UNCLE NE CHAPTER 10 BY NIMCYLUV

UNCLE NE CHAPTER 10 BY NIMCYLUV

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

A gsky lamarin aƙwai abun dubawa,ina yare na haifi ɗa a kirasa da shege,nikam ba zan iya wannan ɗan yan aikin ba,cin amana ido biyu”zubewa nayi a ƙasa tare da dafa ƙafafunsa ina kuka kamar raina zai fita nace “ka taimake ni,kayi min rai babu wanda zan iya tunkara da buƙata ta sai kai,kai ne ka cancanta da kazama uba ga ɗan da zan haifa,bana da wani ƙata kuma burina bai huce ɗan da zan haifa ya samu kyakkyawar mu’amala a wajan Jalal ba,a yanzu burina bai huce na sama yarinya mace ma wacce zan haɗa ta Jalal domin ya zama garkuwa gareta,ina da tabbacin bazai taɓa bari jinina ya hulaƙanta ba sai iya rasa komai akan ya rasa ɗan dana haifa,kaga idan har Jalal na raye Lamir bazai taɓa samun nasarar cutar da ita ko shi ba,dan Allah ka taimaka min Please” na ƙare

maganar ina ƙara sautin kuka na,shuru Alhaji khamal yay,ban san mene yake tunani ba sai kawai naji yace ya “amince amma bisa sharaɗi guda”da sauri nace masa “sharaɗin mene?” Kallonta yaga da gaske take buƙatar abinda take mgn shi gaba ɗaya abun kamar almara,sai kuma yace “idan har kin samu yarinya mace dole ne ki haɗa auranta da Jalal,domin kin san idan ba shi ba,babu yadda za’ai wani ya AURETA musamman idan aka tabbatar shegiya ce…,”shuru yay yana jin kalmar nayi masa zafi a ransa kafin ya ɗura da “idan kuma namiji aka haifa dole ki bawa Jalal riƙon sa domin ni bazan iya ba”banyi tunanin komai ba nace na amince,shuru Mummy tayi da bada labarin idanun na janyewa wata farar kumfa ta fara fita daga cikin bakinta alamar dafara mutuwa tazo gangara, Jalal rasa abin cewa yay sai kallon Nihila yake wacce take ta zabga kuka tare da ihu Mameey ta riƙe ta,runtsa idanunsa yayi zuciyarsa nayi masa zafi komai na kansa ya kunce yana rasa tudun dafawa,da sauri ya buɗe idanunsa sabida wata miƙa da Mummy tayi ta ƙanƙame Jalal,da sauri ya riƙe ta idanunsa ya kaɗa yay jajirrr,cikin sarƙewar numfashi Mummy tace “tun daga wannan ranar muka fara mu’amala da Alhaji khamal,idan ba zaka manta ba ina ce maka zani asibiti to a zahirin gsky bawai asibitin nake zuwa ba, lokacin dana fahimci ina juna biyu sai na sanarwa da Alh khamal kuma tun daga ranar na ɗauke ƙafata ban ƙara zuwa inda yake ba kamar yadda shima bai neme ni ba,cikina yana da wata baƙwai nayi scanning aka tabbatar da mace zan haifa sbd murna sai da nayi sadaka,bayan haka da sati guda wata rana nace gida na samu Lamir a cikin bedroom yana faɗin _ni dai burina bai huce naga na samu kuɗi masu yawa wanda za’a dinga ƙwatance dani ba,shuru naji yayi kafin yace okey idan wannan ne babu matsala dama na taɓa gaya maka tana da ciki yanzu haka gaf take da haihuwa kuma naji ance mace zata haifa kaga abun yazo mana a dai-dai,ni kuma zanta jira har yarinyar ta girma wannan shine kawai_ bayan naji haka da sauri nabar gidan gabana na faɗuwa domin ban san wanne abu ya shiryawa ɗan ciki na ba,kullum cikin fargaba nake da zullumi haka dai naita addu’a ina neman tsari har na haifi baby a ranar dana haifeta ne kuma naje wajan boka domin ya ƙara rufe min bakinka sbd kada ka tambayi yaya akai na samu ciki bayan bamu taɓa tarayya dakai ba,bayan Jalal ya dawo a kuma airport mgnarsa ta farko inda yake cewa _dama za’a bani aurenta_ shi kaɗai ya tabbatar da cewa Jalal yana son baby kuma na ƙara godewa daya bani shi a matsayin ɗan ƴar uwata,tun kuma daga ranar na fara rashin lfy bana faɗawa komai koda naje asibiti aka shaida min Zcyarta ta kamu da ciwo banyi mamaki ba domin yadda damuwa tayi min yawa kullum cikin kuka nake da tunani nasan hakan zai iya faruwa dani” kallon Jalal tayi kafin ta kama hannunsa ta riƙe sannan ta kalli Nihila tayi mata alama da tazo da sauri ta zame jikinta daga na Mameey ta ƙarasa wajan gadon kusa da ita ta zauna,hannunta ta riƙe kana ta sanya cikin na Jalal ta haɗe hannayensu waje guda tace “Wannan amanace gareka ko bayan babu raina,ina fatan zaka ƙarasa cikamin burina ta hanyar auran Nihila,nasan zaka zama inuwarta zaka zame mata Garkuwa,zaka bata dukkan kulawan daya dace,ina da tabbacin ba zaka taɓa barinta tayi kuka ba,nasan ba zaka taɓa bari wata halitta ta cutar da ita ba indai kana raye,dan Allah dan Annabi Jalal ka auri Nihila ka zama nagartaccen miji gareta ina fatan zaka cikamin wannan burin nawa ka kareta daga sharrin maƙiyanmu” wata zuface ta shiga karyowa Abbou kansa ya shiga sarawa,abu goma da ashirin suka taro waje guda sukai masa yawa,da rashin asalin da yake dashi ko kuma da cin amanar da Mummy tayi masa?ko kuma da rashin mahaifiyar Jalal wanda rashinta yake damunsa a yanzu,wato wannan dalilin ya sanya Alhaji khamal yake ƙin haɗa idanu dashi, wannan dalilin yasa sanda yake masa da tasa buƙatar ya tsaya yana masa wani surutai akan hakan bai dace ba,ya tsaya zuwa wani lokaci,da sauri ya juya sbd jin abinda Mummy tace “Bana da bakin da zanyi maka mgn,sannan bana da bakin da zan nemi hafiyarka,amma tun a sali ban aureka domin ina sonka ba,haka kuma bana jin tsanarka a Zcyarta,dan Allah kaji tausayina ka yafemin nasan ni me laifi ce a GAREKU,amma babu yadda na iya garin ceton wasu rayukan nima na jefa kaina ga halaka,dan Allah Abbou Jalal ka yafe min kace ka yafemin kada na tafi lahira da haƙƙinka a kaina,yafiyarka nake nema” kasa cewa komai Abbou sai kuma ya ɗaga kai ya kalli Jalal shima kallonsa yay yana son yaji abinda zai ce,ganin bashi da niyyar magana yasa ya langwaɓar dakai tare da ɗan haɗe hannayensa alamar roƙo, ɗauke kai Abbou yay idanunsa na kawo ruwa yace “babu komai Allah ya yafe mana baki ɗaya Ubangiji ya baki lfy”Murmushi jin daɗi tayi kafin ta kalli Nihila tace “am so sorry my blood,na maki laifi na samar dake ta hanyar da bai dace ace an samu dukkan wata yarinya ko yaro ba,amma zanan ƙaddararki ne haka kuma Ubangiji ya nufa ta haka za kizo,ina neman alfarmarki da kiyafewa mahaifiyarki ko zata samu sauƙin tafiya lahira” cikin kuka Nihila ta riƙe hannun Mummy tace “dan Allah Mummy ki dana faɗin haka ni ba kiyimin komai ba,dan Allah ki tashi haka mutafi gida”ta ƙare maganar tana sakin wani sabon kuka,hannu Aryan yasa ya ɗauke ta daga jikin Mummy, numfashinta ne ya fara fita idan ya fita kuma baya dawowa cikin ƙasa da murya Jalal yace “fita da ita” jin haka yasa Nihila ta ƙara fasa wani kukan tana kiran sunan Mummy,hannun Jalal Mummy ta ƙara riƙe wa tace “idan Allah ya nufa mahaifiyarka na raye kuma Ubangiji ya ƙaddara saduwarku ina son ka nemar min yafiyarta”tana faɗin hakan ta fara miƙa idanunta ya shiga ƙafewa,da sauri Jalal ya shiga faɗin “La’ilaha illallah Muhammad Rasulullah S.w.a³” gaba ɗaya mutanan room ɗin suka shiga maimaita hakan lokacin hankalinta ya fara ficewa sai faɗin “Jalal ga Nihila,bobo Nihila ga baby nan” murza hannunta ya shiga yi yana ɗan ƙara sautin muryarsa cikin sarƙewar numfashi itama ta fara ambaton kalmar shahada kafin tace “Muhammad Rasulullah s.w.a..La’ilaha illallah..,” cak numfashinta ya tsaya yayinda computer itama tai shuru da kukan da take sai kuma wani gudan jini daya fita ta cikin hancinta,runtsa idanunsa yayi tare da kifa kansa a ƙirjin Mummy ya shiga sauke numfashi tare da sauke wasu tagwayen ajjiyar zcya, Mameey ce ta saka kuka ta kiran sunan Allah tare dayin sallati Abbou kallon Mummy yake yana ganin mutuwar kamar almara,gaba aka rasa mai ƙwaƙƙwaran mutsi a cikinsu, Jalal kowa har yanzu yana ƙwance jikin Mummy yana ta ajjiyar zcya,ganin babu wani lokaci yasa Abbou ya ƙarfafa zuciyarsa ya miƙe tsaye tare da ƙarasawa inda Jalal yake zaune ganin yadda ya ƙanƙame gawar Mummy yay a hankali ya saka hannu tare da kama Jalal ya miƙar dashi tsaye, idanunsa a rufe ya nufi hanyar ficewa daga room ɗin yana gaf da ficewa ya yanke jiki ya faɗi a wajan babu numfashi,da sauri Imran ya ƙarasu wajan Mameey kuma tayi waje da gudu tana ƙwalawa Dr kira,wasu likitoci ne wajan guda 4 suka fito lokaci guda kana sukai ɗakin da gudu ganin Jalal yashe a ƙasa yasa suka ƙamashi tare da ɗura sa a kan wani gadon daban, Abbou wani farin abu yasa ya rufe Mummy dashi bayan ya rufe mata idanunta,kallon Dr yay yace “kun gama komai zamu kaita gida ai mata suttura” Dr ya kalli Abbou cike da tausayi yace “eh zaku iya tafiya da ita,amma yallaɓai sai zuwa gobe” jinjina kai Abbou yay kana ya kalli yaran nasa a hankali kuma aka tura gawar Mummy zuwa waje har cikin ambulance aka sanya gawar kana Abbou ya shiga motarsa Imran ya zauna driver Aryan shima motarsa ya shiga ya ɗauki Mameey da Nihila suka marawa motar ambulance ɗin baya, Irfan kuma ya koma wajan Jalal.

Irfan yana shiga ward ɗin ya tarar har an ɗaurawa Jalal drip ga wani bandeji da aka saka masa a gefen ƙoshinsa sbd bigewar da yay lokacin daya faɗi har kansa ya fashe,waje ya samu ya zauna yana mai ƙarewar fuskar yayan nasa kallo,banda yana da zcyar imani ai da sai zcyarsa ta buga amma tunda ya aka fara wannan abun bai nuna wani abu ba sai yanzu da rasuwar Mummy ta bugasa da ƙasa, ajjiyar zcyar Irfan ya sauke yana ta tunanin abubuwa da yawa da suka dinga faruwa,yana zaunan yaji an buɗe ƙofa ganin Dr yasa ya ɗauke kansa, Dr na ƙara zuwa ya kalli Irfan yace “Madam tana shirin farkawa ya kamata ace da wata ko wani kusa da ita” miƙewa Irfan yay kana yace “babu damuwa za’a iya barinsa shi ɗaya ko?” Dr yace “eh babu damuwa” bayan Dr yabi har zuwa room ɗin da aka ƙwantar da Jalilerh,tana ƙwance sai juya kanta take tana sauke numfashi tare dafe kanta,tsayawa yay a kanta yana mai nazarin halinda take ciki,ganin tsaiwar nada yawa yasa a hankali yaja kujera ya zauna kana ya ɗauki wayarsa ya shiga dannawa,kai tsaye I.G ya shiga ya ɗauki photon Jalal wanda ya ɗauka shida Mummy tana Murmushi kana yay sign akan photon ya rubuta R.I.P Mummy,sai kuma wasu sauran baya nan,kana yay posting,yana gamawa ya shiga twitter nan ma yay posting kusan gaba ɗayansu babu wanda yake facebook da whatsapp shiyasa daga nan ya kashe datar wayar ya shiga istigifari a ransa yana mai nemawa Mummy sauƙi wajan Ubangiji..

Tun kafin su isa gidan labari yaje wajansu Mama nan ta ƙara rikicewa ta shiga kuke kamar ranta zai fita,a haka har suka samu Mama nan aka sanya gawar Mama cikin part ɗin Abbou ana shiga matan maƙota suka fara zuwa aka shiga yiwa Mummy suttura akaci sa’a babu kitso a kanta,da sauri aka fara shiryata sbd magrib daya tawo kai,bayan an kammala shiryata Mameey taje wajan Abbou da muryarta da baya fita tace “ba za’a kira Jalal ba?haka za’a kaita?” Kallonta kawai sai kuma yace “shima yana ta kansa ne,idan kun kammala bari mu ɗauke ta” tace “an kammala daman ku ake jira” baice komai ba ya fita can ya suka shigo shida Aryan da Imran sai kuma Alhaji khamal, Lamir yazo Abbou yace “kada ka sake naga hannunka a gawar matata” fita yay daga gidan gaba ɗaya haka aka sallaci Mummy aka kaita gidanta na gsky, Nihila kowa tayi suma yakai uku data farka taga gawar Mummy ko taji ana maganar sai ta ƙara ficewa daga hayyacinta,a haka Abbou yay mata allurar bacci tana surutai..

Misalin 8 na dare a can asibiti Irfan yana can tare da marasa lfy haka yay ta zirga-zirga daga wajan Jalal zuwa wajan Jalilerh,yanzu ma yana zaune gaban gadon Jalilerh ta fara mutsi kafin a hankali ta ɗan fara shura ƙafafunta miƙewa yay ganin kamar ta farka a hankali kuma yaji tana surutai kasa kunne yay yaji tana faɗin “Uncle… Uncle..kai na…ciwo…zai fashe…,”sai kuma yaji ta fasa ihu da ƙarfi tace “Uncle wayyo za muyi accident” a dai-dai lokacin shima Jalal ya mutsa ya shiga buɗe idanunsa a hankali amma ko mutsa kansa ya kasa sbd yadda ya kejin kansa yana sara masa da ƙarfin gaske,bayar da idanunsa yay ya rufe da sauri yana mai danne saitin zcyarsa sbd ihun Jalilerh daya jiyo,sai kuma yaji an buɗe ƙofa da gudu an shigo kafin yay wani tunani yaji ta faɗo kansa tana fasa ihu tare da ƙanƙamesa ta shiga faɗin “Uncle please wake up…dan Allah ka tashi..”kasa mutsawa yay sai hannunsa ɗaya ɗaga a hankali ya ɗura a bayanta ya rungome yana sauke numfashi cikin kuka ta kifa kanta a fuskarsa ta shiga taɓa wajan da yake masa ciwo kafin kuma a hankali ta ɗura lips ɗinta saman goshinsa tana sakin wani sabon kukan…

Jalal jin kukan Jalilerh yake har ƙahon zucyarsa,gashi yay try na buɗe idanunsa ya kasa bare har yay tunanin mutsa jikinsa ya lallasheta,bisa dole ya ƙara maida idanunsa da basu gama buɗewa ba ya rufe ruff yana sauke ajjiyar zcy da sauri da sauri,hakan Jalilerh ta ƙara rikicewa ta shiga rera kuka tana jijjiga Jalal wanda bai ma san abinda take masa sai dai duk ihunta guda yana tafiya ne da bugun zcyarsa da ace kuma zata fahimci hakan da bata tsaya tana masa kuka akai ba,domin kukanta ma wata azaba ce ta daban a cikin ransa,ji yake gaba ɗaya duniyar tayi masa zafi kansa yay masa nauyi,har yanzu ganin abun yake kamar a mafarki wai Mummy ta rasu?da gaske bata raye?shikenan yanzu bashi da wata uwa da zai kalla ya kirata da sunan Mummy,bashi da kowa sai Abbou’nsa, innalillahi wa’inna ilaihir raji’un,kawai yake maimaita wa a cikin zcyarsa,sai kuma a lokacin ya tuna da Nihila runtsa idanunsa yayi da ƙarfi sbd wani bugu da zcyrsa tayi masa,tayaya zai iya zama da ƙanwarsa a matsayin matarsa?tayaya zai kula da haƙƙoƙinta sa zasu rataya a wuyansa?a ɗauka lafiyarsa ƙalau baya jin zai iya tarayya da Nihila a matsayin matarsa,mene yasa Mummy ta ɗura masa wannan abun mai girma?mene yasa ta saka shi cikin tsaka mai wahala?tasan cewa koda bai auri Nihila tana da tabbacin zai kula da lafiyar,iliminta,komai nata zai zame mata Garkuwar da a kullum take faɗa,zai tsaya ya kula da ita sai inda ƙarfin sa ya tsaya,koda zai shiga wani halin indai tana lafiya zai iya jure koma mene amma mene yasa lalle dole saiya AURETA ta zama mata a wajansa?haka yayta surutai a ransa babu wanda yasan me yake faɗa sai ajjiyar zcyar da yake saukewa akai akai,a hankali wani Dr ya ɗauki injection kana ya nufi wajan Jalilerh da ita,duk akan idanun Irfan wanda yake tsaye ya harɗe hannayen sa yana kallon ikon Allah,yadda ta kifa kanta a saman ƙirjinsa yasa bata san abinda Dr ke aikatawa ba kuka kawai take tana kiran “Uncle… please wake up”a haka ya samu tsira mata injection ɗin a kai ɗinta wacce ta baiyana sabida rigar asibitin da aka saka mata iyakarta guiwa,wani ihu ta tsala tare da ƙanƙame Jalal tana sakin wani sabon kukan,shi wata muryar shagwaɓa ta manna lips ɗinta a faffaɗan ƙirjinsa tare da sakar masa cizo, sbd tsaɓar azabar da taji ta allurar,taune lips Jalal yay sbd zafin cizon da yaji har ransa amma still bai mutsa ba,5minutes left yaji saukar numfashinta a ƙirjinsa hakan ya tabbatar masa da bacci ne ya ɗauke ta,sai kuma a lokacin shima ya samu kuzari ya ƙarfafa zuciyarsa ya shiga buɗe idanunsa a hankali kamar mai tsoran buɗe idanunsa daya buɗe yaga haske sai ya bayar ya rufe a haka harya samu damar buɗe idanunsa samar drip ɗin da aka maƙala masa,cikin ransa yake ƙara karanta addu’ar duk da yazo masa,a hankali kuma ya juya gadon da aka ƙwantar da Mummy da sauri ya ɗauke idanunsa sai kuma ya fara ƙoƙarin tashi zaune amma ya kasa sbd gaba ɗaya babu wani kuzari a tare dashi gaba ɗaya ya zama very weak,kansa ya shiga girgiza wa wanda ya keji kamar zai faɗi ƙasa sbd a zaba,hakan yasa Jalilerh dake jikinsa tayi saurin firgita sbd gaba ɗaya a tsorace tayi baccin,cikin baccin ta Turi baki gaba sai kuma ta kwaɓe fuska cikin ƙasa da murya tace “Uncle… Uncle naaaaaa”da idanunsa kawai yake kallonta ko ƙiftawa ya kasa yi,sbd yadda yaga ta zama exactly ƙaramar yarinya wacce bata huce 15yrs ɗin nan ba, lips ɗinta wanda ya jiƙe da hawaye da kuma yawo yay jajirrr sbd taunesa da take da kuma yawan kukan da tayi yayi,da sauri kuma ya janye idanunsa daga kanta, numfashi ya sauke kafin ya kalli agogon warist ɗin yaga lokacin har anyi issha’i,waro idanunsa waje yay duk da cewa baya cikin nutsuwar sa yay missed sallolin amma sai da gabansa ya faɗi, turo ƙofar da akai yasa ya buɗe gajiyayyun idanunsa ya ɗura su a ƙofar domin ganin mai shigowa,sai a lokacin yaga Irfan tsaye yana kallon su,da sauri Irfan ya ɗauke idanunsa sbd kallon da yaga yayan nasa yana masa,shima Jalal ɗauke idanunsa yayi a dai-dai lokaci ne kuma Aryan shida Mama suka shigo cikin room ɗin, Mama na gaba Aryan na bayanta hannunsa riƙe da basket ɗin dinner,kallo guda yay masu ya ɗauke kai Aryan kam kasa ɗauke idanunsa yay daga kan Jalilerh wacce tayi ƙwance jikin Jalal tana bacci hankali ƙwance gaba ɗaya ta nan naɗe ƙafafuwan ta a jikinsa sbd tsayin a.c dake ratsa ta gashin kanta ya baje saman ƙirjin Jalal,sai ta zama kamar wata ƴar baby komai yay mata ƙyau, ɗauke kanta yay yana jin yadda zcyarsa keyi masa zafi da kuma radaɗi, Mama ce nemi waje ta zauna kusa Jalal sai Irfan yace “bari nai Sallah na dawo”kafin ya fita Jalal yay gyarany Murya tare da kallon Irfan,ganin haka yasa Irfan tsayawa tare dayin baya kaɗan,kallon Mama sai kuma ya kalli Jalilerh kamar bai son magana Murya can ƙasa yace “Nima zanyi sallar” Mama dai na zauna tayi jigum tana kallon jikan nata wanda a yau kaminsa suka fitowa sak dana mahaifiyarsa,duk kallon da taka masa yana ji a jikinsa amma ko inda take bai kalla ba,ya shiga ƙoƙarin janye Jalilerh daga jikinsa a hankali sbd bai son ta farka yanzu, Aryan ne ya matso yace “can i help you?” Kafin Jalal yay magana Aryan ya miƙa hannu zai ɗauki Jalilerh Mama tayi saurin faɗin “mene kuma wannan Arwan?a’a Wlh babu ruwana mene zaka ɗauki mace kamar wata muharramakar?ko daman baka da kunya sam ina lura dakai a’a Wlh wannan ɗabi’ar ya hudawan ba dani ba sam³,ohhh³ zamani kenan kawai kai tsakaninka da Allah saika ɗauke ta?yooo ko matarka ce ai kaji kunyar idanuwan nan nawa da suke kallon ka” haɗe fuska Aryan yay kana yace “uhm she’s my wife to….,” Tarin da Jalal yay yasa yay saurin yin shuru yana kallon sa,shikam ko inda yake bai kalla ba ya jajirce ya miƙe tsaye yana gyarawa Jalilerh kwanciya, Irfan ne yace “yaya daka fara cin abinci babu komai cikinka ya” bai kallesa ba sai fesar da iska da yayi daga bakinsa kafin yace “i want to take a shower” “ok” Irfan yace yana shigewa bathroom warm water ya haɗa masa cikin Jacuzzi kana ya dawo yace “You can enter” a hankali kuma cikin nutsuwar data gama ratsa jikinsa ya nufi bathroom ɗin,yana shiga Aryan ya matsa jikin gadon tare da zama saitin kan Jalilerh ya ƙura mata ido yana kallon innocent face ɗinta wacce take cike da ƙuruciya,sosai yaga tayi masa ƙyau cikin kayan marasa lfiyan har wani lumshe idanunsa yake,ga yadda gashin idanunsa yay zara-zara yay ƙwance saman idanunta,a hankali kuma ya kama hannunta yana ɗan murza kaɗan kamar wacce take gani cikin bacci ta fara ƙoƙarin zame hannunta cikin ƙunƙuni kuma tace “don’t touch me” Mama kam salati ta saka kafin tace “iskanci ƙarara ya jama’ar Allah,wannan wacce lukutar masifa ce, ahhh haff bashi yasa nake cewa kuyi auran ana ganin kamar ta kura maku nake ko?to ai ga irinta nan Wlh babu ruwana kai da Muhammadu domin ƴar rainonsa ce tsaf zai rufe idanunsa ya maka ka a court tunda kaji ƙishin² zaɓen yay ƙyau,mukam babu da kuɗin jaya yayya dashi”firgita Jalilerh tayi sbd yadda Mama take rakarkatu zance hakan yasa ta kwaɓe fuska ta saka kuka duk a cikin baccin,sai lokacin Irfan yay magana dake shima mgn bai damesa ba yace “can you shut up or not?haba sai surutai ba kiga marasa lafiya bane ga kuma halin da muke ciki” kuka Mama ta fasa tace “shkknan zageni tasss Urfan,yanzu haka da Dakta zai dobani Nima zai iya bani gadon Wlh,sbd bana son shiga damuwa na biyo wannan sakaran zuwa asibiti ko naji daɗi idan naga Jalalu amma shine zaka ce mutuwar ƴarta bata dame ni,Wlh duk wanda zai ji mutuwar nan a baya nake babu komai Allah dai zai saka min”shi dai yana tsaye bai ƙara magana ba.

Jalal na shiga bathroom ɗin ya tsaya gaban makeken madubin dake maƙale a jikin bathroom ɗin a hankali kuma ya zare rigar dake jikinsa tare da zame boxer jikinsa daman alrdy an cire wandon shaddar,kansa ya ƙurawa idanu ta cikin madubin yana mamakin yadda lokacin guda ya zabge ya faɗa idanunsa suka ƙara fitowa ga wani fari daya ƙara kamar jini zai zoba jikinsa,gaba ɗaya kyakkyawar sumar kansa ta hargitse,a hankali ya sauke ganinsa zuwa mararsa da sauri ya ware manyan idanunsa sbd ganin abinda bai taɓa gani ba, dick ɗinsa ce ta miƙe tayi samɓal ga wasu jijiyoyi da suka fito a jikinta,kamar a mafarki haka yake ganin abun hannunsa ya miƙa tare da kamawa gam cikin wani mmkin yaji tana harbawa,kasa ɗauke hannunsa sbd wani yarrr da yaji a jikinsa da sauri ya zame hannunsa yana ƙara ganin yadda take ƙara girma da kumbura abin har mmki yake bashi, ko da hakan na nufin ya samu lfya shima zai iya samu kyawawan kids masu albarka kamar kowa? ɗauke tunaninsa da yay daga haka domin abinda yake tunanin ba mai sauƙi bane,domin result nawa ya tabbatar masa cewa mazai taɓa iya tarayya da wata mace ba,jikinsa yaja zuwa Jacuzzi kana ya shiga ƙasa jikinsa sosai sai da yaji jikin ta warware masa sannan yay wanka ya brush ya ɗaura alwala,yana tsaye yana tsane kansa dake ɗigar ruwa yaji ana knowking ƙofar,sosai yaji amma ya kasa zuwa wajan sai can ya nufi wajan ƙofar sanye towel buɗewa yay, Irfan ne ya miƙo masa kaya ya amsa sannan ya mayar da ƙofar ya rufe, Brown ɗin jallabiya ce sai boxer da kuma wando 3gauter duk sabbi,sakawa yay kuma sosai kalan jallabiyan ya ƙara haska farar fatarsa,ga yadda gashin kansa ya cikurkuɗen sai ya zama kamar wani balarabe,a haka ya buɗe ƙofar ya fita, lokacin Aryan baya ɗakin sai Mama da kuma Irfan wanda ya shimfiɗa ƙatuwar dadduma mai taushi a tsakiyar room ɗin,wajan Daddumar ya nufa yana zuwa Irfan ya ƙarasa sallar magrib da issha’i suka sallata yayinda zuhur da asr kuma Jalal yace Sai gobe idan dai-dai lutukan sun dawo,daman shi Irfan duk yayi wannan ma don shi ɗaya ne a asibitin,turo ƙofa akai Dr a gaba Aryan a baya,yana zuwa ya miƙawa Jalal wayar hannunsa,yi yay kamar bai san me yake ba hakan ya ƙara sosa ran Aryan daurewa yay yace “Abbou want talk to you” bai kallesa yace “sa handsfree”a fili ya saka wayar Abbou dake can zaune cikin ɗakinsa da Nihila a jikinsa wacce zazzaɓi ya rufeta yace “Muhammad” shuru Jalal sbd ganin ƙannansa a wajan hakan yasa Abbou cewa “guys drop the phone and get out of the room ok” miƙewa Irfan yay ya fita shima Aryan ya ajiye wayar kusan ƙafafuwan Jalal kana ya marawa ɗan uwansa baya,suna fita Jalal yace “uhm…” Abbou ya numfasa yace “how are you feeling now?” Langwaɓar dakai gefe yay kana ya shagway fuska murya can ƙasa yace “Abb…..ou..” Abbou yace “Yes! Sweetheart” kamar zai kuka haka ya ƙara yin ƙasa da muryarsa wacce ya saba amfani da ita idan ya kasance da mahaifin nasa yace “Abbou zcyata babu daɗi komai yay min zafin, can’t believe ace yau bana tare da Mummy she past a way, Abbou Mummy she’s no more,yaya zanyi….?yaya zan da al’ƙawarinta? tayaya zan iya zama da baby as my wife Abbou?” Ya ƙare maganar yana sauke tagwayen ajjiyar zcya,shuru Abbou yayi yana sauraran farin cikin nasa,domin a yanzu Jalal kawai zai kalla yaji daɗi komai yay masa zafi,idan yaji an ambata sunan Jalal sai yaga kamar ya taɓa sanin irin sunan daa,sosai yake iya jiyo yadda Jalal yake sauke ajjiyar zcy kafin yace “take it easy sweetheart komai,dukkan abinda ya faro da bawa muƙaddari ne a allon lauhil mahafuz, Mummy kuma lokacin ta ne yay kuma duk wanda lokacin sa yay ko 1minute bazai taɓa ƙarawa ba dole zai koma ga ubangijinsa,abu guda zakai ka saka mata da alkairi shine addu’a,sannan ka nisanta kanka da ɓacin rai kasan halin ka,kada ka sake ka ƙwana da damuwa please sweetheart, zan iya jure komai amma bazan jure ganinka cikin damuwa ba,kune ahali na kai da ƴan uwanka ku nake kalla naji daɗi tayaya kake tunanin zanso abinda zai taɓa lafiyarku?And bakai kaɗan Oum Jalal ta bari ba,ta barni tabar baby duk muna buƙatar ta,kasan dalilin daya sanya na kiraka at this time?” Girgiza kai Jalal yay kafin yace “uhm” Abbou yace “dan Allah dan Annabi dukkan abinda kasan zai sanyaka farin cikin a yau ka samesa kada ka ƙwana da damuwa please sweetheart” tunanin Jalal ya fara a yanzu a wannan daren tayaya zai iya sanin abinda zai zashi farin ciki?yadda ya kejin ransa babu daɗi shi sam bai ga abinda zai sanya shi farin ciki a yanzu ba,jin shuru yay yawa Abbou yace “where is Jalilerh?” Sai lokacin Jalal ya juya ya kalli Jalilerh yaga har yanzu bacci take idanunsa ya ɗauke yace “she’s with me Dad” kai Abbou ya jinjina yace “ok promise me kaji Muhammad” ɗan shagwaɓe fuska yay yace “ok promise”gaba ɗaya sukai shuru sai can Abbou yace “goodnight take care” da ɗan sauri Jalal yace “how is she?” Abbou yace “who?” ɗan lumshe idanunsa yay kafin ya fesar da iska yace “ba…by.” wani ƙawataccen Murmushi Abbou ya saki a karan farko yace “she’s fine” daga nan sukai sallama Abbou ya kashe wayar sam ya manta da Mama sai da yaji tace “Jalalu yay ƙarfin jiki,ya mukaji da wannan rashin Allah dai ya bamu hqrn rashi,to ba dole muyi hqr ba” yana jinta bai kalleta ba yace “Allhamdulillah” daga nan Irfan ya shigo yace “yaya what about the food?” Girgiza kai Jalal yay alamar bai so Mama tace “a’a Wlh baka isa ba,Wlh ko kaci kona sallamaka ina dalili dame zanji ko kaima su kake na rasa ka  kamar yadda na ratsa iyayenka har biyu?” ɗan mutsa bakinsa yay yace “just tea without milk” Irfan yace “ok” tea ya haɗa masa ya ɗauki lemon zai matsa Jalal yay sauri cewa “No!!” da mmki Irfan ya kallesa sbd kowa yasan baya iya shan tea sai ya matsa lemon tsami, miƙa masa cup ɗin yay bayan ya zoba masa suger guda 4 ya bashi,amsa yay kana ya miƙe yace “Mama taso mu huce gida” Mama tace “to wannan gantalailliyar yarinyar fa? Irfan yace “meye ruwanki da ita kuma kedai muje idan kuma gadon kike buƙata sai a kira Dr” da sauri tayi waje tace “amma kai a mugwaye kaine lamba guda kuma tantiri”bai ce komai ba yay wa yayan nasa sai da safe kana ya ɗauki wayar Aryan suka rufe masa ƙofa suka fita.

A hankali ya dinga shan tea ɗin har ya sha fiye da rabi sannan ya ajjiye,yana nan zaune yana tunani a ransa ya fara jiyo shasshekar kukanta kamar wacce take mafarki can kuma yaji tana faɗin “Uncle ga mota nan,zamu faɗi, Uncle…wayyoooo Uncle!!” ta faɗa cikin ɗaga murya da sauri ya Miƙe tare da zare jallabiyar jikinsa sbd wani zafi daya fara ziyartarsa,hawa bed ɗin yay ganin kamar a tsorace take yasa a hankali ya ɗan ƙwanta kusa da ita tare dasa hannu ya jawo ta jikinsa sosai,jin mutum kusa da ita yasa da sauri ta ƙanƙamesa jikinta duk rawa yake,yana daga ƙwancan ya ɗaga ta cak ya ɗura ta saman jikinsa yay copping face ɗinsu yana kallon yadda hawaye kebin fuskarta ga yadda lips ɗinta suke mutsi she’s try to say something amma ta kasa sai mamulmamul take da lips sunyi jajirr sun ɗan kumbura,a hankali ya lumshe idanunsa ganin har lokacin bata hayyacinta ya ƙara matsu da fuskarta zuwa kan tashi ya zamana bakinta ya kan nashi hanci ido komai, still bata bar firgita ba sai ɗan fisge-fisge take da alamu har yanzu accident ɗinsu ke yi mata gizo a idanunta,a hankali ya ware laɓɓansa ya kama nata ajjiyar zcya duk suka sauke lokacin da ɗumin bakinsu ya haɗu waje guda,shuru tayi sbd wani sihirtaccen ƙamshi da kuma taushi haɗi da ɗumin bakinsa daya ratsa nata, a hankali ta buɗe idanunta ta saukesu akan fuskarta nan taga shima ita yake kallo,da sauri ta janye nata sbd bugawar da zcyarta tayi, still idanunsa na kanta ya kama libo ɗinta na ƙasa ya sanya cikin nashi da sauri ta ƙara buɗe ido sai kuma ta ɗaga fuskarta daga tasa,da ɗan sauri ya mirgina ta ta faɗa saman gadon shi kuma yabi jikinta ya ƙwanta, ƙara ɗago kanta yay zuwa fuskarsa kafin a hankali kuma taushashe cikin wata iriyar murya yace “Please….Jewel…pls..,” bai ƙarasa Maganar yay sauri sanya bakinsa cikin nata.

Da alama Jalal he’s Fall in love with this innocent gril Jalilerh,and what about the promise i mean Nihila???

Waro idanu Jalilerh tayi tare da ɗura idanunta cikin na Jalal,shima ita yake kallo while bakinsa na cikin nata amma koda wasa baiyi try na kissing nata ba,kawai ya tsaya yana kallo erection ɗinta, girgiza kai ta farayi a hankali  still hawaye na bin fuskarta yana sauka a saman tashi fuskar,wani murmushi yay kana ya zare bakinsa a hankali tare da kifa kansa a saman ƙirjinta ya shiga sauke numfashi, cikin Muryar kuka Jalilerh tace “Uncle na yace min aduk lokacin da mukaji zuciyoyinmu babu daɗi muyi kuka,kuka sosai domin kuka na rage raɗaɗi da ƙunci zuciya kafin daga bisa ni mugujewa abinda yake sanyamu cikin damuwa kuma mu roƙin Ubangiji ya sassauta mana abinda mu keji, Uncle kayi kuka koza kaji daɗin zcyarka,kayi kuka ko ƙunci da raɗaɗin da zucyarka take maka zai rago,kayi kuka domin samawa kanka sauƙi da salama a ranka,kayi kuka Uncle ni shi nake buƙata a wajanka kayi kuka kayi kuka kayi kuka UNCLE..”kamar da wasa yaji wasu zafaffun hawaye sun fara bin saman kuncinsa a hankali ya fara sauke ajjiyar zcy kuka tasa itama da rungome sa,gaba ɗaya Jalal mantawa yay shi ɗin babba ne kuma namiji ne kuma wanda yake shirin zama shugaba a wannan garin,wani kuka ne yazo masa kukan da tunda yake a rayuwata bai taɓa irinsa da wayonsa ba,kukan da ko sanda Mummy ta rasu akan idanunsa bai irinsa ba,kuka ne wanda yake tawowa tun daga ƙasan zucyarsa,kansa ya ƙara shigarwa cikin ƙirjin ta ya shiga rera kuka cikin sautin muryarsa daga shi har Jalilerh an rasa mai rarrashin wani ba ita da take macen ba bare shi da yake namiji kuka yake da dukkan ƙarfin sa yana jin kukan na tafiya da zafi da ƙunci haɗi da raɗaɗin da zcyrsa take masa,sai da suka shafe wajan 20minutes suna kuka a tare kafin a hankali Jalal ya fara saita nutsuwar sa  shuru yayi ya shiga sauke ajjiyar zcya 10seconds left yaga taƙi daina kukanta sai shassheƙa take,tsayawa kawai ya fara tunani mezai mata?tayaya zai fara lallashinta?shi sam bai saba kuma bai san yaya ake ba, lumshe idanunsa kafin ya ware su a hankali kuma cike da juriya da jarumta ya ɗan ɗaga jikinsa daga nata domin yanzu wasai ya kejin zucyarsa bai taɓa sanin kuka na sawa aji sauƙin zcya ba sai yanzu, gajiyayyun idanunsa ya ɗaga a hankali ya sauke fuskarta tsayawa yay kawai yana kallonta ganin yadda take da kuka bil haƙƙi kamar ƙaramar yarinya,tashi yay daga jikinta kafin ya zauna a gefen gadon kallonta kawai yake kamar mai nazartar wani abu sai kuma kawai ya saka tattausan hannunsa ya ɗagota gaba ɗaya zuwa jikinsa,jikinsa ta shige tana ƙara sautin kukanta cikin nutsuwa ya ɗura kanta a shoulder ɗinsa ya fara clapping bayanta alamar rarrashi murya chan ƙasa kamar mai kuyan magana yace “Waye?”turo baki tayi tare da shagwaɓe fuska taci gaba da kukanta bakinsa ya ɗura a kunnanta a hankali kuma ya fara yi mata waƙar _WAIT FOR ME🎻_
_🎻🎻I don’t know when am coming back,i will be gone for a little while, but i will keep myself for me and you, i will be back for you,i dunno what the feature brings,but i want you to be with me I go de hope and pray Make You wait for me ,i Will come back for you darling🎻🎻._
Shuru tayi ta shiga sauke ajjiyar zcy tare da ƙare shigewa jikinsa,sosai waƙar tai mata daɗi Musamman kalaman cikinta,jin yay shuru yasa ta ɗago kanta da sauri ta rufe idanunta sbd haɗa ido da sukai dashi, ɗauke kai yana kallon agogo yaga remain 10minutes pass 10,can kuma yace “nayi kuka kinji ko?”kaita gyaɗa masa alamar eh,jinjina kai yay yace “good,da wasa kada ki sake wani yaji cewa nai kuka kin gane” saurin kallonsa tai to ita wa zata gayawa? Dawa take surutu da Mummy kawai take shira sai shi idan yay niyyar magana amma a haka har yake tunanin kada ta faɗawa wani,gira ya ɗaga mata sauri ɗauke kai tayi cire ta yay a jikinsa yace “oyaa look at me,ina son tambayearki” gyara zamanta tayi kanta a ƙasa ta fara wasa da yatsun hannunta domin sam bata jin zata iya haɗa idanu dashi bare har ta tsaya kallon cikin idanunsa, idanunsa a kanta kamar bazai magana ba sai kuma yace “Waye Uncle ɗin da kika faɗa ɗazo?” Cikin ƙaramar muryarta mai cike da ƙuruciya tace “Mom ta cemin kada na faɗawa kowa,amma bana jin zan iya ƙin gaya maka, Abba na ne amma Mummy ta ce min na dinga cewa Uncle” jinjina kai yay yace “to meyasa ya barki har wannan muta nan suke binki?” Shuru tayi na wani lokaci kafin tace “A ranar baya cikin birnin yaje meeting, ƙilan yama manta cewa ranar ce da ake haɗa samari da ƴan mata”taɓe bakinsa yay kana yaja baya ya jingina da jikin gadon kana ya lumshe idanunsa kamar mai bacci, shuru itama tayi tare da ƙurawa fuskarsa idanu kamar daga sama taji yace “Wace Ammi last time da naji kinyi maganarta?”shiru kawai tai masa domin ba zata iya faɗa masa matsayinta a wajanta,tabbas Ammi jigoce gareta duk da cewa bawai tana fahimtar komai bane amma sosai ta kejinta har cikin ransa da jinin jikinta, wasu hawaye ne suka shiga zubuwa daga cikin idanunta ta kasa ce masa komai, kallonta kawai shima yay kafin ya taɓe baki ya janye idanunsa daga kanta,sai tai kuka dan kanta ta hqr baice mata komai ba,ganin ta sauka daga kan bed yasa ya juya harya buɗe baki zai magana sai kuma yay shiru, sauka tayi ta nufi wajan da take ganin shine bathroom tana zuwa ta cire rigar asibiti ta haɗa ruwan zafi ta fara gasa jikinta gaba ɗaya ta manta acikin asibiti take,sai da ta gama wankan tai alwala nan fa ta rasa abin sawa a jikinta,rigar asibitin ta ɗauka zata saka sai kuma taga gaba ɗaya ta jiƙe da ruwa,tana nan tsaye harta shafe 20minutes can kuma ta matsa jikin ƙofar kamar mai raɗa duk tsoro ya gama kamata cikin sanyin murya tace “Uncle..” yana jinta yay shiru kamar bai san me tace ba,kamar zatai kuka ta ƙara cewa ,”Un…cle.. Uncle” gyara kwanciyarsa yay kamar bazai magana ba sai kuma yace “uhm” sound ɗin muryarsa kawai taji tasan cewa yaji me tace sai tace “bani aron rigar ka nasa” kallon ƙofar bathroom ɗin yay kafin ya sauke numfashi yace “idan naƙi fa?” Marai-raice fuska tayi tace “Please Uncle” ɗauke idanunsa yayi kafin yace “fito ki ɗauka”kwaɓe fuska tai tace “a hakan naked?” Lumshe idanunsa yay kamar mai bacci sai kuma yace “to zauna ciki”ya faɗi hakan yana ƙara lumshe idanunsa,jin shuru yasa ta buɗe ƙofar tare da ɗan leƙawa ganin ya juya baya yasa ta fito a hankali cikin sanɗa inda taga jallabiyar sa ta nufa tana zuwa ta ɗauka yana sane ya mutsa tare da karkato kansa aikam da gudu ta kwasa tai cikin bathroom,wani lafiyayyan murmushi ya saki har sai da dimples ɗinsa suka loma,kana yaja idanunsa ya rufe,sai da ta gama saka riga taga tana ja mata har ƙasa fitowa tayi a hankali ganin babu vail ko hijab yasa ta ɗauki wani hirami ta yane kanta dashi a haka ta gabatar da sallar da ake binta kana ta shiga azkar ɗin da Jalal ya koya mata bayan ta gama ta kallesa sai kuma ta kalli basket ɗin dake kusa da ita,sai lokacin taji wata yunwa tana kawo mata farmaki,cire hiramin tayi tare da lankwasa ƙafafuwan ta,jawo basket ɗin tayi warmer ɗin farko taga soyayyan dan kalin turawa sai biyar ƙwai shi kawai ta zuba a plate ta fara ci tunda ta fara buɗe basket ɗin tsorawa bakinta ido yay ganin yadda take tauna abincin kamar bata so,komai a nutse ta keyi ta ƙara ƙyau tayi fresh girmanta ya ƙara fitowa, ajjiyar zuciya ya sauke yana ƙara ware manyan idanunsa a kanta a haka har ta gama ci ta fara neman ruwan sha, ɗago kai tayi da sauri ta rufe idanunta tare da dafe ƙirjinta,juya idanunsa yayi har sai da ta ɗan ƙware sbd wani ƙyau da yayi mata a ido,da hannu yay mata alama da fridge a hankali ta miƙe jiki a sanyaye ta nufi fridge ta ɗauki gorar ruwa mai sanyi ta sha,tana gama ta mayar da raguwar ciki,kanta a ƙasa ta ƙara so wajan sa,shima kallonta kawai yayi bai magana ba,turo baki tayi tai marai-raice fuska tace “toka matsa mana bacci zanyi” ɗauke idanunsa yayi yace “a ina zaki baccin?” Bata ce komai ba ta haye saman bed ɗin tare da kwanciya kanta ta ɗura a hannunsa kafin ta zagaye jikinsa a hannunta baice mata komai sai rufe idanunsa da yayi yana nan har yaji saukar numfashinta alamar tai bacci,ware idanunsa yayi ya sauke a fuskarta sosai take bacci cike da nutsuwa zameta yay daga jikinsa kana ya ƙaro gudun a.c sannan ya juya mata baya a haka shima yay bacci bakinsa ɗauke da azkar..INEC a can hukumar zaɓe sun daɗe da fara irga ƙuri’u dukkan wasu magoya bayan sauran ƙungiyoyin suna nan kowa yana jiran tsammani,yayinda ɓangaren jam’iyyar D.R.P Jafar da Prince Hassan da wasu manyan kusan su ashirin suke jiran abinda zaije ya dawo, Ɓangaren P.D.R kuma Lamir ne da Hon Faisal Lawan da wasu bayan tare kuma da wasu ƴan daba ma’ana dai ƴan bangar siyasa hakama sauran jami’yo kowa da wanda suke jiran jin abinda zai faru,da tafiya tai ta fiya aka fara hangen masu nasara tuni jikin Lamir yay sanyi domin duk akwatin local government ɗin da aka irga Dr Muhammad Jalal Kabeer bobo shike da rinjaye,haka governor Mubarak Yahya cibo yayta kiran Lamir domin yaji meke faruwa abinda ya keji gske ne ko yaya?sbd tuni aka fara sakin result da dukkan local government ɗin da aka irga kuma yana ganin komai koda bai gani ba labari yana iske masa, Lamir ya “kance a’a babu komai ai mune da ruwan to rinjaye ka ƙaddara ma ka zama Governor a ƙaro ma biyu rantsuwa kawai ya rage maka”sosai Governor Mubarak Yahya cibo yake jin daɗi kuma ya ƙara tabbatar masa da maganar boka Saƙib gsky ne daman ya riga ya gama yi masa alƙawarin shine da nasara ba wani ba, lokacin daya rage saura local government biyu a gama irga ƙuri’u sai hankalin sauran jami’yo suka tashi har akaso data rigima domin wasu har shirin sace akwati sukai amma da yake aƙwai ƙyakkyawan tsaro yasa aka kuri masu haddasa rigimar, ƙarfe 2:00 dai-dai shugaban inec RETURNING OFFICER ya fara faɗar sakamako tun daga sama har ƙasa inda aka fara da jam’iyyar P.D.R jam’iyyar Mubarak Yahya cibo kenan suna da ƙuri’u 6.35,165m sai jam’iyar C.C.P da ƙuri’a 4.12,24m sai kuma jam’iyyar P.P.C da ƙuri’a 3,11,12m”shiru RETURNING OFFICER ɗin yay yana ɗan kallon takardun gabansa a yayinda kuma zai faɗi jam’iyya mafi rinjaye,sai kuma yay Murmushi kana ya saita speaker a dai-dai bakinsa, Jafar kam miƙewa yay tsaye yama rasa me zai yi sai zirga-zirga yake a tsakiyar jama’a  kamar daga sama babu zato babu tsammani yaji RETURNING OFFICER ɗin yace “Jam’iyyar P.D.R tana da ƙuri’u ɗai² har 20.88,159m jam’iyya kenan mafi rinjaye….
Kamar a mafarki haka Jafar yaji saukar maganar RETURNING OFFICER ɗin da gaske Jalal shikenan ya zama Governor na?what a wonderful news,hakan na nufin burin Jalal ya cika muradinsa da mafarkinsa duk sun cika ya rabbi ya zujalalu wal ikram, Allah gafurur rahimu shine maiyin komai a duk sanya yazo,duk yadda magauta so kaso daƙusar dashi Allah bai yi yau gashi Ubangiji ya dubi maraicin Jalal da kuma buƙatarsa ya amsa masa addu’ar sa yau Jalal shine zai mulki dubban jama’a shine zai zamo jagora Allah kenan maiyin komai a duk sanda yaso,ansha wahala rai ya ɓaci zuƙata son a zabtu har an rasa rai,gaba ɗaya wajan ya hargitse maguya bayan Jalal sai ihu suke tare da murna suna watsa kuɗi sama,su Lamir kowa tuni suka bar wajan domin a wannan lokacin basu damar cewa basu yadda ba domin komai a tsare aka yi shi sosai bambanci ya bai yana a fili tsakaninsu da Jalal,tun kafin su bar wajan su Imran suka fara kiran Jafar domin su tabbatar da abinda ake faɗa gasky ne ko kuma a’a,cikin dry da farin ciki idanunsa na zubar da hawayen murna yake shaida masu abinda yake faruwa,tun kafin ya gama faɗa suke ihu tare da katse kiran,duk da halin jimami ake na mutuwar Mummy amma hakan bai hana jama’ar gida murna ba musamman Abbou yana ji kamar an rage masa zafi da kuma raɗaɗin abinda yake damunsa,tun a daran labari ya gama yaɗa ko ina ta gidan redio t.v media cewa Dr Muhammad Jalal Kabeer bobo ya samu nasarar cinye zaɓen daya gudana a Yau kowa ya samu labari murna yake tare da sanya Jalal albarka,shikam yana can bai son abinda yake faruwa ba sai bacci yake cikin kwanciyar hankali.
Washegari bayan yay sallar asuba ya tashi Jalilerh tayi sai bai ƙara komawa bacci ba sai wajan 6na safe ya koma bacci a saman Daddumar daya shimfiɗa, yanzu ma yana ƙwance yana bacci can cikin baccinsa ya fara jiyo surutai sama-sama idanunsa yaja ya ƙara rufewa sbd yadda yaji idon yay masa nauyi kamar bai bacci ko kuma dai baccin ne bai ishesa ba, ɗan tsaki yaja kaɗan jin surutan suna ƙara cika masa kunne,ware gajiyayyun idanunsa yayi nan idanunsa ya sauka akan agogon bangon dake maƙale jikin room ɗin asibitin,11:20 salati yay tare da addu’ar tashi daga bacci,kamar ace ya juya nan yaga ashe mutane ne cike room ɗin a hankali ya dinga kallon mutanan ɗaya bayan ɗaya kamar wanda bai san so ba, Irfan Imran Aryan sai Jafar kuma Prince Hassan,sai kuma Nihila wacce ta biyo Aryan tace ita ba zata iya zama gidan ba gani take kamar za taga Mummy,a hankali kuma ya sauke idanunsa akan Jalilerh wacce har yanzu take bacci ɗan ɓata rai yay ganin gaba ɗaya jallabiyar sa data saka ta tattare zuwa cinyarta gaba ɗaya santala santalan cinyoyinta sun bai yana, miƙewa yay ba tare kuma daya ƙara kallo kowa ba a cikinsu,fuska haɗe ya ƙarasa gaban gadon yana zuwa yaja duvet ɗin dake jikin gadon jikin gadon ya rufe mata jiki dashi,kamar ya tashe ta sai ta buɗe idanunta tana kallonsa kafin ta kwaɓe fuska tace “Uncle…” Haɗe rai yayi sai kuma ya juya mata fararan idanunsa hakan yasa ta juya da sauri ta ɗan ware nata idon ganin mutane a ɗakin sai kuma ta juya ta kalli Jalal taga harya shige cikin bathroom, Jalal na shiga bathroom ya sakarwa kansa shower ya wanke jikinsa tass,haka ya lalace taka kallon halittar jikinsa data ƙara girma tsayi kauri fiye da jiya mmki fal ransa ya kuma ƙudurci zuwa wajan likita domin ya duba lafiyarsa, Murmushi mai sauti Aryan yay murya can ƙasa ya kalli Jalilerh yace “Hubby…kin tashi lfy?” Turi baki tai gama bata ce komai ba,satar kallon jama’ar ɗakin yay yaga babu wanda yake kallonsa kowa da abinda yake hannunta ya kama yace “nai missed naki Hubby,kinji zcyata kowa?”nan ma shiru tai bata tanka sa ba sai hannunta data zame,saita Murya yay yace “Please talk to me Hubby,nine fa?”kallonsa tai sai kawai tace “ykk?” Sosai yay mamakin irin gaisuwar da tayi masa,shifa dukkan wanda yace masa ykk sai yaga kamar gaisuwar wulaƙanci ce,basarwa kawai yay yace “ya jikin naki?”bata kallesa ba tace “naji sauƙi”jinjina kai kawai yayi yana binta da wani kallo shi kaɗai yasan son da yake mata har zcyarsa shi kansa mmkin yadda kullum sonta yake ƙara daɗuwa a cikin zcyarsa,shima ya gaji da zarar komai ya lafa zaikai mgnarta auran wajan Abbou domin a sama masa mafita, Irfan ne ya miƙe tsaye tare da ɗaukan ledar hannunsa knowking yay bakin ƙofar yana nan tsaye har Jalal ya buɗe masa ƙofar ledar hannunsa ya miƙa masa sannan ya juya, Nihila dai kallo guda kawai taiwa Jalilerh ta ɗauke kai ta ƙwanta jikin Imran ba tare da tace komai ba,ita kam Jalilerh gaba ɗaya bata san da zaman Nihila sbd ba kowa ta kalla a room ɗin ba,tana nan zaune bata ƙara sauraran maganar da Aryan yake faɗa ba,yana ta dai mata surutai shi ɗaya, Jalal ne ya turo ƙofar a hankali ya fito gaba ɗaya suka bisa da ido banda Jalilerh wacce ta sunkuyar da kanta ƙasa sbd faɗuwar da gabanta yayi,sanye yake cikin comper mai ruwan Brown ɗinkin riga da wando rigar irin half ɗin nan ce sai gajeren hannu shima half ya murza wula black mai gashi-gashi kwantaccen gashin dake ƙwance saman wuyansa ya ƙwanta luff ƙasan hular wajan wuyansa,sai takalmi shima covert shoe baƙi ya ɗaura agogon warist a hannunsa sai zabga ƙamshi yake,gaba ɗaya ƙamshin sa ya cika parlour’n, ajjiyar zuciya Nihila ta sauke lokacin data gama ƙare masa kallo, idanunta taja ta lumshe tana ƙara jin ƙamshin parfume ɗinsa ya cika mata hanci, Jalilerh miƙewa tayi a sanyaye zata shige bathroom kanta a ƙasa take tafiya har tazo Daf dashi Murya can ƙasa wacce ita kaɗai za ta ji abinda yace “kada ki wanka,gida zamu”da sauri ta ɗaga kai ta kallesa taga harya yayi gaba idanunta ta sauke a ƙasa tana mmkin mai yasa zai hanata wanka bayan shi yayi,turo baki tayi tana jin idanunta na kawo ruwa, Imran ne yace “mrng Yaya” bai kallesa ba yace “ykk?” Aryan ne murya ciki ciki yace “Mrng” bai tanka sa ba bawai dan baiji ba yadai masa banza ne,dry Irfan yay yace “Barka da safiya Yaya ya ƙarfin jiki?”kansa a ƙasa yana ƙoƙarin duba wayoyinsa yace “Allhamdulillah”yana yana nan tsaye Jafar yazo da sauri ya rungome sa ɗan waro idanunsa Jalal yay tare da juyawa kwaɓe fuska yay ganin Jafar,cikin dry Jafar yace “congratulations your excellence, Allah ya amshi addu’ar mu, Ubangiji ya kalli ƙyakkyawar zcyarka,hukumar INEC sun tabbatar da kai matsayin Governor Ibadan” lumshe idanu Jalal yay yana jin wani sanyi na ratsa zcyarsa,cikin ransa ya kewa Allah tasbihi,kafin ya ware manyan gajiyayyun idanunsa cikin wata daddaɗar muryarsa yace “Allahamdulillah bira hamatika, Allahamdulillah rabbi allamin,masha Allahu laƙuwata illah billahil aniyar aziiim” ya faɗa yana ɗan matse ƙafaɗar Jafar, Murmushi kawai Jafar yay yana cije lips kafin yace “congratulations Buddy” jinjina kai kawai yay  kafin can ya sauke tagwayen ajjiyar zuciya yace “thank you so much Buddy”Jafar yace “it’s my pleasure ur excellence” hararsa Jalal yay bai ƙara cewa komai ba, Prince Hassan ne ya matsu kusa da Jalal ya zube ƙasa yace “Mrng ur excellence and congratulations to you” sai lokacin Jalal ya kalli Prince Hassan yace “thank you bro,tnx once again” prince Hassan yace “haba² ka cancanci fiye da haka komai mukai maka bamu faɗi ba,kuma wahalarmu mai tashi banza ba munyi winning” jinjina kai kawai yayi bai ce komai ba, Irfan ne yace “Yaya Dr ya sallamu yanzu haka Abbou ya turo mu ɗauke ka” “ok” Jalal yace hakan yasa Irfan ya fita a ɗakin Prince Hassan ya mara masa baya sai Imran shidai yana tsaye yana son yaga duk sun fita,yana nan tsaye har Aryan ya fita sai kuma Jafar bayan ya gama kallon Nihila wacce take zaune, ajjiyar zuciya ya sauke kafin a hankali ya taka zuwa inda nake tsaye yana zuwa yasa hannu ya murɗe kune nan Jalilerh kukan shagwaɓa tasa tana buga ƙafa bai kulata ba ya ɗauki hiraminsa ya ɗaura mata saman kansa sannan ya bata bedroom slippers tasa,kafin yace “Let’s go” gaba tayi yabi bayanta da kallo yadda yaga hips ɗinta yana juyawa ta cikin jallabiyar,baki ya taɓe sai da ta fita sannan ya kalli inda Nihila take zaune haɗe rai yay yace “kee zonan”hawayen da take ɓoyewa ne suka fara zubuwa saman fuskarta,abu guda ya cika ZCY ga rashin Mummynta gashi yaƙi kulata sai ta Jalilerh yake wacce bai ma haɗa komai da itama gashi ita ya shareta.
  _UNCLE NE  littafin kuɗi ne,dan Allah masu fitar min dashi ko daina kunji, And Duk mace mai class bata jiran kayan sata 😂 ƙoƙari take ta mallaki na kanta yanzu yaya zamuyi daku?littafi 300 kawai kuke ƙyashin biya,bayan kuna enjoying labarina what kind of son ZCY? Ni kuma gashi na daina free book,than littafi na gaba 500 nasan baku taɓa karanta labarin da aka sauya star ɗin fuska ba,baƙu taɓa karanta labarin mafarauci ba😂 whatever dan Allah pay before you read just 300 kunji 600 for vip asusun biya 0116886423 sulaiman Naima s union bank evidence of payment 08119237616 thank you Habibaties 🥰_
Ƙarasawa yayi kusa da ita tare da leƙa fuskarta yace “what wrong?”jikinsa ta faɗa ta saki kuka,cikin kukanta ta fara faɗin “Bobo Mummy bata tare dani, Mummy ta tafi ta barni, Bobo da gaske shikenan Ni shagiya sunana?meyasa aka zaɓi zaɓi samar dani ta wannan hanyar?na shiga uku bobo yaya zan yi?rana zafi inuwa ƙuna,mai yasa Mummy za tace Abban Nusaibat shine mahaifina?mai makon tace Abbou ne?shikenan na daina amsa sunan Nihila Kabeer bobo? Bobo ina jin inama nina mutu ba Mummy inama…,”da sauri yasa hannu ya rufe mata baki idanunsa yar sun kaɗa sunyi jaaa,kasa ce mata komai yay sai rungome ta yayi a jikinsa suka sauke ajjiyar zcya a tare..Cikin Wata iriyar murya Jalal yace “shiiit…stop it okay” kaita ɗaga sai kuma ta sauke idanunta daga kallonsa bai ce mata komai ba,ya zare ta daga jikinsa tare da faɗin “let’s go” gaba tayi yana binta a baya lokacin da suka bar ward ɗin suka tarar har sun shiga mota, Jalilerh ya gani zaune gaban motar Aryan suna haɗa ido ya maka mata harara da sauri ta janye nata idanun tana kwaɓe fuska kamar zatai kuka, Jafar ne ya buɗe masa back seat ya zauna itama Nihila ta shiga ciki ta zauna, Jafar kuma ya shiga mazaunin driver, Irfan ya shiga tasa motar Imran ya zauna gaba kasan cewar baizo da motarsa ba, prince Hassan kuma ga zauna baya,motar Irfan ce ta fara tafiya sai ta su Jalal sai kuma Aryan shida Jalilerh a baya,a haka suka jera a tare suka ɗauki hanyar zuwa gida, Jalilerh haka kawai taji wani kuka ya kwace mata tasa kanta a tsakanin cinyoyinta ta dinga rera kuka sai da tayi mai isar ta tai shiru ta shiga sauke ajjiyar zcy, Aryan ne ya kalleta yace “wannan kukan na mene haka hubby?” Cikin Muryar kuka tace “ba shi bane ya harare ni”waro idanu waje yay yace “shi wa?” Turi baki tai tana sauke ajjiyar zcy kafin tace “Uncle mana” shiru yay yana jin zucyarsa nayi masa zafi kafin ya kalleta yace “to meye na damuwa tunda bani na harareki ba?just forget about him hubby”yana faɗin hakan ya juya kan motarsa ya saki hanyar da zata kaisu gida, kallonsa kawai tai ba tace komai ba.gaba ɗaya motocin sukai parking a parking space, suna parking wasu manyan securities suka ƙarasu wajan motar Jalal da sauri wani ya buɗe back seat, lumshe idanunsa yay yana fesar da wata iska daga cikin bakinsa kafin a hankali ya ajjiye jaridar daily trust ɗin da yake karantawa wacce kusan rabin ta duk photonan sa ne da kuma bayanan yadda zaɓe ya gabata,kallon Nihila yay harya buɗe baki zai magana sai kuma yaga Jafar ya ƙara so wajan seat ɗinta ya buɗe ƙofar yana mata magana a hankali, ɗan cije lips ɗinsa kawai yay kafin ya sakko da fararan ƙafarsa zuwa wajan motar,yana gama fitowa gabansa ya yanke ya faɗi,sauri dafe ƙirjinsa yay yana ambaton Allah a jere,kafin securities ɗin su dawo bayansa riƙe da guns manya,a hankali ya fara tafiya cikin nutsuwa kamala haiba da kuma jarumta,kana ganinsa kaga cikakken namiji mai taƙama da dukkan baiwar da Allah ya bashi,duk da cewa ya rame amma har yanzu yana nan tunbinsa ya ƙara ɗagawa ya ƙara faɗin daga saman ƙirjinsa,ga sajensa daya ƙara yawa da tsayi sunyi ƙwance lufff, hannayensa ya zura cikin aljihu ya fara tafiya tsayawa yay sbd abin yaji Imran ya faɗa, Irfan ne yace “to Allah ya sadai lfy,naga tare muka taho dashi”Imran yace “eh,but shine a baya kuma daman tun a hanya na fahimci kamar motar babu lfy sbd yadda motar take tafiya a hankali”Irfan yace “ok!bari mu shiga ciki sai mu kirasa muji,Wlh yunwa na keji gaba ɗaya murna tasa ko tea ban sha ba”dry Imran yay yace “haka dai,na fahimci kafi kowa ci” gaba ɗaya sukai gaba,babu kowa a compound ɗin sbd Abbou yace bai son taran zaman makokin nan,wanda duk yawancin sa gulma ce ɗai-ɗai ne masu zaman Allah,duk wanda yazo masa ta’aziyya, Jalal tuni ya shiga cikin gida bayan ya gama jin abinda suke faɗa amma har ƙasan zcyrsa yasan ba haka kawai aryay yaƙi tawowa ba,gaba ɗaya securities ɗin suka tsaya a bakin ƙofar gidan wasu a compound wasu kuma a chan bakin gate, Jafar gyara tsaiwa yay yace “baby dukkan mai rai ai mamaci ne,kuma kowa da sanadin mutuwar sa,yanzu kukan na kike na tabbatar yana baƙantawa Mummy rai,abu guda zaki ki sama mata nutsuwa da kwanciyar hankali shine addu’a, addu’ar ki kawai take buƙata” shiru tai tana goge hawayen fuskarta matsuwa yay kusa da ita tare dasa hannunsa ya tallafo haɓarta yace “when Zaki last paper naki?,i mean exam ɗin ƙarshen semester na final school ɗin ki” kallonsa tai yay saurin janye idanunsa sai kuma tai Murmushi tace “Nan da 2weeks in sha Allah i will be graduate” Murmushi yay mai sauti yace “ehyee kace na kusa angwancewa,to Allah ya kaimu” gabanta ne ya faɗi sbd gaba ɗaya ta manta cewa jiranta yake tai final exam ai maganar aura su,ga kuma maganarta da Bobo shin ta gaya masa ne ko ta bari yaji a bakinsu Abbou? Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un yanzu me zatai kenan, Jafar zai fahimce ko bazai ba,zai gane cewa babu kaifin wasiyyar Mummy ce hakan,shirun da tayi yasa ya fahimci aƙwai wani abu,sama ya kalla yaga garin yana sauyawa alamar hadari sai ya dawo da kallonsa yace “what wrong?” Murmushi kawai tayi tace “a’a babu” yace “okey! Let’s go inside” a jere suka shiga cikin gidan suna shiga main parlour suka samu Jalal tsugune gaban Abbou ya ɗura kansa a cinyar Abbou yana sauke ajjiyar zcy shi kuma Abbou yana ta bubbuga bayansa,waje ya samu ya zauna yana faɗin “Mameey sannu da gida”Mameey tace “yawwa son ya ƙoƙari muna fa gdy Allah ya saka da alkairi” Murmushi yay yace “it’s my pleasure” kafin yace “ya ƙarin hqr?”tace “Allahamdulillah,Mamanka bata daɗe da tafiya ba,amma tace zata dawo”jinjina kai kawai yay, Abbou cikin raɗa yace “haba gwarzo na,mene na kuka kuma bayan ka samu abinda kake buƙata,kardai ka sauya daga jarumi da kake zuwa wani daban,ko wani kakeso yaga hawayenka yaga rauninka?”da sauri ya girgiza kai yana ƙara tura kansa tsakanin cinyoyin Abbou kana ya shiga goge idanunsa ta yadda babu wanda zai san kuka yay, ɗan Murmushi kawai Abbou yay shi kansa dauriya kawai yake amma rasuwar Mummy ta girgiza sa sosai,tashi Jalal yay yana haɗe ransa kafin ya langwaɓar dakai yace “my phone” miƙewa Abbou yay yace “ok jeka kai breakfast,amma ina Aryan da Jalilerh ne?”Irfan dake nufar danning Area yace “Wlh Abbou masu san inda yay ba,kuma suna tare da Jalilerh”kallon Irfan yay kafin yace “shirme kenan” yana faɗin hakan yay upstairs abunsa Jalal kuma part ɗinsa ya huce ba tare daya ƙara kallon kowa ba, Nihila ma upstairs tayi tana jin zaman parlour’n babu daɗi, Abbou na shiga part ɗinsa ya ɗauki wayarsa ya shiga dailing number Aryan, lokacin Aryan yana cikin wani park zaune saman kujera sai Jalilerh wacce take zaune gabansa,wacce masa mitar gida zata, ajjiye fork ɗin hannunsa yay yace “yau soyayya za muyi,kinga soon za’ai auranmu” ita dai bata kulasa ba, ko kaɗan ta kasa cin cips ɗin da yake gabanta,ana kiran Abbou ya shigo yana kallo yaƙi picking har sai da akai kira wajan uku sanan yay picking cikin faɗa Abbou yace “where are you Aryan?” Aryan yace “Abbou motana ya samu matsala amma yanzo zan tawo gyarawa ake” Abbou yace “ka da ka sake ka ƙara 10minutes a waje ko mata gyaro ba ka hau napep,kaje ka ɗauki yarinya bayan kasan cewa bata da lafiya”yana faɗin haka yay rejecting call ɗin, Murmushi kawai Aryan yay yana maida hankali sa kan Jalilerh.
   _UNCLE NE littafin kuɗi ne akan farashin 300 vip 600 dan Allah kuyi payment kafin ka karanta min book,ina da free books da yawa idan shi kake buƙata,amma wannan na kuɗi ne tun kafin a fara koka san da haka,😂😂 Wlh Anty indai baki biya ba to ke ba babbar kai bace tunda kike jiran abin sata duk wanda yay biya na zai biya ta wannan asusun 0116886423 sulaiman Naima s union bank evidence of payment 08119237616_
Gaba ɗaya suka haɗu saman daining sbd gaba ɗaya ɗayansu babu wanda yay breakfast,baka jin komai sai ƙarar spoon,fork, and knives, Mameey tuni ta koma ɓangaren masu zuwa gaisuwa tana zuwa ta samu Mama zaune tana jan casbawa sai kuma Hajiya Atine mahaifiyar Nusaibat da kuma wasu mata da suka zo daga maƙota,itama dai Mameey danginta suna hanya gasancewar ba ƴar nan bace ita can cameron county take da zama shiya ba koda yaushe familynta suke zuwa ba, wayoyin Jalal Abbou ya kwasa ya nufi side ɗin samarin yaran nasa yana zuwa ya shiga part ɗin Jalal, ƙwance ya samesa saman 3seater daga shi sai 3gauter da farar singlet wacce ta kamasa ya ƙure a.c sam baya iya zama babu sanyi ya sama da Paris su da kullum suke cikin yayyafin ƙanƙara, idanunsa a lumshe kamar mai bacci ganin yana bacci yasa Abbou ajjiye masa wayoyinsa a kusa dashi kana ya gyara masa ƙafarsa data lanƙwashe,samun kansa yay da shiga bedroom ɗin Jalal yana shiga ya dinga bin ko ina da kallo,har idanunsa ya tsaya akan photon Jalilerh wanda ya manna,cikin ransa yake faɗin “yanzu lokacin yayi da gaba ɗaya zaku hqr da juna, Jalal ya zauna da Nihila da kuma wacce na aura masa, Aryan ya zauna da Jalilerh matsayin matarsa, Jafar kuma zan masa bayanin komai yadda zai fahimta daga nan ya nemo wata,su Irfan ma duk su nemo mata a haɗa ai auran lokaci guda kowa ya huta”da wanan tunanin yasa hannu ya cire photon Jalilerh ya saka cikin aljihun wandonsa kana ya fice daga ɗakin,yana fita Jalal ya buɗe idanunsa yabi bayan Abbou da kallo,wyarsa ya ɗauka na yaga kira sama da 50 hadda hukumar INEC da kuma gidan gwamnati sai kuma different numbers sai kuma DM shima babu a dadi, wani message ya gani kai tsaye ya shiga ciki yana shiga ya fara karantawa kamar haka _Assalamu alaika ur excellence hukumar INEC na tayaka murna da samun damar dakai na zama Gwamnan jihar Ibadan congratulations once again yallaɓai, za’a rantsar dakai a ranar 29 ga wanann watan kafin nan kana da meeting a gidan gwamnati by tomorrow morning I have a nice day sir_
       _~from~ RETURNING OFFICER_
Yana gama karantawa ya saki wani lafiyayyan murmushi wanda ya sanya dimples ɗinsa suka loma,gadai mulki ya samu kamar yadda yake buƙata kuma yadda yake cikin burinsa amma mai yasa baya cikin farin ciki ne gaba ɗaya? Mai yasa ya keji gabansa na faɗuwa? Mai yasa zucyarsa take ciki da zullumi da kuma faɗuwar?” Runtsa idanunsa yay yana ƙara jin ransa nai masa suya ƙirjinsa ya kalla nan yaga sunan raɗau kamar yadda yake ko yashe yankan na warkewa sunan na ƙara fitowa,shafar sunan yay kana ya lumshe idanunsa tunawa da Aryan da yay yasa yaja tsaki,wani DM ɗin ne ya ƙara shigowa wannan kuma na ta’aziyya ne da ake ta turo masa tun jiya, lumshe idanunsa yay babu jimawa bacci ya ɗauke sa yama manta da Lokaci domin time ɗin sallar zuhur ya kusa haka ya fara bacci wanda yinsa kawai yake ba dan daɗi ba,Aryan bai dawo da Jalilerh gida ba sai wajan asr prayer wasu masjid ɗin ma alrdy sun idar, parking yay a harabar gidan yana parking ya hangi Alhaji khamal tsaye yana latsa waya, fitowa yay daga cikin motar itama Jalilerh ta fito tana lumshe idanu sbd baccin da ta keji ga jikinta babu daɗi rabonta da wanka tun jiyan,ga wata yunwa dake damunta,bata tsaya sauraran maganar Aryan wacce yake cewa “kada ki faɗawa ko ina mukaji, kawai motarmu ya samu matsala”bata kulasa ba ta shige gida,babu kowa a main parlour da sauri da haura upstairs, Aryan ya nufi ciki da sauri Alhaji khamal ya tsayar dashi yana tsaya yace “ina wuni?” Yace “lfy, Allhamdulillah kiramin Abbou’nnaka” Aryan yace “ok” ciki ya shiga yana shiga ya nufi upstairs,sakin labulan window’n Jalal yay ta saman upstairs bayan ya gama ganin shigowar su cikin gida, dwonstrais ya nufa a hanya yaci karo da Jalilerh bai ko kallo inda take ba ya shige ta tsaye tana kallonsa,haka Aryan ma,yana sauka  ya nufi lambun gidan wata farar kujera yaja kusa da ƙaramar dake wakana a wajan,shiru yay tare da tsorawa ruwan dake gabansa idanu,bai taɓa sanin nada daɗi ba sai yau,da Mummy na nan bazai taɓa kawowa iyanzu bai kai komai cikinsa ba, baya yay tare da kwanciya jikinsa kujerar yana fesar da numfashi, shi Mulkin nan tun ba’a je ko ina ba ya fara damunsa kira kota ina tun kafin ma ya fara shiga office,a hankali Aryan ya tura ƙofar ɗakin tare dayin sallama cikin zcy Abbou ya amsa,yana zaune saman duguwar kujera yana operating system sai coffee dake gabansa dan ya kasa kai komai cikinsa, Aryan ne ya zube gabansa yace “am so sorry Abbou Wlh….,? Dagatar dashi Abbou yay yace “idan wanan ya kawo ka get out of my room,ka riga ka nuna ban isa da kai ba” girgiza kai Aryan yay yace “Wlh Abbou..,”tsawa ya daka masa tace “nace idan wannan maganar ya kawoka ka fice min daga nan tun ranka mai ɓaci Aryan” tsoro yaji sbd Abbou bai taɓa matsa tsawa irin wanann ba miƙewa yay har yaje ƙofa sai kuma ya tsaya yace “Abban Nusaibat na kiraka a compound” yana faɗin haka ya fita waje yana jin ransa babu daɗi, miƙewa Abbou yay ko coffee ya kasa sha,dake a shirye yake tsaf wayarsa kawai ya ɗauka yay waje,yana sauka dwonstrais ya haɗu da Mameey hannunta riƙe da babban tray zatai waje kallonta yay yace “sai ina?” Tace “lambu wajan Bobo tun da suka dawo bai ci komai ba” da sauri ya kalleta sai kuma kawai ya ɗauke kansa ya nufi wajen shima,gaisawa sukai da Alhaji khamal,numfasawa Alhaji khamal yay yace “ni mai laifi ne gareka Alhaji Kabeeru ban san da yaushe na aikata hakan ba,ban san kuma sanda zai daina baka hqr da nai manyan ya fiyarka,dan Allah Alhaji Kabeeru kayi….,”cikin takaici da kuma zallar damuwa ya kalli Alhaji khamal sai kuma ya saki Murmushi yana gyara tsaiwa kafin ya sanya idanunsa cikin na Alhaji khamal yace…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *