WANENE SHI
CHAPTER 5
RANAR LARABA! +
Wajen karfe Takwas saura kwata, Imaran yayi parking motarsa a cikin kanfaninsu, ya fito ya d’an kalli yawan motocin gurin sannan ya gyara tie d’insa ya nufi cikin building d’in
“Barka da zuwa ranka ya dad’e.” malam iliya dake zaune a kusa da k’ofar elavator ya gaishe shi.
“Barkan mu dai Baba, fatan ka tashi lafiya.”
Ya amsa da murmushi, ya san yanayin kallonsa da yake masa na cewar yau ya makara ne, wanda shima bai san ya akayi hakan ta faru ba, da kyar ya iya tashi yau saboda nauyi da jikinsa ya masa da kuma wani irin jiri da ya dinga ji. Sai da yasha duk wasu magungunan kariyarsa harda wanda ya shanye gaba daya ma sannan ya iya shiryawa da kyar ya fito
Ya shiga cikin elevator d’in ya danna floor na shida, ya d’an jingina kansa da gefe yana kallon yadda numbobin ke canjawa suna yin sama.
Tunaninsa ya koma kan jaamil da ya dawo shekaranjiya, dole ne a yau ya neme shi su san yadda zasu shawo kan matsalar nan, tunda ba jikinsa ne ke ciwo ba balle yace irin rashin lafiyar bil’adama ce, tun daga cikin ruhinsa yake jin juyawar komai, kuma hakan ba karamin abu bane.
K’ofar ta bud’e, ya fita da sauri ya nufi office d’insa, kafin ya shiga ya hango Sales Personnel dinsu yana fitowa daga office d’insa, bai ko tsaya ba ya bud’e nasa office din ya shige, don a nasa matsayin na Marketing Manager ba yadda za’ayi ace sun hadu dashi su rasa abin tattaunawa, kuma a halin da yake baya bukatar magana a yanzu, yafi son ya samu waje ya d’an kwanta kad’an ko zaiji daidai.
Sai dai me? Yana isa teburinsa yaci karo da file d’in da aka ajiye masa jiya da yamma, na cewa k’arfe tara zasu shiga meeting da stakeholders d’in kamfanin G&M akan matsalar da suke fuskanta, kuma a matsayinsa na marketing manager kusan shine mai magana a wajen
Yaja k’aramin tsaki sanda ya ajiye briefcase d’insa akan table din, speech din ba abu ne mai wuya ba, ko a wajen he can come with something kawai k’arfin zama a meeting d’in ne matsalarsa. Ya koma ya sawa kofar key sannan ya nufi kan couch d’in dake gefen window, ya zuge curtains d’in yayi kwanciyarsa anan yana jin kowacce jijiya ta jikinsa na fitar da rad’ad’i.
Har karfe tara aka fara taruwa a hall na meeting d’in babu alamun Imran saboda haka shugaban company DR. SULAIMAN TURAKI, ya bada umarnin aje office d’insa duba shi.
Imran ya bude idonsa da kyar sanda aka fara knocking d’in kofar, ba zai iya tashi ba saboda haka ya mik’a hannunsa kawai ya bud’e daga nan. Shamsu ya turo k’ofar ya shigo, ba hasken fitila sannan an rufe labulayen.
Yana ganinsa ya fara k’ok’arin mik’ewa.
“Ya salam, Imran baka da lafiya ne?”
“Wallahi, kaina ke d’an ciwo.”
“To ai da kayi reporting kawai ka zauna gida, iI’m sorry, bari in fad’a musu.”
“A’ah karka damu, yanzu nake shirin tashi dama…Its nothing.”
Ba zai taba iya missing meeting d’in ba, don abinda zaije yayi sune ‘yan kananan abubuwan da zasu hadu su gina masa YARDA a wajen Dr. Turaki, kuma YARDA, itace zata sa ya cimma manufar zuwansa cikin wannan rayuwar, itace zata sa ya cimma burin daya dad’e a zuciyarsa. Saboda haka da kyar ya tattaro duk wani karfinsa suka nufi meeting hall din
Suna shiga Dr, Turaki ya yafito shi, ya zagayo ya biyo ta seat d’insa.
“Where have you been? Ka san we can’t keep this people waiting…” sai kuma ya lura da idonsa. “…baka da lafiya ne?”
“I’m fine, just a minor headache. Bari mu fara.”
Ya samu waje ya zauna, aka fara meeting d’in. Da kyar ya iya jurewa har d’aya kamfanin suka gama presenting reasons d’insu na kin amincewa da janye contract din da zasu yi sannnan ya tashi ya fara opposing komai da suka fad’a, tun suna iya protesting har ya d’aure su da jijiyoyin jikinsu, ba yadda suka iya haka suka yadda aka janye contract din. Wani abu da shi kansa Imran d’in bai san zai yiwu ba, kowa yayi ta zuwa yana taya shi murnar k’ok’arin da yayi sannan Dr. Turaki ma yayi ta shaking hannunsa yana murna, wanda hakan ya k’ara sawa kansa cigaba juyawa
Saboda haka nan da nan ya nemi izinin tafiya gida, aka bashi kuwa da full assurance. Har ya kai k’ofar fita ya tuna ba zai ia driving ba, saboda haka ya dawo ya samu malam iliya ya bashi key d’in motarsa. +
Sannan ya juya ya nufi bayan building d’in, sai da ya tabbatar babu wani ido dake ganinsa sannan yayi wani abu daya kusan manta shi a rayuwarsa, ya rufe idonsa a hankali ya sulale yabi iskar wajen.
****
Zuwa dare jikin Imran yayi tsanani sosai ta yadda baya iya ko mik’ewa, a lokacin sunyi duk wani k’ok’arin da zasu yi shida jaamil amma sun kasa gano komai. Ko sallah ma sai a zaune yayi.
Wajen sha biyu na dare, jaamil ya shigo d’akin ya zauna daga gefen gadon da yake lullube ya dafa goshinsa, har a sannan jikinsa da zafi sosai.
Ya d’an ja tsaki sanda Imran d’in ya bud’e idonsa.
“Na gaya maka ka fita daga jikin nan watakila zaka ji sauki.”
“Nima na gaya maka ba ruwan jikin da abinda nake ji, tun daga cikin ruhina ciwon yake.”
“Dole ne fa akwai dalilin ciwon nan, irin wannan abin baya faruwa haka kawai.”
“Nima tunanin da nake kenan, amma na kasa gano komai.
Jaamil ya d’an yi shiru kafin yace.
“A tunani na kamar wani yana hukunta ka ne akan wani laifi da kayi, kuma a yanzu baka mu’amala da kowannenmu balle muyi tunanin wani, ko kuma ana son wani abu daga jikinka na asali, ko…..”
Bai karasa ba ya tsaya, Imran ya juyo a hankali ya kalle shi, idanunsa sun tafi alamun tunani, kamar zai nemo wani abu daya sani ne amma ya manta.
“Me kake tunani?” ya tambaya da muryarsa mai zurfi da taushi.
“Ina tunanin na gano dalilin rashin lafiyarka….”
“Mene shi?”
Maimakon ya bashi amsa, kawai sai ya mike ya fita daga d’akin
Tun Imran na jiran dawowarsa, har ya samu wani bacci mai nauyi ya tafi dashi wanda bai farka ba sai washegari da safe. A lokacin jaamil ya dawo yana zaune daga gefe yana juya wayarsa a hannunsa.
“Yaushe ka dawo?” ya tambaya yana murza idonsa.
Jaamil ya d’ago ya kalle shi sannan ya jefo masa wayar.
“An kira daga wajen aikinka na gaya musu cewa baza ka iya zuwa ba.”
“Da baka fada ba, don jikina yayi kwari zanje yau.”
“Ba zaka samu damar zuwa ba, akwai abinda zamu yi yau din.”
Jin haka yasa ya juyo sosai ya kalle shi.
“That reminds me, kace ka gano dalilin rashin lafiyata, so ina kaje jiya?”
Jaamil yayi ajiyar zuciya sannan a hankali yace.
“Ya sunan yarinyar nan?”
A lokaci d’aya kwakwalwar Imran ta soma aiki, don mace daya ce jaamil zai tambayeshi ita haka, yarinyar daya riga ya goge komai daya dangance ta daga cikin rayuwarsa ya ajiye a gefe. Me zai kawo zancenta kuma yanzu
Ya had’iye abinda ke bakinsa kafin yace.
“Sa’adha…?” sunan da bai taba tunanin zai sake furtawa ba.
Jaamil ya gyada kansa sannan yace.
“Itama bata da lafiya!”
Wannan fagen ta k’unshi abinda ya faru a baya, (flashback) lokacin da Imran ya fara ganin Sa’adha, har zuwa kan gab’ar da muke. +
Saboda haka wannan chapter babu point of view d’in Sa’adha.
(☆_☆)
Fararen idanunta suka cika kowacce gab’a ta tunaninsa, yadda take juyasu cikin harara kamar zata shak’o mutumin dake gabanta da kuma dan karamin bakinta, yadda yake dunk’ulewa kamar zai koma ciki sanda take fad’an sai an biya su kudin kayan islamiyarsu.
Ya rufe file d’in dake gabansa cikin k’osawa, ya kamata ya cire wannan tunanin daga ransa ya fuskanci abinda ke gabansa, yanzu ya fara komai, bashi da wani experience na sabuwar rayuwar daya fara, don haka bai kamata ya d’auko wani abu da babu shi a tsarinsu ya k’ara ba, Naani baza ta taba son haka ba, balle kuma jaamil.
Gefen bakinsa ya motsa cikin murmushi sanda ya hango yadda fuskar jaamil zata yi in ya san me yake tunani yanzu. Ya kalli cikin office d’in da aka bashi a jiya, babu kaya sai desk da kujeru da kuma side drawer.
Zuwa wani satin zai gyara komai ya maida shi kamar yadda na sauran ma’aikatan yake, ya maida komai na cikinsa irin nasu yadda zai fara shimfida sabuwar rayuwar tasa cikin tsari.
Idanunta suka sake dawowa cikin tunaninsa, sanda ta janye su daga kan masu aikin nan ta kalle shi, bayan yace a tambaye su nawa ne kud’in uniform din nasu, wani abu mai kama da kyalli ya haska cikinsu kamar cewa bata lura dashi ba tun tsayuwarsu. Sannan yanayin fuskarta ya canja daga alamun fad’a zuwa nazari, kamar tana so ta gano zai iya biyansu kud’in ne ko A’ah.
Shima ya zuba mata ido, yana jin kamar ya bud’a zuciyarta yaga irin tunanin da take game dashi a lokacin.
“Kizo mu tafi dan Allah Nanne, Ga ya sulaiman can fa ya fito.”
K’awarta dake tsaye a gefe ta fad’a sanda ta ja hannayenta suka yi gaba. Sai dai basu kai ga shiga gidan dake gefensu ba ta juyo ta kalli masu aikin nan tace.
“Allah ya isanmu!”
Murmushi yayi mai sauti sanda ya tuna hakan. Da gaske ne ba zai iya fara focusing a komai ba sai ya sake ganin yarinyar nan, ya riga ya sani in abu na damun zuciyarsa, toh sai hakan ya shafi dukkan al’amuransa
Jaamil ya gaya masa cewa wannan gidan da har ya biya kud’i ba zai masa dad’in zama ba saboda yawan mutane a layin, don haka yau zaije ya karb’o deposit d’in da ya riga ya bayar. Watakila ya sake ganinta, ganin wadannan idanun nata masu cike tsiwa.
Tun daga wannan ranar, sai ziyartar layin su Nanne ya zama daga cikin al’amuransa. Wani lokacin da safe kafin ya tafi aiki, wani lokacin kuma da yamma sanda zaiga dawowarta daga islamiyya. Zai tsaya daga wajen wasu samari da mafi yawa suke taruwa daga jikin mota a sigar da ba mai ganinsa.
Sai dai a kullum yana gayawa kansa cewa abinda yake ba daidai bane, ba zai taba zama masa alkhairi ba musamman idan Naani taji, amma kuma duk sanda ya kwana biyu bai ganta ba, baya iya focusing akan aikinsa, Saboda haka a kullum zai cewa kansa daga ranar ba zai k’ara ba, amma gobe zai koma.
Bai ankara da cewar abinda yake zai iya zame masa matsala ba sai ranar daya fahimce cewa yarinyar na iya ganinsa bayan kuma yana fitowa ne a sigar da ba wanda ke iya ganinsa. Duk da cewar bai tabbatar ba, amma zai ga kamar ta kalle shi – zata juyo da fuskarta daidai saitinsa sannan tayi saurin juyawa ta kalli k’awarta dake magana. Tun daga wannan lokacin sai ya takura kansa ya rage bibiyarta kusan watanni biyu.
Amma kuskurensa na biyu shine sanda yayi tunanin cigaba da binta har yayi mata magana don kawai ya tsokani jaamil wanda ke tunanin wani abun daban a zuciyarsa.
Sannan Babban kuskuren da yayi shine sanda ya shiga jikinta a islamiyarsu ba tare da wani dogon tunani ba don ya taimakawa tsarinta ya tafi daidai, inda tun daga wannan ranar bai k’ara samun nutsuwa ba har sanda yayi wa Naani rantsuwa cewa ba zai kara zuwa kusa da ita ba, a lokacin yayi rantsuwar har cikin ransa amma ganinta daga baya ya karya zuciyarsa, yaji ba zai iya sawa rabuwarsu aya daga nan ba, saboda haka ya koma ya bata hak’urin wannan zafin daya gan gani a cikin idonta sanda ya ganta ya d’auke kai. +
Daga nan kuma ya takura kansa da goge komai nata daga zuciyarsa don a tunaninsa hanyarsa da tata sun rabu har abada.
Ashe kuma wata k’addarar bata ma soma ba!
****
“Me yasa ka b’oye min tun a lokacin cewa ka shiga jikinta?”
Jaamil ya fada yana kallon imran dake shiryawa a gaban mudubi.
Imran ya had’iye yawu cikin mok’ogwaronsa. Tambayar da yake ta gujewa kenan tun dazu, don bashi da amsarta, bai san taya zai gayawa jaamil cewa shima bai san me ya jashi a wancan lokacin ba, meya jashi ya aikata wani abu da bai taba yi ba, abinda ya kira k’addarar data zo tare da tsautsayi.
Ba tare da ya juyo ba ya amsa.
“Saboda in ka sani, zaka had’a komai da komai ka fad’awa Naani.”
Jaamil yaji zuciyarsa ta kawo wuya, haushin Imran da yake ta dannewa tun a daren jiya ya dawo masa sabo fil!
“Da na fada mata tun a lokacin da tuni ta gano abinda daga ni har kai bamu gane ba, da na fad’a mata da tuni ta tsaida wannan abin dake shirin faruwa…da tuni ba zamu sami b’ata lokacin da ka jawo mana a yanzu ba!” Ya k’arasa muryarsa a sama.
Imran ya juyo sosai ya kalle shi.
“Abinda kake tunani ba haka bane jaamil baka da wata kwakkwarar hujar da zata baka shaidar hakan.”
Cikin wani irin sauri, jaamil ya karaso gabansa ya tsaya, idanunsa na cike da bacin rai yace.
“Abinda nake tunani gaskiya ne yarima, da gaske ne ka shiga jikin yarinyar nan ka bar wani b’ari na jikinka a tare da ita, b’arin da saboda shi muka zo nan wajen, saboda shi komai na rayuwarmu ya canja, kuma sai dashi zamu cika manufarmu!”
“Idan har haka ne ya kamata ka san cewa kuskure nayi, kuskure irin wanda baya wuce kowa!”
Shima ya amsa masa da karfi.
“Babu ta yadda za’ayi in yadda da haka yarima, baka tab’a wasa da duk wani abu mai muhimmanci a rayuwarka, zai iya yiwuwa ko ka canja ra’ayi ne akan tsarin mu na tun farko.!”
Imran baice komai ba kawai sai ya d’auki muk’ullan d’aya motarsa akan gado ya fice.
Har yaje office, kwakwalwarsa juyawa take, yana kokarin ture zargin jaamil, don a tunaninsa babu ta yadda hakan zai yiwu, taya zai rasa wani b’ari na jikinsa baiji alamun hakan ba tsawon wata guda? Ta yaya yarinyar zata iya rayuwa da wani b’ari ba irin na halittar ta ba har tsawon wannan lokacin? Wani irin karfin jini ne da ita haka?
Ya rufe k’ofar office d’insa bayan ya gama karbar duk wasu files da zaiyi aiki dasu a ranar, sannan ya rufe idonsa da niyyar hango meke faruwa a waje, wani abu da d’aya b’arin jikin nasa ne kawai ke iya yi.Sai dai iyakar nisan ganinsa zuwa cikin hallway d’in dake d’auke da k’ofofin ofishinsu ne, ko yaya yayi yunk’urin wuce nan, sai ya sake dawowa dai cikin office d’insa. A haka yayi ta gwada duk wasu abubuwan da ya san d’aya barin jikinsa ne kawai ke iyawa, har ya yardarwa kansa cewa dai, da gaske ne ya bar b’arin jikinsa a wajen Sa’adha!
Lokacin da ya koma gida da yamma, jaamil na zaune a wajen daya barshi ba alamun ya motsa. Ya cire takalminsa daga corridor sannan ya k’araso ya zauna a gefensa ba tare da yace komai ba. Sun d’auki kusan mituna goma a haka kafin jaamil yayi magana.
“Naani bata nan, ta shiga bautarta sai bayan wata biyar zata fito.”
Imran ya gyad’a kai alamun ya fahimta.
“Dole ne mu samo mafita, in ba haka ba, ba abinda zai tafi daidai, yarinyar zata cigaba da rashin lafiya, kuma iyayenta zasu cigaba da abinda suke yi wanda zai shafe ka kaima.”
“Baza su iya cire shi ba.” ya amsa a gajarce.
“Na sani, ko ni da kai baza mu iya ba, saboda haka dole ne mu jira Naani har tsawon watannin nan, kafin nan kuma mu san yadda zamu yi in ba haka ba baza ka sami damar cigaba da aikinka ba.”
Imran ya sake yin shiru, tausayin jaamil yaso ya kama shi don ya san Naani zata d’ora alhakin dukkan laifin ne a akansa, zata ce komai sakacinsa ne.
“I’m sorry for what I did.”
“Ya riga ya wuce, abinda yake gabanmu kawai zamu fuskanta.
“Dame zamu fara?”
“Yau zamu je wajenta!”Bata taba tunanin yaya ake mutuwa ba, ko yadda ruhi ke fita daga cikin jiki. Duk da cewar koda ta yin ba zata taba yarda cewa haka mutuwar take ba. +
Ta tsaida idanunta akan siffofi biyun dake tsaye akanta, bata iya ganin fuskokinsu don a cikin duhu ne, saboda haka bata san ko su waye ba, amma tana ji a jikinta cewa kamar ta sansu ne tun asali, kamar sune wani b’ari na jikinta da ta dade tana nema.
Saboda haka, hankalinta ya kwanta, zuciyarta ta sami nutsuwa, ta maida idanunta ta rufe a hankali sanda hannun d’aya daga cikinsu ya sauka a goshinta, wani sanyi ya ratsa kowacce jijiya ta jikinta sannan duk wani ciwo nata yabi iska!
*****
Lokacin da ta farka da safe, wani abu ya canja, wani abu daban da yadda ta saba gani, ta shiga zagayawa da idonta cikin d’akin. Akwai dai hasken rana dake shigowa ta cikin labule, wanda yayi tar! Kamar an kara masa kala.
Sai kuma ta lura ba hasken bane kadai yayi wannan tar d’in. Komai na d’akin ne idonta ke dauko mata shi haka. Kamar taje wankin ido an cire duk wani datti dake cikinsa. Muryar inna ta fara shiga kunnenta, tana karb’ar gaisuwar mutane da yawa da d’akin ya d’auka da maganganunsu.
“Lafiya kalau mun gode Allah, ya wajen naku kuma.”
Muryar wani namiji ta amsa.
“Lafiya kalau inna, ya kuma mai jikin? Mun shigo ne sai Hajiya take fad’a mana wallahi.”
“Da sauki, da sauki wallahi an gode Allah.”
Jin haka yasa ba shiri ta juyo da kanta b’arin da suke, anan idonta ya gane mata dakin cike taf da jama’a, bayan inna akwai su Aunty maryama da Aunty nafisa, da kuma wasu mata biyu da bata sansu ba. Sai hajiya Babba dake tsaye daga bakin k’ofa ta rako k’aramin k’aninta da yayi aure kwanaki da matarsa, yana rik’e da d’ansu a hannu, sai yanzu ta gane muryarsa ce taji.
Aunty maryama ta taso da sauri ta nufo kan gadon.
“Nanne kin farka, sannu ya jikin naki?”
Jikinta? Me ya sameta? ta kalli sauran jikin nata, sannan kwakwalwarta ta tuna da duk abinda ya faru. Aikuwa da sauri ta mike daga kwancen da take, a tunaninta zata sake jin wannan nauyin irin na jiya.
“Yi a hankali karki fad’i.” Aunty Nafisa ta fad’a rike da ‘yarta, Shukra a hannu.
“Aunty naji sauki, ba wani ciwo a jikina.”
“A’a Nanne jikinki ba kwari, maryama jinginar da ita da filon nan.”
“Inna bana son sake kwanciyar dan Allah.” Ta fada har cikin ranta, don da gaske gani take in ta sake kwanciya zata kasa tashi.
“Inna a barta ta sauko k’asan, ai da alamun sauki a jikinta.” hajiya babba ta fad’a tana k’arasowa cikin d’akin.
Aunty maryama da d’aya daga cikin matan nan suka kama ta aka sauko da ita kan carpet, kowa sai faman yi mata sannu yake.
“Toh mu zamu koma inna, Allah ya kara sauki ya bata lafiya.”
Wannan k’anin hajiya Babba ya fad’a, sannan suka yiwa sauran sallama suka fita shida matarsa. Itama hajiya Babban daga baya tabi su. Aunty maryama ta mike tana fad’in.
“Sannu Nanne, bari in had’a miki tea.”
Dama abinda take shirin fad’a kenan, don yadda take jin jikinta shafal, ta tabbatar harda yunwa ke damunta, aikuwa Aunty maryaman ta hado mata tea mai kauri harda pepper soup din nama da dankali (irish) wanda da alama don ita akayi dama.
Ta cika cikinta fam! Sannan tayi wanka da ruwa mai zafi ta canja kayan baccin dake jikinta tun daren shekaranjiya. Aikuwa har yamma mutane shigowa suke ana duba ta, ‘yan gidan kaf! ba wanda bai shigo ba, harda su ya Ahmad da ya ibrahim masu aure sai da suka zo da matansu bayan sallar maghriba.
Nanne taji wani b’angare na zuciyarta ya fad’a, bata zata kowa na sonta haka ba. Rahma kuwa harda kukan murna data ganta ta farka, a wajen su Aunty Nafisa taji ashe a gidan ta kwana a falonsu, sai da safe ne ta tafi gida saboda zuwa makaranta. +
Duk wanda yazo dubiyar nan kuwa, sai inna ta labarta masa abinda ya faru tun daga farko har karshe, har sai da Nanne ta haddace kalma bayan kalma na abinda take fada. Sai dai kuma wani abin mamakin shine a duk labarin Inna bata ji ta danganta rashin lafiyarta da Aljanu ba, haka ma dukka ‘yan gidansu da ‘yan dubiyar babu wanda ya ambaci hakan, sai kawai fatan sauki da kariya suke.
Saboda haka itama ta ture duk wani tunani a ranta ta sake tana ta cin kayan dubiyar da kowa ke rik’owa in zai zo. Don hatta sadiq sai da yaje can wani bakery na hanyar makarantarsu ya siyo mata irin sandwich cake d’in da ya san tana so. Amma duk da haka saida ya dameta da tsokana, duk sanda ya shigo d’akin zai ta dariya yana cewa ‘yanmata taji azaba idonta yayi wuri-wuri.
Da daddare mama halime ta kawo mata potate d’in dankali da alaiyahu, aunty amarya da mama rabi ma duk sun kawo ‘yan fruits dinsu. Hajiya Babba kuwa manyan carton d’in madara da Bournvita ta kawo wai zasu sa taji kwarin jikinta. Inna sai washe baki take ganin yadda kowa ke nuna kulawarsa. Baffa ma sai da ya shigo da kansa da daddare yaga jikin nata.
Washegari da yamma Amina tazo, don sai a ranar Safiya ke gaya mata a makaranta, duk ta rikice tana ta tambayar jikin nata, Nanne tace ta kwantar da hankalinta don wasai take jinta, tsoronta d’aya ne in dare yayi bata son kwanciya, don a jiyan ma kusan a zaune tayi baccinta.
Aminah ta tambayeta abinda malaman suka ce tace itama bata sani ba, don tunda ta tashi, ba wanda yayi mata zancen, kowa ta ganin ta wartsake yake.
Sai da mutane suka lafa sannan Baffa ya kirata falonsa, yace da farko dukkansu sun danganta ciwonta ne da shafar aljanu, amma malaman da suka zo sunyi duk wani k’ok’arinsu basu ga alamar aljani a jikinta ba, Saboda haka ga magunguna nan sun kawo ta dage da shansu da kuma addu’o’i. Tun daga nan, Inna ta tsaya akanta a kullum sai tasha magungunan sannan zata kyaleta, ga litattafan addu’o’i da carbi har kala uku duk ta siyo mata.
Bayan sati d’aya ta warware sosai ta koma makaranta, sannan ta canja sabuwar islamiyya ta koma wata a hanyar gidansu Rahma, hakan yasa itama Rahman ba yadda ta iya, ta bita suka shiga tare.
A cikin sati biyu, rayuwarta ta koma kamar da, komai ya dawo mata daidai…tsiwa da rashin kunyarta ta d’ora daga inda ta tsaya, don har ya sulaiman saida ya zane ta wata ranar juma’ah. Da magribha ne ta lab’e a wajen barandarsu ta gama jin wayar da yake da girlfreind d’insa duka, sai a k’arshe da taji yayi k’asa da murya yana fad’a mata how much he loves her sannan bakinta ya sub’uce tace A’uzubillahi.
Ai kuwa karaf yaji a kunnensa, ya biyo ta har cikin d’aki ya mammake ta, bai ko saurari kwaroroton inna ba.
Sai dai bayan sati biyu, komai ya fara dawowa sabo…
Maganganun da take ji a cikin kanta suka dawo tare da yawan kiran sunanta da kuma alamun wani abu na tsaye a bayanta.
Sannan ga azababben ciwon kan nan da kuma yawan tsoratar da take yi.
Wannan kwankwasa kofar ma na cikin dare ya dawo…!