WAYE ANGON CHAPTER 16 BY MARYAM JAFAR KADUNA

WAYE ANGON CHAPTER 16 BY MARYAM JAFAR KADUNA

 

kwana ma ba mu da shi alhalin ga dakina can ba kowa cikinsa.” Harararta tayi ta ce,

“Ba abin da zan ce sai, Allah ya kara,

Baba Haruna da Baba Hamza duk kannan Babanta

ne, gidansu a jere suke, Baba Haruna shine madaurin aurenta bangaren Momynta.

Baba Hamza kuma shine madaurin aurenta

Bangaren Babanta. Don haka taja hannun Rafi’atu zuwa gidan Baba Hamza.

Shi ma dai gidan akwai jama’a ‘yan biki, amman duk da haka ba su rasan gurin kwana ba, sauro da zafi ya hanata bacci, duk da ba wai bata jinsa ba ne a’a na yau ya

linka na kullum.

RANAR DAURIN AURE

Tun da safe Momy ta kira ta ta ce “Kina ina ne?” Tace,

“Ina nan gidan Baba Hamza.

‘”‘Ta ce,Ok, to ki zauna

a nan kar kije ko’ina, da an aura za a dauke ki, kin ji na gaya miki ko?” Ta turo baki can ciki ta ce “Eh” Ta Ce,In ji kin bar

gidan kuma.’.” Ta kashe wayar.

Idanunta suka cicciko da kwalla, ta dubi Rafia ta ce Na shiga uku, da gaske da Imran za a daura min aure,ba fa na sonshi wallahi ba na sonshi. Ina jin daci a zuciyata.

Rasame zata ce tayi, sai dai kallonta kurum da take. Baba yasa aka kirata, ya bita da kallo “Ina ki ka kwana ne?”Ta ce,Gidan Baba Hamza.” Ya ce,Da kyau, to ki koma can ki zauna kada kiyi nisa daga nan.

Tace, “To.” Kawai. Tayi wanka da kwalliya ta kawo kayanta ta sa wanda da kanta ta dinka su don fitar biki, tayi kyau sosai, sunanta na amarya ya fito.

A nan suka yi zamansu suna cike da zullumi, yayin da gabanta ke faman dukan tara-tara a kagarce take ranar nan tayi ta wuce, damuwarta ma ta wuce tasan

matsayinta.Ranar tayi mata tsawo matuka, ko ya taji motsi sai gabanta ya yanke ya fadi shin wanene ANGON?

*****

Bangären Sulaiman kamar kullum, bayan ya gama shan kokonsa na ka’ida da dumamen tuwon sama-sama, ya yi bankwana da Inna ta ce,Ho! Sulaimanu kai dai da

rawar jiki ka ke, na rantse in ba ka rage yawan

zumudinnan ba yau ba in da zakaje.”

Ya tsorata ainun, ya ce, “Na bari, na bari Inna.

Tace, Ka ci gaba ma.Ya tsugunna gabanta yana jiran umarninta ya tafi. Kamar kan Kaya yake jinsa. Sai can ta ce,

“Tashi ka tafi.” Ya rankwafa “Godiya

nake Inna, Allah bar girma.Bata ce amin ba ya wuce.Dakin Nafisa matarsa ya shiga, tana kwance hannunta rike da waya ya shigo, tabi shi da kallo tana murmushi ta ce

“‘ Ango-ango kai ne har yanzu ba ka fita

ba, na sha ma ka dade da tafiya.”

Ya ce, “Ina fa na tafi, Inna ta rike ni.

” Tace, To kayi ka wuce kar ta jiyo ka nan, wallahi na kagara kanwar nan tazo.”

Ya dube ta tsaf ya ce, “Wai ke ba kya ma ko kishin nan irin na sauran mata ki tada hankalinki sai nayi ta

lallashi amman ke kike ba da kwarin gwiwa.

Tayi murmushi ta ce, “Yaya kenan, in kaga abin da ya fito da Bera daga rami ya fada wuta ya fi wutar zafi,

don haka ina sonka wallahi sosai, amma yin auranka zai sani farin ciki.

Wani Bangaren ‘yar uwa za a kawo min wacce zamu

hadu mu share hawayen juna, don haka ina murna, Ya ce,

“Da tsiyar da za ku shirya min kenan, kin

sanni kin san waye ni, ki taka sannu

Tayi dariya ta ce,

“Sosai ni na sani, Allah dai ya bamu zaman lafiya, ya kawo ta lafiya.” Ya ce, “Amin yar

Nafisata.” Suka yi dariya.

Sameera tazo wucewa taji dariyarsu ta window, da gudu ta shiga dakin Inna har tana harba takalma, sai daita ganta gabanta.

Tace,Sameera a hankali kike wa ya koro ki?” Tana haki ta ce Kina nan sake da baki ya ce miki ya tafi, to ga shi can akin matarsa ina jiyo ‘yan dararrakinsu,Ai kafin ta karasa ta mike har zani na faduwa ta fice tana cewa,

“Dauko min bakin wuta ki gani.” Da gudu ta

dauko ta mika mata.Sai dai kawai suka ganta gabansu, ba jira ta ci gaba

da zuba mishi, ba shiri ya fice ta ci gaba da bala’i.Niza ka rainawa wayau, ka ce ka tafi ashe nan ka

lababo don ka raina ni, me ka ke a nan din?”

• Ina! Tuni ya dafe keya, ta dubi Nafeesar tace,

“Kekuma za ki sani munafuka, kin san dadin miji, kin murkuso shi daki. Sai na karya miki Kafa.Ta wuce tana kumfar baki, ta bar dakin.

In da sabo ta saba, ta yi murmushi iya fuska tace,Lokacinki ya yi za a kawo wacce zata yi maganinki,insha’Allahu za ki gani.” Ta koma tayi kwanciyarta abinta, hankalinta kwance.

Shin wai waye ma Sulaiman?

HMmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *