UKU BALA’I CHAPTER 2
Www.bankinhausanovels.com.ng
Da sauri ta dauke kanta daga barin kallonsa tana jin yarda sautin bugun kirjinta ke kara sauri cikin wani irin tashin hankali wanda sam ba tayi tsammani ba rintse idanu tayi iyakar karfin da taji a jikinta tana faman ambaton Allah komai nata take jin yana kwancewa komai take ji na duniyarta yana juya mata ji take kamar ba kan kafafunta take ba ji take kamar walagigi ake yi da ita jaririn da take daure a jikinta ji take kamar zai kwance ya fadi kasa da sauri cikin rashin abin yi ta kai hannunta zuwa saitin goyan ta rike sosai rikon da ko babban mutum akai wa shi sai yaji kamar za a dauke masa fata haka ta rike zanin goyan tana kara kankame jikinta waje daya ba abin da take jira sai hukuncin da take hangowa cikin idanun mahaifinta take zaton zai yanke akanta.
A sukwane ya iso gareta ba tare da yayi magana ba ya kama kokarin kwance goyon nata ba karamar faduwa gabanta ya kara yi ba har zuwa lokacin idanunta a runtse suke kawai jira take yi taji duka ko ta ina don tuni ta yanke tsammani akan yarda ta ga mahaifinta ya nuna a fuskarsa na matsanancin bacin rai.
“Mariya me ke faruwa ne?”.
Kamar daga sama ta juyo sautin muryar mahaifinta na fadin haka wata irin ajiyar zuciya ta saki gami da buɗe idanuwanta gabadaya ta sauke su akan sa tana mai faman gyada kai bakin ta na motsi.
“Uhmm dama kawai shine…”.
Da sauri ya daga mata hannu lura da yayi yanayinta ya nuna a firgice take sai faman kucincina maganar ta ta take yi.
“tambayarki nayi ba wai cewa nayi ki tsaya kwan gaba kwan baya ba”.
ya fadi yana mai karasa kwance goyon da tayi ya rungume yaron wanda a wannan lokaci barci ya fara tafiya dashi ya shiga dubansu ita da Goggo Marka wacce ta zuba musu ido tana nazarin inda za ta kullo zanar makircin ta.
“Bello wai ‘yar nan daga cewa bayi naje nayi wa uwarta wanka na fito nayi wa wannan yaron kawai ba da baya ashe ta kandami ruwan sanyi tayi daki ta zunduma shi a ciki ina daga bayani na ya saki kara hakan ya sanya ni fitowa a guje ko da na iso ya shaki ruwa har ya fara sheɗewa”.
Marka ta fadi cikin yanayi na dagaske ne abin da ta fadi har da dauko fuskar tausayi ta azawa kanta.
Sosai yake duban Mariya yana karantar yanayin da take ciki yana kuma nazarin maganar Marka akanta yanayin da ya ga ta nuna alamun tsoro da firgici har da yar kwalla ya tabbatar masa ba tabbas a maganar amma saboda kar ya rikitowa kansa kwandon fitina sai ya dubi Mariya yana mai tsuke fuska.
“me kikayi kenan mai yasa baki yi abin da ta ce miki ke yanzu har kin kai matakin da zata ce karkiyi kiyi sannan kuma ina ke ina yiwa jariri wanka sabon haihuwa kuma da ruwan sanyi ina kika taba ganinka haka…”.
caraf! Marka ta dauka.
“yo hankali gareta ba gwanda ta nuna wa duniya uwarta ta haihuwa ba ga wadanda ba su taba zama a gwuiwa da sunan naƙuda ba”.
ta fadi ita ala dole gaskiya take fadi da neman bin da zai harzuka Bello ya jibgi Mariya.
Riko hannunta yayi a tunzure ya jata kiiiii! Sukayi cikin dakin zuwa lokacin ta gama yarjewa kanta babanta dukanta zai yi nan da nan ta fara zubar hawaye tana faman bashi hakuri har suka isa cikin dakin ganin ba kowa aciki da sauri ya dubi Mariya.
“ina Umman taki take?”.
“tana bandaki don Allah Baba..”.
tun kafin ta ajje maganar ta ta yayi wuf! ya ajje yaron ya fice daga cikin dakin da hanzari cikin kiɗima ya isa banɗakin tana yashe kamar yarda Marka ta barta ko motsi kirki ba tayi ta hade jikinta waje guda ta takure kamar wacce ake kokarin rabata da wani abu nata gabansa ne yayi wani irin mugun bugu har sai da yaji kamar kirjinsa zai buɗe da hanzari ya isa gareta ya na faman ajje numfashi mai karfi ya shiga ambaton sunanta amma ina! ba alamun zata motsa balle ya saka rai zata kalle shi jikinsa na ɓari ya shiga kokari gyara mata zanin da ke jikinta ya miƙar da ita tsaye ya haɗeta da jikinsa wani irin rawa yaji jikinta sosai da sosai.
STORY CONTINUES BELOW
Gabadaya ya hadata da jikinsa wani irin tausayinta yaji yake tsaga duk wani sassan jikinsa lokaci guda yaji kwalla na kokarin zubo masa zuciyarsa sai faman zillo take yi tana faman hasasho masa abin da ba ya so ace ya tabbata domin in har hakan ya tabbata yana cikin matsala matuka gaya wanda sam ba zai samu murmushi ya cigaba da wanzuwa a fuskarsa ba.
Cikin wannan yanayin na rashin tabbas da kwanciyar hankali ya isa da Habeeba cikin dakinta ya ajje Mariya dake can gefe sai faman kallo take bin su dashi gaɓadaya ta rasa gane kan wannan lamari zuciyarta sai wassafo mata abubuwa take wanda ba ta tsammanin na dadin rai ne niswa tayi wasu guntayen hawaye suka surnano mata ta sanya bayan hannunta ta dauke su gami da jan hanci.
“Baba don Allah mu koma Asibiti”.
Abinda ta kokarta fadi kenan cikin muryarta mai rawa da kuka a cikinta.
Ba tare da ya juyo ya dubeta ba ya cigaba da gyarawa Habeeba jikinta kamar ba zai yi magana ba domin bai san abin da zai ce bs ko da yayi niyyar yin magana a hankali yake sauke ajiyar zuciya bayan ya kammala gyara mata jiki ya kwantar da ita.
juyowa yayi ya fuskanci Mariya sosai sannan ya dubi Yaron da ke kwance can gefe yana barci amma kuma hannunsa na cikin bakinda yana ta faman tsotsa kamar zai cinye shi da sauri ya kau da kai domin abubuwan tausayawa ne ya suka caki kirjinsa da sauri ya mai da duban sa ga Mariya.
“nima ina tunanin haka Mariya domin kuwa wannan lamarin ya kamata ace an yi duba a kansa…”.
“wai don Allah ba za ka bar maganar asibitin nan bane Bello wai ina tunaninka ya tafi ne ya kamata ka zauna kayi amfani da MIZANIN HANKALI wajan nazarin wannan lamarin kai yanzu ba abin ka gujewa komawa asibiti bane ka duba ta kalau kuka dauki Habeeba zuwa Asibiti amma ka dubi yarsa ta ko tunda kuka dawo ko tarin ta ban ji ba balle na saka ran naji tana cewa wani abu kai ba abin ka tsorata bane da komawa asibiti in har ka na biyewa Maganar Mariya to tabbas zaka kashe matarka da kan ka domin ita yarinya ce ba ta san abin da ya dace da wanda bai dace ba kawai in haukar ta ta yanko mata zance haka zata faɗeshi ba tare da ta duba shi ba”.
“Amma Goggo…”.
Da sauri ta daga masa hannu alamar dakatarwa sa’anan ta daura da cewa cikin yanayi na bacin rai.
“Shawara na baka in har ka ga za ka iya nikam ka ga tafiya ta”.
tana gama fadin haka ta fice daga cikin dakin zuciyarta sai faman sheka dariya take yi son ranta.
Shikuwa Bello tunda ta saka kai ta fice daga cikin dakin duk yaji komai ya jagule masa shiru yayi yama nazarin maganarta tun yana tsaye har ya koma zaune ya zabga uban tagumi komai yake ji ya kwance masa tufkar da yake yi sai faman warwarewa take yi komai ya kwance masa lokaci-lokaci yake ajje numfashi idanuwanta na kan Habeeba wacce ke takure waje guda ya rasa a ina zai ajje wannan lamarin nata ya rasa me ke damunta likita yace masa lafiya ta haihu amma ya za ayi ace kuma magana ta gagareta yi a karan kanta me haka ke nufi ya kamata ace anyi duba a wannan lamarin sake ajje numfashi yayi ya shi tambayar kan sa abubuwa wanda ko wuka a makoshi zai gani ba shi da amsoshin su
sun jima cikin wannan yanayi har dare ya fara shigowa ka fara kiraye kiranyen Sallaha hakan ne ya fargar dasu daga duniyar tunanin da suka lulaƙa da sauei Bello ya mike yana mai duban Habeeba wanda idon ta yake ƙyar sama ko ƙiftawa ba tayi hakan ya dan fadar masa da gaba da sauri ya isa gareta ya dafata gami sa girgizawa sai yaga ta saki ajiya zuciya gami da lumshe idanuwanta wasu hawaye ne suka surnano mata a kunci hakan yay matukar sanya gabansa faduwa da sauri ya zauna kusa da ita yana kokarin tallabo ta.
“Sannu Habeeba me ke samun ki, fada mani don Allah”.
yana magana bakin sa na rawa amma ita ba alamun za ta yi masa wata magana illa kafeshi da ido da tayi.
STORY CONTINUES BELOW
“kiyi magana mana sanar dani abin da ke damun ki”.
numfashi idanuwa tayi lokaci guda jikinta yayi wani irin fizga shi kansa Bello sai da jikinsa yayi rawa da sauri ya zabura yana mai faman jinjigata yana ambaton sunanta amma ba ta yi magana kuma ba ta buɗe idanunwata illa kirjinta dake bugawa kadan-kadan da sauri ya duba in da Mariya ke zaune amma bai ganta ba sam bai lura da ita kusa dashi tsaye ba idanuwanta na faman zubar hawaye
“sai da nace a mai data Asibiti amma a kace ai magana ta akwai yarinta a cikinta wanda ni A KARAN KAINA na san maganata tana sahun da za ajerata a maganganun da za ayi amfani da su domin ceto Ummata”.
Sosai yake dubanta yana kallon yarda hawaye ke safah da marwah akan fuskarta tausayinta yaji yana tsargar masa ko ina na jikinta yana ganin rashin dacewa da kuma kin yarda da yayi da maganar ‘yarsa wacce ta cancani ace an dubata kuma an daurata a mizanin hankali amma bai yi haka ba har sai da ta budi maki ta nuna alamun kin yarda da kayi da ita.
“Mariya ban ki ta taki ba amma ai abin lura nan shine kina jin abinda Goggo Marka ta fadi kan wannan lamarin kin ga ai bai dace ace anyi gangawar mai da ita Asibiti ba domin tun acan ya kamata ace sun sanar damu abinda ke faruwa amma suka ce damu ba komai”.
tun da ya fara magana take dubansa cikin wani irin yanayi da yarda furucin nasa ke sauka wanda ta tabbata ba a son ran sa yake yin sa ba kawai FIN KARFI ake nuna masa wanda haka sam ba zai haifar musu da ɗa mai idanu ba.
nisawa tayi hawaye na kara samun mazauni a fuskar ta.
“ceton rai daban yake a wajan dangin rai ko wani hali kake ciki in har kana da damar ceton wami rai ko ba makusancin ka ba zaka iya don Allah baba na rokeka mu mai da Umma Asibiti”.
“kiyi hakuri sa kukan haka nan za a mai da ita”.
Girgiza kai kawai take yi domin ba ta ga alamun Eh da gaske za ayi hakan ba kawai magana ce akayi ta wacce sam ba alamun za ayi ta a aikace jinjina kai ta shiga yi tana faman sauke numfashi a hankali cikin jan jiki ta fice daga cikin dakin domin ta tabbata in har ta cigaba da tsayuwa cikin dakin komai zai iya faruwa da ita ba za ta iya cigaba da ganin mahaifiyarta cikin wannan hali ba.
Tana fita waje ta hango Goggo Marka zaune kofar dakinta sao faman kai lomar abincin takeyi bakinta wanda ta tabbata daga gidansu Hafsatu aka kawo mata shi ko kuma taje da kanta ta amso da sauri ta kau da kanta domin bata ga amfanin kallon nata ba illa ya kara mata wani takaicin a zucci.
“wai har yanzun Habeeba ba tayi maganar ba?”.
Kamar daga sama ta tsinkayo muryar Goggo Marka tana tambayarta wani haushi ne ya zo mata wuya domin ita dai ba ta ga amfanin wannan tambayar ba ya za ayi kana cikin gida tare da mutum amma kuma kake tambayar ya yake kai da ya kamata ace sai sai wani ya tambayeka gyada kai tayi kamar ba zata tanka ba amma sai kuma ta fara kokarin motsa baki domin amsa mata ‘ta ce mi’ ta ji wani bangare na zuciyarta tace da ita haka sai tayi gum da bakinta tashiga tsayuwa a kofar dakin domin ita dai ba ta san abin yi ba akan wannan lamarin da ta rasa dame zata fassara shi cikin duniyar rayuwarta
“ai wuya makarantar kare ce duk wanda ya ki ji ba ya ki gani ba nidai iyakata ido kuma fadan da yafi karfin ka dadin kallo gareshi”.
Goggo Marka ta sake fadi tana mai kai loman abinci bakinta takaici ya kume Mariya ji take kamar ta daura hannu aka ta kurma ihu da wannan jirwayen gami da shaguɓe da ake antayo mata duban Goggo Marka tayi tana mai faman kada kai ba shiri ta juya ta koma cikin daki abu dai gashi nan ya zame mata goma da ashirin ta rasa ma ina zata dosa da wannan lamarin.
Haka suka rayu cikin wannan dare tsayin lokaci ko wanne zuciyarsa sam ba kayan jin dadi cikinta komai yayi musu kunci abubuwa maras dadi sai faman wuntsulowa suke yi cikin rayuwarsu cikin lokaci kankani ƙaddara ta juya akalar rayuwarsu zuwa wani fikire wanda ba su taba tsammani ba za su kai gareshi.
A daran Mariya tayi kuma matsananci domin kuwa yanayin da ta ga mahaifiyarta a ciki gabadaya susuta ta, ta rasa mai ke yi mata dadi cikin rayuwa bala’in take gani ya na tunkaro mata wanda take tsammani komai na rayuwarta zai iya raguzama mata shi duk wani kudiri da buri da ta daukar wa kanta cikin duniyar rayuwarta ta fara hango rashin tabbatuwarsa tana hango wata bahaguwar ƙaddara na kokarin tafiya da komai nata na jindadi tana kallon yarda ƙaddara ke kokarin sauya mata akalar yarintar ta wanda ta rasa hanyar da za tabi domin dawo da komai a cikin wannan dare.
Nishi take yi kamar mai kokarin haifo ɗa ta direshi a duniyar nan wani abu ne taji yana tokare mata kirji duk sa’ilin da ta ji Ummanta na fizga kamar wacce aka jonawa wuyar wuta take fizgarta.
“Baba kun ki kamar uzuri ne wallahi uzuri na yana da matukar amfani lokaci tafiya yake yi kuma ba waiwayo mu zai yi ba na rokeka da mu nemi abin yi”.
Magana take yi muryarta na kokarin bayyanar da kukan da take boyewa a zucci laɓɓanta sai faman rawa sukeyi ba ta jin tausayin kanta kamar yarda take tausayin dangin rai din nan gudawa biyo domin yalwar kwanciyar hankalinsu shi ne nata.
“Mariya nayi kuskure da na sani tun waccan lokaci na dauki maganarki…”.
Da sauri ta mike jikinta na rawa sosai ta isa gareshi.
“wallahi yanzun ma lokaci bai kure ba na rantse maka da Allah Baba ka taimaka ka tashi mu tafi mu ceton ran da yake da abubuwan taimakawa sosai a rayuwarmu”.
Ido sosai ya zuba mata yarda yake ganin tausayi da jin kai cikin idanuwan Mariya hakan ya kara narkar masa da zuciya cikin tausayinta yana kallon rashin hayyaci yarda yake da wainiya da ita amma karfin zuciya kawai da ikon Allah ke bata kwarin aiwatar da komai in ba don haka ba komai zai iya faruwa da ita.
“mu bari gari ya waye Mariya dare yayi sosai”.
Sosai Mariya ta kureshi da idanuwanta jikinta lokaci guda ya saki ta zube a kasa kamar wani kayan wanki da aka yasar hannu biyu duk ta daura bisa kanta kamar mai shirin kurma ihu amma hakan ya gagara safiyar da taji ya ambata yafi komai kawo mata tashin hankali cikin rayuwarta a wannan Daren ga take yi kamar KAFIN SAFIYA komai zai iya faruwa kundin ƙaddararta zai iya buɗe mata wani shafin wanda bata tsammani zata iya karance shi balle kuma ace hadda za tayi duban su ta shiga yi duk su biyun idanuwanta na faman hargitsewa kamar wacce ya tuntuli barasa ta kai ma karo hannu ta sauke daga saman kanta ganin ihun yaki zuwa ta kurma shi ta gumi ta zuba hannu bibbiyu sai walanniya take yi da idanuwanta.Misalin karfe shidda da rabi suka isa cikin Asibiti bayan sun kwashi dirama ta kin karawa da Goggo Marka inda ta hau ta dire tace ba ta san zancen ba ba wanda ya isa ya koma da Habeeba Asibiti a karasa kashe ta mutane da yawa suka taru yarda kasan an kamo gobara ce ta kama gidan ba ka jin muryar kowa sai ta ta.
“kasan Allah ba za a je da ita Asibitin nan ba ka na kallon yarda kuka je da ita lafiya kalau amma daga dawowarku ko magana ba ta iyayi balle aji abin dake dawainiya da ita ka ga hakan na nuni da zuwa Asibiti ba shi da amfaninin komai illa a kai mace a kashe ta tun lokacin ta bai yi ba”.
Tun da gari ya waye Mariya ke rusar kuka kamar ranta zai fice daga jikinta komai ya kwance mata musamman yarda ta ga Goggo Marka na nunawa a gareta da uwarta na halin-ko-in-kula sosai take jin bacin rai da takaici sosai taken jin komai na kwance mata na duniyarta rarrashi da ban baki ba wanda ba yi tsakanin Babanta da Goggo Marka ba amma saboda kin jini da rashin son gaskiya haka ta tunkuɗeta daga jikin ta ta na faman zazzaga ruwan BALA’I.
“ke dalla janye daga jiki ko na buge ki ‘ya sai shegen makirci da munafurci duk kece ummul-aba’isin faruwar komai kuma wallahi zan ga yarda za a fidda Habeeba da ga gidan nan a mai da ita wajan wanda za suk kashe ta a banza a wofi”.
A fusace Bello ya shiga dakin Goggo Marka in da ta janye Habeeba tun da safiya ta waye taji suna shirin mai da ita Asibiti zaune ya tadda ta jikinta sai faman mazariya yake idanuwanta na faman zubda hawaye fuskarta ta duk ta kumbure da sauri ya isa gareta jikin sa na rawa ya dago gabadaya kamar wata ‘yar tsana ya yo waje da ita nan mutane suka rufa masa baya lura da sukayi Goggo Marka na kokarin hanawa daƙyar da soɗin goshi a ka fidda ita aka saka a Napep Mariya da Bello suka shiga mai Napep din ya ja aka bar Goggo Marka a nan tana ta faman zazzagawa ruwan bala’i ita ala’dole son Habeeba take yi ba ta so a kai ta inda za a kashe ta ba ta duk mutane kallon ta suke ba sun mai da ita wata mahaukaciya.
Lokacin da suka isa Asibitin ba su tadda likita ba don a ranar bai zo aiki asibitin ba ya tafi can cikin garin Minna (General hospital) domin gudanar da wani aiyuka Nurses kawai suka samu kafin su amshe sai da suka gama yi musu tambayoyin ya akayi suka zo duniya sunyi matukar kuluwa musamman Mariya don ji take kamar ta shake wata figaggiyar Nurses mai zubin mociya ita ce kan gaba wajan jera musu tambayoyi sai da Bello ya shiga hada su da Allah da Annabi sannan suka amsi Habeeba cikin matsanancin halin da take ciki sun ba su gado sai da kuma abin da za ayi mata ne ya gagra domin tunda Nurses suka ba su gado suka je suyi zaman jiran likita har ya dawo sannan ya dubata su kam ba su san abin da za a suyi mata ba.
Mariya ce ta dubi mahaifinta bayan sun shafe sama da minti talatin ba wani canji tunda suka zo ko ta kan su ba a sake bi ba hakan ya kara shigan da su halin kaka ni kayi domin dai ga Habeeba nan akwance yarda take hakan take illa lokaci-lokaci tana figza.
“Baba nikam mai zai hana mu kaita wani asibitin tun da nan din likitan bayanan?”.
ta fadi tana mai goge idaniwanta da suka gaji da zubar hawaye.
Zabura yayi jin abinda tace domin tun dazu tunanin da yake tai kenan amma saboda rashin madafa shiyasa ba nemi hakan ba domin ko yace zai dauke zuwa wani asibitin ya san dole a bukaci kudi wanda shi ya tabbata ko wuka za a saka masa a makoshi bai maganin ko taro domin ko Napep din da suka hau bashi ya biya ba bai san ma wa ya ba mai Napep din kudinsa ba shi ya ga ya na sauke su ya ja abinsa yayi gaba zuwan su asibiti yayi ne kawai saboda rashin abin yi bai san yarda za su kasance ba in likita ya zo bai san me zai ce dashi ba.
“Don Allah Baba”.
ta sake fadi ganin da tayi kamar bai yi amanna da maganar ta ta ba.
Gyada kai yayi yana mai sauke ganinsa ga Habeeba sannam ya juyo ya kalle ta.
“naji ki Mariya amma kuma…”.
Sai yayi shiru yana kureta da idanunsa sa kafin ya sauke wami gumi da yaji ya keto masa lokaci guda.
Ita ma kallonsa take yi sosai da sosai cikin rashin fahimtar in da maganarsa ta dosa sai ta shiga gyaɗa kai.
“Mariya ba ni da hali, babu komai a gareni, komai ya kare”.
Sosai take kallon yarda yarda yake maganar kamar mai son fashewa da kuka maganar yake saki kamar ana rike masa kuzarin harsheksa komai da yake fadi kawai fadi yakeyi cikin rashin abin yi zuciyarsa da ruhinsa a hargitse suke dalilin rashin in da zai sa gaba baya so ace ya nuna rashin jarumta a wannan lamarin ba ya so a ga gazawar so ya ya ne amma ba yarda zai yi sosai yake jin kunar zuciya da yarda yake jin wani makakin takaici da bakin ciki da suke tsarkewa waje guda cikin duniyar rayuwarsa cikin kankamin lokaci yana kallo yarda ƙaddara take kokarin buɗe masa sabon shafi na rashin dadi nisawa ya sake yi akaro na ba a dadi har izuwa lokacin.
idanuwan Mariya na kansa tana kallon yarda komai ke sauya ga mahaifinta tana kallon yarda komai ke canza salo cikin rayuwarsa cikin kankanin lokaci ina ma ace tana da wata dama wacce zata yi amfani da ita domin taimakon rayuwarsu ina ma ina ma.
Haka tai ta saƙar zuci abubuwa da yawa take kudiri da buri cikin duniyar rayuwarta wadanda tayi kasafinsu cikin kankanin lokaci.
“na sani Baba amma rashin babu ba zai hana ku ki kai ta wajan da za a bata kulawa ba, kawai mu dauke mu kai ta wani asibitin duƙ da dai ba mu san yarda zata kasance ba, zaman namu hakan ba komai zai kara mana ba illa shiga wani ruɗanin”.
Gyaɗa kai yayi ba tare da ya tanka ba domin ya rasa me ma zai ce sun jima cikin halin shiru kafin ya kokarta motsa laɓɓansa.
“mu kara hakuri, bari naje naji ko ya kusan isowa”.
ya fadi yana mai kokarin mikewa cikin sanyin jiki ya fice daga cikin dakin.
Mariya ta bishi da kallo kallon tausayin su baki daya tana kallon yarda lokaci guda komai yake kokarin kara riccaɓe musu a duniyarsu tana kallon yarda rashin babu yake kokarin hana komai ya tafi yarda ya kamata a cikin duniyar su ta sani ba su dashi kuma ba in da za su je su samu ba su da wata kadara ta a zo a gani da za su saida tayi musu maganin abin da ke damun su sosai take jin tausayin kan su tana tuno irin rayuwar da suke ciki tun kafin wannan ƙaddara ta fara kokarin ruguzu musu cikin rayuwa ta sani babu tayi matukar taka rawa wajan wanzar da komai a duniyar rayuwarsu ta sani ba su dashi komai ma babu su dashi duk da hakan suna godewa Allah da ya ara musu numfashi cikin duniyar nan har suke rayuwa kala daban-daban.
Hannu ta sanya ta dauke hawayem da suke ta faman zubo mata ba tare da ta hannusu ba ta sani lokacin su ne yayi suna da damar zuba yarda suke so duk da dai ta san zubar na su ba wani abu ne da zai taimaka wajan hana wanzuwar komai ba.
duban Ummanta take yi tana faman gyada kai tana kallon yarda Ummanta ta sauya lokaci guda tana kallon yarda Ummanta komai na ta ya sauya wanda za ta iya cewa ba ta da bambanci da GAWA DA RAI eh mana gawa da rai duk mutumin da zai rasa bakin magana ko wani abin yi yana zaune waje guda shi kansa bai san waye shi ba bai san me ke damun sa ba zai iya fadar matsalar sa ba ai ko za a iya kiransa da haka din.
“nima za ki iya buɗe baki Umma ki fadi abin da ke damun ki, ina ma ace zaki iya kwatanta mani abin da ki ke ji a jikin ki da kuma abin da ya assasa rashin maganarki”.
Sosai taji kuka na taho mata hakan ya sanyata saurin yin shiru gami da rufe bakinta da tafukan hannayenta sai faman girgiza kai take yi kukan na kara kokarin sautin bayyana mikewa tayi ta isa gareta cikin hanzari ta kankameta sosai kamar zata koma ciki kuka take yi sosai mai cike da rauni da karayar zucci kuka take yi mai matukar bai wa mai sauraro tausayi da jin kai kuka ne take yi kamar ranta zai fita.
“Umma bana so haka ta kasance a gareki bana so ki kasance cikin rayuwa a haka bana so na ganki a haka har iyakar numfashi a duniyar nan. Ina son ganin ki kamar yarda kike a da koma fiye da haka don Allah Umma don Allah na rokeki”.
Tun da ya tun karo dakin yake jin sautin kukanta kukan da ya sanyi jikinsa sanyi ya samya zuciyarsa cikin wani irin yanayi lokaci guda tausayi gami da jikan ‘ƴar da matarsa gabadaya sun gama galabaitar dashi lokaci guda a duniyar rayuwarsa sosai yake jin zuciyarsa na kuna sosai yake jin kirjin sa na bugawa a dukkan wani karan sautin kukan Mariya in yaji. Wai shin ya zai yi ne, me ya kamata yayi ne?.
Tsayin dakiku ya shafe a wajan kafin ya fara jan jiki domin isa cikin dakin sosai yake jin faduwar gabansa na daduwa sosai yake jin ko ina na jikinsa na canza sautin rayuwa sosai da sosai yake jn wani yanayi na rashin dadi na ywo da shi a sama a gajiye ya isa cikin dakin yanayin da yaga Mariya rungume da Ummanta yanayin da yake kallon kwayar idonta ta canza gabadaya izuwa ja fuskarta ta fara canzawa ita kanta da sauri ya isa gareta cikin tashin hankali a idanuwansa.
“Mariya!”.
ya ambataci sunan cikin wani irin sauti mai dauke da rauni da amon sauti.
“don Allah Baba don Allah na rokeka”.
abin da ta ke fadi kenan cikin sautin kuka ta yo kasa gabadaya ta dafa kafafuwansa sosai yake jin zafin hawayenta dake zuba akan fatar kafarsa sosai yake jin tausayinta.
“na rokeka ka taimaka…”.
“Mariyaaa”.
ya sake fadi cikin sauti sosai.
Hannu ya saka ya dagota gbadayanta ya hadata da jikinta ya shiga bubbugawa a hankali cikin sigar rarrashi.
“Shiru Mariya kiyi shiru, komai zai zo karshe, likitan ya dawo yanzu…yanzu haka yace zai zo kiyi shiru”.
kawai magana yake yi cikin yanayi na karfin zuciya da ya ruhi sosai yake ajje numfashi ga duk wata kalma in ya furta ta.
A hankali ta dago manyan idanuwanta wanda suka canza kala tana mai kallon sa sosai tana son gasgata abin da take ji yana amsa amo a kunnuwanta da kwakwalwarta sosai take jin saukar kowa kalma da yake furtawa ba tare da tace komai ba ta zare jikinta daga nasa tana ja da baya a hankali sosai tayi nisa dashi har ta kai bakin kofar ta kwasa da gudu tayi waje.
kallo kofar da ta fita yake yi zuciyar cike da fargbar in da ta dosa da sauri ya fara kokarin barin dakin amma sai ya tsaya cak! Motsin da yaji da sauri ya juya Habeeba ce ke kara takure kanta waje daya sosai yake kallon yanayin da ya ga tana yiwa jikinta kamar wacce ake kokarin zarewa wani abu dunkulewa take yi waje guda har sai da ta jingina da bangon dake kusa da gadon da take gyada kai yake yi ya rasa dalili ya rasa me hakan ke nufi ya rasa in da zai saka lamarin ya gano ME KE FARUWA? sosai ya rasa komai na tunanin sa lokaci guda sosai yake jin tausayinta na kara samun gurbi a zuciyarsa kau da kai yayi saboda in har ya cigaba da kallon ta hawayensa za su iya zuba bayan HAWAYEN ZUCIYA da yake ta faman dambe da su amma sun ki tsaya.
da hanzari ya doshi kofar ficewa daga cikin dakin tafiya yake yi cikin ikon Rabbi! sosai yake jin komai na canza ji yake yi ina komai zai fice daga jikin Habeeba ya dawo masa ina ma inama.
da wannan zancen zucci ya isa harabar asibitin ya shiga rarraba idanu domin hango Mariya amma ba alamun ko da mai kama da ita ne bai hanga ba da sauri ya fara nufar kofar Get din domin fita waje cak! ya tsaya muryarta da ta keto cikin iska ta kawo wa kunnuwansa duka nan ya shiga waige waige domin canko inda ya ji sautin muryarta ta mai dauke tausayi sosai har ma da kuka a cikinta.
Idanuwansa ne sukayo waje gabadaya gaban sa yayi wani irin bugu sosai har sai da ya kai hannunsa saitin kirjinsa Mariya ya hango ta na biye da likita kamar wacce za ta kifa domin roko da take yi da hannayenta duk biyu idanuwanta na fidda hawaye sosai shi kuwa likitan sai faman tafiya yakeyi kamar bai wata halitta mai daraja na biye dashi ba sosai yayi kunnan uwar shegu da ita rintse idanuwansa yayi ji yake yi wannan lamari kamar ba gaske ba jin komai yake yi kamar a mafarki.
“Yaa Rabbi!!”.
ya furta yana mai dafe kansa sosai ji yake yi yana juya masa ‘yar sa ta cikinsa take bin wani yana yarfata yana wulakantawa ‘yarsa gudan jininsa kaico ba ya fata hakan ya tabbata ba ya kaunar haka ko a mafarki a halinsa su kasance a haka baya fatan rashin babunsa ya sanya ahalinsa cikin wannan irin hali na kaskaci da wulakantawa a hankali yake kokarin bude idanuwansa yana rokon Allah kar ya sake ganin wannan kaskancin.
Girgiza kai ya shiga yi lokacin da ya buɗe idanuwansa ba tare da yayi arba da mugun ganin da yayi dazu ba da sauri jikinsa na ɓari ya koma cikin asibitin dakin da Habeeba take ya dosa yana jin kunar rai sosai bakin ciki takaici duk sun samu mazauni cikin ransa.
Cikin wannan yanayi ya isa dakin tun a bakin kofa ya ja birki yayi turus! idanuwansa sosai sukayo waje likita yake gani da Mariya tsaye kan Habeeba jikin Mariya sai rawa yake yi sosai da sosai takaicin sa ya kara daduwa lokacin da ya lura da irin kallon da likitan ke wa Habeeba hannunsa a harɗe.
*”eclampsia”.*
Abin ya likitan ya fadi kenan ya na faman gyada kai yana kyaɓe fuska kamar wanda ya ga wani abun ki.
Mariya da sauri ta dubeshi lokacin da taji yayi magana sosai take kallonsa kamar mai son karin bayani bata fuskanci abin da yace ba bata gane me yake nufi da kalmar da ya furta.
Nisawa tayi tana kara kureshi da ido shi kuwa sai faman jinjiga kai yake yi har zuwa wannan lokacin hannunsa na harɗe a kirjin sa.
laɓɓanta ta motsa alamun son yin magana.
“Uhmm…”.
Sai kuma tayi shiru ganin irin kallon da ya cilla mata.
“ai kin ji abin da na ce ko?”.
ya fadi gami da daga mata girarsa.
Da sauri ta shiga gyada kai alamun a,a ba ta fahimci mai yace ba amma sai ya nuna ko a jikinsa domin shi ana nashi bahagon tunanin nuni tayi masa ta fahimta daga kafada yayi gami da juyawa domin ficewa daga cikin dakin.
“Likita!”.
Mariya ta fadi cikin sauti mai dauke da rauni sosai kafin ta dora da cewa.
“Taimako don Allah na rokeka”.
ta karashe tana mai hada hannayenta waje guda alamun roko idanuwanta cike da kwalla.
Sosai yake kallonta bayan ya tsaya jin ta kirasa idanuwansa manya jajaye ya sauke akanta yana faman gyada kai kafin ya saki nishi kofofin hancin sa duk suka buɗe gabadaya kamar wanda ya gaji da gudu fuskar nan tasa bakinkirin sai faman yatsine ta yake yi gami da tabe bakinsa mai kama da jikankiyar ganda.
“Me ki ke so nayi miki yanzu?”.
ya fadi ya na shafar runbuɗeɗan cikinsa mai kama da cikin yan tagwaye wata tara.
Rausayar da kai tayi kwallar da take makalewa suka zobo a kuncinta.
“Taimako don Allah…”.
“Taimako fa kika ce, nikam wani irin taimako zan yi miki a yanzu?”.
Sosai taji gabanta ya buga jin irin kalamansa da kuma nuna halin-ko-in-kula da ya nuna akan ta da kuma maganarta hawaye taji sun sake balle mata ta rasa mai kuma ya dace tayi lallami da ban bakin ta duk sun kare iyakar roko dai ta nema a wajan sa amma duk hakan bai saka ya jikanta ba ko ya ya ne sai kace mara imani da tausai a ran sa gyada kai ta sake yi tana dubanda har da wani murmushi ta saki wanda ita kanta ba ta san daga ina ya fito ba bata san amfanin yin sa ba illa wani kullin abu da taji ya tokare mata zuciya da ruhi.
“Uhmma ban san mai zan ce da kai ba kuma amma… Uhmma taimako dai nake nema”.
ta karasa tana mai sake kai hannu bakinta domin wani irin kuka ne taji yana tasowa tun daga ruhi da zuciyarta yana kokarin samun masaukin a laɓɓanta da sauri ta kallo da kai daga kallonsa sosai take jin haushi a zuciyarta haushi akan likitan da bashi da tausai ko ya ya ne a zuciyarsa ba imani.
Kallon ta yake yi da irin halin da take ciki sosai yake jin wani abu a ransa amma sai ya kau dashi da sauri gami da jan tsaki ya juya cikin sassarfa yana kokarin barin cikin dakin.
A bakin kofa ya ci karo dashi tsaye fuskarsa a tamke kamar bai taba wani abu wai shi murmushi ba sosai yake kallon likatan ciin yanayi haushi da takaicin abin da yayi wa ‘yarsa sosai yake ji kamar ya shako wuyarsa ya hada da bango domin ban ga amfanin sa ba, ba irin wadannan mutanen ake so cikin aikin likitanci ba, ba irin wadannan mutanan ake so a wajan taimako da jin kai gami da tausai ba.
Haka ya cigaba da kallonda har ya rabashi ya wuce ba tare da ya tanka masa ba illa wani irin mugun kallon tsana da yake bin sa dashi ransa a matukar bace ya juyo yana duban Mariya wacce take tsaye waje daya kamar wacce aka dasa sai faman sharar kwalla take yi.
“Me ki kayi kenan Mariya, ina amfanin haka wa yace miki irin wadannan mutanan ake neman taimako wa wajansu?”.
rintse idanu tayi wani ɗaci take ji tun daga kasar ruhinta har zuwa zuciyar.
“na rasa ya za nayi ne, komai ya kwance mani na dauƙa duk mutane iri daya ne a duniyarnan in kaje neman taimako za suyi maka”.
ta karashe tana mai tura laɓɓanta cikin baki gabadaya tana cizawa sosai take jin haushin kanta duk da karancin shekarun ta amma hakan bai hanata jin daci a ranta ba akan abin da bakin mutumin nan mai kama da gwanki ya yi mata ta tsane shi tsana mai tsana ni a rayuwarta ko fuskarsa bata muradin sake gani.
“in jiwa ya fada miki mutane iri daya ne? A halinta ne suke iri daya amma a DABI’A da hali suna da bambanci sosai da sosai”.
Sosai take jin kalaman mahaifinta na shiga cikin kunnuwanta tana fahimtarsu daya bayan daya tana gasgatawa.
‘na tsane shi bana son sake ganin sa, ko A MAFARKINA’
abin da ta ambata kenan cikin kunar rai a zuciyarta tana mai faman dauke hawayen fuskarta
“ina kika ganshi har kike kokarin shiga wani yanayi na rashin jindadi rai”.
gyada kai tayi kamar ba zata amsa masa ba can kuma ta nisa.
“na dauka shine likitan da ake jira shiyasa naje na sameshi da kaina domin ganin da nayi lokaci tafiya yake yi”.
ta karashe tana mai yamutse fuska gami da yarfar da hannu.
Sosai ya fuskanci in da ta dosa tunaninta shine likitan da aka ce zai zo ya duba Ummanta.
“ni ban ma san shi ba ko da na kawo Ummanki ba shi bane ya dubata wani daban ne…”.
Sallamar Dr.Aqeel ne ya sanyashi saurin jinkirta zancen sa ya mai da idanuwansa gareshi ita ma Mariya duban mutumin da yashigo takeyi wanda lokaci guda tayi amanna shine likitan da Babanta ke magana.
“Sannunku ko, ya mai jikin?”.
abin da Dr.Aqeel kenan yake fada fuskarsa na bayyanar da yanayin jimami da sauri ya isa ga Habeeba sosai da sosai yake dubata tsayin wani lokaci kafin ya saki ajiyar zuciya ya dubi Bello da Mariya cikin fuskar tausai
“Uhmm…”.
Abin da yayi kenan cikin cizon laɓɓa yana mai sake duban su.
da sauri Mariya ta isa gareshi.
“Uhmm Likita don Allah…”.
“karki damu na san halin da kuke ciki dukkan ku kuyi hakuri dole ku shiga damuwa da tashin hankali musamman lamari irin wannan wanda ba ku san ina ya dosa ba eclampsia take fama dashi”.
Sosai kalmar da ya furta tashiga yi musu yawo akai cikin rashin fahimtar kalmar wacce lokaci guda Mariya ta gano irin wanda waccan bakin mugun ne ya fadi dazu amma kuma ba ta san me nene ba bata san mai kalmar ke nufi ba?.Sun jima cikin shiru aka rasa mai tankawa a cikinsu, domin sun saki baki ne suna jiran cewar Likita. kamar yarda shima yayi shiru, yana nazarin ta inda zai fara yi musu bayanin lamarin.
Ihun da ya karaɗe dakin ne ya dawo da su daga duniyar shiru da na tunanunnuka da suka faɗa a firgice duk sukayi kanta cikin matsanancin tashin hankali sosai take ihu gami da fizge fizge tana hada kanta da karfen gadon da take hannayenta duk biyu ta rufe kunnuwanta da su da sauri Mariya ta isa gareta tana kokarin rike amma wani wawan fizga da tai gabadaya Mariya tayi kasa ta zube hakan da Bello ya gani da sauri ya isa gareta da taimakon likita shiga kokarin riketa amma ina! wani karfi ne ya ke zuwa mata lokaci guda sosai take fizge fizge su kan su sun rasa yarda za suyi su riketa sai da sukayi da gaske sannan Bello ya samu da kyar ya rike hannayenta ya hadata da jiminsa ta kankame amma gabadayam su sai jikinsu ya kara shiga wani irin shock kamar an jona su da wayar wutar nepa sai mazari jikinsu ke yi.
Da ƙyar da soɗin goshi suka samu fizge fizgen nata ya ragu dalilin irin rikon da Bello yayi mata ba na wasa bane.
Kuka ne ya sake karaɗe dakin amma wannan karo kukan yao ne dake cam yashe wanda sam suka manta da lamarin sa tun da suka shigo Asibitin.
Gabadaya sun manta dashi, sun manta sun zo da wani dangin rai bayan su gabadaya suka juya suna kallon daga in da kukan yake tasowa suka shiga kallon-kallo a tsakaninsu.
Mariya ce ta mike da gudu cikin tsananin faduwar gaba ta isa gareshi ta sungomo shi gami da haɗeshi da jikinta wani irin tausayin sa da kauna taji yana kara wanzuwa cikin jikinta sosai take jin tausayin sa hawaye sai zuba suke saman fuskarta suka gangarowa bayansa gyaɗa kai kawai take yi komai gani take yi yana faruwa kawai amma ta rasa komai na hayyacinta komai kara rikice mata yake yi.
“Yaa Rabbi!”.
ta fadi cikin tashin hankali kafin ta fara tafiya cikin ɓarin jiki ta isa ga Doctor dake ta faman kokarin ganin Habeeba ta daina fizge-fizgen da take yi.
“Likita Taimako don Allah kar bugun yayi yawa na tabbata in dukan yayi yawa komai zai kara jagulewa kanina don Allah ina bukatar rayuwarsa shima shi kadaine dan’uwa na a duniyar nan uwa daya uba daya…”.
ta tsahirta da maganar da take yi kirjinta taji yayi mata nauyi sosai da sosai kafin ta sake kokarta daga laɓɓanta.
“Tun da ya zo duniyar nan..ya fara cikin karo da komai da komai na rashin jin dadi ko..ko abinci bai iya samun ci ba a duniyar nan”.
yanayin sautin da ta ajje furucinta dauke da kuka yayi matukar shigar da likita cikin wani irin yanayi da sauri Dr, Aqeel ya dago kan sa dake wajan Habeeba wacce izuwa wannan lokacin fizgar da take yi ya lafa illa numfashi mai karfi da take ta faman ajjewa.
Sosai yake kallon Mariya yana jin tausayinta na shiga ko wani lungu da saƙo na jinka sa numfashi ya ajje ya na duban Bello a hankali ya furta.
“Gaskiya ne wai haka ba ku ba shi komai ba?”.
Gyada kai ya shiga yi domin bai san abin da zai ce da Dr.Aqeel ba. bashi da abin cewa komai ya sauya masa tunani hankalinsa na kan Habeeba ya sani yana son ɗansa amma kuma ita rayuwarta ya fi so sosai da sosai.
“Uhmm amma likita…”.
Ido ya zaro waje sosai yana duban Bello cike da fargabar abin da yake sanar dashi wanda lokaci guda ya gasgata maganar Mariya.
“Eh haka ne kenan?”.
Dr.Aqeel ya tambaya idanuwansa kafe akan Bello. kai ya shiga gyaɗa masa alamar haka sosai da sosai Dr.Aqeel abin ya taba masa zuciya tausayin jaririn yana ɗalsar masa a rai da ko ina na jikinsa da sauri ya waiga ya kalle shi hannun Mariya yanayin yarda yaga yasaka hannayensa a baki ya tabbatar masa da haka din.
Da hanzari ya fice daga dakin ransa a bace cikin yanayin ganin rashin kulawarsu da nuna adalci ga ɗansu da suka haifa bai kamata ace ɗa jariri dan kwana daya ba ya fado duniya ya ci karo da horan yinwa ina wannan ba adalci ba ne sam!.
“likita ana bashi ruwa fa”.
Bello ya fadi cikin ɗarɗar ganin yanayin da Dr.Aqeel ya nuna a fuskarsa hakan ya tabbatar masa ba su kyauta ba sam!.
sarai! Dr.Aqeel ya ji abin da Bello ya fadi amma hakan bai rage masa jin haushin da yake yi akansa ba.
Mintina goma ya shafe sannan ya koma cikin dakin hannunsa dauke da flas na jariri wacce take dauke da tatacciyar madara wacce ta samu hadi sosai sai gorar ruwa kuma shima dai da ka gani za ka gane na bukata jariri rai ne shigowarsa ya sanya Bello saurim miƙewa daga zaune da yake ya zabga tagumi hannu bibbiyu ita kuwa Mariya har wannan lokacin tana tsaye rungume da karirin.
ko Kallon in da Bello yake bai yi ba ya doshi Mariya.
“Zauna”.
ya fadi yana mai janyo mata kujera dake girke kusa da ita ba musu ta zauna idanuwanta akansa ganin yanayin da fuskarsa ta nuna na rashin wasa.
Mika mata flas din yayi, ba musu ta sanya hannu ta amsa duk da dai ba ta san ya za tayi masa ba duk da dai ta fahimci abin da yake nufi da abin da ya bata sai dai ta ya ya za ta bude har tayi amfani dashi a dan tsora ce ta dube shi.
“Uhmm ya zan yi?”.
bai tanka mata ba illa amsa da yayi ya buɗe mata gami da kaiwa bakin yaron sannan ya saki alamun ta riƙe da sauri ta rike ta sake gyara mata zama a bakin yaron kamar wanda yake ji a dora masa haba! ai sai ya shiga ja kamar zai tsinke bakin har wani sautin kara ke fita na tsotsa da yake yi dosai yake sha Mariya tana kafe da ido sai take jin tausayinsa ta na jin haushin rashin bashi abinci da ba su yi ba ta san laifin su ne a ciki sosai da sosai.
Wata irin ajiyar zuciya ta saki mai karfi ta daga kanta ta dubi Dr. Aqeel da ya kure yaron da kallo yana jin tausayin sa sosai.
“Godiya mai yawa likita”.
Dubanta yayi kafin ya dauke kansa ya fara taku daya bayan daya har ya isa ga Habeeba a daidai lokacin wata Nurse ta shigo hannunta dauke da wani farantin silba mai kyau sai dauƙar ido yake yi ta iso gaban Dr.Aqeel ta tsaya gami da rinsinawa alamun girmamawa.
Hannu ya saka ya dauki abin gwaji da suke amfani dashi mai kama da iyafis sanyawa yayi a kunne sannan ya tunkari kirjin Habeeba da dayan bangaren abun a hannunsa ya dora sosai yayi shiru cikin natsuwa yana fahimta komai gami da gyada kai yana jujjuya idanuwansa tsayin wani lokaci kafin ya sauke ajiyar zuciya mai karfi ya zare abun idanuwansa akan Habeeba wacce itama idanuwanta a buɗe suke akansa a hankali ya dauko ledar ruwan (drap) dake kan faranti ya ratayeta akan dan dogon karfen dake girke a bakin gadon sannan ya dauko wata allura ya tsira cikin ruwan har guda biyu a hankali ya fara kokarin gyara mata hannu sosai yake kula da yanayinta bai som a samu wata mata yake yi a zuciyarsa a hankali ya tsira mata allura a jikin fatar hannunta yayi saitin komai yana kula da yanayin ruwan fara kokarin shiga jikinta sosai ya gyara mata komai kafin ya dube wanda ko gezau ba tayi ba da allurar ta shiga jikinta murmushi yayi wanda iyakarsa laɓɓan bakinsa.
Bello da tun ɗazu yayi ka sake yana kallon sarautar Allah sai yanzu ya ajje numfashi har da ‘yar guntuwar kwallarsa duban Dr.Aqeel yake sosai yake jin kaunar sa a ransa yana jin yarda jindadin abin da yayi masa yake ratsa masa zuciya bai san da wani baki zai masa godiya ba bai san da wani ido zai kalle shi yace dashi ya gode ba ya san duk wata godiya da zai masa tayi ƙanƙanta zai yo masa fatan alheri dafatan nasara cikin rayuwar duniya da lahira.
shiru yayi sosai yana jin wani abu nayi masa yawo akai batun kudi dole ya nemo kudi domin yasan dole a bukaci kudi cikin lamarim nan gabansa ne ya yanke ya fadi lokaci guda ya shiga ambaton HASBULALLAHU WANI’IMAL WAKIL
sosai yake jin tashin hankalin abin da zai faru nan gaba kadan me zai ce da wannan likitan mai mutunci da YAƘANA me zai ce dashi in ya dauko masa batun neman kudi.
‘Yaa Rabbi!’
ya ambata a zuciyarsa wani irin gumi ne yaji yana keto masa ta kowani kafar gashi dake jikinsa sosai yake jin gumin na gangara saman fatarsa sosai bugun zuciyarsa yake ji yana ɗaduwa
“Raina ya baci matuka gaya akan abin da kuka aikata ga wannan rai da bai san komai ba a duniyar nan. Bai kamata ace daga fadowarsa ya fara gamu da BALA’I na horon yunwa bai ya kamata ace kun bashi kulawa a matsayinsa na wanda bai san kansa ba bai san wanene shi ba, bai san ya zai yi ya kula da kan sa ba, bai sam ya zai yi abu wani abu a rayuwarsa ba, sosai da sosai naji haushi”.
Ya karashe yana lanƙwasa yan yatsun hannunsa suna fidd sauti juya yayi ya dubi Mariya da ta kafe shi da idanu hannunta rike da flas din da alamun jaririn ya sha yayi nakas har yaji ba wani sauran gurbi da yayi saura a cikinsa da sauri ta sauke kai ganin yana kallonta.
“me yasa kika daina bashi?”.
ya fadi yana mai da kallonsa ga yaron da yayi shiru yana lumshe ido kamar mai son bingirewa da bacci.
Kanta akasa ta fara motsa laɓɓanta.
“ya koshi ne na gani, ina sanya masa ya na turewa”.
Gyaɗa kai kawai yayi ya dubi Habeeba wacce a wannan lokaci bacci mai nauyi yayi gaba da ita. ajje numfashi yayi mai dan karfi.
“wani hali muke ciki likita?”.
Bello ya kokarta fadi cikin rashin abin fadi, yanayin da yayi maganar gabansa na bugu kadan kadan domin bai san amsar da za a bashi ba.
“sosai take cikin damuwa sosai rayuwarta ke cikin matsala sosai komai na rashin jindadi yake yawo a duniyar rayuwarta na san ka san haka”.
Dr.Aqeel ya fadi yana mai kafeshi da ido kallo ne yake yi masa na TUHUMA da son karin bayani da kuma son samun wasu abubuwa masu kama da satar amsa akan lamarin.
Shiru yayi abubuwa da yawa suke dawo masa akai game da Habeeɓa da irin halin da yasan tana ciki na rashin jindadin rayuwa da damuwa kuma dake ci mata dunduniyar duniyarta gyada kai yayi gami da duban Habeeba sosai yake jin tausayin ta a ransa da ma jiki baki daya.
“Haka ne”.
ya fadi cikin raunin Murya.
“mai yasa haka, meye dalilin faruwar haka, kasan kuwa illar dake samu mace mai ciki in tana cikin damuwa kasan wahalar kuwa da take gamuwa da ita kasan irin kuncin rayuwar da take shi kuwa…”.
Ya tsahirta da zancen nasa ya na faman ajje numfashi.
“ba kuyi mata adalci ba a rayuwa sam! ya kamata ace tana samun kulawa da kwanciyar hankali a gareku da kuke kusanci da ita sosai da sosai ba ma wannan ba yanzu kusan halin kuwa sa take ciki kusan abin da ke tafe da rayuwarta yanzu kuwa to a gaskiya komai zai iya faruwa da ita a kowani irin lokaci”.
“kamar ya?”.
Mariya ta furta ba tare da tashirya yin furucin ba zumbur ta mike tsaye idanuwa warwaje take duban Dr.Aqeel sosai take jin maganganunsa na saukar mata da tashin hankali mai matukar yawa zuciyarta ta shiga zarya kirjin ta na bugu sosai.
“Don Allah…”.
“kiyi shiru tukunna”.
Dr.Aqeel ya tare ta daga maganar da ta dauko tun kafin ta dire.
“ta gamu da cutar jinjiga wacce a turance ake kira da eclampsia a na samun tane dalilin yawan damuwa in har mai ciki tana da damuwa har tayi mata yawa ta kan haifar mata da cutar hawan jini daga wannan lokacin har zuwa lokacin da za ta haihu komai zai iya faruwa da ita har ya kasance bayan ta haihu ta gamu da cutar eclampsia wato ciwon jinjiga”.
ya tsahirta yana kallon su kamar yarda suma sukayi kasaƙe suna sauraron sa ya nisa gami da dorawa.
“cutar ta kan kasance ga mai ita kamar ta hauka mutum mai cutar eclampsia ya kan kasance kamar mahaukaci komai yakan iya sauywa na rayuwarsa ya kan kasance mai fizge fizge ko kuma ya dinga zunduma ihu a ko wani lokaci a takaice dai duk macen da ta gamu da irin wannan cutar tan zama tamkar mahaukaciya”.
Sosai sautin kukan Mariya ke tashi cikin dakin kuka take yi wanda bai da sauti sosai amma hakan bai hana ya gauraye dakin ba sosai take jin tausayin Ummanta da ita kanta da Mahaifinta tun da Dr.Aqeel ya fara jawabin sa take jin komai na tashin hankali na wanzuwa gareta da sauri ta isa gareshi ta durkushe har tana kokarin sakin jaririn dake hannunta.
“Don Allah karka ce Ummata ciwon hauka take yi don Allah likita na roke da ka taimaka kar Ummata da gamu da wannan BALA’In cikin duniyar rayuwarta komai zai iya faruwa da kta ba ita ka dai ba har da mu”.
Sosai kuka ya kwace mata tashiga yin sa kamar ranta zai fita.
Ido kawai Dr.Aqeel ya zuba mata yana kallon halin da take ciki sosai da sosai yake jin tausayinta karamar yarinya kamar ta amma ta fara gamuwa da irin wannan laro tun kafin ta gama sanin ita wacece duban Bello yayi wanda shi gabadaya ya gama susucewa hannu bibbiyu ya sanya ya tallabe haɓarsa sosai yake jin komai na rashin dadi na wanzuwa a gareshi sosai yake jin HAWAYEN ZUCIYA na safa da marwa a gareshi domin duk jarumtakarsa na hana idaniyarsa ZUBAR HAWAYE bai hana zuciyarsa kokawa ba.
A tausashe Dr.Aqeel ya sake dubansu cikin son kwantar musu da hankali.
“Idan mace tana zuwa awon ciki akai akai likitoci kan yi saurin gano za ta iya kamuwa da eclampsia ta hauhawar jininta. Dan haka za su yi iya kokarinsu gurin ganin sun dakile aukuwar hakan, ta gurin ba ta shawarwari da kuma magunguna. Amma matan da basa zuwa awo sun fi kamuwa da cutar ta eclampsia mai kama da ciwon hauka. Duk da ce wa wasun ma ko suna zuwa asibitin suna kamuwa da ita.
Idan mace ta hadu da ciwon kwakwalwarta ce kan juye tamkar na mahaukaci. Dan za ta yi ta surutai da hauka ba tare da ta san tana yi ba. Amma idan aka dage da magani za ta warke.
Wasu kuma idan abin ya taba su sosai ko da sun warke rayuwarsu za ta canja ba kamar da ba, maganarsu da mu’amalarsu da kun gani za ku ce sun taba hauka”.
dakyar! ya tsahirta ganin wani tashin hankali da ya sake wanzuwa a fuskokin su ba kamar Mariya domin kukanta kara tsananta yayi cikim haka ta shiga kanƙame yaron dake hannunta sosai hawaye ke zuba a fuskarta.
“Shikenan ta faru ta kare”.
abin da ta iya fadi kenan cikim hanzari ta mike daga durkushen da take ta nufi in da Ummanta take kwance cikin halin barci sosai dubanta take yi sosai kafin taja wani Numfashi mai karfi tana kara kanƙame yaron dake hannunta ta daga laɓɓanta dakyar domin jin kirjinta take yayi mata nauyi sosai kamar an dauko katon dutse an dora mata.
“wai da gaske Ummata damuwa kika saka a ranki wai haka ne inji likita…”.
ta tsaya da maganar tana cizon laɓɓan bakinta na kasa tana mai nuna Dr. Aqeel kafin ta dora da cewa.
“me yasa haka Umma mai yasa kika saka damuwa a ranki har hakan ta faru ina son ki sosai da sosai Ummata bana son abin da zai taba min rayuwarki don Allah ki tashi sannan ki ciwa likita kin cire damuwar da yace ki na saka wa a ran ki san hakan zai sanya wannan cutar da yace kina da ita zata bar ki bana son komai ya zamto da gaske bana so naji wannan DAYA BALA’I akan ki don Allah ki tashi ki fidda komai a rank…”.
“Mariyaa”.
Cak! ta tsaya da maganar ta ta jin muryar da ta ambaci sunanta cikin sauti mai dauke da kin abin da take fadi.
“Ya haka Mariya ƙaddara ce hakan jarabawa ce daga Rabbi!”.
sosai ta juye ta na duban Dr.Aqeel sosai take jin sautin maganarsa na amsa kuwwa akanta sosai take jin za ta iya yin shiru ta amshi maganarsa amma ba tabbacin zuciyarta za ta iya amsa kau da kai tayi.
Bello ne ya taso cike da sanyin jiki ya isa in da Mariya take ya janyota jikinsa yana bubbuga bayanta yana jin yarda zuciyarta ke harbawa sosai cikin sakanni yama jin yarda tausayinta ke ratsa masa zuciya sosai yake jin zafi a ransa game da wannan lamari.
Sun jima cikin wannan hali tsayin lokaci ba wanda yayi kokarin yin magana a tsakani Dr.Aqeel yayi gyarar murya kafin yace,
“ya kamata ace izuwa wannan lokaci kun gayyato natsuwa cikin duniyarku…”.
“Ya ya hakan zata kasance Likita”.
Sai lokacin Bello ya samu motsa laɓɓansa ya furta hakan.
Sosai Dr.Aqeel yake dubansa musamman tashim hankalin da ya hango girke cikin idanuwansa ya sani dole su ji ba dadi dole si u ji wani iri a ransu musamman irin wannan lamarin da yake da wuyar gane akan wanda mai sansh ba ya sani dole su tsorata sosai da lamarin saboda ganin bakon abu ne a garesu.
Sai dai abin da Dr.Aqeel bai sani ba abin da ke damun Bello shi lamarin Habeeba ya yarda za a bukaci kudi da ya san ba shi da su sam! a bangaren halin da Habeeba ke ciki ya sani komai daga Allah ne komai in ya faru da bawa muƙaddari ne to ya dauka komai ya faru da Habeeba Ƙaddararsu ce daga Rabbi! ba yarda za suyi zai sanya hammu bibbiya ya karba.
“likita naji bayanin kumana gode, da wannan fahimtarwa da kayi akanmu mage da rashin lafiyar da Habeeba ke ciki sai dai kuma Uhmm…”.
Sai kuma yayi shiru ganin irin kallon da Dr.Aqeel ke yi masa mai dauke da murmushin karfafa guiwa ya nisa.
“kar ka damu komai zai zo da sauki da yardar Allah”.
Gyada kai kawai yayi ba tare da ya sake cewa komai ba Dr.Aqeel ya mike yana mai duban Mariya dake takure waje guda sai ajiyar zuciya take kamar wacce tayi gudun ceton rai.
“ki kula dashi sosai in ya tashi kafin na dawo ki sake bashi madararsa ga ruwa nan ma zaki iya bashi amma dai ya fi kyautatuwa ki bashi madarar kawai”.
gyada kai kawai take yi domin bata da karfin iya bude baki ta ce wani abu don ji take bakin nata yayi mata nauyi sosai da sosai.
“Mun gode”.
Bello ya fadi lokacin da Dr.Aqeel ya juyo da kallon sa gareshi ya fara tafiya domin barin dakin.
“zan dawo nan da minti talatin don Allah ku kula sosai komai kuka ya faru kuyi hanzarin nema na kafin lokacin dawowa ta”.
Daga nan bai sake cewa komai ba ya fice daga cikin dakin yana duban hannunsa mai daure da wani ratsattsan Agogo mai kalar whiter and Blue sosai Agogon ya dace da hannunsa mai cike da kwantacciyar suma baka mai dan haske sannu a hankali yake takunsa cike da natsuwa har ya karasa ficewa daga cikin dakin idanuwan Mariya na kansa sosai take son halin mutumin mai tattako lokaci guda taji yna burgeta domin taimakon da yayi mata ba ita kadai ba hatta mahaifinta DR. AQEEL MUNKA’IL ya burgeshi sosai da sosai.Sosai ta shiga duniyar tunani tana kokawa dashi a yarda komai yake cakuɗe mata lokaci guda duk wata tufka da take yi ba a zuwa ko ina take wargajewa sosai take tunani wanda ita kanta bayi tsammanin kwakwalwarta zata iya yinsa ba ba tare da ta tarwatse ba hankalin ta sosai ya karkata zuwa ga duniyar tunaninta ta bar duniyar zahiri.
Tafiya take sannu a hankali wanda ita a karan kanta ba ta ina take jefa kafa ba kamar daga sama taji wata irin kara gabadaya ta karaɗe mata kunnuwa cikin yanayi na tsananin firgice ta dawo duniyarta ta na faman ambaton Allah gabadaya ta daura hannu akai ta rasa ita a ina take a wannan lokacin domin ta gama yanke tsammani komai zai faru a lokacin ba mai dadin ji bane sam! cikin duniyarta sosai take jin sautin na sauka a hankali gabanta ya fara raguwa daga faduwa da yake yi a hankali ta fara kokarin buɗe idanuwanta da suke runtse sosai jikinta gabadaya sai karkarwa yake yi kamar wacce aka jonawa wayar wutar lantarki.
“Ke!”.
Kamar daga sama ta ji wata muryar ta amsa amo ga kunnuwanta sosai taji tsawar a ranta sosai da sosai gabanta ya fadi dalilin tsawar a hankali ta daga kanta da idanuwanta da suka rine sukayi jajir sosai.
Tsakiyar titi ta ganta tsaye ga wata bakar mota mai matukar dauka ido gabanta haske rana sai haske yake yi gefe guda kuwa wani matashi ne wanda ba zai hau shekaru ashirin da takwas ba zuwa talatin baki ne dogo mai kaurin jiki fuskarsa doguwa ce mai dauke da dogon hanci da manyan idanu masu kalar barci (sexy eyes) girarsa cike take da suma baka sidik da ita bakinsa dan madaidaici mai dauke da Laɓɓa Pink kala mai duhu kadan haka kansa akwai suma kwantacciya wanda ta samu gyara sosai tayi luf a samankansa sai faman kyalli take yi jikinsa sanye yake da kananun kaya farin wando jeas sai riga mai kalar Ash-colour a gaban rigar an yi rubutu kamar haka *SO MUCH LOVE YOU* da kalar ruwan Gold kafarsa kuwa takalmi mai kalar silifas mai ruwan kasa-kasa sosai da sosai takalmin ya amshi kamarsa mai dauke da dogayen yatsu wanda suka sha gyarar farata sosai.
Lokacin da Mareeya ta gama ƙare masa kallo lokaci guda ta kau da kai gami da jan guntun tsaki kafik ta sake daga idanuwanta ta dube shi shima ita yake kallo wanda kallon ba za ka iya ajje shi a mataki daya ba ne tausayi ne ko na kiyayya
Gefe da gefen titin kuwa tun da abin ya faru jama’a sukayi cirko-cirko suna kallon abin da zai wakana domin har ga Allah kowa ya sadakar mai Motar nan zai yi sama da Mariya sai dai buzunta amma sai Allah yayi ikonsa ko taba bai yi domin kuwa hanzari yayi sosai wajan taka burki.
“ke wacce irin dakikiya ce baki da hankali ne na lura da alamun kan ki akwai ciwo a cikinsa ko”.
Sosai ya ke maganar cikin fada yana faman daga hannu kamar zai kwashe ta da mari yana kara fiddo da manyan idanuwansa waje yana sauke su akan ta ita har zuwa lokacin idanuwanta na kansa sai dai sun cika kwalla sosai kadan suke jira su zubo.
Nisawa yayi bayan ya gama kare mata kallo sosai da sosai.
“a fuska kamar mai natsuwa amma sam ba haka bane na lura ba ke burik rayuwar duniya cikin duniyar ki sam! bakya lale marhabin da duk wani farincikin duniyar nan a rayuwarki”.
sosai take jin sautin kalaman sa na sauka a kunnuwant suna samun masauki sosai take jin daci da bauri a kalamansa sosai take jin ranta yana baci da sauri ta kau da kai daga barin kallonsa bayan ta watsa masa wani kallo wanda a karan kanta ba ta san tayi sa ba.
“In ba ki son Rayuwar duniyar ai gwanda kawai ki fadi ki samu wani ya turmushe ki da mota ko ya gille maki makoshi da wuka ba wai ki zo ki daura mani zunubin da ba nawa ba haka kawai ban san hawa ba sai naji sauka ki jaza mani BALA’I ki bar ni da zaman gidan kaso”.
Ta fara gajiya da kalamansa sosai komai take ji nata yana jin haushinsa sosai take jin bakin cikin haduwa dashi a wannam lokacin.
“ga ki Mace har mace amma bakin san dadin rayuwar ‘ya mace a duniyar nan ba na lura CUTA KAI ki ke dashi kuma bakin DARAJAR dakike da ita ba da kinsan DARAJAR ‘YA MACE a duniyar nan wallahi ba zaki so mutuwa ba”.
A firgice ta dago idanuwanta wanda a wannan lokaci suka fra zubar hawaye ta sauke akansa mamaki ne ya cika mata kwanya sosai a zuciyarta ba abin da take ayya nawa illa anya mutumin nan na da hankali kuwa anya bashi ya dace alakabawa kalmar hauka ba anya bashi ya cancanci a kira mai CUTAR KAI ba anya bashi kansa ke ciwo ba…
“In da ni ce ke wallahi ko hanya da ganganci da BALA’I yake ba zan bi ba ke Tsautsayi in da ana ganinsa billahillazi ba zan doshi in da zai doso ni ba har ya shigo rayuwa ta ba”.
Ta gaji tayi matukar gajiya da jin maganganunsa komai taji nasa ya bata mata rai sosai ba za ta iya tsayawa ta saurare shi ba abin sai yayi yawa da wanne za ta ji da halin da ƘADDARA ta je fata ko kuma da wannan banzayen kalaman nasa da taji masu kokarin haifar da CIWON RAI.
“Malama yasin ki ceci rayuwarki don duniyar nan gidan zamana gidan kuma jindadi…”.
Ba jira ya dora a zancen sa ba ta mike ta fara tafiya a hargitse kamar wacce ta samu tabin hankali tafiya kawai take yi domin ji take yi kalaman wannan mutumin na koƙarin hauka ta mata hankalinta sosai da sosai hannu ta saka ta rufe kunnuwanta domin bata bukatar ta sake jin ko kalma daya ne daga cikin kalamansa ba ta so ko ganinsa ta sake yi ko a badininta domin ta sani Mummunar ƙaddara ce ta jeho shi rayuwarta ba komai ba domin kalamansa sun gama tabbatar mata da halinsa ta lura duniya gabadaya ta gama daureshi tamau har da rararr igiya.
Tafiya tayi sosai mai nisa daga bakin titi sosai take tunani tana faman sharce gumin da yake karyo mata dayake lokaci ne na rana ba wai zafin ranar bace ta dame ta a,a wannan mummunar gamon da tayi ne gabadaya ya kara jagula mata lisssafin ta sosai take jin takaicin fitowarta sosai take jin haushin wanna rana sosai zuciyarta da ruhinta suke zafi komai yana kara lalace mata.
“Yaa Rabbi!”.
Abin da laɓɓanta suka kokarta fadi kenan cikin wani irin yanayi mai dauke da tashin hankali sosai.
Sannu a hankali ta isa gida kafin ta shiga sai da ta tsaya bakin kofa kamar mai kokarin tunano wani abu kafin ta ja dogon numfashi ta doshi cikin gidan baki ta dauke da Sallama tun daga soro ta fara jin rashim mutane a cikin gidan sosai da sosai take jin shiru ya gauraye gidan ba motsin ko dan tsako a cikin sa a haka har ta isa tsakar gidan ta tsaya yana a yarda suka barshi ko alfarmar shara bai ci ba gyada kai tayi kafinta doshi dakin mahaifiyarta.
Sosai take jin tausayin kanta sosai komai ke dawo mata sabo sosai take tuna ranar sosai take tuna komai sosai take tuna mahaifiyarta da komai da ya faru da ita can baya sosai da sosai taji zuciyarta na kara rauni ruhinta taji yana kokarin ajje mata komai kamar yanzu ya faru.
Kuka ne yake kokarin kwace mata wanda ita kanta ba ta san ya akayi ya zo ba ko da yake bai dace tayi wa kanta wannan tambayar ba domin ta sani ABOTA suka kulla dashi wacce ba ta tsammani akwai ranar yankewar ABOTAR.
hannunta duk biyu ta saka ta rufe bakinta domin ji tayi kukan na kokarin ba da sauti sosai da sosai.
Da sauri ta mike tashiga neman abin da ta zo dauka cikin lokaci ta kammala komai ta hada ta dauka komai tana yinsa ne cikin rashin hayyaci domin ta tabbata in ta zauna cikin dakin nan zuciyarta za ta iya bugawa ba za iya zaman sa ita kadai ba bata so ba za ta iya ba Allah ya gani gabadaya gidan ne ba ta son zaman sa a wannan lokaci ba za ta so ace ta zauka ba domin DUHU take gani sosau wanda yake kokari rufe mata idanuwa har ma da zuciya da ruhi a hanzarce ta bar dakin cikin sakanni ta bar cikin gidan gabadaya har zuwa lokacin hannayenta na rufe da bakinta domin bata bukatar kukan ya fasu.
gabadaya hankalinta ya tafi fatan ta ace ta ganta a cikin dakin dakin da mahaifiyarta take tare da mahaifinta ba ta so ace tayi nesa da su bata so ace komai ya fau bata nan tana so ace komai in ya tashi faru ya faru akan idon ta ta shirya ta shirya sosai da sosai komai za ta iya dauka komai da zai faru ta shirya masa zata iya jurewa za ta yi dauka ko meye ma ta shirya masa…
“MACE ƘYANƘYAWA”.
‘Innalillahi wa’inna ilaihir raji’una’
Mariya ta dankara cikin tashin hankali domin wata katanga ce ta ji ta ruguzoma mata mai dauke da bama-baman tashin hankali sosai taji duniyar na juya mata sosai take ganin wasu taurari masu dauke da kayan yankin kawo mata tashin hankali na shawagi a idanuwanta ba ta san lokacin da ta zubda kayan dake hannunta ba ta daura hannu saman kai tana kokarin kurma ihu amma kafin ta kai ga aikatawa taji wani lallausar hannu yayi wa bakinta ƙawanya habawa ai Mariya ji tayi kamar taji ta ta nutse cikin kasa sosai taji jikinta gabadaya ya tsaya cak! duk sani abu mai rai da motsi na jikinta sai da taji yayi mutuwar wucin gadi zuciyarta kuwa ji tayi kamar ta tarwatse tayi daidai sosai komai ya fara dawo mata jikinta ya dau mazari idanuwanta a rintse sosai.
sautin ajje murmushin sa taji ya dakar mata dodan kunni kafin taji sautin muryarsa.
“Anya kuwa na dauka zan ganki a jaruma lamba guda amma sai na ga akasin haka”.
sosai ta sake runtse idanu gami da sanya hannayenta ta toshe kunnuwanta ba abin da take ambato sai Allah a ranta da ruhi.
“Don Allah”.
Ta fadi cikin tashin hankali da rashin abin yi
Sosai yake kallonta da yanayin da ta firgice lokaci guda gabadaya idanuwansa ya juye akanta yayi mata kur! da idanu fuskarta yake kallo bakinta dake rawa yake kallo sosai da yarda ta motsa laɓɓanta ha ta furta ‘Don Allah’.
“Me nayi miki?”.
a dan tsorace ta bude idanuwanta ta kalle shi ta sauke da sauri domin ba tayi tsammanin idanuwansa na kanta ba.
“Kayi Hakuri…Don Allah”.
Miƙar da ita yayi daga durkushen da tayi sosai yake kallonta yana kallon yarda jikinta ke rawa da alamun tsoro sosai take ji akanta murmushi ya saki kafin ya motsa laɓɓansa.
“Ba abin da kikayi mani, ki natsu mana garki ba da mata mana”.
Ba ta son jin muryarsa balle kuma kalamansa wanda take yi wa kallo a yan ta’adda da fashi da makami domin ba komai cikin kalaman nasa sai kokarin kashe rayuwar wani rai.
“Ya sunanki?”.
Ya fadi a wannan lokacin yayi kasa sosai da muryarsa cikin rarrashi.
ta gefen ido ta kalle shi har yanzu idanuwansa na kanta a dam tsorace ta waje idanun nata sosai tana motsi da baki alamun son magana da kyar ta samu ta furta.
“Mariya”.
A nata tunanin in ta fadi zai sake ta domin rikon da yayi wa hannunta ji take yi kamar wuta domin haushi da takaici gabadaya ya rufe ga kuma tsoransa da take ji ya samu waje a zuciyarta ba ta so ƙaddara ta sake watso mata shi a rayuwa ba ta lura ƙaddara sam! ba ta son ta in dai a faggen natsuwar rayuwarta ne.
Sosai taci dacin abin da yayi mata ya taso mata cikin karfin hali ta dago kai ta watsa masa wani kallo mai cike da gargaɗi kafin ta fara motsa laɓɓanta.
“Meye hadi na da kai na dauka tun dazu muka raba gari da kai ko? to don haka ka rabu dani ka fice daga duniyar rayuwata ba abin da ya gama ka dani ina mai rokon ka ka tafi”.
Tun da ta fara magana yake kallonta yana sakin wani irin Murmushi wanda ya dan tsorata ta amma ba ta bari hakan yayi tasiri a zahirin fuskar taba kau da kai tayi gami da jan guntun tsaki.
Lokaci guda murmushin dake kan fuskarsa ya dauke sosai ya ji zafin tsakin da yaji tayi masa yarinya karama har ta kalli tsabar idanuwansa tayi masa tsaki sosai yaji abin a ransa amma sai ya kanne ya sake gayyato murmushi ya daura a fuskarsa.
“MARIYA”.
ya ambaci sunan cikin amo mai sauti ita kanta sai da taji faduwar gaba duk da taji wani iri da yanayin da ya ambaci sunan nata kamar shi ne ya halicce shi.
Ba tanka ba kamar yarda shima baya bukatar haka.
“HUZAIF”.
ya fadi yana mai haɗe laɓɓansa waje daya yana cizawa sosai yake jin daci a ransa sosai da sosai yake jin bakin cikin abin da yarinyar nan tayi masa ba ya tunanin a duniyar rayuwarsa akwai ‘ya mace mai amsa suna mace ta taba kallonsa tayi masa haka ko a cikin mafarkinsa gyada kai yayi.
“Bani da wata niyya akan ki ta cutar wa ki yarda dani in da ni mai cutarwa ne da tuni komai ya tabbata akan ki na cutarwa”.
Sosai yayi kasa da muryarsa ya na furucin yana kallonta ita kuwa kanta na kasa gabanta na faman bugawa duk sakan sosai take jin tsoro da firgice na mamaye ilahirin jikinta zuciyarta tana amsa amo da sunan da taji ya ambata.
Ba ya zata yarda dashi ba ko kadan, domin dukan farko da yayi mata shi ya tabbatar mata da ko shi waye, don haka dole ta nemi tsari dashi a duniyar rayuwarta da sauri ta durkusa tashiga hada kayanta da suka warwatse bayaj ta fizge hannunta daga gareshi ba ta sake bi ta kanshi ba komai yin sa take cikik hanzari da kokarin barin wajan domin ba zaiya cigaba da tsayu dashi ba ko kadan ba ta muradin hakan.
Huzaif mamaki ne ya cika msa zuciya sosai yarda da ya ga Mariya na komai nata cikin nuna halin ko in kula gareshi ya lura sosai cikin idanuwanta akwai tsanarsa hakan ba karamin mamaki ya bashi ba saboda bai san dalili ba shi dai ya san bai yi mata wani abu na cutarwa ba amma yana mamakin yar da tsanarsa ta sami gurbin zama a kwayar idanuwanta wanda ya tabbatar hakan ne har a zuciyarta.
Murmushi ya saki gami da dunkule hannayensa waje guda ya zuba mata idanu yana kallon yarda take tafiya cikin sauri saurin da daka kalle shi ba jarumta a cikinsa domin tafiya take tana hada hanya kamar wacce tayi tatir da kayan maye.
Sosai Mariya take ji a jikin ta ana kallonta tun da tabar wajan domin tasan dole hakan ta faru dama sosai zuciyarta ta shiga saƙar fargaba domin sosai take jin tsoron Huzaif ko da dai bai nuna mata a kalamansa ba amma ta ji a jikinta haushin ta yake ji haushi na sosai da sosai.
Sai da tayi nisa sosai sannan ta ja burki ta tsaya tana mai da numfashi har zuwa lokacin kuma jikinta bai bar sanar da ita ana kallonta ba. A hankali ta juya sosai gabanta ya yanke ya fadi domin hango shi tayi zaune saman Motarsa mai kirar BMW M6 baka wuluk da ita idanuwansa na kanta da sauri ta dauke kai tana mai ambatar.
“Yaa Rabbi! Kayi min tsari da wannan mutumin da yake kokarin bibiyar rayuwata”.
Kara azama tayi a tafiyar ta sosai take sauri kamar wacce zata kifa kallo daya zaƙayi mata ka tabbatar da ba natsuwa game da ita duk in da ta gilma sai an bi ta da kallo domin kuwa gabadaya a hargitse take daurin zanin da yake jikinta abin a kalla ace ba natsuwa ne haɓa daya ta zanin sai faman reto yake yi yana jan kasa kafar nan ta ta bututu tayi da jar kasar dake hanyar da take bi zuwa komawa Asibitin.
Tunda ta bacewa ganinsa ya koma cikin Motar sa ya yi mata Key ya bi bayan ta a hankali har ya isa Asibitin shi ma can gefe guda ya samu yayi Parking ya fito yana karewa Asibitin kallo tunda daga zubin yanayin Asibitin da tsarinsa ya tabbatar sai marasa hali ne masu zuwa cikinsa don shi dai ya tabbata ko mura yake yi ba zai zo wannan asibitin da sunan neman magani ba sosai ya shiga tunanin abin da ya kawo Mariya wannan Asibitin ya tabbatarwa zuciyarta kila wani nata ne bashi da lafiya lura da yayi da yanayin datake ciki ya tabbata nata ne makusancin na sosai da sosai ba lafiya ji yayi kamar ya shiga asibitin amma sai wat zuciyar ta hanashi tana mai tambayarsa in ya shiga yayi me? A matsayin sa na wa zai je gareta? Tambayoyin da suka taru akansa kenan ya fasa shiga asibitin da sauri ya juya ya fada motarsa ya ja ta ya bar bakin Asibitin.
Da shigar Mariya Asibitin ba in da ta dosa sai dakin da Mahaifiyar ta take a kofa ta tadda Mahaifin nata zaune ya zabga tagumi sosai ya shiga damuwa sosai za ka fahimci yana cikin yanayi matsananci.
“Baaba!”.
Mariya ta fadi cikin sauti da rauni a muryarta kamar zata rushe da kuka.
A hankali ya dago idanuwansa da sukayi matukar canza launi sosai tashin hankali ke zagaye da su.
“Har kin dawo Mariya?”.
ya fadi cikin sanyin murya. Gyada kai tayi gami da samun waje kusa dashi ta zauna tana ajje numfashi da kyar.
Ba wanda ya sake kokarin tankawa a tsakaninsu tsayin lokaci suna cikin halin shiru kafin Mariya ta nisa cikin sanyin jiki.
“Uhmm amma Baba ya na ganka a nan zaune wa aka bari da Umma?”.
Ta tambaya tana mai kafeshi da idanuwanta da suke a hargitse.
Shiru yayi ba tare da ya bata amsa ba har ta fara tsire tsammani da amsawar tana kokarin sake magana taga ya motsa laɓɓansa.
“Barci take yi”.
“Har yanzu bata tashi ba?”.
Ta sake tambayarta domin lokacin da ta bar asibitin a cikin halin barci ta bar ta.
“Ta farka ta sake komawa”.
Mariya ta fara motsa laɓɓanta ta na son yin magana sai ga Dr.Aqeel yayi Sallama garesu amsawa sukayi Mariya tayi masa Sannu da zuwa. Murmushi yayi kafin ya ce,
“Mariya har kin dawo kenan. na zo dazun Abban ki ke cewa dani kin je gida”.
Gyada kai tayi gami da kalato Yaƙe ta ajje a fuskarta.
Shiru ne ya tsake ziyartar wajan ba wanda ya sake magana sai ajiyar zuciyoyi dake fiddo da sauti sosai lokaci yaja a tsakanin su har zuwa lokacin ba wanda yake kokarin tsinkawa.
Dr.Aqeel da ke tsaya hannunsa rike da wani File yana dubawa bayan ya gama ya dube su.
“Hala ciki da zafi kuka zauna a nan?”.
“Ko daya Likita kawai gani nayi tana barci na fito nan na zauna”.
Gyaɗa kai kawai yayi bai sake magana ba ya juya bayan yayi musu sallama ya tafi.
Mariya ta bishi da kallo sosai halin Dr.Aqeel ke burgeta natsuwarsa gami da karamcin sa yana kara mata mutuncinsa a idanunta sosai take ganin girmansa tabbas ta yarda ba duk mutane bane suke iri daya a duniyar nan ta yarda halintar Dan-adam daya ne amma halin kowanne ya bambanta ba ta taba tsammanin za su samu mutum mai karamci da taimako irin Dr.Aqeel a da can ta dauka kowa ba mai kirki bane ashe da bambanci.
“Amma Mariya naga kin jima kafin ki dawo ina kika tsaya?”.
Bello ne ya katse mata tunanin zuccin da take yi da sauri ta dube shi tana faman gyada kai sosai ya kafe ta da idanu ganin halin da ta nuna hakan ya kara daburta mata tunani ta rasa amsar da zata baiwa mahaifin nata shin ta fada masa haduwarta da mutumin da ya kusan kashe ta tun lokacin ta bai yi ko kuwa…
“Kika yi shiru?”.
Ya katse mata tunanin da ta afka.
“Uhmm dama ba abin da ya tsaida ni kawai dai wani ne…”.
Sai kuma tayi shiru ta kasa krasaw domin yanayin da ta ga Mahaifin nata ya nuna sai tayi da nasanin sakin bakin da ta so yi domin ta san tabbas sai ya ji ba dadi in har ta fada masa.
“Wani mutum yayi me?”.
Ya fada ya na kafe ta da idanu sosai hakan ya sanya ta shan jinin jikinta a dan daburce ta daga laɓɓatanta.
“Bakomai”.
Shiru yayi yana nazarin maganar tata ya tabbata akwai wani abu amma da alamun ta na tsoron sanar dashi.
“Allah ya kyauta”.
Abin da ya fadi kenan ya koma ya zabga tagumi.
‘Ameen’
Mariya ta amsa ita ma a ranta gami da mikewa domin kai kayan da ta zo da su cikin dakin.
Dr.Aqeel zaune cikin Office din sa gabadaya hankalinsa ya ta’allaka ga File din dake gabanda yana dubawa tsayin lokaci ya shafe a haka lokaci-lokaci yana sanya biro a bakin sa yana cizawa kamar son samu wata amsa daga gareshi.
Kamar dag sama yaji ana knocking din kofarsa a hankali ya daga kai ya kalli kofar na yan dakiku kafin ya mai da File din ya rufe ya ajje shi gefe sannan ya motsa laɓɓansa.
“Yes Come in”.
ya kafe kofar da ido yana jiran ya ga waye zai shigo sai da aka shafe yan sakanni kafin sautin murɗa kofar ya fara kaiwa kunnuwan Dr.Aqeel sako sosai yake kallon kofar har ta gama bude wani matashi me ya bayyana fuskarsa ba yabo ba fallasa ya shiga takowa har ya iso gaban Table din Dr.Aqeel tun da ya shigo yake bin sa da kallo kallon kamar na san ka amma na kasa tuna baya.
“Dr.Aqeel Munka’il”.
ya fadi yana kokarin zama kan daya daga kujerun dake girki kusa da table din fuskarsa dauke da murmushi.
Sosai Dr.Aqeel yake kallon sa shi ma yana sakar masa murmushin yaƙe.
“Dr.Hisham Muktar Karami”.
Wata irin zabura Dr.Aqeel yayi yana mai zaro idanuwa gami da sakin wata yan kara kadan.
“OH My God! Da gaske kake wai ko wasa ko a tunani ban kawo hakan ba”.
ya fadi yana mai hanzarin baro in da yake zaune ya iso gareshi gami da kai masa wata irin runguma sosai suka sarke a junansu fuskokinsu dauke da murmushi da jin dadi da farinciki sosai sun jima haka kafin su saki juna har zuwa lokacin idanuwan Dr.Aqeel su na kan Dr.Hisham sosai yake kallon sa gani yake yi kamar ba shi ba.
“Please Zauna mana Dr.Hisham ashe rai kan ga rai a duniyar nan ko a mafarki ban yi tunanin zan sake ganin ka ba”.
ya karaeshi yana kokarin isa wajan karamin firij din dake girke a can gefe.
“Hmm Dr.Aqeel kenan ka yada zumunci shiyasa sam ka man ce da in da nake”.
shima ya fadi yana dariya yana bin cikin Office din da kallo yana mai murmushi sosai da sosai ya burge shi musamman tsayin da akayi masa komai nashi tsaf-tsaf dashi.
“Yaa Allah! stop saying wannan maganar ma cos ba ta dace ba sam ka fade ta kai kanka ka sani ba haka nake ba”.
Dr.Aqeel ya fadi yana mai murɗe murfin robar Ruwan EVA mai rangwamin sanyi ya tuntula cikin glass cup din dake aje.
“Bismillah”.
ba musu ya dauka ya kai bakin sa sai da yayi rabon cup din sannan ya ajje gami da ajiyar zuciya fuskarsa da murmushi yake kallon Dr.Aqeel wanda shima idanuwansa na kan sa.
“ka canza gabadaya kamar ba kai ga kayi kiba ga wani tumbi da aka ajje”.
ya fadi yana mai kyalkyalar dariya
” ni da kai waye yafi zama kato ka dube ka fa Dr.Aqeel”.
“Five years is not 2years fa wallahi”.
Dr.Aqeel ya fadi yana mai harararsa cikin sigar wasa kafin dakin ya dau shiru na dan lokaci.
“gaskiya kam! na yarda tun da gashi nan nagani har ka kasa gane ni da alamun nan da shekara goma in ba ka ganni ba ko nace ni ne Dr.Karami ba zaka yarda ba”.
“No ba haka bane wallahi, yanzu dai yakake ya kuma aiki ya bayan rabuwa?”.
“Alhamdulillah mun godewa Allah kasan yanzu ina can Delhi ne acan nake aiki da wani Privter Hospital”.
“Ba Shakka ka ji manya mu ku ga mu nan muna ta fama da asibitocin nakasarmu”.
Murmushi Dr.Karami yayi kafin yace.
“nikam narasa abin da ke damun kasar tamu har yanzu jiya-i-yau ba abin da cigaba na a zo a gani da aka samu”.
“Uhmm kai dai ayi sha’ani kawai Dr.Karami”.
Sosai Dr.Karami ya kafe shi da ido kamar mai nazarin wani abu kafin ya murmusa.
“Ina Family?”.
Ya fadi yana kafe shi da idanuwa.
Murmushi yayi shima yana gyaɗa kai.
“Har yanzu…”.
“Ban yarda ba”.
Da sauri ya tare shi.
“seriuos”.
Shima ya fadi yana murmushi
Sosai Dr.Karami yake kallonsa kamar wanda bai yarda da abin da yace ba ko daya ke ba zai yi mamaki ba in ya yi la’akari da kansa wamda shima ko dam tsako bai ajje ba.
“Anya kuwa Dr.Aqeel kana nufin har zuwa wannan lokacin kai ma bakayi aure ba?”.
Sosai Dr.Aqeel yake kallonsa yana nazarin maganarsa da yarda yake danganta kansa da maganarsa.
“kana nufin kai ma baka yi ba kenan?”.
Gyaɗa kai yayi yana murmushin yake.
Kofar da aka banko ne ya sanya su saurin duban kofar Mariya ce ta shigo a hargitse sam ba ta lura da ko su waye a cikin office din ba idanunwanta gabadaya sun rikice bakin ta ba abin da yake ambata sai sunan Dr.Aqeel.
Duk kan su ido suka zuba mata suna kallonta sosai cike ganin tashin hankali cikin idanunwata da gangar jikinta sosai suke kallon yarda jikinta ke ƙarƙarwa kamar wacce aka tsamo daga kogi Dr.Aqeel ya mike da sauri domin shi yasan komai akan Mariya rike yayi sosai da hannunsa yana faman kiranta amma ina tashin hankalin da take ciki duk ya tafi da yan guntuwar natsuwarta.
“Yaa Allah Mariya me kuma ya faru ne?”.
Sai a lokacin ta lura da Dr.Aqeel da ke rike da ita sosai take kallonsa idanuwanta sai faman zubda kwalla suke bakin ta na rawa tana faman ajje zuciya.
“Ummata Dr. Don Allah…”.
Sai ta rushe da kuka sosai hakan ya kara rikita Dr.Aqeel da sauri ya fara kokarin jan hannunta.
“Dr. Aqeel What is wrong with her?”.
Dr.Karami ya fadi yana mikewa tsaya ya fara takowa har ya iso gabansu sosai yake kallon Mariya tun daga yatsun kafarta har izuwa cikin kwayar idanuwanta da sauri ya kau da kansa ya mai da idanuwan ga Dr.Aqeel.
“Tell me now Please what is wrong with her”.
ajje Numfashi Dr.Aqeel yayi kafin ya dubi Mariya sosai yaji tausayinta na kara samun mazauni azuciyarsa.
“Dr.Karami wallahi mahaifiyarta ne ke cikin Matsala”.
Da sauri Dr.Karami ya dubi Mariya wacce a lokacin ta tsagaita da firgicin da take yi na tashin hankali sai faman ajje numfashi take kamar wacce tayi gudun famfalaƙi sosai yake kallonta wasu abubuwa ne wanda bai dan ina suka dosa ba suke sukuwa cikin zuciyarsa sosai yake jin tausayinta a zuciyarsa tun kafin yasan abin da yake dawainiya da duniyar rayuwarta ita da mahaifiyarta yarinya ce karama wacce ba zata haura shekaru sha biyar ba amma yanayin ta ya nuna tana cikin MATSALAR RAYUWA ba kadan ba daga yanayin ta zaka gane haka.
“Meke damun mahaifiyar ta ta?”.
Dr.Karami ya fadi yana sauke idanuwansa kan Dr.Aqeel.
“eclampsia take fama dashi wallahi haihuwa tayi to tun bayan haihuwan lamarin ya afku”.
Gyaɗa kai ya shiga yi yanayin fuskarsa na sauyawa sosai da sosai tausayi da jin ƙai duk suka kara bayyana sosai.
“Tana ina yanzu haka?”.
“Tana cikin Asibitin nan a kwance yau kimanin sati uku kenan da faruwar abin amma lamarin sai a hankali nayi iya bakin kokarina amma abun ya ci tura domin abin kara hauhawa yake yi”.
“Yaa Allah!”.
Dr.Karami ya fadi yana mai dafe kansa sosai yaji wani iri a game da abin da Dr.Aqeel yace dashi sosai yaji yana son ganin matar yana ji a ransa zai iya taimaka mata domin kuwa yana cikin fannonin da yake aiki akai.
“Muje na ganta”.
Abin da yace kenan ya fara taku yana kokarin ficewa daga Office din kamar ya san in da dakin mara lafiyar yake da sauri Dr.qeel yaja hannun Mariya suka bi bayansa sannu a hankali har suka isa dakin da Habeeba take suna shiga suka tadda ita tayi firgai-firgai da ita alamun ya nuna duk ta hargitsa kanta amma izuwa wannan lokacin tayi lakwas ta hada jikinta waje guda ta saka laɓɓanta cikin baki sai faman cizawa take yi da sauri Dr.Karami ya isa gareta hannunta ya kamo gami da sauri ta fizge ba tare da ta kalleshi ba ya sake kai hannunsa ya kamo hannunta nan mata ta shiga kokarin fizgewa amma rikon da yayi mata a wannan karon bana wasa bane hakan bai bata damar kwace kanta ba illa dago idanuwanta da tayi ta watsa masa su sosai ya shiga karantar komai nata tsayin wasu dakiƙu kafin ya sake ta ya dubi Dr.Aqeel da Mariya da suke tsaya suna kallon duk abin da yake yi.
“yanayin ta ya nuna abun yayi karfi sosai a gareta wanda hakan ya kusan zame mata tamkar hauka ta gaskiya ya kamata ace ta samu kulawa sosai da sosai a wannan matakin”.
Dr.Karami ya fadi Dr.Aqeel ya ja numfashi.
“ka ga dai yanayin asibitin namu Dr.Karami ba komai bane ake samu a cikin sa wai don ma ina cikin sa ne ka gan sa a haka nayi iya bakin kokari akanta amma abin ya so ya faskara”.
Gyaɗa kai yayi cikin yanayi na gamsu da maganarsa ya san Dr.Aqeel gwani ne kuma jarumi ba zai ga gazawarsa ba a fannin aikinsa domin yasan kwarewarsa akan aikinsa sai dai matsalar da ya fara lura da ita a nan ita ce rashin kulawa daga gwamnati da kuma rashin wadatartun kayan aiki da babu dole duk wani likita ya fuskanci kalubale sosai a fannin aikinsa in har asibitin da yake ba kayan aiki numfasa yayi a ransa yace,
‘dadin kasashen waje kenan kumin kankantar Asibiti ba zaka rasashi da kayan aiki ba amma ban da kasarmu ta najeriya komai na su sai ka ga ragwanci a ciki’.
Amma a zahiri sai yace,
“Shikenan Dr.Aqeel ina son wannan lamarin ya dawo hannu na nayi maka alkawari nan da KWANA SITTIN in Allah ya yarda zan yi iyakar bakin kokari na don ganin komai ya zama Normal”.
Dr.Aqeel yayi shiru yana kallon sa yasan ALHERI irin na Dr.Karami tun suna tare acan kasan America ya san shi farin sani mai taimako da jin kai ba wannan bane karo na farko da yake taimaka masa a aikinsa sosai yaji dadin abin da yayi masa fuskarsa da murmushi ya dube shi.
“Anya za ayi haka daga zuwan ka Dr.Karami zaka daukarwa kan ka aiki ko hutawa baka yi ba please leave it I’ll do my Best to Help her…”.
“Please Dr.Aqeel stop saying that, ka bar ni kawai nayi, ai ni nace naji na gani ko, sai dai ban sani ba ladar ce kila baka so na samu kaso na nima”.
ya karashe yana mai murmusawa alamun joking cikin maganarsa.
Shi ma Murmushi yayi masa gami da gyaɗa kai.
“But at Now zan je gida na huta kafin zuwa gobe na zo domin gudanar da komai”.
“Bakomai Dr.Karami ko sati kace zakayi ai ba zan haka wannan damar ba”.
Duk kan su sukayi dariya gami da yin musabaha.
Mariya tun lokacin da suka iso cikin asibitin ta ke gefe tayi musu kuri da idanuwa tana jin maganganunsa sai dai wani lokacin ba ta jin turancin da suke jafawa cikin zancen nasu sosai take mamaki musamman ganin Dr.Karami da yarda lokaci guda ba tare da sanayya a tsakani ba ya bada lokacin sa har yake ikirarin taimakawa mahaifiyarta tabbas na Allah ba sa karewa a duniya nan ba ta taba zaton zata samu mutane masu imani irin haka ba wanda za su ji kansu ba tare da sun san su suwaye ba tabbas ta kara gasgata maganar mahaifinta akan DAN-ADAM ba duk bane halayen su daya suffa ce kawai ta kasance iri daya ba ta dan lokain da wani guntun murmushi ya suɓuce mata ba mai dauke da hawaye hannu ta saka tana dauke su a daidai lokacin Dr.Karami ya sauke ganinsa akanta sosai ya kureta da idanu yana kallo kamar wanda ya ga wata sabuwar halitta sosai Mariya ta kaɗu da irin kallon da ta ga yana yi mata da sauri tayi kasa da kanta gabanta na bugun uku-uku ba kadan ba ta tsorata da kallon da yake mata ta shiga nazarin dalilin kallon nashi akan me yake mata kallo ko ya san ta ne a ina? da sauri ta girgiza kai domin bata tsammanin ya taba ganin mai kalar hauka irin ta firgitacciya sosai ta saka a ranta daga ganinsa dan kasar waje ba dan najeriya bane domin irin yanayin da ta ganshi fes-fes kuma muryarsa bata fita sosai kamar na Dr.Aqeel haka ya kara tabbatar mata kila ba bahaushe bane
“Excuse me. whats is you Name?”.
Ya fadi yana murmushi a fuskarsa gabanta taji ya fadi domin ta tabbat da ita yake magana abu daya ta fahimta a maganarsa wato tambayar da yayi mata sunanta wannan kalmar tambayar kuwa ta ji ma da haddace ta a kwakwalwarta domin tun tana Primary ta san abin da furucin ke nufi a hankali ta dago ta kalle shi sannan ta kalli Dr.Aqeel wanda shi ita yake kallo da alamun jiran abin da zata ce yake yi domin irin kureta da yayi da ido amma da murmushi a fuskarsa a hankali ta motsa Laɓɓanta.
“Mariya”.
Dr.Aqeel da ya yi kasaƙe da baki sai gashi ya zaro ido mamaki da al’ajabi ya cika shi da yaji ta ambaci sunata da alamun ta fahimci abin da Dr.Karami ya tambayeta sosai ya shiga tambayarsa kansa yarda akayi har ta iya bada amsa sam bai yi tunanin za ta iya ba bai yi tunanin ma ta taba shiga aji da sunan daukar karatu ba ganin yanayinta mamaki ya hana shi sakat har sai da ya dubi Mariya yace,
“dama kin iya turanci ne dama kina makaranta ne?”.
Sai ta taji wani iri a ranta ji irin tambayar da yayi mata wato kallon BAGIDAJIYA yake yi mata ma rashin ilimi dakikaya yar kauye sosai taji ranta ya sosu wato shi tunanin sa saboda rashin babun sa yana tunani ya hanata shiga aji har ta nemi ilimi gyada kai kawai tayi gami da kau da idanuwanta daga gareshi gabadaya ta mai hankalinta wajan kaninta dake kwance yana faman barci cikin kwanciyar hankali yaron da aka yiwa Huɗubar suna Ibrahim wanda suke kira Mu’azzam cikin asibiti saboda tashin hankali da suke ciki…
“kiyi magana mana”.
Dr.Karami ya fadi ganin ba ta da niyyar cewa komai kallonsa tayi a hankali ganin murmushi a fuskarsa wanda ta lura kamar hakan a jininsa yake yawan fara’a wanda hakan ke kara masa kyau matuka gaya.
“Eh ina makaranta aji na biyu a sakandiri…”.
“A haka din?”.
Dr.Aqeel yayi hanzarin katse ta da fadin haka yana nuna ta da hannu cikin alamu da mamaki sosai a ransa.
“Masha Allah!”.
Abin da Dr.Karami yace kenan ya kastewa Dr.Aqeel hanzarinsa ta hanyar cewa su tafi sai da suka sake duba Habeeba wacce a wannan lokacin ta daina komau da take yi har da cizon laɓɓanta a tausaye sukayi wa Mariya Sallama suka bar cikin dakin.
Ajiyar numfashi Mariya ta saki gami da zamewa ta zauna kasa kamar wata kayan wanki ta zabga tagumi hannu bibbiyu tana faman kallon mahaifiyarta da kaninta Mu’azzam a wani sashin na zuciyarta kuwa Dr.Karami ne da Dr.Aqeel tana ji ba dadi akan yanayin da Dr.Aqeel ya nuna akanta yarda ya nuna yana mamaki da tace masa tana makaranta me yake nufi da yanayin da ya nuna kenan yana nufin ‘ya’yan talakawa marasa galihu basa makaranta ne ko mi yana zaton rashin ‘yancin ‘ya’yan talakawa har ya kai suka sa yin makaranta su zauna cikin duhun jahilci to tabbas yayi kuskure in har haka tunaninsa ya bashi bai san masu son yin karatu ba bai son masu burin yin karatu a duniyar ‘ya’yan takalawa ma naso sai dai babu ita ce take zame musu katanga da karatu.
Haka Mariya ta zauna tayi ta zancen zuci har zuwa wani lokaci.
******
Dr.Karami cikin Motarsa Kirar 2019 Mercedes-Benz GLA yake tuki bayan ya baro Asibitin Baban Alis tafiya mai dan tsayi yayi kafin ya isa cikin garin Minna Unguwa Tunga daidai wani katafaren Get ya yada zango Horn daya yayi aka buɗe masa ya shiga tsararren gida ne sosai wanda ya ƙawatu da komai na adon gida ba abin da babu aciki can nesa kadan wajan Parking Space ya nufa ya ajje motarsa ya fito hannusa rike da wayarsa sai faman latsa ta yake yi da alamun kira zai yi kafin ya isa kofar da zata sa dashi da Falon gidan ya kai wayar kunnansa sakan ni kadan ya fara magana.
“Am so Sorry Engr.Dangi wallahi lokacin da ka kira ni ina driver ne shiyasa ban dauka ba But Now na dawo gida dafatan dai lafiya?”.
Ya karashe maganar tasa da dora tambaya.
Daga can dayan barin yaji sautin murmushi ya tashi kafin ace dashi.
“Albishirinka”.
“Goro fari tas”.
ya fadi cikin sauri domin tun da yaji Engr.Dangi yayi irin wannan zancen yasan akwai kayan farinciki da suka wanzu kenan.
“Kayi Kani Dr.Karami”.
“seriuos don Allah Engr. Dangi ban son joking irin naka wallahi tell me the True Please”.
Sautin dariyar Engr.Dangi ce ta sanya Dr.Karami kara gasgata maganarsa.
“seriuos Wallahi Safeenat tayi maka kani yana nan mai kama da kai”.
“Masha Allah nayi farin ciki gaskiya Allah ya raya ya dayyaba amma gaskiya Baby din nan bai iya zuwa ba sam sai da ya bari na baro garin sannan zai duro duniya mai makon tun dadynsa na can ya kamata ace ya zo”.
Engr.Dangi yasa ke kecewa da dariya kafin ya ce,
“kai Dalla waye dadyn nasa kai kasan a matsayin kani yake a wajan ka ni ne dady wallahi domin ba wanda zai kalli tazuru irin ka yace masa Dady don haka becarefull”.
In da sabo ya kamata ace Dr.Karami ya saba da tsiyar da abokin nasa yake yi masa na rashin aure domin in sau goma.za su hadu sai yayi masa gorin mata amma sam haka bai ɗaɗashi da kasa ya san komai nufin Allah shi kasan yana son yin auren But bai san dalilin da har yau bai ga matar da ta kwanta masa har yake tunanin zai iya zaman aure da ita ba yanzu in bai manta ba yana 32years kenan a girma ya girmi Engr. Dangi da kusan shekaru Uku amma gashi nan har ya riga shi aure har matar tasa ta haihu.
Gyaɗa kai kawai yayi ya shiga cikin falon bayan ya bude dakin sa ya dosa yana shiga ya ajje wayarsa da key dinda ya zare suit din dake jikin sa ya ajje sannan ya cire fara rigar mai dogon hannu ta cikin suit din ita ma ya ajje sannan ya cire dogon wando bayan ya cire takalmin kafarsa ya tsaya daga shi sai Boxer da singlet Toilet ya nufa ya watso ruwa bayan ya fito ya tsan jikinsa sosai da sosai jallabiya ya zurawa jikinsa mai ruwan jinin kare wanda tayi matukar dacewa da jikinsa sosai Coffee yaje ya samarwa kansa mai zafi sosai sannan ya dawo cikin dakin sa ya zauna kan daya daga kujerun dake dakin sosai da sosai ya nutsu yana shan Coffee din a hankali duniyar tunani ya je fa kansa wasu abubuwa da ya ajje can kasar zuciyarsa ya ji su yo masa sama yana sake maimaita su sosai ya shiga tunano Dr.Aqeel da abin da ya wakana a cikin asibitin sosai yake tuno yar matashiyar budurwar nan da ya jima yana nazarinta wanda ashekaru ba zata haura 15years gyaɗa kai kawai yayi gami da murmusawa.