UMM ADIYYAH CHAPTER 42 BY AZIZA IDRIS GOMBE
Www.bankinhausanovels.com.ng
Ba ta yi minti goma da saukowa ba kuwa, ta ji shigowarsa, Karasawa ta yi inda yake,
tayi masa sannu da dawowa. Zaid kam bude baki ya yi da idanu yana duban Umm
Adiyya, cikin mamakin ganinta haka fes! Cikin kwalliya da kimtsi da gyara, rabon da
ta yi kwalliya haka musamman don shi, har ya manta, sai dai ko ya ga ta yi shirin zuwa Ofis da safe.
Gyarar murya ya yi sannan ya ce, “Yawwa, sannu ya gida?’”’ Lafiya.” “Asma na gaisheki, na je wurinsu yau.” Tsayawa ta yi cak! Take ta ji kamar an nausheta. Mamaki ya hanata magana, wai
yau har Yaya Zaid ne zai iya tafiya wani gari ya je ya dawo, bai fada mata ba har sai ya dawo din, za ta san ya yi tafiya?
Take ranta ya dagule, ta rasa me yake mata dadi.
“Hmm! Na gode, ina amsawa.” Tana fadin haka ta wuce dakinta a sama, ta wargaza
duka kwalliyar ma da ta yi, saboda a tunaninta babu ma amfani, ta riga ta rasa Yaya
Zaid. Ya daina sonta. Haka ta kulle kanta a daki ta sha kukanta. A cikin kukanta ne
ta ji kamar an taba Kofar dakinta, amma da ta saurara, Sai ba ta sake jin motsi ba, haka ta kwana cikin wani irin yanayi. Washegari ta sake komawa kamar da dinta, duk randa ta gaji ko ya gaji, sai ya fada mata matsayinta, don ita kam ba ta san me za ta ce masa ba, tunda shi ya zabi ya daina sonta. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ba abinda ta sa a gaba, sai shan Cornflakes dinta, da dunkulewa a kan gado, da saka dogin riguna masu roba-roba.
******
“Zaid ni fa na sanka, babu yadda za ayi wai ace matsala haka ta yau da gobe ta sa ka fita a hayyacinka, ana magana, hankalinka ba ya ma kai. Ba dai wani attack aka kaiwa kamfani ba kuma?”
Zaid ya sa hannu ya shafi fuskarsa cikin damuwa, “A’a babu ko kadfan, kaina ne
kawai ya kulle kan wasu al’amura, na san abinda ya dace na yi a tunanina, na yi su maimakon a samu mafita, sai ma abubuwa suka sake kacamewa. Umm Adiyya ce.” Salisu ya dan ware idanunsa, “To! Gaba daya?”
Nan ne Zaid ya fada masa halin da suke ciki, ya dora da cewa “Wasu lokutan I just feel like giving up. Ta kasa fahimtar inda na dosa, yanzu ta dauko wani fushi ta dora kacokam! A kaina. Ba ta ma jin magana bare lallashi. Na zama kamar maKiyinta.”
Salisu ne ya nisa ya dubi abokinsa, “A‘a kai ma dai ka ce aiki ka daukowa kanka ido
a rufe. Of course! A idanunta kai ne maKiyinta mana. Gaskiya ni ban ga laifinta ba. Ba yadda za ayi ka samu macen da ba ta taba haihuwa, ba ka ba ta shawarar farawa da tsarin iyali. Sannan bayan wancan evaluation (gwajin) da ka ce an mata
lokacin da ta samu bari, ai ba ku sake komawa asibiti ba, bare a san ko daga ina ne matsalar take ba.
Ni dai shawarata, ka dauketa ku koma asibiti, idan ma maganin ne zai kawo sauKin lamarin to, idan ta ji daga bakin Likita za ta fi saurin amincewa, idan ya so sai kai ka mara mata baya ka nuna kana tare da ita akan hakan. Amma yanzu gani za ta yi ba Www.bankinhausanovels.com.ng
wanda ya kai ka tsanarta, tunda ka kawo mata wannan batun.” “Dama ina da niyyar yin hakan, don Likitan ta yi tafiya ne shi ya sa, amma zan kira
na ji ko ta dawo, na fi so ta ga wacce ta saba da ita, ka san idan na kai ta wani wuri za ta ma iya tunanin cewa mun hada baki da Likitan ne ya ce mata hakan.”
“Kai mata kenan, haka dai za mu yi ta hakuri da su. Allah ya sa a dace. Ya gyara al’amuran.”
“Ameen na gode sosai. Yaya batun Chips din can kun samu ne?” Salisu ne ya banka masa harara, “Kai Wallahi ban san wane iri bane, ko yaushe aiki
a Kwakwalwarka, ba dole ‘yar mutane ta nuna ma fushi ba, kai da an samo yadda za
ayi, za ka koma gida ka yi lallashi, ka zo ka na min batun Computer Chips. Ko mun samu, ba zan sayar maka ba.” Zaid ya yi dariya iya isarsa, sannan ya mike. “To na ji, ka gaida Madam. Sai Hajiya ta sauko za ku ganmu.” “Ka je dai a fara maka magana tukun.”
“Kai ka ga sharrinka kenan, shi ya sa ba na sirri da kai.” Salisu yana dariyar abokin nasa ya mike ya taka masa zuwa wajen mota.
********
Kallon wayar ta yi a karo na bila adadin, ta yi Kara ya fi sau biyar, yanzun ma ta daga ne kawai saboda ta ji, don me aka katse mata jin daciin rayuwarta.
“Ki sauko mu tafi.” Zurfaffar muryarsa ta kwararo a karon farko da ta daga wayar. Oh, ta ma mance. Tun jiya da safe ya shigo ya sameta, wai yana so su koma asibiti tare, jinsa dai kawai take yi, don ta samu ta huta da batun, ya sa ta gyada masa kai.
Yanzun shi ne har da cewa za su tafi asibiti, ita dai koma me za ayi, sai dai ayi, ba abinda za ta dura ma wa cikinta. Abaya ta janyo ta sa a saman kayanta, sannan ta fita, a mota ta same shi. Ba su ce da juna komai ba, har suka isa asibitin. Tana zaune, shi ya bi duk abinda ya dace, sannan suka wuce kai tsaye ofishin Likitar da take ganin Umm Adiiyya,Www.bankinhausanovels.com.ng kasancewar ya mata waya, ta san da zuwansu
dama, sannan ba su samu layi ba a wurin. Madam Cry-Cry, sannu da zuwa.” Dr. Zainab ta fada tana murmushi cikin tsokanar Umm Adiyya, saboda kowa ya san irin kalar shagwaba da borinta.
Umm Adiyya ta rufe fuskarta tana dariya. Zaid kam Kura mata idanu ya yi, zuciyarsa
ta yi tsalle da jin amon muryarta mai dadin saurare, sannan a lokaci guda zuciyar ta matse cikin wani yanayi mai zaki da daci, rabon da ya ga dariyar Umm Adiyyarsa haka har ya kusa mantawa.
Nisawa ya yi, “Ina kwana Dokta?” Zaid ya fadi sannan ya gyara kujera daya ga Umm Adiyya, shi ya samu daya kujerar ya zauna. Lafiya, yaya Madam Patient?’ “Yanzu kam ai ta warware, sai duri.”
Ya fada yana kallon Umm Adiyya a fakaice, tana dai nan ba yabo, ba fallasa, wani dan Karamin murmushi ne a makale a fuskarta, irin wanda dai za a ce da babu gwamina ba dadi.
“Aha, Likita kamar yadda na fara miki bayani, na kawo Madam ne ki fayyace mana komai game da shawarar da na zo miki da ita kwanaki, don dai ga ta nan ta tubure, tace ita ba ta san zancen shan magani ba.”Dariya Dr. Zainab ta yi ta ce, “Ina kuwa za ta so zancen shan magani Yallabai,
shawara ka yi ai, amma kyawunta dama da kanta za ta zo a Kara tattauna matsalar, sai kuma a aunata a ga me ya dace da ita daidai matsalarta. Bayan ka yi min waya dazu kafin ku zo, na sake duba Case dinta.” Umm Adiyya ta Kara gyara zama a kujerar, cikin jin dadin inda zancen ya karkata.
“Ah, ita dama wannan matsala ta yawan Dari ta kan samu a dalilin ababe da dama,
wasu Za a iya taresu a magance kai tsaye, wasu kuma sai dai a gwada a kuma jira aga yadda abubuwan za su kasance. To sau da dama, sai an gwada ake sanin me yake janyo wannan Darin. Wata Kila wasu sinadarai ne suka yi Karanci a jikinta, ko kuma matsala daga Kwayar halittar
kwayayen ko dai zai iya yiwuwa daga siffar Www.bankinhausanovels.com.ng mahaifarta da ma dai sauran ababe da dama. To idan ba an gano an tare shi ba. Idan na gyara ne a gyara, idan kuma wanda ba na gyara bane, a jira lokacin da ya dace, to fa komin hutun da mace za ta dauka, za a zo a kuma maimaita abinda ake gudu ne. Kafin a sallameta wancan karon munyi gwaji don ganin me ya janyo mata wancan barin na farat daya. Mun kuma fahimci daga Hormones dinta ne. To ba
babban abin damuwa bane, idan muka duba muka ga za a iya magance shi, wannan yasa da ka zo da batun son ta huta, na ba ka shawarar wancan magungunan. Akwai wadanda muka ga wannan dan hutawa na tsakanin bari da samun sabon ciki yana rage Tendency na wahalar da mahaifa, ya kuma kare faruwar wani barin. Ba
wai za ayi ruling out (cire tsammanin) ba zai sake faruwa bane, amma dai an rage kaso mafi girma. Kuma za a samu wata horaswar jiki a tsakani, wanda zai shirya mace wurin sake daukar wani sabon cikin.
Saboda abinda yake faruwa, yawanci idan akwai matsala irin na yawan bari, to ana
so a dauki wasu matakai kafin a sake daukar ciki, na farko yanayin abinci ya canza,
da rage yawan damuwa, da ma dai sauran ababe, ya kamata a canja na aKalla watanni uku, wasu har ma shekara ko shekaru biyu, ya zama komai ya daidaita,
sannan a sake gwadawa. Amma tunda yanzu ke ba ki son amfani da maganin hana daukar ciki, akwai wasu
hanyoyin da za a iya amfani da su, wandanda za su sa ki huta ba tare kuma da kin sha komai da zai taba miki lafiyarki ba, don su ma shan wadannan Kwayoyin na tsawon wani lokaci, yana da nasa _illolin. Musamman idan kafin haihuwar fari ne.”’ Zaid ya nisa, “Likita to me ya sa ake amfani da su, bayan sun kasance suna da illa?’ A’a don na dan lokaci kadan ne, wannan ba matsala bace, kawai ba a so a dade
ana shansu ne na tsawon shekaru.” “To Doctor, ba damuwa.” Yanzu zan mata bayanin ko wane hanya na tsarin iyali, sannan a yi mata gwaji aga wanne zai fi dacewa da jininta, nan ne za mu fi sanin wanda ya fi dacewa da ita. Idan akwai buKatar dukanku ne kuma za ayi gwajin, bayan early results dinta kuma
sun shigo nan ma dai duk sai a rubuta.” To mun gode. Bismillah, bari na bar ku, ku tattauna.” Ya fada hade da miKewa ya ba su wuri saboda su fi sakewa, yana fatan ta ja hankalin Umm Adiiyya ta amince. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ummu dai tunda Dr. Zainab ta fara bayananta, kallonta take yi har ta kai aya, ba wai
don ba ta gane me take fada ba ne, sai don ta san koma me suka zaba, ba yi za tayi ba.
Haka aka je aka zuki abin zuka a kai mata duk gwajegwajen da suka dace, saura kuma an ce sai bayan kwana biyu su koma. Har suka dauki hanyar komawa gida, bata ce uffam ba.
“Twinkle.” Hannu ya sa akan nata da ke kan cinyoyinta, ya riKe. “Ba ki ce komai ba,
tunda muka bar asibiti, yanzu kam hankalinki ya kwanta ai, no need ki sha komai baya ga Maca Roots da ta ce zai taimaka, idan lokacin da muka shirya sake gwada samun baby ya yi. Za mu saurari sakamako, sai mu yi fata da addu’a ya zama ba wata matsalar da za a samu.” Zare hannunta ta yi daga nasa ta juya kallonta zuwa ga tagar motar. Daga nan jikin Zaid ya mutu ya san akwai matsala. “Adiyya, please.” “A’a ni ka ji na ce wani abu ne? Kai ka ce mu je asibiti, ban maka musu ba, na je,
kasa Likita tambayata tambayoyin duniya, na ba ta amsa, aka caccakala ni, duk ban
ce komai ba, ku ka yanke shawarar abinda ya dace, duk ka ji na ce wani abu? To
tunda ban ce ba, ai shi kenan, ka yi naka, ni kuma ban jin yin amfani da duk abinda
ku ke so, tunda ni ba zai kai ni ga cimma burina ba, don haka ba abinda zance.”
Girgiza kansa kawai ya yi, ya sauke ajiyar zuciya har suka shiga gida. Haka
zamansu ya Kara komawa, watau zaman doya da manja, daga ranar ya rasa irin
taurin kan yarinyar, ya kuma rasa yadda za ayi ya shawo kanta, ya ma ce ya
hakuran gaba aya, amma ita wai nan fushi take yi, akan ya daina sonta ne. Www.bankinhausanovels.com.ng
Wataran yadda mata suke tunani, yana daure masa kai, abu ne mai sauki, amma gaba daya ta dagula masa lissafi a kai.
******???
Ya dade zaune cikin motar, yana kallon gilas din gaban motar, shi bai fita ba, shi bai
tada motar ya tafi ba, can kuma ya kwantar da kansa kan sitiyarin motar, ya runtse
idanu, Kwakwalwarsa ta rabe kashi daban-daban da har suke neman hautsina masa
lissafi, wayarsa da ke ajiye a gefe ya ji tana ruri.
Ta yi da farko, har ta katse. Aka sake bugowa, hannu ya sa zai aga, nan take wata
zuciyar ta tunasshe shi. “Zaid me ka ke yi? Me za ka koma a rayuwarka? Bayan duk
lokacin nan da ka diba, ka na neman gafarar
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG