UMM ADIYYAH CHAPTER 47 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 47 BY AZIZA IDRIS GOMBE

                Www.bankinhausanovels.com.ng 


Innayo dai ganin ba ta motsa ba, abin sai ya ba ta tsoro, ta kidime. Wayar Maami ta
nema, ba tare da Data lokaci ba.
“Eh, ina ga ba ta da lafiya ne, shi ma Yayan ya fita baya gida.” Www.bankinhausanovels.com.ng
“To ki zauna tare da ita, zan taho yanzu.” of oie 2 2

*******

BABI NA TALATIN DA BIYU

Innayo dai sai gyaCla kai take yi kamar Kadangaruwa. Ita dai ta san koda rashin
lafiyar ma, akwai babbar matsala tsakanin uwayen gidan nata. Don cikin kwanakin
nan dukkansu babu mai walwala a gidan, kai an yi watanni ma ba walwala a gidan
nan, sabanin zuwanta a karo na farko yadda ta sansu.

Kamar daga sama ta ji magana can Kasa-Kasa, da sauri ta Karasa inda Umm Adiiyya
ke kwance. “Hajiya Ummu, wani abu ki ke so?”
“Da ba ki kira Maami… Ba.” Ta fadla tana hadliye yawu da Kyar, tana numfarfashi. Da
sauri Innayo ta mike ta samo mata ruwan sha ta ba ta.


“Ga shi ki sha ruwa ko za ki ji dama-dama. Ko za ki koma saman gado ne ki kwanta
da kyau?” Www.bankinhausanovels.com.ng
“Na gode, amma hakan ma ya yi. Idan kin fita, ki jawo min Kofar cakin.”
Nan ta ci-gaba da kwanciya har ta ji tsayuwar mota a Kofar gidan. Gabanta ne ya yi
mummunar factuwa, shi kenan yanzu kam nata ta sameta. Amma ko me zai je ya zo,
hakan dai za ta fadla masu abin da ake ciki.
Ta san ba za su karbi labarin ta dadfin rai ba. Saboda rabin ransu baya laifi a
wurinsu. Koda yake ba laifinsu bane, haka nan Zaid yake da shiga zucci, ko ita nan
duk abin da suke ciki, bai rage mata abin da take ji game da shi ba, rayuwar ce dai Www.bankinhausanovels.com.ng
kawai ba zai yiwu su yi ta a tare ba.
Domin da alama, hanyar jirgi daban, ta mota ma daban. A lokacin ne ta Kara jin wata
fargaba ta sauka mata, shi kenan yanzu Zaid ya saketa, ita ma aurenta ya mutu, ita
ma za a fara Kirga ta zawarawa kenan, tunda miji ya saketa. Amma fa duk ita ta ja
wa kanta…
Tana cikin wadannan saKe-saKen ta ji an turo Kofar fakin an shigo. Salati ta ji
Maami ta saka, murmushin Karfin hali ta yi ta ce, “Maami ba mutuwa dai na yi ba da
saura na tukun.”
“Wane irin abu ne haka za ki dagawa mutane hankali, iye Ummu?”
“Maami!” Tana fadar hakan, kawai ta fada jikin mahaifiyarta ta sa wani kuka mai
tada hankali. “Ke Ummu, meye hakan? Dubeni nan.” Justice Khadija ta dago ‘yarta
daga jikinta tana kallon yadda gaba daya ta hautsine, fuskar nan ta yi jazur! Don
kuka, idanun ma haka duk sun yi luhu-luhu!
Hannunta na rawa ta mika wayarta wa Maami, inda saKon Zaid yake rubuce a kan
fuskar wayar. Ba ta fice daga wurin ba. Ta san ba ta kyauta ba, da ta nuna wa
mahaifiyarta abinda ba uwar da take so ta gani a rayuwar ‘yarta mace. Www.bankinhausanovels.com.ng
Bare Maami da take fuskantar hakan a karo na biyu, ta san ba mutumin da ya kai ta
son kai a wannan lokacin, amma ba yadda ta iya, dole ta nuna mata, domin labbanta
ba za su iya furtawa ba. Da sauri Maami ta saketa kamar ta riKe wuta. “Burinki ya cika yanzu kam, kin samu abinda ki ke so ko? Sai ki zuba ruwa a Kasa ki sha, tunda kin samu rayuwar da ki ke so.
Da sauri Umm Adiyya ta koma kusa da Maamin ta riKota, “Maami da gaske ba laifina bane.”
“Laifin waye to? Ko kin dauka duk abinda ki ke yi tun farkon auren naku, ba mu sani
bane? Yanzu ba ga shi ba kin Kure shi. Allah kadai ya san me ki ka aikata masa, har
ya rubuta miki takardar saki. Ya yi miki kyau ai hakan. So ki ke yi mu koma mu jera, mu yi ta zama a gidan ko? Ba damuwa bace wannan, zan fadawa Abbanki abin da ake ciki, amma ina so ki
sani, ba inda za ki a nan gidan za ki zauna, ki yi zaman iddarki, yadda addini ya
tsara. Idan kin ga dama, sai ki kashe shi, don Kiyayya.”
Bude idanu ta yi tana kallon Maami, ta san iyayenta da tsauri kan wasu abubuwan.
Amma ba ta taba tunanin za su sa ta ci-gaba da zama ba, don haka ta saka wani
sabon kukan. “Maami ki yi haKuri.”
“Ai ba ni ki ka yi wa laifi ba wannan tsakaninki da Ubangijinki ne. Ni meye nawa?
Kanki ki ka yiwa. Ki ka Hata ma duk ruwanki.”
Har yanzu dai gunjin kukan ta sake sakawa hace da dunKulewa wuri guda. Ba ta da
bakin cewa komai akan Zaid, kamar yadda ba za ta iya Kirgo laifuffukansa ba, haka Www.bankinhausanovels.com.ng
nan ba za ta iya bada nata uzurin ba.
Ita ta san hikimar zaman idda, kuma ta san muddin ta zauna din, hikimar zai iya
tasiri a kanta, domin soyayyar da take yi wa Zaid da tausayinsa da take ji, za su iya
karya mata zuciya ta kaucewa Kudurin Kwakwalwarta. To amma yaya za ta fadawa su Maami wannan duka su fahimta? Tana ji Maami ta kira Abba a waya ta ce, idan ya samu sarari ya Karaso gidan Zaid. Tunda Abba ko ya ji haka, ya san akwai matsala kenan, don haka nan dai kawai
dukkansu ba mai Claukar Kafa ya je, idan ba da dalili ba.

******

Falon dai ya yi tsit! Tun bayan da Maami ta nunawa Abba sakon Zaid, kuma tun
bayan da ya gani, yake ta neman wayar Zaid din, amma baya samunsa.
“Sai ki zauna a nan din idan muka yi magana ko ma menene ake ciki, sai a sake
zama, ban yarda kuma da wata fita ta ba gaira ba dalili ba, ki na ji ko?” Kai ta gyada
masa cikin sanyin jiki, saboda ko ba komai. Abba bai hau ta da facia kamar yadda ta
yi tunani ba, wannan ya sa ta tunanin wata Kila shi ya fahimci halin da take ciki ne.
Ai kuwa suna fita a gidan ya ce da Maami, “Ni ina ga akwai wata babbar matsala ce,
domin kuwa Mamana akwaita da zurfin ciki. Sannan ba ta da son kai duk yadda ki ka
ga haka. Zaid ma na da ta sa matsalar.” Justice Khadija ta ce, “Wallahi Abba ka na ba ni mamaki, haka kawai sai ka zage ka
bi bayan ‘yarka, bayan ba ka ji daga bakin mijin nata ba? Sannan mutum mai Www.bankinhausanovels.com.ng
gaskiya, ai baya taba tsoron fadiin gaskiyarsa a duk inda yake bare game da batu irin
na aure, da zai iya ginawa ko rusa rayuwar mutum.”
“Haka ki ka gani, sai dai idan sanin gaskiyar zai iya yin barnar da rashin sanin bai yi
ba. Saboda haka na ke so, ki kira ko Zubaida a waya ne, ta yi magana da ita, mu ji
meye matsalar, tunda kin ga duk gyarar da muke ganin mun yi a baya, bai yi tasiri
ba. Ko kafin nan, shi Zaid din za a same shi a waya. Zan nemi Yaya na fadia masa
abinda yake faruwa, tunda dai abin har ya kai haka.”
Hakan ko aka yi. Maami a take ta kira Zubaida take shaida mata matsalar da ke
faruwa.
Hankalin Adda Zubaida ya tashi haiKan game da labarin da ta riska, nan take ta ji
tana zubar kwallah, ba Karamin tashin hankali bane jin labarin mutuwar aure, ko
yaya kuwa, bare na Umm Adiyya da Zaid da suke ganin kamar sun daidaita
tsakaninsu. Har ma suke masu kallon sun tsallake siraciin dacen abokin rayuwa.

*******

Tun fitar su Maami da Kyar Umm Adiyya ta samu ta ja jiki ta yi wanka, ta sa wata
doguwar riga, sannan ta ci abincin da tun safe Innayo take ta lallashinta da ta ci. Ba
ta dai san me yake faruwa ba, amma tunda ta ga Alhaji Zubairu ya zo, ta san da
wani abin kuma. Koma dai menene, fatan ta daya. Allah sa a warware lafiya.
Karatun Al-Kur’ani ta dukufa yi ko zuciyarta za ta yi sanyi. Ji take yi kamar an mata
sata a jikinta, domin wayam! Take jin kanta. Wayar Adda Zubaida ce ta katse mata
karatun nata. Sakin ranta ta yi kadfan, sannan ta amsa wayar.
“Adda Zubaida ina wuni? Yaya su Safiyya?”
“Lafiya Kalau, Ummu A. Me na ke jin yake faruwa wurin Maami? Wai da gaske ne
Yaya Zaid…” Www.bankinhausanovels.com.ng
“Ya sake ni? Eh da gaske ne, amma kar ku ga laifinsa a wannan karo, don ni na
nemi rabuwar. Adda Zubaida kin san komai, na yi iya KoKarina, amma ba na
tsammanin zamanmu tare yana cikin Kaddararmu duk da kuwa son da na ke masa
da wanda yake ikirarin yake min. Akwai abubuwa da dama a cikin rayuwar aure
sama da soyayya. Ina ga rabuwarmu, shi ya fi
alkhairi, domin zaman mu tare akwai cutarwa.”
Tana kai aya. Adda Zubaida ta ce, “A’a ni ban yarda da wannan batun naki ba, ai
komai da ki ka gani na rayuwar nan fa sai da hakuri, da kauda kai, ba ki san zurfin
haKurin da za ki yi a aure ba, har sai wannan jarrabawar ta kama ki.”
“Uhm-Uhm! Banda idan zai shafi addininku, ko kuwa rayuwa da mutuwa.”
Tana fadin hakan ta yi da-na sanin faci, domin babu wanda ya san wannan
Bangaren na fadanta da Zaid.
“Ummu A. Akwai abinda ki ke boye mana ko? Wai ni yarinyar nan kin dauki kanki
bankin matsaloli ne, ko meye da za ki yi ta shanye komai ke kadai? Meye amfanin
‘’yan-uwa, meye amfanin shawarwarin da muke ba ki, idan ba za ki yi aiki da su ba?”
“Yanzu kam ai komai ya wuce kuma, komai ya Kare. Na gode da shawarwarinku
kuma ko ba komai, dole na godewa Allah da ya ba ni ‘yan-uwa kamar ku.”
“Yanzu dai mu bar maganar nan haka, gobe muna hanya da Baban Walid Inshaa
Allah, daman zai taho, za mu shirya mu biyo shi, sai mu zauna mu yi magana sosai.
Maganar nan ba ta waya bace.”
“Adda Zubaida. Allah ba sai kin zo _ ba, makarantar su Walid kuma fa? Akwai Www.bankinhausanovels.com.ng
Islamiyya ai.”
“Don dai na rana daya kam sa hakura da karatun ai.”
Adda Zubaidan ba ta jira komai daga Umm Adiyya ba ta kashe wayarta cikin
tsantsar damuwa. Kalaman Adiyya ne suka kulle mata kai, me take nufi da matsalar
da za ta shafi addinin mutum, ko kuma rayuwa da mutuwa?
Zaid ta sake nema, amma har yanzu duka layukansa biyu a kashe suke, don haka
ne ta nemi SaadikK suka yi magana, shi ma dai ya ce bai ji daga Zaid clin ba tun jiya
da rana.
Ita ta san fargaba da tashin hankalin da yake
cikin mutuwar aure, bare irin na Umm
Adiyya da ba Dboyayyan abu bane, kowa ya san irin son da suke yiwa juna, daga ita
har Yaya Zaid din, ta san dole rabuwar nan ya kassarasu ko ita Ummu A. Din ko
kuwa Yaya Zaid cin kansa.
Har yanzu ba za ta manta abinda ta fuskanta ba a aurenta na farko da Isa. Wannan
ya sa ba ta fatan ko wace ‘ya mace ta sake fuskantar irin wannan. Ya zamo lallai ta
zauna da Umm Adiiyya su yi magana na sosai.

*********

Ba abinda ya damu su Abba da Maami da ma ilahirin zuri’ar Muhammad Nafada da
suke da labarin abinda ya faru, illa rashin ji daga Zaid, an tada Faruk da Fa’iz sun je har ofis, amma an tabbatar masu cewa bai je ba tun jiya. Wayoyinsa ma duka a Www.bankinhausanovels.com.ng
kashe ba sa shiga.
Koda aka samu Femi, ana cigiyar Zaid abin ya daure masa kai, don shi dai
maganarsu ta Karshe ce masa ya yi tafiyar gaggawa ta kama shi, amma bai fadii ina
bane zai je. Don haka ba su samu wani Karin haske daga Femi ba.
Yaaya Saadik ne ya nemi Salisu a waya don ya ji.
“Lallai mun yi magana da shi akan zai yi tafiya, amma bai facia min inda zai je ba so,
na zaci ma game da aikin da suka fara ne na kwanaki a Ohio.”
“Subhanallah,” Nan ne fa Yaya Saadik ya fada masa abinda ake ciki.
“Ya Salaam! Malam ne ya aikata wannan aikin? Amma shi ko me zai shiga kansa
har hakan ya faru?”
“Kai dai ka bar sha’anin, yanzu su Abba duk sun sani a tsakiya, wai dole na san inda
yake. Na san sun damu ne saboda abinda ya faru, amma bai kyautu ace ya tafi haka
siddan, ya bar baya da Kura ba,”
“Gaskiya hakan bai yi ba sam. Musamman da ya san ga abinda ke hannu. Akwai ma
sha’anin mutuwa ai, wani abu idan ya faru ba a san inda yake ba fa?”

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *