UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 5 BY SHATU

UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 5 BY SHATU

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

Tunda muka sauke su Ammah a kasuwa, motar ta Yi shiru se da muka koma hanya kafin love birds din ciki Suka isheni da lovey dovey din su. Se na ayyana kenan haka nake damun Rayha ni da Dr Bature? Tuno shi da nayi se naji I’m missing him, da tuni ni ce zaune gaban mota munata Hira, Ammi ta kirashi tace Kar yazo akwai me kawo mu, shiyasa Bai zo ba. Ganin da gaske sun manta Dani cikin motar Dan Yaya Fahad na tambayar ta wai wanne suna zasu sakawa first daughter dinsu,jin haka yasa nayi murmushi na janyo littafin physics Dina Ina Kara solving linear expansion. Muna zuwa Bakori Yaya Fahad ya tambaye mu ko zamu wuce Funtua muga Baba, cikin sauri nace+

” A’a mu tafi school kawai’

Tunda muka dawo hutun sau daya kawai yaje Gumel ya ganmu, tun muna tambayar Ammi yaushe Baba zai zo har dukkanku muka hakura, saboda na lura idan muka tambaye ta tayar Mata da hankali muke, Ina fata wannan sabuwar rayuwar da zata fara ya kawo Mata farin ciki da nutsuwa a ciki. Yaya Fahad ya kaimu school kafin a Gama clearing dinmu Sega Dr Bature ya iso, Ina hango shi na saki murmushi nace

“Oyoyo!”

Harara ta yayi mikawa Yaya Fahad hannu sukai musabaha yace

” I’m Bature!”

Se shi Kuma yace

” Fahad”

Suka gaisa muka gaishe shi sannan ya fito da teller dinmu da sauran expenses na makaranta da Baba ya bashi ya kawo. Ammi da kanta tayi Mana provision Shima Kuma yayi mana yadda ya Saba Mana harda Kari ma, bansan me yasa tayi ba ko kuma tsoro take kada yaki Yi. Yaya Fahad ya wuce cashier desk din Dan Gama Mana komai, na tsaya ni da doctor yace

” Potential graduate! Ki nemana bakiyi”

Nayi murmushi nace

” Naga tunda ka tafi baka kirani ba”

Na fada Ina langwabar da kaina, yayi murmushi yace

” To ai Kinga baki da waya, Kuma ni bazan ta Kiran Ammi Ina damunta ba ko”

Se nayi shiru kafin nace

” To ai da munyi graduating Baba zai siya Mana waya, so we can talk about everything ko?”

Ya gyada Kai yace

” Ni Zan saya Miki ma kafin ya saya Miki”

Na girgiza Kai, muka taba Hira har aka zo aka Gama muka tafi hostel.

Ammi da Ammah Suka Gama siyayya tsaf a kasuwa, sannan Yaya Fahad ya dakko su ya dawo dasu Gumel, Kaya masu kyau Yan saffasaffa, bazaiyi baki taba business ba Dan Zaki fara ki saka duka abinda kike dashi, ya kamata ki fara duba mutanen da kike tare dasu meye suke bukata, meye ake wahalar samu a gurin kafin kiyi supplying. Ammah ta Mata register da wani online Female enterprenuer Wanda suke tallata maka hajar ka. In takaice muku komai went smoothly a ranar, Ammi ta fara kasuwancin dashi zai dauke Mata hankali.

A hankali rayuwa ta tafi, lokuta Suka cigaba da shudewa, lokacin yin JAMB yayi muka tafi Kano nan ne center dinmu ta yin JAMB din, Baba da yaushe rabon mu ganshi shi yazo ya dauke mu ya kaimu gidan Ummaah. Tunda muka gaishe shi bamu Kara magana ba se tsakanin mu ni da Rayha muke magana. Shi ma lokaci lokaci Yana amsa waya Wanda na fahimci da Anty Rumasa’u yake magana, Dan Yana ta fada Mata a inda muke. Kullum Rana addua nake Allah ya kawo ranar da zanga karshen Anty Rumasa’u, nasan ba kowanne hukunci Allah ya keyi a duniya ba, wata shariar se a lahira, Ina tsoron kada Baba ya mutu cikin halin da ya ke ciki Babu shakka zai tashi bangaren shi daya a shanye saboda ya aura Mata biyu baiyi adalci tsakanin su ba. Dukda kowa na cewa asiri akai Masa dukda haka dama tun kafin ta samu tayi asirin ya fara daukar Hanya, ya fara nuna Mana ita ce Mata uwar mu ba mace bace, ba tada daraja a gurin shi. Tun da Baba yayi parking na hango Yaya Ismail tsaye a balcony dauke da coke Yana Sha, nayi saurin dauke kaina Dan na manta dashi, fitowa mukai nace

STORY CONTINUES BELOW

” Baba sannu”

Ya gyada Kai sannan mukai ciki, Ummaah na parlor a zaune, ta harder tana zuba mulki, muka zauna a kasan carpet muka gaishe ta, tana dauke da murmushi ta amsa tana kallon Baba tace

” Ashe yaran nawa sun girma,ko Dan lokaci fa yayi”

Baba yayi murmushi suka gaisa, tasa aka kaimu dakin da muke sauka idan min zo, duk yawancin yaranta sunyi aure Yaya ramlah kawai ta rage Kuma tana London tana karatu, se maza da suke zaune da yaran Yan uwan baban su. Ni na fara wanka sannan Rayha ta shiga. Ina zaune Ina tunanin me zamu saka a jikin mu se gashi an kawo Mana Kaya, na saka gown din na koma kan gado na zauna Ina taje gashin kaina, inada gashi, banbanci na da Rayha kenan, ita ta fini kyau ta fini haske ni Kuma na fita gashi. Na taje kan duk ya zubo fuskata, na sunkuyar da kaina Dan na samu na taje tsakiyar kan, turo kofar akai, duk tunani na Memuna Mai aikin Ummaah ce Amma se hancina ya fara jiyo min sassanyan kamshin turaren da jikin Yaya Ismail na taba jin shi, hakan yasa nayi saurin girgiza kaina Dan gashin ya koma baya, dukda haka akwai Wanda suke a gaban fuskar tawa Basu gama komawa bayan ba Amma a hakan na ganshi tsaye ya canja Kaya zuwa jallabiya black, se sheki take. Band Dina na sa na Kama gashin sannan nace

” Yaya Ismail wannan dakin Mata ne fa”

Yayi murmushi yace

” I never knew haka kike da gashi, I so much love it!”

Na Bata fuska na Mike na saka hula kaina sannan na nufi kofa, tsorona kada Rayha ta fito da towel ta gan shi tsaye. Nufar shi nayi ya faminci fita zanyi se kawai ya fita, Nima na bi bayan shi na tsaya a corridor nace

” Yaya Ismail”

Ya dage min girar shi Yana jiran na Fadi menene, nace

” Ka daina shigo Mana daki”

Ina fadar haka na juya Zan koma cikin, se naji palms dinsa masu sanyi akan wrist Dina, da sauri na juyo na kalli hannun mu sannan na kalleshi nace

” Sake min hannu!”

A lokacin gani nayi ya Dan zaro idanu, yayi saurin sakin hannun nawa ya Dan ja baya saboda yadda nayi maganar so domineering, akwai traces na anger a ciki.

” Sofiyya!”

Banma jira abinda zai ce ba nayi shigewa ta, ban Kara fitowa ba ko lokacin da aka aika mu fito Ummaah zata fita nace kaina na ciwo Rayha tace karatu take. Sega Ummaah ta hayo saman Dan dama Bata Hawa saboda ciwon kafa, Ina kwance na takure Ina duba English PQ na JAMB, yayinda Rayha ke zaune tana kallo.

” Baku gaji da zaman shirun ba, ku zo muje saboda ku Zan fita fa dan ku ga gari”

Haka muka Mike muka bi bayanta, Yaya Ismail ne zaune gaban mota, Ummaah ta sani na zauna gefen shi sannan Suka Shiga baya itada Rayha, muna fita gate Sega motar Anty jidda, ta leko tace

” Yaran Ammi ne!”

Yadda ta fada tana tabe baki muka gaishe ta, ta amsa sannan ta dubi Ummaah tace ta sakko magana zasuyi, haka ta Mika masa credit card dinta tace Mana se mun dawo. Tunda muka dauki hanya nake kallon kyakyawawan titun da Suka kawata jahar Kano, flyovers da underground passage masu kyau. Chickenza ya fara kaimu sannan muka je sahad yace mu zaba duk abinda muke so, Rayha ta dauka perfs ni Kuma na wuce wajen books na jida, Yana tsaye yana kallona seda na gama sawa cikin cart yace Mana

” Shi kenan?”

Nace

” Eh”

Da kanshi ya fara tura cart din ya dinga jido Mana sweets dasu chocolate, se perfs da ya siya min, da ribbons da man gashi, nayi murmushi a raina nace eh lallai kana son gashi. Daga nan se ya kaimu masarautar su gidan kakkanin shi, kamar Yar kauye haka na sake baki Ina kallon ancient buildings da aka zamanin ta su. Har bayan maghrib sannan muka dawo. A Hanya nace

” Yaya Ismail can I use your phone?”

Yace

” Sure!”

Tareda Miko min wata Samsung dinsa me kyau. Number Ammi nayi dialing Babu jimawa ta dauka, tana jin muryata ta sake jikin ta munata Hira sannan na bawa Rayha, tace muyi addua itama tana Yi Mana, sannan muyi hakuri da duk yadda rayuwa zata zo Mana. Bayan mun gama wayar na fara dialing number Dr Bature Shima ya dauka nace

” Doctor!”

Daga bangaren yace

” Sofy! How are you?”

Ina murmushi nace

” I’m fine”

Kafin ya bani amsa naji an zare wayar daga kunnena, na dago na kalleshi fuskar shi a murtuke, ya kalleni yace

” How dare you use my phone ki Kira wani useless whosoever you call him?”

Na Bata Rai na juya kaina, yace

” Kinsan Ina son ki me yasa kike acting dumb?”

Na kalleshi dukda I was expecting hakan Amma banyi tunanin zai fada da wurwuri haka ba. Nayi murmushi a raina nace lokaci yayi da zanyi laying cards dina a table!!!Na Kara kallon motocin nasu sannan nayi murmushi, Dan a raina nasan dukkansu sunyi zuwan banza. Gurin Yaya Fahad na fara zuwa na bude bayan motar na zura paper bag din hannuna sannan na gaishe shi, baima lura Dani ba Dan gimbiyar shi na gaban shi. Inda Dr Bature yake na nufa Ina kallo Yana duba agogon dake daure tsintsinyar hannun shi. Da murmushi nace+

” Ka gaji?”

Yayi saurin dagowa yace

” Ni bance ba, I was scanning my eyes Naga ta inda Zaki bullo”

Nayi murmushi Wanda indai Muna tare na dinga yi kenan bansan dalili ba, duk lokacin da muke tare se naji I’m Happy, Ina jin yanayin yafi kowanne dadi da tsayawa a Rai, lokuta da dama nakan zauna Ina rewinding maganganun da mukai sede kawai na dinga murmushi ni daya kamar tababba!

” Tunanin me kikeyi?”

Ya fada yana waving hannunshi akan fuskata, nayi saurin girgiza Kai nace

” Baba ne yace kazo? Yaya Fahad already yazo ha Yaya Ismail ma”

Se ya gyada Kai yace

” Oh baisan zasu zo ba shiyasa yace nazo, yaje Zaria ne”

Nace Masa I see sannan na raka shi inda Yaya Ismail yake zaune cikin motar shi, tunda muka taho na fara jin karfin idanun shi a kaina, Amma Bai dameni ba hirar mu kawai muke nida doctor har muka karasa. Dan knocking nayi a window, yayi wining din shi kasa nace

” Yaya Ismail!”

Ya Dan yatsina fuska sannan ya fito, ya mikawa Bature hannu Suka gaisa, ni nayi introducing din su ma junan su, kafin nace

” I’m sorry duka kunzo, Yaya Fahad already yazo”

Bature yace Babu matsala Bari yaje su gaisa da Fahad din kafin ya wuce, ya tafi na dubeshi nace

” Why did you come unannounced? Kasan Baba zai turo a dauke mu ko”

Maimaikon ya amsa tambayar Dana Masa se yace

” Who’s that guy I don’t like him!”

Nayi saurin dariya nace

” Ba Dole se kaso kowa ba, beside Shima he’ll not like you”

Ya Dan karkato kanshi daidai kunnena yace

” I’m not here to impress anyone but you”

Na tabe baki na Yi gaba abuna, da sauri ya kulle motar ya biyoni, muna zuwa Bature yayi Mana sallama ya tafi, na Kara binshi na barsu da Ismail dake ma Fahad korafin me yasa zai zo daukar mu duk ya Bata Masa plan din shi, yasan Kuma bazan taba binshi ni daya ba. Seda ya daidaita seat belt dinsa kafin ya Miko min karamar leda da kwali a ciki, na kalleshi Ina girgiza Kai, se ya zare min idanu da yasa nayi dariya na karba, Shima yayi dariya yace

” As I promised ni Zan fara saya Miki waya. Gata nan komai is set a ciki”

Na kalleshi na kalla wayan na rungume ta a kirjina Ina kallon shi se Naga ya lumshe idanun shi nace

” Thank you so much! Amma me yasa ka saya min Baba zai saya Mana fa”

Ya danyi murmushi yace

” Na sani wannan shi ne gift dina gareki, kije ku tafi karki dare”

Na gyada Kai na na Kara Masa godiya sannan mukai sallama ya tafi. Ina zuwa na azalzali Yaya Fahad akan mu tafi, ai Yaya Ismail yace Shima nan zai bar motarsa ya Kira wani mutum anan malumfashi zai zo ya Kai Masa Kano, nayi tsaki na shige Bayan motar ya biyoni ya zauna gefena, hakan Yaya Fahad da Rayha na dariyar fushin nawa Suka shiga muka dauka hanya. Duk yadda yake kokarin Jana da Hira naki bashi hadin Kai, se ya kyaleni but I can sense the disappointment a yanayin shi. Hannun shi ya kai kan paper bag dinnan zai bude nayi saurin dauke wa nace

STORY CONTINUES BELOW

” Wai menene?”

Yace

” Ba Kya Sona har yanzun?”

Maganganun shi mostly na Yara ne, na Bata rai nace

” Da nace Ina sonka ne?”

Se ya gyada kanshi kawai Bai Kara cewa komai ba se idanun shi daya lumshe kamar me bacci, Nima na juyar da kaina gefe Ina ayyana kamar bana kyautawa abinda nake Masa, shi ba laifin shi bane haifar shi da Ummaah tayi, to me yasa Zan dauki laifin uwarshi na daura Masa, na saki siririn tsaki da yasa shi kallona. Na ayyana to shi dinnne yayi ta damun mutum ni na riga na fada masa bana son shi Kuma bana tunanin akwai abinda zai saka na so shi din. Seda muka iso Kano muka sauke shi Bayan min kaishi gida Amma bamu Shiga ba Dan Yaya Fahad yace Masa sauri yake, muka dauka hanyar Gumel dake Shima gudu ne dashi tuni muka iso gida. Na shaki iska bayan na fito nayi murmushi Ina ayyana yanzun se maganar wani abin Kuma an gama zancen wani secondary School!

Ammi na parlor tayi bakuwa parlon nan cike da atamfofi dasu laces an babbaje su matar Baeta zaba. likafa ta cigaba, dama tunda tazo visiting ta fada Mana har ta Kama babban shago a plazan dake tsakiyar Gumel, tayi naming gurin ARE YOU THE BRIDE?  Ni Bata shawarar fara sayar da kayan amare daga masu sauki har masu tsada saboda yanzun kowa Yana bukatar saka me kyau idan zaiyi aure Kuma zuwa Kano ya danyi nisa. Matar muka gaida tana fadin Masha Allah wai munyi Mata kyau, aka shigo da kayan mu se kawai muka Shiga wanka. Kafin mu fito Ammi ta gama hada Mana abinci, itada Yaya Fahad muka same shi Yana zaune suna Hira. Na fito na fara daukar meatpie din na Kai bakina, nace

” Ammi ya Anisah?’

Tace

” Anisah na school shekaran jiya naje”

Na zauna Ina ayyano Anisah a school, tana js1 a Adams academy dake majiya. Mun Sha Hira har dare na nunawa Ammi wayar da Dr Bature ya bani dukda Ina tsoron kada tayi fada Amma seda na nuna Mata ta karba infinix ce me kyau ta dauki wayar ta ta kirashi tana korafin bayan wahalar kaimu da dakko mu Kuma harda ta waya, se naji tayi mishi godiya. Bayan mun Gama tace na Kira Baba na fada Masa, na Kira shi yace to ya gode Shima ending week zasu zo. Nace Allah ya kaimu!

Har Zan kwanta na tuna sakon da na karbo wajen TD teacher, da sauri na dakko jakar na zazzage ta, greeting card na fara saka hannuna akai, a jiki an rubuta congratulations Love, se academy cap da Dan ribbon. Ina budewa idanuna yaci Karo da Usman Dikko can karkashin card din. Na saka hannuna Ina tracing sunan deep in thought, Bai mantani ba kenan, na ayyana sannan na dauka books din da ya sako wajen 10 copies se chocolate da Pringles a ciki, bansan me yasa indai zaimin kyauta se ya saka Pringles a ciki ba dukda nasan ban taba fada Masa Ina so ba. Se wasu frames masu kyau da motivational quote a rubuce. Study room Dina naje na jera su sannan na aje frames din, na dauki daya a cikin books din na koma bedroom din mu, Rayha ta dauki wayar ta ta fara waya a raina nace kilan yarinyar nan kawai aure zatayi b zatayi karatu ba, Dan yadda suke itada Yaya Fahad abin tsoro yake bani.

A weekend Baba ya dawo, tunda duka munada waya se Bai saya Mana ba instead ya siya Mana dankunne. Ammi yasa na Kira Masa dake daki tace nace Masa tana zuwa. Zan fita yace na zauna se na zauna dama tuntuni ita Rayha na zaune. Ammi na zuwa ta zauna kujerar dake facing din shi, ya kalleni yace

” Uwarku ta Zama me kudi! Ganin ta ma se anyi cikecike”

Nayi Dan murmushi bance komai ba, ita kuwa fuskarta Babu annuri ta zauna, se yace

” Na tambaya Rayhana da gaske tana son Fahad ta Kuma amsa min da eh. Naso ace zatayi karatu Amma Kuma kamar yadda na Miki bayani Fahad ya samu admission a Quwait zai tafi da ita itama tayi karatun ta acan”

Ammi tace

” Babu damuwa mun Gama maganar da Hajiya Hannatu, Allah ya Sanya alkhairi”

Yace

” Amin”

Na kalla Rayha dake danne murnar ta, na danyi murmushi Ina musu fatan alkhairi. Baba yace

” Sofy!”

Na dube shi nace

” Naam Baba!”

Yace

“Ko kema kina son na biya Miki ki fita kiyi karatun?”

Nayi saurin girgiza kaina Ina murmushi nace

” A’a Baba. Zan zauna anan nayi Allah ya Sanya alkhairi”

Mukai musu sallama na koma daki na tarar wayata na ringing, Bature na kirana. Na zauna na dauka wayar ya tambayeni yadda nake sannan muka danyi Hira kadan sannan mukai sallama. Na juyo na dubi Rayhana nace

” Amarya! Amarsu I’m so happy zakiyi aure”

Na rungume ta and I felt heartbroken se kawai na fara kuka, Itama ta fara kuka nace

” Ki daina kuka, I’m overwhelmed ne zanyi missing dinki, ban taba kawowa zamu rabu so soon hakan ba”

Tayi Dan murmushi tace

” Ki yarda Dan Allah muje Quwait din tare”

Na buga kanta da Wasa nace

” Dama kinsan da maganar Kika boye min kenan?”

Tace cikin damuwa

” Nasan na fada Miki Dole Zaki damu shiyasa na rufe Miki”

Nace

” Allah ya Sanya alkhairi. We’ll throw a huge wadding”

Se muka koma hirar yadda bikin zai kasance, inata farin ciki bana jin wai dama ni ce saboda idanuna kawai hango ni yake a jamia. Muna fita Baba ya ware kudin da zaa siya Mata komai na furniture da kayan kitchen idan ta dawo tunda yanzun ba Zama zatayi ba.

Ban taba tunanin Yana da fada ba, saboda yadda yake girman Kai ne kawai abinda zaka fara fahimta kenan. Yayi fada har muka iso gida, uffan ban ce masa ba seda yayi parking na fara kokarin dakko Kaya yace+
“Keep them, zaa shigo dasu”
Bance komai ba kuwa na nufi parlor, Rayha na dariya kasakasa na Harare ta nace
” Munafuka! Kiyi dariyar ki Mana”
Tana dariyar tace
” Kece ai, kinsan abinda yake nufi Amma kikai provoking din shi”
Nayi murmushi ban Bata amsa ba saboda isowar mu parlon Ummaah, suna zaune itada Anty jidda, Bayan duk awoyinnan ko mayafinta Bata cire ba, a raina nace anata kulla sharri kenan. Zama mukai muka gaishe su, Ummaah na tambayar mu yadda fitar ta kasance muka ce Mata mun ji dadi mun gode. Har zamu koma sama nace Mata
” Ummaah gobe karfe takwas zanyi jarabawar”
Ta gyada Kai tace
” Allah ya bada saa Ismail Zak raka ki”
Ba hakan naso ba Amma hakan Zan hakura, na wuce bayan munyi sallama da Anty jidda dake Mana kashedin saura mu ki zuwa gidan ta, a raina nace se kace yayanta na zuwa namu gidan ne. Muna karsawa daki na kwanta, Rayha tace
” Ba zamu je gidanta ba wallahi, munafuka”
Nayi murmushi nace
” Rayha ki rabani da zagin da kike ma dangin Baba Babu ruwana”
Tayi tsaki bayan ta gama cire kayan ta tace
” Yunwa nake ji, Bari na sauka na kawo Mana abinci”
Na gyada Mata kai ta sauka, ni Kuma na Yi wanka sannan na fito na samu Bata dawo ba, se kawai na shirya, Ina Zama naji anyi knocking kafin nayi magana kofar an bude ta, Yaya Ismail ya shigo, na Bata fuska tareda dauke kaina na mayar kan tv dake aiki, gefe ya samu ya zauna tareda hade hannayen shi biyu yace
” I’m sorry I shouted at you”
Bance komai ba na janyo littafi Dan fara karantawa se ya taso zai dawo inda nake, abinda na fahimta dashi Bai dauki body contact matsayin wani laifi ba, ganin zai taho yasa nace
” Karka zo! Just stay inda kake”
He comply, ya koma ya zauna ya marairaice fuska yace
” I love you…”
Zai cigaba da magana na katse shi da fadin
” Karatu zanyi fa”
Yayi shiru na Yan sakanni Yana kallona kafin ya sauke ajiyar zuciya ya fara kallon TV din, shigowar Rayha da tray yasa ya Mike ya aje min wayar shi yace
” In case you need it. Zan kiraki”
Bance Masa komai ba ya fita, na dauki wayar nayi dialing contact din Ammi tana dauka muka fara waya Ina fada Mata duk abinda ya faru a ranar. Rayha ta karba tace
” Ammi kinyi suruki fa”
Saboda yadda muke da Ammi, yadda take janmu a jiki yasa bama kunyar fada Mata komai, we believe Ammi kawar mu ce, Bata da Wanda zatayi Hira dasu se mu din dai, mu ne sanyin idaniyar ta!
” Wallahi Ammi wai Yaya Ismail ke sonta, Amma kinsan ba zata taba yarda tayi camping da enemies dinki ba”
Ina kurban tea Ina murmushi, Rayha ko banyi magana ba tasan me nake nufi tasan bazan taba yarda da zancen Ismail ba Amma a kasan raina I’m using him to avenge abinda akaiwa Ammi. Bayan mun Gama da Ammi ta Kira Yaya Fahad sunata hira ni Kuma Ina karatu.
Washegari very early na Gama shiryawa, tea kadai Nasha na fita, Yaya Ismail na jirana a mota muka tafi center Dina, muna zuwa baifi 30 mins ba muka Shiga, tabbas nasan nayi karatu, tunda na durkusar da kaina Banda solving da clicking Babu abinda nake, in less than an hour na Gama, na Kara komawa na dudduba sannan nayi submit na fito, I felt relaxed se adduar nasara kawai dake bakina. Tunda ya hangoni ya fara sakar min murmushi, na danyi yake Dan nasan ba murmushi nayi ba, Ina bude gefen shi na zauna ya Miko min chilled freshyo, kamar yasan Abu me sanyi nake bukata na amsa tareda Masa godiya na fara Sha, yace min a hankali kamar yadda maganar tashi take, yafi wata macen sanyin murya
” How was the test”
” Alhamdulillah!’
Na bashi amsa Ina aje bottle din hannuna,se mukai shiru se can yace
” Me kike planning bayan secondary?”
Na Dan kalleshi nace
” Nothing special! Karatu zanyi”
Ya Dan langwabar da kan shi yace
” Ki Bari muyi aure I promise you Zan kaiki duk inda kike…”
Nayi saurin katse shi nace
” No! Baba ma bazai yimin aure yanzun ba, karatu zanyi gaskiya. Beside ni bana sonka”
Seda na fada sannan naji maganar ta yimin nauyi a harshe na, you can’t take back the word that’s already out! Dan haka na Bata Rai na dauke kaina, ya Jima in shock din me na fada kafin yace
” Sofy just give me chance I’ll prove myself!”
Daga haka bamu Kara magana ba har muka karaso gida, Muna shiga nayi breakfast Dan shi daki ya wuce, Nima na Gama na wuce daki bayan munyi Hira da Rayha na fara baccin gajiya. Tunda ya Shiga daki Bai fito ba se Bayan azahar, Ummaah na ganin shi tace
” Me ya sameka haka?”
Ya zauna gefenta Yana Dan tura baki yace
” Tace Bata Sona fa!”
Ummaah tayi dariya tace
” Shi ne abin tashin hankalin, rabu da ita itama yarinta me damun ta, ka Bata lokaci”
Lokaci zai fada idan yarinta ce ke damuna ko kuma akan Hanya nake. Kwana biyu muka Kara Rayha tayi tata sannan Ismail ya maida mu, shopping din da mukai na bashi books nace ya aika min su Gumel. Na bude kofar Zan fita yasa hannunshi ya riko nawa, na saurin juyawa nace
” Ka manta?”
Ya sakeni Yana murmushi yace
” Mantawa nayi. Tafiya zakiyi ba Zaki yadda ba?”
Na girgiza Kai nace
” Spare me! Allah ya kiyaye Hanya mun gode sosae”
Na zura kafata kasa na fita ko juyawa banyi ba saboda na fara jin zuciyata kamar zata ji tausayin shi, idan na Bari ta yimin hakan to tayi betraying dina. A hostel muka aje Kaya , bamu Kara kwana biyu ba JAMB ta sake results Kuma munci Rayha nada 220 ni Kuma 260 haka mukai. Ranaku na tafiya muka fara waec na rage bacci se karatu Yan class dinmu suyi ta tsokana ta Amma Ina ruwana ni karatuna nake. A hakan muka gama, bamuje gida ba se visiting Ammi ta zo Mana itada Baba, ba wani magana suke ba Amma Ina hango canji a tattare da ita, ta Kara Zama babbar mace ko daga maganar ta na fahimci nutsuwar da take dashi.
Mun fara neco Babu jimawa itama mukai muka Gama, Ina kan paper karshe TD teacher yace idan na Gama na sameshi, Muna fitowa se murna muke Muna exchanging contact mun Gama secondary School, na samu na wuce office din shi kafin Baba yazo Dan jiya munyi waya dashi yace zaizo ya dauke mu. Na gaishe shi ya min murna dukda banyi TD ba Amma malamai da yawa sun sani matsayin Senior prefect sannan yawancin haduwata da mutane karatu nake. Na mishi godiya sannan ya bude locker dake kusurwan office din shi ya ciro katuwar paper bag ya Mika min yace
” Idan kin samu time se ki duba, I wish you all the best”
Na mishi godiya na fito, Ina tunanin me ya hadani dashi da zai min kyauta har haka, na cigaba da tafiya Ina jin nauyin jakar tareda tunani kalakala. Can na wuce inda wasu har sun fara tafiya, motar yaya Ismail na fara hangowa sannan se ta Dr Bature, daga gefe na hango Na’ila da Rayha tsaye jikin motar yaya Fahad, nayi murmushi Ina ayyana waye zai dauke mu?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *