SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 30 KARSHE
Mansur kula da Nazeefa yakeyi sosai, Duk yawancin aikin gidan indai yananan baya barinta tayi, shi Da kanshi yakeyi, Riritata yakeyi kamar wata karamar baby, ita kuma dagata ana ji da ita kara langwabewa takeyi Kamar karamar yarinya.+ Bangaren Ummie kuwa tunda taji labarin Su mansur zasu tashi tasama ranta duk yanda zatai ta aureshi sai tayi, tinani tayi tace a wannan time din ne ya kamata na hargitsa komai dan ya aureni! Wani tinani tayi tace kaka yau bikin ya mansur wata nawama? Tace eh Ya kusan wata shida fa, Ummie tace tabdijam Allah yasa matar ba juya bace bata haihuwa Dan ko bantajin labarin ba Kaka tace to nimadai hakan nake tinani Dan banga alamun ciki a tare da ita ba, komai da karfin jiki takeyi Ummie tace tab Lalle kuwa AI dolema Mansur ya Kara aure, Kaka tace ba dolenshi yaushe za’aita zama haka tab *** Bangaren Abdallah kuwa matarshi har ta haihu anyi suna ansa ma yaron AbdulKareem Ana cemai Abdul, yaron Yaci sunan mahaifin Abdallah, Yaron masha Allah tabarakallah Bangaren Ameerah kuwa soyayyansu sukeyi da Mubeen dinta, Gininshi na school da yakeyi ankusan Karasawa saura kadan, Gidan da zasu zauna da Ameerah kuwa an gyarashi, Itama ba zama takeyiba Dan shige da fice na amare, Dr Bashir kuwa Cikin ikon Allah ya shiryu, hatta frnds dinshima ya chanza ya samo na kwarai Feeezz kuwa shima ya sama aiki, Amma be Fara neman aureba Dan yace aure ba yanzuba Faeeza kuma ta sama wani lecturer Da yake A.B.U sun tsaida maganar aure dashi soyayya sukeyi abunsu gwanin sha’awa Dan kunsan faeeza ba kanwan lasa bane wajen Iya soyayya, kullun birkita Mr lecturer dinta takeyi da kalamai masu Ratsa zuciyar masoya *** Bangaren Gidan su Nazeefa kuwa iyayanta sunje Chan kauyensu sun taho da wata mata da mijinta da yara Uku mata biyu namiji daya, yar uwar Umma hafsatu ce, suna zaune a safe contain din gidan, Mijin na kula da flowers din gidan da bude gate, ita kuma Matar tana ma Umma hafsatu shara da wanke wanke, tun basu sabama har suka saba abunsu! Yaran kuma kanana ne, babba sunansa jamilu, Se Rashida da karamarsu Masa’uda Nazeefa tace asasu a makaranta daidai bame tsadaba saboda basusan muhimmancin karatuba, Iyayansu dai sukai godiya. Dadi sukeji wai gasu a birni suna shan jar miya kuma Suna kallon fanka na juyi a sama, Ga duka gidan yasha interlock sukace AI ko a kasa sasa suci abincinsu, Lol *** Lokaci nata tafiya, a kwana a tashi ba wuya har anyi ramadan angama, Bikin Su hassan shima ansaka kafin babbar Sallah, Su Mansur kuwa Suma sunata shirye shirye Dan Sun kusan komawa Chan, kuma se sun koma za’ai bikinsu Hassan din Kusan lokaci dayane dana Mubeen da Ameerah ___ Chan gidansu Hajiya mum Mansur, hankalinta itama a dan tashe saboda taji shuru, Alhajine yace haba hajiya karkiban kunya mana, shifa mutuwa aure da haihuwa duk lokacine, Idan har Mansur basu haihuba Zan Iya cewa gadone! Saboda kinsan ana gado, kuma shi kadai muka haifa, Kema ku biyune a gidanku daga Maman ummie sai ke, kinga kuwa Idan har Allah yasa basu sama haihuwaba ba wata Matsala bace Share hawayen da ya zubo a idonta tai tace dukda haka Alhaji ai itama nazeefan ita kadai aka Haifa watakil ta wajentane, Hmm yace Mata kenan, wai me yasa wani lokacin tinaninku kadan ne? Tace bazaka ganeba Alhaji, Yace to ganar dani tace kodai ze Kara aurene? Kallonta yai yayi murmushi yace Karki manta da Kafin ya aure Nazeefa me Dr yace mana? Karmu dinga barin ranshi ya baci amma idan yazo ki sameshi kui magana nidai baruwana, kinga idan hankalinshi ya tashi ya Shiga damuwa sai mu rasashi gaba daya STORY CONTINUES BELOW Saurin share hawayenta tayi bakinta nason furta wani magana amma sam ta kasa, Daga hannu tayi tace ya Allah ka azutasu da yara dayyaba, da sauran masu neman haihuwa Amen, Alhaji kallonta yayi yace KO kefa? Tace hakane *** Nazeefa cikin baccinta tai mafarkin Ga wata nan Ta biyota tana seta kasheta, Firgigit ta tashi, ta sanar da mansur, Yace Love kodai kinada Aljanune? Tace Aa Wallahi, Yace OK inshaa Allah bakomai, I’ll be by your side duk rintse duk wuya tace OK Safiya nayi as usuall, kaita wajen aiki yayi sannan ya wuce nashi aikin, Koda yaje around 10, Samun Ummie yayi a entrance din shiga, kallonta yayi ya watsar, Seda ta tabbatar yaje office dinshi sannan ta biyoshi, da da farko an hanata shiga seda tace ita kanwarshi ce sannan aka barta Shiga tayi da sallama, Ya mik’e yace Ummie meyasa bakida hankaline? Nice zakace banda hankali tana magana tana tunkaro wajenshi tana kokarin tabashi Hasbunallahu yace hade da cewa get out a daidai lokacin Wani Oga shima ya shugo, Yace Oga meke faruwa? Ummie jikintane ya fara rawa sosai, tana tsoron Karya dis gata Mansur ne yace Wai aiki take nema nace Mata idan ansamu Vacancy Zan kirata shine Kullun fa se tazo, Oga Muktar yace baiwar Allah wannan me adalcine indai Takardunki sunkai yanda akeso za’a daukeki kiyi hakuri komai a hankali akebi, Sannan yai ficewarshi Yana fita ta kureshi da ido, Ita jitai ma ta Kara sonshi, Hugging dinshi taje zatai ya wanka Mata Mari yace stupid girl! Fuuu taji haushi tace zakaga stupid girl kuwa, Tana fita Gidan Nazeefa ta nufa Koda taje Nazeefa bata nan Dan haka ta jirata seda ta dawo Mansur na shirin kiran nazeefa kenan akan yau karta koma gida zaizo ya dauketa Call dinta ya shugo tace Ai tama dawo amma shi Sam hankalinshi be kwantaba yace ba yanzu zedawoba se Chan anjuma saboda zai bada record din komai Da komai ne tunda zebar aikin se sunga komai, tace OK karka damu Tana ganin Nazeefa ta shiga gidan ta bude tazo ta fara knocking Koda taje bude gate din ta gane voice dinta Dan Tasha zuwa tagama iyayinta ta koma, Bude Mata kofa nazeefa tayi tace Sannu da zuwa, tsaki Ummie taja ta zage Nazeefa sosai, tace mata juya Mara haihuwa, kinbi kin asirce mana shi munkasa gane kanshi Tuni zuciyar Nazeefa ya hassala suka Fara musayen baki, Mansur na Chan hankalinshi a tashe dan yasan comfirm Ummie Zataje Chan gidan! kiran Abdallah yayi yace Dan Allah ya lekamai gidanshi yaga KO Nazeefa ta dawo tunda basu da nisa, hikama yamai Dan karma ya gane akwai wani abun, yace OK Ina hanyama yanzu Zan wuce ta kofar gidan Zan tsaya na duba Yana zuwa yaga Ana fada da Ummie da Nazeefa yaji Ummie se Zagin Nazeefa takeyi amma batace komai ba, kokarin rabasu yayi sannan yai maza ya Kira Mansur yace yazofa akwai matsala. tuni ya dauka excuse ya dawo gida Koda ya dawo Abdallah ya budemai kofa ya shugo, Ummie ya gani a gefe, Kallon Banza ya watsa mata, Yace ahakane Zan aureki? Kina zuwa har gida kina cima matata mutunci, Nazeefa tace ohh Ai se yanzu nagane, Dama sonshi kikeyi? Gashinan saiki aureshi in nine banda matsala kizo mu zauna, Jikin Ummie ne yai sanyi, Jin kalaman Nazeefa, Wayyo Allah tace bakin alkalami ya bushe, inama nabi abun nan ta Lalama Sannan Mansur yace duk su Hajiya sai Sunji Nan take ya kirasu ya Sanar dasu, salati suka saka sukace gasunan zuwa Ba’ai 30mins ba Dad mansur sukaje suka dakko kakus, Suka taho tare, Ummie Duk kunya ya kamata tanamai nadamar abunda tai Mum Mansur tace kinban kunya, Nan take ta sanar da mahaifiyarta, tace Anshiga uku, ba ummien bata akai tasa loudspeaker tai mata tatas, sannan tace ta taba Nazeefa hakuri, ashe bance Kar inji wannan zancen ba? Mansur kuwa yaji wani karfi ma yazomai aranshi yace Alhamdulillah dama ita kadaice matsalarshi Nan Gaba daya sukaba Nazeefa hakuri, tace bakomai, komai ya wuce yunkurin amai ta fara kan kace meye Ta Fara amai a gaban su mum da dad Tuni Dad yace akaita asibiti duk yanda akai bata saba da hayaniya ba, su sam basu kawo komai a ransuba, suka wuce gida Mansur da Abdallah kuwa suka kaita asibiti Awwwn Muje Zuwa Kai Nazeefa asibiti sukai, Koda sukaje chan zazzabine me zafi ya rufeta, Gwaje gwaje akai mata Sannan Ta samu tadanyi bacci+ Bangaren Ummie kuwa koda suka dawo gida kakus sata agaba tayi sosai tanata Mata fada, Ummie duk taji ba da dadi ga mutuncinta daya zube gaban su hajiya, ba Wanda ya bata shawara ita da kanta tace zata koma gida lol Dan wannan abun datai da kunya Washe Gari, Umman Nazeefa ce tazo ta zauna da ita saboda mansur ze fita wajen aiki, koda yaje duk bayan 20mins yake Kira ya jikinta sai Umma tace da sauqi Haka ya dinga Kira har ya gama aikinshi sannan yai resigning letter yakai musu, sukaimai fatan alheri Dan Dama cikin week dinnan Da zamu shiga zasu tafi Chan garin Ya rabu da kowa lafiya wajen aikinsu sannan suka nuna dai basuji dadiba Dan yana daya daga cikon masu kwazo na wajen aikin Koda ya dawo, nan nan ya farayi da matarshi, har Umma tadanji kunya Dan soyayya yake nuna mata a gaban kowa shi ba abun daya shafeshi, Umma kuwa komawa gida tayi Dan bazata iya ganin wannan soyayyar tasu ba Chan da yamma result ya fito Nazeefa is positive tanada Ciki, Kara kallon result din yayi yace Alhamdulillah, tana kwance yakai mata wani irin kiss yace Maman boy ko baby Binshi da kallo tayi tace uhmmm, yace kinada cikifa! Wani yunkurin tashi tayi yai sauri yace nooo kwanta babyn baby, maman baby kuma, wani murmushi tayi ta daga hannu sama tace Alhamdulillah… Murna sosai yayi Kiran mahaifiyarshi yayi tace har muna shirin zuwa, Yace Mum albishirinki? Tace goro, dad ne ya kalleta da tace goro yasan albishir za’ai Mata Yace Nazeefa nada ciki, mik’ewa tayi tace Alhamdulillah Alhamdulillah Dad yace meya faru kashe wayar tayi tace Alhaji tashi mu tafi Nazeefa nada ciki, Kai Alhamdulillah. Baban Mansur kuwa shima daga hannu yayi yace Alhamdulillah, Allah ya inganta nima nace Alhamdulillah Ameen Tashi sukai suka tafi hospital din, koda sukaje su mansur ne kadai, a dakin, Kiran Umma hafsatu yayi ya sanar da ita, kai Alhamdulillah tace itama baban Nazeefa na zuwa tamai albishir shima yace Alhamdulillah kowa yayi murna matuka Dr Ne ya shugo ya basu supportive drugs (magungunan) dazai Kara tema ka Mata, yace kuma ta dinga yawan shan ruwan gishiri Da sugar, Sukace sungode Gida suka wuce, mansur kuwa se kiran yan uwa da abokan arziki yake tayi yana sanar dasu, kowa sedai yace Alhamdulillah, Allah ya inganta Amen Tunda suka dawo gida daidaida cukali Nazeefa bata ta dauka komai Mansur yake Mata Hajiyar Mansur itama kullun seta Kira kusan sau 7 tana tambayarta ya jikin nata, tace da sauqi Chan Gidan sarkin yobe kuma, An gina ma su Nazeefa katafaren gida da inda Su hassan zasu zauna da matayensu, Su Hajiya kuma suna tare da su hajiya asma’u da sarki Chan zasu zauna tare Ana Jibi zasu tafi Nazeefa ta roka beloved husband dinta tacemai Dan Allah zataje gidansu ta kwana tayi bankwana da Iyayanta, Qin yarda yayi wai zata barshi Shi kadai wazai tayashi kwana Hajiya ta Kira tace Dan Allah taiwa mansur magana tanaso taje gidan ummanta ta kwana, tace ok diyata ba matsala, Suna gama waya ta kirashi tace ya barta Aikuwa dakyar ya barta, kafin yakaita kuwa yasha shawaba mansur ya dawo kamar wani karamin Yaro, kwana day an nan dazatai ji yake kamar zatai shekara Hakanan duk wasu abubuwa da takeso ta kwashe takai wa mamanta Dan chan gidan Sarki sabon zubi za’ai musu, ciki harda mota ta Kai gidansu, sannan aka sama wani Dan amana yana kula da inda Nazeefa ke zuwa aiki STORY CONTINUES BELOW *** Kwananta daya randa Mansur zaizo daukarta tayi kuka sosai Dan har kawarta Ameerah seda ta Kira sukai sallama, sunsha kuka sosai kamar karsu rabu, Kamar tace bazatajeba, mahaifiyarta ta Kara da cewa tayi hakuri, gidan sarki ne, na tabbata suna Sonki so Dan Allah karki damu, ke dai kasance me hakuri da tsoron Allah, tace inshaa Allah, tace kuma kinga cikine dake, karkisa wani damuwa aranki, ga waya nan da kinji missing dina Ki kirani tace OK Ameerah tace tabbas kuwa, Chan dare Mansur ya zo dauketa daganan ya ajiye Ameerah sunata yan koke koke, gidan hajiyar mansur suka wuce, inda da zasu zauna suka nufa suka sauke gajiya Dare nayi Hajiya ta kira mansur tace suzo sui dinner, Gaba dayansu suka zauna kan dining table sukaci sukasha Suna zaune Sarki ya Kira Dad mansur yace an matso da bikin su hassan nanda sati biyu, Dad mansur yace to bakomai gobe din munanan zuwa yace OK Chan Fadar Sarki, sanar da matarshi yayi hajiya bilkisu akan cewa gobe sunanan zuwa! Alhamdulillah tace, ta Kira jakadai akaje aka Kara gyara inda Mansur Da Nazeefa zazu zauna ** Su mansur suna komawa part dinsu, Nazeefa tace mu kwanta kaji dear, yace wani kwanciya yau baza’a bani ba? Eh tace kaga ina gidan surukai nane karmu makara, Shagwaba ya fara yace jiyama haka fa ban samuba, bakomai, Nazeefa Dariya tai sosai tace I love you,love of my life. Sannan suka kwanta Saboda sun gaji har makara kam sukai, tana tashi ta Fara shirya kayan break fast, yace noo Hajiya zatai komai, tace too amma fada da kunya Suna cikin hakane aka kawo masu break fast sukaci, sannan Dad yace su shirya zuwa 10 flight dinsu zai tashi Wanka sukai suka shirya, suka fito waje, Dad yaiwa me gadi warning akan ya kulamai da gida, wanda suka shifting dashi shima yana tsaye a wqjen, yace dukansu kuje Ku dawo da matayenku nan nidai a kulamun da gida zamu dinga dawowa time to time kuma kunada number wayana in akwai wani abu Ku kirani sukace to Mungode Allah ya Kara daukaka, Kai ma driver ga part din mansur chan Wanda kafin yai aure yake zaune ciki bakomai, ka dauka daki daya me toilet din Ku zauna a ciki, Ku uku naba amanar gidana sukace mungode Airport suka nufa, jira kadan sukai jirginsu ya Iso, basui 1hr ba suka isa yobe, garin Fulani! Already sarki ya turo masu da driver’s da body guard da dogarai, suna isa suka shiga mota se Fadar Sarki Suna zuwa suka tadda gidan kamar ana biki, ashe hajiya Bilksisu me gagon zinari ta shirya wani hadadden Liyafa Dan taron Amarya Nazeefa, suna zuwa aka shiga da Nazeefa wani daki, nan take jakadai suka shiryata ta fito a cikin alkebba, aka sa Mata kayan sarakuna! Shima mansur Haka tsab ya fito cikin Kayan sarakai Zama sukai kamar sabbin couple, Mansur jiyai kamar yau yake cikakken ango Dan wani nishadi da yakeji An gayyace mutane sosai ciki harda Wanda su Hassan da Husaini zasu aura, Da yawa yan wajen sunsan mansur saboda ya taba za a gidan Nan aka farawa Nazeefa kirari kamar sabuwar Amarya anyi biki Iya biki, Se Wanda ya gani, chan angama hajiya Bilkisu ita da kanta ta dauka Nazeefa ya kaita dakinta, Tace ki zauna damu tamkar mu muka haifeki Nazeefa Ina sonki harga Allah, Allah ya Kara baku zaman lafiya tace Amen Nan ta kawo mata bayi guda 10 Wanda zasu dinga mata aiki, da duk abunda takeso! Angama biki lafiya kowa ya koma gidanshi, Hajiya mum Mansur kuwa tayi farin ciki sosai, suma waje aka basu a gidan ita da mijinta Dan girman gidan Sarki Ya Kai wata unguwar .. Inda akakai Nazeefa kuwa Wasu plats ne ne guda uku aka sata ana tsakiyan, daya hassan daya kuma Hussaini Alhamdulillah tace data fado family din da ake sonta sosai, kallon Gidan tayi ta window taga kamar ba ban ta taba zuwaba, Dan gidan ya chanza ashe an sakemai tsarine ga ko Ina flowers, taga falon fa take ciki yafi nada Wanda aka kaita tana amarya Alhamdulillah tace ta kwanta a gado, Wani sanyin Ac me shigarta ta ko ina Mansur ne ya shugo, sanye Da kayan sarakai tace prince, yace ta princess “tace kayi kyau yace kema haka, Nan Hajiya tace kowa yabar sasan abarsu suci soyayyarsu Dan tasan suna cikin farin ciki Dad mansur kuwa da mum dinsa godiya sukai musu Dan basu taba tsammanin hakaba, sukace matsayinku yafi haka Nazeefa da mansur kuwa kamar zasu cinye junansu a ranar, dan suna making love ne In a cool and fashion way! Hankalin kowa kwance, Washe gari Nazeefa ta kira mum dinta ta sanar da ita ga irin tarban da akai musu, tace kinganiba ba kisa hakuri a ranki haka suketa rayuwa kowa hankakinshi kwance! Hajiya bilkisu kuwa matar sarki dataji Nazeefa nada ciki dadi taji sosai Tace badan badan ba da ta dawo part dinta tana kula da ita, kowa kokarin farantawa Nazeefa rai yakeyi Dan tazama super star na gidan Wash….. Bikinsu hassan da Hussaini Tun Ana sauran sati daya yan uwan suka fara zuwa! Nazeefa kuwa Idan mansur sun fita dasu hassan dakin mamanshi take zuwa tai kwanciyarta, Taita tambayarta meta keso, sedai tace bakomai Ga baki sunzo Dan haka nazeefa ta tafi sashen hajiya bilkisu, tana sonta sosai kuma tana jin dadin hira da ita, mansur ne ya Shugo wai suje su kwanta, makalewa tayi a bayanta tace ita sam bazata je ba hajiyane tace meya faru? Da yake nazeefa ta sake jikinta da ita sosai tace wai yace muje Mu kwanta kuma ga baki a gida, Hajiya bilkisu tace gaskiya anan tadan fika gaskiya Ga baki kaje ka kwana dasu hassan mana da yan uwanka, ni nama taba ganin bita zaizai irinka kuwa? Kunya yaji yai ficewarshi, Nazeefa kuwa tamai gwalo, Sannan Ta dauka wayarta ta mai text I’ll miss you to night, I love you, Karantawa yayi, reply yai mata yace bawaninan zamu hadune ai duk sena fanshe Lol, yana tura mata, karantawa tai, Smiling tayi ta ajiye wayarta Hajiya Bilkisu kuwa Gyara mata gadonta tayi tace inzaki kwanta gashinan, hada mata ruwan wanka masu aikin sukai ma nazeefa, zuwa tai tai wankarta tana dawowa ta ga ankawo mata kunun gyada me dadi! Zama tai tasha hankalinta kwance sannan tahau gado tai baccinta me dadi *** *Agurguje……* Ranar daurin aure an daura auren Hassan da matarsa Zainab, Shi kuma hussaini da matarsa Maryam! Anyi biki Iya biki se wanda ya gani Koda aka kawosu gaba daya aka hadasu akai musu fada, Akace nazeefa ce babba su zauna Lafiya lau banda rigima, nan duk toshe dayane, sukace inshaa Allah Ango Hassan da Hussain se rawar kafa sukeyi ankawo Musu amaransu, Mansur yaita tsokanarsu yana JJC sukace eh din sunji Dazasu shiga dakunan su mansur yace adaiyi ahankali sedai sukai dariya sukace ance maka mu irin kane? Yace Oho bansa niba, Dakunan su suka shiga Kuwa yaci angwancinsa yanda sukeso, Gasu ga Nazeefa amma basu taba haduwa ba sai Bayan sati daya koshi Mansur din, randa suka hadu kuwa sunsha tsiya wajen mansur “yace ku haka akeyi daga kawo muku amarya se inji shuru, Lol da yake nimadai inada mata, Hassan ne me Iya magana a cikinsu yace eh din Kaifa ka sa mana ido, Kai inaji kayi wata ma baka fitaba, Mansur kyalkyalewa da dariya yayi Dukansu Zaman lafiya sukeyi abun se Wanda yagani, jikinsu yayi kyau kamar wasu yan Mata, kansu a hade yake duka su 3 din, yau aje sasan wane ai hira gobe aje na wanchan haka suke tayi Su Mansur da hassan da Hussaini suma an Neman masu aiki kowa na zuwa Watarana Da daddare kowa na zaune da matarshi me martaba ya kirasu dukansu, Kowa yazo suka zauna a fadan tsarki, Yace to Alhamdulillah inshaa Allah this year zaku tafi Hajji kowa da matarshi zasu tafi, dadi sukaji sosai, Sannan yai musu addu’a sukace Amen Kowa dakinshi ya koma, nazeefa na shiga dakinta wayarta ta dakko, Ta Kira ummanta take sanar da ita Ummanta tace Masha Allah muma zamu tafi, inata tinaninki nace kodai zamu biya dake ne ashe kema zakuje, to Masha Allah, Allah ya Kara hada kawonanku tace Amen Cikin Nazeefa yadan fito, Hajiya bilkisu da asma’u kowa Iya gwada mata So, infact gaba daya gidan sunason Nazeefa *** Lokacin tafiya hajjinsu tayi, Dan haka suka shirya dukansu Ranar da zasu tafi kuwa Aka kaisu airport, jirgi na sauka, kowa ya rike hannun matarshi suka tafi, koda sukake chan kowa na makale da matarshi, STORY CONTINUES BELOW Kwanansu kusan 6 saiga ummanta da babanta sunzo k’asa me tsarki, nan sukai waya da mamanta, tace ga inda suke sannan dukansu sukaje suka gaisar da mahaifiyar Nazeefa, Zainab da Maryam kam sukace wallahi kuna kama da mama sedai kawai kinfita haskene *** Sunyi aikin Hajji lafiya, Sundawo gida, kowa ya siyo tsaraba daidai gwargwado, Zamansu lafiya sukeyi, Sedai nazeefa yau lafiya gobe ciwo, saboda Cikinta yadan kara girma, idan mansur bayanan kwanciyarta take tai ta bacci, idan ko yananan yadinga damunta kenan Wata ranar litinin tana zaune Ameerah ta kirata tace kawata yaushe zakizo kinsan this week ne bikina Nazeefa Tace kai dan Allah, inasha sefa next week kice mu Fara shiri! Ameerah tace eh an matso dashine tace OK Inanan zuwa inshaa Allah sannan sukai sallama Mansur na dawowa tamai sannu Da zuwa Ta kawomai abincinsa, yace meya farune naga se murna kikeyi? Tace Bikin Ameerah ne this Week in Allah ya yarda, Dan tsuke fuska yayi yace to Allah ya bazasu zaman lafiya amma ba inda zakije! Kallonshi ta tsaya yi tace banganeba! Yace yes dama bazaki ganeba, salon kije wazai dinga kula dake kinsan kinada ciki! Beside ma bazan Bari kije ke kadaiba saboda Bro dinki mubeen, Sunan da taji ya ambata tace Alright bakomai, bazanjeba koda kabarni ma kuwa! Dakinta ta shige tanata kuka Kuyangi kuwa se zagaye sukuyi a sasanta, Mansur hakuri taketa bashi yace Sam ba inda zaki kuma nasanki, karki kuskura ki sanar da Hajiya mummy KO Hajiya Bilkisu, Kallo ta bishi dashi tace bakomai *** Bayan kwana biyu, tace da gaske bazaka bari najeba? Yace dama wasa nakeyi? Tace OK, to akwai kayan dana siyo matane harda zannuwan gado nace Zan bata da kudade, yace wannan ba matsala bane, ki aika mata da kudin ta account sannan Kuma ki dakko Kayan yanzu muje a aika mata dashi ta mota tace toh Kiran Ameerah tai tace ta turo Mata da account number, yace nawa zaki tura Mata? Tace 50K yace OK KO tura Mata da 150K Zan baki 100k din tace Tom, Sending Mata Kudin tayi tana gani, ta mik’e da yake tana tare da kayeanta tace 150K suma zare ido sukai sukace angon ne ya turo? Tace. aa wannan kawar tawace Nazeefa, suma Zare ido sukai sukace wannan tana sonki fisabillah, Kiranta Ameerah tai tace kudin sunshugo nagode, Nazeefa tace bakomai, Anjuma zamu aiko da kaya idan kayan ya iso sai kije ki amsa Dan Allah bazan sama zuwaba kinsan cikina na bani wahala Ameerah taci Ayyah sannu, nima nayi tunanin hakan walhi, Allah Kara sauki tace Amen Sungama wayar suka tafi garage aka aikamata da sakon sannan suka dawo gida Chan yamma suka kira Ameerah sun iso Dan haka taje ta amsa sakonta, Dadduma guda 4 tace taba baba da mama 2 seta rike 2, da misk Dan saudiya da zannuwan gado guda 2 na 40K ga wasu night gowns, da jallabiya guda 4, se Takalma da turaruka, se dabino, bagaruwa da Ruwan zamzam da yawa Ameerah ta bude tagansu, tai Mata addua sosai sannan ta kirata tace naga sako wannan kayan arziko haka? Nazeefa tace bakomai Ana tare Bayan kwana 4, Aka daura auren Mubeen da Ameerah, Nazeefa jitai kamar tai tsuntsu, dan Ameerah ta Turo mata da pics dinsu sunyi kyau Sosai perfect match nazeefa nan ta jera Pics dinsu a status, Mansur na viewing yaji kishi, yai mata magana ta chat din yace duk pic din da akwai mubeen ki cireshi, Tana karanta message din taqi goge status din Shuru yai mata, ya duba yaga bata cireba Tana shiga toilet yai maza ya dauka wayarta ya goge da kanshi, Sannan ya duba mutanan da take chat dasu, Mubeeeeeeeeen yaga ansa yai maza ya shiga chats din yaga sun gaisa har tanamai fatan alheri, Allah ya basu zaman lafiya, yace ameen sisi for life nagode STORY CONTINUES BELOW  Nan take Mansur yaji ranshi ya baci, blocking number yayi sannan ta fito a toilet, hannunshi ta kalla taga rike da wayarta “shikkenan tace, wani kallo yai mata da seda hanjin cikinta ya kada, Kusa dashi tazo tana cewa kayi hakuri Dan Allah, Wani ajiyar zuciya yayi yace Nazeefa inasonki Dan Allah ki guji batamun rai, Amma sedai fa kiyi hakuri nayi blocking number shi Bataji dadi ba Sam, amma tasan hakan shine ya dace, karma yazo ya Fara zarginsu, tace Kayi hakuri bazan sakeba yace kima sake ki gani Lol, tun daga ranar tamaida hankalinta wajen MT dinta suna zaune qalau abunsu Bangaren Mubeen kuwa an angwance shima, Love kamar zai maida Ameerah ciki, sonason junansu Sosai *** Haka rayuwarsu taci gaba gwanin sha’awa kowa na zaune lafiya lau ba wata matsala se abunda baza’a rasaba Cikin Nazeefa nada kusan wata 5 su Zainab da Maryam suma suka sama ciki, Kowa kokarin farantawa matarshi rai yakeyi, su 3 dinnan sun zama shalalen gidan sonsu akeyi, Idan Sarki zai siyo musu abu duk iri daya yake siyo musu, sukam Alhamdulillah sunji dadinsu ba wani sabanin nan irin na mata! *Bayan Wata 3* Lokacin Cikin Nazeefa ya shiga 8month tun da ya shiga bata jin dadi sosai, duk ta Dan chanza saboda cikin na bata wahala ga ciwon ciki da take fama dashi! Cikin darene ta tashi kamar zata mutu dan ciwon ciki, kaita asibiti akai akace haihuwane! Kowa yayi surprise saboda 8months ne ga cikinta yai kato sosai, akace bazata Iya haihuwaba dole Aiki Za’ai Mata Nan Mansur hankalinshi ya tashi, da akace yasa hannu, Dan za’a iya rasa yar ko Maman! Mansur kuwa cikin kankanin lokaci ya birkice, mahaifinshi yasa hannu Aka shiga da ita theater room Suna shiga Cikin ikon Allah aka fitar mata da twins, daya mace daya namiji, Dr dinne yazo ya sanar dasu, Budan bakin Mansur yace Ina matata take? Yana magana idonshi na gab da zubar da hawaye Wata Dr ce mace ta fito hannunta sanye da hand gloves tace Ina mijinta? Yai sauri yace ganinan, kallonshi tadanyi tace ka shiga ciki Ahankali ya ce ta mutu Ko yana Mai kallon Dr din itadai batace komai ba, shiga yayi ya hango matarshi kwance, Da sauri ya karasa gunta sukai 4eyes wani rungumeta yace Alhamdulillah Sannu yace tace yauwa, Kallon twins dinsu yayi yai murmushi, yace Allah yasa muki albarka Sannan likitocin sukace ya fita Da Murna ya fito kowa na ganinshi yace Alhamdulillah, hankalin kowa ya kwanta Kwanansu 4 a hospital aka sallamesu, babies din da Mamansu kowa lafiya lau Iyayan Nazeefa da yan gidan su Faeez kowa yai Murna Ameerah ma da taji labari tace Alhamdulillah Allah ya raya ranar suna akasama yara. Hassana da husaini, Amma ana kiransu da Arfat da irfan, Anyi suna iya suna, Dan yaron sunzo da farin jini, sune jikoki na farko a gidan, gashi sun dakko hasken babansu Dan farine sol Mansur kamar balarabe, Amma suna kama da nazeefa sema macen kamar nazeefa tayi kaki Arfat da irfan sunyi wata kusan 4 sannan Matar hussani ta haihu da kusan sati biyu Ita kuma matar hassan ta haihu itama Gidan Masha Allah ansama yara hudu, Arfat da irfan sunyi wayau sosai Dan suna samun kulawa, kafin sui shekara suka Fara tafiya! Kowa nasunsu a gidan, kallo daya zakai musu kaji sun shiga ranka kamar uwarsu Nazeefa ** Bangaren Ameerah kuwa itama harta haihu ansama yarinya mace, Dan haka Sukai shawara da mubeen wani suna ya dace asa mata, Ameerah tace tanason NAZEEFA dan haka akasa, Ana ce mata baby, Da nazeefa taji labarin akwatin baby ta hada Mata Dan taji dasi ansa man mata takwara! ___ Yaran NazeefabSunada 2years nazeefa ta kara samun ciki ta haifa Namiji, Aka samai Abdallah sunan abokin babanshi Lokacin arfat da irfan suna 4 years Shi kuma Abdallah yana 1year Mansur yace zai zauna kasar waje Dan chan yakeso yaranshi sui karatu, iyayanshi basui musuba sukace Allah ya tsare Kafin su tafi kuwa, Haka Nazeefa tazo da yayanta uku gidan iyayanta, Sunji dadi sosai, Babanta yana ma arfat wasa yace yau nayi sabon amarya, Arfat da maganarta tace nibanason tsoho, gashin kanka yayi fari na babana kuma bakine! Yaran idan suna zaune suna wasansu saikatacin Dariya, haka sukai 1 week a gidan sannan suka koma Chan yoben Shima the following week suka wuce Dubai, zasui kwanaki kadan sannan su wuce Sudan Dan Chan zasu zauna saboda yaranshi su suma katatun Islamiya Haka sukaci gaba da rayuwa komai natafiya normal Alhamdulillah hankalin Mansur kwance, Nazeefa kullun salo salo daban takemai, Kullun kara sonta yakeyi, haka yaransu suka taso cikin so da kauna da kulawan iyayansu, sun basu tarbiya mekyau Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah, Anan na kawo karshan book dina mai taken *SILAR GIDAN AIKI* Yah Allah ka yafemin kuskuran danayi a ciki ka gafarta minsu.