WATA BAKWAI CHAPTER 7
Tunani yake in ya tafi har kano bai fada ma natacciya ba sam bai kyauta ba. Yasan ba magana take hadasu ba sam. Amman duk da hakan baya son rashin adalci. Beside zai fada matane kawai ko da wani abu ya faru. Tashi yai daga kwanciyar da yake ya fito. Ya koyi sa.a ta rage masa wahalar zuwa bedroom dinta dan tana zaune falon su na sama tana kallo. Gidan ba kaman na kano ba. Da kowa yake da part din shi. Duk da nan dinma dai part dinsu daban amman falo ya hadasu. Sallama yai mata. Yana neman waje kusa da ita ya zauna. * Kamshin shi kawai husna taji tasan ya nufota. Ta lumshe idanuwanta ta budesu a hankali. Batason fitina da yammacin nan. Cikin sanyin murya ta amsa sallamar shi hankalinta na kan t.v. Remote ya dauka da yake kan Centre table din wajen ya kashe kallon da take. Hakan yasa ta fuskantarshi. Idanuwanta a kasa. Shisa bayason mata magana sai dole. Bayason yanda take yin kaman bata son ganin shi. Kaman wata kazanta ce a jikin shi. A nutse yace. “Zanje kano gobe in Allah ya kaimu. But ba dadewa zan ba. Kwana uku zuwa hudu” Shiru tai ta kyale shi dan bataga dalilin da zaisa ya fada mata ba. Asalima taga zuwan shi kano ba damuwarta bane. Ba magana suke ba. Saitai kwana biyunma bata saka shi a idonta. To wacce gulmar zata kwaso kafafunsa yanzun? Kilanma da yai shiru har yaje ya dawo ba kula zatai ba. Bama ta damu ba. * Abu na farko da ya tsana shine yai magana ai shiru. Dafe kanshi yai na yan dakikai. Ranshi ya soma baci. Bayason yanda take bata masa rai sam. Muryarshi a dake yace. “Magana nake miki” Kaman wadda akaima dole tace. “Naji ka” Mikewa yai kawai ya nufi bangaren sa. Dan inya biye ta natacciyar nan zai yi abinda zaizo daga baya yana dana sani. Saboda tagama kure hakurin shi. * Wani karamun tsaki taja ta dauki remote ta kunna kallonta. Share bangaren zuciyarta tayi dake mata fadan cewar ko yankar naman juna suke da natacce dayazo yace mata zai tafiya tai masa addu.a “Allah ya tsare hanya” ta fada a hankali dan tasan ba zata zauna lafiya da zuciyarta ba inhar bata fada ba. Zatai tajin wani irine tunda ba sabawa tai ba. * Tun da yai asuba baima koma bacci ba. Dan jirgin karfe 9 na safe zaibi zuwa kano. Bayason ya kwanta baccin bai gama isarshi ba yai ciwon kai. Tun takwas yagama shiri. Babu wasu kaya dazai dauka. Dagashi sai I.D card sai wayoyi. Driver ya dauke shi daga gidan zuwa Airport. Headphones ne a kunnuwanshi yana sauraren karatun Qur.an. Jiyai kaman driver din na magana kasancewar bai kure maganar ba. Ya saka pause ya zare daga kunnuwanshi yace. “Magana kake?” A tsorace yace. “Rankai dade kamar ana binmu ne. Tunda muka fito gida wannan motocin ukku suke biye damu” Tunda driver din ya soma magana zuciyar prince ishaq ke dokawa. Yasan ba karamar wauta yai ba fitowa babu security. A nashi zaton duk wannan zai kara janyo hankalinsu ne. Bai zata sun biyo shi abuja ba. Addu.o.in tsari ya shiga karantowa dan yadan samu nutsuwa. “Kaci gaba da tuki. Karkai gudu” Ya fada a hankali. Wayarshi ya dauka ya kira kamala. “Muna hanyan airport akwai motoci uku suna binmu. Do what you can and make it snappy” Kamala baima amsa shi ba ya kashe wayar. Ko mintina biyar ba aiba tsakani suka soma jin jiniyar motar yan sanda. Cikin rawar murya driver din yace. “Rankai dade sun sha U-turn” Wata ajiyar zuciya ya sauke. Mutanen nan so suke suga bayansa. Har airport yan sandan suka rakasu. Tukunna. Text ya turama umman shi saboda ya tabbata abinda ya faru a abuja dan kadanne da abinda zai iya faruwa a kano. * Wayar ammar ta tasheta daga bacci. Muryarta can kasa tace. “Hello” Dariya ya kama yi mata. “Tawan koma baccinki” Kamun ta amsa ya kashe wayar. Kwanciya tai shiru dan inta tashi bacci takan dade batai magana ba. Sai da ta wartsake sannan ta tashi. Brush kawai ta sake yi dan tai wanka tun da asuba. Kawai sai take jin mugun kewar yan gidansu. Duk da babu wanda ya kirata har yanzun. Ta kuma son fushin suke basu huce ba. Bayan ita akaima rashin kyautawa aka liqa mata nataccen can da bata so. Wayarta ta dauka ta kira maheer kaninta. Wayarshi a kashe. Ta tuna safiya ce kuma ranar laraba. Yana makaranta. Dining ta nufa ta ci dankali da kwai ta koshi abinta ta koma falo ta zauna. Batasan gulmar datai zuciyarta tunanin ko natacce ya sauka lafiya ba. Kallo ta kunna dan bata son yanda yai mata katsalandan cikin tunani. Kwanan shi biyu kano yagama abinda zaiyi. Jirgin yamma yabi zuwa abuja.+ A falo ya zauna. Sai lokacin duk gajiyar daya kwaso take tambayarshi. Ya sake gyara zama cikin kujerar yana lumshe idanuwansa. Magrib kawai yake jira tayi yai sallah yadan kwanta. * Husna kam tana son fita sosai. Danma ta kira kausar ta kawo mata kayan sawa. Akwatin data dauko shirmene kawai cikinsa. English wears ne da bata tunanin zata iya saka su tsautsayi ya gifta natacce yaganta cikinsu. Sai fama take da alkyabba kullum. Data sakasu saita dora dan ta rufe mata jiki indai zata fito falo. Sai hijab dinta ta sallah. Tasan da wahalar gaske abarta ta fita. Bama tason zubda aji shisa sam bata gwada ba. Zata jira sai ta hadu da natacce inya dawo kenan. Ta sauke ajinta a gefe tai masa magana ko dogayen riguna ne ta fita ta siyo tunda da yan kudinta a hannu taba kausar ATM ta ciro mata. Falo ta fito. Kamshin shi ta fara ji kamun taganshi. Zuciyarta ta wani doka. Hannu tasa kan kirjinta tana so ko bugun da zuciyarta yake zai dan dai-dai ta amman a banza. Kafarta har wani rawa take abin takaici. Karasawa tai inda yake da sallama. Idanuwan shi ya bude ya sauke su akanta da doguwar hijab sanye jikinta har kasa. Amsa mata sallamar yai a kasalance. Sai taji muryarshi ta kara budewa. Bata son yana mata magana saboda tayar mata da tsikar jiki yake. Tana son taji muryar namiji babba haka. Saidai ammar dinta muryarshi yar karama ce.1 Da sauri kamun kwarjinin dayai mata yasata kasa tambaya tace. “Ina son fita zan siyayyar kaya” Idanuwan shi kawai ya zuba mata. Babu yanda za.ai ta fita saboda yanayin tsaro. Banda kamala babu wanda ya aminta dashi cikin gida. Kudi zai iya siyan kowa yaci amanarsu. Baya son karin matsala. Ko dan darajar auren da aka liqa masa na natacciya. Tana karkashin kulawar shi. Bazai bari komai ya samu yar mutane ba. * Husna kam harta kawo iya wuya. Dole ce tasa ta tambaye shi ya zuba mata idanuwansa yana kallonta. A dakile tace. “Magana fa nake maka” Idanuwan dai su ya zuba mata. Ya gaji sosai. Idan yagaji baya son surutu. Wannan yarinyar bata ganewa ne. Ta kyale shi baya son naci. Yana kallo ta tashi tabar wajen. Ya maida kanshi ya kwantar jikin kujera ya lumshe idanuwanshi. Yana zaune a wajen har aka kira sallar magrib ya tashi yaje yai sallah. A masallacin cikin gidan yai zaman shi. Sai da yai sallar isha.i tukunna ya koma cikin gida. Apple ya diba a dining din dake cikin falon ya wuce dakin shi ya ajiye su kan gado. Jikin shi duk ciwo yakr mishi. Wanka yai sannan ya kwanta. Yana gama addu.a bacci ya dauke shi ko apple dinma bai ci ba. * Wasu hawaye masu dumi ta goge. Dan taje wajen shi ta tambayi alfarma ne zaisa ya wulakantata. Zata hakura tai amfani da kayan da take dasu. Inyaso ta kira kausar taji yaushe zata sake shigowa sai ta sissiyo mata. Wayar da sukai da ammar ne ma ya rage mata bacin ran da take ciki. * Washe gari da safe tun da ta gama baccinta ta tashi wajen goma. Sai da tai wanka sannan tasa aka kawo mata brkfst har daki. Batason fita taga nataccen nan ya sake wulakantata kaman jiya. * Duk da wankan dayai gajiyar jiya bata gama sakin sa ba. Shadda ce a jikin shi dinkin kaftan. Ruwan toka da hula mai cizawa kalar aikin jikin shaddar takalminsa ma haka. Bai manta da abinda natacciya ta tambaya ba jiya. Maganar ce baiga damar yi mata ba saboda yagaji. Bangarenta ya karasa. Ya kwankwasa kofar tace ya shigo. * Abinda take ci taji ya tsaya mata a wuya. Bata zata shi bane. Ca take ma daya daga cikin hadiman gidan ne. Hijab din da take gefe tai saurin dauka ta saka. Kallonta yake yi. Taso tabashi dariya ma. Kome take boye mishi oho. Gefen gadon ya zauna ya mika mata dan notebook karami da biro. Bai jira ta karba bama ya ajiye akan gadon kusa da ita. Kanta a kasa dan bata son idanuwanshi cikin nata. “Ki rubuta abinda kike so. Da sizes za.a kawo maki. You can’t go out a yanzun” Yai maganar a nutse. Yama raina mata hankali. Wato sai yanzun yaga dama. Muryarta can kasan makoshi tace. “Kabarshi kawai na fasa” Hannu yasa ya dago mata da haba. Bayason yanda bata iya kallon shi tai masa magana. Ture hannun shi tai kanta na kasa. Tanajin hawayen da suka cika mata ido. Bata son yanda zuciyarta ke saurin karaya a gabanshi. Sake dago mata da haba yai. Wannan karon data kawo hannu ya ture nashi yasa dayan hannunshi ya rike nata gam. “Bana son gaddama. Ki kalle ni kimun magana. And ba tambayarki nai ko zakiyi siyayyar ba. Canai ki rubuta. Akwai bambanci tsakanin biyun” Bata yi kokarin kwace hannunta ba saboda rikon dayai mata bana wasa bane. Muryarta na rawa tace. “Ka sakeni in rubuta” Sakinta yai. Wannan yanayin irin na rannan dabai san fassarar shi ba yake ji. Tafin hannuwan shi ya murza tare yana son ya goge yanayin da yake ji a jikinsu. Bayason tabata. Saidai gaddamarta ce take ja masa wannan wahalar. Yana kallon yanda hannunta ke rawa wajen rubutun. Hakan ya mishi saboda bata da girma da ajin da zata dinga raina shi. Miko masa tai kanta a kasa. Ya tsaya ya zuba mata idanuwa. * Tanajin yanda idanuwansa ke mata yawo ta kuma san abinda yake jira. Dakyar ta dago da kanta ta sauke idanuwanta kan fuskarshi. Ta mika masa littafin da biro din. “Good girl” Ya furta a hankali sannan ya karba ya mike ya fice. Yana ja mata kofar ta diro daga kan gadon. Mukullin tasama kofar jikinta ba inda baya rawa. Ta cire hijab din da kayan jikinta tai toilet. Kwamin wanka ta shiga ta sakarma kanta ruwa. Soso da sabulu ta saka ta dinga gurzar hannunta inda take jin shatin dumin hannun nataccen nan a jiki. Amman a banza tanajin shi har lokacin. Kuka tai mai isarta tana tunanin yanda zata soma bi ta kashe auren nan. Dakin shi ya koma ya zauna. Saboda yana son duk abinda yake ji yadan tsagaita tukunna.+ Yakamata ace ya daina taba yarinyar nan. Saidai ita take ja. Hakan ne kawai yake sakata ganin girmanshi. List din ya duba. Riguna ne kawai ta rubuta. Kamala ya kira ya ce masa ya samu wata designer ya tambaye ta tai list na abubuwan da mata suke bukata a turo mishi. Ba afi mintuna goma ba text ya shigo wayarshi. Wani dogon list yagani da karanta shi ma ciwon kaine. Don rabin abubuwa bai san suba. Wasu kuma ana bukatar sizes. Shi bazai iya komawa bangaren yarinyar can ba. Don haka yaima kamala text cewan ya dibi ko nawa yake bukata. A sissiyo kayan su taho da matar ta zabi wanda yai mata a koma da sauran. * Da zundumemiyar hijab dinta ta fita falo ta dibo fruits taji sallama bata mutum daya ba. Haka yasata fitowa daga dining din babu shiri tana amsawa. Hadimaine sunkai shidda da kaya niqi-niqi. Sai wata mata mai matsakaicin shekaru. A ladabce ta gaishe da husna. Ta amsa fuskarta babu yabo ba fallasa. Hadiman suka ajiye kayan husna tace musu zasu iya tafiya. “Ki zauna mana” Husna ta bukata. Da fara.a a fuskar matar tace. “Bama sai na zauna ba. Ki duba kayan nan ki dauki size dinki. Zankoma da sauran” Ta karasa maganar tana ware wasu ledoji. Da mamaki husna ta dauka ta duba. Bra’s ne da panties. Ta juya idanuwanta tadan dafe goshi. Har ta bude baki tace bata bukata a mayar ta tuna jan kunnen da natacce yai mata. Ta kuma san tabbas bada wasa yake ba. Dan haka ta duba ta dauki size dinta. “Nagode fa” Tace da matar. “Babu komai. Nabarki lafiya” Ta fadi tana tattara kayan da zata koma dasu ta nufi hanyar benen dan ta sauka. A wajen husna ta tsugunna ta dinga duba kayayyakin. Wasu dogayen riguna data gani sun bala.in burgeta. Gaba daya kayan sunyi kyau. Harda takalma. Flats din kawai ta dauka aka mayar da hill dan ba damunta sukai ba. Gani tai kayan da yawa. Dole ta kira akazo aka daukar mata zuwa bedroom. Wannan karin ba zatai ma kanta karya ba. Kayan sun bala.in burgeta. Harda hijabai aka kawo mata. Taso ta yaba zurfin tunani irin na shi ta fasa. Beside shisshigi yai mata. * Kwanci tashi babu wuya wajen Allah. Haka rayuwar take tafiyar musu. Abin har mamaki yake ba husna. Wai wata na hudu kenan da wannan kadararren auren nata. Zamansun nan yana mata dadi. Balle a satikan nan da zatai kwanaki ko giftawar natacce bata gani ba. Saidai ko in ta fito falo zataji nataccen kamshin shi din nan dayake tsaya mata. Komai na amfani tana dashi. Dan haka bataga amfanin me ganinshi zai mata ba. Sai biyu yazo dakinta. Duk lokuttan yana gaya matane zai je kano. Ta kuma rasa dalilin shi na fada mata hakan. Matsalarta dayace. Ammar ya soma gajiya. Ya soma damunta kan maganar kashe auren nan. Batasan ta ina zata fara ba. Kukantane kawai yake saka shi yai shiru. Banda maheer bata waya da kowa a gidansu. Tayi kewarsu sosai. * Lokutta da dama mantawa yake da natacciyar nan dan abubuwa sun masa yawa. Hidimomin da ya kawoshi garin abuja ya shiga yi. Hakan ya bala.in rage masa tunani har yammaci. A hanyarshi ta dawowa gida yana bayan motar yana tunanin komawarsa. Baisan ko rashin huddy bane yake saka zuciyarsa numfasawa natacciyar yarinyar nan. Yasata yi masa katsalandan cikin tunani. Baya son tuna yanayin dayaji game da ita lokacin da jikinsa ya hadu da nata. Qamshinta. Idanuwanta da suke kallonsa da yanayin tsanarsa da tai. Idanuwanta masu bayyana kome zuciyarta take ji.1 Har yanzun idan ya tuna sai yaji wani iri. Ya girgiza bai taba ganin tsana da rauni hadi da tsoro irin wanda yagani a idanuwan natacciya ba. Dafe kai yai. Ya Allah! Meke damuna ne haka? Yake tambayar kansa dan yaga daga jiya da daddare zuwa yau gabaki daya zuciyarsa ko ta kawo mishi tunanin huddy zata tattara ta danganto shi da natacciya. Ya rasa wannan naci. Yau yakai kwana hudu bai sata a idon shi ba. Akan me zata dinga cuso masa kai cikin tunani.2 Wayarshi tahau ringing ya dauka “sweet Qani” yagani a rubuce. Mamaki ya bayyana a fuskarshi. Saboda number din naseer ce ta nigeria. Dauka yai yakara a kunnensa hadi dayin sallama kaman yanda tsarinsa yake. “Yaya ina qofar gidanka!” Naseer ya fadi cike da doki. Murmushi yai. Yakan jima yanzun bai hakan ba har manta kalarsa akan fuskarshi yake. “Qanina babu sanarwa koh?” Dariya yai “Ai nace maka ka shirya zan baka mamaki ko ka manta?” “Hakane harka shiga cikine?” Ya buqata. “Um um yanzun zan shiga wajen antyn nan tawa inga wannan data qoqarta wajen daukemin hankalin yaya.” Nas ya fadi cikin siga ta tsokana. “Kai dai bakajin magana zanzo in sameka ne ai.” Dariya yake sosai ya furta “Allah ya huci zuciyar sarki ishaq.” Baisan lokacin da dariya ta subuce masa ba. Kashe wayarshi yai sai yake jin kaman sabon abu. Ta wani bangaren kuma ya na tunanin kalar tarbar da natacciya zatai ma kaninsa. Kaninsa dayafi so duk cikin gidansu. Dafe kai yai yana sauke wani numfashi. Bayason damuwa sam.