UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 8 BY SHATU
Www.bankinhausanovels.com.ng
Ayaan! Ayaan!!”
Ta Shiga fada a firgice, Baba dake gefenta ya Mike tareda saka wayar shi ya haske fuskarta, gaba ta jike da gumi, kafafunta dake a kannanade se shura su take, haka hannunta da take ta mikawa alamar Ayaan din take son kamawa, wani takaici ya lullube Baba yaji tamkar ya dada Mata duka, ya girgiza kai tareda saka hannun shi ya bubbuga kafadar ta, tayi saurin bude idanunta a gigice, tasa hannunta ta dafe goshinta Jim yadda ruwa yake diga kawai se ta fara sharce gumi tareda kallon Baba dake gefenta, bakinta se rawa yake tace
” Mafarki nayi! Wai…”
Tsaki kawai yayi ya juya baya yayi kwanciyar shi, idanunta ta zaro cikeda mamaki tace
” Likita magana nake maka fa, na tsorata fa Amma ka juya min baya”
” Me kike so na Miki? Dare ne Dan Allah ki barni nayi bacci”
Daga haka ya kashe flash light din wayar shi ya juya Mata baya da niyyar komawa bacci,a wasu lokutan baka sanin komai ya lalace maka se ya Gama kwabewa kafin kake ankarewa, to Anty Rumasa’u is a victim, ta hadiyi yawu tareda kallon Baba dake kwance haka duhu ya mamaye dakin, take mafarkin ta ya fara dawo Mata, se take ganin kamar sarkar da aka sakale ta da ita, ita ce ake nufo ta da ita, wata Kara ta saki tana kankame Baba, mikewa yayi ya janye ta daga jikin shi sannan ya dauki wayar shi da pillow ya bar Mata dakin, wayatta ta laluba ta kunna se ta saki ajiyar zuciya Amma duk da hakan a firgice take, a haka ta kwanta tana tunanin me ya faru Baba yayi Mata hakan, bawai wannan shi ne Karo na farko da ta fara ihu cikin dare ba, idan zata tuna hakan ma ya zame Mata jiki kullum cikin mafarkai take masu ban tsoro, Kuma duk lokacin da hakan ta faru to shi zai zauna tare da ita, har zuwa lokacin da zata nutsu, to me ya faru yau Kuma.
Washegari saboda Bata Yi baccin kirki ba se ta kwanta tana ta bacci har Ayaan ta gama shiryawa haka Baba suka fita Amma tana bacci. Se can wajen daya sannan ta tashi, ta mike ta Dan gyara gidan itama mutum ce me tsafta, ta gyara gidan sannan ta shiga kitchen ta daura abinci, ta Jima zaune tana tunanin abinda ya faru cikin dare, har shinakafar dake kan wuta ta fara kamawa sannan tayi snapping daga tunanin da take, ta juye cikin warmer sannan ta koma parlor ta dauki wayar ta ta fara Kiran mahaifiyar ta, Mama Altinne tana dauka tace
” Mama Kinga ban daina mafarkan ba”
Ko gaisawa basuyi ba, Mama Altinne tace
” Kinje kin duba binnin da kikai?”
Ta girgiza Kai tace Mata zataje ta duba sannan zata kirata, tana aje wayar ta nufi can Bayan bangaren Ammi inda anan ne ta binne kayan Tsubbin nata, tana zuwa gurin taji gabanta ya Fadi saboda tsiron da komai sun bushe, ta dafe cikin ta ta zaro Ido ta Kai hannunta ta fara hako gurin Amma komai ya bushe se bibbige, juyawa tayi ta koma ta dauki wayatta ta Kira Mama
” Komai ya bushe, Kuma wallahi Mama duk bayan kwana biyu se na bawa abin ruwa, ko shekaran jiya ma haka!”
Maman tace
” Ikon Allah! To Amma ba ciki ya shiga jikin ki ba?”
Anty Rumasa’u ta shafa cikin ta tace
” Eh Mama ciki ne dani wata daya”
Wani ashar ta kunduma Mata tace
” Ke mahaukaciyar Ina ce da Zaki cire implant din, to ki sani kiyi hanzarin cire cikinnan!”
” Haba Mama kina kallo shekarar Ayaan bakwai ban Kara haihuwa ba, ni dai haihuwa nake so, gashi babanta ya canja min, dazun kamar zai mareni cikin dare!”
” Kadan Kika gani, matsawar baki cire cikin ba kin dinga ganin bakin ciki kenan. Ke kanki kinsan yace ciki da wannan aikin ba zasu hadu ba, kwana nawa ya rage ki Bari yace ki samu ciki Bayan yace a wañnan auspicious time din Zaki Haifa namiji”
” Nidai Mama kawai ki Nemo min mafita, wallahi idanun Likita dazun ba karamin tsorata ni yayi ba, kamar yasan abinda nake aikatawa Kuma cikin jikina bazan iya fitar dashi ba”
A bangaren Anty jidda ta Gama hada duk wani Abu da take ganin zai kaita ga ci ta Kuma kawar da duk abinda zai kawo Mata obstruction. Wata kawarta Hajiya Laila ita ke Kara zuga ta tana Kara Hira Kai. A bangaren Hanifa Bata San abinda uwarta ke shiryawa ba, ranar Friday ta shirya cikin fitted gown wadda hannunta da kirjin ta duka net ne, rigar tamkar a jikin ta aka dinka, ta dauki katon hijab ta saka sannan ta hada kayan da zatai amfani dashi cikin jakar ta ta fito ta dubi Amira dake zaune a parlor tace
” Idan Mom ta fito kice mata zanje get together”
Amira ta dubeta tace
” To meye Kika zumbula hijab, tsoron wancan tababben kike?”
Hanifa tayi dariya tace
” Baki ji me Kika ce ba tababbe, yanzun se yace zai dakeni Kuma Mom Babu yadda zatayi”
Daga Mata hijab tayi Suka kwashe da dariya, Amira tace
” Abasu kala Yar gidana”
Daga haka ta fice, Haruna shi ne babban yayan su da suke uba daya, mahaifiyar su ita ce matar baban su ta farko da ta rasu se ya auri Anty jidda, da tazo seda ta baza su, su uku uwar su ta Haifa, Haruna, Mubarak se autar su Asiya, wadda azabar Anty jidda ta sa ta koma Danbatta dangin babanta, yanzun haka tayi aure harda yaranta, Mubarak shi Kuma kamar Anty jidda din ce ta haife shi yayi blending sosae da life style dinsu shiyasa Amira ke shiri dashi, shi kuwa Haruna makiyi kenan, tababbe suke ce Masa saboda Yana tsare su.
Driver na hango ta ya taso ta Shiga ba tareda ta yiwa Haruna magana ba Shima kokarin alwalar sallar maghrib yake se ya kyaleta ta gama ai zata dawo ta sameshi. Seda ya kaita zoo road tayi makeup ta cire hijab aka Mata dauri kamar amarya ta saka jewelry sannan ta fito Suka nufi Chicken republic inda akai reserving na yin get together, tana Shiga ta samu Wanda shigar su tafi tata rashin mutunci, Amma itama ba baya ba.
Se wajen Sha daya sannan ta dawo gida, tunda driver yayi parking tana fitowa wannan Karan da ainahin shigar data fita da ita, Dan Bata Yi tunanin zai jira har ta dawo ba, tana fitowa ya karaso Yana kallonta kasa da sama yace
” Daga Ina kike?”
Ta mishi banza ta nufi cikin gida har tana hardewa saboda kada ya kamo ta, kyaleta yayi har ta Shiga parlon Babu kowa Dan haka ta lallaba ta shiga dakin su, Amira na zaune tana waya, ganin ta ta kashe tace
” Kin dade, Abba yazo nemanki”
Tayi tsaki tace
” Rabu dashi, wallahi abubuwa sukai zafi bansan dare yayi ba”
Ta gyada Kai tareda karbar wayar tana kallon hotunan da sukai, tana ta squeeling na murnar kyau. Washegari Anty jidda ta shigo ta dubesu tace
” Haneey Ina Kika je Kika Kai dare har wancan mahaukacin ya fadawa Babanku?”
Hanifa ta mirtsika idanu tace
” Get together naje, shi ya fiya saka Ido. Tukun ma Mom se yaushe zaayi auren ne?”
Tayi murmushi a ranta tace aiki yayi kyau kenan, tunda Suka je gurin malamin Hajiya Laila tace sede wata ba Hanifa ba. A wañnan ranar ta saka kwalli ta tafi gidan Ummaah, tunda suka hada Ido Ummaah ta fara fadin
” Jidda sannu fa, meye labari?”
Anty jidda tayi murmushi tace
” A aurawa Hanifa Ismail”
Ummaah tace
” Hakan yayi, nagode sosae. Yaushe kike son ayi auren?”
Tace
” Ending next month”
Ummaah tace angama, kafin kace meye wannan Shirin biki ya kankama sosae, kowa yaji zancen bikin se yayi mamaki, Ismail ya kirani Ina makaranta yake fada min, naji tausayin shi sosae saboda na fahimta pains din da yake ciki, na lallashe shi na nuna Masa tasa kaddarar kenan!