WAYE ANGON CHAPTER 17 BY MARYAM JAFAR KADUNA
Wacce Inna? Meye matsalarta, duk ku min afuwa zaku ji nan gaba kadan.
Bangaren Imran kuwa Ango, tun safe yake tare da abokansa su shiga nan su fita, yayin da wasu ‘yan uwansa suka zo daga kasar Saudiyya, wasu kuma daga
England. Har ya shiga wanka wayarsa ta dinga kuka, ya share ya ci gaba, da wankansa, ganin kiran ya yi yawa ne yasa ya fito jikinsa da kumfa, ya dauki wayar.
‘My little Sharifat’ ya gani, ba shiri ya kai kunne yana dariya.
*Oh sorry my dear, ina wanka ne fa. Yanzu haka akwai kumfa jikina.Daga can ta 6ata rai cikin shagwabar da ta saba yi mishi ta ce, *
“Ni ban yarda ba tun
yaushe na sauka ina nan airport amman ka share ni ba ka murna da zuwana ko?”
Ya yi dariya har taji sautinta me dadì ta lumshe
idanuwa saboda jin dadin kasancewa tare da shi. Ya ce,Na miki alkawari minti goma ba zan kara ba zan zo na dauke ki.”
Tayi dariya Kada ka damu ka
shirya a nutse yau rana ce mai girma da muhimmanci gare ka, ba a bukatar gaggawarka. Kayi kwalliya mai kyau wacce zata rikita mutane, don ranarka ce kayi kwalliyar da baka taba yi ba, zan jira
ka har lokacin da zaka zo.”Ya ce
“Thank my dear, I miss youuu!”Tayi dariya
daga can ta ce,Me too my dear, I love you.
.” Ta sakar masa kiss. Shi ma ya mayar mata;
“Am coming bye!” suka
kashe wayar, wanke kumfar kawai ya yi ya zura jallabiya jikinsa har rawa yake ya dauki keyn motarsa ya fice zuwa airport.
Da gudu ta taho da ta hango shi, shi ma cikin doki ya nufota da zuwa ta fada jikinsa. Shi ma ya rungumeta tare da yi mata kiss ya dagota yana farin ciki, ya ce “You are welcome.
“‘ Tayi dariya bakinta ya kasa rufuwa,
Suka wuce yaja ‘yar jakarta zuwa mota, suna tafe suna hirarsu mai dadì na yaushe gamo da tsananin kewar junansu har suka iso gida.
Da gudu ta fito daga motar tayi ciki tana Kwalawa Momy kira.
“Momy! Momy!!” Ita ma daga can ta jiyo muryarta ta fito cike da murnar ganinta, tana zuwa ta fada jikinta tana cewa,
“Nayi missing naki Momy. Tayi dariya ta ce,
“Ita ma Momynki tayi missing
dinki Tana rawar jiki take cewa “Ina Anti Amarya matar yayana?”Ta ce,Ba ta nan kuwa tana gidan Babanta.Tayi sukut tare da cewa “Kai Momy, me yasa ba ki fada mata zan zo ba?”Ta ce, “Kiyi hakuri yanzu sai Yayanki ya kai ki can ba abin damuwa bane.Suka zauna tana cewa,Momy ya hidimar duk kin
fadama mutane ko?” Ta ce, “Ke dai bari Sharifa, sai a hankali. Hidima ba abu na wasa ba ne. Ta ce,Ayya Momy, sorry za ki warware big bro ya wahalar mana da ke.Daddyna fa?”
Ta ce,Yana hanya, yanzu zai sauka.
“‘ Ta ce, Daga ina?”Ta ce,America.
Ta ce,Oh Daddy dai tafiye-tafiye yake ana bikin big bro ma?”To ya za a yi, shi ma bai so ba dole ce tasa yaje din.”In ji Momy. Sharifat tace, Allah Sarki Daddy, Allah saukeka kalafiya.Tun karfe daya da rabi ‘yan daurin aure suka fara taruwa ta kowane Bangare, gidan Baba Haruna makil da Jama’a, hatta angwaye sun zo.Turawa da Larabawa da ‘yan Najeriya waje babu masaka tsinke, Maroka sai kewaye-kewaye suke da Mabusa, suna ta kara yayada “Za a daura auren Imrana Umar tare da Amaryarsa Mabaruka Yusufa, a kan
Sadaki Naira dubu dari lakadan.”Yan cikin Mabarukar suka juya, zufa ta karyo mata
tamkar an watsa mata bokiti na ruwa, jikinta ya hau rawa. Ta rike Rafia gam tana mata wani tsorataccen kallo.
Ta Ce,Na shiga uku! Rafia za a daura ba da
Sulaiman dina ba, ya haka? Me yasa za a riga daura wannan auren? Biyu saura fa yanzu?”
Rafiar ta kasa cewa komai, hankalinta ita ma ya kada matuka.
Ganin taruwar mutanen dandazo guda, duk an
halarta ba wanda ake jira sai kawai aka bada sanarwar aN daura kawai tunda kowa yazo, saboda haka aka fara addu’a. Runtumawa tayi a guje zata fice, Rafiatu da sauran
kawayenta suka rukota, cewa take
“Na shiga uku! Na shiga uku!! Za a daura za su daura min aure da
makiyina, ku bar ni naje na hana su kar suyi.”
Ta dinga fizge-fizge kamar sabuwar hauka. Inta kwace ta bige wannan sai wannan ya rikota, duk ta bi
birkice, gashi ya tashi buzuzu ta dinga ihu kamar zata shide.
Baba yana Masallaci sallar azahar, yayin da Jama’ar Sulaiman sun fara taruwa ango yana kan hanya da waliyyansa.
Abu kamar wasa Limamai suka daure Mabaruka a