WAYE ANGON CHAPTER 12 BY MARYAM JAFAR KADUNA

WAYE ANGON CHAPTER 12 BY MARYAM JAFAR KADUNA

 

 

yi farin ciki da aurena ba, bare ka samu nutsuwar da ango yake smau in ya yi aure.

Kaga da ni da kai zamu yi rayuwa cikin kunci da hakuri da juna tun da kuruciyarmu mu gagara moreta.

Amma idan kayi hakuri da ni sai Allah ya sauya

maka, ya baka wacce ta fini, wacce za ku yi rayuwa ta

farin ciki da ita, ni ma in auri wanda nake so in yi walwalata da nishadina da shi a kan mu kasance da juna

ba cikin farin ciki da walwala ba, mu rasa samun

nutsuwar da ma’aurata ke samu.

Auren tursasawa ba shi da dadi Imran, sai bacin rai da takaici.

.»° Ta saurara tana sauraron me zai ce.

Ya numfasa ya ce,

“Mabaruka kenan, maganarki

gaskiya ne tabbas! Amman abin da nake son ki sani.

wannan son da ki ka ga ina miki ba ni na sa ma kaina ba,

Allah ne ya sa min shi, da zan iya cire shi wallahi da tuni

ya dade da fita a raina, tun kan lokacin nan don na sami

sauki kema na barki ki huta

Ta katse shi cikin fada.

“Kaso hakanne, tun yaushe

za ka cire shi in ka sa wa ranka?”

Shi ma ya ce “To naji, ke me yasa ba ki cire tsanar

tawa ba ki ka sa son nawa in har ni zan iya cire sonki?”

Tayi shiru tana harararsa.

Ya ci gaba “Wannan ba shine abin da yasa na nace da

auranki ba, illa dalilina daya. Tabbas! Ina sonki amma ni

ma ta wani bangaren zai iya zama tursasawa daga

mahaifina kamar yanda mahaifiyarki ta tursasa ki.

Da zan fada miki yanda muka yi da shi me yiwuwa

da kin fahimce ni, amman akwai abu daya da zan miki,

Momy ita ta haife ki nasan za ta fahimce ki, kije ki same

ta ki fada mata ra’ayinki a kaina, ki ce mata nina turo ki.

Idan ta amine ta janye aurenmu to wallahi nayi miki

alkawarin na janye na hakura, gwanda na mutu da

sonki, nayi miki wannan alkawarin.

Ta marairaice kamar zata yi kuka ta ce,

“Wallahi na

gwada haka amman taqi yarda, nayi mata kuka na roketa,

na muna mata amman taqi fahimtata, tayi

rantsuwa sai na aureka, tunda naje ni kai sai ka gwada Ya kalleta ya yi murmushi ya ce,

“Ba zan iya ba

Mabaruka, hakan yana daga cikin alkawarin da nayi wa mahaifina, ba zan iya karyawa ba.

Ba juyin duniyar da bata yi da shi ba amman ya nace

a kan alqawarinsa, har biyu na dare suna abu daya, tayi

masa kuka ta durkusa gabansa tana rokonsa.

Hankalinsa ya tashi, ya tada ta shi ma ya bata hakuri

ba zai iya ba, amman taje ta gayawa Allah shi ma zai yi

addu’ar ya zaba musu abin da zai fi zama alkairi kafin

jibi.

Mikewa tayi a fusace tà harare shi son ranta, sannan

ta wuce. Har taje bakin kofa ta juyo tana kallonsa.

Ta ce,

“Shawarar da zan ba ka, kada ka yarda a hada

wannan partyn da za ku yi, don ba zan je ba wallahi. Idan

kuma a ka tursasa ni naje, na rantse za ka sha kunya

gaban mutanenka da abokanka, sai kayi kuka wallahi!”

Daga haka ta doka masa kofa ta fice a fusace.

Yaja ajiyar zuciya ya ce,

“Na bar maka komai a

hannunka Ya Allah, ka kawo min agaji da mafita,

” Daga haka ya mike ya shiga bandaki ya dauro alwala ya zo ya

shimfida darduma yana kai kukansa ga Allah.

IMRAN KENAN.

Yayin da ita kuma ta koma dakinta tana tafe tana

bala’i, “Wallahi za ka gani, ba ka san wacece ni ba, za ka

shamamaki in halinka kafiya.

Bacci dai ba ta yi ba a ranar, haka ta kwana tana juye-

juye tana doka tsaki, tsanarsa tana Kara ruruwa a ranta

Yayin da shi tunda ya gayawa Allah ya sami

nutsuwa, nan da nan bacci ya kama idonsa, a nan ya

bingire har asuba.

Washegari ana gobe daurin aure a gidan su Sulaiman

tunda safe karfe bakwai ya fito ya shiga dakin Inna

(mahaifiyarsa) tana zaune tsakiyar daki tana daura suga

a leda na sayarwarta.

Ya tsugunna yana gaisheta, ta bishi da kallo ta ce,

“Sulaimanu ina za ka haka tun da safe?”

Ya ce yana mikewa,

“Wallahi ina da uzururruka yau

kasancewar gobe daurin aure, shine nake ta sauri naje

na aiwatar kar ranar ta min kadan.

“Ta tabe baki ta ce, “Um, sai ka ce kanka aka fara aure,

sai rawar jiki ka ke na rasa dalilin rawar kafar nan da ka

ke wa yarinyar nan, kai ba auren farko ba bare ka ce ba

ka taba yi ba.

Ya yi murmushi yana sosa keya a kagarce yake ya

fice kar ta hana shi fita, duk yanda yake kokarin boye

dokinsa sai da ta gano.

Tace,

“Ko kokon ba za ka tsaya ka sha ba? Ga shi can

Sameera ta dama.

» Ya ce,

“Inna sauri fa nake kin ta

katse shi “Yau naji ikon Allah! Yau aure zai hanaka shan

koko Sulaimanu? Wai wannan wace yarinya ce za ka auro mana?”

Ya yi shiru tamkar saman kaya yake, a tsorace ta ce,

“To zauna sai ka sha sannan ka tafi, so ka ke kaje ka

fadi?” Ya sani ba shi da ikon cewa uffan a kan abin da ta zartar.

Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *