WATA MACE CHAPTER 7 KARSHE BY SANA S MATAZU
Www.bankinhausanovels.com.ng
Sunkuye take tana hura wuta da bakinta, gaba ɗaya tokar karan ta yayyaɓe mata fuska. Nishi taketa yi ga kuma zufa. Kai ta ɗaga sama tana hangen hadarin daya gangamo. Gabanta ya faɗi ras! Wasu ƙwala suka kwaranyo mata wai yau ita ce take hura wuta da karare lallai duniya labari.
Ta tuna irin rayuwar data gabatar a baya, zuciyarta ta cika da ƙuncin halin da take ciki. Sai dai tasan ko giyar wake tasha Tukur ba zai saketa ba shiyasa ma ta haƙura ta miƙawa ubangiji lamuranta. Tana nan tsugune ta rasa madafa, har haɗarin ya gama kankama. A gefe kuwa facalolinta sai dariya suke tiƙa mata saboda murna. Cikin ikon Allah sai ga tasowar iska, wannan iskar ita ta taimaka mata ta hura wutar nan da nan ta tuƙa tuwo ta kwashe.
Sai bayan isha’i ta gama komai kamar an bada umarni kuwa sai ga kecewar ruwa kamar da bakin ƙwarya.
A gajiye liƙis ta samu guri ta zauna, idanunta har wani yaji-yaji suke yi mata saboda tun asuba bata runtsa ba. Tana jin shigowar Tukur ɗakin ya jiƙe sharkaf nan tsakiyar ɗakin ya cire kayansa dagashi sai gajeran wando ya buɗe kwaba ya ɗauki wasu ya saka ya haye gado ya ƙudundune. Takaicin bar mata kaya da ya yi anan ya sake kasheta. Kamar ba zata tankaba ta daure ta haɗiye abinda ya tsaya mata a maƙoshi ta furta,
“yanzu saboda Allah ka cire kaya ka bar su a nan kuma jiƙaƙƙu?”
“Ke Labiba kin fa cika ƙorafi wallahi, ke komai wai abin magana ne a wajenki. Idan ma barin kayan na yi mene ne amfaninki, aurenki fa nake yi dole ki yi min bauta kamar yadda KOWACE MACE take bautar aure a gidan mijinta. Mtssss! Ni an haɗani da aiki wallahi, mace sai mitar jarraba ke bakisan mace me mita aurenta saurin mutuwa yake yi ba?”
Wani ƙududdune ya tahomata tun daga tsakiyar ka be sauka ko ina ba sai tsakiyar cikinta, tana jin lokacin da ɗan cikinta ya yi wata irin motsawa. Ta cije baki tana tuna daidai da rana guda bata taɓa zuwa awo ba bare ta san ya lafiyar abinda yake cikinta.
Ƙiri-ƙiri mahaifiyar Tukur ta haramta hakan. Ta tuna cikin Ummi yadda Yusuf yake jelangiyar aro machine yana kaita awo ya ɗaukota. Hawaye ta share, zuciyarta na faɗa mata ba zata bari Tukur y shata bulus ba.
“Tunda kasan da hakan me ya hana ka yadda ƙwalon mangwaro ka huta da ƙuda?”
“An zo wajen! Ahaf to anƙi a sake kin” Ya furta yana zabura kamar wanda aka yi wa allaura “kin nufin in sakeki Labiba? Haaaaaa” ya yi dariya me sauti duk da ruwan da yake zuba,
“ko karan hauka ya cijeni wallahi ban shika miki ko igiya guda. Waga batun ki sakayashi cikin zuciyarki zama dani haihata Labi baby”
Yadda ya furta baby ɗin ya fi komai yi mata ciwo dan haka ta ja bakinta ta yi shiru kawai.
Suna nan zaune ɗakinta ya soma zuba yoyon ruwa ta tsakiya. Ido ta ɗaga kawai sai ta soma hawaye. Zuciyarta ta yi wata irin matsewa ƙwarai ta sani girbin aikinta da ta shuka take yi amma batu na gaskiy ta gaji da yanayin tana buƙatar sassauci.
Wata zuciyar ta tanasar da ita cewar addu’ar bayi na saurin amsuwa yayinda ruwan sama yake zuba. Kamar wadda aka yi wa allura haka ta ji wani kuzari ya shigeta ta ɗaga dukkan hannayenta sama. Kuka take me sauti, me fita da yanayin da ya ke nuna neman agaji. Laɓɓanta suka motsa da wani irin karsashi data manta rabon da ta ji makamancinsa.
“Allah na tuba, na kaskantar da kaina a gareka ya ubangiji ka dubeni badan ni ba badan halina ba. Allah ni baiwarka ce me saɓo a gareka, ina ta wasulu da sunayenka tsarkaka ina tawasuli da alƙur’aninka me girma Allah kadda ka dubi tarin zunubaina, Allah ka dubeni da rahamarka ka kawomun sassauci cikin rayuwar danake fuskanta”
Sautin kalamanta har kunnuwan Tukur da yake kwance, wani irin sanyi jikinsa ya yi ga wani tausayinta daya mammayeshi. Tsam ya tashi ya kwashe kayan da ya zubar mata a tsakar ɗaki tare da ɗauko roba ya tara a wajen da yake zubar ruwan. Ƙarasawa ya yi kusa da ita, kallonta yake ya kasa ce mata komai, ita ma kallonsa take tana jin wani wannan nauyin na ƙirjinta na raguwa a hankali.
***
Washegari kamar almara ta tashi da baƙuncin Amne, karon farko tun watanni goma na aurenta. Lallai yau tana cike da murna, da fara’a da komai ta tareta abin mamaki hadda Umminta. Duk yanayin nauyin jiki da take ji be hanata zaryar sama musu abinda zasu sa a bakinsu ba. Fita ta yi ta samo musu a wara a bakin hanya, ta dawo ta ajiye musu tare da ruwa.
Sai zuruftu take yi, Amne kuwa sai binta take da idanu cike da tausayi.Lokaci-lokaci takan faki idonta ta share hawaye ƙwarai tana tausayin rayuwar da ɗiyartata ta riski kanta amma tasan ita ce sillar rushewar farin cikinta.
Anata ɓangaren Labiba so take ta nemi yafiyar Ummi amma nauyi ya sa ta kasa koda tambayarta ina ɗan uwanta tun bayan gaisawa da suka yi babu abinda ya ƙara haɗasu.
Yanayin yadda take bin yarainyar da ido ya karyarwa da Amne guiwa. Tabbas sai yanzu take ƙara hango kuskuren da suka tafka na wargaza rayuwar uwa da ƴaƴanta.
Haka Labiba ta daure ta dinga jan Ummi da hira tana tambayarta makaranta da ƙananta. Uwa uwa ce koda kuwa ta buzuzu ce sai gashi Ummi ta ware harta sake da ita ta shiga bata labarin yadda Shukura take kyautata musu. Ba ƙaramin daɗi ta ji ba, duk da ana bata labarin hallacin matar amma jin daga bakin Ummi ya bata tabbaci domin tasan zaman uwar wani da wani sai Allah.
Da zasu tafi ƙuli-ƙuli me yawa ta siya wajen surukarta ta ba Ummi da daddawa ta ce ta kaiwa Auntynsu. Amne ma ta bat hada kukar kaɗi. Haka suka rabu cikin kewar juna sossai ta yi mata nasiha tare da alƙawarin aiko mata da jari ta kafa sana a domin tsayuwa da ƙafafunta. Aikuwa kwananta uku da tafiya ta yo mata aike. Cikin ikon Allah ta soma sarin buhun gyaɗa ɓararriya a ɗaya daga cikin shagunan da Yusuf ya buɗe, wani abin armashi shi yasa yaransa suka kawo mata a mota bayan ya ƙara ƙarfin jarin nata da cewar ga nasa taimakon nan. Domin duk halin da take ciki tsegumi na zuwa kunnansa dan dai ba me tankawar bane. Ranar yini ta yi tana jinjina karamcin Yusuf da kuma kyakyawar zuciyarsa.
Cikin ikon Allah ta soma sana’arta cikin nasara, hata Baba Harira bata yi mata buƙulu ba a wajenta take siyen gyaɗa da ma sauran matan ƙauyen masu sana’ar ƙuli. Sai ga shi har wani kumari ta yi saboda yadda kuɗi suke shigo mata. Shi kansa Tukur ya rage kaso goma na hallayarsa domin dai yanzu sana’ar wankin hula da wanki da guga yake a shagon daya buɗe a ƙofar gidansu. Kasancewar ya yi zaman maraya abin na shi a ƙawace yake yinsa sossai yake samun ciniki.
***
Sanɗa take da dukkan wani taku data san ta mallaka domin gujewa farkawarsa. Tun lokacin da ya shigo da baƙar ledar ta ƙyala ido ta ganta hankalinta ya karkata kan yadda zata ɗauket.
Ganin ya samu bacci yasa ta shiga ɗakin da sanɗa, da dukkan zuciyarta take jin yau lokacin mutuwar aurenta ya yi matuƙar ta sami nasarar ɗaukar kuɗin.
Kabir da baccin takaicin Ramla ya kwashe shi be san wainar da ake toyawa ba. Tun lokacin da ya shigo yunwa na ƙwaƙularsa ya tambayeta abinci ta murguɗa baki tare da cewar bata yi ba ya shige ɗakinsa ya barta a nan. Kwanciya ya yi yan tunanin Zahidaht idanunsa har haska masa imagine ɗin rayuwarsu ta baya yake yi. A haka bacci ya kwasheshi cike da mafarkanta marasa kangado wanda akasari duk acikin korayen ciyayi yake ganinta.
Juyi ya yi sai ya buɗe ido kaɗan, hango Ramlatu ya yi tana laɓe-laɓe ta nufi ledar da mahaifinsa ya aikeshi ya kai masa saƙo banki. Shi kwata-kwatama ya manta da batun. Be motsa ba, so yake ya gasgata zatonsa. Ya sha ajiye kuɗi da shadodin da be ɗinka ba ya wayi gari babu, idan ya yi magana ta hayayyaƙo masa da masifa kan cewar ajiya ya bata. Dan haka sai ya ƙara lamɓo yana jin zuciyarsa na dokawa.
Tabbas kuwa sunkuyawa ta yi ta kwance ta ɗauki bandir na ƴan dubu-dubu guda biyar. Ta maida ledar kamar bata taɓa ba. Mamaki ya kashe shi yana daga kwance.
Kamar ya barta ta tafi haka ya ji a ransa, amma sanin wace ce ita ya sa ya yunƙura da wani irin karsashi ya sha gabanta. Ta razana matuƙa, baikinta ya soma karkarwa ya nunata da yatsa yana hucci.
“Dama ke ce ki ke min sata Ramlatu?”
“Babe ka tsaya ka saurareni…”
Wanke mata fuska ya yi da mari, karon farko da ya ji baya shakkar dukkan mace tun bayan dukan Zahidaht, yau kam ya karya alƙawarin da y ɗaukarwa ransa. Sai dai ko kaffarar ce ya yi ta dag baya. Sossai ya zage ƙwanji ya zanneta. Da bakinta ta dinga faɗa masa irin abubuwan data ɗaukar masa da kuma dalilinta na auransa harma da cikkunansa data zubar. Ƙwalla kawai ya ke sharewa yana kukan zuci.
“Na tuba Allah Zahi ki yafemun wallahi na horu”
Shi ne abinda bakinsa yake furtawa yana kallo ta kwashi kayant ta fice. Ramlatu ta tafi tana kuka zuciyarta cike da nadamar sakin da ya yi mata. Rayuwar da zata yi a gidansu kaɗai take hangowa. Na ɗaya su goma ne biyu ne kaɗi ƴan mata dukkansu zawarawa ne. Kowa ce gashin kanta take ci. Mahaifinsu ba wani damuwa ya yi da lamarinsu ba saboda matarsa ta ɗauke hankalinsa. Lallai sai yanzu take hango babban kuskuren data tafka na suɓucewa auren Kabir.
Kabir ya jima anan zaune, gaba ɗaya jikinsa ya gama yin sanyi. Ya sani ya zallunci Zahidaht amma yana jin ankai gejin da bashi da ƙwanjin ɗaukar waɗanan zunuban. Shi kam ya haƙura da kowa ce mace a yanzu zai maida sauran rayuwarsa gaba ɗaya wajen bautar ubangiji ko ya samu sassauci. Koda batun sakin ya shiga gida ba ƙarmin faɗa ya sha ba bai ɓoye musu komai ba ya bayyana musu dalilonsa na sakinta. Mahaifiyarsa ta tausaya masa tare da yi masa kyakyawan fata.
***
Kwanci tashi babu wuya wajen ubangiji Labiba ta sauka lafiya. Ta haifi yaranta guda biyu mace da namiji. Tukur baki har kunne hakama mahiafiyarsa. Ranar suna Tukur ya yi mata bazata. Sunan Yusuf ya saka mata. Ita kuma ya sakawa macen sunan mahaifiyarsa amma Labiba ta sakaya mata da faɗin Ahyana.
Ba ƙaramin martaba ya ƙara a idanunta ba, ƙaunar yaron take da dukkan zuciyarta. Sunan mahiafinta. Sunan mijinta abin sonta data rasa sanadin son ranta. Kuma sunan ɗanta na biyu. Tabbas Tukur ya kafa babban tarihi a rayuwarta. Dan haka ta ƙara kwantar da hankalinta biyayya take masa kamar KOWA CE MACE.
Bayan suna da kwana sittin ta shirya ya rakata suka je ganin gida da zaga dangi. Ta yi kyau abunta kamar ba ita ba saboda ta sakama ranta nutsuwa. Su kansu ahalinta sunyi mamakinta. Har gida ta je ta sake neman gafarar Yusuf tare da yi wa Shukura godiyar kulawa da yaranta. Anan ta ga ɗiyar Shukuran da suka yi wa Zahidaht takwara. Yarinyar sak mahaifinta. Ga ta kyakkyawa ga shiga rai. Da zasu tafi Yusuf ya tambayi Tukur sana’arsa ganin ya kama kame-kame ya sa Shukura ta ɗauko masa dubu ɗari biyu da hamsin ya ba shi ya ce ya ja jari. Sai ga Labiba na kuka tana godiya. Amne ma har gida ta zo ta yi masa godiya tare da neman yafiyarsa.
Yusuf ya zamo tauraron zuri’arsu domin dai gaba da baya shi ya gaji mahaifin Labiba. Duk wata hidima da yake yi ya ɗora a kanta kuma da jiki da zuciyarsa yake yi. Ya yi duk iya ƙoƙarinsa ya fahimtar da ahalinsa illar auren haɗin da suke yi ba tare da yarjewar yaransu ba. Tabbas sun gamsu tare da kashe wannan ƙuduri a ahalinsu amma ba gaba ɗaya ba idan kuna son juna sukan haɗaku aure haka kuma idan ka kawo ta waje suna maraba da ita domin Shukura ta zamo musu aya.
Komawarsu Labiba ba ƙaramin martaba ta ƙara samu wajen surukarta ba. Hatta facalolinta shakkarta suka soma yi. Kowa na nan nan da ita. A hankali ta soma jan ƴan matan ƙauyen tana wayar musu da hankali kan tsafta da kuma addinni. Nan da nan sunanta ya yi fice kowa ita. Tukur na ɗagawa da alfaharin aurenta.
Jarin da Yusuf ya bashi ya zamo masa tsani, noman albasa ya ke yi kuma Allah ya saka masa albarka sossai a harkar. Ya haɗa da noman rani sai ga Tukur na fita da kayan miya mota-mota zuwa jihar legas. Labiba ta yi amfani da damarta wajen ƙara wayar masa da kai. Da kyautatama ƴan uwansa.
Allah me yadda ya so sai ga soyayya ta ƙulu tsakanin Maito autarsu Tukur da Yaya Khamis. Amne ta fi kowa murna domin yarinyar ta nutsu ta koma ta hanun daman Labiba. Matarsa kuwa kamar zata yi hauka sai dai kashedin mahafinsu ya ratsa kunanta na cewar matuƙar ta kashe auranta badai gidansa ba. Sai yanzu ta shiga nadamar abinda take yi wa Amne na rashin kyautawa. Hajiya Mawwaddah kanta ta shiga taitayinta.
A hankali farin ciki ya zagaye ɗaukacin ƊAN SAƁALO FAMILY. Suna kishi da alfahari da junansu. Suna kyautattawa junansu ga kuma taimakon na ƙasa dasu. Kawunansu a haɗe yake sossai abin sha’awa.
TAMMAT BI HAMDULLAH.