UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 13 BY SHATU
Www.bankinhausanovels.com.ng
Naji saukar shi daga gadon, naji Kuma fitar shi daga dakin, Amma gajiyar da Kuma baccin da ke cikin idanuna se Suka hana ni na bude idon, ban Kara kwakwaran motsi ba se wajen karfe goma na safe sannan na tashi, shima Rana ce ta cika dakin ta damu idanuna, Babu yadda zanyi Dole haka na Mike Ina jin jikina duk yayi min tsami kamar nasha duka. Na daga kafafuna cikin dabara na wuce toilet, daga idanuna nayi na kalla toilet heater se Naga ta ma tafasa, I had a hot bath da yasa na danji Dadi sannan na fito na dawo dakin, yadda na barshi haka nan yake, se na fara tunanin Ina Albi yaje da safiyar nan, se na Kuma tuna ko ya leka wajen matar shi. Na zauna gefen gadon bayan na jona hair dryer a socket na busar da kon sannan na shafa Mai na Kama da band. Na goge jikina na
shirya cikin bakin lace me adon orange flowers. Nayi stretching sheets din gadon, daga karshe se na yaye sheet din na dakko sabo na shimfida, sabuwar rayuwa na ayyana a raina, na kalla komai na dakin Wai mallaki nane, nawa ne duka.
Ina fitowa parlor ana kawowa wuta se kawai na kunna incence burners Dan turara gidan. Wayata na Nemo na kunna na fara Kiran Ammi Bata dauka ba se Anisah ce ta dauka, se naji dadi naji Ina missing gida, Ayaan ce muka gaisa karshe sannan na Dan kwanta na lumshe idanuna Ina jin yunwa na kwakular cikina. Can na kasa hakuri har Sha daya ta kusa se kawai na nufi kitchen na hada tea na fito dashi a mug Ina juyawa Dan ya huce, turo kofa naji anyi se Kuma ya bayyana gaba daya, hannun shi dauke da ledoji da waya a kunne alamar waya yake, Yana sanye da Ash top se bakin wando. Tea din na aje na karasa inda ya tsaya na karba kayan hannun shi sannan na zauna na fara shan tea din, gefena ya dawo ya zauna tareda aje wayar hannun shi ya daura kan table din dake gefen mu ya shafa fuskata
” I’m sorry na fita na barki da Yunwa, na fita na samo Miki abinda Zaki ci. Ya Kika tashi? Ya jikin naki?”
Bawai maganar tashi bace tasa na kusan zubar da tea din hannuna a’a yadda yaki tsayar da hannun shi a jikina yasa tea din ya nemi zubewa, dariya ya fara Yi a hankali ganin duk na rikice ga kuma Bata Rai da nayi, yace
” Why are you frowning, ko gaida ni ma bakiyi ba”
Na janye jikina nace
” To ba Kai bane ka tafi ka barni ba”
Ya Mike bayan yace nayi hakuri, da kanshi ya dakko plate ya juye abincin daya kawo cikin disposable packs, sannan na sakko muka fara ci, seda na koshi sannan ya ballo min pain relievers na karba kaina a kasa nasha. Ni na tattara gurin na dawo na samu ya fita, Bai Yi minti goma ba ya dawo ya sameni Ina kwance nayi shiru deep in thought,
” Menene?”
Ya fada Yana dago kaina ya daura saman laps dinsa, kaina na girgiza Ina murmushi nace
” Babu komai”
Yace
” Baki jin dadin zaman ne, kinyi shiru”
Na girgiza Kai Ina murmushi nace
” Kai Albi waye ya Fadi haka? Ai baka nan shiyasa yanzun tunda ka dawo se muyi ta magana”
Ya gyada Kai ya fara min Hira, Ina dariya Ina Kuma sauraran shi,seda aka Kira azahar yace min zaije masallaci me zanci ya taho min dashi, nace
” A’a zanyi girki”
” No! Ko na yau ne kadai Zan kawo idan yaso gobe seki fara”
Haka ce ta faru seda nayi kwana biyu shi yake siyo Mana abinci se a Rana ta uku sannan muka fita da yamma Dan yin cefane, bayan nayi sallar laasar na shirya cikin abaya maroon, na saka golden din turban cap a kaina sannan na yafa veil din abayar, wayata kawai na dauka na fito, na kulle part din sannan na nufi bangaren Maman Afaf, shima shi yace nace Mata Zan fita, da sallama na shiga parlon tana zaune ta daura kafarta akan center table tana kallo, na shiga Bayan ta amsa na zauna na gaishe ta, idonta na kan tv din ta amsa, nace
” Zan fita ne”
Se ta kalleni sannan tace
” A dawo lafiya”
Na amsa da Amin na Mike Zan fita se na juyo nace
” Su Afaf basa nan ne?”
Ba tareda ta kalleni ba tace
” Eh!”
Se na gyada kaina kawai na fita, tabbas Kubra da gaske take da tace Bata iya munafurci ba, ni hakan yayi min, da ta nuna tana Yi Dani ta fitine ni gwara kowa yayi ta kanshi, tashi ta fushe shi. Se wajen maghrib muka dawo Dan seda muka tsaya gidan Adda Nanah dake kusa da inda muka je. Zama nayi na gyara kayan Miyan na saka cikin freezer komai na Masa guri tunda Naga muna samun wuta sosae. Ranar da na cika kwana biyar ranar nayi baki, tun dare Baba ya fada Masa zuwan su, Dan haka Ina tashi da safe na hada stew se wajen eleven na Gama girkin sannan nayi wanka na shirya. Wajen Sha biyu Sega Ummaah, Anty jidda, Anty Safara’u, Anty lubabatu, Maman Yaya Fahad, da wasu aunties Dina su uku. Dukda yawancin su bana shiri dasu Amma hakan Bai Hana naji dadin zuwan su ba, nayi ta murna na bisu na rungume su sannan na kawo musu abin da zasu Sha, mun Dan fara Hira Ummaah tace na raka su wajen Kubra. Haka na dakko hijab Dina na tafi bangaren ta, su Afaf na Wasa sun dawo a makaranta ko uniform Basu cire ba, tana ganina ta taho ta fado jikina, nayi murmushi nace
” Ina mamanku?”
” Tana daki” ta bani amsa nace tace Ina parlon Ina magana, se gata ta fito kanfin ma Afaf din ta Shiga, na gaishe ta tayi kyau cikin shigar shadda ja da tayi, ta amsa nace Mata
” Aunties Dina Suka zo zaku gaisa”
Tace
” Tohm Bari nazo”
Nace
” Ba se sunzo ba kenan”
Tace eh, se na juya na koma naji dadi ta girmama su. Babu jimawa se gata taso da fara’ar da ban taba gani ba a fuskarta Suka gaisa ta musu Allah ya Sanya alkhairi sannan ta tafi, se yamma Suka tafi bayan sun kawo duk abinda na Bari da komai na alaadar mu. Haka zaman ya cigaba Babu ruwan kowa da kowa tsakanina dashi mun dauki hanyar Gina rayuwa me dadi, da fahimtar juna. Seda nayi sati sannan ya koma side dinta, Bayan sallar maghrib na dafa noodles na zauna da sabon littafi a hannuna Ina karantawa, ya shigo da sallama bakin shi, hannun shi cikin na Amna, littafin na aje na maida hankalina kanshi
” Amna yanmata zo nan”
Ta karaso gurin da muke zaune ta rike hannuna,
” Zaki iya kwana kuwa? Da nace Khadija tazo ta Taya ki kwana? How do you see?”
” Zan iya kwana ni daya”
Ya janyo ledar yace naci sannan ya dubi TVn yace
” Bazakiyi kallo ba”
Na girgiza Kai nace
” Nifa kasan bana son kallo, I’ll read”
” Na manta fa! Good night”
Ya fada tareda Dan squeezing hannuna dake cikin nashi, na gyada Kai naje na kulle kofar bayan sun tafi na kashe komai na wuce daki na kwanta, na Jima Ina karatu seda na fara kokarin bacci sannan naji kewar shi ta mamaye gurin, jikina, gadon da Kuma zuciyata, ko Ina kewar shi yake. Se shedan ya fara kissima min su cikin idanuna, da suari na fara auziyya sannan na janyo wayata na danyi karatu kafin bacci ya daukeni.
Babu jimawa aka fara Shirin babbar sallah, ranar sallah a girkin ta ne Dan haka ita dashi suka yo cefane ni Kuma yace naje muyi girkin tare, a part dinta muka Yi aikin abincin da kannenta Yan Mata biyu sun zo, sunata hada Fadi ko magana basuyi min ba. Nima bance dasu uffan ba har muka gama sannan ta bani zobo na saka a fridge dina se ayar da Zan Nika da safe nayi kunun Aya. Ni kadai Nasha ruwa dukda ya leko ni yafi na irga but still inajin da ace ni daya ce sede muyi komai tare to Allah ya tsara akasin ni yadda na tsara.
Tunda na saka kafata gidan Albi, duk lokacin da Ammi zamuyi waya da ita to se tayi min nasiha akan hakuri, ta fada min Zama da wata babban kalubale ne Wanda idan Ina ganin na sani to ban sani ba, tunda ita da Anty Rumasa’u basu ci talata da laraba tare ba, dukda haka an samu matsala balle ni da muke tare. Nayi hakuri dukda tasan yanzun banida hakuri dangin ubana sun canja min halayena gaba daya, ku kanku kunsan da ba hakan nake ba.+
Bayan ansha ruwa se naji kaina na yimin masifar ciwo, da kyar na Dan taba abinci na tafi daki na kwanta, bama bacci nayi ba Amma dai kawai nayi shiru ne Ina tunanin rayuwa, se Dana ji Kiran sallah sannan na tashi nayi sallah anan cikin bedroom din, Ina zaune naji sallamar shi, na dago Ina amsawa har ya karaso ciki, Zama yayi gefen gado yana kallona yace
” Kinsha ruwa lafiya?”
Nace
” Lafiya Lau! Kaima kasha lafiya?”
Ya gyada kan shi sannan yace
” Naga kamar Baki ci abincin ba, are you ok?”
Hannuna nasa na rike kaina nace
” Ciwo yake min ne”
Dakkowa yayi ya dawo gefena tareda zare hijab din jikina ya taba wuyana da goshi na, inata kallon shi Yana bin skin Dina da hannun shi Dan yaji temperature Dina, se naji zuciyata tayi melting, na rike hannun shi Ina Dan murmushi nace
” Ba fever nake ba, ianga stress ne Nasha magani fa”
Se ya saki ajiyar zuciya yace
” Ki huta kinji, if there’s anything just call me kinji ko?”
Na gyada Kai na se ya Mike tareda kissing hannuna dake cikin nashi ya min seda safe, Bayan shi na bi na rufe kofar sannan na tattare kayan dake parlor na Kai kitchen na koma daki na kwanta, bansan dalili ba kawai se na fara kuka, na rufe fuskata da hannuna Ina kuka a hankali a hakan bacci ya daukeni. Ko da na tashi da asuba da zazzabi na tashi, Amma haka na daure naje nayi alwala sannnan na Nika ayar dake jike tun jiya, na hada komai se naji ana taba kofa, ya bude ya shigo ckin Ash jallabiyya, na gaishe shi ya tambayi jikina na amsa da sauki sannan ya tafi masallaci, Nima se nayi sallah sannan na zuzzuba cikin robobi na mayar cikin fridge, nayi wanka na koma na kwanta Ina jin zazzabin na raguwa, wajen bakwai na tashi jin wayata na ringing, na duba Naga Albi ke kira,
” Ki fito zamu tafi masallaci yanzun”
Na tashi na zauna nace
” Ban shirya ba ai”
” To mu zamu wuce kawai se min dawo”
Ko Allah ya kiyaye ban ce Masa ba na aje wayata na Mike Ina jin Raina ya fara baci, ya kamata tun jiya ya fada min zamuje masallaci na shirya da wuri Amma seda ya fito tukun zai ce na fito, koma ba zai fada ba ya kamata ya fada min da ya shigo da asuba. Na tashi na gyara gadon, nayi shara na gyara gidan sannan na dawo na sake wanka na fara neman kayan da Zan saka, wani farin lace na hango na fara kokarin janyo shi se na fasa na dakko wata brown shadda da aka hada min a lefe na, dinkin skirt da riga aka min, da bead work me kyau, na saka a jikina nayi barin turare, na gyara fuskata da gashina sannan na wuce kitchen nayi wanke wanke, abincin da ban ci ba na juye a wani kwano na saka hijab na bawa me gadi, Yana ta min godiya na koma ciki na kunna turare sannan na daura dankwali Wanda gashina dake daure da band ya samu damar fitowa. Parlo na zauna nayi tilawa sannan na janyo wani SciFi novel na fara karantawa, anyi basing dinsa a Mexico, suke tada wani beast ya tashi ya addaba gaba daya garin. Ina daga zaune naji parking din motar shi, na Mike na Nemo katon baho na juye zobon da kunun ayar duka sannan na dawo na zauna, wajen after ten minutes Ina jiran shigowar shi Sega Amna a guje ta shigo, ta riko hannuna
STORY CONTINUES BELOW

” Daddy ki zo”
Haka take magana, Bata iya hada sentence da kyau, na mike Dan kawai shi ya kirani Kuma sawa yayi a kirani if not bazan zo ba, Dan kawai kada na bada shi ne, ko kuma na bada gap a tsakanin mu tun yanzun ya fara Bata min Rai, da kaina na dauka na wuce part dinta, bayan na lulluba mayafi da yayi matching da kayan jikina, dukka suna parlor a zazzaune banda shi, Ina shigowa Naga duka suna kallona, na aje abin hannuna na zauna muka gaisa da ita, Afaf ta taho ta zauna gefena,ta kalla kannen nata tace
” Baku iya gaisuwa ba”
Suka Kara hade Rai sannan Suka gaishe ni na amsa a ciki ciki, Dan su San gaisuwar su ba komai bace, da kanta ta kawo abinci ta shirya abinda na kawo cikin fridge se gashi ya fito, anan na saki murmushi a raina Ina fadin what a lovely coincidence, kayan dake jikin shi irin nawa komai da komai, I guess anko ma yayi Mana, shiyasa Naga anata kallona. Gefena ya zauna tareda taba wuyana yace
” Zazzabin ya tafi”
Na gyada Masa Kai bance komai ba, muka ci abinci Wanda kadan na tsakura na aje plate din ya kalleni bayan ya aje spoon din hannun shi yace
” Hey me ya faru?’
Na langwabar da Kai nace
” Na koshi”
” No ki Kara ko kadan ne Mana”
Na Dan turo bakina Wanda yake tempting dinsa nace
” Allah na koshi, Nasha tea ai”
Gyaran murya tayi ta tuna Mana tana gurin fa, nayi murmushi na Mike da kunun Aya a hannuna nace Mata
” Zan koma, idan zaa fara aiki,se kiyi min magana”
Banma jira ta bani amsa ba nayi wucewata, Babu jimawa se gashi ya biyoni, Ina kwance akan kujera na lumshe idanuna, naji kawai duniyar Bata min dadi saboda yadda jikina Babu dadi, hannun shi yasa ya dago ni Yana fadin
” Meke damun ki?”
Na girgiza Kai Ina ture shi nace
” Nothing kawai Ina son na huta ne”
Na koma Zan kwanta ya hanani, Dole na zauna yace
” I’m sorry, ban tafi dake ba dazu ko? Naga Baki jin Dadi ne shiyasa”
Bance Masa komai ba nayi shiru haka ya gaji ya fita, se azahar aka shigo da aikin, lokacin na sake wanka na saka purple top da wani zani se chiffon scarf na daura akaina, na dauka sallaya da hijab, ruwa me sanyi cikin water bottle na nufi inda suke. Ta fara hada wuta na Taya ta muka hada sannan na daura muka koma karkashin rumfa muka zauna, shima yazo ya zauna suna Hira Amma ni duk hankalina Yana kan Naman da nake ta juyawa akai akai. Can munyi rabi fadila da Farida suka shige ciki ya zamana daga ni se ita shima ya tafi yace bacci yakeji, daga karshe mu biyu muka karasa muka gyara gurin daf da maghrib. Ina shiga parlona na wuce toilet se amai kamar Zan fitar da kayan cikina, na dauraye bakina na fito naji Yunwa nake ji. Gashi zai dawo dakina a wañnan Daren, sallah kawai nayi na fada kitchen na hada simple abinci, Ina gamawa ana sallar Isha nayi sannan na shiga wanka, ya riga ya fada min zaije gidan Baffa, Nima na shirya nayi kwalliyya kafin na fito ya sameni a daki, na rungume shi Ina shagwaban na gaji, da naga alamar lissafin shi zai kunce se na gudo parlor na barshi Yana fadin Zan Shiga hannun shi ne. Ina hada Masa salad, fadila ta shigo itada Afaf, ba sallama haka ta shigo shiyasa ko magana ban Mata ba, shi ne ya tambayeta ya akai ta bashi Abu cikin bakar Leda, ya kalla sannan ya kalleni Ina gefe Ina kallon su yace
” Meye wannan?”
Tace
” Anty ta Rana nama tace a kawo Mata”
Yayi tsaki ya Mike fuuu ya fita, ita dama ta rigashi fita, Yana shiga yaji tana fadin
” Ba seda nace idan yana nan ki dawo min dashi ba, shi ne Zaki Bata salon ki jawo min magana!”
Ya shigo ya dubeta yace a dakko Naman gaba daya, da kanshi ya raba ya deba min nawa sannan yace Mata
“Dan na baki dama bashi yake nufin ki taka kowa ba, na baki dama saboda kece babba, kinsan bana son son zuciya”
Daga haka ya dawo, na fahimci ranshi a bace yake Dan haka kafin ya fara cin abinci seda nasa ya manta damuwar shi sannan muka ci abinci a nutse. Washegari Bayan min Raya Daren da soyayaya data nuna min kwana biyu bama tare, Wanda ke yanka nama yazo wajen takwas ya Gama komai ya tafi, Yana gamawa muka fito muka fara aiki, wajen Sha daya munyi nisa se gashi ya fito Ina tsaye bakin murhu Ina zuba spice cikin kasko yace min
” Fav Ina wayarki?’
Na juyo nace Ina kankance idanuna saboda hayaki nace
” I left it a caji”
Ya danyi shiru kafin yace
” Kiyi hakuri, muje Gumel”
Da sauri na juyo na aje container hannuna na nufo shi gabana na faduwa nace
” Me ya faru?”
Yayi shiru yana Kare min kallo, na ruko hannun shi Ina Kara tambayar shi,se can yace
” Kiyi hakuri Baba ya kirani yace Gwoggo Allah ya Yi Mata rasuwa”
Bance komai ba, saboda wani Abu naji kamar ya daki kirjina har throat Dina, ban ma kula da kallon da suke min ba na nufi part Dina, na tarar ya hada min Kaya, ko wanka ban sake ba na canja Kaya, kaina kamar an saka bomb an tayar haka nake ji. Ya shigo ya tarar Ina kashe wutar parlor yace
” Kiyi hakuri Allah ya jikanta!”
Kaina kawai na gyada Masa, ya fito na kulle komai sannan na koma Dan yiwa maman Amna sallama, tun kafin na karasa naji tana fadin
” Wallahi sede a ware Naman kowa idan ta dawo ta soya nata,ni jakar ta ce”
Fadila tace
” Ko Babarta ce ta rasu ai a Bari se gobe Amma wata Kaka ma for that matter”
Na karasa nace Mata
” Zan tafi”
Na juya jin Bata tanka ni ba na sameshi a mota Yana Jirana, seda muka kebe muka dauka hanya sannan na fara kuka, Ina jin alhinin mutuwar Gwoggo, tsohuwar arziki.
I’m sorry for misnumbering of page 44, se daga baya na fahimta, to show you how much I’m eager to complete it. Thank you for everything!
Nasha kuka a hanyar tafiyar mu Bai hanani ba se ya kyaleni nayi me isata, saboda yadda nake bashi labarin Gwoggo da matsayin ta da role din data playing cikin dawo da Ammi gidan mu da Kuma rayuwar mu baki daya yasan it’s din me muhimmancin gaske ce, so dole ya kyaleni nayi kuka, da nayi me isata se na jingina da abin kujerar da nake se bacci ya daukeni. Tafiya sosae mukai dukda yawanci Ina bacci akai kafin muka karasa Gumel, straight gidan makokin muka wuce, Dole ta baya muka zagaya saboda irin cikowar dake kofar gida, na share hawayena bayan yayi parking, hannuna ya riko yace+
” Ya Isa, you’ve cried enough, Allah ya jikanta yayi Mata Rahma. Kinji? Kiyi hakuri”
Kaina na gyada Ina Kara bawa wasu hawayen damar sakkaowa, janyo ni yayi jikin shi ya bubbuga bayana sannan ya bude motar ya fito Nima ya bude min na fito, tsabar gajiya se naji wani mummunan jiri Yana Neman yarda ni, nayi saurin rike kofar motar Ina maida numfashi na lumshe idanuna, gabana ya dawo ya tsugunna ya riko hannuna Yana tambayar
” Are you ok?”
Kaina na gyada na bude idanuna na Mike Amma na kasa tsayawa Dole na koma na zauna, wayar shi ya Ciro ya fara Kira Babu jimawa naji Yana magana sannan ya kashe, a hankali na bude idanuna saboda kmashin turaren da naji na tabbatar Yaya Ismail ne, na dago idanuna na dube su, shida Hanifa me tsaye, itada tsohon ciki tayi kiba, fuskarta duk ta canja ta kumbura, Amma wannan gayun Yana nan ko yanzun ka kalleta kasan Yar gayu ce, chewing gum ne bakin ta tana taunawa, shikam Yana gefenta yayi Rama ya danyi Baki, se lokacin na tuna ni ban ganshi gurin bikina ba, nasan ya tura min 200k Wai na sayi wani abun, Amma a lokacin ko tunanin abinda ya Hana shi zuwa banyi ba. Ya mikawa Albi hannu da bakin su a bude
” Royal prince! Ismail kana nan kenan?”
Ya shafa kanshi Yana Dan murmushi yace
” Ashe Kaine angon? Usman Dikko shekara nawa?”
Ni se naji sun Bata min rai, Muna mourning rasuwar Gwoggo sun zo suna wani shekara nawa, Hanifa da tuni tana gefena ta riko hannuna Dan nace Mata jiri nake ji, kafin Ammi ta Aiko Anisah da Ayaan har mun shiga ciki, Hanifa tace min
” Se Kika ji rasuwar Gwoggo Kuma?”
Na girgiza Kai nace
” It was a huge blow, Allah ya jikanta”
Ta amsa da Amin muka karasa ciki, nan ma Babu masakar tsinke, gefen Ammi ta kaini sannan ta tsugunno tace
” Me Zaki ci na kawo Miki?”
Na girgiza Kai nace nagode kawai se ta harareni ta tafi, dama can tana da kirki na sani, ni da ita ne bamu jituwa plus Yaya Ismail dake tsakanin mu Amma ita mutuniyar Rayha ce. Ta wuce na gaida su Ammi sannan tayi min gaisuwa, na saka kaina cikin hijab Dina na dinga kuka se Rayha ta dauka, Ayaan dake gefen mu itama tana Taya mu, haka Anty Safara’u da Anty Hadiyya. Dama haka gidan makokin yake idan wani yazo se ya Kara dawo muku da ita sabuwa, seda Hanifa ta kawo min tea ta zauna nasha sannan ta rakani nabi anties Dina su Tara na musu gaisuwa, matan uncle Dina uku harda Ammi ta hudu, kowa se yace Amarya kin samu zuwa kenan? Haka na dawo, umma Hannatu sirikar Rayha tasa aka Kai Masa abinci. Se can dare muka koma gida nayiwa Baba gaisuwa, Baba zubairu, Baba umaru da Baba Ahmadu. Washegari da wuri muka koma gidan gaisuwar, na danji karfin jikina Amma dukda haka se da nayi zazzabin dare, tareda Yaya Ismail, Yaya Fahad da Yaya Nasir Albi ya kwana, da safe tare Suka shigo na raka shi gurin Wanda ya dace ya musu gaisuwa sannan na bishi wani zaure, nace
” Yau zaka tafi ko?”
Kanshi ya girgiza yace
” Zan jira ayi sadakar uku tukunnan”
STORY CONTINUES BELOW

Na gyada kaina na Masa godiya ya harareni sannan yace
” Fari kike karawa, are you sick?”
Na girgiza Masa Kai nace ai shock ne kawai, se ya hakura ya tafi, a wañnan safiyar Sega Mama da Aysha sunzo min gaisuwa, tana ta bani Baki ganin Ina kuka se yamma Suka tafi. Ranar sadakar uku Yan gidan su Albi na Gombe sukazo, dukkan su tun daga Baffa, Mama, Adda Asiya har zuwa Khadija. Se Maman Afaf da ta biyo su, naji dadi sosae, anan rumfar da Ammi ke zaune Suka zauna, muka gaisa sannan naje na kawo musu ruwa da lemu, Rayha ta kawo musu abinci Bayan sun nutsu na raka su Suka ma sauran gaisuwa sannan Ammi tace muje gida su huta, ta baya muka fita Ina cewa Maman Afaf me yasa Bata zo dasu ba tayi murmushi kawai. A gida muka Jima dasu se wajen laasar sannan muka dawo suka dauki hanya, se lokacin muka gaisa da Baffa sannan Albi yayi min sallama akan zaizo bayan kwana daya da sadakar bakwai.
A hankali gidan ya baje muma muka dangana kowa ya koma normal activities dinsa, seda na Kara kwana biyu Bayan sadakar bakwai sannan yazo muka tafi. Tun a hanya zazzabi ya rufeni se na balla pcm kawai nasha Dan nayiwa Baba complain yace kada Ina Shan magani, a hankali zai tafi ko daya ban kawo ma abinda su suke kawo ba. Tareda Khadija mukai aikin gyaran gidan sannan ta min sallama ta tafi, na kunna burners na Shiga wanka, na shirya sannan na shiga kitchen yin girki, tunda na kunna gas din naji wani irin tashin zuciya kamar zanyi amai, da sauri na fita na dauki chewing gum na sa a bakina sannan na koma nayi girkin. Banma lura ba a kawo min nama ba, ni na manta ma tace ba zata soya ba. Kayan cikin da muka soya shi na dakko na saka a gaba da lemu na dinga ci ga littafi a hannuna Ina karantawa, can naji an dauke ledar na dago idanuna se kawai idonmu ya hadu da nashi Yana murmushi
” See this one, Naman Zaki cinye lokaci daya?”
Na danyi dariya nace
” To kawai bakina ne Babu dadi”
Ya aje min sannan yace
” Cin dare daya kumburin ciki”
Nayi dariya, na aje littafin hannuna nace
” In kawo maka abinci?”
Ya gayda kanshi , na Mike ya biyo bayana har na hado abincin muka zauna ci, Muna cikin ci nace
” Albi Ina ka aje min Naman sallar”
” Kura Kika Zama ne? Nidai nasan da Baki damu da nama ba”
Nace
” Wallahi kuwa, I dunno why.”
Se yace min ai Yana freezer baa soya ba, shi yace kada su soya a barmin Koda akwai abinda nake son Yi dashi. Nayi murmushi na Kuma yaba Masa na kokarin Kare martabar matar sa da yake. Bayan mun Gama cin abinci naje nace Mata ma dawo na Mata godiya dukda a ranar ma nasa Albi ya turon contact dinta na Mata godiya.
A bangaren Hanifa Bayan ta koma Kano da kwana biyu labor ya tasar Mata cikin dare, aka kaita asibiti se gata da sunkuceciyar yarta mace. Tun a asibitin Amira tace Mata ai taji a Gumel ana cewa Ismail zaiyi aure, ta kuwa Mike daga kwancen da take tace
” Zaiyi aure Amira Kika ce? Wa zai aura? Waye ya fada miki”
Amira ta zauna tace
” Daga gidan su dai, can masarautar, ramlah ta fada min wai Anty Nabiha ta bada shawarar yayi aure tunda kina ma Ummaah rashin kunya “
Hanifa ta kunduma zagi tace
” Wallahi Basu Isa ba, tayi kadan, ki barni da ita, Anty Nabiha munafuka ce ita Kuma. Ita Kuma se tasan ni ba wadda zaa ma munafurci bace’
Gaba daya hankalin Hanifa ya tashi, Amira tace ko mum dinsu Bata fadawa ba saboda taga an musu mutuwa, gashi kwana biyu taga alamar kamar Anty jidda na cikin damuwa. Koda Yaya Ismail yazo ta dubeshi tace
” Ka yiwa Babyn huduba?”
Ya zauna gefenta Yana daukar ta a cikin shawl Yana murmushi yace
“Tun kina bacci nayi Mata”
” Meye sunan?”
Ta tambaya a takaice
” Furaira! Sunan Ummaah”
Se tayi dariya tace
” Se kace a BC, zakace Furaira. A’a wallahi ka Nemo wani sunan Amma yata bazaa saka Mata wannan sunan ba”
Kallonta Ismail yayi da mamaki, kodan ba abin mamaki yace
” Hanifa sunan Ummaah ne…”
Ta katse shi da fadin
” Nace bansani bane ba? A’a na sani kawai ba zaa saka bane..”
” You don’t have that right kin gane? Ki Shiga hankalin ki sunan yarinya Furaira it’s final”
Amira na gefe tana kallon su , dama tasan zaayi haka Dan ramlah ta fada Mata anyi maganar sunan baby, fucewar shi yayi ya barta gurin. Mikewa tayi tace a Kira a zo ayi discharging dinta akwai inda zataje, private facility ne suna zuwa Suka sallame ta, ko Mom din su Bata jira ba balle ta Kira Ismail da sukai rabuwar tsiya ta Tara me napep ta goya yarinyar tace
” Amira ki wuce da kayan, ni zanje na dawo!”
Amira ta tsaya kallon ikon Allah, ta Ciro waya ta Kira ramlah ta fada Mata abinda ke faruwa sukai dariya tace
” Can da yawar su, Ina fada Miki an kawo syrup din Zan bashi ya kawo Miki anjima”
Wani Dan tsalle Amira tayi tace
” What a good news, thank you sister”
Alakar Amira da ramlah akwai tambaya, Dan ko nida Hanifa ramla ta girme mu, shiyasa tun a bikina nayi mamakin ganin su tare Ashe Suma wata harkallar suke.