WANENE SHI
CHAPTER 4
Ta murda ta jijjiga, ba alamun kofar zata bude. Zuciyarta ta shiga dukan tara-tara don a cikin tunaninta ba zata iya tuna inda mukullan k’ofar nan suke ba, in ma suna nan din kenan.
“Akwai mutum anan?” Ta daga muryarta da karfi ta kira.
“Idan wani na jina dan Allah a bud’e kofar ta rufe dani.”
Shiru ba motsi, sai tashin kid’an waje da take jiyowa kawai daga nesa. Hannayenta dake rike da k’ofar suka shiga rawa, ta cigaba da tsayawa a wajen tana rarraba zuciyarta waje-wajen neman mafita, aikuwa take ta tuna da tagar dake cikin d’aki wadda zata fitar da ita jikin barandar saman, ta koma da sauri wajen ta shiga kokarin zura mukullin, sai dai bata kai ga sawa ba lokacin da hasken tvn bayanta ya sake kamawa, sannan muryoyin cartoon d’in dake magana da larabci ya karad’e ko’ina a d’akin
Ba shiri ta cusa mukullin ta murda sanna ta fad’a ciki, ta ture net d’in daya rufe tagar sannan ta dira waje, bata san cewa sauri take ba sai da ta kusa yin karo da wata mata dake kokarin shigowa gidan bayan ta sauka k’asa.
“Ke hankali mana, bakya gani ne?”
Bata ko bi ta kanta ba tayi cikin tururuwar mutanen ta nemi hanyar gate, kafin ta karasa kuwa ta hango Aminan na sake shigowa.
“Ke na taho dubawa fa, kin dad’e wallahi.”
“Yi hakuri.” Ta mika mata dankwalin da sauri.
“Toh shikenan sai jibin, Allah huta gajiya.”
“Ameen.” Ta amsa a hankali. Saboda saurin da Aminan keyi, bata ko lura da yadda jikinta yayi sanyi ba, ta d’an rungumeta kawai sannan ta juya
Daga nan mik’ewa tayi wajensu Inna, ta samu waje a gefenta ta zauna ta dunk’ule jikinta waje daya tana jinta wani iri, zuciyarta sai k’ara hasko mata da duk abinda ya faru take, tana ganin komai kamar Almara ko wani labari.
Bata kara tashi ba sai tare su innan, lokacin mutane sun fara tafiya, sannan cikin gidan ma an daddawo anata kacaniyar sallar isha, don cikin d’akinsu ma sanda suka shiga wasu ne ke ta sallar a falo. Sannan tvn a kashe.
“Nanne bud’e cikin d’akin muma mu dauro tamu alwalar.”
Muryar inna tasa ta kalli kofar d’akin dake k’ulle, wani yawo ya zarce cikin makogwaronta don ta san sanda ta bud’e bata ko tsaya rufewa ba ta fita, ya akayi yanzu take a rufe? Kawai sai ta matsa kusa da innan sosai tace.
“Inna akwai wanda keda muk’ullan d’akin nan ne bayan na wajenki?”
“Kamar k’ak’a? Da kika shigo kinga an d’auki wani abu ne? Shi yasa fa nace dake tun shekaranjiya ki maida duk wani abu mai amfani cikin d’aki saboda mutane ba kowa ne….”
“Inna ba wani abu aka dauka ba..” tayi saurin katseta kar mutanen gefensu suji.
“Toh menene?”Har ta bude baki zata ce wani abu kuma ta maida shi ta rufe, don bata san ta ina zata fara bayanin ba, irin wannan bayanin da ba kowa ne zai yarda ba, koda innan ce kuwa, don ita kanta a yanzu gani take kamar a tunaninta ne komai ya faru.
“Ba komai.” Ta juya ta bud’e kofar aka fara layin alwala.
Har tayi sallar ta saka kayan bacci tunanin abin nan bai fita daga ranta ba koda minti d’aya. Wata dattijuwa mai suna falmata ta taimaka ta d’auko mata bargo daga can saman wardrobe d’insu, ledarsa duk tayi kura ta kakkabe shi ta d’auko, sannan ta d’auki filonta ta fito falo
“Inna zanje wajen mama azumi acan zan kwana yau.”
“Saboda me? Ku uku ne ma fa yau kawai a d’akin, mu da kiga ganmu duk nan zamu yada kai mu kwanta.”
Kan ta amsa wata tsohuwa tace.
“keh rufa mana asiri kar daga zuwanmu ace mun kori ‘yar masu gida.”
Tayi guntun murmushi tace.
“Wallahi Gwaggo ba haka bane, can din kawai nake son kwanciya.”
“‘Yo ku kyaleta mana…” wata daga gefen inna ta karba.
“…Ran da muka zo nata bikin ai ba inda ta isa taje, sai mun ga dama ma zamu bawa angon.”
Suka kyalkyale da dariya gabadaya. A haka ta juya ta bar d’akin, don ta sa a ranta cewa ba zata kwana anan ba.
****
Washegari da akayi kamu, Nanne bata kara bari ta zama ita kad’ai a waje ba, saboda haka babu wani abu daya k’ara faruwa irin jiya. Sai dai kawai jikinta ba dadi, yayi wani irin shafal! tana jin kamar bacci take ji amma ko ta kwanta baya tab’a zuwa.
A haka har akayi kamun aka gama, da daddare ma ta sake d’ebo kayan kwanciyarta tayi d’akin su mama Azumi, sai dai a yau ta lura da kallon da inna ke mata, kallo irin na rashin yarda cewa k’in kwananta a d’akin ba don wani dalili bane
Washegari da rana wajen uku tana kwance a tsakiyarsu innan da wata Gwaggo ladi, a lokacin an fara shirye-shiryen tafiya wajen mother’s eve d’in, masu wanka da shiryawa nata yi. Aunty maryama ta shigo (D’aya daga cikin ‘ya’yan kanwar inna) tana kara rok’on su akan su shirya aje wajen event d’in dasu suma, inna ko ta dora daga inda ta tsaya a daren jiya, wai biki in ya wuce cikin gida ya koma party, su ko tsoffai-tsoffai dasu ba zasu party ba.
“…in banda abin su hajiya Babba suma ai ba inda ya kamata suje, wajen da akace surikanka maza zasu zo, me zai kai k’afarka?”
Nanne ta tab’e bakinta.
“Inna duk wannan abin fa kauyancin da ne, don kawai surikansu zasu zo sai suk’i zuwa bikin ‘ya’yansu? Kenan duk randa suka zo gaishe su har gida ma sai suk’i fitowa.”
Kan inna ta amsa gwaggo Ladi ta karb’e.
“Rabu da ‘ya’yan yanzu Ramatu, ba abinda zasu gane ai, abinda yanzu za’ayi auren yarinya washegari ta fito tsabar rashin ta ido? Ni sanda aka kaini d’akin miji sai da na shekara biyu cur! Sannan da yarsa ta haihu yace in shirya inbi ‘yanuwansa ranar suna, ke zo kiga farin ciki wankana uku a ranar nan.”
“Yo komai ai ya canja, bikin ma dai ana yinsa ne kawai, amma ace abu baza a fara ba sai bayan la’asar a dawo tsakar dare. A da biki ai tunda duku-duku maza na dawowa daga asuba zaku tafi aje a yini, da anyi sallar magriba kuma kowa ya dawo gida, kuyi abinku a mutunce. 1
Nanne tayi shiru tana sauraren hirarrakinsu, idonta na hasko mata komai da suke fad’a cikin nutsuwa. Doguwar riga ce a jikinta sai bata d’aura dankwalin ba kawai ta yafa shi, fuskarta tayi fayau! filon da take kwance na daga tsakiyarsu, sannan ta jawo jelar kitsonta d’aya tana kanannad’ewa da yatsunta. Zuwa can taji inna tace.
“ke baza ki soma shirin bane, an kusa la’asar fa.”
“Inna nayi wanka ai, kaya kawai zansa kuma sai Aminah tazo.”Suka juya suka cigaba da hirarsu.
Tun tana jinsu har bacci ya fara shirin d’ibanta a cikin hayaniyar d’akin, sai dai me? Ba zato ba tsammani kawai taji alamun wani abu kamar hannu mai taushi ya shafa fuskarta, tun daga farkon sumarta har zuwa gefen hab’arta. +
Ta bud’e ido da sauri ta dafe wajen, zuciyarta na bugawa ta d’ago ta kalli su inna ko sun lura da ita amma hankalinsu na kan kulolin abincin da ake shigowa dashi d’akin.
Ta shafa wajen taji yayi sanyi k’alau kamar an d’ora k’ank’ara. Kowacce jijiya ta jikinta ta shiga aiki, Ta kasa d’auke hannunta gabanta na cigaba da fad’uwa. 2
A lokacin ne abin ya faru.
Wannan muryar…wannan muryar mai taushi ta cika kunnuwanta.
“Kinyi kyau!”Wallahi Aminah da gaske nake miki a dakin nan k’ofa ta rufe dani tv tayi ta kunnuwa ita kad’ai, jiya kuma gaba d’aya jikina ba dadi, yadda kika san wata bugaggiya haka na koma, duk inda na samu waje in kwanta amma ba baccin. Sannan yanzu na gaya miki murya naji sosai ta min magana a cikin kaina.” +
Aminah tayi shiru zaune daga bakin gadon.
“Kuma kin tabbata ba wanda yaji maganar.”
“Ba wanda yaji, a cikin kunnena kawai naji ta fa, kamar irin nasa earpiece.”
Suka sake yin shiru gabad’ayansu.
“Me kike tunani?”
Kamar ba zata yi magana ba sai kuma tayi ajiyar zuciya tace.
“Anya sa’adha kina tunanin ba aljanun ne suke tsorata ki ba?”
Ta girgiza kanta da sauri.
“Ni dake fa mun san ba haka bane tunda pretending nayi, kawai dai ina tunanin wani abu ne daban.”
“Wani abu daban kamar me? Kin san dai mutane basa jin irin haka, kuma aljanu ne kawai zasu iya irin wannan abin.” ta sake girgiza kanta.
“Duk da haka gaskiya ba aljanu bane, bana ji a jikina hakan ya dangace su, sai dai wani abin daban.”
“A’ah, dama kuna nan?…” Aunty ni’imah ta shigo tana fad’a, biye da ita wasu matan ne guda biyu.
“Nanne baki shirya bama? An fara tafiya fa.”
“Yanzu zansa kayan.”
Suka juya suka fara kwalliya da d’aurin d’ankwali a gaban mudubi, suna yi suna hirar dangin mijin jamila da suka zo daga nijer a yau d’in. Aminah ta jawo wata leda a kusa da kafarta tace.
“Ga d’ankwalinki da mayafin.”
“Material d’in ya min kyau, ankon su waye?”
“Nasu hajiya Babba ne.” Ta amsa a tak’aice tana zaro rigar daga cikin wardrobe.
Kamar yadda yake a al’adarta, doguwar riga ce akayi da material d’in (lemon green&milk) mai bud’ewar umbrella da d’an karamin hannu. Ta saka sannan tayi d’auri mai kyau, ta yafa lemon green mayafin da Amina ta kawo mata a kafad’a, hoda kawai ta shafa da lip balm mai kyalli ta saka silver d’ankunne da abin hannu, amma tayi kyau sosai fuskarta tayi fresh da kuma kyau.
A wajen event d’in suka cigaba da tattauna matsalar, sai da Rahma tazo wajensu ne sannan suka yi shiru, don Nanne ta nuna bata so wani d’an gidansu yaji.
Wajen biyar da rabi Amaren suka shigo tare da Angwayensu, kowacce da irin kalar kayanta itada angonta. Jamila da take Babba ce ta fara shigowa itada zugar k’awaye da cousin d’inta masu anko, tayi shigar ash and black shima Angon nata yasa shadda ash da aikin black, sai wani d’add’age gira yake yana kallon mutane d’aid’ai. Abokansa mutum hud’u ne kawai a bayansu.
Nafisa da maryam su ankon Maroon colour suka yi duk su biyun kayansu iri d’aya, don dai su nuna cewa su ‘yan d’aki dayane, ‘yanmatansu masu ankon lace d’in da akace yafi na kowa suna farko da bayansu. Sunyi kyau sosai, don Angwayensu ma duk brown shadda suka sa amma kowa da aikinsa.
Kafin Aisha da Angonta su shigo sai da aka canja wak’a aka sa na step dance d’in ‘yanmatanta, su safiya da surrayya na ciki suna bin rawar kamar kowa, abin ya burge mutane yadda suke takawa a hankali, daga bayansu kuma Aisha ta shigo da nata Angon cikin kwalliyar Royal blue da milk, shima yasa milk shadda sai washe baki yake yana dariya.
Ga tarin abokansa a baya suna shigowa kamar baza su k’are, kafin su k’arasa wajen zamansu ya sunkuya ya rad’awa Aishan wani abu, aiko ta tuntsire da dariya tana sunkuyar da kai.
Duk wannan abin, Nanne bata ga ko d’aya ba, don tana zaune bata tashi ba, tunaninta gaba daya ya tafi wajen neman abinda ke damunta. Sai da suka gama zama Mc ya kiran masu bud’e taro da addu’a sannan tace dasu Aminah tana zuwa, ta mike tayi wajen fita, a hanyar ta had’u dasu Aunty maryama sun d’ebo jakunkunan souvenirs, kowannensu ya kama fad’an wai me yasa bata shiga tawagar su Aisha ba, ga anko a jikinta amma ta zauna kamar ‘yar gaiyata.Ta juya idonta, ita ba abinda ke gabanta kenan a yanzu ba, so take kawai ta fita ta samu waje a tayi tunanin dake cikin kanta. +
“Rike wadannan maza, mu fara rabawa daga can.”
Ba yadda ta iya haka ta karb’a ta bisu. Har aka tashi daga bikin kuwa bata sami wannan hutun ba, don daga k’arshe ma sai sulalewa tayi tabi Aminah da aka zo d’aukanta suka sauke ta a gida.
Har aka gama bikin ranar lahadi aka kai amare Nanne bata k’ara samun walwala ba, mutane suka yita tambayar meya sameta ganin duk ta rage tsiwarta da surutu amma duk cikin tarin jama’ar nan ta rasa mutum d’aya da zata gayawa matsalarta, don in ba harkar taro ba bata fiye ganinsu ba, ba wanda sabonsu yayi karfi da ita a cikinsu. Inna ce kawai kuma bata jin zata fahimce ta a wannan lamarin.
Saboda haka Aminah bata yi niyyar zuwa ranar d’aurin auren ba amma ta takura mata sai da ta shigo, tayi ta mata k’orafi na yawan farkawar da take yi a kullum cikin dare ba tare da dalili ba. Aminan tayi-tayi da ita akan su fad’awa wani amma taki yarda don a tunaninta duk wanda yaji zaice aljanu ke damunta, ita kuma tayi rantsuwa cewa ba aljani a jikinta. 1
A haka sati biyu cike da taraddadi a wajenta suka wuce, ‘yan k’ananan abubuwa kala-kala suka yi ta faruwa da ita.
Kamar yawan maganganun da take ji a cikin kanta wanda yanzu bata iya fahimtar abinda muryar ke fad’a, ko kuma kamar ana binta a baya in tana tafiya ko mutum ya tsaya a daidai bayanta, yawan kiran sunanta da take ji daga can nesa, da kuma alamun wani abu na tab’a fuskarta ko jan jelar gashinta.
Tun Inna bata lura da ita har tazo ta fara fahimtar wani abu, saboda yawan tsoratar da take yi da kuma azabar ciwon kai, sannan sau biyu tana tashinta cikin dare tace ana kwankwasa musu kofa alhalin ita bata jin komai.
Abu d’aya kawai dake sawa taji sauk’i a ranta da kuma rage mata tsoro shine yawan addu’o’in data rik’e bisa shawarar Aminah, Sannan bata tab’a zama ba d’ankwali a kanta.
Amma kallo d’aya mutum zai mata ya tsinto rashin kwanciyar hankali a idanunta, don gabad’aya sun d’ashe sannan sunyi fari fat! Ta rame kuma ta rage yawan magana. Ko sadiq yazo da tsokanarsa sai dai yayi ya gama bata iya biye masa, inna ma idan tana hirarta sai dai tayi ta binta da eh ko A’ah.
Mama Azumi da Rahma ba tambayar duniyar da basu yi mata ba amma tace musu ba abinda ke damunta. Daga k’arshe sai mama Azumin kawai ta b’ige da kawo mata jik’e jik’e tana tunanin ko shawara ce ke damunta.
A sati na uku baffa ya kirata akan rashin walwalarta da ya lura kwana biyu, shima ta kasa gaya masa abinda ke damunta sai shiru kawai. Ba yadda ya iya haka ya sallameta da umarnin ta koma islamiyarsu wani satin. Ta amsa sannan ta tashi ta tafi.
Sai dai kuma dukkaninsu ba wanda ya san me wani satin zai zo da dashi, satin daya rufta da wani b’angare na rayuwar gidan!RANAR LARABA!
Wajen karfe biyar da rabi na safe, inna ta fito daga cikin band’aki da alwalarta, ta tashi Nanne dake dunk’ule a cikin bargo sannan tayi falo inda daddumarta take.
Nanne ta bud’e idonta a hankali tana jin kamar baccin bai isheta ba, amma ba yadda ta iya ko bata tashi yanzu ba, ba zata kara minti talatin ba saboda tafiya makaranta. Tayi yunkurin tashi, a nan ne fa taji wani irin nauyi ya danne ta, gabanta ya fad’i ta sake yunk’urawa amma ta kasa, taji kamar wani gingimemen abu aka d’ora a jikinta,
Ta tattaro dukkan k’arfinta ta tara shi a hannayenta amma ta kasa mik’ewa, tsantsar mamaki ya rufe ta, me ya same ta kuma? Ta yaya zata kasa tashi? Meye akanta? Ta juya idanunta ta kalli jikinta babu komai sai wannan bargon da take lullube. Toh me ya faru da ita?
Sai kawai ta bud’e baki da niyyar kiran Inna ko har a lokacin bata tayar da sallar ba, anan ne zuciyarta tayi tsalle ta fice daga k’irjinta, don ta bud’e baki har ta furta sunan Innar amma babu sautin daya fito. Ba tare da ta tsaya wani tunani ba ta d’aga muryarta ta sake kiran, amma ta gagara tsinto sautinta.
Ta maida idonta ta rufe lokacin da k’arar bugun zuciyarta ya cika kunnenta, yana jijjiga ta kan cewa ta farka daga mafarkin da take, saboda haka ta tamke idonta ta sake bud’ewa sannan ta yi yunkurin tashi game da furta kalmar Bismillah amma ba abinda ya canja daga d’azu.
Zuciyarta ta k’ara tsalle cikin fargaba, kanta ya shiga juyi? Me kuma yake shirin faruwa da ita? Bayan duk abubuwan da take jurewa? Tana tunanin zasu wuce zuwa wani lokaci.
Ta sake yunk’urawar dai da dukkan wani k’arfi na jikinta amma wannan nauyin, wannan nauyin dake samanta ya hana jikinta d’agawa. Da gaske ne wani abu ya faru da ita ko kuma yana faruwa a yanzun, in ba haka ba ta yaya kawai zata kasa tashi, taji duniyar ta tsaya mata cak! Yanzu in bata mik’e ba me zai faru da ita kenan? Zata dauwama ne a haka? Koma mutuwa zatayi? Wannan tunanin ya k’ara rura mata wutar sabon k’arfi a cikin jikinta, tayi ta yunk’uri tana motsa yatsun hannu da k’afarta amma ba wani abu daya sauya.
Har k’arfe shida lokacin da inna ta idar da duk wasu nafilfilunta bata ji motsin Nanne ba, hakan yasa ta dawo cikin d’akin ta tsaya daga k’ofa ta kira sunanta.
“Har yanzu kina kwance? Yaushe kika koyi nauyin bacci ne…ga lokacin shiga wankan ki har yayi.”
Shiru bata yi magana ba kuma bata motsa ba, ta sake kira ba amsa, sai ta k’arasa a hankali ta yaye bargon
“Idonki biyu ashe? Ko ba zaki….”
Bata k’arasa maganar ba sanda ta lura bakin nanne na magana amma bata jin me take cewa.
“Baki da lafiya ne?”
Nanne ta girgiza kai tana kara gaya mata cewa ta kasa tashi ne da kuma magana amma ba alamun innar ta fahimce me take cewa.
“Yi magana mana inji, muryarki ce ta rike ko mura kike yi?
Ta cigaba da girgiza mata kai tana fad’ar wani abu amma maimakon ta fahimta sai kawai hakan ya k’ara hargitsa ta, ta hau salati tana kokarin taso da ita, nan ma abu ya gagara sai kawai ta kara rud’ewa tayi waje da d’an saurinta tana neman wani.
Kafin k’arfe bakwai na safiyar, gabadaya kowa na gidan ya shiga tashin hankalin abinda ya sami Nanne, don wani abu ne da a tarihin rayuwar kowannensu bai tab’a gani ba, yayyunta maza haka suka yi ta k’ok’arin ciccib’arta daga kan gadon amma abu ya faskara, daga k’arshe suka yanke shawarar kawai a kira likita har gidan amma baffa ya hana, don tunda ya shigo cikin d’akin yaga yadda take dunk’ule a gado tana ta k’ok’arin yiwa kowa maganar da ba’a iya ji ga kuma hawaye ko’ina fuskarta, sai ya koma falo kawai ya kira waya yace da na ciki yazo.Bai k’ara cewa komai ba daga nan, sai sanda hajiya Babba ta shigo yace ta taimaka ta taya su mama rabi bawa Inna baki ta rage kukan da take, don da mama Azumi ce ke bata hak’urin itama kuma daga baya ta fara nata. Mama halime ita ta tsugunna a gaban Nanne ta dinga karanto addu’o’i kala-kala tana tofa wa a koina na jikinta. Sadiq kuwa tunda ya shigo yaga yadda Nanne ke kuka sosai tana ta motsa bakinta alamun magana, ga kuma yayyansu duk sun taru sai kokarin d’ago da ita akeyi, ya koma d’aki yaci kukansa.
Hatta Aunty amarya da mama rabi sai da jikinsu yayi sanyi, don suna tsaye daga cikin d’akin kusan awa biyu kafin malaman da baffa ya kira su iso.
Anan suka umarci duk matan su fita, inda da kyar aka fita da Inna tana kuka tana a barta taga abinda zasu yi da idonta
Su uku ne malaman, wanda yake Babbansu shi ya tsaya daga daidai kan Nanne ya d’ora hannunsa akan goshinta. yayi ta wasu addu’o’i tana kuka tana raba ido tsakanin yayyenta da kuma baffa dake zaune akan stool d’in mudubi.
Kusan mituna goma sha biyar kafin ya kammala, sannan sauran guda biyun suka fito da wasu papers da aka rubuta wasu keb’antattun ayoyin alqur’ani suka fara karantawa cikin had’in baki a tare kuma da karfi.
Me zai faru?
Basu yi nisa ba sanda idon kowa dake d’akin ya gane masa komai. K’afafun Nanne dake dunk’ule suka mik’e a lokaci guda, haka ma hannayenta, sannan jikinta ya shiga wata irin jijjiga yana d’agawa sama kamar dukka gab’ob’inta zasu b’alle