ZABI NA CHAPTER 2 BY FADEELARH

ZABI NA CHAPTER 2 BY FADEELARH

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Bayan wata daya da auren su ne Sameera tayi shawara da Farouq akan tana so ta fara sana’a da kudin gadon ta.. ta tsayar da shawarar fara kunun aya saboda ta kula mutane suna siya sossai..+

Yayi farin ciki da jin hakan. Ya tabbatar Sameera ba lazy mutum bace kamar Hindatu.

Nan da nan ta bayar da kudi aka siyo mata ‘yar madaidaiciyar deep freezer, buhun aya da na sugar, bottles, flavour da duk wasu abubuwan da zata buqata.

Tuni ta fara yin kunun ayan ta.. tayi ma makwabta talla… Kunun ayan Sameera yana da masifar dadi.. hakan ya sanya nan da nan kasuwa ta bude mata. Idan tayi kunun aya kafin kace kwabo ya qare.

Duk qarshen wata idan ta hada ribarta sai ta ba Farouq ya zuba mata a account dinta.

Hindatu dai tana nan zaune babu aikin fari bare na baqi.. sai tijara da baqin hali.

Sossai Sameera take son Layla amma Hindatu ko daukar ta bata bari tayi.. Haka Sameera zata shiga kasuwa ta ga abubuwa ta siyo ma Layla ta kawo kuma babu kunya sai ta karba babu ko godiya.. tun halin Hindatu yana ba Sameera mamaki har ta daina.. Yau da gobe ma sai ta saba!

Lokutta da dama idan Farouq baya da kudi a hannun shi, Sameera ce take bashi.. Tabbas to him Sameera is a blessing in disguise.

A lokacin da suka yi wata hudu da yin aure ne Sameera ta samu ciki… kamar yadda yayi murna lokacin cikin Layla haka yayi wannan karon.. duk abinda Sameera take buqata kuwa yana kawo mata dukda ma lokutta da dama ba tambaya take yi ba.

A wannan lokacin ne Farouq ya dakatar da ita akan sayar da kunun aya saboda baya so tana wahala..

☆☆☆☆☆☆☆

A lokacin da cikin Sameera ya kai wata tara daidai ta haihu.. ta haifi ‘yarta mace wadda ta ci suna Ameera.

Hindatu dai ganin yarinya baqa kamar uwarta ta dinga dariya tana fadin ‘yarta dai ta fi kyau sannan duk inda aka hada su ‘yarta za’a zaba.

Wannan kalaman na Hindatu suna matuqar ba Sameera mamaki.. wani lokaci kamar takan manta cewar Allah ya halicci kowa da komai yadda yake so.

☆☆☆☆☆☆☆☆☆

A haka dai shekaru sukayi ta tafiya. Tuni Hindatu ta qara haihuwa yara maza guda uku.. Ibrahim, Munnir da Suleiman.

Ita kuwa Sameera namiji daya kawai ta qaro wanda ya ci suna Aliyu Haidar. Aliyu ya kasance tsaran Munnir don haka kan su daya.

Tunda yara maza na gidan suka taso kawunan su a hade suke.. Ibrahim, Munnir, Suleiman da Aliyu tare suke yin komai. Abban su ya gina musu daki mai dan girma a waje suka yi zaman su a ciki yayinda ya qara dakuna biyu attached to the main house.. Ya dauki daki daya sannan ya bar ma yara mata dayan dakin.

A bangaren ‘yan matan kuwa tunda suka taso Mama (Hindatu) ta sanya ma Layla qiyayyar Ameera da Ummanta (Sameera) a cikin zuciya. Layla ta girma bata qaunar Ameera da mahaifiyarta.

Har a wannan lokacin kuwa Umman Ameera bata daina yi ma Layla da Mamanta abin alkhairi ba.. Duk wani abinda ta siyo ma ‘yarta sai ta siyo ma Layla kuma su karbe babu ko godiya. Hakan kuma bazai hana anjima suyi ta jefo musu baqaqen maganganu ba.

STORY CONTINUES BELOW

A lokacin da yaran ta suka yi wayau ne ta cigaba da sana’ar ta. wannan karon kuwa harda masu taya ta aiki ta samu wanda take biyan su a duk qarshen wata. Babu laifi tana samun riba don kuwa duk qarshen wata bata rasa dubu ashirin zuwa talatin da take aikawa a sa mata a banki.

Akwai lokacin da Umman Ameera tayi niyyan canza gadon dakinta da kudin da take tarawa na sana’arta amma ta kasa saboda tana gudun kar Maman Layla tayi qorafi- tayi tunanin mijin su ne ya canza mata tunda dai ta raina sana’arta, tace wai ribar naira ashirin a kan kowanne goran kunun aya shirirta ce.. bata san cewar wadannan kudaden idan suka taru ba qananan kudade suke komawa ba.

Umman Ameera dai har sai da ta tara kudin da zai canza gadaje biyu sannan ta sanar da mujinsu abinda tayi niyya… sossai yayi mamakin abinda take da niyyar yi.. Da farko ma hanawa yayi amma ita Umman Ameeran ta gwada mishi babu komai.. da haka kuwa ta canza musu gadajen su ita da kishiyarta amma aka bari akan cewar Mijin su yayi musu.

Tsakanin Farouq da Sameera a kullum sai sanya albarka da Addu’an fatan alkhairi.

☆☆☆☆☆☆☆☆

Layla Farouq yarinya ce fara sol kyakyawar gaske, tana da dogon gashi sossai sannan doguwa ce with beautiful body.. Idanuwan ta grey ne, gaba daya duk duniya mutum kashi takwas a cikin dari ne suke da kalan idanuwan ta.. they are so unique and beautiful.

A dayan bangaren qanwar ta Ameera baqa ce amma ba wuluk ba.. ba lallai bane kana kallonta sau daya ka hango kyanta, kyanta a boye yake. Gashinta yana dan da tsawo babu laifi amma yana da cika da tauri. Zamu iya kiran Ameera siririya domin kuwa batada qira da diri kamar ‘yar uwarta Layla.

A dalilin bala’in kyan Layla ne idan ka kalli Ameera zaka ce mummuna ce amma in all she is not bad.

Ameera ma’abociya sanya hijabi ce yayinda Layla ta kasance mai yafa gyale, shima gyalen da an sakar mata fuska da bata yafa shi ba..

Tunda suka taso makarantar su daya.. tare suke zuwa sannan su dawo. Abban su ya tsaya tsaye wurin tabbatar da kawunan su a hade yake shiyasa Layla bata samun damar cin zarafin Ameera kamar yadda take so amma fa dukda hakan tana musguna mata a bayan idon Abba.

Tsakanin Layla da Ameera shekara biyu ne.. Haka a class shekaru biyu ne a tsakanin su.

Sossai Ameera take da qoqari a makaranta.. abinda aka koya musu da wanda ba’a koya musu ba duk ta iya.. shiyasa kullum ita take na daya a ajin su. Ita kuwa Layla da qyar take haye mai zuwa qarshe a ajin su.. Gaba daya ba karatu bane a gaban ta. don ma an takura ne amma sam da bata je school ba ma.

A lokacin da Ameera zata shiga JS1 ne tayi entrance examination tun daga aji biyar kuma ta ci don haka ne bata yi primary six ba sabanin Layla wadda tayi.. daga nan ne ya rage tsakanin su aji daya.

Suna qara girma yayinda kyan Layla yake ta qara bayyana… Sossai yarinyar take da kyau. She spends most of her time trying to look beautiful a rayuwarta.. Abinda kadai take so su ne kayan kwalliya da qyale-qyale.. gashi uwarta ba gwanar neman kwabo ba balle ta dinga siyo mata abubuwan kwalliyar. Har gobe kuwa Umman Ameera tana yi musu siyayya idan ta shiga kasuwa kuma kamar kullum su karbe babu godiya.

Tuni Abban su ya sama musu a daidaita sahu wadda take kai su makaranta ta dawo da su tunda ba motar hawa gareshi ba.. Dan mashin gare shi wanda yake zuwa ofis da shi. Dayake makarantar su Layla daban ne da na su Ibrahim sai an kai su sannan ake dawowa a kai su suma.

Islamiyya kuwa tun Ameera tana Js3 tayi sauka.. ita kuwa Layla dai babu abinda ta sa a gaba sai shiririta.. a qarshe ma daina zuwa tayi. Abba yayi fada har ya gaji ya qyale ta..

STORY CONTINUES BELOW

A lokacin da Layla take SS3 ta zana jarabawar fita daga Secondary School… Hakanan take zuwa ta rubuta jarabawar, ko karatu bata yi.. toh wane karatu zata yi bayan ko Cikakken note batada shi?

A lokacin da jarabawar Layla ta fito ta fadi sossai.. bata ci Jamb din ba sannan bata ci WAEC ba. Abban su yayi ta mata fada sossai yayinda Mamanta ta dinga bashi haquri tana kare ta.. Daga baya ne ya haqura tare da jaddada mata lallai idan bata ci ba next year zai yi mata aure.. zai aura mata duk wanda ya ga dama.

Jin haka kuwa hankalin ta ya tashi.. sai ta qudiri niyyan lallai zata yi qoqari don kuwa bata shirya ma auren dole ba.

Sai ya zamanto tare da Ameera zata maimaita jarabawar.. hakan yayi mata dadi don ta san ko banza zata kwashi amsa daga wurin Ameeran tunda surname din su daya (meaning tare zasu zauna a jarabawar) sannan su biyun Subject combination dinsu daya ne (she made sure of that)

A haka dai suka cigaba da rayuwa har shekara ta zagayo.

A lokacin da jarabawar su ta gabato Ameera ta mayar da hankalin ta sossai kan karatu.. ita kuwa Layla kamar wancan karon ko bude littafi bata yi.. Gashi har lesson teacher aka samo mata yana yi mata revision har na tsawon watanni uku amma a banza.. Abban su ya kashe kudin shi a banza.

Ko da aka fara jarabawar gaba daya a wurin Ameera ta dinga copying komai.. Duk ranar da aka kama ta tana satar amsa a wurinta kuma a canza mata wurin zama tayi ta kumburi tana zage-zage.

A haka dai suka gama zana jarabawar su suka koma zaman jiran sakamako.

Suna cikin jira ne Ameera tace ma ummanta tana so ta fara zuwa computer school.. Dayake hidima tayi ma Abban su yawa sai Umman ta tace zata biya musu ita da Layla su fara zuwa tunda ya fi zaman banza.

Kai tsaye Layla tace bazata yi computer school ba.. haka Ameera ta shiga computer school abinta yayinda Layla ta cigaba da zaman banza.. sai aukin kwalliya da zuwa gidajen qawaye da burin samun saurayi mai arziki.

Presently, shekarun Layla Goma sha tara a duniya yayinda Ameera take da Goma sha bakwai!!

☆☆☆☆☆☆☆☆

The faithful day!!

A lokacin da jarabawar WAEC dinsu ta fito ne suka shirya suka je Cafe don dubawa ta online.

A ranar kuwa hankalin Layla a tashe yayinda Ameera ta qagara ta ga grades dinta.

Ko da suka je Cafe din na Ameera aka fara dubawa.. Gaba daya courses dinta ta samu distinction.. Suprisingly itama Layla tayi qoqari don kuwa ta samu B guda daya sannan sauran duka C.

Sossai ta cika da murna don kuwa ta tabbatar Abban su bazai yi mata auren dole ba.

A lokacin da suka fito daga Cafe zasu tafi gida suna tsaye bakin titi suna neman adaidaita sahu ne suka jiyo sallama cikin wata daddadar murya..

Gaba dayan su suka juyo da sauri suna kallon shi yayinda Ameera ta amsa sallamar cikin wata muryar da bata tantance ko nata bane.

Kyakyawan gaske fari sol.. Ga gashin shi mai laushin gaske ya kwanta a kan shi da fuskar shi wanda ya qara mishi masifar kyau.. dogo ne kuma ba mai jiki ba.. Yana da wani dan tabo a bisa goshin shi daga gefe amma hakan bai sa yayi muni ba.. Saboda bala’in kyan shi kamar ace shi yayi kanshi…

A wannan ranar sanye yake cikin qananan kaya na wandon Jeans wanda ya nuna alamun kodewa, da gani ka san ya gurzu a wurin shi.. T-shirt din polo da take jikin shi ma ta jigata amma duk da hakan he was looking extremely handsome.

STORY CONTINUES BELOW

Daga Layla har Ameera sun kasa motsi.. babu abinda suke yi banda qare mishi kallo.. Gaba daya kyan shi ya birkita su.

Zayd dai idanuwan shi suna kan Layla.. Ko sau daya bai kalli Ameera ba wadda ita ta amsa sallamar shi.

Ameera dai ta saba da hakan tunda Layla ta fi ta kyau nesa ba kusa ba.. Gata fara sol, dole ne duk wanda ya kalle ta sau daya sai ya qara kallon ta musamman don ita tana sanye da Hijabi sabanin Layla wadda ta caba kwalliya ta yafa dan qaramin gyale..

Ba tare da bata lokaci ba ya gabatar da sunan shi a matsayin ZAYD MUHAMMAD wurin Layla.. Ya gabatar da kanshi a matsayin wanda yake sonta and ya nemi sanin sunan ta da kuma inda gidansu yake.

Ita dai Layla a wannan lokacin da ta qare mishi kallo tas ta kula babu alamun wadata a tattare da shi.. burin ta tayi mu’amala da masu kudi, ta auri mai kudi amma wannan din bata san ya aka yi ta ji tana so ta dan saurare shi ba..1

Ta sani sarai bazata dade da shi ba don kuwa ba kalar ta bane haka kuma bazata iya korar shi ba don haka ne ta amince da buqatar shi.. ta sa ran ko banza zata samu na Jan baki a wurin shi.

Ba tare da bata lokaci ba kuwa ya buqaci lambar wayar ta amma ta fadi mishi bata da waya don haka ne ta bashi lambar Mamanta. (dama dai Umman Ameera ce tayi musu alqawarin zata siya musu waya idan sun ci jarabawar su)

A cikin torchlight phone dinshi yayi saving sannan yayi mata sallama ba tare da ya kalli Ameera ba.2

Suna kallon shi ya tsallaka ya koma wurin da ya faka mashin dinshi ya hau ya tada.. Aikuwa sai da suka firgita ganin yadda ya fizgi mashin din kamar wani dan koyo..

Layla tsaki tayi tana yaba kyan shi amma tana kushe yanayin shi wanda ya tabbatar mata da lallai talaka ne.

Ameera wadda bata daina kallon shi ba har sai da ya bace mata ce take yi mata wa’azi kamar kullum akan ta daina wulaqanta mutane saboda basu da wadata.. bata san me Allah zai mayar da su ba a gaba amma kamar kullum sai ta hau ta da fada har suka tare adaidaita suka shiga..

A ranar kuwa har suka isa gida Layla tana ta yi ma Ameera masifa.. Daga baya ma haquri ta bata sannan ta ja bakinta tayi shiru.

☆☆☆☆☆☆☆

Tun daga wannan ranan kuwa Zayd ya fara zuwa gidan su Layla..

Da farko ya samu Abba ne ya nemi izini a wurin shi.. Abba dai tunda ya ga yanayin hankali da natsuwar shi ya yaba qwarai.. Zayd yayi mishi bayanin cewar Iyayen shi da qannen shi suna can qauye a garin Kano, shi kuma sana’a ta kawo shi garin Kaduna… sannan yayi mishi bayanin ya kammala karatun shi kuma yana kan neman aiki ne. Abba dai ya bashi izinin ya cigaba da zuwa wurin Layla sannan ya sanya mishi albarka.

Ita dai Layla ta fahimci cewar Zayd baya aikin komai.. a yadda ya fadi mata dai ya gama karatun shi amma kuma bai samu aikin yi ba don haka ‘yar buga-buga yake yi.. Layla ta sani cewar talaka ne shiyasa bata wani sakar mishi fuska amma sam hakan bai dame shi ba, A kullum yana cikin qara jaddada mata irin son da yake yi mata.. Sossai yake bata haushi na yadda baya da aikin yi sai zubo kalaman soyayya kamar soyayya ce za’a ci.

Sai ta roqe shi ya kawo mata abu sau biyar da qyar yake samu ya kawo mata sau daya. A kullum ji take yi kamar ta kore shi ta huta amma kuma sai ta kasa.

A wannan lokacin Layla bata da samari dayawa sannan yawancin su duk tagajan-tagajan ne shiyasa ma take ta maneji da Zayd din tunda ko banza shi yana ma da kyau… don kuwa duk yadda take jin kanta Ya fi ta kyau nesa ba kusa ba.

A bangaren Ameera dai tun daga ranar da ta dora idanuwan ta akan Zayd ya kwanta mata a rai sossai.. Dukda bata taba yin soyayya ba, bata taba sanin ya take ba amma ta sani sarai son Zayd take yi.. Mutumin da ko kallonta bai yi ba, bai ma san ta ba sannan bai san tana yi ba.. Saurayin ‘yar uwarta Layla wadda ko alama bata ma damu da shi ba.. wadda a kullum idan yayi sallama qofar gidan su da fushi da zage-zage take fita.

Roqon Allah ta dinga yi akan ya cire mata son maso wani daga zuciyarta amma sam abin ma sai gaba yake yi.. A kullum idan Layla tana zagin Zayd sossai zuciyar Ameera take quna.. Haka duk abinda ya kawo mata sai ta raina, sun sha yin fada da ita a duk lokacin da zata fadi mata gaskiya.

Zayd dai yana ta zuwa wurin Layla.. watarana ya tafi cikin dadi watarana kuma ya tafi cikin bacin rai. Ita kuwa Ameera a kullum ji take yi dama itace Layla, dama ita ce Zayd yake so haka don kuwa bala’in son shi take yi!

Bayan dan lokaci ne Admission dinsu ya fito inda suka samu gurbi a KASU zasu karanta Economics.. Layla dai ta zabi course iri daya da Ameera ne saboda ta dinga kwasar amsa when the need arises.. ta tabbatar idan tana tare da Ameera toh batada matsala… (amma fa ko kadan bata qaunar ta)3

Ko da suka tashi yin registration dinsu Umman Ameera ce ta cika kudin domin kuwa kudin yayi yawa sannan Abban su bayada isassun kudi a dalilin ya biya ma su Suleiman school fees dinsu su ma. Dama dai Kullum ita take rufa mishi asiri idan bayada kudi shiyasa yake kiranta ‘yar aljannah.

A yanzu haka akwai wata qawar Layla mai suna Bilkisu zata yi aure shine ta nuna ma Zayd anko din bikin don ya siyo mata shine ya siyo mata roba-roba tana ta zagin shi as usual.

Kamar kullum idan ta zage shi a gaban Ameera sossai ran ta yake baci.. ita dai Allah ya sani Ameera tana son Zayd. If only he knows how much she cares about him but unfortunately Layla yake so kuma bai ma san ta ba.. Sau daya ta taba ganin shi amma hoton shi yana nan maqale a zuciyarta…2

Ta tabbatar ma ba lallai bane idan ya ganta a kan hanya ya gane ta tunda ko ranar da ta fara ganin shi bai kalle ta ba…

♤♤♤Kwance take a kan gadon dakin Mamanta yayinda suke ta hira.+

“Wallahi Mama wai kawai sai ya kawo mun roba-roba. toh ni yanzu ya zanyi?? dagaske idan na je bikin da wannan atamfar qawayena zasu gane”

“toh ba sai ki fasa zuwa bikin ba.. ni dai na fadi miki bani da kudin da zan baki na anko.. kin sani sarai Umman su Ameera ce mai qoqarin dinka muku kaya”

Layla ta turo baki tace “toh wai ke Mama meyasa bakya sana’a irin yadda Umma take yi?? na tabbatar..”2

Kafin ta qarasa maganarta kuwa Umma ta kai hannu zata make ta yayinda tayi saurin kaucewa.

“Dan ubanki ni zaki gaya ma maganar banza? wato ni malalaciya ce kenan kike nufi ko me??”2

“kiyi haquri Mama, ba haka nake nufi ba fa”

Mama tayi tsaki sannan tace “dama kin tashi tsaye kin bude idanuwan ki kin nemo samarin arziki wadanda zaki mora ba irin wadannan sakarkarun ba.. A yadda kike kyakyawa haka bana so kina sauraron talakawa.. So nake ki shiga manyan mutane wadanda zaki mori arziki har nima in samu. Bazan so ki tashi a cikin maneji sannan ki qare a talauci ba”

Layla tana murmushi tace “kar ki damu Mama, ni fa dama na riga na tsara komai.. jira nake kawai in fara zuwa KASU inda zan hadu da mutane.. zan samu qawaye masu arziki da samari masu kudi”

“da kyau Layla ta… Allah yayi miki albarka” cewar mama

Qwanqwaso qofar dakin akayi yayinda Mama tace “waye??”

“Aliyu ne” ya fada cike da tsoro.

“me kake yi mun a qofar daki??”

“dama Umma ce tace in fadi miki an gama abinci”

“toh na ji”

Bayan yayi tafiyar shi ne Layla ta miqe tare da fadin “yauwa, wallahi dama yunwa nake ji.. bari in je in ga abinda ta dafa”

☆☆☆☆☆☆☆

A lokacin da Layla ta shigo kicin din ta tarar da Ameera tana ta qoqarin tsaftace kicin din yayinda Ummanta take zuba ma su Suleiman abinci.

A kullum dama idan har Ameera tana gida tana bin Ummanta su shiga kicin tare.. Hatta su Suleiman tare da su ake shiga kicin din.. dukda ba wani abu suke yi ba haka kawai suna son kasancewa da Umman su Ameera. wani lokaci ma ji suke yi dama ita ce mahaifiyarsu.

Tun Maman su tana masifa akan su daina shige ma Umma har ta gaji ta qyale su.. dama su maza basu da baqin hali sossai irin wannan.

A yanzu haka Ameera babu kalan abincin da bata iya ba. A kullum idan sun gama sai Ameera ta gyara kicin din sannan take daukan abincin ta.

“ina abinci na???” Layla ta tambaya cikin gadara.

Ran Ameera ya baci matuqa na yadda Layla tayi maganar.. ai ko babu komai dai yakamata tayi ma Umman ta sannu da aiki sannan.

“Haba Ya Layla.. yanzu kawai daga shigowar ki sai ki kama tambayar abinci bazaki ko yi ma Umma sannu da aiki ba???” cewar Ameera

“ban gane in ce mata sannu da aiki ba.. toh dama wai ba girkinta bane?? she is supposed to cook for us ai” Layla ta fada ba tare da tunanin rashin dacewa furta kalaman da tayi ba.

STORY CONTINUES BELOW

“Haka ma zaki ce??..”

“Me ke faruwa ne???” suka jiyo muryar Mama daga bakin qofa.

Layla ta fashe da kuka ta nufi wurin Mamanta tace “Mama kin ga Ameera tana ta zagi na don kawai na zo in dauki abinci na..”

“Ni?? Ya Layla yaushe na zage ki??? kawai fa cewa nayi…”

“rufe mun bakin ki a nan wurin.. baqar banza kawai mai baqin hali. Haka kawai kin tsani yarinya ta saboda kin ga ta fi ki kyau.. don uwarki ba ubanta ya kawo abincin ba?? Akan wane dalili zaki zagar mun ita?? toh wallahi ki kiyaye ni”

“Mama wallahi Ya Ameera bata zage ta ba..” cewar Suleiman.

“Rufe mun baki shashasha kawai.. duk an asirce ku kun daina ganin uwarku da daraja.. sakarkarun banza kawai”

Ita dai Umma tana jin su bata ce komai ba… Asali ma bayan ta gama zuzzuba abincin wucewa tayi ta bar kicin din yayinda ta bar Ameera tana share hawayen fuskarta.2

Hakan ba qaramin haushi ya ba Mama ba.. ta so ace Umma ta tanka ta don ta ji dadin fadin maganganu amma sai ta ga sabanin haka.

Tsaki tayi tace “je ki dauki abincin ki wuce mu tafi..”

Layla ta je ta dauko abincinta sannan ta bi ta gaban Ameera harda yi mata gwalo sannan suka wuce suka fita.

Anan suka bar Ameera tana ta goge hawayenta yayinda su Suleiman suke ta bata haquri.

Munnir ma har cewa yayi “wallahi Mama da Ya Layla basu kyautawa.. sai Allah ya saka muku”

Shi kam Aliyu dama idan irin haka ta faru baya magana amma fa da ka kalli fuskar shi zaka ga tsananin bacin rai.. idanuwan shi rinewa sukeyi su koma ja yayinda yake ji kamar yayi ma Layla dukan tsiya.

Banda don Abba da tsaya tsaye akan tarbiyar yaran da ba qaramin rashin kunya Layla zata janyo ma kanta ba daga wurin qannen nata.

Ameera da Aliyu dai sun sani sarai ko dukan su Mama zata yi Umman su bata cewa komai.. sun rasa dalilin da ya sanya bata magana.

A haka dai ‘yan mazan suka lallashi Ameera yayinda suka taya ta qarasa aikin sannan duk suka dauko abincin su suka fita.

☆☆☆☆☆☆☆☆

Zaune take a kan gadonta tana lissafin kudaden da za’a kai mata bank.

Kudaden dubu ashirin da biyar ne.

Ameera ce tayi sallama ta shigo dakin ranta a bace ta haye kan gadon Ummanta tace “Amma Umma meyasa idan Mama tana yi mana fada tana zagin mu baki cewa komai? kina nan fa komai ya faru”

Umma wadda ta gama lissafa kudadenta ce ta zuba a leda sannan ta ajiye a gefe ta miqe ta shiga bathroom dinta ta wanke hannunta ta dawo.

Zama tayi a kan gadon ta janyo Ameera jikinta ta rungume.

“Ameera na ga dukkanin abinda ya faru.. kuma nayi shiru ne ba don ina tsoron yin magana ba sai don gudun abinda zai iya biyowa baya idan nayi magana.. Kar ki manta ina zaune tare da matan nan tsawon shekaru goma sha bakwai da watanni.. babu halinta da ban sani ba. A tunaninki me ya sanya na iya zama tsawon wadannan shekarun tare da ita?? HAQURI. Shi komai na zaman duniya dan haquri ne.. Komai mai wucewa ne. Abubuwan da take yi mun a da sun fi wannan muni, da ace ina biye mata da yanzu ta kashe ni da baqin ciki..”

“toh amma Umma meyasa take kirana baqa mai baqin hali?? me nayi mata da kullum zata dinga..”

Umma tayi saurin rufe mata baki tace “Ameera ina so ki dinga yin haquri da dukkanin abubuwan da suke faruwa, kiyi haquri da abubuwan da ake yi miki a cikin gidan nan.. Babu abinda kika yi mata, tsanar da tayi mun ne ya sauka kan ku. Ko kadan baki da baqin hali kuma duk wanda yace baki da kyau qarya yake yi.. ke kyakyawa ce Ameera. Don kina da Baqar fata bai zama cewar ke mummuna bace.. Kowa da irin kyan da Allah yayi mishi, wani kyan a bayyane yake sannan wani a boye. Kina da hali mai kyau kuma ina alfahari da kasancewar ki ‘ya ta. Ina so ki riqe halayen ki masu kyau sannan ki qara da haquri.. Mai haquri yakan dafa dutse har ma ya sha romon. Ina so ko bayan rai na…”

STORY CONTINUES BELOW

Da sauri Ameera ta tashi zaune ta rungume Ummanta gam yayinda hawaye suka wanke mata fuska tace “don Allah Umma ki daina fadin wannan maganar.. bazaki mutu ba”

Umma tana murmushi ta rungume ‘yarta tace “banda abinki Ameera Mafificin halitta ma Allah ya dauki ranshi balle mu?? babu wanda bazai mutu ba.. kowa lokaci yake jira.. fatan mu Allah ya kyautata qarshen mu ya sa mu cika da imani”

Tayi breaking hug din sannan ta share mata hawayen ta tace “yanzu dai mu bar wannan maganar..” ta janyo ledar kudaden da ta gama lissafawa tace “Gobe idan Allah ya kai mu zaki kai mun wadannan kudin banki.. Gwara in dinga tara miki kudi yadda idan maganar auren ki ya taso zan rage ma mahaifin ku wani nauyin.. “

Zuciyar Ameera ta buga da jin wannan zancen.. Babu wanda tayi picturing a matsayin mijinta sai ZAYD a wannan lokacin. Allah ya sani bata shirya yin aure ba a yanzu amma kuma ta tabbatar da Zayd zai ce tana sonta kuma yace suyi aure she will be more than glad and very much ready!!

Hmmm… Mutumin da bai ma san ta ba!!

Ajiyar zuciya ta saki sannan ta bata rai tace “ni kam Umma kiyi ta tara kudin ki don ba yanzu zanyi aure ba..”

“ban gane ba yanzu zakiyi aure ba.. shekarun ki goma sha bakwai yanzu Ameera. Zan so kiyi aure da wuri don in ga ‘yan jikoki na kafin in tafi”

“Umma don Allah ki bar fadin zaki tafi… insha Allah muna nan tare da ke”

“toh Allah yasa Ameera..”

A haka dai suka cigaba da hira kala-kala.

☆☆☆☆☆☆☆

Wuraren qarfe takwas na dare Ameera, Ibrahim, Suleiman, Munnir da Aliyu suna zaune a falo suna kallon Indian film.

Tuni Ameera ta koya ma yaran kallon India.. a yanzu har sun fara jin yaren kuma suna yi. Tun suna yi Ameera tana gyara musu har suka iya sossai.

Layla ce ta fito daga dakin su sanye cikin wata doguwar riga irin ta zaman gida dinnan. Rigar ta bi jikinta tayi mata kyau sossai.. Ta kama gashin kanta wanda ya sha gyara a tsakiya.. In all she looked so beautiful.

Kujerar da take kusa da ta Munnir ta zauna. Fuskarta a tamke tace “kai bani remote”

Gaba dayan su suka juyo suka kalle ta cike da mamaki.

Suleiman ne yace “Haba Ya Layla, mun fa kusa gama kallon nan.. ten minutes fa kawai ya rage..”

“Rashin kunya zaku yi mun?? ina wasa da ku??”

Ita dai Ameera shiru tayi tana sauraron su. Ta sani cewar Layla tana jira ne tayi magana don ta samu damar zagin ta… Ita dama Ameera a wuri biyu ne take sa ma Layla baki. Na daya akan rashin kunyar da take yi ma Umman ta sannan na biyu akan wulaqancin da take yi ma Zayd.

Wayar Layla ce tayi ringing yayinda ta duba. Wani mugun tsaki ta buga da ganin sunan shi a kan fuskar wayar.

Zayd

Sai da ta kusa gama ringing ne tayi answering a wulaqance.

Ji suka yi tace “mun fita tare da Mama” can ta dan yi shiru sannan tace “a’a wallahi kar ka jira mu don ba yanzu zamu dawo ba.. kawai ka yi tafiyarka”

Gani suka yi ta kashe wayar tana fadin “Ni kam wallahi yau bazan fita in sha sanyin banza ba.. mutum ko mota baka da shi kullum sai zama kan dakali”

Ni kuwa nace dayake ubanki yana da motar ba mashin yake hawa ba…4

Su Suleiman dai shiru suka yi basu ce komai ba.. Sossai suka tsani halayen Layla.. Gwara ma su uwar su daya. Shi Aliyu ma wani lokaci ji yake kamar ya shaqeta ta mutu ya huta.

Ameera wadda take sauraronta sossai ran ta ya baci.. Ji tayi kamar ta kwashe Layla da mari. Ya ma za’ayi ta samu namiji kamar Zayd ta dinga wulaqantawa.. A yau da Zayd zai bude baki yace yana sonta she will no doubt be the most happiest woman on earth.. idan kuwa yace ta aure shi ai sai ta suma don farin ciki.. Talaka ne shi ta sani amma ita duk wannan ba matsalarta bane.. Ita kam shi kadai take so.

Ranta a bace ta miqe zata wuce daki.

“Ya Ameera ba’a gama film din ba zaki tafi?” cewar Munnir

“Kai na ya fara ciwo Munnir.. idan an gama zaku bani labari”

“Ke dai ba wani nan, ran ki ne ya baci saboda na zagi Zayd a gaban ki.. Sannu uwar Zayd. Da kin taimaka mishi kin je kun yi hirar tunda na san yana nan a wajen bai riga ya tafi ba” Layla ta fadi tana dariya.5

Ameera dai ko juyowa bata yi ba balle ta kalle ta.

Zuciyarta tana ta zafi ta shige daki ta fada kan gado tana kuka. Ita ta fara damuwa da yadda take jin mugun haushi a duk lokacin da Layla ta wulaqanta Zayd.. mutumin da bai ma san ta ba, bai ma san tana yi ba.

Shin wacce irin fitinaniyar soyayya ce wannan?? A kullum soyayyar shi qaruwa take yi a zuciyarta.. shin hakan daidai ne?? Mutumin da ta taba gani sau daya amma kuma hoton fuskar shi na nan maqale a zuciyarta…

What is going on????5

♤♤♤♤♤A yau satin su uku da fara zuwa KASU. Kamar yadda na fadi muku ajin Layla daya da Ameera.+

Mai adaidaitan su yake kai su sannan ya dauko su. Da zarar sun shiga makarantar kuwa Layla da Ameera suke kasancewa tamkar ba daga gida daya suke ba.

Layla dai tun ranar farko da suka fara zuwa tayi screening ‘yan ajin gaba daya.. tuni ta gano clique din manyan yara.. don haka ba tare da bata lokaci ba ta shige musu. Da ganin Layla dai ka san ba ‘yar mai kudi bace amma kuma a dalilin bala’in kyan ta sai ta samu shigewa cikin su.

A yanzu haka clique dinsu su Hudu ne- Haleema (leema), Maryam (Mari), Yusrah (Yussy) sai ita Layla.

☆☆☆☆☆☆☆

HALEEMA IDRIS BUNGUDU: Mahaifinta Alhaji Idris Bungudu shine mamallakin IB Oil and Gas Nig. Ltd. Shahararren Oil and gas company dinnan wanda yayi fice wurin shigowa da fitar da mai a qasar nan.. Alhaji Idris yana da kudi sossai domin kuwa babu state din da babu gidan man shi a arewacin Nigeria. Haleema wadda aka fi sani da Leema ita kadai ce ‘yar shi don haka ta taso cikin gata.. Babu abinda ta nema a rayuwarta ta rasa.. Haka kuma duk abinda take so tana samu. Sossai iyayen ta suka sangarta ta- they never say No to her. Da farko dai iyayen Haleema sun tura ta qasar America ne don tayi karatun jami’ar ta a can amma da zuwan ta wata daya aka kira mahaifinta ya zo ya tafi da ita saboda she was disregarding the school’s moral ethics… Ko da aka mayar da ita Qasar Ingila nan ma haka.. Taurin kan bala’in Haleema ya hana ta zama.. Babu dama ka ce mata tayi abinda bata son yi… Da wannan ne mahaifinta ya dawo da ita Nigeria.. Da farko ya so ya sa ta Nile ko Baze a Abuja amma tace ta fi son KASU.. ta fadi hakan ne saboda ta raina ma makarantar, ta sani cewar zata iya yin duk abinda take so sannan ta taka duk wanda ta ga dama tunda dai Money speaks for her and mahaifinta made sure of it. Tunda ta shiga KASU kuwa sai ta ga dama take shiga class din, Haka lecturer bai isa yace mata tayi wani abu ba don kuwa babu wanda bai san she is untouchable ba. Haleema tana da manyan samari masu kudi.. Irin samarin nan da suke ji da kansu, irin spoilt brats dinnan… Haleema har party tana zuwa.. sai ta kwana a waje ba tare da iyayen ta sun damu ba. Yanzu haka tana da motocin hawa har guda uku and shekarunta Goma sha tara.

MARYAM SANI DAURA: Marainiya ce, iyayenta sun rasu tun tana qarama.. Ta girma a hannun babban yayan ta Mansir Sani Daura Manajan Banki a nan Kaduna. Iyayen su kafin su rasu sun tara dukiya mai yawa domin kuwa sunyi aiki a World bank na qasar Ingila tsawon shekaru. A dalilin tausayin Maryam da yake yi shiyasa yake yi mata duk wani abinda take so. Babu laifi Maryam tana da hankali, tana da qoqari a makaranta sannan tana girmama na gaba da ita. Wannan ne ya sa matar yayan ta take jin dadin zama da ita. Ta saba da familyn yayan ta sossai shiyasa ko da ta gama secondary school da yayanta yace ta zabi duk qasar da take son yin karatun jami’arta sai ta ce ta fi son KASU. Ta fi so ta cigaba da zama tare da su. Da wannan ne ta shiga KASU din. Maryam wadda aka fi sani da Mari dai tana mingling da Haleema ne ba don komai ba sai don Social class din su da ya kusa zama iri daya amma ba don hali ba.. Asali Haleema da Maryam are two different personalities.. Kusan a dalilin Maryam da Yusrah ne ma Haleema take shiga class. Maryam tana da motar hawa sannan shekarun ta goma sha takwas a yanzu. Tana da saurayinta mai suna Khalil Muhammad Bicci wanda yake karatun Law a qasar Ingila.. tuni maganar su ta kai wurin manya don haka jira kawai ake yi ya kammala idan ya dawo ayi bikin su.

STORY CONTINUES BELOW

YUSRAH SADIQ: Yusrah wadda aka fi sani da Yussy ta tashi a gidan mijin mahaifiyarta ne. Mahaifin ta ya rasu tun lokacin tana shekara hudu don haka ne mahaifiyarta ta sake yin aure.. ta auri Alhaji Musa Kyari Babban ma’aikaci a NNPC na Abuja. Dayake mai kudi ne ya dauki Yusrah a matsayin ‘yar shi sannan ya dauki nauyin duk wani expenses dinta.. Matan shi guda uku ne, First wife dinshi tana zaune a Maiduguri yayinda second din take Abuja sai ita mahaifiyar Yusrah ta zabi ta zauna a Kaduna saboda business dinta da take yi anan.. Tana da qaton shago na siyar da gwala-gwalai wadanda ake shigo mata da su daga qasar saudiyya. Yusrah ta taso cikin qannen ta maza guda biyu Muhseen da Mahmood wadanda mahaifiyarta ta haifa tare da Alhaji Musa Kyari. Mahaifiyarsu ta sa business dinta a gaba ne kawai domin kuwa gaba daya ta sakar ma masu aiki kula da yaran nata.. Sun taso basu san soyayyar uwa ba amma fa duk abinda suke so komai tsadan shi idan dai kudi na siyan shi to fa zata siya musu shi… Dukda Daddynsu ba wani zuwa yake yi sossai ba tunda yana da wasu matan sun fi son shi fiye da ita kuma sun fi sabawa da shi.. Babu restrictions a gidan amma dukda haka yaran sun san limit dinsu when it comes to iskanci. dayake a cikin masu aikin gidan akwai wadda ta dinga koya musu karatun addini tun suna yara sossai suka girma da tsoron Allah a zuciya. Shekarun Yusrah Goma sha bakwai don haka ne step father dinta ya hana ta fara tuqa mota.. Ya bata personal driver wanda zai dinga kai ta duk inda take so har zuwa lokacin da zata kai shekara Goma sha takwas. Ita ma Yusrah babu laifi tana da qoqari.. she is an average student. Mijin mahaifiyarta yana da policy na babu wani yaron shi da zai yi karatu a qasar waje don haka sai dai ka zabi kowacce makaranta ce a cikin Nigeria.. Ganin haka ne Yusrah ta zabi KASU tunda babu nisa da gidan su sannan qawarta Maryam Sani Daura ma can ta zaba. Yusrah da Maryam sun kasance qawaye tun kafin su shigo KASU don kuwa secondary school daya suka yi. Da suka shigo KASU ne suka hadu da Haleema sai daga baya Layla and they formed a clique. A yanzu haka Yusrah batada saurayi.. ko kadan ta qi ta saurare su, a cewarta ba soyayya bace a gaban ta.

Haleema, Maryam da Yusrah kyawawan yara ne amma ko kadan basu kai Layla ba… Layla ta fi su kyau nesa ba kusa ba, ta fi su body mai kyau sannan ga unique eye color dinta wanda duk KASU babu mai irin shi. Kyanta ya sanya suka janyo ta cikin su don ta qara haskaka su.. afterall su basu damu da social class dinta ba.

☆☆☆☆☆☆☆☆

Ameera on the other hand harkar gabanta kawai take yi.. Da farko ma babu ruwanta da kowa. Kullum zaka gan ta zaune a gaban class tana sauraron lecturer yayinda ake lecture.. A duk qarshen lecture kuwa idan lecturer yayi tambaya ko neman qarin bayani akan abinda daliban suka fahimta a darasin da ya koyar zaka ji muryar Ameera.. Idan ta fara magana zaka ji ‘yan ajin sunyi shiru suna sauraron ta, sossai take birge lecturers da daliban.. Ba tare da bata lokaci ba aka bata class rep na ajin don kuwa she knows what she is doing and she is very good.

Akwai wata a ajin wadda take sanya Hijab mai suna Zarah Aminu.. Shiru-shiru ce don kuwa bata cika magana da kowa ba.. Abinda dai ‘yan ajin suka kula da shi shine babbar yarinya ce don kuwa tana zuwa da manyan motoci daban daban.. Haka kuma a yadda suka fahimta kamar matar aure ce but still babu wanda ya tabbatar. One thing is for sure, ana respecting dinta a ajin sossai.

Zarah dai tunda ta ga Ameera ta ji tana sonta don haka ne tayi qoqarin zama close to her dukda ta kula Ameera bata cika son mutane ba but a dalilin nace mata da tayi dole suka zama friends..

Wannan kenan!!

☆☆☆☆☆☆☆☆☆

A yau bayan an gama first lecture wasu sun fita don hutawa a garden, wasu kuma don su ci abinci a cafeteria yayinda wasu suke zaune a class ana ta hira, wasu kuma suna qoqarin kammala Assignment din da aka basu.

Haleema wadda take tsaye a gaban qawayenta ce tace “babes please ku zo mu je Caf, wallahi yunwa nake ji”

“Leema kin cika cin tsiya I swear  yanzu kina nufin baki yi breakfast ba kika fito??” cewar Maryam

STORY CONTINUES BELOW

Halima ta harare ta tace “Mari take time ooo.. dagaske na yi breakfast amma wannan uban zaman da muka sha yanzu ai ya ci ace cikin mutum ya zazzage.. Ni fa wallahi banda don kun matsa mun in zauna lecture dinnan da ban zauna ba… Lecture awa biyu??? ina laifin minti talatin??”

“ashe ba ni kadai na tsani lecture din ba” cewar Layla.

Maryam tana dariya tace “Allah ya shirye ku.. ni dai kiyi haquri bazan je ba don wallahi ban gama assignment dina ba.. I need to complete it”

Layla ce ta fiddo nata assignment din tace “gashi kiyi copying.. ni nayi”

Cike da mamaki suka kalle ta.

“Like seriously??? how comes? wa yayi miki? don fa wallahi na san baki iya ba” Yusrah ta fada.

Layla tana dariya tace “My step sister..” ta nuna musu Ameera wadda take zaune a can gaba tare da qawarta Zarah.

Gaba dayan su suka juya suka kalli Ameera yayinda Maryam tace “wai dama dagaske class rep sister dinki ce?”

“Step-sister, Yeah Mari. Infact abinda ya sa na zabi course iri daya da ita saboda in dinga zama kusa da ita a examz.. Abba yace idan nayi failing examz aure zai yi mun”

Gaba dayan su suka fashe da dariya yayinda Maryam tace “aikuwa muma zamu dinga zama kusa da ku don muyi copying wanda bamu iya ba”

Haleema ta tabe fuska tace “ku kenan ma da kuka dan san abinda kuke yi.. ni kam don Allah ku zo ku raka ni in ci abinci”

Layla ta miqe tace “mu je in raka ki..”

Yusrah da Maryam kuwa tuni sun bude assignment din Layla sun fara copying wanda basu yi ba.

A lokacin da Layla da Haleema suka wuce ta gaban su Ameera zasu fita ne Zarah tace “wai dagaske Layla sister dinki ce???”

Ameera tayi murmushi tace “yeah.. my step sister”

“I am sorry to say this.. gaskiya I dont like her at all. She is beautiful and all amma I dont like her personality”

Murmushi Ameera tayi tace “maganar gaskiya, I dont nima, especially because of abubuwan da take yi ma Ya Zayd”

“waye shi???”

“Her boyfriend”

“toh ke meye matsalar ki da su??”

“My problem is that I love him and she doesn’t..”

“What????” Zarah ta fada cike da mamaki. Hakan kuwa sai da ya sanya wasu suka juyo suka kalle ta.. probably the first time some of them are even hearing her voice.

Itama waigawa tayi ta ga ana kallon su yayinda ta kalli Ameera tace “har kin sa ana kallo na. biko tell me, ya akayi haka?”

Ameera ta fara bata labarin haduwar su da Zayd da yadda Layla take wulaqanta shi da kuma yadda take ji a zuciyarta a duk lokacin da Laylar ta wulaqanta shi…

“I swear Zarah I love him very much amma bai san ina yi ba.. ko kallo na bai yi ba ranar.. he just walked pass me like I was invisible”4

Ta share hawayen da suka fara gangarowa daga idanuwanta tace “saboda ni bani da kyau, ni baqa ce sannan ina sanye cikin hijabi shiyasa bai kalle ni ba, saboda Ya Layla tana da kyau, fara ce, tana da beautiful body, beautiful eyes and…”

“hey stop it..” Zarah ta dakatar da ita.

“who told you baki da kyau?? wa ya fadi miki cewar everything is about physical appearance.. He must even be a fool to have not noticed a beautiful soul like you..”

“from what you just told me yanzu ma I am sure yana bata lokacin shi ne a wurin Layla don kuwa I doubt zata aure shi.. abinda nake so da ke shine ki dage da addu’a Allah ya zaba miki mafi alkhairi.. idan har Zayd mijin ki ne zaki aure shi..”

Ameera tace “nagode qawa ta”

“but I swear I cant believe cewar yadda yake talaka kuma kike son shi sossai..”

Ameera ta girgiza kai tace “Zarah bazaki gane bane, ni fa a rayuwa abinda na dauka talauci shine wanda bazai iya ciyar da kanshi ba ko ya tufatar da kanshi, wanda bazai iya samun wurin da zai kira gida ba.. that is talauci. Ya Zayd fa ba talaka bane tunda yana iya qoqarin shi ya nemi na kanshi, yana ciyar da kanshi yana tufatar da kanshi and he has a roof over his head… He even has a bike which is a form of luxury and not a necessity.. Baki san wani abu ba, buri na a rayuwa shine in auri namiji wanda zai so ni tsakani da Allah ya nuna mun zallar soyayya sannan ya bani dukkan kulawar shi.. my husband’s love and attention is all I need.. Bana son auren mai kudi wanda zai aure ni ya ajiye ni a gida yayi tafiyarshi tsawon lokaci ba tare da ya damu da ni ba.. I prefer true love and care than money. I have always lived a simple life and I want to continue living that way”

Zarah dai sakin baki tayi tana kallon Ameera da yadda take magana babu alamar wasa a ciki.. Sossai tayi mamakin jin hakan daga bakinta don kuwa bata taba sanin a zamani nan akwai mace wadda zata ce bata son auren mai arziki ba.. ita kanta a lokacin da ta auri Mustapha bata san Status dinshi ba toh amma soyayyar da suka qulla ta gaskiya ce don haka ko daga baya da suka yi aure ta gane ko shi waye it never really affected their relationship.. a yanzu haka he travels alot but they are still good. Ita Ameera da alama idea din mai kudin ne ma bata so, it doesn’t even matter ko ta samu soyayyar, a dalilin rashin zaman shi dole ne bazata samu irin kulawar da take so ba…

ZAF… shine ya fado ma Zarah a rai!

“hmmm.. har kin sa na tuno ZAF, shima yana nan ya dage akan cewar he is still searching for his true love kuma yayi ma kanshi alqawarin duk inda take sai ya nemo ta.. mace yake nema wadda zata so shi tsakani da Allah ba don wani abu ba”

Ameera wadda ta zama confused ce tace “ZAF kuma?? waye ZAF??”

Zarah ta dan yi murmushi tace “Best friend din miji na ne.. Shima sunan shi Zayd, Yana nan ya dage akan yana neman True love, The last time da muka yi zancen I remember him saying that zai yi dedicating plenty of his time to find his true love.. the time that he doesn’t even have, I wonder how he will do it”8

Ameera ta girgiza kai tace “wai dagaske Zarah ke matar aure ce? ni fa kawai nayi zaton kin fadi hakan ne saboda baki so samari suna bibiyar ki”

Zarah ta fashe da dariya tace “I am married Ameera.. ba qarya nake ba. Wata na biyar kenan da yin aure..”3

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *