, ya ba ta, idan ba zai ba ta ba, kowa ya yi zamansa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ajiyar zuciya ta yi ta Karasa kicin din. Tun shekaranjiya Innayo ta tafi ganin gida sati
biyu za ta yi, sannan ta dawo. Don haka take da tabbacin ko karyawar ma bai yi ba ya fice.
Zuciyarta ta ji ta yamutse. Wani zazzafan hawaye ne ya sulalo mata, ta rasa a daidai wani gaba alakarta da Yaya Zaid ta sauya, ta dawo haka cikin dare daya. Ta daina walwala, kuka shi ne abokin hirarta, ba ta son shiga mutane tun asalinta,
amma faruwar wannan matsalar, ta sa ko wayar da da take KoKartawa tayi ma yanzu duk ta daina. Ta zama cikin kaddaicin da ba ta taba tsammanin za ta tsinci kanta a ciki ba, tunda ta samu Yaya Zaid.
Tun randa ya furta mata kalmar so, take shawagi a wata duniyar da ba ta taba sanin
Dan-adam zai iya riskar kansa a ciki ba na tsantsar shauki da Kauna da komai na jin
dadi. Rana tsaka, kalamansa sun cire mata bandejin da ya rufe mata idanu, har ma
ta fahimci babu namijin da baya Kona matarsa, koda macen da yake so ne kuwa. Tasan ba za ta taba daina sonsa ba, har nata Karshen rayuwar ta zo.
Amma hakan ba wai yana nufin ta sakar masa ragamar rayuwarta sai yadda ya yi da ita ba, ko sau daya bai gwada sa kansa a Kafafunta ba, ya ji yaya take ji game da hukuncin da ya yanke a matsayin “shawara” haka nan baya tunanin illolin da yake
sanyata a ciki, a dalilin wadannan Kwayoyin, bayan kasancewar ba ta ma gwada haihuwar sun ga za ta iya ba. Washegari da sassafe ta fito, saboda kar ma ya wuce ba su hadu ba, don wunin jiya
kaf ba ta ma gan shi ba. Abinda ya Kara sawa ta fara sarewa da al’amarin Yaya Zaid Www.bankinhausanovels.com.ng
kenan. Ta yi kusan minti arba’in kan Kafafunta tana shirya masa gangariyar abin karyawa.
Ta fito daga kitchen din tana jera abubuwan a kan teburin cin abinci ne, ta hango shi
yana saukowa daga sama, wani irin tsalle ta ji zuciyarta ta yi, na lokaci kadan, ta ji
numfashinta ya toshe, wuyanta ya yi dumi
daga waje, fatan ta daya. Allah sa fuskarta ba ta yi jazur ba.
Yaya Za ayi, bayan abinda take fama da shi, ya zama ko a jikin Yaya Zaid? Tamkar ma ana wani Kara masa Kwarjini da kyau, da cika idanu ne. Yanzun ma haka ya fito
cikin jamfarsa ruwan bula, ta yi kuwa masa kyau kamar ta ajiye a akwatin hoto, ta yi
ta kallo. Ta yi nisa wurin kallonsa, zuciyarta na gudun famfalaki da har ma ba ta san lokacin da ya iso inda take ba. Gyarar murya ya yi, ita ma ta yi nata gyarar muryar, abin ya so ya ba ta dariya,
saboda lokaci daya sai ta yi tunanin Zaid a matsayin maza masu shigowa gidansu da gyarar murya, sabanin yadda suka saba da, yana shigowa yake sakata a jikin sa ko ya dagata. Akwai lokutan da suke mantawa da Innayo ma tana gidan, saboda
shauKin junansu, amma yau ga shi ga ta, amma ba wanda yake dokin zuwa kusa da dan-uwansa.
Ina kwana Yaya?”
Kallonta ya tsaya yi da budadden idanu cikin mamaki, saboda tunda ta saka masa suna Noorie, zai iya Kirga sau nawa ta kira shi da Yaya Zaid, ga shi yau kam a Yaya ma kadai aka tsaya. Bai samu arziKin samun Zaid din bama. Murmushi ya yi wanda zurfinsa iya lebe ne kawai. “Lafiya Kalau.” Www.bankinhausanovels.com.ng
‘**A saka maka Breakfast ne?” “A’a ku bar shi, ni ina azumi.” Girarta duka biyu ta daga sama lokaci guda, “Az..Azumi Yaya? Yau Juma’a fa?” Eh jiya ma ai na yi.” “Oh. Ban san ana binka azumi ba ai, da an hada maka kayan buda baki. A ina kayi buda bakin to?”
“Sanin bai da muhimmanci. Ki bar abincin kawai, ba sai kin yi komai ba.” Baki ta bude tana ganin ikon Allah. “Azumi ka ke yi, sannan ka ce ba sai na yi maka
abin buda baki ba? Ina za ka je ka yi buda bakin to, da ya wuce nan? So ka ke yi ace ba na maka abinci ko meye? Zan shirya maka abin buda baki idan ka taso ofis ka zo ka yi.” Daga kanta da ta yi ne ,ta ga kallon da yake mata, ya sa tsigar jikinta ya tashi,
gashin Keyarta suka mike. “Ban ga amfaninsa ba, don haka kar ki bata lokacinki.” Ya fadia hade da sa kai ya wuce, shan gabansa ta yi ta ce, “Da gaske ba za ka daina cin abincina ba, don waye to na ke tashi na yi? Ka ajiye abinda ya faru a gefe, amma ka zo gida ka na cin abinci.” Kai kawai ya gyada mata ya fice daga gidan. Zama ta yi ta sha kukanta, ta gaji kuma
ala dole ta shirya ita ma ta nufi wurin aikin. Ko sun hadu a ofis din ma, baya wani kula ta, idan da mutane a wurin, iyaka ya yi mata murmushi, amma baya wani jan hira da ita, har ta yi tsawo. Tun daga ranar, idan baya azuminsa, zai sauko kai tsaye ya ja Www.bankinhausanovels.com.ng kujerarsa ya ci abincinsa, ya tashi ya tafi, idan kuma yana yi, baya ma kallon tebur din yake wucewa abinsa.
**********
Ranar Lahadi da yamma tana karatu a falon, ta tsaya cak! A tsakiyar karatun nata
saboda wayar da ta gani na Adda Zubaida, ba tun yanzu take mata wayar ba, tana
Kin dauka, daga baya ne dai ta daga.
“Adda Zubaida ni me ki ke son na yi?” Duk dauriyarta, sai da ta fashe da kuka.
“Duk da abubuwan da suke faruwa, ni na san cewa Yaya Zaid yana sonki. Saboda
kowa ya san ba boyayyen al’amari bane idan har Yaya Zaid ya so mace, to ya sota
ne tsakani da Allah, saboda a rayuwa baya son komai, bayan aikin sa, to amma
haduwarki da shi kowa ya san yadda ya canza, saboda haka akwai hope har yanzu, kar ki ce za ki yi fushi, ki yi ta lallaBa shi dai.” Adda Zubaida har yanzu bai cire wancan batun a ransa ba, saboda miscarriages
biyu? Komai ai na Allah ne ai, sai Allah ya
Kaddari zamansu, sannan za su zauna, ai ba dabarar mu bace da samu da rashin.”
“Ki ganar da shi hakan a hankali, ki kuma janyo hankalinsa gareki, na tabbata zai
sauko.” “Hmm! Adda Zubaida ba ki san shi bane.”
Ganin irin kukan da take yi, ya sa Adda Zubaida ta ce, “Ummu A. Akwai abinda ki ke boye min ko?”
Sam ba ta son kowa ya san halin da take ciki, yaya ma za ta fadawa Adda Zubaida
cewa Yaya Zaid ya bar zuwa inda take, dan ta ce ba za ta yi amfani da maganin tsarin iyalin da ya ba ta ba. Yanzu ta zamo kamar wata muharramarsa a gidan, iya kanta ta gyara masa gida ta
ba shi tuwo shi kenan, ya jingine ta tamkar hoto. Ita ba ta ga so a wannan al’amarin ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Ummu A. Shin ki na ganin akwai wanda ya cancanci ya san damuwarki, baya ga ni da Asma? Ko Maami ba zan so ki kaiwa kukanki ba, saboda ita uwa ce, sai abu ya faru, ke ki manta, amma ita mahaifiya ba za ta mance ba, za ta rinKa ganin mijinki da wannan abin da ya yi miki na batanci, don haka mu ne tsakaninmu za mu kokawa juna, mu kuma sharewa juna hawaye.”
Jin haka ya sa ta zayyanewa Adda Zubaida komai.
Ita kanta sai da ta girgiza da jin bayanin ‘yaruwarta. “Yaya Zaid din ya fadi haka? To
wai kan wane dalili? Sai ka ce bai yarda da Kaddara ba, to an ce masa kowane ciki
ne zai zube ko kuwa wayo zai yi wa Allah? Ke dai ki rabu da shi, ki yi sha’ aninki kar ki yi fushi, ki daura dammarar jawo hankalinsa gareki, ki na macen da yake so, Karyarsa ya ce zai iya jure zama gida daya da ke a haka. Kin dai gane me na ke nufi? Ki yi ta sa shi kuma a addu’a. Allah ya ganar da shi ya kuma karkato da hankalin shi kanki.” Ta ji shawarar Adda Zubaida, wannan ya sa ta daure zuciyarta, ta Kudurtawa ranta samun Yaya Zaid a yau din nan ba sai gobe ba. Za ta dauki mataki a hannunta, hukunci kuwa na ‘Ya mace, idan ya san wata, ai bai
san wata ba. Don haka dakinta ta koma a sama ta bude wadrof dinta, ta dade tana
tsaye a wurin kafin ta takarkare ta dauki abinda take buKata. Banddaki ta fada ta yi
wanka, ta kalelaye jikinta da turarruka masu dadin Kamshi, sannan ta koma daki ta
shirya a cikin kayan da ta zaba, gyara gashinta ta tsaya ta bata lokaci, ta yi, saboda
ta san abinda Yaya Zaid ya fi so kenan.
Bayan ta gama shiryawa ne, ta Karewa kanta kallo a madubi, ta yi ‘yar dagwas! Da
ita a cikin wata riga mai launin Light peach, an yi mata ado da sheKi, ta samansa,
wanda ya tsuke, bai da cikakken hannu, inda Kasar rigar ta fi sauka daga baya,
wanda aka dinka ta da yadin Chiffon. Jan igiyar rigar ta yi ta daure ta gaba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Wani murmushi ne ya ziyarci labbanta, sannan ta juya ta fita daga akin. Kitchen ta shiga, don ta Karasa kimtsa komai kafin ya shigo.
BABI NA ASHIRIN DA TARA
********
Ba ta yi minti goma da saukowa ba kuwa, ta ji shigowarsa, Karasawa ta yi inda yake,
tayi masa sannu da dawowa. Zaid kam bude baki ya yi da idanu yana duban Umm
Adiyya, cikin mamakin ganinta haka fes! Cikin kwalliya da kimtsi da gyara, rabon da
ta yi kwalliya haka musamman don shi, har ya manta, sai dai ko ya ga ta yi shirin zuwa Ofis da safe.
Gyarar murya ya yi sannan ya ce, “Yawwa, sannu ya gida?’”’ Lafiya.” “Asma na gaisheki, na je wurinsu yau.” Tsayawa ta yi cak! Take ta ji kamar an nausheta. Mamaki ya hanata magana, wai
yau har Yaya Zaid ne zai iya tafiya wani gari ya je ya dawo, bai fada mata ba har sai ya dawo din, za ta san ya yi tafiya?
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE