WATA BAKWAI CHAPTER 14
Sai daya gama kallo tsaf sannan ya juyo yace “kinada duk kayan nan na ciki? Ko nai waya a kawo” Ta girgiza kai “tace dryer ne babu irin nasu sai karami na riqewa a hannu…sai clips in nan suma babu” Wayarshi yake dannawa. “Me zakai?” Ta tambaya. Zan wayane akawo. Kamun ta sake magana harya ce “Hello…..” Hakan yasa tai shiru tana kallonshi yana bada umarnin akawo duk wani kayan da za.a samu a saloon. Saida ya gama tsaf ta ce “gentle yanda kake fadar nan sai kace saloon zamu bude” Murmushi kawai yai. Ba ai awa dayaba aka kawo kayan. Hadiman gidan suka dauke suka kai bangaren husna. Saida suka gama tsaf suka koma nasu wajen sannan prince ishaq ya miqe tsaye yace ma husna muje. Sai da taji gabanta yadan fadi. Yau akwai rigima kenan gashinta ba wani mai tsaho bane can saidai warwarewarshi ne aiki tunda rubber ne. Takan godema Allah data biyo jinin fulanin babansu ta bangaren gashi. Kanwarta taita cewa daman ita. Dan nata gashin dakyar yake parking. Haka tabi bayanshi har toilet din bangarenta. Duk da ta rage zama da hijab sosai in tana tare dashi. Cire dankwalinta a gabansji ba karamar wahala yai mata ba. Sai taji gaba daya kunya ta rufeta. Da kanshi yaje ya dauko stool din dake dakinta yana fadin ta zauna akai kamun su siyo nasu kujerun wanke kan. Ta zauna wajen abin wanke kai. Prince ishaq yazo ya warware ribbon da ta kulle gashinta dashi. Ya dauko comb ya soma tajewa. Tai mamakin yanda yake bi a hankali kaman ya sabayi daman. Fuskarshi take kallo ta cikin mudubin toilet din yanda ya nutsu sai kace yana wani muhimmin aiki. Sai taji wani yanayi a zuciyarta data kasa fassarawa. Shampoo yasa ya soma cakuda mata gashi. Wayarshi dake ajiye gefe ta soma ringing. Ya share ya cigaba da abinda yake yi harta yanke. Yatsun sa yasa cikin gashinta ya yamutsa hakan yasa tsikar jikinta tashi. Kula yai da hakan yace “da zafi ne?” “A.a” ta fada dakyar muryarta can kasa saboda wani yanayi data tsinci kanta cikinsa. Haka ya wanke gashin tas. Yasa oil ya fara daukar abinda ake maqale gashi yana kallon su. “Hussy” Ya kirata. “Naam” ta amsa tana goge kunnuwanta da towel. “Ya ake maqala wannan abin ma?” Dariya tai sosai tace “ba zaka iyaba kabarshi” tana kokarin karbar clip din daga hannunshi. “Um um” ya fadi yana janyewa ya dora da “ni fa sai nayi ki fadamun yanda zansa kawai STORY CONTINUES BELOW Ta kula prince ishaq ba karamin dan rikici bane. Dole a haka daqyar tare suka maqala clips din. Ya dan koma da baya ya kalleta kinyi kyau ya fadi. Tai murmushi a kunyace. Dryer ta shiga suna dan hira da prince ishaq din kadan kadan. Har kanta ya bushe. Clip daya ya cire yako hado da gashinta ouchh! tai yar qara tana kai hannu wajen. “Sannu sannu da zafi ko?” Yake fadi yana shafa mata wajen.A hankali yabi ya cire clips din duka. Tana miqo mishi kalar man dazai shafa mata. Ya gama suka taje kan tsaf tasa abu ta daure. Sannu da aiki gentle. Ta fadi tana kallonshi duk ya wani burgeta. Sauke numfashi yai yace mata “yawwa kinga kin huta da zuwa saloon ko? Tunda na iya” Dariya tai kawai dan tama rasa me zata ce mishi. Suka dawo falonta. Ya dauki wayarshi ya duba. Ya kalli husna yace mata “Zan fita” “Allah ya tsare ya dawo dakai lafiya” Ya amsa da “amin” Miqewa yai kaman zai tafi ya dawo ya sumbaci kuncinta sannan ya wuce. Ta lumshe idanuwa tanajin qamshinsa daya cika wajen. Har lokacin tana jin hannuwansa cikin ko ina nakanta. Zuciyarta tai mata wani nauyi mai wuyar fassarawa. * Har tai sallar isha.i bataji dawowar shi ba. Haka kawai sai taji ta damu tasan wanne hali yake ciki. Ta dauki wayarta ta kirashi wayarshi a kashe. Tai ta trying bata samu ba. Hakan yasa ta shiga tai wanka ta fito tai shirin bacci ta kwanta. Amman zuciyarta dauke take da damuwa musamman da ta sake kiran lambarshi taji wayar a kashe. Tashi tai ta koma bangarensa ta kwanta falonshi kan doguwar kujera. A zuciyarta tana fatan Allah yasa lafiya. Bata san lokacin da bacci ya sace taba. Ji tai ana taba mata fuska a hankali ta bude idanuwanta ta sauke su kan prince ishaq dayake mata wani kallo da ba zatace ga fassarar shi ba. A kunyace ta sauke idonta tana fadin “ka dawo? Inata kiran wayarka shiru” “Chargy na ya kare ban sani ba sai yanzun nagani” Ya bata amsa. Miqewa zaune tai duk kunyarshi ta rufeta saboda yanayin kayan dake jikinta.Shikam ko a jikinsa. Tashi tai tace mishi “saida safe daman dan inji shigowarkane yasa nazo” Kallonta kawai yake baice mata komai ba harta fita daga dakin. Yanda yake ji a zuciyarsa idan ya tsayar da ita komai zai iya faruwa. A hankali yake son ya saka mata sonshi a zuciyarta. Baya son gaggawa a rayuwarsa. Daqyar ya iya tashi ya qarasa ciki ya rage kayan jikinsa ya watsa ruwa. sai juye juye yake kan gado ya rasa abinda yake masa dadi. Ga jikinshi ciwo yake sosai. Ba saba wannan zirga zirgar yai ba. Kasa bacci yai ga yunwa na damunshi. Ya mike ya fito wajen dakin. Da niyyar zuwa ya duba abinda zaici ya fito amman zuciyarsa da kafafuwansa bangaren husna suka kaishi. Saida ya tura dakinta a hankali tukunna yasan me yake. Saidai bazai iya juyawa ba koda yaso. Karasawa yai. Bacci take hankalinta kwance. Ya zauna gefenta ya zuba mata idanuwa kawai zuciyarshi dauke da wani nauyi da ya rasa na menene. Hannu yasa ya shafi gefen fuskarta. Hakan yasata bude idanuwanta cike da bacci ta sauke su kan fuskarshi. “Gentle” ta fadi muryarta ta mishi dadi yanayin yanda taja sunanshi. “Yunwa nakeji hussy” yace mata yana langabe kai. Ga mamakinsa lokaci daya ta mike. Takai hannu ta kunna normal wutar dakin dan marar haske ce bata ma kashe ba bacci ya dauketa. Sai lokacin ya kalleta sosai. Tana murza idanuwanta. Gashinta duk ya hargitse wani ya zubo gefen fuskarta. Dariya yai a hankali. Ta harare shi “ni ko gentle? Zaka nemo mai kawo maka food tunda dariya kakemun” Ta fadi tana komawa kwanciyarta. Dariya yaci gaba dayi yace “Yi hakuri hussy taso ki rakani in samu abinda zanci” Yanda yai da fuska yasa ta kasa mishi musu. Ta miqe zaune tare suka shiga kitchen. Sai tarin snacks. Don haka ya dibi cake da apple sai fresh milk. Su yaci husna na zaune tana kallon shi. Kominshi a nutse yake yinsa. Yanayin taunar abincin ma zaka rantse yanga yake kuma ta kula haka halittarsa take. Saida ya gama tsaf ya sa mata rikici saita rakashi yai brush. Dole ta bishi nasa bangaren yai brush ya dawo dakin baccinsa.Miqewa husna tai ya riqo hannunta. “Ina zakije?” Ya tambaya. Hannunta take kokarin kwacewa tace “bacci nakeji zanje in kwanta” Girgiza mata kai yai alamar a.a sannan yace “nan babu wajen kwanciya?” Fito da idanuwa tai ta langabar dakai gefe guda tana fadin “gentle bana son rikici ka sake ni in tafi” Janyota yai da duk karfinsa ta fada jikinshi. Yasa hannuwa ya rungumeta sosai yana sauke numfashi. Saida ta hadiye yawu yafi sau uku kamun ta samu muryar ce ma “bacci nakeji” Cikin kunnenta yace “hussy…….. Yanayin yanda yaja sunan da muryarshi suka saukar mata da kasala. Ga zuciyarta dake dokawa. Ki kwanta anan. Magana take shirin yi ya cizar mata kunne cikin sigar data sa duk wasu kalmomi suka bace mata. Shiru tai. Jin haka yasa prince ishaq gyara kwanciyarshi sosai. Itama ya gyara mata tata kwanciyar. Tanajin shi yana karanto addu.o.in tsari da saida ya burgeta. Ya tofa ko ina na daki. Ya sake yin wasu ya tofa musu shi da ita. Bata ganin fuskarshi yanayin yanda ya kwantar da ita. Bayanta ne a kirjinsa. Sumba ya manna mata a wuya hadi da fadin “sleep well hussy” Yaja blanket ya lullubesu. Bacci mai nauyi ya dauke shi. Husna kam zuciyarta dokawa take da wani irin yanayi da bata saba jin shi ba. Koya tai motsi saiya sake riqeta a jikinshi. Ta jima batai bacci ba kuma ba zatace ga abinda ya hanata bacci ko kuma ga abinda take tunani ba. Tana da tabbacin koma meye yana da alaqa da prince ishaq. A haka har bacci ya dauketa……..! Bacci take sosai taji ruwa ya digo mata a fuska. Ta bude ido.+ Prince ishaq ne ya sakar mata murmushinsa mai taushi. “Lazy bones” yace cikin sigar tsokana. Ruwan ya sake digo mata. Ta kalle shi. Da alama wanka ya fito dan rigar wanka ce a jikinshi ga gashinsa nan jiqe da ruwan dayake digo mata. Takan jima batai magana ba inta tashi bacci da safe. Dan haka batace mishi komai ba. Ta matsa gaba ta sauka daga kan gadon. Bandakin shi ta shiga taga brushes da yawa. Ta dauki daya ta bare tai amfani dashi. Tai wanka itama sannan ta dauro alwala ta fito. Ga mamakinta kayanta tagani kan gadon prince ishaq bama guda daya ba ba biyu ba. Sunfi kala goma a ajiye. Shikuma yana tsaye sanye da jeans blue sai riga fara kal har shiga ido take kaman yanda kyanshi yake mata wasu lokuttan. Gani yai tana kallonshi ya daga mata gira cikin alamar yadai? Kaman ya fada a fili tace mishi “kayana nagani anan” “Ni ne na dauko” ya amsa mata a taqaice yana dorawa da “ki saka muyi sallah lokaci na wucewa” Jikinta babu karfi ta dauki doguwar riga daya. Duk yawancin kayan ma sababbi ne.Hanyar bandaki ta nufa taji muryarsa yace “Ina zakije?” “Kaya zan sake” ta amsa mishi a sanyaye. Da murmushi a muryarsa yace “nan zakibi to…” Ta juyo ta kalli inda ya nuna. Bama ta taba kula da kofa a wajen ba. Tazo ta gabanshi ta wuce ta shiga inda ya nuna mata. Dakin canza kayane. Babu komai ciki sai wardrobe da wajen shiri. Inda zaka rarrataye kaya da wajen takalma. Dakin kanshi da tsarinsa abin kallo ne. Dan ta tabbata shagon wani ne a kasuwar sabon gari. Kaya ta sake. * Shi kam prince ishaq har lokacin murmushi yake. Yanzun har mamakin kanshi yake. Yana yawan fara,a kuma yanajin farin ciki har ransa. Husna alkhairi ce a tare dashi. Dole ya tura mata sonshi kamun lokaci ya cika. Da duk ranakun da suke wucewa da kusancin alkawarin daya dauka. Ya sauke numfashi. Dai dai fitowar husna. Ta mishi kyau. Namiji ne shi da baya son kwalliya mai yawa jikin mace. Baiqi yaga fuskarta fayau din nan ba. Babu ko powder balle wani janbaki. “Barin sauri in dauko hijab” ta fadi tana nufar kofa batare data jira amsarshi ba. Murmushi ya sake yi. Batai minti biyarba ta dawo. Shiya ja sallar har suka idar. Husna tai azkar dinta na safe data saba tai addu.o.inta,taima nasir na samun sauki. Saita tsinci kanta da yiwa prince ishaq addu.a da fatan tabbatar alkhairi a zamansu. Abinda bata taba yi ba. Har wata nutsuwa ta daban taji ta shigeta. Mikewa tai takoma kan gadon ta kwanta. Prince ishaq kam Qur.an taga ya bude drawer in kusa da gado ya dauko. Tanata kallonshi ya bude yana karantawa a hankali yanda shi kadai zaiji sautin muryarshi. Sai taji zuciyarta na mata wani iri. STORY CONTINUES BELOW Tana son jin muryarshi yana karantawar. Dan haka tace “gentle kayi yanda zanji Kaga kai ka samu ladan karatu nikuma na saurare ko?” Bude murya yai yaci gaba da karatun. Ta nutsu tana saurarenshi. Kira.arsa na burgeta. Muryarshi na shiga wasu wajaje a jikinta da bata san akwai su ba. Harya idar yai addu.o.i sosai ya sauke idanuwansa akanta. “Ina kwana” ta furta a hankali. “Kin tashi lafiya?” “Alhamdulillah” ta amsa mishi. Bai sake ce mata komai ba. Ya ja kafet din dayai sallah akai ya linke shi. Kan kujera ya koma ya zauna ya zuba mata idanuwanshi. Tama soma sabawa da yanayinshi. Zasu iya awanni a haka. Yana kallonta baice mata komai ba. Ba koyaushe magana ke damunsa ba. Bata san sanda bacci ya sake daukarta ba dan bai wadace taba daman. Saidai tashi tai ta duba ko ina dakin bataga prince ishaq ba. Ta shiga bandakinshi ta wanke fuskarta da bakinta ta fito. Wajen falon ta fita baya nan. Ta duba agogo goma harta wuce. Shisa take jin yunwa na damunta. Dining ta nufa ta dibi iya abinda take jin zataji. Dan har mamaki take. Abincin da ake dafawa bata san ya zasuyi dashi ba.1 Ko sun kai su goma ya masu yawa. Dan gashi nan kala kala. Saidai suci su bari. Ta gama tsaf. Ta je dakinta ta dauko wayarta. Ta dawo babban falo. Prince ishaq ta kira ringing din farko ya dauka. “Kin tashi?” Ya tambaya. Ta amsa da “um banganka ba ka fitane?” “Ina garden zaune ina kallon tsuntsaye sunata kukansu. Bakyaji ne?” Ya fadi. Sai lokacin ta nutsu take jin kukan tsuntsayen. Cike da mamaki tace mishi “Ina garden din yake?” “Cikin gidan nan zakizo ne?” Ta girgiza kai kaman yana ganinta ta dora da “Kazo mu tafi wajen Nas” “Tam kin shiryane in taso?” Ya fadi daga dayan bangaren. “A.a barin tashi. Nan da minti talatin kazo nagama.” Ya amsa da “Tam”1 Ya kashe wayan. Tashi tai ta nufi bangarenta. Ta sake yin wanka ta shirya. Tana fitowa ta ga prince ishaq ya shigo. Kinyi kyau ya fadi yana matsowa dab da ita. Zuciyarta taji tana dokawa tana jin kamshinsa ya cika mata hanci. Hannuwanshi yasa ya tallabi fuskarta. Sumbatarta yai a kunci sannan yace “Mu tafi ko?” Kai ta daga masa dan bakinta ya mutu. Jikinta ma ba shida kwari. Ya kama hannunta suka fita. * Kan kujeru suke zaune sun tisa nas a gaba kaman kallon da suke mishi ne zaisa ya bude idanuwanshi. Doc dinshi yace musu tun farkawar dayai bai sake ba. Amman babu wata matsala har yanzun. Su duka bamai magana kowa da abinda yake sakawa a zuciyarsa. Husna nata kallon Nas. Can taga kaman ya motsa. Matsawa tai da kujerarta kusa dashi sosai ta sake kallonshi aikam ya sake motsawa. “Gentle!” Yanayin yanda ta kirashi sosai yasa shi dagowa ya kalleta. “Nas motsi yake fa ta sake fadi” Shima matsawa yai kusa suka zuba mishi ido. A hankali ya bude idonshi yana kallon wajaje cikin dakin. Kamun prince ishaq yace komai husna ta fice da gudu ta kira doctors. Husna kam ba zata iya kallon koma menene zasuyi ba. Don haka ta fita ta zauna daga waje. Ba afi minti ashirin ba suka fito. Akace ma husna zata iya shiga. Hamdala suke tayi daga ita har prince ishaq ganin Nas ya nata kallonsu duk da har lokacin baice kala ba. Saidai murmushi dayake ta musu. Amman likitanshi yace ba komai bane. Zai magana idan ya shirya. Sunkai awa biyu a asibitin har saida bacci ya dauki Nas. Daqyar prince ishaq ya lallaba husna su koma gida da yamma su dawo. Suna cikin motane ya kira gida yake fada musu. Kowa yaji dadi ba kadan ba. Anata ma Allah godiya dan babu wanda yaba Nas din tashi. Suna karasawa gida husna zata fita daga mota prince ishaq yace+ “zanje wani guri i will call you ok?” Tadanyi jim sannan tace mishi “to please take car” Murmushi ya kwace mishi. Batasan lokacin data sa hannu taja mishi hanci ba hadi da fadin “murmushin me kake?” Ya daga mata girarsa cikin sigar dake kara masa kyau yace “bakomai naji dadine kin damu dani” Dariya husna tai kawai ta juya ta bude murfin motar zata fita. Riqo mata hannu yai yana fito da idanuwa. “Hussy ina zaki? Bawani a dawo lafiya kiss? Kawai zaki barni” ya fada a tabare. Wani lokaci har mamakin shi take. Fuskarshi ta tallabo da hannuwanta ta sumbace a kunci kaman yanda yake mata. Ta hada da fadin “tam a dawo lafiya” “Ko kefa” Ya fadi yana daria. “Saina dawo” Ta fita daga motar bata amsa shi ba. Saboda wani nauyi da bakinta yai mata. Tasan kota tsaya gardama ko dai tai mishi koshi yai mata. Datai masa ma sai yafi mata sauki. Kamshinsa kawai taji. Da shi yai mata kafafunta sanyi zasuyi. Ta kuma rasa dalili. Tana shiga daki alwala tayi. Tai sallah sannan ta sake kayan jikinta ta saka doguwar riga dan duk kayanta sune ta koma babban falonsu ta zauna. Bata jima ba prince ishaq ya shigo. Sallamarshi ta amsa yace kinyi kyau. Ta kalli kanta cike da mamaki. Fuskarta dai ba kwalliya. Karasawa yai inda take ya zauna yana mata murmushin sa. Hannu yasa ya zagaye lebenta sannan yace “yes kinyi kyau. Ban cika son kwalliya a fuskar mace ba” Kallon mamaki take masa a ranta tana fadin. Mutane iri iri. Kowa da kalar nasa ra.ayin. Iska taji ya hura mata cikin fuska ta rufe idanuwanta tana dariya. “Nagaji fa” ya fadi da wani yanayi a muryarshi. “Sannu gentle” husna tace tana kamo hannun shi. Lokutta irin haka ita kanta mamaki take ba kanta. Haka suka zauna shiru dan ta soma sabawa ma. * Sun kai mintina talatin a haka kamun yace ma husn “in tambayeki?” Tace “why not” “Menene burinki a rayuwa?” Dariya tai kawai dan burinta shine ta auri ammar kuma sai komai ya canza. Hannunta taji ya dumtse cikin nashi kamun yace kinyi shiru. A hankali tace “Najima banida wani buri saina ammar ya karasa karatu ya samu aiki muyi aure and komai saiya canza” Lumshe idanuwansa yai yanajin wani daci a zuciyarsa. Duk da hakan bai hana ce mata “i am so sorry hussy” STORY CONTINUES BELOW Kallon fuskarshi tai “saboda me?” Ta bukata. Saida yaja numfashi ya sauke shi sannan yace mata “saboda nasan yanda akeji in burin mutum bai cika ba. Zanyi komai dan kauce ma shiga tsakanin wani da burinsa” Hannunshi ta sake dumtsewa sosai tana son fada mishi abubuwan data rasa kalaman da suka fi dacewa ta cikin hannuwan nasu. Muryarta na rawa tace “ba laifinka bane” “Hmm” kawai ya fadi yana sake kwanciya cikin kujerar abinshi. Basu san lokaci yaja ba saida sukaji ana kiran sallar la.asar. Su duka suka tashi kowa yai bangarensa. * Alwala husna take zuciyarta cike da saqe saqe. Sallar la.asar ta yi ta zauna kan daddumar tana karatun Qur.ani. Data idar ma bata tashi ba. Akai tai zamanta tana tunanin abinda ta rasa dakuma abinda takejin ta samu a yanzun. Saidai batasan me zuciyarta take ciki ba game da auren su da ishaq. Kwankwasa kofa taji anyi kamun ma ta amsa ya turo kofar ya shigo. Yai mata kyau sosai cikin shaddar shi light blue da alkyabba dark blue. Kodan bata saba ganin shi da kaya masu kala bane. Shisa taga ya mata kyau haka. Kan gadonta ya zauna. “In shirya ko?” Ta tambaye shi. “Ki dora abu saman kayanki. You are more than ok” ya amsata. Hakan kuwa tayi. Tare suka fita driver ya kaisu asibiti. Suna shiga doc din nas suka gani. Da fara.a yace “yanzun kaizan kira Nas ya tashi yana tambayarku” Basuma amsa shiba da sauri suka nufi dakin Nas din. “Antina” Nas ya fadi muryarshi can kasa. Prince ishaq ya daquna fuska yana fadin “ita ka soma gani Nas?” Dariya husna tai ta juya ta mishi gwalo.Ta karasa ta zauna gefen gadon Nas. “Alhamdulillah Nas sannu kaji Allah ya kara baka sauqi” husna ta fadi muryarta na rawa saboda kukan da taji yana shirin zuwa mata. “If you cry bacci zan koma Nas ya fadi” Sukai dariya gaba dayansu. prince ishaq ya kama hannun Nas yama kasa cewa komai dan farin ciki. Haka sukaita hira kadan kadan kamun wata likita tazo tace musu zasu gajiyar da Nas lokacin allurar shi yayi. Fuska a hade Nas yace “bafa maimun allura. Yaya kwanana nawa a kwance? Kumin alwala in rama sallolin da ake bina tukunna” Husna tace “Nas zaka iya kuwa? Jikinka babu karfi” Prince ishaq yace “yeah kana da gaskia a kira su su ciccire maka wannan tarkacen if motsaka babu matsala” Haka kuwa akai. Daqyar likitocin suka yarda dan Nas din da prince ishaq sun dage. Daga zaune Nas ya rama duk sallolin da ake binshi suna zaune suna hira. Prince ishaq ya kamashi ya koma kan gado. Aka kira doc dinshi. Ana masa allura bacci na daukarsa. Basu suka koma gida ba sai wajen 9 na dare. Kowa ya wuce bangarensa. * Wanka kawai prince ishaq yai dan sunyi sallolinsu tun a asibiti. Ya saka kayan bacci ya kwanta. Wayarshi ya dauka ya kira husna. Ringing din farko ta dauka. “Hello…” ta fadi muryarta da alamar bacci. “Hussy…” ya ja sunanta. “Gentle na fara bacci fa” ta fadi a shagwabe. “Kizo please” ya bukata. Husna ta girgiza kai kaman yana ganinta tace “kayi baccinka nima bacci zan” Kashe wayar yai. Baya son gardama ko kadan. Ta kira yanaji harta gama ringing bai dauka ba. Yakai hannu ya kashe wutar dakin. Yai addu.a yaja bargo ya rufe jikinshi duk da yasan ba baccin zai ba. Yanata tunane tunane abinshi sam baiji turo kofar ba sai motsin mutum dayaji. Hannu yakai wajen switch din dakin ya kunna wuta haske ya gauraye ko ina. Husna ce kwanciya tai batace masa komai ba. Ya rikota jikinshi. Sam taki kallon fuskarshi. Ya sumbaci goshinta yana fadin “haba mana hussy.” “Kaine na kira baka dauka ba” ta fadi da wani yanayi a muryarta. Sauke numfashi yai yace . “banason gaddama ne kuma banason takura miki” Shiru tai tana kwantar da kanta a kirjinshi. “Saida safe” ya fadi. Ta daga mishi kai. Saida yai mata addu.o.i ya tofa mata sannan ya kashe wutar dakin yana gyara mata kwanciya a jikinshi. Yana jin canzawar numfashinta alamar bacci ya dauketa. Yai murmushi a zuciyarshi yana lissafa watannin daya rage masa ya tura mata sonshi. Kamun shima ya rufe idanuwansa bacci ya dauke shi.