WAYE ANGON CHAPTER 14 BY MARYAM JAFAR KADUNA

WAYE ANGON CHAPTER 14 BY MARYAM JAFAR KADUNA

 

 

Lokacin da taji shigowar text a wayarta ta jawo ta duba ta karanta, ta ce “Allah ya isa, mugu!” Idanuntasuka ciko da kwalla.

Suka juyo suna kallonta Rafia, ta ce “Menene?

Ke da wa?” Hararar Rafiartayi. Suka gaji suka kyaleta. Karfe hudu tuni an gama gyarata, tayi wani irin kyau. Daman ga ta fara ta kara rikidewa kamar ba ita ba,

jikinta har santsi yake, ga lallan da aka zuba mata ya yi

wa farar Fafarta kyau a kai mata kwalliya.

A ka bata kayan da Imran din ya aiko mata bayan

fitarsa, wanda zata sa suyi anko a nan aka dinga rigima da ita tace wallahi ba za ta sa ba, har Momy tazo. Ta ce,

‘”Baza ki sa kayan ba saboda me?” Kai tsaye tace;Ba zan je ba ne.”

ta ce,Saboda wane dalilin

kenan?” ta ce,Don ba na sonsa, ba na son abin da zai

hada ni da shi.”

Ran Momy ya baci, ta fidda hannu ta mareta ta ci gaba da fada.

“Uban wa ya haife ki? Ke ki ka haifi kanki da ki ke son ranki? Wa yake da alhalin zaba miki miji? Cutarki a kai aka hada ki da dan iska bare ki min rashin kunya? Kin fi ni hankali ne?” Ta saurara. Yayin da ita kuma take cizgar kuka kamar ranta zai

fita. Momy ta ci gaba.

“To don ubanki kar ki sa kar kuma kije, idan naji labarin kinje sai na taka miki wuya, kici gaba da mishi rashin kunya.

.” Daga haka ta fice mutane na ta ba ta

hakuri. Ita kuma ta ci gaba da kuka kamar ba za ta daina ba.

Rafi’atu ita ke rarrashinta, amman taqi sauraron kowa

bare ta bari sai don kanta, idanunta suka yi ja sun kumbura sannan ta bari, ciwon kai ya dameta.Rafi’atu ta ce,

“Kinga ran Momy ya baci har ta kai ga

taba ki, kin fiye kafiya Mabaruka, ki mata abin da take so zuwa party ba zuwa gidan Imran ba ne, kije awa daya ya yi yawa ki dawo sai ki samu sauki daga fushi.

Don wallahi tayi fushi sosai, ga mutane suna taruwa ana kallon kuna sa’insa da mahaifiyarki kina gaya mata

magana son ranki, wanda ba tarbiyya ba ce sai a tafi anaYi da ke.

Kiyi hakuri don Allah Mabaruka kar ki bata kunya,

kar a. daura miki aure tana fushi da ke, kiyi kokari ku rabu lafiya tana sa miki albarka.

Ta ci gaba da share mata hawayen, da kanta ta dauko

kayan tasa tana yi tana turo baki a ka sake mata kwalliya.

Masha Allah kowa yake cewa, tayi kyau fiye da

tunanin mai tunani, tamkar ba ita ba, kayan sun mata cas! Kamar an gwadata.

Less ne hadin fari da pink riga fara sikyat pink sai gwaggwaro pink tayi cas! Sai walainiya take cikinsu an

zubo da gashin gefe guda ga sarka wacce ta dace da

kayan, agogo zuwa ‘yan hannu.

Aka dinga daukarta hoto duk da ba fara’a a fuskar sai

zumbura baki da harare-harare, ji take kamar tasa qaya

jikinta saboda amfani da tayi da kayan makiyinta.

Tasan kudinshi yasa ya siyo tabbas hannunsa sun taba kayan. Zuciyarta ta dinga tashi ta dinga yatsine-

yatsine tana tara miyau.

Abin mamaki kawayansu suka ga suna ta tururuwar

zuwa sun cika dakinta kowaccensu tasha kwalliya,

akwai masu shirin kwana ma kowa in tazo da tsegumi

wai a ce ba a gayyace ta ba.

Rafiar ke cewa da ba za a yi komai ba suma sai yau

suka sani, haka dai kawaye suka yi dandazo, wasu har

kan gado.

Kowa sai da suka yi hoto da ita daga wayoyinsu, still

dai fuskarta ba walwala. Sai suke tsokanarta ta fara

kukan aure ne?

Ba a sami tafiya ba sai bayan sallar Magriba, sannan

a ka zo aka dinga daukar-kawaye da wasu iyayen zuwa

tsararren hotel din da a ka tsara aka yi kwalliya da kalar

kayan ango da amarya.

Duhu ya fara sanda za a dauke ta aka tsayar da motar

gabanta har wani walainiya motar take da ganinta

sabuwa ce dal. Aka ce ta shiga, to da duhu ba ta san akwai wani ciki

ba, da shigarta ta ji ta ta fada jikin wani abu mai laushi,

zata yi ihu-ya yi saurin sa hannu ya do de mata baki, dole

tayi shiru ta kasa kwatar kanta.

Ya kunna hasken wayarshi ta haske mishi fuska,

kawai taga Imran ne. Ta fiddo idanu tana kallonsa cikin

tsananin haushi da takaici, ta ci gaba da harararsa.

Yayin da shi yake dariya ya yi kyau cikin irin

kayanta, kamshinsa yana dokar mata hanci, ta yunkura

zata kwace kanta ya riketa gam!

Ta harare shi ta ce, “Sake ni.

.” Ya ki, ta kakalo miyau

(yaw) ta to fa masa a fuska, tare da cewa “Allah ya isa.”

_Ba shiri ya sake ta, yasa hannu ya shafo miyan. Ya yi

murmushi ya kalleta da take harararsa ya ce,

“See.”

Kawai taga ya lashe shi ya kara gogo wani ya lashe shi. Sannan ya ciro handkchief daga aljihunsa ya goge

fuskarsa. Yasa a hancinsa ya shake shi har da lumshe idanuwa. Ya bude yana kallonta ita ma duk tana kallonsa.

HMmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *