HEEDAYA CHAPTER 2 BY By Khaleesat Haiydar
Www.bankinhausanovels.com.ng
Heedayah ta fi minti biyar a tsaye tana Shesshekar kuka, jin bbu alamar xai dawo ta fara tafiya a hankali tana yi ma
kanta jagora da hannuwanta biyu, da tayi tafiya kadan sai ta tsaya, ihun da taji aka yi wajen ya sa ta tsaya a mugun
tsorace, ji tayi kamar an hankadata da katon abu ta fadi kasa, tun tana jin surutun jama’an wajen sama sama har ta
daina ji kwata kwata. A hankali Heedayah ta bude ido tana laluba inda take kwance, muryar namiji taji a gefenta
yana cewa “Alhamdulillah she is back (Ta farfado….)” Ya kamo hannunta yana mata sannu murmushi dauke
fuskarsa, kanta da yyi mata nauyi kawai take gyadawa tana kokarin mikewa xaune, ya komar da ita ya kwantar yace
“A’a bari likita ya xo ya duba ki, bari in kirasa, ina xuwa ynxu” ita dai kai kawai take gyadawa, ba a dau lkci ba sai
ga mutumin ya dawo da likita, directly Heedayah ke kallon fuskar likitan, ya sakar mata lallausan murmushi wanda
bata san ma yana yi ba, likitan ya xaunar da ita ya dafa goshinta yace “Ya jikin baby girl?” Kifta ido ta shiga yi tace
“Where am I? (Ina ne nan?)” Yana murmurshi yace “Hospital dear, fatan dai babu inda yake maki ciwo” kanta ta
nuna masa, yace “Xai daina in sha Allah, xa a baki magani yanxu” shi dai wanda ya kirawo likitan kallonsu kawai
yake, A hankali tace “Xan yi fitsari” likitan ya saukar da ita kasa, yana nuna mata kofar bandaki, hannunsa ta kama,
yace “Xa ki iya dear, walk gently now (Kiyi tafiya a hankali….)” kin motsawa tayi, sai kuma a hankali tace “I can’t
see (Bana gani)” da mamaki likitan da Mutumin da ya kawo ta asibitin ke kallonta, likitan yace “Why? is the eyes
paining you? Idanuwan suna maki ciwo ne” Ta girgixa masa kai yace “Toh yi tafiyar ki da kanki” ta rike hannunsa
gam kamar xata yi kuka tace “Ae ni bana ganin hanyan” sosai hankalin likitan ya tashi, haka zalika Mutumin dake
Ward din da ya mike shima yana kallonta, don gaba daya tunaninsu a lkcn ta dalilin accident din ne vision dinta ya
samu matsala, Banda innalillahi wa Inna ilaihi raji’un bbu abinda Mutumin ke furtawa yana kallon Heedayah.
Likitoci sun fi biyar a kan Heedayah, all trying to figure out where the problem is, ko wannensu na kokarin gano
inda matsalar take amma abu ya ci tura, ita dai sai bin duk inda ta ji motsi take da manyan idanuwanta, duk da ba
ganinsu take ba, daga karshe dai aka ba Mutumin da ya kawota shawara kawai ya kai ta asibitin ido, ba karamin
tashi hankalin wannan mutumin yyi ba, haka dai ya biya bill din asibitin ya dau Heedayah xuwa asibitin ido dake
nan cikin garin kano. Dai dai lkcn da suka shiga haraban asibitin motar optician din dake duba Heedayah tun da aka
haifeta har kawo lkcn da aka yi referring dinsu india kuma na fita daga asibitin. Mutumin dake rike da hannun
Heedayah bayan ya sauketa daga motar ya duka dai dai fuskarta cike da damuwa yace “Daga yaushe kike daina gani
Little girl? What was the last thing u saw? Meye abu na karshe da kika gani?” Tayi shiru sai kuma tace “Nima ban
sani ba” Damuwa ne sosai fuskarsa, yace “Toh daga ina kike jiya da magariba kuma ina xa ki? Where are ur parents?
Ina iyayen ki” Shiru tayi, staring at him kamar tana ganinsa, nan ya shiga tantaman ganin da tace bata yi, ganin
yanda take masa kallon cikin ido ya kai yatsunsa har kusa da idonta yaga bata rufe ba har sai da ya taba lashes dinta,
kikkifta idon ta shiga yi, yace “ki min magana, Where are ur parent? Ina iyayenki” Ta girgixa kai tace “I don’t know,
(Nima ban sani ba)” da mamaki yace “Baki san inda iyayenki suke ba, ina xa ki jiya?” Ta fashe da kuka tace “Nima
ban sani ba, kawai an saka ni a mota aka wuce da ni, sai na ji an sake hawa da ni bicycle kuma ynxu ban san inda
aka kawo ni aka ajiye ni ba” rasa abun cewa yyi yana kallonta, can dai yace “Ya sunan garin ku?” Tace “Abuja” ya
xaro ido ganin dai a garin kano suke ynxu, yace “Ya sunan baban ki?” Tace “Abba” yace “Abba??? Mamarki fa?”
Cikin rawar murya tace “Ammi” Innalillahi ya dinga nanatawa a ransa, sai kuma yace “Abuja ya sunan anguwan
ku?” Tace “Abuja ne” mikewa yyi just as confused as she is, ya kalli agogon wrist dinsa dake nuna goma na safe,
yana rike da hannunta yana mata jagora suka shiga asibitin, Ba su suka fito ba sai kusan Azhar after series of
Diagnosis da ya tabbatar da she was born with the blindness, a haka aka haifeta, kuma tana stage din operation din
karshe kenan wanda xa ayi mata idan ba ayi nasara ba she will remain blind till the end (Xata xauna a makauniyar ta
har karshe…) Alhaji Ahmad na rike da hannun Heedayah xuwa gun motarsa a haraban asibitin, bai ta6a shiga rudani
irin na ranan ba, to ina xai kai wannan yar baiwar Allahn, kara kallonta yyi yaga bata wuce autarsa Rabi’ah ba,
yanxu ina xai samo iyayenta ko wani wanda ya santa??? Yanke shawarar kai ta police station kawai yayi, yasan su
xa su san yanda xa su yi da ita, driving kawai yake absentmindedly ya ji Heedayah tace “Abba, yunwa nake ji” ya
d’an kalleta yana ci gaba da tukinsa yace “Me xa ki ci?” Tace “Shayi da bredi da kwai” sake kallonta yyi sannan ya
dauke kai, Mintuna kadan ya rage ya isa nearest Police station, sbda yunwan da tace tana ji ya dau wata hanyar
daban xuwa wani restaurant, abinda ta ce take so ya sa a kawo mata, ya tabbatar shayin ba xafi sosai sannan ya bude
mata bread din da kwai ya mika mata, ganin yanda take ta lalube lalube kar ta kwa6ar da shayin ya mike ya koma
kusa da ita, feeding dinta yayi har ta ce ta koshi, Banda kallonta bbu abinda yake yi cike da tausayinta, Bai taba
ganin irin haka shi dai ba, yar karamar yarinya da makanta, tace “Abba…” Ya shafa kanta yace “Daughter murmushinta me kyau tayi tace “Thank you” Bai ce komai ba, Amma naxari me iri iri yake yi a ransa, bayan few
seconds ya kalleta yace “Ya sunanki?” Tace “Heedayah” Ya lumshe ido ya bude yace “Heedayah baki san anguwan
ku a Abuja ba? Ki tuna da kyau ki gaya min daughter” Tace “Abuja ne gidanmu” ya girgixa kai ya mike yace “Tashi”
tashi tayi ya kama hannunta kasancewar ya biya bill din suka fita xuwa gun motarsa, bayan sun bar Restaurant din,
ya dau hanyar police station, Yana rike da ita suka shiga ciki, Bai bata lkci ba bayan yayi report ya bar Heedayah
tare da su don yana da meeting da xai shiga karfe daya kuma a ranan yake son barin garin kano, sai dai har ya isa
inda xa shi hankalinsa ya ki kwanciya, gaba daya ya rasa sukuni…. Washegari karfe takwas a police station yayi ma
Alhaji Ahmad to be sure an samu iyayen Heedayah duk da yasan da kyar hakan ya faru a rana daya kawai, Bayan
sun gaisa da policemen dake wajen suka sanar masa an kai ta orphanage for the meantime, shiru yyi na few seconds
kafin yace “Shikenan, nagode….” Wani police officer yace “We will try our best in sha Allah, an kuma riga da an
fara broadcasting tun jiya, so hopefully she will get back to her parent soon, (xa mu yi bakin kokarin mu na ganin ta
koma ga iyayenta)” Alhaji Ahmad yace “Allah ya sa hakan” Sallama yyi masu ya bar station din. Ammi dake xaune
saman gado a dakin asibiti da take ta kai hannunta xuwa na Mahaifin Heedayah dake xaune gefenta sai dai yyi nisa
tunanin da yake, juyawa yyi ya kalleta, hawayen da ke gefen idonta ya gangaro cikin sanyin murya tace
“Muhammad pls let nothing happen to my daughter, plss nothing shud happen to Heedayah, (Kada wani abu ya sami
Heedayah) ku dawo min da yarinya ta” Uncontrollably ta fara kuka, tun xuwansu asibiti kwana biyu kenan sai yau
tayi magana, Alhaji Muhd ya na rike da hannunta trying his best to be strong yace “Nothing dear, I mean nothing
will happen to our daughter, (Babu abinda xai sameta) in sha Allah, zata dawo garemu soon da izinin Allah, hukuma
na bakin kokarinsu, ki kwantar da hankali don Allah” Kuka kawai take bata ce komai ba, she looks so weak, ya sake
hannunta ya fita don kiran likita. Da yammacin ranan Alhaji Ahmad ya gama shirin komawa kaduna, sai da ya bar
gida sannan yyi deciding kafin ya tafi ya fara xuwa orphanage da yan sandan suka ce masa an kai Heedayah, Bai yi
wani wahalan shiga gidan marayun ba bayan ya nuna Identity dinsa, ya dinga bin yaran dake wasa a waje da kallo,
lkci daya idonsa ya sauka kan Heedayah dake rakube can gefe ita kadai staring into space, hannunta rike da ledan
biscuit, kallonta ya dinga yi kafin ya nufeta ya duka kusa da ita har sannan bai daina kallonta ba hawaye ne cike
manyan idanuwanta, lkci daya ya ji jikinsa yyi sanyi sosai, ya dafa goshinta yace “Heedayah” Hannunsa ta kama
kamar tana jiransa a lkcn, sai ta fashe da kuka tace “Abba” Ya jawota jikinsa yace “Why are you crying? (me yasa
kike kuka” Cikin rawar murya tace “Suna min dariya bana gani, wata ta karbe min biscuit guda daya, Abba ka kai ni
gida gun Ammina….” Bai ce komai ba, can ya mike yana rike da ita yace “Toh daina kuka” goge idonta tayi, yana
rike da ita still ya tafi office din shugaban wajen, bayan sun gaisa yace “What are the process before adoption of a
child in here? (meye matakan bi kafin daukan yaro a gidan marayu)” Tana kallonsa tace “It’s a very long process
mister, (Matakan suna da yawa gaskiya” yace “Alright…. I will be back in some minutes time (Xan dawo nan da
wani lkci)” kuka Heedayah ta dinga yi sosai da ta gane tafiya xai kara yi ya bar ta, haka nan ya bar ta gun masu kula
da marayun wajen ya wuce, police station ya koma. Asp ya ajiye pen din hannunsa yana kallon Alhaji Ahmad yace
“So you mean kana son tafiya da ita har lkcn da Allah xai sa a samu iyayenta” Alhaji Ahmad yace “Yes exactly sir”
Asp yace “Sai dai kasan da cewar you didn’t adopt her, duk lkcn da iyayenta suka bayyana xa a mayar masu da ita”
Alhaji Ahmad yace “In sha Allah, Ni ma nafi son haka, and as I have said sbda health issues dinta yasa xan tafi da ita,
she won’t cope in the orphanage, i will be dropping all necessary information kamar yanda ka bukata duk da ni ba
bako bane a gun ka, idan ma baka san ni yanda ya kamata ba, na tabbata kasan Yayana ai” Murmushi Asp yyi yace
“Sure, I am not doubting you Barrister, Allah ya taya ka riko har kafin Allah ya bayyanar da mahaifanta” Alhaji
Ahmad yace “In sha Allah, nagode sosai for understanding me” Wani short note Asp din yyi a takarda yayi stamping
sannan ya kira wani police officer ya koma orphanage din tare da Alhaji Ahmad don dauko Heedayah. Har sannan
Heedayah na xaune inda Alhaji Ahmad ya bar ta tare da daya daga mai kula da su, sai dai mai kula da su din bata
gun, ita kadai ce xaune gwanin ban tausayi, har sannan ta ki cin biscuit din, Bbu 6ata lkci aka basa ita ya bar
orphanage din bayan ya sallami police officer din, he can see how happy Heedayah was bayan sun shiga mota, ganin
tana ta kokarin bude biscuit din hannunta ya amsa ya bude mata ya mika mata, tace “Abba xaka maida ni gun
Ammina da Abbana?” Ya shafa kanta yace “In sha Allah daughter” tayi murmushi sosai tana cin biscuit din hannunta,
seat belt ya sa mata, yana kallon agogo dake nuna masa biyar saura yan Mintuna, ya gama addu’o’in da xai yi sannan
ya dau hanyar fita kano xuwa garin kaduna…..Har suka shigo cikin garin kd wajajen karfe tara na dare bacci Heedayah take, slowly yake driving bayan ya shigo
anguwar da gidansa yake, anguwar so silent ga fitilu ta ko ina da ya haska anguwar kamar da rana, bakin wani gate
ya ja ya tsaya yyi horn, wanda hakan ya farkar da Heedayah, laluba motar ta shiga yi tace “Abba….” yana kallonta
yace “I am here…” Bata kuma cewa komai ba dama kawai so take ta tabbatar bai bar ta bane, ya d’an yi murmushi ya
ja motar xuwa cikin babban compound dake dauke da gida ginin duplex bayan Mai gadi ya bude masa gate da sauri,
parking yyi a space din da aka tanadar domin parking a compound din, wani matashi ne da baxai wuce 28 ba ya fito
daga cikin babban building din gidan, ya nufo parking space din, Alhaji Ahmad ya kashe motar ya bude ya fito,
Matashin ya d’an risinar da kansa yace “Sannu da hanya Abba” Alhaji Ahmad yace “Yauwa sannu, but ka damu ka
kirani tun jiya da kake min sannu da hanya ynxu??” Yana fadin haka ya wuce sa ya xaga daya side din motar, da ido
dogon Matashin ya bi sa bai ce komai ba, Alhaji Ahmad ya bude door din side din da Heedayah take, ya kamo
hannunta ya sakko da ita daga cikin motar, Matashin ya d’an koma baya yana kallonsu a bit surprised, Alhaji Ahmad
yace “Ka fiddo min laptop dina bayan motar, they are some other things ma ka taho da su ciki” Yana fadin haka ya
nufi entrance din shiga gidan yana rike da Heedayah, Matashin ya bude motar ya dauko abinda yace masa sannan ya
bi bayansu, Alhaji Ahmad na shiga parlor Rabi’ah da Khadija suka taso da gudu don rungume sa, sai dai ganin
Heedayah da yake rike da duk suka tsaya basu karasa gun nasa ba, Khadija tace “Who is she Dad?” Yana kokarin
cire takalminsa yace “Sabuwar ‘yar uwar ku” kallon juna Khadija suka yi da Rabi’ah, ya karasa parlon ya xaunar da
Heedayah kan kujera sai dai ta ki sakin hannunsa kmr xata yi kuka tace “Abba kar ka bar ni don Allah” Yace “Noo
baxan bar ki ba, we are home yanxu” Yana fadin hka ya kalli Khadijah yace “Ina Mumyn ku?” Khadijah ta d’an
cinno baki tace “Upstairs” ya daga Heedayah ya wuce sama da ita, Khadija da Rabi’ah suka juya suna kallon
yayansu dake tsaye bakin kofa yana kallon ikon Allah shi ma, da sauri suka nufesa a tare suka ce “Ya Shuraim who
is she? Wacece ita” Ko kallonsu bai yi ba, ya nufi part din Abbansu don ajiye masa system dinsa dake hannunsa.
Alhaji Ahmad ya bude kofar parlon Mai dakinsa still holding Heedayah’s hand, dai dai fitowar ta daga bedroom
dinta, ya xaunar da Heedayah saman kujera kafin yace komai tana kare ma Heedayah kallo daga sama har kasa tace
“Waye wannan kuma Barrister?” Yace “sannu da hanya ya kamata ki fara min sannan tambayoyin ki su biyo baya” a
takaice tace “Toh sannu da hanya, wacce yarinyar ce wannan ka shigo min da ita har parlor?” Sai a sannan ya daga
kai ya kalli matar tasa yace “Bakuwa ce” Ta d’an yatsina fuska tace “Bakuwa kuma? Daga ina? Kuma ina xa a kai
ta?” Yace “Eh bakuwa…. Daga kano, kuma nan xata xauna in sha Allahu rabbi” Da mugun mamaki tace “Yar wacece
ita din?” Yace “Baiwar Allah ce…” A kufule tace “Plss be straight barrister, ina ka samo yarinya? Kowa ma bawan
Allah ne ai” Barrister yace “Gashi nan na gaya maki, what else did you want to know, me kuma kike son sani”
kamar jiran tambayar take ta mayar masa da amsa da sauri tace “Manufar xuwanta gidan nan, sannan mun hada wani
dangantaka ne da ita??” Ya gyara xama yace “Manufar xuwanta gidan nan shine don ta xauna da mu na wani d’an
lkci, dangantakar mu kuma kawai shine kasancewar ta ‘yar uwar mu musulma” Kallonsa ta dinga yi, surprised,
Furious, and mad at the same time…. Blankly tace “I don’t get you Abban Shuraim, ban gane abinda kke nufi ba, a
ina kasamo wannan yarinyar??” Ya mike yace “Her parents are missing, so we need to look after her kafin Allah ya bayyanar da iyayenta, all that aside, she is blind Hajiya Maryam, makauniya ce….” Yana fadin haka ya fita daga
parlon….. Hajiya Maryam da ta bi sa da kallon mamaki lkci daya tace “Tabdijam!!! Toh sannu Humanitarian, Do�gooder…. sai kuma nace maka gidana orphanage ne (Gidan marayu) ko kuma police station?? to wllh ka saurareni da
kyau, yarinyar nan dai baxa ta xauna gidan nan ba, me muka hada da ita daga ganin yarinya a titi ka kinkimota ka
kawo mana gida wai iyayenta sun 6ata kamar wasu gyada, Anya ma Barrister kasan me kake yi kuwa, yanda duniyar
nan bbu gaskiya kwata kwata kowa ya xama mugu ya xama abun tsoro ka dauko mana yarinya ka kawo gida?? A’a
wllh ba gidana ba, ka dauketa ka kai ta police station ko kuma ka kai ta gidan marayu” tana fadin haka ta wuce
dakinta rai 6ace don daukan wayar ta, Heedayah dai na xaune sai kallon direction din da masifar ke tashi take yi,
gaba daya a tsorace take, lkci daya hawaye ya kawo manyan idanuwanta…. Bayan minti biyar Hajiya Maryam ta fito
dakinta tana kallon Heedayah tana huci ta daka mata tsawa tace “Ke maza tashi ki fita ki ban waje kar in illata ki….”
Mikewa Heedayah tayi da sauri ta fashe da kuka tana laluben hanya tace “Abba where are you” muryarsa ta ji yace
“I am here….” Har ya karaso cikin parlon kallon Hajiya Maryam yake, calmly yace “Wannan ya xama na karshe a
gidan nan, kar ki sake yi mata tsawa, nace a gidan nan Heedayah xata tsaya har sai an samo iyayenta, I mean my
words” bude baki tayi tana kallonsa da farko, sai kuma tayi wani murmushi me sauti tana tafe hannu tace “Toh sannu
Humanitarian, idan ni ban kai inyi magana ka ji ba nasan baxa a rasa wa enda xa su yi maka ka ji ba, look Ahmad
it’s not as if i am being wicked, ni ba muguwa bace Allah ya ga xuciyata kawai xamanta ne damu bna so don
hankalina bai kwanta da hakan ba, to wai ma akan me xata xauna da mu, kai da kke lawyer ai ya ci ace ka fi ni sanin
me duniya ke ciki, to idan ba akwai wani boyayyen lamari a kasa ba daga xuwa meeting kano sai ka dawo da
yarinya wai ka tsince ta a titi bbu iyaye, Kar ka manta idan kai lawyer ne to ni kuma matar lawyer ce….” Ya dakatar
da ita yace “Wallahil Azeem Maryam wannan yarinya a hanya na hadu da ita kamar ynda na fada maki, mota ce ta
bigeta muka yi asibiti da ita, I was there har ta farfado…. Let just stop all this, Maryam put Rabi’ah or Khadijah in
her shoes plss” a mugun fusace tace “Allah ya kiyaye, I can’t imagine my children in her shoes, why will I? Kar ma
ka gaya min haka, Ni dai abinda na sani shine hankalina bai kwanta ba kuma baxai ma ta6a kwanciya da yarinyar
nan ba, wa ya sani ma ko aljana ce da gashi haka??” Bai kuma ce mata komai ba ya kama hannun Heedayah dake
kuka a hankali ya fita parlon da ita xuwa downstairs…. Hajiya Maryam ta kasa zaune a parlon nata sai xagaye take,
bude kofar aka yi Shuraim ya shigo da sallama can kasa, Hajiya Maryam ta kallesa da sauri tace “Shuraim kana
ganin mahaifinku koh? Me yake nufi da kawo mana yarinya gida ba dangin Iya balle na Baba, ya san yar wacece ko
ma shegiya ce bai sani ba kawai ya kawo mana ita gida, wllh something is fishy, kuma in dai yarinyar nan xata
xauna gidan nan sai dai mu bar masa gidan shi da ita gaskiya, don mu ba gantalallu bane, wai kuma makauniya ce
kai ka ji fa???” Tun fara maganar ta sai a sannan Shuraim ya kalleta da sauri jin wai makauniya ce, Tayi mitsi mitsi
da ido tace “Wllh haka yace Makauniya ce bata gani, kuma naga alamar hakan, she is blind, oh innalillahi wa Inna
ilaihi raji’un, me ya samu Barrister ni Maryam… Anya kuwa yana right senses dinsa??” Shuraim dai bai ce komai ba
ya juya xai fita, a mugun fusace tace “Toh malam ba shiru xaka yi ba ka wani juya sumui sumui xaka wuce, xuwa
xaka yi ka samesa tunda yana jin maganar ka, ka lallabasa ya fitar mana da yarinyar ya kai ta police station, bbu
ruwana da gayyar tsiya, yarinyar nan baxata kwana gidan nan yau ba…” Shuraim na fita ya nufi Part din
mahaifinsa, ya bude kofar parlon da sallama, Heedayah ce kawai xaune kasan carpet dake parlon ga cup din fresh
milk a hannunta, jin an bude kofa ta dakatar da shan madaran da take yi tana waige waige, bai kalli direction dinta
ba ya nufi dakin Abbansa, sallama yyi bayan ya amsa masa ya shiga, xaune ya samesa gefen gadonsa, ya karasa ya
xauna nan kasa gabansa yana kallonsa yace “Ya hanya Abba?” Abba ya kallesa yace “Alhmdllh…” Shuraim ya d’an
shafa kansa yace “Abba, akan wannan yarinyar…..” Sai kuma yyi shiru, Abba yace “Yes, what about her? Ina jin ka”
Shuraim yace “Is she suppose to be here?” Abba yace “Of course, ai nan din gidana ne ba na wani ba, so why won’t
she be here?? Me kuwa xai hana xamanta a nan tunda na amince da hakan?” Shuraim ya girgixa kai alamar ya rasa
abinda xai ce, Abba yace “Yes gidana ne, ba naka ba, balle na Mahaifiyar ka” Shuraim yace “But Abba hakan ba dai
dai bane, bbu abinda muka hada da ita, ba mu san ta ba, we don’t even…” Dakatar da shi Abba yyi so pissed off yace
“Get out my frnd, who are you to question my orders? And don’t u even have human conscience? Xaka so kanwarka
ta tagayyara a rayuwa?” Mikewa Shuraim yyi yace “I am sorry” daga haka ya nufi kofa ya fita, satan kallon
Heedayah yyi, lkci daya ya wani hade rai ya fice daga parlon.⁴