ZUCIYA CHAPTER 8

ZUCIYA CHAPTER 8

Washe gari da safe Habib yaje makarantar mahaifinsa yama Nafi takardun karya na primary da kuma Js 1 and 2, sai dai takardun sun nuna sam batada kokari. + Nan ya taho da shi gidansu Ashraf. Yau gidan an tashi kowa zuciyarsa ba dadi musamman ma Umma da Aneesa, Little kam ta fita makaranta. Itakam Nafi tana kitchen ta zake sai aikin girki take, sunayi suna ‘yar hirarsu da Goggo. Suna gamawa ta fito duk jikinta ya d’an baci Amra ce ta karaso gunta da gudu tace ” Wai kizo inji yaya. ” Nafi ta kalleta cikin zak’uwa tace ” Ya Ashraf? ” kai Amra ta d’aga mata ai kam Nafi da sauri ta nufi b’angarensa tana tafe tana gogee fuskarta da hannu, tun jiya takesan ganinshi sai dai ba yanda zatai. Fuskarta a sake ta kwankwasa kofar, ta saba in yana ciki sai dai yace ta shigo in dai har ba makulli yasa ba, sai dai yau gani tai anzo an bud’e da fara’arta ta kalli mai bud’ewa tace ” Yaya ina kwa…… “kalamanta ne suka tsaya ganin Habib a tsaye yana mata murmushi. Jin ta tsaya da magana yad’an kanne ido cikin salonsa yace ” Haba Nafi ba ni kika so gani bane? ” Da sauri ta girgiza kai alamar a’a sannan ta d’ora da cewa ” ba haka bane Ya Habib. ” Habib ya d’an matso kad’an hakan yasa ta d’an kara matsawa, kara matsowa yai itama ta kara matsawa, sam bata kula tazo karshe ba tayi baya zata matsa kawai taji zata fad’i, da sauri yasa hannu a kugunta ya tarota. Nafi kam har ta runtse idanta kam, jin an riketa yasa ta bud’e ido a hankali, Habib ya sakar mata wani lalausan murmushi, sannan ya matso da fuskarsa yace ” Me yasa kika tsaya da maganar ki to? ” Yawu ta had’iya da karfi sannan ta d’an motsa baki tace ” Ya Habib d’an sakeni. ” Jin ta waske bata bashi amsa ba yasa ya d’agota tare da sake cewa ” Shikenan na hakura da gaisu…. ” Bata jira ya karasa ba tace ina kwana? ” Dariya ya d’anyi sannan yace ” Nafi kina burgeni na rasa me yasa. ” Kasa tai da kai dan itakam tasan wasa ne ace tana burge wani. Ashraf dake zaune a kujera duk yana kallan me sukeyi kasancewar kofar a bud’e Habib ya bata yaja wani karamin tsaki tare da girgiza kai yace ” in kun gama sai ku shigo, dan ni inada abinyi. ” Nafi ta kalli inda Ashraf yake haka kawai taji gabanta ya fad’i tare da tsananin takaicin ganin ta dayai. Habib ya matso da niyyar rike mata hannu da sauri ta b’oye hannun a baya kallanta yai fuska a sake sannan ya d’anyi gaba yace ” Ki shigo. ” Da sauri ta shige jikinta duk yai sanyi. Ashraf na zaune yana kallo ta karasa tare da zama a kasa, Habib ya kalleta yace ” zauna a kan kujera mana? ” Ashraf ya bugamai wani mugun kallo yace ” Mu sa’aninta ne? Kai meyasa kake kokarin zubar mana da mutunci agurin yara kanana? ” Nafi wacce ko alamar tashi dama batai ba ta d’ago ta kalleshi sai dai zuciyarta ta d’anji ba dadi. Ashraf ya d’auke idansa, Habib ma kasa magana yai, Shiru ne ya d’an biyo baya kafin Ashraf yace ” Nafisa! ” Gaba d’aya tun daga kan yatsar kafarta har zuwa kanta sai dataji wani abu ya wuce mata, d’agowa tai a hankali ta kalleshi. STORY CONTINUES BELOW Ashraf kam ko a jikinsa yace ” yau zuwa gobe zakuje da Little da kuma mumy xakuje siyayyar kayan makarantarki. ” Kallonsa tai cikin mamaki batasan sanda tace ” naam? ” Ya had’e fuska sosai yace ” bakiji me nace ba? ” Tace ” Naji kace makaranta. ” Yace ” eh, in kun gama siyayya da komai zuwa jibi zaki wuce makarantar kwana dake kazaure. ” Nafi kam idanunta ne suka ciciko, wani irin farin ciki ne wanda ita kanta batasan irinshi ba yake ratsata, Ashraf yace ” meye hakan? ” Hawayenta ta goge wanda suka zubo, ta girgiza kai tace ba komai. Habib cikin damuwa yace ” Bakyaso ne? ” Kai ta girgiza da sauri tace “a’a ba haka bane. ” Ashraf ya d’an kuraa mata ido kamar yanasan gano wani abun, idanunta tai saurin yin kasa dasu tace a hankali tace ” Yaya babana fa?” Jiyai ransa ya b’aci ya ce ” Bansan inda yake ba, kuma bana fata insani, sannan in har da haka kike tunanin yin karatun to gwarama karkije, dan ni na tsani mutum mai raunanniyar zuciya. ” ya mike yai ciki. Kallo ta bishi dashi zuciyarta tana dana sanin tambayar datai, sai dai duk yanda taso da daurewa ai dole ne tai rashin mahaifinta. A ranta ta maimaita Raunanniyar Zuciya? Me kenan? Kamar Habib yasan meke ranta yace ” karki damu da fadan Ashraf dan shi yawancin maganarsa haka take. ” Nafi tabi d’akinsa da kallo tanasan ta bashi hakuri ta kuma tambayeshi ciwon sa, daurewa tai ta kalli Habib tace ” Ya Habib meye raunanniyar zuciya? Ma dai san me zuciya take nufi” Dariya yai yace ” rauni fa? ” Tace ” na sani. ” Ya sake dariya yace ” to sai ki had’asu guri d’aya ki gani. ” Tace ” Rauni Zuciya? ” Wannan karan dariya sosai Habib yai yace ” lalai Nafi inkinje makaranta cikin mutane a hankali zaki fahimta. ” Tace to, sannan ta sake kallan d’akin Ashraf sai dai ba yanda zatai, mikewa tai zata fita, Habib yace ” aiki kikai ne? Naga kayanyi sun b’aci kamar daga kitchen kika fito. ” A’a kawai tace tai saurin fita. Tana gaba kad’an sai ga Aneesa wacce tasha kwalliya tana tafe kamar sarauniya. Idanunsu ne suka had’u, gaban Nafi ne ya fad’i bawai dan tsoro ba a’a sai dan ganin kyan datai, a cikin zuciyarta tace ” Dole Ya Ashraf yasoki. ” Tun datazo gidan bata taba ganin Aneesa ta d’au kwalliya irin haka ba, ba namiji ba ko mace ce ta wuce dole ne ta kalleta dan tayi kyau sosai, Aneesa wacce takura ma Nafi ido cikin tsananin takaici ta karaso. Kwalliya tai dan taje su shirya da Ashraf amma me take gani haka? A zuciye ta karaso tare da kallan Nafi cikin tsananin takaici tace me kike anan? ” Nafi ta kalleta sai dai ta kasa cewa komai, Aneesa ta sake kuluwa tace ” ke dan gidan ku ba magana nake miki ba? ” Nafi ta daure kawai jitai ta sami kanta da cewa” Ya Habib ne ya kirani. ” Aneesa wacce bata gamsu da zancen ba tace ” Nafi karkiga jiya nazo da niyyar dukanki ki d’auka wai ko kishi nake dake ko wani abun. ” Ta d’anyi dariyar kissa tace ” Tausayi kike bani, kinfi kowa sanin ni dake ba d’aya bane sannan ke da kanki zaki iya warewa kisan wa ya dace da Ashraf ko ince wa Ashraf yake so, dan haka ina baki shawara in ma da wani shirme ko yarinta akanki gwara tun wuri ki cireta dan kinsan wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa, ke ko masu aikin gidan nan sun fiki daraja. ” Ta bangaje ta tai gaba, jitai ranta yayi sanyi ta tuno maganar Umma datace ” ki nuna mata ita ba komai bace ta hakan ne inma da wani munafircin a ranta zai sa ta shiga hankalinta.”juyowa tai ta kalli Nafi tana nan a inda ta barta, ta sake dariya sannan tai gaba. Nafi kam sai juya kalamun take a ranta, tafi kowa sanin Ashraf yafi karfinta, ta kuma sani ko kata sun kare ba abinda zaiyi da ita sai dai meyasa takejin zuciyarta ba dadi? Wata zuciyar tace kema Nafi kina ganin mai mace kamar Aneesa me zaiyi dake? Jiki duk a rame? Gaki yar kauye wacce ake neman biyan bashi da ita? ” Da kyar ta karasa d’aki tai wanka sannan tasa abinci a gaba, da kyar takeci ta rasa me yasa batajin dadin abincin sam. Aneesa kam tana shiga taga Habib zaune a kan dinning yana cin abinci, tai murmushi tace ” Yaushe a gari d’an uwan Ango? ” Habib ya kalleta yace ” Amarya irin wannan kwalliyar kamar yauce ranar? Ko dai anzo seducing d’in d’an uwa nane? ” Aneesa ta d’anyi dariya har hakoranta suka fito ta d’an karkace kadan tace ” me? Kana tsoro ne? Ko kuwa kishi kake ba kada me ma?” Habib ya rike haba yace ” tab lalai d’an uwana yana cikin tashin hankali gwara muyi sauri mu kawoki kafin ki burkice mana d’an uwa.” Aneesa ta d’an fara tafiya cikin salo tare da cewa ” ah to wayace kukai bikin da nisa?” Habib ya bita da kallo yana murmushi. D’akin Ashraf ta murd’a, kai tsaye ta shiga, Ashraf wanda ke kokarin shiga wanka ya kalli kofar kansa tsaye ya d’auka ko Habib ne, ganin Aneesa yasa ya had’e fuska tamau, ta sakar nai wani murmushi tace ” Sorry Hubby ashe wanka zakai. ” Ya kalleta yace ” Aneesa bakisan ya ake sallama ba ko kwankwasa kofa ba? ” Ta shagwab’e tare da shiga ta zauna a bakin gado tace ” nida d’akin mijina? ” Ya girgiza kai cikin takaici yai hanyar toilet sannan ya tsaya ya kalleta tare da cewa ” nine mijin kuma banaji na bada sadaki bare a shafa fatiha, dan haka ki kiyaye shigomin d’aki kai tsaye.” yana kainan ya shige toilet. Aneesa ta turo baki cikin jin haushi sai dai ta kasa cewa komai sannan tana kunyar fita kar Habib ya mata dariya…… Tana nan a zaune jugum har ya fito daga wanka, daga bakin kofa ya kalleta fuskar nan a had’e tam yace” me kikeyi har yanzu? “+ Mikewa tai ta d’anyi rau da ido tace ” Haba Hubby na taya na ciwo kwalliya dan in birgeka zaka dinga wulakantani haka? Tunda kaga nazo ai kasan hakuri nazo in baka. ” Ashraf ya wani saki murmushin rainin hankali sannan ya mata wani kallo wanda ita da akawa ita kadai tasan me yake nufi yace ” Ko? ” Tace ” bangane ba? ” Ya d’an juya kai gefe yace ” ke kina tunanin har kinkai matsayin da zaki tozartani a gaban mutane sannan ki biyo ta baya kice zaki ban hakuri? ” Aneesa ta d’an canza fuska kad’an tace ” Amma Yaya kasan dai ko waye dole yaji haushi, ko bakasan na dinga kishin ka? ” Kallanta yai sannan yad’an girgiza kai na takaici hanyar waje ya nuna mata da yatsarsa yace ” yi nan. ” Ta kare lagub’e fuska, yace ” kinfi karfi? ” Juyawa tai a hankali tai waje tana fita yasama kofar makuli, tare da jan tsaki. Nan ya shafa maganinsa sannan ya shiga kokawar sa kaya, bayan yasa ma kwanciyarsa yai a kan gado. Itakam Aneesa tana fita Habib ya kalleta tare da guntse dariyar datake kokarin tahomai yace ” Badai fada kukai ba? ” Ta kalli Habib kamar zatai kuka sai kuma ta daure tace ” a’a kaya zai sa. ” Habib ya jinjina kai, zama tai a kan kujera shikuma ta mike yai waje, Aneesa ta dade a zaune tun tana irgaminti har ta dawo hour, ganin hour din Ashraf biyu a ciki gashi har bacci yana neman d’aukan ta yasa ta mike kamar ta kurma ihu. Abin haushi taje tana kwankwasa kofar Ashraf sai ga Habib ya shigo, yana ganinta baisan sanda dariya ta zo mai ba. Aneesa takalleshi cikin kuluwa tace ” Abokin Ango meye hakan? ” Habib ya had’e hannayensa biyu alamar ban hakuri yace ” Tuba nake Amarya amma naga kamar fada kukai da Angon.” Aneesa wani takaici ya kara kamata ta kalli kofar Ashraf sannan ta kalli Habib dake juya kai yana d’an dariya haushi yakamata kawai ta tsugunna a gun tasa kukan shagwab’a. Kuka take sosai Habib ganin haka ya kara komawa waje. Ashraf kam wanda kukan duk ya dameshi ya mike jiki a sanyaye ya bud’e kofar, Aneesa tana jin ya bud’e ta kara sautin kuka. Ashraf ya tako a hankali, ya tsugunna shima tare da sa hannu akan kafad’arta, kamar jira take dama ya tab’a ta kawai ta kankameshi tana kuka, Ashraf ya shiga kokarin zare jikinsa amma ta kankameshi tamau sai kuka take. Ganin bata da niyyar sakinshi yasa ya mike da karfi, Aneesa ta d’ago fuskarta wacce duk ta b’aci kaca kaca sakamakon kwalliyar datasha, Ashraf ya dafata yace ” Anie na fada miki ba sau d’aya ba kidaina kankameni haka.” Ta turo baki tace ” kai fa mijinane. ” Ashraf yace ” banzama ba tukunna, sai an d’aura mana tukunna, sau nawa ina sanar dake hakan? ” Aneesa ta kara share hawaye tace ” Yaya naji to zan daina amma d’an Allah kadaina wahalar da zuciyata. ” Mikewa yai batare da ya amsa ba ya bud’e kofar d’akinsa yace ” zo ki wanke fuskarki. ” STORY CONTINUES BELOW Ta turo baki tace ” bakasan kwalliyar? ” Kai ya girgiza alamar a’a yace ” ki shiga kya gani ” Ta mike zuciya ba dadi tai toilet. Tana shiga taga fuskarta a madubi kamar dodo, da sauri ta matso liquid soap ta shiga wanke wa tana yi tanajin haushin ganinta a haka da Ashraf yai. ¤¤¤¤¤¤ Da yamma bayan little ta dawo Mumy ta sasu a mota suka fita shopping, sunyi siyayyar kayan abincinta sannan aka sai uniforms, da house wear sannan suka wuce gun mai d’inki, nan suka bashi sannan suka amshi ragowar sababbin d’inkunenta, wannan kuma akan gobe za’a mata tunda uniform ne bawai style za ai ba. Nafi kam kana kallanta zakasan tana cikin farin ciki dan little ma sai tsokanarta takeyi. Sun gama komai kafin su nufi hanyar gida, Little ta kalli Nafi tace ” Nafi kinsan Ice cream?” Kallan mumy tai wacce tai kamar batajinsu sannan ta kalli Little ta girgiza mata kai alamar a’a. Little ta zunguro kusa da Mumy tace ” mumy asai mana Ice cream. ” Murmushi Mumy tai tace ” to. ” Nan suka karkata suka gangara 212, Little ta kama hannun Nafi suka shiga ciki, Nafi kam sai sadda kai kasa take, dama Mumy bata bisu ba tana zaune cikin mota sai dai tabi Nafi da kallo wacce ta ke kula da nutsuwarta tunda suka fito. Tana jinta sanda suna siyayya tana tab’a Little akan wai duk kayan na makaranta ne? Ai sunyi yawa ina zata kaisu? Tanaji sai dai Little tai dariya tace “ke dai me ya dameki? ” Mumy ta saki fuska tabi bayansu da kallo. Sukam suna shiga Little ta shiga zab’an abubuwan da zasu siya da yake duk sunayen da turanci take fada yasa Nafi kawai ta zura mata ido tanaji inama itama tasan ke ake cewa? Sunyi siyayya sosai kafin su fito, Nafi ta kalli Little tace ” ku kam wani irin kud’i gareku? Na ga sam bakwajin wahalar kashesu. ” Little ta d’an harareta tace ” Ke dai in an miki abu kawai kiyi godiya ki daina cewa ya miki yawa. ” Nafi bata amsa ba sai dai ta bita da kallo, nan suka koma mota. Mumy ta ja mota suka tafi, sun isa gida mumy tai parking zasu fito Nafi tace ” Mumy angode Allah ubangiji ya kara bud’i.” Murmushi Mumy tai sannan ta amsa da Amin. Zasu fita sai ga Habib da sauri ya karaso, shiya rike musu kofar motar, Little kam wani shaukin farin ciki ne ya ziyarci zuciyarta tace ” Ya Habib? ” Yakwantar da kansa a jikin kofar kad’an yace ” My Little Princess i really miss u” Little wacce zuciyarta ta kara yin haske ta juya fuska cikin shagwab’a tace ” bayan yaya ya daina damuwa dani? ” Habib ya kalli Nafi ba tare daya ba Little amsa ba yace ” Nafisa ba magana? ” Ina wuni ta fad’a cikin sanyin muryarta, Ya amsa tare da kallan cikin motar yace ” Mumy sannu. ” Mumy ta fito tare da cilamai makulli tace ” akwai kaya a boot ka tayasu kwasa zuwa b’angarensu. ” Ya chafe tare da yi mata salute yace ” yes maa. ” Mumy tai gaba, Little ya kalla yace ” Little Princess ba a huce bane? ” Tace ” Yaya Allah kuwa….. ” Ya katseta tare da had’e hannayensa biyu alamar ban hakuri, hakan yasa ta kasa karasawa, itakam Nafi dama tad’an matsa nesa da su kad’an, jitai Habib yace ” To gimbiya sai ki matso mu kwashi kayanki ko? ” Da mamaki ta juyo tace ” Ba dai nice Gimbiyar ba ko? ” Habib yai dariya yace ” me? Bakyasan sunan? ” Zatai magana Little tace ” Ni Princess ita Gimbiya? Ya Habib to meye marabarsu? ” Ya saki dariya yace ” Princess ba dai tana kishi ba? ” Da sauri tace ” ni dai bance ba. ” Nafi itakam ta karaso ta d’au ledoji manya manya ta nufi hanyar ciki, Habib da sauri ya sha gabanta yace ” ta ina mace yarinya kamarki zata iya d’aukan kayan nan? ” Nafi ta kalleshi tace ” zan iya, kai dai kaba Maryam hakuri. ” Ya kalli Little sannan ya juyo da niyyar yima Nafi magana sai dai can ya ganta tayi gaba, ya saki murmushi tare da shafar keyarsa sannan ya koma gun Little. A falo Nafi ta tadda Aneesa da kawarta a zaune suna hira, Nafi ta tsugunna ta gaidasu sannan ta nufi hanyar d’akinsu, Aneesa ganin manyan ledoji yasa tace ” ke zo nan.” Nafi ta juyo ta kalleta sai dai bata karasa ba, Aneesa tace ” ke munafuka ba dake nake ba? ” Nafi ta ajiye kayan a bakin kofa ta nufi gunta, cikin masifa Aneesa tace ” da ke da kayan nakesan ganinki. ” Nafi ta koma ta d’auko kayan ta karasa gunta, gyara zamanta tai sannan ta fizgi Ledar da karfinta ta shiga bincikewa, Nafi kam yau ta kulu, har ranta sai dataji haushin wannan abun, tana kallon Aneesa ta juye ledar ma gaba d’aya akan carpet dai dai nan Little ta shigo falon, mamaki ne ya kamata tace “me kenan? ” Habib ya karaso shima ya kalli wannam cin mutuncin, ga Nafi a gefe ta tsugunna, Aneesa ta bugama Little harara idanta ya rufe ko Habib bata gani ba tace ” Little wa aka saima kayan nan? ” Little ta kalleta rai b’ace tace ” Ya Neesa me ya dameki da wanda aka saiwa? ” Aneesa ranta ya b’aci ga kawarta a zaune a kusa da ita, tace ” mene?” Little a zuciye ta karaso tace ” Ya Neesa wai meke damunki ne? Taya zakiga kayan mutane kawai ki zubar a kasa? ” Kawar Aneesa ta kalli Little tace ” lalai Little yaushe kika zama mara kunya haka? Aneesa ba yayarki bace? Sannan yanzu da kika ganni anan tsara shirye shiryen da za’ai da bikinta da yayanki mukeyi ai ko bata zama matarsa ba ai yayarki ce bare an kusa. ” Little ta kalleta a kule sai dai ta kasa magana ta kalli Nafi cikin takaici ta wani takure kanta a kasa zatai magana kawai sukaji ance “Tsugunna ki kwashe kayan da kika zubar. ” Gaban Aneesa ne ya fad’i ta juyo a tsorace, ba ita ba Little da Nafi ma kofa suka kalla haka ma kawar. Ashraf ne a tsaya kana ganinsa kasan ba wasa a fuskarsa, Little ta kalli Habib wanda ke tsaye daga kofa, a ranta tace ” yaushe ya kira shi? ” Aneesa ta kalleshi tace ” Yaya…. ” Wani kallo ya mata wanda yasa ta had’iye maganar ta cikin tsawa wacce ta razana kowa dake falon yace ” Kowa ya fita.” Nafi kam jikinta rawa ya kauri dashi, bata tabajin yayi tsawa haka ba, Little ta kamata sukai waje a sukwane itama kawar Aneesa da sauri tai waje ta nufi d’akin Umman Aneesa. Ya rage daga Aneesa sai Ashraf a d’akin, ya kara kallanta yace ” ba dake nake ba? ” Idanunta na kansa kallan mamakin dizgata dayai take, ta daure tace ” Yaya ni zaka wulakanta akan Nafi? ” Shi baimasan a hannun Nafi aka anshi kayanba, shidai Habib yace yazo akwai matsala a b’angaren su Little, da ya iso shine yake cemai Mumy ta siyo kaya Aneesa ta zubar. Ashraf ya kara kallanta, idanunta suka ciciko tace ” Yaya kana san ka nunamin ka fifita Nafi akaina kenan ko me? ” Ashraf ya kalleta cikin tsananin takaici zaiyi magana kawai sai ga Asim da Umma sun shigo cikin masifa…….. Nafi wacce little ke janta akan su tafi b’angaren Mumy tana ganin Umma da Aslam sunyi b’angarensu a fusace yasa ta turje tare da kallan Little tace ” Maryam wannan abun duk laifinane, kina ganin abun nan yana neman ya zama babba? Sannan ni kuma in gudu?”+ Little ta tsaya itama tare da cewa ” Laifinki? Ta ina ya zama laifinki?” ” laifinane mana tunda dai a hununa aka amshi kayan.” Haushi ya kama Little ta rasa Nafi wace irin yarinya ce, ta kalleta tare da dafata tace ” Naji a kaddara laifinki ne mai zakiyi in kika koma?” ” Hakuri zan bada mana kina ganin su Umma sun tafi nasan kowa laifin yaya zai gani.” Ta karasa maganar cikin rawar murya. Little ta kalleta sai dai ta rasa me ma zata ce mata, gani tai Nafi ta fara tafiya nan ta bita tana mata magiya akan su tafi sai dai itakam gani take gwara taje kawai. A falo kuwa Ashraf ne ya had’e rai kamar zai dake Aneesa ita kuma tana tsaye kyam kusa da kaya, ta kalleshi tace ” Yaya nice fa?” Ya buga mata wani kallo yace ” kece wa? Ko dama a duniya akwai wanda ya isa inyayi ba daidai ba a kasa hukuntashi?” Daga bayansa yaji ance kwarai kuwa, Asim ne yai maganar ya sani shiyasa kuma bai juya ba, Asim ya karaso rai b’ace sannan ya sa hannunsa ta bayan Ashraf iya karfinsa da niyar kai mai duka, Umma tai saurin rike hannun tare da balamai hararra. Ashraf ya kalli Aneesa yace ” idan kika bari na irga uku acikin raina wlh sai kinyi dana sanin wannan ranar.” Umma tai charaf tace ” ai kuwa sai dai tayi dana sanin dan kaf duniya ba wanda ya isa ya sa ‘yata ta kwashi kayan wannan yar kauyen.” Ashraf bai kalli Umma ba haka kuma bai bata amsa ba sai Aneesa da yake kallo yace ” kin amince da abinda aka ce?” Aneesa ta goge kwallarta tace ” yaya me zakayi in na ki kwashewa? Badai cewa zakai ka fasa aurena akan wannan shirman ba?” Ashraf ya saki wani mugun murmushi yace ” me? Kina ganin bazan iya ba?” Kallan mamaki sukamai su duka ukun, Aneesa wacce duk ta gama rikicewa tace ” Ya Ashraf me kake fada haka?” Ya kalleta yace ” in kina tunanin bazan iya ba ki bar kayan nan har na karasa bakin kofa, ni kuma zan nuna miki magana d’aya nakeyi.” Nan ya juya Aneesa ko kara wata maganar batai ba ta shiga saurin kwashe kaya kamar zata kifa kansu, Ashraf kam ko a jikinsa ya wuce ta jikin Asim ba tare da ko kallan su yayi ba, bai kuma kara duba Aneesa ba dan yasan tabbas zata kwashe kayan nan. Ana kai kofa, Nafi wacce ke tsaye jikinta sai rawa yake ta kalleshi a tsorace, bai kulata ba yai wucewarsa, Little ta dafa Nafi tace ” Nafi jikinki rawa yake.” Juyowa Nafi tai cikin tsananin tsoro tace ” Maryam wani irin mutum ne yayanki? Da gaske sai ya raba auren nan a dalilin da baikai ya kawo ba?” Little tai shiru dan itama abin ya bata tsoro, Nafi ganin haka yasa ta girgiza kai tace ” Maryam yayanki na bani tsoro dan ko Baffa banajin tsoronsa kamar yanda nake jin na yayanki.” Little ta dafata tace ” yayana yaga rayuwa wanda itace ta maidashi haka, baya tausayin kowa ba kuma ya shakkar kowa, abu d’aya ya tsana kuka bayan wannan banaji akwai abinda ke tab’a mai rai.” Nafi tabi bayan inda Ashraf yabi da kallo, ace wacce zaka aura kuma kake so ita zaka dizga haka agaban iyayenta da yayanta? Kuma ya juya ya fita kamar ba abinda ya faru? Little ce ta katseta da cewa “Nafi ina zuwa.”ta juya da sauri. A falo kam Aneesa tana ganin fitarsa bayan ta gama kwashe kayan ta tsugunna agun tare da fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi, Umma ta karaso kusa da ita jikinta itama a sanyaye ta jawota jikinta. STORY CONTINUES BELOW Kuka sosai Aneesa takeyi, Asim ya kalli Umma cikin takaici yace ” Umma haka zamu zauna yaron nan yqna ci mana mutunci?” Umma ta kalli Aneesa tace ” da kinsani baki kwashe ba inga ta karyar iskanci.” Aneesa ta mike daga jikin Umma tace ” Umma kamar bakisan Ashraf ba? Kin manta abinda ya faru shekarun baya da suka wuce? Kina sane da ciwon danai tayi a lokacin dayace bazai aureni ba, ya kuma daina kulani.” Umma tai shiru, Aneesa cikin kuka tace” alokacin bansan ciwon kaina sosai ba, kina tunanin inya fasa aurena yanzu zan iya rayuwa?” Asim a kule yace ” Dalla yima mutane shiru, sai ki kasa rayuwa dan an rabaki da Ashraf?” Aneesa ta harareshi sannan ta mike cikin fushi tana kuka tace ” kana tunanin in Ashraf bai aureni ba zai barka a matsayin da kake ne? ” Asim yai shiru, Umma tace ” ya isa, taya za’ai ma muso auren ya rabu ba, kinsan dalili shima Asim d’in ya sani, mu tabbatar mun rufe maganar nan ma kafin Abbanku ya sani.” Nafi wacce ke tsaye duk taji me suke cewa tai shiru jikinta duk yai sanyi, ta fahimci wani abun amma bata gane wani abun ba. Jin alamun zasu fito yasa tai saurin lab’ewa, Umma har tazo kofa ta juya tare da kallan Aneesa tace ” karki kara yadda kuyi fada da Ashraf akan wannan kucakar yarinyar wacce riga ma bata fara zama mata ba bare….” Ta juya, Nafi ta kalli rigar jikinta cikin ranta tace ” bai fara zamamin ba?” Ashraf kam yana shiga d’aki ya d’au littafin dake kunshe da wasiyar mahaifinsa ya bud’e wani shafi da mahaifin yace ” Babban burina a rayuwa bai wuce na hada aure tsakanin d’ana da ‘yar Kanina ba.” Sannan a kasa aka sa” Ashraf ka taimakeni ka cigaba da kula da zumuncin nan ko bayan raina.” Kai ya dafa, a cikin ransa yace ” Abba meyasa kakesan wad’anda ba sanmu suke ba? Kasan yanda nakeji a raina in na tuna mahaifiyar Aneesa da tawa Mahaifiyar wai kishiyoyi ne?” Ya kwantar da kansa a jikin gado, a da bai d’auki wasiyyar nan da wahala ba amma yanzu ya gane tafi komai wahala a rayuwar duniya. ☆☆☆☆☆☆☆ A can garin kachako kuwa D’an litti yana kwance a wani kango duk kayansa sun fara yagewa sai ga wani babban mutum yazo wucewa, ganin mutum kwance a kango cikin rana yasa ya karasa inda yake, hannu yasa ya tab’ashi yace ” Bawan Allah me kake anan?” D’an Litti ya mike zaune a zabure, yace ” Wlh I am the one.” Kallansa mutumin yai sannan yai dariya yace ” me kayi kuma?” Ganin mutum yasa yasan ba mafarki yake ba, ya kalleshi baice komai ba, Mutumin yace ” Sunana Malam Kabiru, ina zaune akarshen layin can, kai fa dan naga kamar ba daga nan kake ba.” Nan D’an litti ya kwashe komai ya fadamai, wani gurin yai dariya wani gun ya tausaya mai, nan yace yazo su tafi gidansa inya tara wani d’an kudin sai ya tafi kano ya nemi Ashraf d’in. Sosai D’an litti yaji dadi ya kalleshi yace ” Amma ta ina zan tara kud’in?” Malam kabiru yai dariya yace ” bakace kana tuka babur ba? Sai muje in baka babur d’in yarona wanda yai tafiya ci rani sai ka d’an tara.” Murna sosai d’an litti ya shiga yi cikin tsananin murna nan suka tashi suka tafi….. ☆☆☆☆☆ An anso d’inkunan Nafi sannan Littl da kanta ta zauna ta dinga mata bayani akan yanda zatai amfani da kayayyakin, sun dad’e sosai a daren ranar suna hira dan gobe akesa ran tafiyar ta, murna kuwa agunsu Aneesa da sukaji ba’a magana. Sun nitsa cikin hira Nafi tace ” Maryam in na tafi kuma shi kenan ko?” Little ta kalleta cikin mamaki tace ” shikenan me?” A ranta tace ” kafin in dawo Ya Ashraf yayi aure mana.” A fili kuwa sai tace ” zamu dade wai bamu had’u ba.” Little tai dariya tare da gyara zama tace ” Nafi inza’ai bikin yaya inzo ni da Ya Habib mu d’aukeki?” Nafi ta kalleta cikin mamaki tace ” a’a nida na tafi karatu? Sannan shima in yayan yaji ai kinsan fada zaiyi.” Little ta tab’e baki tace ” shi da yaketa hidimar biki inama zai kula dake? Hmm ai ina cin burin bikin nan sosai wlh.” Nafi ta juya tare da gyara kwanciya tace” hmm.” Little kam ta zake sai zuba takeyi akan shirin biki, itakam Nafi a kwance kawai take sai eh kawai da take cewa dan itakam ta rasa me yasa batajin dadin hirar ta yanzu……

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *