UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 12 BY SHATU

UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 12 BY SHATU

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

Saboda yamma tayi, Albi Kuma yace na kwana haka muka koma gidan ta muka daura sabuwar Hira. Ranar munyi hirar yaushe gamo ga mijinta baya nan se abin ya Kara Mana lokaci. Washegari da wurwuri na tashi na gyara Mata gidan sannan na fara Shirin tafiya, lokacin d ta tashi a bacci na Gama komai hatta breakfast, ta zauna tace+

” Ke Sofy Wai da wurwuri Zaki tafi haka?”

Na Dan Harare ta nace

” To kwana Zan Kara Yi?”

Ta girgiza Kai tace

” Ina ce Albinki yace zai zo ku tafi tare”

Na girgiza kaina nace

” No min fasa wannan, Bari kiga”

Na Mike na hada tea na fara Sha

” Sofy yaushe za kice Masa ya tura ne”

” Lokacin daya shirya, nikam ai banida option Kuma”

Se ta gyara zaman ta tace

” Se Naga kamar Baki murna da tarayyar ku, se Naga Baki dokin shi kamar Bai dameki ba ma”

Nayi dariya nace

” Eh hakane, bansan dalili ba Amma bana jin irin wannan farin cikin ko kuma doki akan shi, how can I possibly do that? He’s nothing near what I want, kawai dai Allah ya kaddara ne Babu abinda Zan iyayi”

” Sofy har yanzun kinada chance idan kina ganin Baki son Usman don’t force yourself saboda kaucewa wani abu, beside har yanzun bakiyi girma ace bakida miji ba”

Na gyada Kai na nace

” Ba wai bana son shi bane, ba Zaki gane yadda nake ji bane, I’m in a state of despair, komai ya fita a kaina Rays, kullum mafarkina rayuwa ta nida Jaafar, ban taba kawowa Zan rayu da wani bayan shi ba se gashi ya tafi…”

Se nayi shiru kawai saboda yadda naji Abu Yana tsaya min a makoshi, hannuna ta riko tace

” Dan Allah ki daina fadar hakan, Jaafar is already in the past, idan Kika cigaba da sakoshi hakan zai raunana Miki imanin ki, to every action of Allah akwai great wisdom da mu ba zamu fahimta ba se shi kadai, you can’t possibly question Allah akan abinda ya hukunta a rayuwar ki. Sofy kiyi hakuri ki karba koma menene Allah ya tsara Miki”

Har naje Gumel Ina tunanin maganganun ta, it really made sense ya kamata na hakura da Jaafar haka, idan na tuna shi addua kadai ta isheshi. Allah ya dauke shi a duniya saboda we were never meant to be.

Kamar yadda kowa zaiyi tunanin zamuyi soyayya sosae bamuyi ba ni da Usman, relationship dinmu is a bored relationship wani daga farko, wani lokacin se muyi sati bamuyi wayar minti uku ba, sede kullum zai kirani yaji yadda na tashi, Nima hakan Bai dameni ba. A hakan ya turo iyayen shi akai formal magana sannan aka saka Rana watanni bakwai zuwa lokacin na kusa final exams Dina, Ranar da ya kirani shi ne mukai kusan minti talatin Muna magana dashi, he kept complaining me yasa zaa saka wata bakwai1

” Kai Albi wata bakwai din fa kamar yau ne”

Se yayi tsaki yace

” Ba Zaki gane ba Gem, na jira da yawa fa”

” Bana son muyi aure Kuma Ina tafiya school, nafi son na Gama school I can dedicate myself to you”

Yayi murmushi yace

” Gem ke Kika fadar haka? To shikenan Allah ya kaimu lokacin”

Mun Jima muna tsara rayuwar mu ranar. Bayan nan na fahimci wani Hali da Usman yake dashi, shi mutum ne da baya nuna true feelings dinsa, duk yadda nake ganin I’m reserved to shi ya fini, halayensa suna da sanyi, Kuma Bai iya chasing Abu ba, akwai mutane da duk yadda suke son Abu they can’t chase it, wannan dalilin yasa lokacin da yake Bina na aureshi idan naki se ya kyaleni, idan ya Kara samun chance se ya dago da maganar idan naki se ya hakura, akwai ranar da ni na kirashi na dawo daga clinic, Bayan mun gaisa ya tambayeni ko naci abinci nace naci se muka fara Hira har nace mishi4

” Albi Ina son na tambayeka”

” Oya go on Ina jinki”

” Me yasa lokacin idan nace bazan aureka ba kake hakura baka kokarin tura kanka gur ina. Kasan Mata basa son irin haka”

Yayi dariya kadan yace

” Wallahi na sani Nima bansan me yasa nake haka ba, kawai dai hali nane, bawai zuciya nake ba Amma bana son takurawa mutum. Amma kinsan se inajin what if idan na rasa ki gaba daya Kuma, ba yadda zanyi ne”

Na gyada Kai nace

” Wannan halin naka Yana taba ego din Mata, yawanci min fi son a dinga binmu head and toes”

Yayi dariya yace

” To ai gashi Allah yayi, saboda I didn’t chase you Wai saboda bana sonki ba Aa kawai Ina ganin rayuwar ki ce, ke Zaki zaba yadda kike so”

Bayan wannan se wani halin shi Dana karanta Kuma, shi ba mutum bane Wanda yake bada time din shi, ni dashi muna speaking different love language, maimaikon mu dinga samun matsala ko nayi ta complain se na Bari akan ni Zan canja shi, Zan maida shi ya fara speaking yaren da nake fahimta. A wañnan watannin da Suka rage Mana se Dana tabbatar mun fara fahimtar junanmu.

Na tashi da safe na Gama dukkan abinda nake, na saka labcoat dita Dan zuwa clinic, wayata na Ciro na fara Kiran shi, kafin ta katse ya dauka

” Good morning!”

Yana murmushi ya amsa ni sannan na gaishe shi nace Masa

” Albi Zan tafi clinic na Kira na fada maka Kai min addua”

Ki a yanayin maganar shi nasan yaji dadi yace

” Allah ya bada saa ya tsare min ke, kiyi hankali da patient din ki Kar su cije ki”

Nayi dariya saboda na tuna na bashi labarin Kare ya kawo min cizo, daga haka mukai sallama yace min shima ya fita aiki. Can da Rana na Kara Kiran shi naji yadda yake,se ya zamana ni nake calling din. Seda nayi sati daya kullum duk abinda zanyi se na fada Masa shima zai fada min nashi, bayan sati se na daina Bai Kira ba shima se washegari very early daidai time din da nake fita ya kirani yace min zai fita, ni na fita nace Masa Ina dai kokarin fita, daga haka se ya zamana duk abinda zaiyi zai fada min, a kalla a Rana zamuyi waya kamar sau uku sannan muyi chatting. Abinda nake son mu gane there are things that you can change through action, ba wai se magana ba, a zauna baka Kirana, idan kana son Abu ba zaka ce side daya zai ta Kira ba, dukka ku biyu have to make effort to make it happen.

Haka muka cigaba da tafiya, relationship dinmu was slow and steady, ba irin me zafin nan bane, kafin wani lokaci na fara jin shi a cikin duniya ta, naji Babu yadda zaayi na hada soyayyar shi da ta wani, it’s a taboo wani ma ya kalleni yace Yana Sona. Tafiyar mu tayi nisa munata Shirin aure muna Kara fahimtar junan mu.

Usman Dan bafullatanin adamawa ne, iyaye da kankanni duk can suke Amma Kuma shi a Gombe aka haifesu. Mahaifiyar shi bakanuwa ce typical bahaushiya, shiyasa ba zaka kalle shi kallon farko kace shi fulani bane, sosae yake Kama da mahaifiyar shi. Mahaifin shi sun rabu da mahaifiyar shi tun Yana yaro, ya tashi a adamawa wajen kakar shi, dukka sauran Yan gidansu yan uba suke a gurin shi. Bayan ya Gama primary kakar ta rasu Dole aka dawo dashi wajen Babar su Anty yusra. Zaman dai Babu dadi ko kadan, haka a daddafe yake zaune Amma Yana zuwa Kano wajen mahaifiyar shi data riga tayi aure ta Tara nata iyalin. Kubra ita ce matar shi ta farko da aka Masa auren gata da ita, Dan lokacin daya aureta ko aiki Bai fara ba, baima Gama service ba. Tana da kirki kamar yadda Anty yusra ta fada min, dukda shi baya zancen ta, idan Muna magana baya kawo zancenta, Nima nafi son hakan. Yayi karatun shi na engineering a BUK. Yaran shi Afaf da Afreen.

Ba komai ke zuwa maka a matsayin pleasure ba, rayuwa gaba daya trial and test ce. A hanyar da kake tafiya zaka hadu da tudu da gangare, yau zaka ji dadi gobe zaayi akasin hakan, bazai zaman kullum yadda kake so haka ce zata kasance ba, wani lokacin ma abinda kafi ki shi Allah yake baka Dan ya gwada imanin ka, Dole kayi accepting whatever life throws at you and you cannot question Allah akan hukuncin shi.+

Nayi karatu na novels kala kala, romantic da genres kalakala, na karanta yadda ake samun pleasure a gidajen aure dukda ni nasan aure is not all about pleasure tunda Ammi ta Isa ta zame min misali akan hakan, Amma zuciya kullum tunani take tana hasaso Abu mai dadi, ban taba kawowa ba zanje da gaske in tarar da UWARGIDAN BAHAUSHE cikin gidan Usman Dikko tana jirana.

” Yusra! Yusra!! Yusra!!!”

Cikin sauri Anty yusra ta fito hannunta rike da babyn ta Dan kwana ashirin jin Kiran da mahaifiyar ta take Mata Babu ji Babu gani, ita tunanin ta wani abun ne yasa ta fito tana fadin

” Mama lafiya kike Kirana?’

Ta fada tana Zama kan kujerar dake facing wadda matar ke zaune, duk inda kake Neman mutum karami ka sameta to ka koma ka samu, ta dubi yusra tace

” Bazan kiraki ba seda wani dalili? Ke me nake ji kamar Hamman ku zaiyi aure?”

Anty yusra ta sauke ajiyar zuciya tace

” Kai Baki sani ba? To ai Banda an Kara sati uku da tuni Nanda sati biyu anyi”

Ta kankance idanu cikeda fada tace

” Ni meye amfanin zamana a gidannan kenan? Har ni zaa ware ko ni ba uwar shi bace ai dai na rike shi”

Anty yusra ta girgiza Kai tace

” Mama wallahi ki daina haka, kin manta Hamma yazo zau fada Miki Kika ki bashi fuska”

Ta tabe baki tace

” Ina ce dai ba yarinyar matsiyata zaije ya Kara dakkowa ba kamar yadda ya auro Kubra?”

Ita dai Anty yusra se ta fara breastfeeding babynta kawai ba tareda ta amsa ta ba, haushi ya Kara Kama Mama yace

” Banza Kika min kenan? Irin banida amsa ko? To Kin kyauta”

” Mama ni ta Ina Zan San matar shi Dan Allah? Kuma meye damuwar mu da wani kudi ko rashin shi, itada ba ita zata ciyar dashi ba . Kede kiyi addua kawai ta gari ce”

Mikewa Mama tayi tana fadin

” Ai ya kamata a bani girma a fada min, ko ban Haifa ba ai na rike. Kuma yarinya Yar arziki ai yafi bangirma ko ba komai kace kasan manyan mutane, da namiji da Allah Bai bani ba bawai baya Sona bane ba.”

Sanin halinta yasa Anty yusra Bata Kara ce Mata komai ba, Itafa Mama Bata taba haifar namiji ba, duka yaranta mata ne gaba daya. Shi kadai ne namiji, Amma idan kuka ji yadda take buri akan matar Dan ta zakiyi tunanin gobe zaa ce zata haifa namiji.

Ammi kullum maganar ta yadda bikina zai kasance, da yake ni ba mutum bace me high taste dinnan ba yasa ko siyayya idan zataje sede suje itada Anty Safara’u ko Anty Siyama kanwarta da Rayha. ko sun dawo sede na kalla kawai nace yayi. Bikin saura sati uku Gwoggo ta fara rashin lafiya Dole aka daga bikin, ga Kuma exams Dita da zanyi finals. Dan haka na Dan samu lokaci na nutsu na fara exams. Sati biyu na Gama exams Dita na Zama cikkakiyar vetenary doctor ko nace likitan dabobbi, kaf class din mu mu uku ne Mata, mukai applying Kuma ni kadai na Gama. A matukar gajiye Baba da Ammi suka sameni, Ina ganin Baba na tafi na rungume shi, ya shafa kaina tareda fadin

STORY CONTINUES BELOW

” Allah ya Sanya alkhairi ya kawo babban rabo”

Nayi mishi godiya sannan na koma gefen Ammi dake kallona da idanunta da suka haska saboda farin ciki, na kalle su yadda suke cikin farin ciki da kwanciyar hankali ban kawo cewar komai zai zama stable a kwana kusa ba. Kaduna muka wuce munata Hira ni Kuma na turawa Usman sakon na riga na wuce. Mental asylum din da Anty Rumasa’u take muka je muka dubata, tana nan jiya iyau ta Kare kamar kudin guziri, Amma dai Babu laifi jikin da sauki dukda nurses din sunyiwa Baba complain Bata complying a treatment din da ake bata. Ni kaina seda naji Babu dadi yanayin da na ganta. Bayan mun dauki hanyar Gumel Baba ya dubi Ammi da tayi shiru duk jikin ta yayi sanyi

” Madam ya akai ne?”

Se tayi Dan Jim kafin tace

“Akan maman Ayaan ne, baka ganin ya dace a gwada Yi Mata rukiya, se Naga kamar akwai tabin aljanu a abin”

Ya Dan buga steerer kadan yace

” Tohm Bari na sallama Sofy se na dawo kanta”

Ammi ta gyada kanta, Bayan mun koma gida gurin Gwoggo na fara zuwa Naga jikinta sannan na dawo gida, Ina fitowa a wanka Sega Kira a wayata na dauka dukda bansan me Kiran ba, yace min sako aka bashi daga Kano ya kawo min Yana Tasha, Aisara na Kira cousin Dina nace ya taimaka ya karbo min. Na koma na zauna Ina Wondering sakon meye. Seda aka kawo sannan na hangame Baki ganin Albi ne ya turon. Naji dadi sannan na kirashi na Masa godiya.

Gyaran jiki Kam Maman Farida ita tayi uwa tayi makarbiya wajen gyara ni, a hakan tukwici ne na gudun mawar ta daga group din Anty Takori, jarkoki na tsumi har seda na fara daina daga kiranta, Dan tace ita Bata Wasa da wannan maganar. Idan ku ganni zakiyi tunanin sake ni akai saboda yadda suka jikina ya canja, fata ta tayi wani irin kyau me daukar Ido, ko Ina na zauna na tashi se kamshi. Albi ma ya Zama very busy Dan haka Bai ma zo ba, sede waya akai akai wani lokacin har video call muke. Satin biki ya Kama Rayha har ta fini doki ta taho itada Little su Anisah na hutu, kullum suna cikin tsara yadda zasu Yi kwalliya. Nikam gaba daya jikina a sanyaye yake, na kalli Ammi nace

” Ammi fa and kusa sallah babba, Wai Dan Allah bazaa daga bikin se bayan sallah ba”

Tayimin wani kallo tace

” Idan kinyi sallar anan uwar me Zaki min”

Na danyi dariya nace

” Kai Ammi in samu Mana in Kara cin nama Mana”

Anty Safara’u dake hade min kayan da Zan saka cikin trolley ta dago ta kalleni tareda fadin

” Yadda zata ji dadin ce Masa ai mu muka Kara ba, yaji haushin mu”

Rayha dake ciccire sauran kayan daga kan kabbasa tana mikawa Anty Safara’u tace

” Haka zatace Albi Ammi tasa an daga bikin, tana Yi kamar Bata son shi Amma…”

Pillow na wurga Mata Ina kwabe fuska kamar zanyi kuka na Mike na wuce daki abuna, kamar jira yake Ina shiga wayata ta fara ringing, nayi murmushi na Kai hannuna na dauka nace cikin shagwaba

” Albi!”

” Ya akai amaryar Albi”

Na Kara kwanciya Ina jin kamar Zan narke saboda yadda muryar shi ke zagaya min jikina,

” Kuma bayan bikin da kwana goma zaayi babban sallah shikenan se anyi bikin”

Ya danyi dariya gently yace

” A daga bikin kenan saboda sallah? To me zakiyi idan an daga, har rago na saya Miki fa.”

Haka na dinga mishi shagwaba tun yana murmushi har yace min

” It’s affecting me walalhi, ki Bari Mana”

Se naji kunya ta Kama ni Kuma, muka fara Dan Hira. Ammi taga ruwan mutane sosae har Wanda Bata taba expecting zasu zo ba, anyi biki daidai Wanda zamu iya affording dukda ni bana son ma yawan hayaniya sosae. Kamu kadai akai da dare Bayan an watse zazzabi me zafin gaske ya rufeni, ga ciwon kai me azaba shima, na fito daga dakin mu na nufi na Ammi Amma ban same ta a ciki ba, haka na koma na kwanta, da asuba na farka da amai Wanda kakarin shi yasa Rayha da Widad Suka tashi, Babu shiri suka Kira Ammi tazo ta tsorata da yanayina aka Kira Baba. Allurai yayi min sannan na samu bacci me nauyin gaske ya dauke ni. Har aka Gama Shirin tafiya daurin aure bacci nake, Anty Safara’u ta Hana a tsaheni so har aka daura aure Sha daya da rabi na safe ban tashi ba. Usman tun safe yake nema na, Amma Bai sameni ba so har Suka iso Gumel din baya cikin nutsuwar shi, a gurin daurin auren ne yaga Yaya Fahad dama mun taba zuwa gidan dashi sun Kuma hadu, se ya tambaye shi ko zai Kira Rayha ya tambayi inda nake, duk taron mutanen seda ya Kira aka ce Masa Ina bacci sannan ya nutsu, har aka daura aure Suka taho gida gaida surukai ban tashi ba,ana cikin ihun da gudar shigowar shi da abokan shi na farka, ni daya ce cikin dakin se drop din da Bai karasa Shiga ba na diga a hankali, mikewa nayi na zauna Ina kallon agogon dake dakin Naga har Sha biyu ta wuce, Zama nayi Ina kokarin cire fluid din naji sassanyan kamshi ya Shiga hancina Wanda yasa na dago a hankali na dube shi a tsaye, yayi kyau ya gaji da yin kyau, yana cikin farar shadda dake maiko da kyalli tayi Masa kyau kan chocolate skin dinsa, idanun shi ya zuba min Wanda yasa naji duk na takura, kallon kaina nayi naga Ashe kayan bacci ne jikina, wata riga ce iya gwiwa, hannunta ya fado Wanda ya bayyana Rabin jikina a waje, ta kasa ta tattare hatta thighs Dina a exposed, bedsheets din na tukunkuno na lulluba dashi Ina tura bakina, ya karaso ya zauna gefena Bai jira komai ba ya hadani da jikin shi tareda hade bakinmu guri daya! O ya subhannallah ban mayi brush ba, Dan haka na dinga kokarin kwatar kaina yaki bani dama, Allah ya taimake ni se wayar shi ta fara ringing cikin aljihun babbar rigar shi, Dole ya sakeni nayi baya saboda yadda naji jiri, Dan guntun energy Dana samu ya tafi, Bai barni nayi baya ba ya rungume ni jikinshi, and I found myself crying childishly, ya tsura min idanuna dake lumshe sannan ya kwantar dani tareda Kama hannuna yace

” Fight this for me, Allah ya Baki lafiya. I love you wife!”

Daga haka ya fita, ai kamar jira suke ya fita Naeeyla ta shigo itada Rayha, ganin Ina goge hawayena yasa Rayha tayi dariya tace

” Iyeeeeeee, an fara kenan? To meye abin kukan kowacce mace da haka ta fara”

Ban kulata ba Dan kukan se ya tashi daga shagawaba ya koma na kukan barin gida da tuna Bature, familyn sa duka seda suka zo da gudunmawar su me yawa. Mama seda tayi kuka da ana kamani Kuma nasan shi ta tuna. Anty Safara’u ta min zaga zaga Dole na bar kuka aka shirya ni duk tunanina zaa Kara sati daya Amma a adren aka kaini Kano wajen mahaifiyar shi. Mata dattijuwar ta kirki, ta karbemu hannu bibbiyu dukda inata kuka ta saka aka kaini bedroom dinta, banma San Yan uwana sun juya ba, se Bayan maghrib sannan ta shigo ta saka nayi sallah tasa aka kawo min abinci Amma naki ci se kuka nake, Ina tuna yadda muka rabu da Ammi, tana kuka inayi su Anisah nayi.

Se Bayan sallar Isha sannan na hakura na daina kukan saboda Naga kaina ya fara ciwo, na Kuma San wannan kukan da nake bawai zai maidani gaban Ammi bane ba. Sister shi da suke Mama daya saata Aisha ta shigo lokacin na idar da sallar Isha Amma ban tashi akan praying mat din ba, ta zauna fuskarta dauke da murmushi tace+

” Anty Amarya kukan ne Bai isa haka ba?”

Na danyi kasa da kaina Ina jin jikina yayi zafi alamar zazzabin na son dawowa, tea ta hada min ta Miko min Babu musu na karba Dan yunwar nakeji seda na kusan shanyewa sannan na aje tare da janyo jakata na balla drugs Dina na sha, wayata dake gefena ta katse min tunani, na dauka cikin kasa kasa da murya na fara gaishe shi

” Mama tace min kinata kuka? Kiyi hakuri kinji, Zan shigo kafin kiyi bacci”

Na gyada Masa kaina sannan ya saka na dauki abincin Ina ci Yana min Hira har na gama na Sha ruwa. Ina aje wayar Mama ta shigo, har lokacin Ina zaune kan carpet, ta zauan gefen gado tace

” Zaki kwanta ko? Nasan kin gaji gashi da wuri zaku dauki hanya”

Na gyada kaina se ta min sallama Bayan ta bani directives akan na rage kayan jikina na kwanta, har nayi bacci Bai shigo ba, saboda yadda na gaji ko kwakwaran juyi banyi ba se asuba. Na fito daga bandaki Ina kokarin tada sallah se gata ta shigo sanye da hijab, na tsugunna Zan gaisheta ta dago ni tana murmushi hade da girgiza Kai

” Yi sallahr ki, se mu gaisa idan kin idar”

Ta juya ta fita nayi sallah a nutse, na Jima Ina adduar alkhairi cikin sabuwar rayuwar Dana shiga, nayiwa Ammi da Baba sannan mijina kafin na cire hijab na Shiga wanka, ban Jima ba na fito na shirya cikin wata exclusive wax me onion colour da coffee se Dan fari daya watsu a jiki. Tayi kyau atamfar dinkin zani da riga, wayata na dauka naga Ammi ta kirani haka Baba haka Albi shima, Baba na fara Kira sannan Ammi daga karshe Ina kokarin Kiran Albi se gashi yayi sallama ya shigo, dagowa nayi Ina kallon shi, ya shirya cikin shadda Ash me haske babbar riga da Yar ciki, fuskar shi Banda annuri Babu abinda take fitarwa, ya karaso inda nake nayi saurin matsawa nace

” Ina kwana”

Ya riko fuskata Yana kallona cikin eyeballs Dina yace

” Babu dadi, jiya na shigo kinyi bacci, I didn’t get to talk to you”

Nayi murmushi Bayan na janye fuskata kada Mama ta shigo nace

” Baka zo da wuri ba shiyasa, I was very tired”

Ya Dan Bata rai yace

” I never wanted you coming here, Mama ta dage Wai se kinzo, da tuni na Dade da Zama ango na kashe bakin man naki”

Na Harare shi Ina nufar kofa, yayi dariya ya biyo bayana Yana fadin

” Kinga abinda na fada Miki Ina magana kin tafi, ai Dole na daidaita ki”

Na tsaya cak, ban taba kawowa Yana da magana har haka ba, rungume ni yayi, lokaci daya muka saki ajiyar zuciya ya juyo Dani Ina kallon shi shima Yana kallona, bakin shi ya matso dashi daidai nawa, nayi saurin lumshe idanuna Ina jiran saukar tattausan lips dinsa kan nawa, Amma se naji shiru hakan yasa na bude idanuna, Yana tsaye se kallon fuskata yake wadda ta Zama very close to his, Yana ganin na bude idanuna ya saki dariya, na Bata fuska but dukda haka Murmushin Jim kunya so yake ya kwace min, hannuna na Kai na dake shi a kirjin shi, da sauri ya rike hannun Yana dariya yace

” Ashe you enjoyed na jiyan, to karki damu wannan naki ne”

Ya fada Yana nuna bakin nashi, knocking kofar akai ya dubeni yadda nayi saurin matsawa Ina kokarin daukar veil Dina,karasawa yayi ya bude kofar, mama ce tsaye ta harde hannayenta a kirji, da dukkan alamu Aiko shi tayi Bai bada sakon ba,

STORY CONTINUES BELOW

” Fita a dakinnan!”

Babu musu ya fita Yana Sosa keya tareda gyara zaman hular shi, kamar nayi dariya Amma na gimtse, na Bata Rai irin dama takura min yayi, ta karaso na tsugunna na gaishe ta tana murmushi ta Kama hannuna tace

” Maza tashi, ki saki jikin ki kinji, Kar ki kula wancan ce mishi nayi kizo kiyi breaking fast Amma shiru”

Na danyi murmushi nabi bayanta, shap shao naci toast Dina da tea, ta kaini wajen me gidanta yayi Mana nasiha tareda Sanya albarka sannan muka fito zuwa bangaren mahaifiyar shi, ta manyanta sosae, suna kiranta Hajiyar Charanci, asalin su Yan Charanci ne ta katsina, hatta accent dinsu na can ne, da muka danyi Hira da ita tace min

” Kema Yar katsina ce ne? Naji hausarki irin ta garinmu”

Kaina na girgiza nace

” Mun dai zauna a huntua be”

Ta gyada Kai daga haka muka barta, wajen karfe goma muka dauki hanyar Gombe, tunda muka dauki hanya muke Hira na sake sosae se can bacci yayi gaba Dani. Lokacin da muka Isa an idar da azahar, wata anguwa me kyau na manyan mutane, more of a layout, duk inda zamu wuce zai min bayani gurin Wai yanzun na Zama Yar Gombe. A waje yayi parking muka Shiga ciki, masu gadi Suka gaishe mu hannun shi cikin nawa muka Shiga katon parlon, da Anty yusra na fara hada idanu, ta taho da sauri tana murmushi ta rungume ni tana fadin

” Anty Amarya! Oyoyo”

Taja hannuna muka zauna sauran sisters din shi su biyar muka gaisa dasu masu kirki,

” Ina Mama ko ta fita?”

Yayar Anty yusra wadda take bin Bayan Albi ta riko hannuna tace

” Anty Amarya muje ku gaisa, Hamma Bata fita ba jiran ku muke”

Hañunta cikin nawa muka nufi saman Yana biye damu sauran na bayan shi suna Hira. Tana zaune itada mahaifin su dake cin abinci, Yana kallon mu ya saki fuska haka itama ta taso ta rungume ni tana fadin

” Ga yata ta karaso”

Na Dan zame na tsugunna na gaishe ta, ta amsa sannan na karasa gefen Baffan dake murmushi kamar yadda Albi ya tsugunna nace

” Baffa Ina wuni? Mun sameku lafiya?”

Kaina cikin veil, haka Albi yace na gaishe shi idan nazo, Yana murmushi yace

” Barka da zuwa Yata Safiyya,Allah ya albarkaci rayuwar ku, Allah ya Baku zaman lafiya, tashi ki zauna”

Na koma na zauna gefen Hamma kamar yadda aka maida ni, Adda Asiya itace babba take bin Hamma, ita mahaifiyar su ta fara Haifa Bayan dogon lokacin data dauka Bata haihu ba, se Adda Nanah, se Anty yusra, se Adda maimuna da Khadija wadda yace min saata ce. Gaba dayan su suna da kirki, ko mahaifiyar su Bata nuna min komai ba. Na gaji sosae amma hakan muka zauna se yamma muka tafi, Anguwar mu Babu nisa sosae daga main gidan su, tun da ya tsaya Yana jiran a bude gate ya kalleni yace

” This is home, anan zamu zauna. Ina adduar Allah ya bamu zaman lafiya me dorewa, I’ll be whatever you want me to do”

Na gyada kaina lokacin gate din aka bude, mutumin Yana ta bashi hakuri Wai Hajiya ce ta aike shi,Kai ya gyada Yana amsa adduar da yake Masa na aurena. Yana Gama parking Yara biyu suka sheko da gudu suna fadin

” Daddy oyoyo! Daddy welcome”

Ya Dan rungume su yace

” Afaf ga Umminku”

Ta juyo ta kalleni,na saki fuskata, tace min

” Ummiey Ina kwana?”

Na rike hannunta nace

” Sannu Afaf”

Hannuna ya Kama yace

” Let’s go,ki gaji da yawa”

Na gyada Kai Afaf da Amna Suka biyo bayan mu, key ya Ciro ya bude part din dake can gefe ya kalleni muka Shiga Ina nanata adduar da Ammi da Anty Safara’u suka fada min. Na shiga parlon daya kawata da komai colors din komai ya burgeni. Afaf suka zauna yace min

” Lemme give you a tour kafin Isha ta karasa”

Wucewa mukai ya kaini ko Ina sannan yace nayi wanka kafin ya dawo, yaran na zaune yace musu suzo su tafi, nayi wanka na Kira Ammi da Aisha Akan ta fadawa Mama min karaso. Cikin Maroon kace na shirya na zauna Ina jiran ya dawo, Bai Jima ba ya shigo yace

” Muje part din Maman Amna”

Tare muka fita Ina addua cikin Raina, a gefena part dinta yake komai iri daya building din, Kaya ne kowa da anshi, Banda kamshi Babu abinda ke tashi, Babu kowa a parlon se tv na aiki, na karasa na zauna kamar yadda yace min shi Kuma ya wuce daki, sun Dade har naji na gaji kafin ya fito fuskar shi Babu annuri, itama fitowa tayi fuskar ta Babu yabo Babu fallasa ta zauna can gefe tace

” Sannu da zuwa Amarya!”

Na dago na kalleta, kyakyawa ce ta gaske Dan ta fini fari, nayi murmushi nace

” Ina wuni!”

Ta amsa da lafiya sannan ya Dan Mana nasihar da ake sannan ya dubeta yace

” Akwai magana”

Ya girgiza Kai tace

” Kowa ya zauna lafiya shi yaso, ni ban iya munafurci ba kowacce ta zauna inda ka aje ta, ba sai kowa ya shiga harkar kowa ba. Zancen kwana inace Kun riga kun kwana daya a kano? Shida ya rage Mata kenan”

Tunda ta fara magana nake kallonta da mamaki, how can she not conceal abinda take ji, ya kalleni yace

” Gem ki jirani a parlonki”

Na gyada kaina na Mike na tafi, sabuwar rayuwar kenan, wato ita da abinda zaa fara da ita kenan. Na danyi murmushi na nufi part dina Ina ayyana zaman lafiyar ta shi ne ta bini a hankali, idan Kuma ta nuna ba hakan ba Nima tabbas Zan nuna Mata ni wacece, Babu wata mace data Isa na aureshi ta nemi juyani, yadda take jin gidan ta ne Nima hakan nake ji. Ina Shiga na zauna Ina kallon yadda ya cika kan center table din da ledoji, wayata na dauka Ina random dube dube, shigowa yayi ya kulle kofar sannan mukai sallah yace

” Kiyi hakuri, Dan kishin Mata ne”

Na gyada kaina, Yana ta kokarin lighting mood Dina na sake jiki muka ci Naman da ya kawo dukda inata Dan jin tsoro da Kuma nauyin hakan. A Daren ya nuna min abinda yake nufi da zai rufe min bakina, ya nuna min wata duniya wadda ban taba sani akwaita, na tabbata mallakin sa!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *