WATA MACE CHAPTER 2 BY SANA S MATAZU

WATA MACE CHAPTER 2 BY SANA S MATAZU

                   Www.bankinhausanovels.com.ng 

Kamar yadda me karatu ya sani a baya, Yusuf ɗa ne ga Baba Ɗangaladima, abin soyuwa ga kowa tun yana ƙarami haka har girmansa. Sai dai Yusuf ba shi da nasibi akan komai. Duk ƙaunar Baba ɓaure na Yusuf ya yi zurfin karatu abin ya faskara. Sau biyar yana faɗuwa jarrabawar gama secondary ƙarshe dai sai Jawwad ne ya zana masa. Shi ma ba asami wani abin kirki ba. Hakan yasa Baba ɓaure ya ja shi jikinsa ya ɗorashi harkar kwangilolinsa. To shi ma dai tana kasa tana dabo. Yau riba gobe faɗuwa, babu wani cigaba da aka samu. Daga faɗuwa sai ayi aiki a sami matsala. Gona kuwa ko ya noma ba a samun abin kirki. Akasari ma

ƙwari ne suke cinye shukar tun kafin ta yi nisa. Tun abin baya damunsu har ya soma damunsu. Kowa a zuri’arsu yasan da wannan TAMBARI a tare da Yusuf.

Gori daga shi har mahaifiyarsa suna shan sa, sai dai kasancewarsu mutane masu haƙuri ko ɗaga kai basa yi bare su tanka. Tun ana yi a bayan idanunsu har ya kai ana yi gabansu. Sai ya zamana Yusuf ya soma ja baya da Baba ɓaure sossai. Ya sha ganinsa idan zai fita yana sa yara nemansa haka zai laɓɓe saboda mudun suka fita tare abu ne mawuyaci bai bashi kwangila ba, kuma ba a samun nasara sai faɗuwa shi yasa ya zaɓi nisa da shi fiye da kusancinsu. Ya fi ganewa ya fita ya yi buga-bugarsa kamar ba ɗan cikin ɗan saɓalo estate ba. Bai cika shiga cikin ƴan uwansa samari ba, rayuwarsa ya ke yi shi kaɗai. Kama daga kan dako, aikin gini koyon ɗinki babu wanda ba ya yi, duk kuma abin da ya samu yakan yi ƙoƙarin ya raba ya siyi wani abu ya kai cikin gidan. Wannan na ƙara masa martaba da mutuntaka sossai a idanun masu mutuntakar gida.+

***

Zahidah ɗiya ce a gidan Baba ɓaure. Yarinya ce mai tsanin natsuwa da haƙuri ga sanin yakamata. Akasarin rayuwarta tafi yinta ne ɓangaren Baba Ɗangaladima wajen Hajiya Hauwa. Ko kuma gidan surukarta Yaya Amina matar Adam babban ɗanta. Hakan yasa suka shaƙu matuƙa da ita, hakama Yusuf akwai shaƙuwa tsakaninsu. Tana da kaifin ƙwaƙwalwa sossai ga wayau da kuma girmama manya. Hajiya Hauwa ta sha hasashen a haɗa auranta da Yusuf kamar yadda aka saba haɗa auratayya a danginsu. Sai dai da yake yanzu zamani ya ja, sukan bari yaran su haɗa shekaru shatakwas cif lokacin sun kammala karatun gaba da primary. Badomin komai ba sai dan ɓarakar da suka soma samu na shigowa cikin ahalin na dojewar wasu a wajen haɗin. Alla bashi sai yaran su haɗa kawunansu da kansu,  su kuma su aurar dasu amma babu batun ka aure wata a waje. Su kuma mazan lokacin ko sun gama karatu ko suna dab da gamawa.

Wannan sauyi da aka samu ƙwarai shi ya daƙilar da burinta na son a haɗata da Yusuf. Zahidah mace ce mai ƙulafuci, idan tasa abu aranta sai Allah. Shiyasa kaf sa’aninta ta rugasu kammala karatunta na gaba da primary. Tsabar ƙoƙarinta, bata isa zana jarrabawa ba, aka yi mata jumping (tsalake). Haka kuma ta haɗa saukarta hadda. Tana da burin cigaba da karatu sossai. Kowa ya son burinta, dan da ya wa agidan sukan yi mata laƙabi da *ƳAR BOKO*. Kuma takan amsa kai tsaye ba tare da shakka ba, domin tasan akwai tsarin cigaba da karatu bayan aure acikin zuri’arsu.

Mace ce mai tsanin tsafta da son kwaliya, ƙunshi kafin wani ya disasshe anyi mata wani. Saboda zaryar gidan ƙunshi ta koyi yankan salatif kala-kala wanda har ya zame mata sana’a kuma take samu da shi matuƙa. Dan ko a iya cikin zuri’arsu kuɗin da ta ke samu da salatif Allah Ya yi yawa da su. Wasunsu na ganin kamar wahalar banza take yi, amma ita kaɗai take sanin nishaɗin da take ji a tare da ita idan tana aikinsa. Domin ta haƙiƙance zana shi baiwa ce kuma wanda ubangiji ya so yake bawa. Dan haka tun abin yana damunta har ya bar damunta. Masu manyan sana’ar da yawa sun sha zuwa wajanta rancen kuɗi, takan yi murmushi idan ta tuna su ne gaba wajan kushe hikimarta.

STORY CONTINUES BELOW

***

Jawwad shi ne kaɗai ɗa namiji a gidan Baba Iro. Baba Iro kaf ƴaƴansa mata ne, ya yi aure-aure ya kai goma domin Allah Ya bashi ɗa namiji amma duk matan da ya aura basa rufe wata goma suke haihuwa. Sai dai kash babu wadda ta haifa masa burinsa sai ƴar uwarsa Sadiya. Wadda kafin ya karɓi auranta an sha ƙwarbai da shi. Lokacin da ta haifi Jawwad babu irin ɓarnar kuɗin da bai yi ba. Sadiya tana takaicin yadda ƙiri-ƙiri ya ke nuna ya fi son ɗa namiji akan mace. Duk da kasancewar Jawwad ya taso a tsakiyar mata ƴan uwansa hakan bai hanata ƙoƙarin bashi kyakkawar tarbiya ba. Sai dai kuma mahaifinsa ya ɓata komai ta yadda ya dinga fifitashi kan komai a kan ƴan uwansa. Duk wata kaddara da ya mallaka tun Jawwad na ƙarami ya maida sunansa akai.

Duk inda zashi to tare da shi yake tafiya. Ƴan uwansa sun sha nuna masa kuskuran abinda yake yi amma ƙarshe da faɗa suke rabuwa. A haka yaro ya tashi a sangarce, babu kwaɓa babu harara. Jawwad Matashi ne mai jini a jika kuma ɗan ƙwalisa.  Sai dai tun tasowarsa fitinanne ne baya jin magana. Tun yana shekara goma sha takwas ya ƙware a bin mata da kuma tare yara a hanya yana ƙwaƙƙularsu. Wannan kowa ya san shi da wannan TAMBARIN a zuri’arsu. A silarsa iyayansu suka so dawo da al’adar aurar da yaransu suna shekaru goma takwas maza amma hakan bai samu ba. An yi masa aure ya kai sau uku amma kuma baya shafe wata biyu da matan yake sakinsu. Hakan yasa aka haƙura aka zuba masa ido ana binsa da addu’a domin sun haƙiƙance duk zuri a sai a sami wari guda.

***

Kabir ya fito ne daga zuri’ar Baba Muttaka ɗan uwargidansa ne Hajiya Fure. A zuci fir’una a fuska Musa kenan. Kafatanin hallayar Jawwad irin ta Kabir ce sai dai kuma ga wanda ya san baɗinin Kabir kenan ga wanda yasan zahirinsa kuwa ba zaka taɓa cewa yana da wani aibu ba. Yana da suffar kamala sossai, akwai shi da iya taku da nutsuwa ga tausassa kalamai. Idan yana magana da kai dole ka ji ya burgeka, duk wani salo na tausasawa ya sani. Allah ya bashi kaifin fikra da balagar harshe. Shi yasa ƴan mata da yawa suke rubibinsa. Akwai masu kuka akansa.

***

Labiba, ɗiya ce ga Baba ɓaure kuma ita ce ƙarama a gidan cikin mata, sai dai mace ce me ji da kanta. Ƴar ƙwalisa ce ta ƙin ƙarawa. Bata da kunya ko kaɗan, bata ragawa na sama da ita haka ma ƙananun dake ƙasanta. Yanzu yaro zai mata abu bako kunyar idon mahaifiyarsa zata kwafɗeshi. Gata gaɓuwa ko kusa bata iya magana ba, duk yadda tazo bakinta haka zata furzota ba tare data taunata ba. Ba namiji ba hatta mace ƴar uwarta takan jinjina wautarta idan ta yi wata maganar. Bata ganin kowa da gashi musamman yadda take la akari da mahaifinsu ne ginshiƙin *ƊAN SABALO ESTATE*. Sangarta take zubawa son ranta kuma mahaifiyarta na ɗaure mata ƙugu.

Labiba baƙa ce amma kuma ta kwaso kyawun mahaifiyarta wadda ta kasance ƴar asalin garin sumalia. Tana da kyawu daidai gwargwado. Ga kuma cikar hallita. Duk wata budurwa mai ji da kanta a estate ɗinsu bata kama ƙafarta ba. Duk gayun Labiba bata san idan ta cire kaya ta sauya ta ɗauke ba, mahaifiyarta ko kuma yaran da ake riƙo a ɗakinsu sa’aninta wanda ɗakin kwanansu ɗaya su suka san wannan hidimar. Bata san ta yi kwaliyya ta kwashe kayan data yi amfani da su ba. Bata san ta ci abinci ta ɗauke kwano ba.

Tun suna kai ƙara har suka haƙura domin Amne bata goyon bayansu. Haka batasan wanke kai ta yi kitso ba, zadai ta kimma acuci akanta yana sumbuƙa wari ba damuwarta bace domin zata buleshi da turare. Babu tazara tsakaninsu da Zahidah sa’anin juna ne. Sai dai kowa hidimarsa yake, idan sun haɗu to anzo taron cikin gida ne ko kuma islamiyya domin Zahidaht bata son raini ko kaɗan. Bayansu akwai ƴan mata shida masu irin shekarunsu. Husnah, Amira da Maryam  da Mashiɗa da Zuhuriyya sai kuma Kamila.

***

Kwanci tashi babu wuya wajen ubangiji, ƙarshan shekara na gabatowa haka kuma batun shirya-shiryan aurar da ƴan matan *ƊAN SAƁALO ESTATE* ya soma kankama. Ko wace nada zaɓinta in ka ɗauke Zahidaht da Labiba. Haka ma matasan kowa da zaɓinsa idan ka ɗauke Kabir da Yusuf da kuma Jawwad. Wanda Jawwad da Kabir ana dakon fitowar jarrabawarsu ne, da suka zana ta zangon karatunsu na biyu. Awannan lokacin da yawa basa lissafi da Jawwad a auran saboda bama shi da wadda take sauraronsa cikin zuri’arsu. Kasancewar a lokacin ya saki mata guda biyu, ɗaya ɗiyar Baba Khamis ɗaya kuma ɗiyar Baba Muttaka. Wanda abin har ya so taɓa zumuncinsu. Kasancewar duk matan da ya saki na baya sun yi aure amma waɗanan sai auran nasa ya zame musu TAMBARI kwata-kwata babu mai sha’awar auransu cikin zuri’ar.

Kabir kuma yana ɗaya daga cikin waɗanda gwamnan dake ci alokacin, ya nemi alfarmar a barshi ya tafi ƙaro karatu. Baba ɓaure bazai iya karya wa gwamna bille ba, abokinsa ne tun yarinta hakan yasa ya amince da buƙatarsa ya tara sauran ƴan uwansa suka yi shawara aka haɗa da Jawwad aka biya masa suka tafi. Karon farko da wani matashi wanda bai taɓa aure ba a zuri’ar ya tafi ƙaro karatu, kuma ba cikin Sakwwato ba ƙasar waje. Daidai lokacin da ake shirin aurar da ƴan matan gidan su kuma sun zo gida ne hutun jarrabawa. Iyaynsu kuma suka yanke a dakata jiran jin yadda sakkamakon ya yi kyau, alla bashi sai a ɗaura auren su juya da matan.

Wannan fifiko da suka samu ya ƙarawa Jawwad da Kabir girman kai da kuma samun wani fili a zuƙatansu na cewa su ɗin sun kai. A ɗage suke kallon kowa, sun raina da yawa cikin matasan gidan musamman Yusuf. Babu yadda Jawwad da Kabir basu gwada hikimarsu ba, ko Labiba zata amince da buƙatarsu domin suna ganin su suka dace da ƴar ƙwalisa irinta amma ta shafawa idonta kwalin audi ta nuna bata san suna yi ba. Ɓangaren Jawwad dama shi soyayyar zamani yake biɗa, daya ga ba fuska sai ya haƙura. Shi kuwa Kabir zahiri da gaske yake son auranta shi ma dai babu fuska dole ya haƙura.

Daga gefe guda kuma, Zahidaht ta makance akan soyayyar Kabir, ba dan komai ba sai dan tunaninta shi ne daidai da ita. Ɗan gayu ga ƙwalisa ga kuma ilmi. Koba komai zai tuntuɓawa mafarkinta tabbata na cigaba da karatu. Sai dai ta kasa tunkararsa koda wasa, domin baya wasa dasu kwata-kwata. Tun ana zunɗenta a gida taƙi fitar da tsayayye, duba da yadda Salihu yake sonta har aka soma yasar musu da habaici a tsakar gida ita da mahaifiyarta. Hankalinta ya tashi matuƙa, musamman da mahaifiyarta ta soma sakata a ɗaki tana nuna mata ta rufa mata asiri ta karɓi tayin Salihu. Sossai ta shiga damuwa, zuciyarta ta soma aminta da karɓar ƙudurin mahaifiyarta kodan sama mata natsuwa.

Ɓangaren Yusuf kuwa baya kula kowace mace cikin ahalinsu da sunan so, yana ganin wace ce zata so shi a hakansa? Hakan yasa koda wasa bai ɗorawa kansa kula *WATA MACE* cikin zuri’arsu da sunan soyayya ba, in ka ɗauke gaisuwar mutuntaka. Hakama mahaifiyarsa tana goyon bayansa. Mace ɗaya ce ya ke hango nutsuwarta ta kwanta masa, sai dai koda wasa baya tunanin zata karɓi tayinsa shi yasa ya haƙura.

Gaba ɗaya ya maida hankalinsa ne ga sana’ar hannu da kuma nacin karatun al-ƙur’ani. Kaf zuri’arsu babu mai baiwar karatunsa, shi yasa ya ware aji guda na ƙanannun yara masu rasowa yana koyar dasu ƙira’a. Kuma alhamdullilah, duk wata gasa ta karatu acikin garin Sakwato matuƙar aka ɗauki yaran da yake koyarwa to *ƊAN SABALO* sukan yi nasara. Ya goge a fannin sanin alƙur’ani da ƙa’idojinsa.Safiyar wata Asabar garin Sakwato an tashi da wani irin muku-mukun sanyi. Labiba na ƙunshe cikin lallausan bargonta, gaba ɗaya ƴan ɗakin da suke kwana tare sun farka, wasu na ɗakin girki wasu kuma na cikin gida. Wasu kuma da yawa suna islamiyya. Miƙa ta yi tare da sako ƙafaffunta ƙasa, ɗan turo baki ta yi ta yatsina fuska. Kai tsaye banɗakin Amne ta shiga, cikin mintun ta fesa wankanta tare da wanko baki ta fito tana taku ɗai-ɗaya. Sai da ta shari lokaci wajen shiryawa daga bisani ta fito babban fallo. Bata sami kowa ba hakan kuma bai dameta ba, duk da tasan ta karya dokar zuwa islamiyya haka ta kaɗa kai ta tafi bayan ta karya kumalo.

Tana gab da shiga makarantar gabanta ya yanke ya faɗi, ba dan komai ba sai dan tunawa da yau kowace rana ce. Ilai kuwa tana saka ƙafa cikin makarantar ta haɗa idanu da mahaifinta. Harara ya wurga mata ta sune kai ƙasa domin tasan laifinta. Ita shaf ta manta yau ne ƴan ajin Zahidaht da kuma ajin Yusuf suke gwajin gasar karatu, ƙa’idar islamiyyar ne duk ƙarshan wata sukan shirya gasar karatu daga wannan aji zuwa wannan aji. Ajin da ya yi nasara zai kara da dukkan ajujjuwan idan ya yi nasara shi ne ajin da zai jagoranci estate ɗinsu a gasar da suke fita ta ƙarshen shekara. Da babu abin da zai sa ta shigo makarantar ma, saboda tasan rana irin wannan tana haɗa duk wani uba na cikin zuri’arsu. Lallaɓawa ta yi zata zauna sai jin sautin muryar mahaifinta ta yi,

“Yusufa ga Labiba can yi mata bulala!”

Da hanzari ta ɗago kanta, gaba ɗaya sai ta muzanta yadda idanun sa’aninta na yawo a kanta. Har ta hango Husnah ɗiyar Baba Mu’az da Maryam suna ƙunshe dariya. Wani takaici ya kamata, kwata-kwata ta tsani abinda zai muzantata cikin sa’aninta. Ga mamakinta sai ta riski sautinsa cikin sanyin da ya zame masa ɗabi’a,

“Baba ai Labiba bata makara, ayi mata uzuri”

Sai ya ɗauke kai ya cigaba da abinda yake yi, kamar ba shi ya yi furucin ba. Gaba ɗaya kuwa su Husnah suka rakashi da idanu suna mamakinsa. Saboda sun sa yadda take kayawa tsakaninsa da ita matuƙar ya daketa shi yasa ma ya sahalewa kansa dukan nata.

“Bani bulalar!”

Ya furta a fusace, jiki a sanyaye ya miƙa masa, da kansa ya taso har inda take ya yi mata bulala goma, lafiyyayu. Tun tana daurewa har ta soma kuka don ta tsani duka. Ai kuwa filin wajen ya yi ɗif ana jin shassheƙar kukanta. Sai ajiyar zuciya take saki. Daidai lokacin Kabir da Jawwad suka ƙaraso wajen, akan idanunsu aka yi komai har gwalo ya yi mata da suka haɗa idanu da shi.

Iyayyen suka shiga gaisarwa ɗaya bayan ɗaya, har suka zo kan Baba ɓaure idanunsa akan Jawwad ya sha aski irin wanda ake kira hana sallah. Ga uban zanzaro da ƙaramar riga iya ƙugu. Kabir kuwa shigar shadda ya yi da hula zanna bukar suna taku ɗaiɗai. Yana shirin tanka musu ne daga gefe kuma cikin taro, aka gabatar da Zahidaht domin gabatar da buɗe taro da karatun alƙur’ani. Wannan dalili ya dakatar da Baba ɓaure daga ƙudurinsa na hukunta kowannansu, sai dai ya ƙuresu da idanu yana ajiye kowanensu a hukuncin da ya ke hangen ya dace da shi ciki kuwa hadda Zahidaht da sautin karatunta ya dira a kunnunwansa cikin taushi da nutsuwar murya.

Ɓangaren Labiba kuwa, bayan ta gama shan kukanta duk fuska ta dame da kwaliya. Da mamaki ta dinga satar ajiye kallonta a saitin Yusufa, ba yau ba ya saba tareta a makara ya yi mata alfarma ba wai saboda wani abu ba. A rayuwar Yusuf ya tsani ya daki yarinya ta tafi tana yi masa ƙunƙuni. Ita kuma ɗabi’arta kenan, duk da cewa bashi da zafi kan sauran Malam amma ya salaɗewa kansa dukan Labiba tunda ya fahimci bata da kunya. Amma bata taɓa kawo zai tsallake umarnin mahaifinta a kanta ba. Kanta a ƙasa har aka gama taron baki ɗaya, ƴan ajin Yusuf ne a kan gaba sai kuma na Zahidaht da suke bi musu baya.

Ba a tashi taro ba, sai da Baba ɓaure ya sami matsaya kan hukuncinsa. Ya kuma yi na’am da hakan, karon farko da yake ji aransa zai karya dokar da suka gindaya a zuri’artasu. Iyaye da dama sun yi jawabi mai ƙayatarwa, tare da nuna jin daɗi da kuma godiyarsu ga Yusuf. Daga bisani aka sallami kowa tare da kyaututtuka ga ɗaliban da suka yi nasara. Sai kuma sanarwar ƙarshe ta taron family da za a gudanar bayan azahar.

Jiki a sanyaye Labiba ta miƙe zuwa cikin gida, bata yadda ta jera da sa aninta ba, tunda yau sun sami abinda suke so kanta. Da Kabir ta soma karo,

“Su Laby manyan mata!”

Ya furta yana dariyar shaƙiyanci, sunan da yake kiranta da shi kennan, kuma yara da manya sun kama, wasu kan ce Yaya Laby, wasu Anti Laby wasu kuma Laby ɗin kai tsaye. To ita ma dake uwar iyayi ce sai take amsawa duk da Amne na masifar sunan. Bata biye masa ba ta yi gaba abinta. Sai dai kuma tana shiga babbar mahaɗar shiga gidan ta sami su Husna ana hira da shewa, ana ganinta kuma aka yi ƙusu! Bata raba ɗayan biyu da ita suke, ɗauke idanu ta yi ta hangi Zahidah na sawa Yaya Amina ƙunshi ta ƙarasa,

“Kai ya yi kyau! Zeedat zaki yi min ni ma?”

Ta furta tana tsaresu da idanu,

“Laby baki da kunya wallahi, ko ki gaishe ni kin wani tsayamana akai”

Ade ta furta tana zare idanu, yaya Asabe ta yi murmushi tana auna gajen haƙuri irin na matan yayyun nasu. Shiyasa duk Labiban ta bi ta rainasu bare kuma Amne na ɗaure mata ƙugu. Ilai kuwa, yaya Asaben kaɗai ta gaisar, don duk tsaurin idonta tana raga mata, bata wasa da yaro gata da kyauta abin da bai rufe mata ido ba. Sai ma juyawa da ta yi, tana ƙara nanatawa Zahidaht zata yi mata ƙunshi, ita ma dake ƴan miskilancin na kanta kai kawai ta ɗaga mata. Be dameta ba, ta wuce tana jin yadda suke mata cari. Tana shiga ta sami Hajiya Muwaddah da Amne na haɗe kayan da za a raba wajen taro na ci.

Zama ta yi ta jefa hannu a robar cake ta hau tauna tana lumshe idanu, bata tantama wannan aikin Mamarsu Yusuf ne, shi yasa kullum take dakon zuwa gaisheta da safe ko ba komai takan fito da tsabarsu tunda sana’arta kenan kuma ta ƙware sossai. Kamar an mintsineta ta turo baki, ta hau bawa Amne labarin abin da Babansu ya yi mata. Ai kuwa Amnen ta shaƙa, amma tasan ko giyar wake ta sha ba zata ce don me ba. Sabida ita kanta ya sha jan kunnanta kan makarar Labiba, duk cikin sa aninta ita kaɗai ce bata yi sauka ba, saboda fashi da latin islamiyya. Kaɗa kai kawai ta yi, Hajiya Muwwadah ta yi ƙwafa,

“Ina ma Yusufan ya bugeki da yagane!”

“Mama ai shi yana da kirki, ni ba ya dukana ba fa ko makara na yi a islamiyya. Shi kam matarsa ta huta wallahi yana da sanyin hali”

Karaf! Sautin maganar ya sauka akan kunnuwan Baba ɓaure. Ita kuwa Laby tana furta hakan ta miƙe tana ƙoƙarin shigewa cikin ɗakinsu, duk suka rakata da idanu.+

***

Gaba ɗaya ɗakin taron cike yake da ahalin gidan, Husnah da Maryam da Zahidah su ne suketa kujuba-kujubar gyara yaran da suka ƙi zama. Can Maryam da ta fisu rashin haƙuri ta ja ƙwafa tare da taune gefan bakinta,

“Wai ku mu kaɗai zamu yi aikin nan ne, ina ce hadda Laby Baba ya haɗamu. Ita wata fi ne da duk lokacin da aka samu aiki sai ta noƙe?”

Zahidaht ta murmusa, tare da dafa kafaɗarta,

“Daɗina da Maryam ragon azanci. Shin idan mun yi faɗuwa muka yi? Ita fa taga zata iya kowa da kiwon da ya karɓeshi. So hurry up mu yi abin da yake gabanmu”

Bata da yadda zata yi tunda Zahidah ta furta hakan, koba komai gaba take da ita. Kuma basu da tsarin raina nagaba cikin ahalinsu. Dan haka ta cigaba da aikin amma tana yi tana ƙunƙuni. A haka wajen ya kammala kowa ya hallara. Iyayye da jikoki da ƴaƴa babu wanda babu. Duk wurin da ka wulga hayaniya ce tare da tashin muryoyi ana hirar zumunci. Baba ɓaure ne ya ɗauki abin magana tare da yin gyaran murya, gaba ɗaya wurin ya yi tsit!

Godiya ya soma yi ga ubangiji, daga bisani ya faɗi irin nasarorin da ahalin ya samu daga kowane ɓangare. A hankali har ya gangaro kan maƙasudin taruwarsu, wato batun aure. Kowa ya nutsu ya kasa kunne yana sauraron bayaninsa, masu murna na yi akasin hakan kuma dai yana cikin ransu. Maganar daya furta ce ta ɗauke jin wasu daga cikin mazauna wajen na ɗan lokaci,

“Mun yanke zamu haɗa Yusuf da Labiba aure, Jawwad da Khamisa, da kuma Zahidaht da Kabir”

Dum! Sautin ya sauka a kunnuwansu, da fari kalon-kalo aka soma yi tsakanin, Amne da Hajiya Muwwadah. Haka ma tsakanin Yusuf da Ummunsa sai Labiba da take ji kamar almara. Wani irin yanayi ta sami kanta, ita ba farin ciki ba ita ba takaici ba. Haka dai tsaka tsaki, kafin daga bisani zuciyarta ta soma wassafo mata wasu cikin kamalolin Yusuf ɗin. Sai ta sami kanta da sakin murmushin da ita kaɗai ta san manufarsa. Ɓangaren Zahidaht kuwa, farin ciki ne ya mammateyeta tako’ina jinta take a duniyar sama. Gaba ɗaya wajen ya ɗauki kaburburi ana nuna jin daɗi,

“Alhaji ina da magana!”

Cewar Amne tana haɗe girar sama da ƙasa, ba ta saurareshi ba ta ci gaba,

“A tarihin wannan zuri’a kowa ya santa da auren zumunci amma kuma kowa ya san cewa auran na ƙuluwa ne bisa ra’ayin ma’auratan. Ta ya ya lokaci guda zaka dawo mana da shuɗaɗɗan tsarin da mun riga mun kawar da wanzuwarsa”

“Ƙwarai kuwa Hajiya Amne wannan abu dubawa ne, an tambayi yaran?”

Cewar Hajiya Muwaddah tana murmushin mugunta, duba da yadda taga kowa na bin Amnen da idanu. Dama haka ta saba ta hankaɗata ta magantu akan kowace muƙala ta gidan ita kuma tana daga gefe tana rura wuta. Baba ɓaure kansa ya ɗaure, a zuciyarsa ayyana ya aka yi rainin da matarsa ta yi masa ya kai haka? Har ya gindaya hukunci ta fito tana addawa da hakan. Lallai a wannan karon zai nuna mata so ba ya hana hukunta masoyi.

Ƙanannun maganganu ne suka soma tashi, ƙus-ƙus musamman ɓangaren Kabir fiffiƙa ya soma yi yana baya son Zahidaht. Abin da ya haifar mata da faɗuwar gaba mai tsanani, tare da soma tunanin wace irin rayuwa zasu yi tare. Domin ta san tunda Baba ɓaure ya furta, to fa ba fashi sai wani hukunci na ubangiji.

“Yusuf!”

Baba ɓaure ya kira sunansa, murya a kausashe ga kuma ɓarin ran daya gaza ɓoyuwa a muryar tasa. Hakan yasa kowa ya shiga taitayinsa,

“Na’am Baba”

“Zaka iya auren ɗiyata labiba?

Ya furta yana kafeshi da idanu take jikinsa ya yi sanyi, yana jin wani irin rauni yana kewayashi. A karon farko mutumin dake ƙumaji kullum wajen taimakon rayuwarsa yana neman alfarma mai matuƙar wuya gareshi. Ya sani bashi da matsala da mahaifansa, haka karan kanshi zai iya karɓar komai daga baban nasa amma kuma zuciyarsa ta fi tafiya kan tunanin Labiba da Amne fa?

“Idan baka ra’ayinta babu tursassawa tsakaninmu. Kaima ɗana ne kuma mafi soyu ba gareni. Zan iya jurar kowane sauyi daga gareka…”

Ya ƙarasa murya a raunane, domin ya gama karantar saƙon dake cikin zuciyar Yusuf ɗin, yadda yake ganin kaf ahalinsu babu mai iya ɗaukar tarangahomar ɗiyar tashi guiwarsa a sanyaye take da gazawar wanda ya ta’alaƙa da burinsa gareshi.

“Baba ka yi haƙuri bazan iya…!”

Ɗas! Ɗas!! Ɗas!!! Gabansa ya tsananta faɗuwa sakammakon haɗa idanu da mahaifiyarsa.Baba ka yi haƙuri, ba zan iya musu bisa umarninka ba. Ko da baka bani umarni ba Labiba ƴar uwata ce!”

Gaba ɗaya wajen ya ɗauki kabbara, jikin Baba ɓaure har tsuma yake tsabar farinciki. Labiba kuwa ji ta yi kamar an ɗaureta da sassari, me kalaman Yusuf suke nufi, yana nufin sonta yake yi ko kuma manna masa aka yi?”

“Labiba kina son ɗan uwanki?”

Muryar Baba Ɗangaladima ta ratsa cikin tunaninta, kanta a ƙasa bakinta ya yi nauyi. Ba zata taɓa iya kunyata mahaifinta ba duk rashin kunyarta. Sai kawai ta gyaɗa kai, wata irin ajiyar zuciya mahaifin nata ya sauke. Haka ma Zahidaht dai ta amince duk da tana tararrabin amsawar Kabir. Amma ga mamakinta koda aka tambayeshi kai tsaye ya amsa da yana sonta. Ta yi mamaki ƙwarai da gaske. Shi kuwa Kabir ya amsane, ganin Laby ta kuɓce masa kadda ya yi biyu babu kuma Zahidaht dai ba baya ba. Haka taro ya tashi rayukan wasu a daɗaɗɗe wasu kuwa sai ikon Allah.

Ba ƙaramin ɓaci ran mahaifiyar Labiba ya yi ba, ga kuma ƙawarta na ƙara ingizata. Tunda ta shiga gida take kai kawo tsakanin falo da cikin ɗaki. A haka Labiba ta risketa, idanunta ƙur a kanta tanata huci. A zuciye ta kai hannu ta damƙeta,

“Me yasa kika amince Labiba? Kinsan kuwa me ki ka aikata? Ki rasa wanda zaki aura duk taron samarin gidan nan sai wanda bai san ya tsinanawa kansa komai ba?”

“Amne ba zan iya kunyata mahaifina ba gaskiya, shi ma Yusuf ɗin ai baya ra’ayina daga dukkan alamu, amma kuma ya kasa kunyata Abbana sai ni da ya haifa?

“Allah Ya yi miki albarka Labiba”

Muryar mahaifinta ta ratso kunnuwanta, dukkansu suka juya domin basu san shigowarsa ba sai sautin muryarsa. Ya ci gaba,

“Sa’adatu wallahi baki isa ki ɓatamin rai akan auran nan ba, kin ji na rantse zan iya sahale naki auren da shikka uku ƙwarara matuƙar wata ɓaraka ta taso. A yanzu dai na gamsu Labiba ta haifu, dan haka duk wata ɓaraka da zata taso a nan gaba dake zan koka!”

Ficewa ya yi ba tare da ya tanka mata ba. Jiki a sanyaye suka wuce ɗakunansu. Kwana Amne ta yi tana tunanin mafita, sai dai kuma furucin mijin nata ya ɗaga mata hankali. Basu taɓa irin haka da shi ba, dan haka ta haƙure zata bishi yadda yake so kafin ta sami mafita.

Furucinsa ya zauna mata a zuciya ƙwarai. Bisa wannan dalili ne ya sa gaba ɗaya ta ɗauki ɗamarar saki jiki a gudanar da sha’anin bikin ba tare da ta nuna bata so ba. Sai dai a ƙasan ranta bata da maƙiyi sama da Yusuf ɗin. A gefe guda kuma Hajiya Muwaddah na ƙoƙarin zugata amma taƙi bata fuska kwata-kwata. Shi ma ɓangaren Kabir duk tunaninsa ya gaza gano makusar Zahidaht, tako’ina mace ce ta tserewa sa a. Dan haka ya tattara ya haƙura ya rungumi auren gadan-gadan, tare da nuna mata tsantsar kulawar data mantar da ita AUREN HAƊI za’ayi musu.

Yusuf ne dai kadaran-kadahan baya shigewa Labiba, ba kuma ya wasarerre da ita. Sossai Labiba ta saki jiki ta ƙara fuskantar Yusuf ɗin, sai ta ga ya yi dai-dai da ra’ayinta. Haka aka gudanar da biki hankali kwance, Kabir ya cale da amaryarsa ya cigaba da karatunsa haka ma Jawwad.

***

Zaman Labiba da Yusuf zamane me armashi, domin dai ta sameshi yadda take buƙata fiye ma da tsamaninta. Duk wata hidima ta gida tare suke yinta, haka zai gama ya fita buga-bugarsa ya samo kuɗinsa. Babu ƙyashi ko nawa zai samo to zasu ƙare ne a hidimar Labiba.+

Labiba ta sami yadda take so, tana burin auren miji bawan mace. Uwa uba kuma Yusuf mutum mai haƙuri, ga kawaici da kuma tsanin tsafta komai take so yana koƙarin yi mata shi koda kuwa ransa baya so. Ita ma kuma ta ajiye son jikinta, gidanta ƙwas-ƙwas irin na amare musamman idan yamma ta yi haka zata kunna tsintsiyar ƙamshi ya yi ta tashi. Kwanakin amarcinsu sun kafa tarihi mai girma a rayuwarsu, tare da alƙawarurruka wanda suka fi yawa sune yadda zasu kula da yara idan Allah ya basu.

Wata ɗaya biyu uku, a hankali ya soma fuskantarta. Gaba ɗaya malalaciya ce bata san aiki, ga shi kowace magana ta faɗo bakinta to zata yaɓa masa ba tare da la’akari da yanayinsa ba. Cikin wata biyar da auransu kayan ɗakinta sun fita daga hayyacinsu. Ɗan wanka da kwaliya da ƙamsassa gidan da take yi duk ta watsar dama na marmarine. Haka Yusuf ya dinga ƙoƙarin gwada mata kuskuranta, abin da ya soma haifar musu da saɓani kenan.

***

Kwanci tashi babu wuya wajen ubangiji. Suna shekararsu ta farko da aure ne al’amura suka soma ja baya. Bikinsu dama kafin azumine aka yi, basu da matsalar abinci sakammakon kayan gararta ga kuma kayan azumi da aka rarraba a ahalin nasu. Haka suka yi sallah kashirɓan cikin wadata ga ɗinkuna da Yusuf ya zuba a sallar ya samu kuɗi sossai. A haka suka gangara babbar sallah ma ya yi ɗinkuna babu laifi. Bayan sallah ne al’amuran suka soma ja baya, samunsa ya ragu sossai babu ɗinki sai ya koma harkarsa ta leburanci. Kwatsam ciki ya bayyana a jikin Labiba, ita da shi gaba ɗaya sun yi murna, haka suka dinga rainon abinsu. Da daɗi babu daɗi Yusuf yana ƙoƙarin faranta mata.

Tunda ta sami ciki ya hanata wanki, shi yake wanke musu kaya duka ya share gida ita kuma ta ji da hidimar girki duk da cewa idan ta dafa ba samun ciyuwa yake wajantaba. Matsalar da suka soma fuskanta gaba ɗaya Labiba ta ƙara ƙazancewa, ko ina zubar da miyau take yi, sai ya zamana ɗakinta baya zaunuwa saboda ƙarni. Ga rainuwa ta masifa, komai ya kawo a wulaƙance take karɓa tana mita. Baya ko ɗaga kai ballantana ya nuna mata ya damu. Musamman da ya lura da yanayin da take ciki. Duk wata kulawa data dace da mai irin lallurarta yana ƙoƙari sossai a kanta.

Ƙazantarta na damunsa musamman shi gwanin tsafta, haka zai zage ya gyara ko’ina. Ya sa turare amma kafin sati komai wajen zamansa daban. Ba ruwanta da idan ta cire kaya ta ɗauke. Wasu lokutan hadda masu lema, sai ɗakin ya dinga warin ruma. Haka ya yi ta yi mata uzuri, la’akari da masu juna biyu kan tsinci kansu a yanayin da ya fi natama. Dan haka ta miƙe ƙafa tana zuba taɓara son ranta.

Cikin ikon Allah cikinta ya shiga watan haihuwa mahaifiyar Yusuf ta rasu. Mutuwar data girgiza kaf ahalinsu domin Hajiya Hauwa’u mace ce mai yakana. Bayan makoki da sati uku Allah Ya sauki Labiba lafiya ta sami ɗiya mace. Ai kuwa murna wajen Yusuf kamar ya goyata, ranar suna yarinya ta ci sunan Hajiya Hauwa suke kiranta da suna Ummi. Baba ɓaure da Baba Ɗangaladima basu bar Yusuf ya kashe taronsa ba, komai su suka yi tun daga hidimar haihuwar har zuwa ragon suna. Anyi suna da kwana biyu, Labiba ta dawo gida wanka. Amne ta zage ta kula da ita yadda ya kamata. Ummi yarinya mai haƙuri da saurin shiga rai, kowa na ƙaunarta kodan dattakon kakkaninta da mahaifinta. Kullum Baba Ɗangaladima kafin ya fita sai ya leƙo ya ganta, da tsokana da komai zai ce,

‘Ku kawomin akori kishiya!”

Amne kan ce,

“Kakanin zamani da babu kunya a idanunsu, sun iya biyo jikanya”

Duk da yasan shaguɓe take masa, yakan maida abin a wasan dare domin cikar mutuntaka. Takai ta kawo tsegumi kala-kala cikin gida, tun wasu na mitar rashin kawaici, har suka sa idanu. Sunan a kori kishiya ya so yin tasiri ga Ummi sai da Labiba ta nuna jan ido sossai sannan aka daina faɗa.

***

ZAHIDA.

Zahidaht kuwa zaman nasu ba acewa komai, domin dai satinsu huɗu ta soma fuskanta asalin waye Kabir. Bata taɓa sanin halinsa haka yake ba, ta shiga nadama mara iyaka daga bisani ta rungumi ƙaddara tana yi masa addu’a.

Matsala ta farko da suka soma fuskanta, maganar karatu da ta yi masa. Nan ya sawa idonsa kwalin Audu ya nuna be son batunba, tun suna yi ita su kaɗai magana har kunnanan Baba ɓaure amma ya ƙyirmushe ya ce bazata yi ba. Tilas tana ji tana gani ta haƙura. Bata da aiki sai zaman gida kamar me gadi. Ganin zaman bazai mata ba yasa ta soma saida kayan gargajiya, wanda Yaya Asabe ke mata aikinsu ana turamata ƙasar da suke tana saidawa. Su kuka, daddawa kayan ƙamshi da sauransu har ma da lalle da salatif. Akan zuzzubasu cikin roba, tare da mana tambarin sunanta da addreshi. Ai kuwa nan da nan ta yi sabo da mutane irinta ƴan asalin nijeriya, idannunta suka ƙara buɗewa tana fuskantar rayuwa yau da gobe. A irin haka ta gano mijinta manemin matane ta hanyar wata mai siyan kayanta ƴar bariki kuma mashayi.

Ranar ta yi kuka ba kaɗan ba, babu wanda ta sanarwa sai Yaya Asabe, ita kuma ta fututtuke kan ta baro ƙasar domin ba zata zauna da fasiƙi ba. Sai dai kuma ƙiri-ƙiri ta nuna mata ba zata iya fuskantar iyayensu da mummunan labari ba. Kuma tana son mijinta zata iya zama da shi ta yi masa addu’a. Yaya Asabe ta ƙulu matuƙa, tana son ƙwatarwa Zahidaht ƴancinta sai dai ta lura so ya rufe mata idanu. Ta ciza ta hura amma ta ƙeƙashe ƙasa ta ƙi karɓar batun. Hakan yasa ta watsar da sha’aninta tare da yi mata gargaɗi kan nan gaba kadda ta nemi taimakonta kan matsalarsa. Ta kuwa amince da hakan ɗari bisa ɗari.

Sai dai tako’ina bata jin daɗin zama da shi. Zai shawo giyarsa idan ta gaya masa ƙarya ya naɗa mata duka. Hakan ba zai hana idan ta tashi ta kyautatta masa ba. Ya zageta ya hantareta kuwa ba komai ba ne, amma murmushi ne aikinta tare da furta,

“Na gode mijina!”

Kabir mugune sossai, ba shi da mutunci ga izgilanci da nuna kowa ba kowa bane. To itama Khamisa kusan duk matsalar ɗaya ce. Haka take ƙoƙarin danewa sai dai ta zo gun Zahidaht ta ci kukanta. Wani lokacin KUSKURAN WASU IYAYEN take gani, sun san halin namiji su ɗauki nutsatsiyar ɗiya su bashi kawai dan taƙamar cewa mace zata saitashi. Ita a rayuwarta bata taɓa ganin an ɗauki mace mara ji ba an bawa namiji, da sunan wai zai saitata. Hasalima gudun auransu ake koda kuwa cikin dangine amma namiji sai ka riskeshi da tarin guma-guman aibu sai ace duk abin da ya yi ADO NE.

Tana mamakin yadda laifi yake zama ADO! A saninta duka tabo sunansa tabo wala ga mace wala ga namiji. Sau tari Zahidaht ita take kwakkwafarta domin shi iskanci nasa ya wuce na Kabir gida yake komai gaban idanunta. Sai dai kuma, matsalar da aka samu Khamisa mace ce mai zurfin ciki da saka abu a rai. Gata da san a kula da ita kamar me, dan haka ta matsawa kanta da damuwa sossai.

A hankali ciwo ya soma cin Khamisat, kafin a farga ya ci ƙarfinta. Sau biyu tana yin ɓari saboda damuwa da tunani, asibiti sun yi iya bakin ƙoƙarinsu wajen nuna mata illar abin da take yi amma a banza haka ma ƴar uwarta. Damuwar data sawa ranta, ita ta haifar mata da ciwon zuciya ta mutu farat ɗaya. Tabbas mutuwarta ta taɓa iyayyensu, musamman da suka sami labarin abin da ya yi sanadin mutuwarta. Daga wannan lokaci suka sallama Jawwada, ba kuma su yi tunanin bincikar Kabir ba domin zahirinsa ya gamsar da su.

Mutuwarta ta sukurkuta Zahidaht ƙwarai, sai ma ya zamo sillar asassa damuwarta domin Jawwad dai gidansu ya dawo da zama kacokan kuma aciki ya cigaba da gudanar da rayuwarsa yadda ya saba. Bata da ikon magana, Kabir zai ci mutuncinta. Haka ta cigaba da haƙuri da daɗi babu daɗi. Komai ta yi a hantare. Babu yadda bai yi da ita ba akan ayi mata allurar hana ɗaukar ciki taƙi amincewa. Hakan yasa yake amfani da wani mai duk lokacin da zai kusanceta. Wanda matuƙar akwai ciki jikinta to kuwa a daren take ɓarinsa. Ba tare data ankare ba, cikin shekara guda da auransu ɓarinta biyar.

Tilas aka yi mata ɗaurin bakin mahaifa saboda tana neman samun matsala. Lokacin da ta sami labarin haihuwar Labiba kamar ta yi hauka. Kwata-kwata bata san cewar Kabir ne yake mata bita da ƙuli ba. Sai baƙar izaya da yake mata kullum. Tana da son ƙananun yara haka zata bi constomer ɗinta ta yi ta yi wa yaransu kyautar kayan wasa.

Wulaƙanci dai ba kama hannun yaro, tun tana daurewa har ya zamana ta soma yunƙurin barin gidansa. Sai dai bata da me goyon bayanta. Yaya Asabe ce dama maogararta kuma bata bata dama ba tun farko. Sai yanzu take hango KUSKURANTA da a baya ta ƙi amincewa da ƙuduri yayartasu. Sai dai kuma kash, a wannan lokacin bata da me goyon bayanta. Domin dai Yaya Asabe nuna mata ta yi ta je ta yi haƙuri, haka kowace mace take yin haƙuri da mijinta. In ta samu wannan, ba lalai ta sami wannan ba. Babban abinda ya ke ƙara dakusar da ita kuwa, ganin cewa da wuya ka ga a zuri’arsu wata ta kawo karar miji. Wannan na sarar da guiwarta matuƙa. Kabir kuwa sai abin da ya yi gaba. Musamman da ya kasance makarantarsu ana damawa da shi, akwai kwanya shi ne first class dan haka ƴan mata binsa suke ba shi ne yake binsu ba uwa uba ga kyau tsayayyen namiji ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *