WAYE ANGON CHAPTER 15 BY MARYAM JAFAR KADUNA

WAYE ANGON CHAPTER 15 BY MARYAM JAFAR KADUNA

 

Ya ce, “I will keep it, ba zan taba wanke shi ba nayi miki alkawari, don in dinga shakar kamshinsa ina jin dadi thanks

.” Ya maida aljihu. Ta kauda kanta tare da jan

tsaki Rafa ta shiga gaba

direban daya daga cikin

abokansa yaja motar suka yi gaba.

Ta koma jikin kofa ta rabe, bata son jikinsa ya hadu da nata, gefe kuma tana jin wani. takaicin yanda jikinsu

ya gogu har ya taba ta, ta ci gaba da yin Allah ya isa a ranta har suka isa.

Suka fiffito, suka tsaya aka sa kawayanta gaba don suyi mata rakiya zuwa wajen zamansu, wasu kuma a

bayansu aka saka su tsakiya ita da shi.

Sunyi kyau matuka, in ka gansu zaka ce wallahi babu masoyan da suka dace da juna irinsu, abin ya burge

mutane sosai, aka ci gaba da daukar su hotuna zuwa bidiyo.

Aka ce su kamo hannun juna su shigo hall din. Ta juyo ta harare shi ta ce,

“Wallahi ka kuskura ka taba ni sai ranka ya baci.” Ya yi murmushi ya ce,

“Ni ma ba zan fara ba

Bayan sun zazzauna aka fara abin da ya tara su. Abubuwa sun yi kyau matuka, kowa yana yabawa, duk

da ita amaryar tana yin nesa-nesa da angon.

Kamshin turaransu daddada mai tsada dan waje, shi ya zamar mata kamar tana shakar Kwan da kaza ta fara kwancinsa ya fashe, haka take ji ta koma tana dode

hanci har zuwa lokacin fuskarta babu annuri.

Wasu sun fahimci wani abu, yayin da wasu ba su lura ba. Amman da mamaki amarya ranar partynta bata fara’a sai gumtse-gumtse da ‘yan harare-harare.

Idan abokansa sun zo suna gaisheta sai taja tsaki ta kauda kanta, ba wanda take amsawa. Wannan shi ne kadai abin da tayi ya Bata masa rai, amman hakuri irin nasa sai ya share kawai. Jikin abokansa ya yi sanyi, duk sun fahimci wani abu game da amaryar tasa.

Lokacin da suka dawo ana tsayawa zata fice ya yi saurin tsayar da ita ya ce,

“Ba za ki min sallama ba?” Harararsa ta yi kawai ta fice tana cewa, Don Allah ka

sakar min mara nayi fitsari, na dai yi abin da ka ke so ko, to ka Kyale ni.

.” Ta fice tare da turo kofar,

Ganin yanda ta fito ne yasa Rafi ‘atu ta biyo ta.Da shigarta ta fara yakice kayan tana wurgarwa,Tir! Da kayannan, ba zan iya ci gaba da zama da ku jikina ba.Rafi’ar ta shigo ta tsaya tana kallonta, daga ita sai

under wear tayi sama da shi, ta ce

«Wannan wane irin hauka ki ke? Ai suma na jikinki din nashi ne sai ki maida

hankali ki cire su.Kan ta gama rufe baki ta yayumi tawul ta wuce bayi

tana cewa “Har wanka sai nayi don na tsarkake jikina daga kayanshi.” Ta banko kofar.

Ta zaune bakin gado tana cewa Allah ya shirya ki Mabaruka. Ta canja kaya da riga da zani ta kawo hijab tasa, Rafi’ar ta bi ta da kallo ta ce “Ba ki sallah bane?”

Tace,Tafiya zamu yi.

.”‘Ta wuce tana duba drower tace

“‘Tafiya! ina zamu?”

Ta ce, “Gidan Babanmu,

“° Ta ce “Ke ba inda za ni yanzu kin san karfe nawa?” ta ce

lokacin da take dagowa.

“Na sani mana, ina son ganin Babanmu yau dinnan

ba sai gobe ba

Duk nacin Rafi’a sai da ta jata suka tafi.

Baban ya dinga yi mata fada a kan me za ta bar gida

daidai bikinta, ta marairaice fuska ta ce;

“Kun sa ni a

tsaka Baba, kai ka ce kaza ita ma can ta ce kaza, wai ya

kuke so nayi??

Nan anje an yi jere an karbi sadaki, ita ma can ta karba. Wai ba kwa tunanin ya abin nan zai kasance fisabilillah, kar fa ku jawa zuri’arku abin kunya. Ta ya ya

za a daura min aure da maza biyu Baba?

Ya ce,

“Ke ban san maganar banza, ni dai ni ne

ubanki, to don haka ban san wani miji naki ba sai wanda

aka ba ni sadakinki, ban taba ganin inda mace ta daura

Wa”yarta aure ba sai mahaukaciyar uwarki, ko ta daura a iskane don ba waliyyinki.

Don haka Sulaiman shine mijinki na halaliya, ki bar zancan Innarki, aurenta ba aure bane.?” Ta ce,

Amman Baba, Baba Haruna shine wanda ta

wakilta kuma kaninka ne uba daya uwa daya. Ko a Musulunci ya daura min aure, aure ya dauru sadakina tuni yana hannunsa

Ya dubeta da kyau ya yi shiru, sannan ya ce,

“Za mu riga daura namu kafin nasu, kije kawai ki kwantar da hankalinki ba ki da miji sai Sulaiman Sam bata nutsu ba, jiki a sanyaye ta wuce cikin gida

suka karasa ita da Rafia, sai da taji daman ba ta zo ba

saboda cinkoso in da za su kwanta, babu wasu ma sai a

zaure za su kwana an cika dakuna biyun daman a

kuntace suke ba su da girma, haka nan an cika tsakar

gida yara da manya, gidan har wani huci yake fitarwa.

Ta tuno dakinta na gidan Momy za a hade dakunan

da kucicin tsakar gidan wanda mutum bakwai ba za su

kwanta ba, a hada da zauran shine girman dakinta, ga

toilet. ciki ga iska mai dadin kamshi na fesowa daga na’ura.

Ga kuma nau’ikan abincin da sai ta zaba taci. Ta dafe kai ta dubi Rafia ta ce,

“Da na sani ban zo ba, gurin

HMmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *