UMM ADIYYAH CHAPTER 50 BY AZIZA IDRIS GOMBE
Www.bankinhausanovels.com.ng
Mun tsaya
Kin ga Ummu, na san yanzu abin nan yana cikin zafi, duk lokacin da aka ce
zukatan mutane sun sare da al’amuranku, zai iya yiwuwa ayi gyara, amma fa kar ki
manta har abada wannan abin ba zai taba goguwa a idanun kowa ba. Ina wayonki
Ummu? Ina iliminki, da har sai kun bari duniya ta ji me ku ke ciki, kafin ku iya
magance matsalarku? Ina ce duk yana cikin wayewar, ku zauna ku fuskanci juna,
zama na mutanen da suka mallaki hankulansu, ku magance matsalolinku?”
“Ku yi haKuri Aunty, Wallahi da-na sani da ban ce ya sakeni ba, raina ne yake
Konuwa a lokacin. Ban yi tunanin abinda zai faru ba cikin dangi, ban yi tunanin
komai ba. Ban taba jin fushi bane da tashin hankali irin na lokacin…” Www.bankinhausanovels.com.ng
“To kin ga shi ma kuma sai aka yi rashin sa’a lokacin ya samu tashin hankalin har ya
biye miki, ya yi miki yadda ki ke so. Ummu girman miji ya wuce duk yadda ki ke
tsammani, sai ya kai ki wuta, ya kuma kai ki aljanna. Idan wuya ki ke sha a duniya, ki
na kuma Kuntata masa, sai ki sha wuya biyu duniya da lahira, amma idan har ki ka
kyautata masa iyakar iyawarki, ki ka koma ga Allah. To tabbas ki na da rabo. Kin
sani kam?” Kai ta gyadlawa Anti.
“Yanzu tunda kin huce, za ki koma gidanki ko?”
Umm Adiyya kam shiru ta yi, “Ina sauraronki, za ki iya fada min komai ba wanda zai
ji, ba zan fadlawa kowa ba, mu biyu ne a clakin nan. Kuma zan ba ki dukkan goyon
baya, idan har na fuskanci ke ce da gaskiya.” “Anti, shi ne ai ya…”
“Baya kula ki ne?” Nan da nan Umm Adiyya ta shiga girgiza kanta, a’a idan ta faci
hakan ma ta san sharri tayi masa, tunda ita ta ce ya nisance ta, ba za ta kuma yi
Karya ta ce ya yi hauka ba, duk da kusan haukar ce wancan karon.
“Dukanki ya yi?” Anti ta tambaya ta san dai su ne cin zarafin da namiji zai yiwa
matarsa ya Konata har hakan.
“Anti fin Karfi yai min.” Ta furta hade da sakin wani gunjin kuka mai tada hankali. Anti
ko nan da nan jikinta ya yi sanyi murus! Tana salati tana sa lallami. “Zaid din?”
Umm Adiiyya tana kuka tana gyada mata kai.
“Wayyo Allah, Ki yi hakuri, ki yi hakuri,
sam abinda ya yi bai kamace shi ba, bai dace ba ya kuma yi miki cin mutumci na Www.bankinhausanovels.com.ng
Karshe, amma dai duk da haka, sai na ke ganin da wani abin ko? Ba wai ina cewa
abinda ya yi, ya yi daidai bane, koda kuwa menene dalilinsa na yin hakan.”
“Anti don Allah kar ki fada masu, kar ki fadawa kowa.”
Nan da nan zuciyar Anti ta motse, ta ji wani tausayin Umm Adiyya ya kamata, “Ya
Salaam, ki na sonsa har haka me ya sa ki ka bari har ku ka kai haka, ke da ki ke da
hanyoyin rike kayanki? Yanzu kam tunda batu ya zo har nan, kamar kun tonawa
kowan ne, tunda dai yau ilahirin jama’ar gidan nan da suka taru ga su Umma, ga su
Mama ga Maaminki, kowa ya san daga yadda ku ka yi shiru ku na ta koke-koke,
hankalinsa zai ba shi ga makamancin dalilin. Amma me har zai kawo wannan danyen aikin?”
“Ni na ce ya nisance ni… tunda… tunda ya ce
baya son yara lokacin, kenan baya sona ni ma ai kenan ko?” Anti ta sake tabe hannu ta tabo haar ta cikin mamaki, ta ma gaza rufe baki, da Kyar
ta iya cewa, “Amma haka ku ke tafka yaranta a gidan naku dama? Duk iya lokacin nan ba wanda ya sani? Sai da ku ka gama kwaba-kwabenku? Wa ya ce miki ana hana namiji wannan? Gaskiya na ga wautarki sosai, ba na wasa ba. Ai irin hakan ke tura su su fara neme-neme, daga haka kuma idan ba ki ci sa’a ba,
kin yi wa mijinki bye-bye. Yanzu ki share hawayenki, ki zo mu koma falon Baffan ko?”
Kai kawai ta gyadla mata, ta shiga bancfakin da ke cikin dakin Antin ta wanko
fuskarta. Ta kalli kanta a madubi, saura kacfan ta gaza gane kanta, ba wai muni ta yi
ba, ko ta canza halitta, duk da akwai alamun canza halittat ma a tare da ita.
Abin da ta gani a madubin, ya sa ta gaza gane kanta, wai yau ita ce ta tona kanta a
gaban Anti, ba ta so ta yi hakan ba gaskiya, ba ta so hakan ta faru tsakaninsu ba, ba
ta so ta Ki shi ba, sannan ba ta so komai ya faru ba. Amma komai ya faru, kuma
komai ya Kare. Wai an yiwa mai dami Claya sata.
Zukar numfashi ta yi ta zari (Toilet Paper) ta goge fuskarta. Jin KwanKwasa Kofar
Anti ne, ya sa ta tuna ana jiranta. Dole ta fita waje, duk abinda su Baffa suka yanke a
shirye take ta karbe shi. Domin yanzu kam ba ta da abin fadi. Www.bankinhausanovels.com.ng
Sallar magariba aka shiga yi, wannan ya sa aka tsaya cin abinci. Aka yi Issha’i kafin a koma zama na biyu.
**************
BABI NA TALATIN DA HUDU
Adda Zubaida ce ta ja ta gefe a can Clakin yara, “Ummu A a ganinki hakan ya dace?
Ace don ke kawai an hada (Family Meeting) na gaggawa? Yau waye ba ku tabawa
zuciya ba a gidan nan?”
“Ban san za su hadcfa ba ai.” Ta facfa tana goge idanunta da dunkulen Tissue da ke
hannunta.
“Sannu Sarauniyar sabolotaye. Wallahi ina jiye miki fushin iyaye da kowa da kowa.
Maza idan kin shiga, ki bawa kowa hakuri dama, ki kuma tattara tunaninki, ki san me
yake miki zafi, ai ba ki fada min komai da komai ba, da tuni na dacle da gyara miki
seti.” “Me zan yi to?”
Adda Zubaida ji ta yi kamar ta kamota ta lakadla mata duka, ko za ta huce haushi.
“Dama can ke wawiya ce ko a sama ki ka samu lalurar wautar? Wata Kila fadfan ki
da Yaya Zaid ya dan juya miki Kwakwalwar. Mu je na raka ki, ke ki ka sani, duk
yadda suka yi da ke, tunda kanki bai iya daukar magana ba.”
Kai ta gyadla, ta fara bin bayan ‘yar-uwarta da ta sake komai ta tattaro iyalanta, don
dai ta ga Karshen matsalolinta. Ba za ta taba manta rawar da kowa ya taka baa
nan, muddin ta koma gidanta. Koma ba ta koma ba. Wannan ya tuna mata da Adda
Asma ko me ya faru, tunda aka soma rikicin nan ko wayarta ba ta samu ba, bare ta
jajanta mata. Bayan ita ta fi kowa sanin menene matsalarta. Www.bankinhausanovels.com.ng
Kau da wannan tunanin ta yi daga zuciyarta, sannan ta maida kanta kan abinda ta sa a gaba yanzu.
Tunda ta shigo falon, gabanta ne ya yi mummunar facluwa da idanun Yaya Zaid
suka sauka a cikin nata, inda ta samu suna Clan magana da Yaya Saadik. Wani irin
nauyin idanunsa ta ji sun sauka a kanta. Musamman idan ta tuna yau ta bankade
abinda ta dace tana Doyewa a ranta, ta fadawa Anti komai, ta sa girmansa ya ragu a idanun ‘yan-uwa.
Kunyarsa ce ta kamata, har ta ji ba za ta iya Claga idanu ta dube shi ba, kau da kanta
ta yi gefe tana kallon Hangaren da manyan tuntum din Baffa suke jere a wadataccen falon.
Shigowar Umm Adiyya falon, kafin su Baffa su shigo, idanun Zaid suka facla kanta,
yana neman wata alama daga wurinta, sai dai abin da ya karya masa zuciya, suna
hada idanu ta kau da kanta, wannan ya sa ya san cewa babu amfanin sulhun, tunda da alama ba ta daddara ba. Lokacin kallo ya koma kan Zaid, ana jira ya ce. Ajiyar zuciya ya yi, sannan ya ce, Baffa, maganar da zan yi ba don na rainaku ko don ban dauki abinda ku ka fada mana ba. Na yi shi ne bayan na yi nazari, na kuma duba abubuwa da dama. Na
Dauki komai a matsayin Kaddararmu, yadda ta zo haka za mu karfe ta. Ku yi hakuri
Baffa, amma har yanzu ina kan bakana, muna buKatar lokaci.” “Ba za ka mayar da ita ba kenan?”” Baffa MaiKano ya tambaya cike da mamaki.
“Idan mun samu fahimta a gaba, wata Kila hakan ta yiwu, amma a halin yanzu matsayata kenan.”
Gaban Umm Adiiyya ne ya yanke ya fadi, ta ji wani sauti ya cika mata kunne mai toshe ji. Har ta fara ganin dakin na juya mata.
Shiru falon ya yi na lokaci mai tsawo, kafin Baffa ya ce, “To, wai ana cewa ka haifi
yaro, amma ba ka haifi halinsa ba, yau kam Allah ya gwada min, ni kuma tawa
jarabawar kenan, ganin wannan ranar.
Wai shin a iya karance-karancenka, ba ka taba sanin cewa mafi munin halas a wurin Allah shi ne sakin aure ba?” Kansa na Kasa bai ce komai ba. Wannan ya sa Baffa ya ce, “Da kai na ke magana.”
“Na sani Baffa, amma idan daya daga cikin su yana ganin ana tauye shi, maimakon su ci-gaba da zaman daukar zunubi da tauyewa juna hakki gwamma kowa ya hakura. Wannan ya sa na yanke shawarar da na dauka.” ” To ina so ku sani, dukanku biyu ba ku isa ba. Ai kafin auren naku na ce kar ayi, kuka zo min da labarai shimfidaddu har da sako Zubairu a maganar, ina ce ga abinda ake gudu nan? To kun ji na fada maku wannan abin ya faru ya Kare a kanku, kar
kuma ku yi tunanin zai taba mana zumuncinmu ni da dan-uwana koma wani daga cikin gidan nan. Idan an fita a falon nan, an kulle batun aurenku. Ba mai sake dago zancen, an gama shi ya Kare. Allah hada kowa da rabonsa, ku tashi ku koma inda ku ka fito.”
“A’a Yaya ya dai sake dubawa, amma ai ba za a taru haka ba a fidda maslaha ba.”
“Maslaha? Mai-Kano? A gabanka dai da ni da kai duk kunnuwan kowa na aiki,
yanzu ya gama jawabinsa, idan har da sauran abinda ya rage na tozarci da ya rage
mu gan shi kuma, to muna sauraro.”
Ajiyar zuciya Baffa Mai-Kanon ya sake yi, “Yaya, Kyalesu haka nan, ina tsammanin
kowa ya samu abinda yake so cikin al’amarin, ai dukkansu sun mallaki hankulan Www.bankinhausanovels.com.ng
kansu. Allah ya huci zuKatansu. Idan har da rabo a gaba, sai ka ga da kansu sun
gyara komai. Yanzu kam ko mun ce za mu yi gyara, za a kwata irin na da din ne dai a sake taruwa anan.”
“Don ba mu da aikin yi, sai na su? Ke Ummu, idan kun tafi, ki koma dakinki ki yi
idda, idan zai zauna a Kasar ya zauna, idan Kaura zai yi ya bar miki gidan, ya yi
Kauran, ke dai ki yi yadda addini ya tanadar miki.” “A’a akan me ya sa bayan baya sonta? Mu
muna sonta, duk gidan da take so ta
zaba can za ta zauna.” Hajja Ku ta kwararo bayani, suna son su mata bayanin
yadda addini ya ce ayi. Amma ranta ya gama dagulewa, an taba mata tokenta (mai
sunanta). Ba wanda ya isa ya ce mata wani abu, yanzun za ta hada da shi.
Abba kam tunda ya buga tagumi ko numfashi Kwakkwara bai sauke ba, ya zubawa
sarautar Allah kallo. Kasancewar ba ayi zaman farkon da shi ba, sai wannan zaman,
amma ya fahimci cewa batun ya yi musu ma da Yayan nasa bai taso ba.
Jikin kowa a mace aka tashi, aka bar falon. Lokacin ne Anti ta shiga sashen Baffan
don ta jarraba nata gyarar. Amma haka nan dai ta fito. Baffa ya ce ya rufe maganar.
Umm Adiyya dai idan ana da ma’adana na hawaye, ranar nata ya ci ya Kare. Don
Kafewa suka yi daga baya, sai ajiyar zuciya kawai take yi da shessheKa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Tunda Zaid ya fita daga falon Baffa, ya yi hanyar Kofar gida. Tsayawa ya yi a cikin
zauren gidan, wanda Kwan wutan ya mutu, wani numfashi ya zuKa, kansa ya sara.
Yayin da ya maida numfashin, yau ya amince da duk abinda ya faru kawai Kaddara
ce mai Karfi. Tsakaninsa da Umm Adiiyya komai ya Kare kenan? Wasu hawaye masu Zafi ne ya ji sun zubo masa. Wayarsa ce ya ji tana Kara, yana kallon sunan “Mama’ akai ya ji wani diri ya ratsa
shi, ai tuni ya manta da ciwon kansa, hannu ya sa ya share fuskarsa. Da sauri ya
kanga wayar a kunnensa, ya amsa cike da ladabi.
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG