WATA SHARI’A CHAPTER 1

WATA SHARI’A





CHAPTER 1 NEW




Yammaci ne mai cike da, iska na kadawa ta ko’ina, ganyaye sunyi tsanwa shar abun gwanin ban sha’awa, sama tayi luf da hadari kwance a cikinta, ko’ina yayi tsit babu ko kukan tsuntsaye, kowa ya 
ladaftu a gidansa dan gudun saukowar ruwan sama. 
Tuki yake da karfin gaske kamar mai shirin tashi sama, Daga gefenshi (kujerar zaman banza) wata mace ce ta hakimce fuskarta sanye da dark glasses, kyakkyawace ajin karshe, tanata taunar chewing gum cikin natsuwa take kallon 
yanda namijin yake sharara gudu abunshi. 
“Dan Allah Honey ka rage gudun nan da kake, ka bimu a hankali mana” ta fada bayan ta zare glasses din dake idonta. 
“Ai dolece tasa kikaga ina gudun nan Sultana, bakiga yanda saman take bane? Ina gudun kar ruwan sama ya saukone, kinsan watan August ruwan sama baya alerting kam yazo saidai kawai aganshi yazo, kuma da karfl yake zuwa yanda dole sai munyi parking har sai 
lokacin daya tsaya sannan mu tafi” ya bata amsa still yana shararar gudunsa. 
Shiru tayi bata kuma fadin komai ba, ganin ya kara yawan gudun da yake yasa ta sake 
maimaitwa, “Abban Hafsa dan Allah ka rage gudun da kake, kasan fa bana son gudu da mota
Bai ko kalleta ba yaci gaba da tukinshi. 
“Nikam wai kodai duk cikin fushin nayi winning dinka a shari’ar yaune yasakaka wannan 
gudun tsiyar? Nikam karka zubar damu garin fushinka”. 
A fusace ya rage gudun motar ya koma tukata slowly, “Sultana an fada miki wai naji haushine dan kinyi winning dina shari’ar yau? Kika sani ma koda gangan na barki kikayi winning din nawa dan na ganki sabuwar lawyer ne?” 
“Kaidai fadi gaskiya Honey” ta fada cikin zolaya tana masa dariya. “Kaga ai gashi yanzu nasa ka rage gudun ko? Inda ace ban maka hakaba da yanzu kana 
nan kana sharara gudu damu”. 
“Au! Haka kika fada? Zakija inci gaba daga inda na tsaya kuwa” ya fada yana kokarin 
cigaba da gudunshi. 
“A’a nidai dan Allah kayi hak’uri tunda ai mun kusa isa gidan ma”. 
Tana gama fadin haka kuwa ruwan sama ya sauko da karfin gaske mai hade da iska sosai, 
“Kinga abunda nake fada miki ko? Inda kin bari naci gaba da gudun aida tuni mun isa”, 
“Ehh nidai na yarda kabi a hankali din koma dai yaushe ne zamu isa babu matsala”. 
Saida ruwan sama ya yawaita sosai sannan suka iso gida, Saida yayi horn sau uku kam maigadi ya fito hannunshi rike da lema ya wage gate din 
gidan, Daga ma maigadin hannu yayi alamar gaisuwa tareda tsaida motarshi a daidai inda aka 
tanada domin ajiye motoci. 
A hankali ta bude motar ta fito, irin rigar nan ta barristers ce sanye a jikinta da hular kayan, shima namijin irinsu ne a jikinshi, a bayanshi ta boye bayan ya rufe motar dan bata son ruwan sama ya tabata ko kad’an sannan suka shiga cikin gidan. 
Da shigarsu kuwa saiga wata yarinya ‘yar kimanin shekara bakwai, sanye take da doguwar riga armless baby pink din colour, da sauri kuwa ta taso 
“Oyoyo Momy” ta fada bayan ta rungumi mamarta, 
“Oyoyo my Hafsa” itama ta fada tana mata murmushi, 
“Au! Momynki kawai kika sani ko? Nima barinje wurin nawa baby’n yanzu” namijin ya fada bayan ya dauke kanshi daga garesu. 
“Am sorry Abbana, yanzu zanzo wurinka kaima” Hafsa ta fada bayan ta saki momynta ta koma ta rungumi Abbanta. 
“Ina Haydar ne?” Ya tambayeta bayan ya cire hular kanshi. 
“Haydar yana wurin Nany, suna upstairs” ta bashi amsa, “0k kije kice ta kawo minshi, nayi missing nashi tun safe rabona dashi” Da sauri kuwa ta haye sama don ta kira Nany din da Haydar kaninta. 
“Ammafa Abbah nayi mamakin yanda nayi winning shari’ar nan ta yau, ni kaina nasan ka sakar min itane kawai”, 
“Thank God da kika fahimci hakan da kanki, yunwa nakeji wallahi”, 
“0k am sorrie, bari in shiga yanzu in dafa maka favorite naka” ta cire rigarjikinta da hular ta shiga dakinta ta ajiyesu sannan ta fito domin nufar kitchen. 
Karar shigowar text message taji a wayarta, da saurinta ta ciro wayar daga cikin jakarta ta bud’e sakon. 
ldo bude take karantashi cikin mamaki, bayan ta gama karantawa ta kalli mijinta tace “Abbah! Kalli sakonda aka aikomin yanzu”. Karbar wayar yayi ya fara karantawa a bayyane. 
“Kamar yanda Allah yayi ku masu taimako keda mijinki, nake amfani da wannan damar domin rokonku wata alfarma, 
An cuceta kuma an hanata kuka, ku taimaka ku taimaketa, ku fiddata daga mawuyancin halinda take ciki”. 
“Subhanallah! To waye yayi wannan rubutun? Kuma da alama koma waye ya sanmu, kuma gashi babu wani cikakken bayani” Barrister Umarya fada yana kallon matarshi 
Barrsiter Sultana. 
“Kaima kenan Honey, nikam banma fahimci komai dake ciki ba, bansan inda maganar ta dosa ba”. 
“Barin kira numbern inji, dan wannan ba abune wanda za’ace wrong number ba, dama da niyyar mu din aka turomawa” kaFIn ya
gama rufe bakinshi shima wayarshi tahau ruri alamar shigowar text message, exactly irin wanda aka turoma Sultana shima shi aka turo mashi, 
Bayan ya gama karantawa yace “akwai matsala kam, kinga” ya mika mata wayar, “nima irinshi aka turo min yanzu babu ko banbanci, barin kira dai”. 
Kiran lambar ya latsa amma da mamaki sai yaji ana fadin “the number you are tyring to call does not exist, please check the number and try again”, “A’ah” ya fada bayan ya sake gwada lambar, still dai abunda aka fada ne aka maimaita. 
“Ya akayi? baka samu bane?” Sultana ta tambayeshi tana kallonshi. “Wallahi kuwa babu itama wai sukace kiji tsiyar MTN, kiri kiri yanzu aka turo min text da 
number amma wai ace babu ita, wannan karyane” ya sake kiran layin. 
Saida ya kira sau goma amma babu ita, hakan yasa kawai ya hak’ura ya ajiye wayar idonshi lumshe yana tunanin wanda ya masu wannan text d’in. 
“Barinje in dafa maka abincin yanzu honey” ta fada bayan ta tashi ta nufi kitchen. 
Hafsa da Nany ne suka sauko daga upstairs Haydar na goye bayan Nany, Har kasa ta duka tace “sannu da dawowa Alhaji” shiru yayi kasantuwar zurfi da yayi da tunanin wanda ya turo masu wannan text d’in, “Ina yini Alhaji” ta sake maimaitawa dan tasan baijita ba daya amsata. 
“Lafiya Safiyya ina gajiya?”, “Ba gajiya, Momy fa?”, “Gata can a kitchen, kawo Haydar d’in” Mikoshi tayi, bayan ya karbeshi tace “Alhaji an kawo wata takarda dazu da bakunan. 
Haladu ya miko yace wani yaro ya kawo wai a aje maku kaida momy”. 
“lkon Allah! Ina takardar take?” Ya tambayeta bayan ya tashi zaune daga kishingid’awar 
da yayi. “Gata” ta mika mashi tare da nufar kitchen domin ta taya Sultana aiki. 
Bude takardar yayi yaga an rubuta “nine dai wanda ya rubuto maku sakon waya, yarinyar tana cikin matsanancin hali, an cuceta kuma an hanata kuka dan anga halinda 
suke Ciki itada mahaifiyarta 
Kada ku wahalar da kanku wurin kiran lambartawa saboda ba zaku sameni ba, nasan 
kunada halin taimakon nata, kuyi bakin kokarinku na rokeku karku bari wanaan damar ta taimakon musulmai ta kufce maku, Allah kad’ai yasan ladar da zaku samu”. 
“Sultana!” Ya fada bayan ya gama karantawa. 
“Na’am honey” ta fito da sauri saboda yanda ya kirata ta tabbatar da akwai matsala. Gabanshi ta gurfana tace “lafiya dai honey?”, Karanta kiga wannan”, 
Goge ruwan hannunta tayi a zanin jikinta sannan ta karbi takardar a hankali ta fara karantawa. 
“Towai waye yake aikoda wannan sak’on? Waya kawo takardar?” Ta tambayeshi tana kallonshi, 
“Safiyya ta bani ita, wai Haladu ya kawo yace ta ajiye mana idan mun dawo ta bamu”, 
“Safiyya!” Ta kira sunan mai aikin tata. 
Bayan tazo tace “jeki kiramin Haladu kice yazoshi da sauri yabar duk abunda yakeyi, kar kuma ki biye masa kuita shirmen fadan nan naku, dan nasan ku bakwa haduwa wuri bakuyi fad’a ba”, 
“To momy” Safiyya ta fada tare da fita da sauri harda gudu gudu takeyi. 
A waje ta sameshi yana ban ruwan flowers, Murmushi yayi daya ganta yace “ahh! ‘Yan matana kece da kanki?”, Bata fuska tayi tace “nifa bana son shashanci waye ‘yan matan taka?”, “Kece mana Safiyya, ai banida wata budurwa wadda tafiki”, 
“Kai ni ba shirme ya kawoni ba, kajeka momy na kiranka, kuma tace kayi sauri yanzu take son ganinka”, 
“To kije gani nan zuwa” ya fada yana mata wani murmushin, “Tace muje tare, dan haka kazo mu tafl kana batamin lokaci”, 
“Ahh lallai ‘yan matana ta fara sona tunda har takeson mujera tare, mu tafi to”. 
Bata kuma ce masa komai ba har suka isa, bayan sun zauna Sultana tace “Haladu waye ya baka takarda dazu yace ka kawo mana?”, Shiru yayi yana tunanin wace takardace take nufi? Sai daga baya ya tuna yace “wani 
yarone ya kawota nima dai bansan yaron ba, yace min wai an bashine ance ya tabbatarda ya kawota gidan nan”. 
“Oh my God! To waye wannan wai? Ai ya kamata koma waye ya bayyana mana kanshi mu taimaki baiwar Allah‘n tare dashi, boyon ai bashida amfani” Sultana ta fada. 
“Wama yasan ko karyar banza yake‘! Irin mutanen nan ne dai masu son su shiga 
sha’aninmu, dan haka ki fita batun wannan maganar nima na fita, ku tashi ku tafi”! Haladu” yayi musu sallama. 
Tashi kuwa sukayi, Haladu ya kalli Safiyya yayi mata murmshin soyayya sannan ya tafi, ita kuwa harararshi tayi sannan ta koma kitchen Sultana ma tabi bayanta har yanzu batace komai ba sai tunane tunane da take, 
Ta tabbatarda akwai magana, bazai yiwu ace koma waye ya kirk’iri maganar nan ba kawai dan yaji dadi, zataci gaba da bincike har sanda Allah zai bayyana wannan boyayyen al’amarin. 

Hmm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *