UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 4 BY SHATU

UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 4 BY SHATU

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

Na dawo na zauna a parlon na rasa me yake min dadi a zuciyata, na saka kaina cikin cinyoyina na fara kuka a hankali, saboda komai nawa a nutse yake. Ina cikin kukan naji muryar Baba Yana sallama, nayi saurin mikewa na goge fuskata sannan na amsa masa Amma muryata Bata fita ta rigada ta dashe. Daya shigo seda ya kalleni for like 30secs kafin ya dauke kan shi yace

” Har yanzun Kuna zaune Baku shirya ba?”

Na sunkuyar da kaina jin hawaye Yana ziraro min ta gefen idanuna, nayi saurin saka hannuna na goge Amma na kasa Masa magana, haushin shi nake ji kamar na rufe shi da duka Allah ya yafe min,

” Ni zamu wuce da Rumasa’u da Ayaan, kawun ku zai zo ku tafi”

Na gyada Kai Ina sake goge idanuna Bai jira komai ba ya fice daga gidan, na bi bayan shi da kallo se Naga he seems strange kamar ba Baba Dana sani ba. Na Kara sakin kuka Anisah na kuka jikina, nafi awa zaune kafin na Mike na fara harhada kayan namu, na Gama da dakin shi na hadawa Anisah ruwan wanka sannan na sata tayi wanka, na shiga na samu Rayha na kwance se gunjin kuka take, se ta Kara karyar min da zuciyata, na zauna gefenta Ina kuka Nima, nace

” Haka zamu zauna bamu da uwa?”

Na tambaye ta Ina hawaye, ta mike tace

” Ina son nayi Masa uzuri na kasa na tsane shi bana son shi”

Nayi saurin rufe Mata baki na girgiza Mata Kai nace

” Ki daina fada! Baba baba ne komai zaiyi ba zai canja sunan shi ba”

Na Mike na harhada kayan mukai wanka, kamar jira yake kawu yazo, cikin gida mukaje Dan Yi musu sallama. duka fuskar mu tayi jawur, ni idanuna har sun tashi, kawu na ganin mu ya fara tambayar me ya same mu Amma ba Wanda ya bashi amsa, illa ni Dana Kara sakin kuka se ya kyalemu yace muje muyi sallama da Gwoggo mu fito. Muna shiga parlon muka tarar da Ummaah da Gwoggo suna hira, Dan Bata tafi ba se wani satin, tunda muka shigo Ummaah ke kallon mu har muka zauna, Ummaah tace

” me ya samu fuskokin ku ne?”

Na girgiza Mata Kai Amma bakina ya kasa budewa nayi magana, saboda ji nake kamar zuciyata fitowa zatayi ko kuma I’m gonna break down again! Rayha tace

” Gwoggo zamu tafi, sallama muka zo”

Gwoggo tayi shiru duk damuwa fuskarta, hannuna ta riko tace

” Takwara menene? Me ya same ku? Ina Hajaran?”

Se na saka hannun Gwoggon kan fuskata Ina kuka, Rayha nayi Anisah na Taya mu. Ummaah ta tashi ta zauna tareda fadin

” Wai meye ya samu Hajaran ne?’

Ta fada ta kwalawa kunyangar ta Kira akan ta kawo Mata wayatta ta Kira Baba, da sauri Rayha tace

” Baba ne…”

Se nayi saurin sakin hannun Gwoggo na toshe bakin Rayha, Amma seda ta karasa

” …ya saki Ammi”

Wani salati duka Suka saki, Ummaah tace

” To shi Abdullahin shaye shaye ya fara? Ba shida hankali zai saketa”

Har zuciyar ta take fada se na fahimci Babu saka hannunta a ciki Amma bashi yake nufin na yafe Mata cin mutuncin da ta yiwa uwata ba. Gwoggo se ta fara kuka tace min

” Ina shi Babandin yake yanzun?”

Nace

” Sun tafi shi da Anty Rumasa’u Funtua, kawu Yana jiran mu a waje”

Ummaah tayi ta Kiran Baba Amma yayi blocking duka calls,se ta Kira Ammi itama wayatta a kashe, ta daura hannun ta saman fishing ta tace

” Gwoggo ki Dena kuka, wannan abin ba hakan bane”

Rayha tace

” Allah ya sake ta Sofy ya bawa takardar ta bata, Kuma tun dazun ta tafi ta barmu”

A wañnan ranar bamu koma Funtua ba, duk wani tashin hankali da kuke tunanin zamu Shiga to min shiga, wayar Ammi Bata shiga haka Baba yayi blocking calls din mutane, ni dai kafin gari ya waye fuskata ta kumbura. Da asuba bayan mun Yi sallah na takure akan sallaya kaina Yana masifar min ciwo nace

” Gwoggo kisa a maida mu gida kada Baba yaji haushi bamu dawo ba”

Ta gyada min Kai sannan tace

” Kuyi hakuri inshallah Hajara zata dawo dakin ta, alkawari nayi muku”

Na gyada Kai kawai,wajen Tara na safe aka raka mu har mota, duk mun jeme muka tafi, magana ta Shiga dangi cewar Baba ya saki Ammi. Mutane se jajanta wa suke, wasu na murna Amma abin mamaki Ummaah bayan Gwoggo tafi kowa nuna tashin hankalin ta akan maganar, tunda muka Shiga mota na karba wayar kawu nayi dialing number Ammi Amma maganar daya ce wayar a kashe take, na mayar Masa da wayar deep in thought, ya Ammi take yanzun ko me takeyi? Se naji aure, maza, soyayya komai na tsane shi. Seda muka je Kano sannan bacci ya daukeni aikuwa har mukaje Dayi bacci nake, se da muka Kai malumfashi sannan na farka. Babu jimawa muka Isa gida, ta gate dinmu ya sauke mu, da key hannuna na bude muka shiga da kayan, se naji duk girma ya kamani, na gyara gidan ba tareda sun Taya ni ba, saboda tausayin suke bani, na hada kayan wanki da na guga sannan Rayha ta daura Mana abinci. Part din Anty Rumasa’u na nufa, tun daga part dinmu nake jin hayaniya da dariyar ta, na daure na Shiga da sallama, kawayen ta ne dun hadu su wajen biyar, trays da bowls da flask a baje, ga lemuka da ruwan roba Wanda na manta rabon da Baba ya siyo lemo ya kawo bangaren mu, idan muna son Sha sede Ammi ta bada kudi a siyo Mana, ruwa ma na famfo muke Sha Babu abinda ya dame shi, se na Kara fahimtar rashin adalcin namiji precisely rashin adalcin da Baba keyi, Ammi tayi hakuri Kuma Bai tsinana Mata komai ba

” Ya akai?”

Naji maganar ta ta daki kunnena, na girgiza Kai Dan dawowa hayyacina nace

” Baba nake nema”

” Baki ga mutane ba,baki iya gaisuwa ba”

Ban Bata amsa ba ban Kuma gaishe su ba na juya na tafi, Ina jin suna zugata ta bini ta dakeni, ta sani dukana shi ne mistake na karshe da zatayi ta bar gidan mu. Baba Bai dawo ba se dare, ya shigo bangaren mu ganin bulbs din mu a kunne, Muna zaune munyi shiru ko tv bamu kunna ba, Nima bana karatu bamu Hira, se ya karaso da sauri ya dauki Anisah tareda dariya yace

” Aniso!”

Na gaishe shi, Rayha ta gaida shi itama sannan ta shige daki, Anisah ta sakko daga jikin shi tazo ta lafe a jikina, yace

” Ashe Kun dawo? Kunci abinci?”

Se na fara kuka na sakko kasa nace

” Baba Dan Allah Dan girman Allah kayi hakuri ka dawo da Ammi, Dan Allah ka yafe Mata idan ta maka lai…”

Na kasa karasawa saboda kukan daya kubce min, daga ni yayi yace

” Don’t think too much, muje ki koma bangaren Rumasa’u, baza kuji dadin kwana ku kadai ba”

Na juya na canja Kaya, Anisah ta canja Amma Rayha tace Allah ya kashe ta idan taje wani gurin, da mamaki nace

” Rayha Baba ne yace fa”

Tace

” Ko waye bazan je ba. Shi idan Yana da kunya ya kallemu?”

Na daka Mata tsawa nace

” Are you stupid Rayha, Baba ne fa”

Naja hannun Anisah muka fita, can muka nufa tana zaune ta Sha kwalliyya da yarta nata rarrafe, fuskar ta Banda annuri Babu abinda ke fita, da sallama na shiga tana ganin mu ta Bata Rai tareda kallon Baba tace

” Su Kuma fa?”

Se Naga ya duburburce yace

” Dama…zasu kwana anan ne”

Saboda mamaki idanuna kamar zasu fado kasa, ta buga wani uban ihu tace

” Kwana?! Ban saka ka saki Babar su Dan na rike su ba, wallahi bazasu kwana anan..”

Tun kafin ta gama magana na juya, idanuna sunyi taf da hawaye nace kenan ita tasa Baba ya saki Ammi. Inshallah se tayi Dana sani!Haka muka dawo ni da Anisah muka shiga ciki muka kwanta, Bayan duk sunyi bacci na kasa bacci se tunanin Ammin nake, she’s so much extra careful akan kada mu kwana mu kadai, dalilin da yasa Bata fiya yin bulaguro ita daya ba se damu, duk Dan kada mu kwana mu kadai, Amma kalla mu kadai din muke kwana. Nanma se na dasa sabon kuka kafin bacci me nauyi ya daukeni. Bayan munyi sallar asuba na dakko littafai na fara boko saboda I’m far left, gashi mun kusa komawa makaranta baifi kwanaki ya rage ba.+

A Dan ladin gumel, Ammi ta Isa gida da tsakar Rana, kallonta kadai idan kayi kasan Bata cikin nutsuwar ta Koda da abinda ke jikinta ya Isa ya baka amsa. Babu tsammanni se sallamar ta Baba ta ji, gidan duk ya tashi Inna ta rasu, ta ukun ma ta rasu, dama sune Yan mulki su Suka Hana zaman lafiya gidan Kuma duk Basu nan, yaran gidan duk sun dare yawancin sunyi sure wasu kuma sun tafi wajen nema ko makaranta, Yan gidan su Ammi su ashirin da biyar ne, ita kadai ce Bata da mahadi, ita daya Baba ta haifeta. Da anyi zaman kishi, zaman tsangwamar juna, iñna tayi mulki ta juya gidan dashi kan shi Alhaji, to Amma meye makomar ta? Cuta tayi kamar ta haukace, tana daki sede ku ganta tsakar gida, idan Baku rike ta ba se ta fice. Yayan da tayi fada akan su suka kasa tsinanan Mata abin kirki, which is obvious, hakan Yara suke ki saida komai naki saboda su, ki zalunci wasu saboda su Amma karshe ba abinda zasui Miki, Dan kullum yayanta cewa suke ta cuce su! To me yayi zafi?. Ya kamata mun hankalta mu gane Allah yace namiji yayi aure Kuma a gidan aure shi ne shugaba, there’s no point ko reason da mace zatai seizing wannan damar ba, idan kikai haka kin bijirewa umarnin shi, kinyi fito na fito da ayoyin shi. Har kullum Mata ba zamu daina Shan wahala ba saboda mune matsalar kan mu, Abu me wuya, ni ban taba ji ba ace uban mijin ta ya takura Mata, sede uwar miji, ita kanta mace ce Kuma kilan ita ta uwar mijinta treated her right Amma ke tace baza ki Sha ruwa me dadi ba, Ina ce Mata min ce ciwon ‘ ya mace na ‘ ya mace ne? Ko mun hakura munyi giving up, idan dangin miji kike fama da matsalar su zakiga yawancin su Mata ne, su sun manta Suma wani dangin suke aure. Idan kishiya ce Kuma haka zata dinga muzgunawa Yar uwarta mace, da ace zamuyi teaming akan namiji Allah Bai Isa yayi wani abin ba, the more we divide haka zamu ta Shan wuya. Ya kamata mu farka mu fahimci how far muke destroying kan mu. Mu Mata ne ya kamata muyi sticking for our women bawai mu uzzura musu ba. Yawancin Wanda suke kangararru gidan miji ki duba zakiga they were traumatized, either kishiyar uwarta ko kuma dangin ubanta sun muzguna ma Babarta shiyasa take ganin ki dai ta Rama, ko kuma fear din Kar ta Kare kamar uwarta se itama ta kauce Hanya. Kije kiga matar da kishiya ta uzzura Mata, ko kuma miji ya zalunce ta, duk ranar da ta bar gidan tayi wani auren se ta nemi Hana zaman lafiya a sabon aurenta, saboda tana ganin ba zaa maimaita ba.

A cikin zuciyata babban tanadi na yiwa kishiya, inada cikinta bazan taba Bari bakin cikin da Ammi ta dandana Nima na dandane shi ba, tun a wañnan lokacin nayi deciding, banida fitina Amma Baba ya dasa min iya cikin zuciyata! shiyasa zamana da Kubra ya Zama tashin hankali! Baba taji gaban ta ya Fadi ganin Ammi da tsakar Rana, tana shiga ta zauna tareda cire hijabin jikin ta tace1

” Baba Ina wuni?”

Baba ta amsa jikin ta a sanyaye, mussaman jin muryar Ammi da tayi Babu kuzari, ga damuwa a tattare da ita, Kuma tasan irin zaman da Ammi keyi da Baba. Ruwa ta kawo Mata tace

“Ki Sha! Zakiyi wanka?”

Ta gyada kanta sannan ta hada Mata ruwa, gidan an gyara shi sosae saboda an samu masu rufin asiri cikin zuriar tasu, dukda Ammi ma ba karamin kokari tayi ba. Ta zage tayi wanka Allah ya taimaka tana da Kaya baifi guda uku ba data taba kawowa ta aje, se kawai ta saka ta samu tsakar dakin ta kwanta, gidan shiru se ta fara tuna yadda gidan su yake, lokacin kowa ba wani santa yake ba, ba dama tayi motsin kirki, dadin ta daya mahaifiyar ta da mahaifin ta, su Suka taimaka wajen zamewar ta uwa ta faru gare mu, gashi yanzun ta dawo matsayin bazawara Kuma, ita ce aurenta da Baba ya mutu, ita ce Baba ya saka sakin wulakanci, yarta ya bawa takardar sakin ta, tayi tunanin duniya ta kasa figuring laifin da ta yiwa Baba, tasan lafiya kalau Suka kwana, Dan wannan Daren he kept telling ya Yi kewar lokacin yarintar ta dukda ba wani canja Masa tayi ba, tana nan a hajarar da ya sani, they were so intimate a Daren, tamkar zai maida ta cikin shi, da zai tafi sallah lafiya Suka rabu, to me ya faru…Ta kasa daina tunanin possibility sakin, Bata son zargin kowa Amma ta sani ba zata taba yafewa Wanda ya dagata daga kan yayanta ba, se kuka, ta fara kuka data tuna mu, ta tuna how fragile we were, rayuwar mu uwar mu kawai muka sani, komai ita ke Mana, duk abinda muke so gurin ta zamuje, yau ta tashi Bata tare damu. Cikin kukan taji sallamar Alhaji da Baba da kuma Kawu Saleh babban yayan su, Yana son Ammi ko da can, ya damu da lamuran ta saboda Yana ganin gaba daya rayuwar ta abin tausayin ce. Ganin kukan da take yasa duka Suka tsinke da lamarin, Babu tantama auren ya mutu, ko da suka zauna haka ta fada musu. Alhaji yace kada taji komai, aure dama Rai ne dashi ta kwantar da hankalin ta Allah yayi zaman su ya Kare, mu kuma Allah zai kiyaye mu, Kawu Saleh ma haka ya Mata nasiha se taji sanyi tunda ta samu support dinsu, ita tashin hankalin ta mu ne, a wanne Hali muke ciki? Ta tuna yadda muka rirrike ta da zata tafi Muna kuka tareda rokon ta kada ta tafi.

STORY CONTINUES BELOW

A Gumel Gwoggo ta Kira Baba Ahmad, shi ne babban yayan Baba a Abuja yake aiki Shima sunzo da family shi,dake basuda hayaniya baka ma jin labarin su, sede yaran shi na son mu, Dan yanayin mu irin nasu ne, mutane ma na fadar kamar mu, tunda babansu na Kama da Baba. Ta zauna ta zayyana Masa komai tace tana son suje su dawo da Hajara, yayi ta fada ya Kira Baba Amma wayar shi Bata shiga ba, se dare sannan Baba ya saci jiki yaje asibiti anan ya kunna wayar, messages ne kalakala Wanda duk na korafin abinda ya faru ne se masu tambayar shi ko lafiya wayar shi a kashe. Yayi expecting message din Ammi Amma ko daya Babu, se ya fara kiranta Wanda Bai San me yasa yake Kiran nata ba, Amma wayar a kashe, Bai Kai ga Kara Kiran ba wayar Baba Ahmad ta shigo, Yana dauka ya rufe shi da fada yace

” Ko me tayi maka Bata cancanci saki ba, ya yaranta zasuji, ka Basu takadda su bawa mahaifiyar su haba Babandi! Se kazo Gumel Gwoggo na nan Bata cin abinci saboda abinda kayi”

Wannan shi ne babban tashin hankalin sa Gwoggo, shiaysa Dan kada su hadu ya gudu. Hankali tashe ya dawo gida, dama tunda ta mishi tsawa gaban mu bay Kara ganin mu ba, sede yasa Bature yazo ya duba mu, Rai da mantawa har mun fara hakura mun saki jikin mu, mun rungumi sabuwar rayuwar da tazo Mana ammma dukda haka zance daya biyu to na uku na Ammi ne, zamu ce da Ammi na nan da anyi kaza, we were badly missing her. Duk abinda ake bamu sani ba. A washegari zamu koma makaranta, Baba da sassafe ya salleme mu akan Bature zai zo muta fi,,shi baya gajiya Bature, he’s too kind. Ya dauka Anisah suka tafi Gumel yamma nayi muka kulle ko Ina muka boye key inda Ammi ce kadai zata gani muka tafi. Muka koma bakin fama bakin aiki. A wañnan term din Kuma Usman zai Gama service dinshi sanann a term din ya fara fada min Yana Sona.

” I can’t gaskiya “

Na fada Masa dukda nauyin rejecting din shi da nayi, na farko ni nasan Baba ba zai min aure yanzun ba, nasan karatu zanyi, so Babu dalilin da zaisa na Bata lokaci na akan shi yanzun, na biyu Yana da aure ni Kuma Ina son na Zama UWARGIDA a gurin wanda zan aura Dan nayi turning tables around, na uku a halin da nake ciki na bansan makomar Ammi ba banida Lokacin wani tunani balle har nayi weighing gem din da nake kokarin losing, Amma Bature yace ” what’s meant for you will definitely find it way back”

” Na zata zakiyi tunanin maganar tawa, ba Zaki yanke hukunci so soon ba”

Na Dan girgiza Kai na har lokacin kaina a kasa nace

” Kayi hakuri am too young da soyayya inada abubuwan dake jirana Bayan secondary”

Se ya Kara marairaice fuska yace

” Dan Allah Safiyya think about us, bawai gobe Zan aureki ba, Nima I’m too young to take two wives yanzun haka, Amma we get along saboda idan na tafi bansan yaushe zamu Kara haduwa ba”

Na rasauyar da kaina banji tausayin shi ba duk yadda yake looking pitiful nasan Yana aurena zai maida uwargidan shi bola, ta Zama UWARGIDAN BAHAUSHE kenan, ni Kuma ba haka nake ba, nayi alkawarin bazan Zama silar pain din wata ba.

” Dan Allah Baban Afaf Kai hakuri, ni ban hango possibilities din zaman mu tare ba, ka bar maganar”

Yayi mamakin bravery Dina yayi tunanin yadda nake so helpless a zahiri haka zuciyata take itama, baisan Baba da Rumasa’u sun canza Safiyya ba. Karshe haka muka rabu baa cimma matsaya ba, ko a jikina, ban taba soyayya ba so bansan ya take ba Amma yanzun ban shirya ba, sede waye yace min ana shiryawa kafin a fara soyayya, Ashe ma ba soyayyar bace, Nanahn Abba Prof ita zata bada labari, ita Bata ma yadda da soyayya ba karshe ta shigeta ba tareda sanin ta ba, nima Kuma haka ta min. Har sati ya Kare lokacin tafiyar su na matsowa Amma ban bashi fuska ba, ya hado min gift Daren da zai tafi yace duk ranar Dana canja shawara ta Yana Kirana. Washegari ya tafi Ina daga window class na hango shi tsaye da wata Mata sanye da atamfa da yarinya dauke hannunta se dariya suke, se naji idanuna sun ciko da kwalla, me yasa naki shi? Me yasa ban bashi chance kamar yadda ya nema ba. Na girgiza ganin Yana Willa yarinyar a sararin sama Yana cafe ta, which shows happiness da yake ciki, se na tuna muma Baba ya Mana haka Amma yau watan mu biyu ko visiting Babu Wanda yazo Mana se aike da ake kawo Mana.

Ina tsaye very deep in thought har ban San matar ta shiga mota ba, haka shi Kuma ya juyo wajen block din mu da yarinyar sabe a kafadar shi, tunda ya shigo block ake ta kukan tafiyar shi kaji shishiggi da zakewa! Class dinmu ya nufo lokacin na dawo daga tunanin da nake na samu baya nan, I thought ko ya shiga motar Shima se na koma seat Dina na Ciro understanding chemistry, to meye ma bansani ba a littafin, duka text book Dina nasan content din su tsabar karatu, ko yanzun a kawo waec a gani nasan da A1 Zan fita. Jin kamshin turaren shi yasa na dago se Naga ya aje min yarinyar kan text book Dina, kamar su daya dashi, idanun shi da Suka fi komai kyau fuskar shi shi ne a Bata, yarinyar ta kalleni ta kalleshi se ta wage baki ta fara dariya, na dauke ta na Mike Ina murmushi nace

” Afaf ce?”

Ya gyada Kai dukda leken mu da ake, da ihun Yan class dinmu na sun tabbatar da zargin su nikam ko a jikina. Na shafa kanta nace

” Allah ya kiyaye Hanya ya kawo babban rabo”

Ya gyada kanshi ya karba Afaf Yana kallona cikin idanu Wanda take suka saukar min da kasala Allah ka yafe min, yace

” You still not gonna reconsider? Babu damuwa take your time Usman na Safiyya ne!”

Ina kallo haka ya juya  ya fita, na koma seat Dina nayi zaman Yan bori, zuciyata kept saying Sofy tafiya yayi fa, Sofy ya tafi ba zaki bishi ba? Se naji haushin zuciyar tawa nake, tamkar na Ciro ta na wurgar haka nake ji. Rayha da Na’ila Suka shigo class din mu suka zauna gefe na, Rayha tace+

” Are you ok?”

Na gyada Mata Kai kawai na cigaba da bude pages din understanding chemistry, se Suka rabu Dani Suka koma classes dinsu. Wajen karfe Sha biyu aka zo kirana, Ina fitowa Naga an Kira Rayhana ma, muka nufi admin block, Rayha tace min

” Yau Baba ya tuna da ‘ya’yan shi kenan?”

Nayi dariya nace

” Da ya manta damu ne?”

Tace

” Alamu sun nuna ai, da da Ammi na nan ya taba sati biyu Bai zo ya ganmu ba”

Na tabe baki Ina Kara jin ciwon rashin Ammi, bamu taba kaiwa wannan dogon lokacin bamu ji daga gareta ba ko Bata zo ba, nayi mamaki sosae dalilin da ya saka dukda Bata gidan mu Amma Bata zo Mana visiting ba. It’s doesn’t matter a Ina take, what matters shi ne mu ‘ya’yan ta ne.  A office din senior master muka same Dr Bature, abin ya bani mamaki. Yana ganin mu ya saki murmushi se naji wani warmness ya mamaye min jikina. Shiga mukai muka gaida senior master sannan ya fita ya bamu guri. Muka gaisa yace Kano zaije shi ne ya biyo ya ganmu. Kinji dadi sosae, ya gama ya bamu kudi har da shopping yayi Mana sannan ya tafi. Muna komawa class nace

” Twin Dr Bature kirkin shi na da yawa! Ko dai Yana son ki ne”

Ta dage Hira tace

” Kinada matsala wallahi, someone can’t be good for no reason”

Nayi murmushi nace

” Allah ya baki hakuri”

Ta cigaba da cona baki har mukaje class, seda muka tashi sannan muka kwaso kayan. Babu jimawa muka fara exams cikin kankanin lokaci muka Gama se hutu daga mun dawo Kuma zamu fara waec da neco. Kamar ko yaushe Bature yazo daukar mu ni a raina har tunani nake wai baya gajiya ne, Tunda muka zauna yace Baba yace Gumel zaa kaimu Nima se na ji dadin hakan saboda Ammi Bata gidan meye amfanin shi. Tunda muka dauka hanya yake min hira Dan Rayha purposely ta tsiri bacci, Naga kamar tunda na tsokane ta akan ko Yana sonta ta fara creating distance tsakanin su. Seda muka Kai har Gumel Yana ta fada min yadda rayuwar shi take, da steps din daya ke son dauka nan gaba. Anan na fahimci bashi da aure Kuma kamar bama ya Shirin yin auren. Mutum ne shi me surutu inda Suka Sha bambam da Usman kenan, tarayyar su Kuma duka suna da kirki, maza ne Wanda suka San kansu. Maimaikon ya kaimu cikin gida kamar yadda muke expecting kawai se Naga ya wuce damu gidan mu, bance komai ba har yayi packing muka fito, kayan mu ya shiga fito Mana dasu, mutanen dake gurin Suka Taya shi ya shigar Mana dasu ciki. A hankali na zura kafata cikin gidan se na fara jiyo ihun Anisah tana fadin

” Ammi da gaske su Yaya Sofy sun dawo!”

Da sauri na karasa ciki na samu Ammi ta fito daga parlor bakinta se murmushi take, da gudu na tafi na rungume ta, Wanda Allah kadai ya tsare bamu Fadi ba, haka Rayha tayi itama, ita harda kuka . Dariya tayi Amma a karkashin wannan dariyar lies a lot of pains.

” Kun bar doctor a waje, kunzo duk Kun gajiyar Dani”

Na sake ta Dan zuwa na Kira shi, seda Ammi tasa yaci abinci sannan ya Mana sallama, ni bana parlon ma,Ina daki Ammi tasa Anisah ta kirani, na fito har na shirya cikin fitted gown da akai pleating Bayan ta, hijab na saka sannan na fita kofar gida inda yake tsaye yana jirana, na tsaya Ina murmushi nace

STORY CONTINUES BELOW

” Tafiya zakai?”

Ya gyada Kai yace

” Ko Zaki bini mu koma?”

Na girgiza Kai nace

” A’a ni! Allah ya kiyaye Hanya se mun dawo”

Har Raina na zata hutu muka zo Gumel Ashe Zama ne na dindindin. Seda ya fita a layin sannan na koma ciki Ina jin a bit kewar shi. Gidan kamar ba namu ba duk yasha renovation, katon tsakar gidan duk Baba ya gine shi, mun tashi da four bedrooms ga kitchen da toilet kowanne daki, duka tsarin gidan ya canja, haka komai sabo ne, har study room akai min, se Naga komai namu na Funtua ya dawo nan. Ban tambayi Ammi ba seda na gama cin abinci sannan nace

” Ammi mun dawo nan gaba daya ne?”

Ta shafa kaina tana murmushi tace

” Mun dawo nan, yafi Dadi”

Se naji dadi dukda zanyi missing Funtua Amma indai Ammi na farin ciki Babu damuwa. Se yamma muka fita zuwa cikin gida, Gwoggo na zaune hannunta da carbi a saman sallayya alamar yanzun ta idar da maghrib. Muma alwala mukai mukayi sallah Dan a Hanya ta Kama mu, sannan mukai shiru Dan Kar mu katse Mata lazimin da takeyi. Seda muka idar da sallar Isha sannan ta fara murmushi tana fadin

” Lale barkan ku da dawowa Yan matan Hajara”

Muka gaishe ta tace

” Na cika alkawari ko?”

Rayha tace

” Kin cika mungode”

Nima na Mata godiya tayi Mana addua sannan ta saka aka zubo Mana abinci, muna ci tana tambayar mu makaranta da karatu. Sallama mukaji daga kofa, duka muka dubi parlon muna kallon me shigowa, sure na sanshi shi ne Yaya Fahad babban Dan Baffa Muhammad yayan Baba, tsakanin su wajen mutum uku. Ya shigo Bayan mun amsa masa sallamar, gefen Rayha ya zauna Yana gaida Gwoggo dake fadin

” Sarkin Makkah! Yaushe a gari”

Ya Dan mikar da kafar shi alamar ya gaji yace

” Wallahi yanzunnan na karaso, ya gida”

Ta amsa Masa sannan ta tambaye shi su Amma maman shi, seda suka gama gaisawa sannan ya dube mu yace

” Wannan Yan matan fa?”

Ya fada hankalin shi ya fara karkata akan Rayha da tayi kasa da kanta, nayi murmushi muka gaishe shi lokaci daya, ya amsa sannan ya dubi Gwoggo Yana Kara maimaita Mata tambayar da yayi Mata, tace

” Zumunci ya baci ikon Allah! Yaran Babandi ne babanka fa”

Ya rike bakin shi yace

” Wai Sofy ce da Rayha. Lallai it’s been long”

Gwoggo tace

” Dama ku ko Gumel din Baku zuwa da kyau gashi ba wani nisa kukai ba, shiyasa ba Wanda zai sanku”

Ya Sosa Kansa yace

” Ki Bari kawai tsohuwa Amma fa ni ki shige min gaba a bani daya, Dan gaskiya Naga Mata!”

Gwoggo bakinta kamar zai yage saboda farin ciki, hantar cikina seda ta kada se na samu kaina da adduar Allah yasa bani ba. Gwoggo ta katse min tunani da fadin

” Wannan Safiyya ita ce babba takwara kenan, se wannan Rayhana sunan Rahane ke gareta ta Dan ladin gumel. Yanzun sun kusa Gama makaranta”

Ba zaka taba sanin kakkani are annoying ba se anzo neman aurenka,matar nan harda Fadi ba a tambaye ka ba, na dubi Rayhana dake takure a gefe se Wasa take da hannunta tana murmushi, ya kallemu sannan yace

” Ni Rayhana nake so!”

Se kuwa ta mike ta fada bedroom din Gwoggo wai taji kunya, me zanyi Banda dariya, Gwoggo tace

” Jaira Ashe tana kunya, to a gabana ka fada Kar naji wata magana wadda ba daidai ba, bazan dauki yaudara ba”

Yaya Fahad ya dubeni yace

” Anty Safiyya kinji wai yaudara! Ni nace Ina sonta fa ta Yaya Zan sata kuka”

Se naji ya burgeni saboda he’s kind Kuma he’s straight forward kamar Yar gidan nashi, nayi murmushi nace

” Dan Allah call me Sofy, Nima Ina Bayan Gwoggo”

Gwoggo tayi dariya tace a kawo Masa abinci, Muna ta hira mostly tambayar akan Rayha ce Nima Kuma na Yi kokarin nuna Masa she’s all o have bazan tolerating wani ya data cikin kunci ba, plus na nuna Masa kyawawan halayan ta. Dake Ammi Bata samu matsala da Amma ba Dan itama su Ummaah ba wani sonta suke ba se Naga Babu matsala. Karshe dai shi ya Kai mu har gida ya Shiga ya gaida Ammi itama kamar tasan future in law dinta ne ta karbe shi hannu bibbiyu dukda haka take, she has a kind nature.

Washegari jumaa, a gida Yaya Fahad yayi breakfast bayan ya tafi na fadawa Ammi abinda ke faruwa dukda Ina tsoron fada amma se tace Mana

” Bazan Hana ku soyayya ba, saboda Dole watarana zakiyi, aure Dole ne duk Wanda lokacin shi yayi to se yayi. Amma Ina son kuyi karatu kuyi ilimi ku tsaya da kanki, ni Ina son na zame muku misali da ace nayi karatu ko Ina Sanaa bana tunanin matsalolin Baban ku zai dameni, Amma ku kalla yadda baban ku ya dawo dani nan ya Yar tamkar ba aurena yake ba..”

Se tayi shiru tareda sakin murmushi me ciwo tace

” Fahad yaran kirki ne, mahaifiyar shi Hajiya Hannatu mutuniyar kirki ce, ki bashi dama”

Daga haka ta cigaba da aikin ta, na Mike muka cigaba da aiki Amma zuciyata na Raya min Ammi na cikin damuwa, she always support Baba Amma shi Bai ma damu da ita ba. Da yamma muka kammalla abinci muka gyara gidan, Ammi ta gyara kanta, nida Rayha muna karatun PQ na JAMB, Anisah na kallon jimjam dukda itama na fara daura ta kan karatun. Sallamar Baba muka ji, ya shigo fuskar shi Babu annuri, na mishi sañnu da zuwa, Rayha ma tayi Masa magana sannan yayi dakin shi Anisah na biye dashi,daki na nufa nace da Ammi Baba ya dawo, ta fito ta nufi dakin nashi, Babu jimawa ta dawo parlon ta zauna tana kallon abinda Anisah ta Bari nayi jikin screen din tv. Bai Jima ba ya fito yace na kawo Masa abinci,na dubi Ammi dake zaune nace

” Ammi abinci inji Baba”

Tace

“Kije ki Kai Masa”1

Haka na Mike jikina a sanyaye na dakko abincin na Kai Masa, books Dina na tattare na wuce daki Raina a bace.

Abu kamar Wasa kwata kwata Baba ya birkice ya canja ma Ammi gaba daya, Abu daya na fahimta dashi, tunda dole aka masa ya dawo da ita, to gashi ya dawo da ita taci uwar da zata ci. Ban taba jin hutu ya isheni ba kamar wannan hutun, naji na tsani komai musamman idan akace Friday tayi se naji bacin Rai nake, saboda nasan he’ll be back treating her unfair. Ranar Muna zaune daga ni se Ammi a daki nace+
” Ammi!”
Tace
” Ya akai?”
Nace
” Dama kiyi hakuri Ammi, Ina ganin kamar I don’t have right na Fadi haka Amma me yasa Baba dake kuke fada. Na zata Kun shirya bayan Kun dawo”
Se tayi murmushi tare da mikewa ta shafan Kai tace
” Kada kiyi tunani da yawa, it’s nothing”
Bata ma jira abinda Zan fada ba ta tafi. Nayi shiru Ina kallon yadda tayi murmushi ta fita, jikina Babu dadi na zauna tareda dafe kaina Ina ayyana yadda zanyi, to ya zanyi kuwan tunda iyayena Babu yadda zanyi dasu, da ace Zan iya da Baba Zan samu nayi maganar dashi. A hankali Kuma ranakun suka wuce har hutun ya Kare, Wanda idan muka koma Kuma bana tunanin zamu sake dawowa har se munyi graduation. A day to zamu tafi Ammi tayi bakuwa, Ammah ce tazo daga maiduguri, ita ce mahaifiyar Yaya Fahad. Ita dashi suka zo, Ina zaune na shimfida carpet ina koyawa Rayha construction na maths, se munyi mun Gama idan na samo Mata wani question din kan construction se tace wai ita Bata gane ba, na yaga paper nace
” Ammi Kinga Taki tsayawa ta koya ko?”
Ammi dake gefen mu tana ninke Kaya tace
” To tayi ta Wasa ai, idan akai tambayar a exams ta Fadi”
Ta Bata Rai ta karba set square hannuna ta fara kokarin pointing figures din, na tabe baki Ina lura da ita , Ashe iskanci ne kawai Dan ta wahalar dani, Bata Kai rabi muka ji sallamar Ammah, ta shigo sanye da lafaya tana ta kanshi, matar ta saje da zama da kanuri, dake min Jima bamu ganta ba yasa bamu wani santa ba, bayanta itada Yan Mata ne guda biyu kusan saanin mu dukda daya zata girme mu, Ammi na dagowa ta aje silk din hannunta tareda sakin murmushi tace
” Barka da zuwa. Sannun ku da zuwa”
Itama ta fadada fara’ar ta tace
” Maman Sofy kwana da yawa”
Ammi ta shiga dasu ciki muma se muka Mike muka rufa musu baya, tana kallon mu tace
” Mashaaa Allah ki kalla yadda su Sofy suka girma, banyi tunanin zatai tsayi ba fa”
Ammi tace
” Kinga Sofy nan, wannan Rayha ce”
Ta rike baki tana Murmushin da fadin mashaaa Allah, Ammi tace
” Ba ku santa ba?”
Na gyada kaina ni da Rayha, tace
” Maman Fahad ce!”
Na kalla Rayha Naga tayi saurin sunkuyar da kanta, nayi dariya sauran ma dariya sukai se muka fita zuwa dakin mu , babbar irin sunana ke gareta ana ce Mata Mami, se dayar Amira.
Yaya Mami tace
” Yaya Fahad tunda ya dawo kullum zancen ki yake, duk kin saka ya susuce”
Rayha tayi murmushi ni ce nace
” Itama haka, kullum zancen Yaya Fahad take”
Ta kaimin duka Amira tace
” Kai Yaya Sofy, she’s too innocent for that”
Se Yaya Mami tace
” Waya fada Miki akwai anyone innocent akan soyayya? Bana tunanin akwai”
Munata Hira Ina Kara fahimtar Rayha ta gama saa ni ce na rage Kuma. A parlor na Gama kawo abinci da ruwa da lemon Dana bayar aka siyo, Suma na daki na hada Mana a tray kamar yadda yaya Mami yace.
” Mun Dade bamu hadu ba, Ina tunanin tun haihuwar Anisah rabo na dake”
Ammi tayi murmushi tace
” Aikuwa dai, ni kaina na manta karshe da na ganki”
Ta sauke ajiyar zuciya tace
” Fahad ya fada min, yace Yana son Rayha, da farko dai tun suna Yara na riga na dasa musu kiyayyar dangin mahaifin su, saboda duk yadda nake jin labarin wahalar da kika Sha tawa tafi Taki, Baban Fahad ya aureni ban Kai Sha biyar ba, Dan haka Gwoggo kadai ta Soni, ni lokacin da nayi aure da yawan su basuyi aure ba, Kuma anan gidan su na zauna, bani ba ‘ya’yana ma Basu tsira ba, Naga wulakanci kala kala iri iri. Dalilin su yasa ya daukeni ya maida ni maiduguri shiyasa kikaga baki taba haihuwa nazo Miki barka ba, tunda na fahimci rayuwa shikenan na ce sun Gama min rashin mutunci, na fitar harkar su, ko Abu suke na daina zuwa Kuma ‘ya’yana ma bazasu zo ba tunda ni na haife su, ba Wanda yayi min nakudar su, na Sha fada musu Babu Wanda ya Isa ya auro min wani daga Gumel, suje ga Yara nan a titi su aura Amma Banda auren cikin gida. Dangin Baban su Babu abinda Basu fada, na Hana Yara zumunci, ni tunda bazan zo ba su Ina turo su, Babu maganar da basuyi ba Amma na maida su banzaye, na nuna masu Basu Isa ba sunyi kadan, to Amma me yasa nayi winning saboda na nemi na kaina, na kafa kaina Ina sanaata, duk wani Hali da kike ciki na sani Kuma Ina hango wautar ki, ya kamata ki tashi kiyi Sanaa ki nema kudin ki, idan Babandi yazo kanshi idan Bai zo ba damuwar shi, dangin shi ki daina shiga sabgar su wallahi Ina tabbatar Miki se sun Mika wuya. Ita Kuma waccan matsiyaciyar da take tunanin ta gama dake, ki rabu da ita, Allah Bai hallatawa kanshi zalunci ga bayin shi ba, balle mu muyi. Allah zai bi maki hakkin ki, Amma Ina son yau ki canja zaman nan. Irin wannan Yana weakening yaran mu, musamman Mata, zasu ga kamar aure haka yake saboda haka suka ga anayi a gidan su, ko kuma suce Suma se sun muzgunawa Wanda suke tare dashi. Ya kamata ki tashi ki Zama strong not for him but for these lovely kids. A gurin Babandi bakida sauran martaba tunda ya iya dakko ki ya dawo dake nan, yanzun ba lokacin ya zaayi a gyara zaman ku bane, bazai gyaru ba mutum Bai Isa ya gyara ba, kiyi addua nasan Allah will not shun you! Amma ki nema naki, kiyi Sanaa tunda Bai barki kinyi karatu ba, idan yaso ni Kuma na Miki alkawarin I’ll support you”
Ammi ta Yi ta kuka kamar dama jira take, an Sosa Mata inda yake Mata ciwo, ganin hakan Ammah ta Kama hannunta Suka koma bedroom dinta Dan kada muji, seda ta daina kukan sannan Ammah ta cigaba
” Ki daina kuka, duk wannan ki dauka a da ne. Nayi mamaki da Fahad ya sameni da maganar Amma Yana fada min nayi nazari na karbeta, dama Ina tunanin zuwa muyi magana Sega babban rabo ya Kara hada mu. Allah ya tabbatar musu da alkhairi!”
Ammi ta amsa da Amin sannan Suka koma zancen abinda Ammi zata na siyarwa, da kanta ta saka Ammi ta Bata hundred thousand cikin kudin da Baba ke Bata lokaci zuwa lokaci, ta Mata bayanin cewar zasu dinga zuwa Kano tana siyan atamfofi tana siyarwa maaikata karshen wata ta hada kudin ta, sannan ta fara online business. Ammah har yamma suna gidan mu, Kuma suna daki itada Ammi se dare suka tafi, washegari Yaya Fahad ya dauke mu zuwa Funtua ita Kuma Ammah da Ammi aka sauke su kasuwar kwari Dan a fara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *