WANENE SHI
CHAPTER 6
Ya d’ago da kansa a hankali sanda aka rufe main kofar shigowa falon.
“Watarana idan na gaji, zan shak’e wuyanka ne kowa ya huta.”
Imran ya juyo daga cire takalmansa da yake ya kalli jaamil dake zaune daga kujerar dining na falonsa.
“Yaushe kazo? Ka dade kana jirana ne?”
“Tun sanda ka bar wajen aikinka ka tafi yawon zagaye gari nake zaune anan.”
Imran ya k’araso da murmushinsa.
“Toh me yasa kawai baza ka dawo nan bane, kaga ka huta zirga-zirga, kuma akwai spare d’aki…biyana kawai zakayi ka shiga.”
Jaamil bai saurari k’arshen zancen nasa ba ya kalli ledar daya ajiye akan table din.
“Meye wannan kuma?”
“Abinci ne nayi takeaway, don har yanzu bana jin k’arfin jikina, ba zan iya girki ba.”
“Wai me yasa ka damu kanka da abincinsu ne?”
Ya d’aga kafada kad’an.
“Saboda yana min dadi.”
“Ranar da komai zaizo karashe zanga yadda zakayi.”
“Me kuwa zanyi, zan cigaba da zuwa ne ina siya.”
Har jaamil zai bashi amsa suka tsinci knocking daga k’ofa. Ya juyo ya kalleshi.
“Meye kake kallona? Gidanka ne fa.”
Yaja k’aramin tsaki.
“Ba sai ka tuna min ba ai, ban taba yin bak’i bane thats why.”
Yana bud’e k’ofar, yaci karo da wasu ‘yanmata biyu a balcony d’in. Ya d’an bude baki saboda mamaki sanda kowaccensu ta fad’ad’a murmushinta.
“Ina wuni.” suka fad’a a tare.
“Uhm…lafiya kalau.”
“Dama mu mak’otanku ne, tunda aka tare ne bamu shigo ba shine muka ce bari yau muzo mu gaida matar gidan.”
Imran ya d’anyi shiru sannan ya cusa yatsunsa cikin sumar kansa yace.
“Mungode…sai dai kuma ba mata a gidan.”
Suka zare idanunsa sannan d’aya ta kalli daya.
“Oh sorry, bamu sani bane wallahi…sai anjima.”
“Its nothing, sai anjima.”
Ya rufe k’ofar ya dawo ciki. Jaamil yana dariya k’asa k’asa yace.
“Yanzu a kawo maka ziyara ka hana su shigowa? Bayan kaine matar gidan?”
“Wallahi k’arya suke, ina ganinsu fa in na dawo sun san babu mace a gidan.”
“Kaima ka san me suke nufi ai.”
Bai saurare shi ba yayi hanyar d’aki kawai. Bayan kamar minti talatin ya fito sanye da wasu kayan, ya jawo kujerar gefen jaamil ya zauna ya fara cin abincinsa.
“Meya faru?”
Ya tambaya ba tare daya kalle shi ba.
“Ciwon yarinyar yana shirin dawowa.”
Da jin haka imran ya saki cokalin hannunsa.
“Tun yanzu…? Jaamil gaskiya dole mu sami wata hanyar, ba zan iya ba wallahi nayi losing k’arfi da yawa kuma i’m still picking up.”
“Na sani.””Na san ka sani mana, I’m asking me ka samo? Don ba abinda zan iya nan gaba idan dai ni zan cigaba da controlling d’inta.”
“Da ace ban samo komai ba yarima, bazaka ganni anan ba.”
“Okay ina jinka.”
Jaamil yayi ajiyar zuciya mai nauyi yana kallon set d’in cokula da table knife d’in dake jere a cikin gidansu na katako daga tsakiyar table din
“Wai taya ka iya tsara komai na gidan nan ne ma?”
“Wani Decoration company na biya suka had’a min. Ina jinka me ka samo?”
Jaamil ya sake yin shiru, abinda zai fada nauyi yake masa, kuma shi kansa har yanzu ya kasa yarda cewa hakan shine kad’ai a hanyar samun saukinsu, wani abu da babu shi a tsari ko tunaninsu.
“Yarima abinda na samo mai girma ne, ni kaina na san ba zai yiwu ace duk bayan sati biyu kana k’arar da k’arfinka wajen controlling d’inta ba, amma ka yarda dani ba yadda zamu yi ne.”
“Nima na san da hakan, saboda haka ka fad’a min kawai me ka samo?
“Hanya d’aya da zai sa ciwonta ya tafi gabad’aya shine in yarinyar tana kusa da kai!”
Imran yayi shiru yana kallonsa, hannunsa rik’e da cokalin daya d’ebo abincin. Sai kuma ya sake shi cikin plate d’in sannan ya gyara zamansa sosai.
“Ban gane me kace ba…”
Jaamil yayi ajiyar zuciya, yana jin shima kamar abinda ya fad’a ba daidai bane.
“D’aya b’arin jikinka ne kad’ai zai iya controlling wanda ke jikinta, saboda haka idan kuna tare a kullum d’aya b’arin zai dinga jin alamun d’ayan a kusa dashi saboda haka ba zaiyi k’arfin da zaiyi tasiri ba, kamar dai sanda duka biyun suke jikinka
Amma in har d’aya yayi nesa da d’ayan, ciwonta zai ta taruwa ne ta yadda duk sanda ka tashi zuwa kwantar dashi, sai kayi amfani da k’arfi mai yawa. Wanda in kuma kana yawan yin hakan toh k’arfinka zaita tafiya kullum ka zama baka da kuzari.”
Imran ya tsura masa ido, yana jin kowacce kalma tana bi ta kan fatarsa tana nutsewa cikin kwakwalwarsa. Amma kuma ya gagara fahimtar ma’anarsu. zuwa can ya daure yace.
“Jaamil ban gane ba fa, ta yaya yarinyar zata zama a kusa dani? Ka san dai ba zan iya zuwa inda take kullum ba?”
“Na sani.”
“Toh ta yaya hakan zai yiwu? Kuma ka san ba zamu iya sace ta mu cigaba da zama a garin nan ba, dole za’a nemo mu ko kuma yarinyar ta gudu…sannan in muka bar gari kuma zan samu matsala da wajen aikina. Wajen da saboda shi muka shigo rayuwar nan kuma nayi abubuwa da yawa ba zai yiwu mu b’ata komai ba…mu bar abu mai muhimmanci don gyara kuskurena.”
“Nima duk nayi wannan tunanin yarima, kuma na ga hakan ba zai yiwu. Shi yasa na ture komai na samo hanya d’aya kawai da zata fitar damu, mu sami komai kuma a sauk’ake.
“Wace hanya kenan?”
Kai tsaye jaamil ya amsa.
“Shine ka AURE TA!”
*****
Jikinta kwata-kwata ba kwari, yayi wani irin shafal kamar fallen paper, ta rufe idonta tana sauraren maganar Inna, tana ta gaisawa da amare, zainab ce a kusa da ita tana kira mata su d’aya bayan d’aya, kowacce sai ta tambayi jikinta kasancewar duk sunji labarin.
Ji take yi kamar zata yi bacci amma kuma yak’i zuwa, ko sallar azahar d’azu da kyar tayi tana jin layi, abinci ma bata ci ba saboda ko kad’an bata jin sha’awar komai. Ta cusa yatsunta cikin gashinta tana rokon baccin ya d’auketa.
“Zainab mama na nemanki.” muryar safiya ta shigo d’akin.
“Ta dawo ne?” zainab d’in ta tambaya.
“Eh yanzun nan da zamu hawo suka shigo.”
“Toh bari in kira wa inna jamila tukunna.”
Nanne ta bud’e idonta a hankali sanda safiyyan ta k’araso wajen kujerar da take kwance. A gefenta wata yarinya ce da a lokaci d’aya ta cilla zuciyarta cikin tunani, tunanin wannan fuskar da ta kasa fita daga ranta….IMRAN.Tun ranar da ya shigo cikin gidansu da daddare, bata kara jin labarinsa ba balle ta ganshi. Sannan rashin lafiyar da tayi ta kwanan nan ta ture duk wani abu dake zuciyarta, dalilin da yasa bata k’ara tunawa dashi ba kenan
“Wai bacci kike yi?” safiyya ta fad’a tana zama a hannun kujerar.
“A’ah wallahi kawai jikina ne ba dadi.”
“Sannu, ya jikin?” yarinyar ta tambaya, ta juya ta kalle ta sosai sannan ta amsa.
“Walida ce take son style d’in doguwar riga, shine nace bari muzo wajenki kece mai su.”
“Ta kuwa yi sa’a jiya aka kawo min wanki, ki d’ebo mata suna wardrobe.”
Bayan safiyya ta d’ebo wajen kala goma suna d’agawa ne ta kalli walidan tace.
“Wai kowacce kice tayi miki, toh guda nawa zaki d’auka ne?”
“Ko duka ne fa ni d’auka zanyi, sauran sai in karbi na riga da skirt a wajenki.”
“Kaya nawa zaki d’inka ne wai?”
“Goma sha hudu ne, ummah tace harda na sallah amma ni wallahi duk d’inke su zanyi.”
Safiyya ta gyad’a kai tace.
“Gaskiyane, dama ke kad’ai ‘yarta dole kiyi abinda kike so.”
Kamar a mafarki Nanne taji kalmar, saboda haka ta bud’e idonta da sauri ta kalle su sanda walida ke fad’in.
“Kowa wai sai yace don ni kad’ai ce, kuma wallahi abubuwa da yawa ba haka bane, kinga yanzu fa na d’an kwana biyu banyi d’inki ba.”
Kafin safiyya ta bata amsa, Nanne ta riga ta magana.
“Baki da yayye dama?”
Walida ta gyada mata kai tana murmushi.
“Ita kad’aice fa a gidansu daga ita sai mamanta da babanta, ‘yar gata ce ai.”
Nanne taji kanta k’ulle, komai ya tsaya mata cak! Kamar yaya? Dama Imran ba wanta bane? Toh ya akayi kullum take ganinsa a k’ofar gidan duk tsawon watannin nan? Idan ba anan yake ba toh daga ina yake zuwa. Ta sake kallon walidan tace.
“Akwai wani da yake zuwa gidanku Imran?”
“Imran? Kai anya kuwa na sanshi? Ganinsa kika yi a gidan?”
“Ina yawan ganinsa ne a k’ofar gidan naku.”
Ta kalli safiya tace.
“Kin gane wa take nufi?”
“Ta yaya zan gane, nina san duka ‘yan uwanku ne?”
“Toh ai kina yawan zuwa.”
Safiyya ta jiyo ta kalli Nanne tace.
“Waye shi?”
Ganin dai da gaske basu gane ba yasa kawai ta rabu dasu ta cigaba da kwanciyarta, suka d’ebi kala takwas sannan safiyya ta mayar mata da biyu suka fita.
Har dare tunanin Imran bai bar cikin kanta ba, mamaki take yi in ba gidansu walidan yake zuwa ba me yake kawo shi? tunda dai bayan gidan nasu ba wani gida a gefensu duk kangwaye ne. Ta tuna kuma yace mata wani lokacin yana zuwa wajen ya umar, amma in har wajensa yake zuwa ya kamata ace ta tab’a ganinsa a cikin gidan nasu ba sai ranar ba kawai, tunda duk wasu abokan yayyunta masu zuwa ta sansu.
Sai kuma ta tuna a cikin samarin nan dake yawan zama akan wata mota take ganinsa, in har hakane su zasu sanshi kenan, saboda haka tayi niyyar tambayar sadiq gobe.
Sai dai har ta kwanta bacci a ranar, kwakwalwarta tambaya d’aya take nanata mata.WANENE SHI?
Imran ya shigo kicin ya dauki ‘yar kettle d’in da yake had’a coffee ya nufi jikin despenser ya fara tsiyayo ruwa a ciki.
“Wai ta yaya ne zanyi ta binka tun jiya akan magana d’aya?”
Muryar jaamil ta fad’a daga bayansa.
“Wai ta yaya ne zanyi ta maka bayani guda d’aya tun jiya?”
“Yarima ya kamata ka zauna muyi bayanin nan sosai, ka fahimci abinda nake nufi.”
Ya juyo ya bud’e cabinet d’in sama ya d’auko containers guda uku, na coffeee powder, madara da kuma sugar, ya zuba kowanne sannan ya maida kettle d’in jikinta ya kunna socket.
“Na fahimce ka tun jiya jaamil kuma na gaya maka cewa ba zai yiwu ba.”
“Bamu da wata hanya bayan hakan yarima, saboda haka ba abinda zai hana shi yiwuwa.”
“Okay then, let’s talk.”
Yaja kujera daga jikin island d’in ya zauna.
“Zauna.” ya fad’a ganin jaamil d’in bashi da niyyar zama. yaja kujerar a hankali shima ya zauna.
“Ka saurareni da kyau don Allah….sanda kayi wannan tunanin Auren a cikin kanka, na san kayi la’akari ne da abubuwan da suka faru a baya, so lets make things clear, Bana son yarinyar nan kuma ban taba sonta ba, kawai da farko ne kafin in san rayuwar nan, yanayin maganarta ke burgeni shine har ka tab’a ganina a wajenta.
Amma tun daga ranar da na yiwa Naani alkawari cewa ba zan k’ara zuwa kusa da ita ba, na goge duk wani abu daya shafeta a zuciyata, kuma tun daga wannan lokacin i try my best to keep away from her. So abinda kake tunani ba zai taba yiwuwa ba!”
Jaamil yayi shiru na kusan minti d’aya yana kallonsa, sannan yace.
“A yaushe aka tsara cewa zamu yi iya abubuwan da kake so ne?…nayi tunanin muna yin duk abubuwan da zasu samo mana mafita ne.”
Bai amsa ba ya cigaba.
“Ya kamata nima ka saurerini da kyau yarima, sanda ka shiga jikinta baka yi wani tunani ba balle shawara, kayi abinda ka san cewa kuskure ne, yanzu kuma da matsala ta b’ullo me yasa kake zaton zaka sami zab’i a cikin kuskurenka? Dole ne ka hak’ura ka karb’i duk wata dama da muke da ita hannu biyu.
Sannan dama bai kamata ka so yarinyar ba, saboda gabad’aya auren zai zama cikin abinda baifi wata biyar bane kawai, duk lokacin da Naani ta fito zamu ciro d’aya b’arin naka ba tare da ta sani ba sannan ka rabu da ita, mu k’arasa abubuwan da zamu yi mu koma rayuwarmu.
A ina kaji dole sai da zancen so abin zai yiwu?”
Imran yayi shiru yana saurarensa, abu d’aya kawai ya fahimta tun farkon zancen, shine duk wannan abin laifinsa ne bana jaamil ba, saboda haka da gaske ne bashi da zab’i, bai kamata ma ya samu ba, don in har ya samu d’in za’a iya kiran hakan da son kai.
Abinda yayi wani kuskure ne da babu shi a lissafinsa, bai ma tab’a tunanin abu makamancinsa ba, a rayuwarsa yana taka tsan-tsan da komai mai muhimmanci, baya tab’a bada k’ofar da wani abu zai kawo masa cikas!
Watakila shi yasa jaamil d’in ma yaji haushinsa a baya, yayi tunanin ko ya canja ra’ayi ne akan abinda suka tsara tun farko. Kafin daga baya shima ya gane cewar tsautsayi ne ya fad’a masa, ko kuma k’addara wadda bata wuce kan kowa.
Cikin tunaninsa ya tsinto muryar jaamil yana cigaba da magana, ba yadda zaiyi, dole ne ma ya yarda da shawarar nan, in ba haka ba zai cutar dashi ne, shi d’in dake ta fad’i tashi wajen ganin komai ya tafi musu daidai, komai kuwa…komai d’in da ba laifinsa bane.
Ya lumshe ido yana sauraren k’arar tafasar coffee d’insa daga baya. Ya riga ya yarda da duk abinda yake fad’a, saboda haka babu amfanin sauraren, sai da yaji ya kai k’arshe sannan yace.”Ta yaya aure tsakaninmu zai yiwu?” ya tambaya daidai sanda kettele d’in ta kashe kanta da k’arar k’assss! Alamun tafasa.
“Yarima, na fad’a maka na tsara komai kafin na tunkare ka da wannan zancen, in har ka amince insha Allah komai zai yiwu cikin k’ank’anin lokaci.”
Lokaci. Kalmar lokaci ta d’auki hankalinsa, ya bud’e idonsa sosai sannan yace.
“Jaamil aurensu yana d’aukan lokaci, ta yaya zanje har ta sanni na aureta kafin wata biyar kawai?”
*****
Sulaiman ya shigo cikin falon baffa da sallama. Babu kowa a ciki don haka ya samu waje ya zauna, don a lokacin k’arfe goma ne saura na safe.
Kusan mintuna goma kafin Baffan ya fito daga cikin d’akinsa.
“A’ah ashe kaine…”
Ya fad’a sanda ya taho kan kujerarsa ya zauna, a lokacin sulaiman yayi saurin saukowa k’asa.
“Nayi zaton ai Ibrahim ne yayi sammako, don yau zamu je wajen commissioner dashi akan maganar kwangilar nan.”
Ya zauna sosai, sannan sulaiman d’in ya gaishe shi ya amsa.
“Dama wad’annan malaman da suka duba Nanne jiya ne suka zo, da tun jiyan ma suka so ganinka sai kuma baku k’araso da wuri ba.”
“Toh…toh suna nan ne yanzu?”
“Eh, suna tsaye a compound.”
“Toh shigo dasu mana, jeka ce dasu su k’araso. Koda kuma Ibrahim d’in yazo kace dashi ya dakata mu gama tukunna.”
Minti biyu bayan hakan, malaman nan su biyu suka shigo falon baffa, suka yi musabaha d’aya bayan d’aya tare kuma da gaisuwa kafin su zauna a kujerun dake gefe.
“Ashe kuma jiya ma kunzo. Munje kaduna ne kuma mota lalace mana a hanya, shiya sa dare yayi mana.”
Babban cikinsu ne ya amsa.
“Ya salam! Allah ya kiyaye gaba, haka shi sulaiman d’in yake fad’a mana wallahi, Da yake hajiya ce (yana nufin inna) tasa aka kira mu akan dai batun yarinyar nan.”
A daidai wannan lokacin lami tayi sallama ta shigo, ta ajiye musu tray d’in hannunta dake d’uke da flask, sukari da kuma k’ananan cups d’in shan tea sannan ta fita.
“Alhaji a gaskiya munyi duk wani iya k’okarinmu harda taimakon wasu ma, don jiya mu bakwai muka zo gidan nan amma wallahi duk k’ok’arin namu ba muga wani aljani tattare da yarinyar nan ba.
Shi yasa muka sami matsaya d’aya wadda itace kowannenmu ya yarda da ita, cewar Aljanun ne ke k’ok’arin shafarta, kuma da alama daga cikin jinsi mai k’arfi ne duba da yadda take wahala tun yanzu.”
Baffa ya gyad’a kansa alamun ya fahimta.
“Sannan kuma kamar yadda muka yi bayani ne a baya, hanya mafi k’arfi da yarinyar zata kiyaye kanta shine dole sai tayi rik’o da addu’o’i, da kuma yawan zama da alwala da karatun alqur’ani, idan har babu wad’annan magungunan da muka bayar ma ba lallai ne a samu tasirinsu ba.”
“Toh su cikin gidan kun sake yi musu duk wannnan bayanin?”
“Eh duk mun fad’a musu, amma akwai wani dalilin daban wanda dole kai ya kamata mu samu, shine ma dalilin dawowarmu.”
“Ina saurarenku..” ya amsa a hankali.
Malamin ya d’anyi shiru kamar yana jin nauyin abinda zai fad’a.
“Alhaji inda ace yarinyar tana da aure, ko kuma za’ayi mata aure nan da wani lokaci, hakan ba k’aramar kariya zai zame mata ba, don irin wad’annan Aljanun suna mu’amala ne kawai da matan da basu tab’a aure ba.
Amma in har mace bata da aure, da kyar ne su rabu da ita.”
Baffa ya k’ank’ance ido ta cikin glass d’in dake fuskarsa yana kallonsa. Ba zaka yi iya banbace wane irin yanayi ne a fuskar tasa ba.
Haushi? Mamaki? Nazari ko kuma rashin yarda?A cikin mafarkinta na biyu, duhu ne sosai kamar wancan karon, sannan dogwayen mutanen nan biyu na tsaye a kanta. Jikinsu na daga karshen gadon amma kuma sunyi kusa sosai yadda bata ganin wata tazara tsakaninsu.
Bata iya ganin fuskokinsu, iya kafad’ansu ne kawai, kuma duk iya kokarinta, duk yadda ta kokarta ba abinda take gani a wajen da ya kamata ace kansu ne, bata ganin komai sai duhu.
Taji ta k’agu, kamar ta bud’e baki ta roki daya daga cikinsu ya d’ora hannunsa akan goshinta kamar wancan karon, wancan karon da tunda sanyin fatarsa ta ratsa jikinta, duk wani ciwo nata yabi iska.
Ta rufe idonta a hankali sanda ta hango hannun nasa na tahowa kan fuskarta, a hankali sanyin fatarsa ya ratsa kowacce jijiya ta jikinta sannan duk wani ciwo nata yabi iska!
******
A satin da tayi wannan mafarkin, bata k’ara fuskantar wani ciwo ba, jikinta ya koma k’alau kamar yadda take a da, sai dai kuma ba wanda ya yarda da ita akan hakan. Kowa yana binta ne da kallon mara lafiya musamman inna, dake takura ta akan yin abubuwa, bata isa ta tsallake wani tsari na shan magungunanta ba koda kuwa sau daya ne a rana.
Duk da cewar tasha yiwa inna bayani cewa ita bata ganin magungunan zasu kawo mata sauki, don wani abin ma kamar k’asa ce kawai, amma inna ta rantse ba abinda zai hana ta daina sha, a lokacin taji kamar ta bata labarin mafarkin da tayi har sau biyu amma ta fasa, don wani abu ne da cikakken mutum ma ba lallai ne ya yarda ba, Balle kuma Inna da rikicin tsufa ya fara kamata.
Saboda haka ta barshi a ranta kawai don babu na biyun inna a wanda zata fad’awa sirrinta.
Babban abin mamakin daya same ta ya faru ne bayan ta koma sabuwar islamiyyar data canja, anan ne ta gane cewa gidan da Imran yake a layin dake gaba kad’an da islamiyyar yake, Don ba sau d’aya ba sau biyu ba tasha jin wasu daga cikin ‘yan makarantar na hirarsa, hirar had’uwarsa, da kuma abubuwa da yawa wanda muhimmi shine zancen shi kad’ai yake zaune a gidan da yake, don akwai wadda ta rantse ma ta san wadda taje har k’ofar gidan nasa ya tabbatar musu cewa ba mata a gidan. Kuma a kullum shi kad’ai ake gani yana shiga gidan.
Ranar data fara jin zancensa daga bak’in wasu ‘yan ajin nasu, bata tab’a kawowa shi bane, sai da yazo wucewa a mota daidai lokacin tashinsu taji suna nuna shi tare da bayanin da aka gama a aji. A lokacin k’afafunta kusan mak’alewa sukayi a inda take tsaye, don tun ranar data fahimci ba’a gidansu walida yake ba, bata k’ara sake ganinsa ba kusan wata sati uku.
A lokacin har sadiq saida ta tambaya amma yace bai gane shi ba, duk da ya san kusan mazan dake layinsu. Tun daga wannan ranar kuwa sai ta fahimci kusan rabin hirar ‘yanmatan makarantar in an had’u a masallaci kafin a tayar da sallar la’asar ta Imran ce. Kuma kowa da irin albarkacin bakinsa da yake fadi game dashi. ‘yan k’alilan ne ke fad’an abubuwan alkhairinsa, kamar yawan sallah a jam’i da kuma kyakyawar mu’amalarsa da suke ji daga bakin yayyensu, amma da yawansu sunfi sukar zamansa shi kad’ai a gidan ne da cewar wani abu ne da ba’a saba ba, kuma ake masa kalon laifi, wasu kuma zancensu bai wuce yabawa komai na tsarin halittarsa da kuma yadda suke mafarkin samun miji ko saurayi irinsa ba.
A cikin satin, Nanne ta ganshi har sau uku amma ko kad’an bata bari ya ganta, duk da cewar daga cikin mota take hango shi kamar ya dawo daga aiki ko wani waje. Sai dai har cikin ranta tana so ko sau d’aya magana ta shiga tsakaninsu, watak’ila hakan yasa ta samu yi masa tambayoyin dake cin ranta game dashi. Tambayoyin da a kullum k’aruwa suke musamman yanzu da take jin hirarsa wajen mutane daban-daban.
****
Ranar Alhamis tana tsaye daga jikin mota a cikin asibiti tana jiran fitowarsu inna, wadda suka shiga ita da aunty amarya wajen gashin k’ashinta.
Da a cikin motar take kuma sai ta fito waje shan iska, don yau kwata-kwata bata son shiga ciki, Allah yaso sun taho da Aunty amarya ne itama zata ga likitanta, da ta san ba yadda za ta yi dole sai ta shiga.
Ta jingina bayanta tana kallon dogwayen bishiyun wajen, suna kad’awa a hankali kamar masu rangwada. Ta juya gefe ta kalli tsilli tsillin mutanen dake harkokinsu a harabar wajen, tana son irin yanayin nan, kamar ruwa zai sauka sannan kuma kowa na harkar gabansa.
Daga can ta hango wani container na kanti saboda haka ta tafi da niyyar siyan ruwa. Har ta siyo kuwa ta dawo da kusan mintuna goma sannan su inna suka fito. Tana hango su ta bud’e gaban motar ta shiga.
Idris direba ya taho shima daga jikin famfon da yake wankewata jarka ya shigo motar.
“Zamu biya ta Al-karama idris zan tsaya in sayi magani dan Allah.”
Aunty Amarya ta fad’a daidai sanda idris d’in ya tada motar.
“Toh shikenan hajiya.”
Nanne taji dad’i ak’alla tana so su dad’e a waje saboda yanayin garin, kuma Al-karama yana da nisa daga gidansu.
Ta juya ta karbo wayar inna wadda kusan tasu ce su biyu, ta d’auki earpiece akan dashboard d’in motar ta cusa a kunnenta, sannan ta jingina kanta da glass d’in motar. Iskar dake shigowa na kad’a ta kota’ina.
A cikin wak’ar da take ji ta jiyo inna na fad’an wai bata sa dankwali ba, don abaya ce a jikinta sai kawai ta dauko d’an bakin mayafi mai adon jajayen dutsuna ta yafa, tunda suka fito innan bata lura da ita ba kenan sai yanzu da taji dad’in k’afafunta.
Ta k’ara lumshe idonta tana jin Aunty Amarya na gaya mata cewar ai haka yaran yanzu suke wai safiyya ma na yawan yin hakan, ta rasa wak’ar take ji ko hirarsu saboda haka ta ware volume d’in ta juya tana kallon titi.
Sun iso daidai Al-karama dake d’aya tsallakensu, idris yace ba sai ya juya ba bari ya tsallaka kawai ya karb’o, saboda haka Aunty amarya ta shiga binciko takardar maganin da kud’in daga jakarta sai dai bata kai ga d’aukowa ba wayarsa tayi kara, ya d’auka ya shiga magana k’asa-k’asa, daga baya kuma sai ya fita waje ya koma bayan motar.
Inna tace.”Yo kinji shakiyanci, maimakon ya karb’a kuma ya tafi yana wayar sai mun jira shi ya gama abinda yake kenan?”
Aunty Amarya ta juya bayan motar ta ganshi yana ta sunkuyar da kai saboda haka tace.
“Toh watakila wayar mai muhimmanci ce, tunda naji ance ya fara neman aiki.”
“Au ya gama karatun ne?”
“Inna tun yaushe kuwa, har ya kawo takardar gamawar tasa gida ana tayi masa murna, shekara biyu ne ai da yake diploma suka yi.”
“Wallahi na manta, bawa Nanne toh ta tsallaka ta k’arbo miki, kan nan ya gama.”
Da kyar Nanne kuwa ta karb’a ta fito, don ta riga taji dad’in zaman da tayi. Ta kashe wakar, ta ajiye wayar akan seat d’in sannan ta rufe k’ofar motar ta matsa gefe.
Ta tsallaka titi na farko kafin almarar da ta zama sanadin k’addararta ta faru.
ALMARA.
Don banda ita da ta tabbatar babu mota a kusa kafin ta tsallaka titi na biyu, babu wani d’an adam a wajen da zai iya bada shedar ga ta inda motar ta fito. Kawai sunji k’arar takewar birki ne da kuma wani irin ihu wanda karad’e wajen baki d’aya.
Nanne taji tayi sama, numfashinta ma yana tafiya tare da ita, sannan a lokaci d’aya kuma taji ta fad’o da k’arfi ta daki k’asa. Wata irin k’ara mai amo ta fito daga makogwaronta ta ratsa cikin kowacce gab’a ta jikinta. Taji kamar bayanta ya b’alle ne sannan dukka jikinta ya mata nauyi.
Numfashinta ya tsaya cak! a iya kirjinta, ta dunkule hannunta wajen k’ok’arin jawo iska ta shiga jikinta, a lokacin ne taji wajen ya rud’e da salatin mutane, muryoyi da yawa suka cika kunnenta, taji bata gane komai.
Idanunta suka shiga k’ok’arin rufewa, amma tana iya ganin dishi-dishi na tarin mutanen dake ta shigowa cikin ganinta. A lakacin ne, taji wani ya d’aga hannunta dake da nauyi, sannan wannan muryar, wannan muryar mai taushi tayi magana.
Kunnenta ya ture duk surutan mutanen dake wajen ya d’auko mata abinda muryar ke fad’a. Abinda muryar ta saba fad’a.
“SA’ADHA!”