UMM ADIYYAH CHAPTER 45 BY AZIZA IDRIS GOMBE
Www.bankinhausanovels.com.ng
ya hada
goshinsu wuri guda, yana zubar Kwalla, kamar ba shi Zaid Abdur-Rahman Nafada ba. “Na gode. Thank you so much.” Mikewa ta yi ta kauce masa, ta bar shi a durkushe a wurin yana bin ta da kallo.
Haka ya tashi jiki ba Kwari, ya san ta yi ne, ba don shi ba, sai don iyayensu.
************
Tana taya Maami hada abin karyawa ne washegari, amma gabaki daya ba ta cikin
hayyacinta. Tafiya take yi kamar wata mutummutumi. “”Ummu?” Ta ji muryar mahaifiyarta ta fito a tsanake. A hankali ta dago kanta tana
kallonta “Na’am Maami?” “Zo ki fada min menene yake damunki?”
“Maami…” Ta dan soma murmushi, sai kuma hawaye ya Dalle mata, jikin
mahaifiyarta kawai ta fada tana gunjin kuka, wannan ya tsinkawa Maami zuciya.
Sam ba ta son a kuma abinda ya faru a auren Zubaida na farko.
“It’s okay, babyna. Yi hakuri.” Hannunta ta ja zuwa falo suka zauna. “Menene?”
“Maami, yana yiwuwa mutumin da ka ke so, ka yarda da shi, ka ba shi komanka, ka zo ka daina sonsa?”
“Sai dai idan ba soyayyar ta gaske bace, dole akwai wani gurbi da ke rike da wannan a Kasan zuciyar mutum.”
“Maami Yaya Zaid fa ya daina sona, baya sona yanzu. Kuma da gaske na ke yi…”
“Ki daina fadin haka, na san rai ya kan baci, ana kuma samun sabani tsakanin
ma‘aurata, kowa na samun sabani. Amma haka ake daurewa a yaki wannan
matsalar, saboda duk aiki ne na shaidan. Shi yake cusa wasi-wasi a zuKatan
ma’’aurata ko yanzu na san kawai dai hakan ne ya faru. Ki yi hakuri, kin ji?”
“Maami me ya Sa sai ayi ta cewa mutum ya yi hakuri, bayan ba asan me yake Www.bankinhausanovels.com.ng
damunsa ba? Me ya sa ake tsammantan kullum mace ce ke laifi ko kuma kullum ita
ake tsammanin ta kasance mai hakurin?”
“Ba zan ce ki fada min me yake damunki ba, saboda wata Kila jin hakan zai iya sawa
na bi bayanki, saboda ni uwa ce, kuma ya zama na bi bayanki akan rashin gaskiya,
ko kuma na ji abinda zai sa na tsani mijinki, saboda bai kyautata miki ba. Idan da
sauran rabon zamanku kuma, hakan ba Karamin gibi zai kawo wa alaKarmu ba. Don
haka na ke roKonki, idan za ki iya, ki kwatanta yin hakuri, ki koma dakinki.
Ba zan iya facfa miki halin da iyaye suke shiga ba a duk lokacin da aka ce ‘yay’ansu
suna cikin tashin hankali a dakunansu ba. Abin da ciwo da cfacin rai, ba zan danne
ki, ki zauna ba, saboda na san me Kunci da frustration (bakin ciki) za su sa ki aikata.
Amma na san abu guda. A tafiyar nan gaba daya Ummu, daga ke har Zaid ba wanda ya fadi takamammen Www.bankinhausanovels.com.ng
abin da ya faru, ki na sane tare muka hacfaku da Abbanku, don mu ji meye yake
faruwa, amma dukkanku ku na rufawa juna asiri, kun Ki ku ce komai. Abbanku ya
bar ki, bai ce da ke ki koma ba, saboda yana da tabbacin wata Kila Zaid yana da laifi
ko kuma yana rufa miki asiri, mun bar ki, ki zauna ne, saboda hankalinki ya kwanta,
ki sake nazari kan al’amarin. Sai ga shi ku na rufawa juna asiri.
Idan ku na da wannan alaKar a tsakaninku, me ya rage maku? Bayan ku godewa
Allah, ku gode masa da ni’imar da ya yi maku, na samun hadin kai, da Kauna mai
zurfi. Ki na sane da halin rayuwar yau da inda aurarraki ba sa kai labari. Ku zauna ku
tattauna matsalolinku, ku magance su, kin ji ko?”
Kai kawai ta gyadawa Maami, ta kwanta kan cinyarta hadle da dunkulewa akan
dogon kujerar falon, haka Maami ta biye mata, tana shafa kanta har wata ajiyar Www.bankinhausanovels.com.ng
zuciya ta Kwace mata, barci ya yi awon gaba da ita.
*********
BABI NA TALATIN DA DAYA
Da yamma Abba ya nemi ganinsu duka su biyun, ya sa su a gaba a falonsa, don ya
yi masu magana. Ta kan Umm Adiyya ya fara.
“Duba ki gani Mamana, ga Maaminku nan yau shekarunmu Talatin da shida tare,
muna sabawa yau da gobe, dole akwai wannan, amma kin san me ya sa tsawon
wannan shekarun ba mu taba kai Kara ba, ko kai matsalarmu gaba?
Saboda idan tana fushi, ina saukar da kaina na danne zuciyata, haka ita ma idan ina fushi take kawar da kanta. Dadin Karawa tsawon wannan
shekarun ba ta taba nuna
min raini ko kasawa ba, duk da ta yi ilimi na zamani, ta taka matsayi na shugabancin
Alkalanci. Amma a gidanta ta san tana Kasan wani, tana ba ni girmana a matsayina na mijinta.
Ni ma kuma ban yi Kasa a gwiwa ba wurin tallafa mata, na riKeta cikin aminci,
saboda duk lokacin da aka ce ki na girmama tunanin namiji, ki na girmama
al’amuransa, ki na duba shawarwarinsa, to sai ki ga kin yi nasara a kansa. Don haka
na ke so ki natsu, ki tattara tunaninki gu Claya.
Aure ba abin wasa bane, da duk lokacin da ki ka ga dama za ki Cauki mayafinki, ki
tafi gidanku hutu, ko kuwa ki ce ke ba kya yi, kin gaji, ibada ce, idan kin rike shi a
hakan ya zo miki da sauki, domin duk abinda aka ce hanya ce ta shiga aljanna. To Www.bankinhausanovels.com.ng
lalle shaidlaan sai ya yi ta kawo cikas a cikin
Ba, babu abinda kuma shaidfaan ya fi
tunKaho da farin-ciki akai, irin ya ga ya raba mata da miji. Shin so ki ke yi, ki zama ta
hannun damar shaydaan?”
Umm Adiyya na hawaye, tana jin kalaman Abba, ina ma za ta iya jurewa ta yi yadda
suke so? Ta san idan ta faci yadda abubuwa suke za su fahimta, sai dai har yanzu
duk abinda Yaya Zaid ya yi, duk abinda zai mata, koda ta san girman laifin ba za ta
taba tona masa asiri ba, bare ta tonawa kanta.
Kallonsa ne ya koma kan Zaid. Wanda kansa yake Rasa, ”Zaid, Idan na ce zan yi
maku sulhu, ban sa da kai a ciki ba, tabbas ban yi adalci ba. Kai a nan gidan ka
tashi, ka san ko ni wanene, ka san kuma ba na wariya tsakaninka da su Saadik. Duk
da kasancewar duka daga kai har Adiiyya ba wanda ya fadi abinda ya faru. Amma
na fahimci ai ruwa baya taba tsami banza.
Su mata yadda suke tunani daban ne da namu, shi ya sa ake so mu mu ria finsu
hangen nesa, sannan kuma mu fi juriya da hakuri kan lamura. Ka san dai hakKin
iyalinka a kanka. Ummu amana ce a gunka, dubi ta yadda aurenku ya zo a jirkice
kadai ya isa ya sa ace ka kasance mai takatsantsan! Ita ikonka ce, kai za ka sa ta,
ka kuma hanata, haka nan kai za ka crata akan turba da take dai-dai. Www.bankinhausanovels.com.ng
Kai rufin asirinta ne, haka nan ita ma, kwanaki kun burgemu yadda ku ka fuskanci
matsalolinku tare, har ma babu wanda ya ji cikinku, sai da ku ka kawo Karshen
matsalar, duk da dai mun maku fadan hakan, amma wannan ya nuna mana cewa
kuma kun girma, kun mallaki hankulanku, za kuma ku iya daukar cawainiyar kanku.
Sai ga shi yanzu abu ya kai ga ku na so ku tona kanku har ma ke Umm Adiyya ki na
iya tattaki ki taho gida da sunan yaji? Ban ji dacfin hakan ba sam. Ban ji dadfi ba
Wallahi. Don haka Zaid ya kamata ku zauna ku tattauna matsalolinku, ku tuna kuma zaman
nan da ku ke yi don Allah ne, ibada ku ke yi, dole ku kasance masu jajircewa, domin
shaydaan na nan ta ko ina, jira yake yi ya kawo maku hari. Allah ya kad fitinar da
ke nan, ya kareku daga sharrin shaydclaan, ya ba ku zuri’a dayyaba.”
“Ameen, Abba mun gode.” Zaid ya amsa. Yana jin rushin kukan Umm Adiyya na
tashi. Amma haka ya daure, bai kalli inda take ba. Yanzu sai ya fi da jin nauyi, domin
ita ba ta cire abin da yake mata ciwo a ranta ba, sannan ga Abba ya yi mata fadia.
*********
A daren Abba ya ce Zaid ya dauke ta su koma, amma Zaid din ya ce, “Ba damuwa
Abba koda safe sai su koma, mun yi magana da Asma’, ta ce gobe ma suna hanya,
saboda su tayata kimtsawa.”
Hakan kuwa aka yi, sai washegari Adda Asma wacce take ta ba ta baki, tun
zuwansu a Safiyar ranar ta raka ta. Sai dai ganin baby Khadija (Maama) ya Kara
Haro mata komai sabo. Innayo dai da Asma su
suka yi ta bidirin gyara mata wuri, ita
kam dai tafe take kamar wacce Kwai ya fashewa ciki.
Lokacin da Zaid ya dawo gida, ya ji Kamshin turaren wuta, lumshe idanu ya yi yana
hamdala a ransa, bai san sanda idanunsa suka yi maiko ba, ji ya yi numfashin da yake shaka ya koma sabo. Www.bankinhausanovels.com.ng
‘Dakin sa ya wuce kai tsaye, ya watsa ruwa ya yi nafila hacle da godewa Allah. Yau
kam Umm Adiyya ta dawo, bai da sauran burin da ya wuce faranta mata rai da share
mata hawaye, ya kuma mantar da ita duk wani bakin-cikin duniya. Da da halin ya
shafe mata laifin da ya yi mata, da ya shafe, domin ba abin da yake dlaga masa
hankali irin idan ya kalli idanunta, ya ga irin kallon da take masa wanda har yanzu ya kasa fassara shi.
Ya dai ci yaki daya, ya samu ta dawo, sauran kuma aikin sa ne, an ce dabara ta
ragewa mai shiga rijiya.
A hankali ya tura Kofar dakin ya shiga, jin Karar Kofar ne ya sa Ummu Adiyya ta dan
dago kanta, ba abinda yake yawo a kanta, sai fadfan da su Maami suka yi mata kan
ta dawo. Wannan ya sa ta daure, ta tashi zaune ta gaishe shi.
Sanye yake da baKar soci mai gajeren hannu da wandon jins mai duhuwa a jikin sa,
Kamshinsa duk ya gauraye dakin, idanunta ta sadda Kasa, “Ina wuni?” Ta fada a
Sanyaye.
Murmushinsa na gefe mai matuKar tasiri a gareta, ya sakar mata, ’Lafiya Twinkle,
barka da dawowa.”
Yake ta yi masa, ta koma ta kwanta had da juya bayanta, wasu zafafan hawaye ne
suka bi fuskarta.
Ta tsani sanin cewa wannan barakar ta shiga tsakaninsu, kuma ba yadda za ayi ta
gyaru, akwai wani abinda ya _ rugurguje tsakaninsu, lokacin da take roKonsa da ya
Kyaleta, amma ya Ki Ryalewar. Lokacin da ya tsallaketa, ya bar ta a cikin mawuyacin
hali, lokacin da ya yanke shawara ya Zo ya yi mata wannan tozarci da wulaKancin.
Hannunsa ta ji yana shafa kanta ta saman gashinta a hankali, cikin alamar lallashi.
Daskarewa ta yi idanunta suka firfito waje. Da sauri ta miKe daga kan gadon, Www.bankinhausanovels.com.ng
tsayawa ya yi yana kallonta cikin mamaki, kafin ya fahimci me take nufi.
“Oh, sorry ban yi niyyar… oh.. zo ki kwanta, ba abinda zan miki…” Hannu ya sa ya
shafo saman kansa, kafin ya mike da shirin barin dakin.
“Yaya Zaid…”
Cak! Ya tsaya kamar falwaya a tsakiyar Cakin. Idanunsa a runtse, bai taba jin
mutuwar jiki da matsannancin da-na sani ba irin yadda ya ji a daidai lokacin da ya ga
kallon tsantsar razana da tsoro a Kwayar idanun Umm Adiyya, wannan ya hana shi
hacla idanu da ita, koda ya juyo yana fuskantarta.
“Don Allah, don Allah kar ka sake taba ni.” Ta facla idanunta a bushe. Amma shi ya
hango wannan karyayyen Oangaren Umm Adiyya, shi ya aikata haka gareta, shi ya
karya ta. Kai ya gyada mata hade da lumshe idanunsa.
“Nayi alkawari. Sai duk randa ki ka ce da kanki. Idan ba ki ce ba, ba zan Kara zuwa
inda ki ke ba.” Yana fadlin haka ya fice daga Cakin yana takawa ta baya-baya.
Sai da ya fita, Umm Adiiyya ta rushe da kuka mai tsannani, “Ya-Salaam! Allah gani
gareka. Allah Ka nuna min hanya ma fi daidai. Allah ka ba ni juriyar sauke nauyin da
yake kaina.”
Daga wannan lokacin ta Kara debe darenta wurin bautawa Allah, dama tsayuwar
dare Cabi’arta ce, don haka Kaimi ta Kara akan na da. Ba inda take fita ta je, abinci
ma dai tana cinsa ne, don kar ta yi wa kanta illa.
A wata ranar Laraba ne ta bude Kofarta za ta sauka Kasa cikin doguwar rigarta mai
roba-roba, ta yi kicibis da shi a nan.
Idanunsa sun yi duhu, sun dan fada kwarminsu, amma har lokacin Kwarjininsa bai
bar shi ba, saukar da idanunta ta yi, saboda nauyin nasa idanun a kanta. “Lafiya ki Www.bankinhausanovels.com.ng
ke dai ko, ban ji ki ba jiya da yau?”
Kanta ta gyada masa. Kallon idanunta ya yi, yadda suke kumbure sun yi luhuluhu,
hannunsa ya daga zai shafa Kasan idanun, gaba daya ta canza kamar ba Umm
Adiyyarsa ba, mai murmushi da kawaici, da shiru-shiru, mai shiga rai da tsokana da
ban dariya da shagwaha da dirama.
Sai ya tuno alKawarin da ya yi mata, nan da nan ya maida hanunsa ya dunkule,
saboda wani matuKar buKatar riketa a jikin sa ya ji, ya ba ta hakuri, ya rarrasheta ya Www.bankinhausanovels.com.ng
zare mata ciwon da ya haddasa mata.
“Ehm! Ba kya zuwa aiki. Department sun yi korafi.”
“Oh! Na zaci kai ne shugaban wurin.” Ta facla a sanyaye, amma ya san ma’anar da
ke oye cikin kalamanta.
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG